Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a gidan har Aneesa tai shekara biyar Baffa yazo zai karbe ta dan kyan ya mace ta tashi akulan mahaifi amma Ammi tace bazata bayar ba, babu yanda basuyi da ita ba taki basu ko ranan nan maganan dayazo mata kenan zai tafi da Aneesa amma taki yarda harda kukan ta wai mesa sukeson rabata da yarta.







Addu'a yagama tofama Aneesan dake bacci ya juyo ya kalli Ammi yace "ai yanzu hankalin ki ya kwanta ko Maman Fateema? Yarinya babu wuyan duniya dabaki bata, yau tana kasuwa, gobe tana gidan chan yin lalle, wanchan garin yin lalle, ketai aiki takawo miki kudi, kaganta tana shagon chan tana shagon nan, babu kalan Iskan duniyan nan da yarinyar nan bata shaka, ba baki barin yarinya tahuta ya za'ayi bazatai rashin lafiya be eh? An gayamiki ita injin ce?" da sauri Kawu Sani yace "ya isa Yaya yanzu ba lokacin fada bane muna asibiti" cikin fushi Baffa yace "sai anyi fadan, ka barni nafada mata gaskiya tazaci tsoronta akeji, ni uban yarinyar nanne" ya nuna Aneesa dake kwance kan gado yace "ni mahaifin tane, duk duniyan nan a yanzu babu wanda keda iko da ita kaman ni, koko idan aka barki da ita zaki iya aurar da ita ne iyye?" ya tambayi Ammi cikin fushi, yace "tabani yarinya natafi da ita kaduna ta shiga cikin yan uwanta su Rukkaya, da Asiya, da Maimunatu amma taki koko ance miki idan natafi da Aneesan cutar da ita zan dinga yi ne kokina ganin zan zauna nabude ido ina gani ana cutar da Aneesa agida nai shiru ne? Ballema nasan inhar ina raye babu wanda ya isa ya cutar da ita" dan shiru yayi yana kallon Ammi data saukar da kanta kasa yace "wlh kawai banson na tauye miki hakki ne, amma inhar baki shirya kula da yarinyar nan da hannu bibbiyu ba karbanta zanyi kome zai faru yafaru kina jina" dan murmushi Ammi tayi aranta tace "maza kenan su kullum gani suke baka kula da yara da kyau" kujera Baffan yaja yazauna shikuma Kawu Sani yazauna abakin gadon, dago kai Ammi tayi ta kallesu dan murmushi tayi koba komi Baffa tsoho ne kuma yayan baban yarta ce dole tabashi hakkin shi tasan ya isa da ita bawai bai isa bane kawai bataso ya karbe mata abu daya datake gani taji dadi ne aduniya, ahankali tace "kayakuri Baffa, kuyakuri dan Allah, zan kara kiyayewa" shiru yayi baice mata komiba ahankali tace "akwai abinci Baffa nazuba muku" girgiza kai yayi tareda saukar da ajiyan zuciya yace "kibari muyi magriba tukunna, inane ofishin likitan muje maganshi musan nawa zamu biya?" "kana fita ka mike gun zakaga ofishin" kallon sani Baffa yayi yace "kaimuje sabida kome aka rubuta ka karantomin naji" tashi yayi suka wuce suka fita koda sukaje wajen likita cemusu yayi wanda yakawo su jiya asibitin yabiya kudin komi addu'a suka dingamai su Baffa, Dr yace karma suji komi anjima zaizo zasu ganshi saisumai godiya atare duk suka wuce masallaci danyin sallan magriba.






Shigowa sukayi dakin harda likita har lokacin bacci take, Baffa yace "likita wanan baccin baccin lafiya ne daiko" dan murmushi Dr yayi yana zuba wani allura a drip din yace "eh na lafiya ne, wanan ruwan da ake karama ta shike sata wanan baccin shizai sa magun gunan subi jikinta" "to masha Allah" bude kofan da akayi yasa daukan su harda Ammi duk suka juyo suna kallon kofan, Dady ne sanye da manyan kayan dake jikinshi tunna safe sai bodyguard dinshi daya dake biye da shi yariko manya manyan ledoji bin kowa na dakin Dady yay da kallo kafin yakara so ya babbasu hannu suka gaggaisa ya kalli Ammi dake gaban gadon yace "yamai jiki bacci takene" gyadamai kai Ammi tayi ta kalli su Baffa tace "Baffa kutaya mu godiya shiya kawomu asibiti shiya taimaka mana" ta kalli Dady tace "Alhaji ga kawun nin Aneesa daga kaduna suka zo yau" kafin ma Dady yay magana Baffa yakara bashi hannu suka gaisa yace "angode, angode, angode, munji duk abinda kamana daga bakin likita, ubangiji Allah yasaka da alkairi bamu da abin biyanka saidai muna rokon Allahu Subhanahu Wata'ala ya sakamaka da alkhairi" murmushi Dady yayi yace "kudena godemin dan Allah inda ace d'ana baida lafiya koyana neman taimako na tabbatar zaku taimaka mishi kuma ai koba hakaba?" da sauri Baffa yace "maganan ka gaskiya, zamu taimaka mai, ai shi d'a dakake gani nakowa ne, Allah dai ya shirya mana su sanan ya raya mana zuri'a yakare yakuma tsare mana su" atare duk sukace Ameen, Dady ya kalli Ammi yace "tom saida safe, agaidamin da y'ata inta tashi" dan murmushi Ammi tayi tace "Allah yasaka da alkhairi mun gode da dawainiya" Dady ya kalli Baffa da Kawu sani yace "bismillah Alhaji" da sauri Baffa yace "to, to, to, bismillah muje" bude kofa Dady yayi yafita Baffa da kawu sani suka bishi a baya har zuwa wajen asibiti, wani eatry Dady ya shiga suna biye da shi suka zauna kan table, Dady yace "meza akawo mana Alhaji" hannu Baffa yadaga yace "masha Allah akoshe muke, mungode" murmushi Dady yayi still yasa aka kawo musu drinks sanan ya gyara zama yace "masha Allah inamai tsananin farin cikin ganinku ayau, da farko dai sunana Alhaji Muhammad Ibrahim Darham, ina aiki amatsayin senate president of Nigeria, matana uku sanan yarana ashirin, namiji daya gareni wacce matata tafarko wacce Allah yama rasuwane ta haifamin shi" atare Baffa da kawu sukace "Allah yamata rahama" "Ameen, Aliyu sunan yaron saikuma sauran yarana mata, bazan muku karyaba Jiyan nan nafara ganin mahaifiyar Aneesa wuraren sha biyun dare wanda nafi yarda kaddara ce yahada mu dan bancika yin dare a anguwan hakaba na taimaka mata mukakai Aneesa asibiti, Alhaji" yakira Baffa ahankali, amsawa Baffa yayi yace "na'am Alhaji Muhammad" dan murmushi yayi yace "muba yara bane munriga mun manyanta munyi kwana biyun, tun ajiyan dana fahimci kaman mahaifin Aneesan yarasu ne naji mahaifiyarta ta kwanta min arai ainun inata tunanin yanda zan bullowa al'amarin sai gashi kicibus Allah yahadani daku yau kaga yanda Allah ke abunshi ko" yafada yana murmushi yace "da izinin ku amatsayin ku na yan uwan mahaifin marigayin mijinta nakeso inhar kun yarda inason mahaifiyar Aneesa so na aure, auren sunna, kuma karkuji komi Aneesa nariga na dauke ta amatsayin ya inada yara mata guda goma sha tara karata cikin yarana su zama ashirin abin alfahari ne agareni, wanan ce daman maganan danake so namuku da fatan banyi laifi ba bankuma yi karambani ba" washe baki Baffa yayi murmushi fal fuskarshi yace "masha Allah, masha Allah, Alhaji Muhammad ina cikin tsananin farin ciki da wanan batu naka badan komi ba dan shi auren nan dakake ganinshi rahama ne sanan rufin asirin y'a mace ne, tun Fateema na yar shekara biyu mahaifi ta yarasu amma mahaifiyarta taki yarda tai aure, bazan boye makaba banji dadin yanda take rayuwa daga ita sai Aneesan, banji dadi sabida Aneesa yanzu ta tasa wata rana dole tai aure idan tai aure haka takeso ta cigaba da zaman kadaici? Aisai wani ciwo yakamata, abinda za'ayi shine zan sameta da maganan nan yau yau dinan kome tace zan sanar dakai gobe dan zanso ayi auren kafin nakoma kaduna to anriga an girma me za'a wani daga biki kaman bikin yara? To kagani dazaran ta yarda ana sallaman Fateema daga asibiti gobe ko jibi zamuje masallaci adaura auren, zaman su gida su kadai hadari ne gwara yanzu dazaran tadawo karkashin ka saika killace ta nima hankalina zaifi kwanciya nasan cewa na sauke nauyi na lura sanan nakula da iyalin kanina nabada matar shi aure gun kamilin namiji, sanan abu na karshe dazan fadama Alhaji Muhammad shine nayaba da hankalin ka dakuma mutuncin ka yasa kaga na amsa maka maganan nan siteret, dan haka karike amana, karike su amana, kai babba ne, kanada yara mata ka rike Aneesa da mahaifiyarta amana, idan Aneesa na rashin ji kotama badaidaiba ka kirani ni dinan zanzo har gida na lallasa maka ita, ina kuma rokon Allah daya sanya alheri da albarka ciki, mahaifiyar Aneesa kuwa karka damu zamu shawo kanta" murmushi sosai Dady yayi kaman anmai kyautan Aljanna yace "nagode Alhaji, in sha Allah bazaku taba samuna dacin amana ba" murmushi kowa yayi suka mimike bayan Dady ya biya kudin suka fito daga wajen Dady yamusu sallama yatafi.


_*duk wacce takaranta min littafi batare data biyaba, Allah ya isa, idan kinason book dinan chat me up 07012181461*_*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_





_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤




_✍🏿M Shakur_



2️⃣7️⃣




Saida suka fara tsayawa sukai isha'i sanan suka shiga asibitin, sallama sukayi tareda bude kofan dakin har lokacin Ammi na zaune kan kujera tana kallon Aneesan, zama sukayi abakin gadon sunama Ammi sannu, ahankali Ammi tace "nakawo abinci Alhaji?" girgiza mata kai Baffa yayi yace "bari tukunna yanzu akwai maganan damuke so muyi" dan gyara zama Ammi tayi tace "to Baffa" dan shiru Baffa yayi saikuma yace "Maman Aneesa tsawon wanan shekarun damukai tare tun ina miki kallon matar kanina yanzu kallon kanwata na jini nake miki wacce nakeda iko da ita koba hakaba?" gyadamai kai Ammi tayi tace "hakane Alhaji" gyadakai Baffa yayi cikin nuna gamsuwa da amsan data bayar yace "tsawon wanan shekarun dakika nuna kezaki rike Aneesa bazaki bamu itaba dudda naji haushi amma ban takura mikiba, kikazo kikace ke zaman rainon yarki zakiyi bazakiyi wani aure ba shima ban takura miki ba na barki, ayau nakawo miki wata babbar magana da bazan boye mikiba sonake yau kibani girmana a matsayina na mahaifin yarki sanan waliyinta, kimin biyayya sanan kisani kome nakeso nayi abu mai kyau ne agareki sanan abinda zai ban kwanciyan hankali ne kinajina" gyadamai kai Ammi tayi ahankali gabanta nadan faduwa, dan shiru Baffa yayi yana kallon fuskarta ganin yanda ta natsu duk tabashi hankalin ta tana sauraronshi yasa yace "sonake kiyi aure maman Fateema" da sauri Ammi tadago kai ta kallai cikin wani irin yanayi na damuwa tace "aure Alhaji?" "e, aure maman Fateema nakeso kiyi, aure rufin asirin mace ne, yarinya dake duka dukan ki nawane da zaki ce zaki zaune ahaka ke bazakiyi aureba zaki dinga kula da yarki ne angayamiki hakan zaiyu ne? Banda ma haka amusulunce hakan baida kyau, kin taba tunanin yanayin da zaki shiga duk randa zaki aurar da Fateema kiyi watanni shekaru baki ganta ba kintaba tunanin yanayin da zaki shiga yanda zakiyi coping?" shiru Ammi tayi tana kallonshi takasa magana, dan murmushi Baffa yayi yace "to kingani, gwara kiyi aure duk randa zatai nata auren kina gidan mijinki karkashin mijinki akwai wanda zai dinga debe miki kewa kinajina" gyadamai kai Ammi tayi ahankali, murmushi yasake yi ganin batamai gardama ba, ahankali yakira sunanta "Maman Fateema" ahankali tace "na'am Alhaji" anatse Baffa yace "Alhaji Muhammad Ibrahim wanan mutumin daya taimaka miki yakawo Aneesa asibiti dazu yasame mu da wata magana da tamin dadi ainun, ya nunamin shi daga ranan daya fara ganinki yaji yana matukar sonki ainun" wani irin murmushi Aneesa da tun dazu dasuka fara magana yatashi tayi cikeda jin dadi, da sauri Ammi ta kalli Baffa, gyada mata kai Baffa yayi yace "inaso kiyi tunani sosai bazan takura miki ba, gobe nakeso kibani amsa kuma ko kadan banso adau lokacin dazaran an sallami Aneesa za'a daura auren dan zanzo mu daura auren kafin mubar garin nan, Inaso ki natsu kiduba lamarin da kyau, kuma namiki alkwari gobe ni nan da Na Sani zamu fantsama garin nan muje muyi binciken halinshi inmun dawo zamu fadamiki maimuka gano sanan saimuji amsan ki saimu kirashi, inamiki kwadayin aure sosai, so kiyi tunani kinji karki takura ma kanki, Allah ya sadamu da alkhairan shi" gyadamai kai Ammi tayi ahankali tace "Ameen" murmushi yayi yace "to bamu abincin muci mutafi" plate tadauka ta zuba musu tavasu sunaci ana hira sama sama saida suka gama sanan suka mata sallama suka tafi.





Tagumi Ammi tabuga tana tunani sosai sai hango fuskan Dady take, dan motsin da Aneesa tayi yasa tadago kanta ta kalleta ganin idanunta abude yasa ta tashi da sauri tareda daura hanunta kan goshin Aneesan tana murmushi tace "Aneesa na kin tashi zakiyi fitsari nakaiki bayi?" girgixa ma Ammi kai tayi tana murmushi, murya chan kasa tana lum lumshe ido tace "Ammi ki yarda ki aureshi ni inason shi wlh, inason Abba Ammi, please ki yarda kinji" Aneesa tai maganan tana murmushi sosai baki Ammi tabude cikeda mamaki tana kallonta tace "ke, so dama idanunki biyu kinajin duk abinda muke cewa ko" gyadama Ammi kai tayi tana murmushi sosai tarike hanun Ammi tace "Ammi please kinji ki yarda, dan Allah" hararanta Ammi tayi tace "Common kimin shiru anan, zakiyi fitsarin ko bazakiyi ba" turo baki tayi tace "ni banaji, kuma inyazo gobe sainace mai Ammi na ta yarda su Baffa su daura auren" haba Ammi tarike tana kallon Aneesan cikeda mamaki tace "kaman rashin lafiyan nan yasamiki rashin jine ko Aneesa wanan magana haka" dan murmushi Aneesa tayi tace "inda ni namiji ne dani zan badake Ammi" daka mata duka kadan Ammi tayi acinya hakan yasa tafashe da dariya sosai Aneesan tana safe kanta dake mata ciwo Ammi tace "ahh lallai lafiya tasamu, zanci gadanku ne" rungume cikin Ammi tayi tace "please Ammi na ki yarda kinji for me Ammi na, ni inason shi" shiru Ammi tayi tana sauraron ta kafin tadan sauke ajiyan zuciya tace "to shikenan, zanyi tunani in sha Allah" matseta Aneesa tayi tace "yauwa Ammi na, my Ammi najin magana ta, my Ammi is a good girl" dariya sosai Ammi tayi tana shafa kanta tace "Allah shirya" haka suka dinga hira kasa kasa harta sake komawa bacci._*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_





_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤




_✍🏿M Shakur_



2⃣8⃣




Tunda asuba ta tashi ganin tanada dan karfi yasa Ammi ta kaita bayi tamata brush tareda dauraye mata jiki da towel da ruwan zafi ta taimaka mata ta chanza kaya hakan yasa taji dadin jikinta sosai suka fito, a zaune tai salla sanan takoma kan gado Ammi tahada mata hot tea mai kauri tabata tasha dan yamata dadi sosai nan da nan tafara zufa dan sauki yasoma samuwa kafin daga bisanni tai bacci.





Wuraren biyun rana su Baffa suka iso kowannen su dauke da murmushi akan fuskar shi suka zazzauna nan suka shiga bama Ammi labarin binciken dasuka yo, Dady nada kirki ainun ga taimakon musulmai, sanan baida zalunci, matayen shi duka suna tare bai taba sakin mata kodaya ba, gidan shi ba'ajin kansu awaje atakaice dai basuji any bad halin Dady ba daidai da kwara daya, hakan yasa Baffa ya gyara zama yace "todai kinji komi, me kikace dan kiranmu yake jira, eh maman Fateema me kikace?" dan ajiyan zuciya Ammi tasauke kafin ahankali tajuyar da kanta ta kalli Aneesa dake bacci tai shiru kafin tafara zancen zuci. "hukuncin dazan yanke yanzu sabida kene Fateema na, I know, ni karan kaina nasan yanda zuciyar ki ta kwadaitu, tana neman wanda kowani safiyar Allah zaki kalla ki kirashi da Baba ko Abba ina kwana, kema ki sami wanda zaki kalla ki kira da mahaifi, bakomi zaisa na yarda da auren nan ba saidan inga farin ciki akan fuskarki, farin ciki wanda ni mahaifiyarki ce tasanyaki ciki, nothing beat seeing your child happy and as a mother I have to make you happy, zan yarda da auren nan for you Aneesa na dan naga yanda kikeson Alhajin nan banda hakaba ma ta sanadinki muka hadu" ajiyan zuciya ta sauke ta juyo da kanta ahankali ta kalli su Baffa dasuke jiran me zatace gyadamusu kai tayi ahankali tace "na yarda Baffa" wani iri washe baki da sukayi zaka dauka an musu bushara da aljanna ne Baffa yace "masha Allah Masha Allah, naji dadi, ina kuma rokon Allah daya sanya albarka awanan lamarin, ya kade fitina, yanzu Na sani tashi muje musanar dashi me akeciki kaga nasan zaiyi farin ciki sosai" cikin jin Dady suka tashi suka fita, dan murmushi Ammi tayi harga Allah tunda Aneesa ta nuna tanason Alhajin sai itama taji tana sonshi sosai bana wasaba kuma zata so ta kasance tareda shi har abada, dan dugo dakai tayi ta sumbaci goshin Aneesan dake bacci tana murmushi tanata kallonta ahankali tace "Allah yabaki miji nagari wanda zai soki sanan ya kulanmin dake aduniyan nan" karan dataji na shigowan message a wayanta ne yasa ta mike tsaye ta dau Jakarta dake kan saman drawer, wata savuwar number ce tatura mata sako, zama tayi abakin gadon tabude.

_Assalamu Alaykum, Rukayyah_
_Hakika yau kin sani cikin tsananin farin cikin dana dade ban shiga irinshi ba, naji amsan ki daga bakin Alhaji, Masha Allah, Alhamdulillahi Rabbil Alameen, alkawari daya zan miki shine bazaki taba samuna dacin amana ba, zan rikeki amana, Aneesa tadawo y'ata zan riketa amana sanan zan bata tarbiya amatsayina na mahaifi agareta, karkiji komi zan kasance miji nagari da zaki dinga alfahari dani akodayaushe. Ina kaunar ki sosai Rukkayah Sainazo_
_Alhaji Muhammad_




Dan murmushi Ammi tayi ta ijiye wayan tareda sauke ajiyan zuciya tana tunani wai yanzu itane zatai aure? Abinda bata taba kawowa zai faruba, Allah kenan dazaran yace lokaci yayi to yayin nefa, Allah sa mudace! Ameen.







Da sallama Dady ya shiga part din Aliyu, jin shiru bai amsaba TV ne kawai ke aiki a falon yasa yay bedroom dinshi, ahankali yabude kofan babu kowa a bedroom din sai kamshin da dakin yakeyi, fitowa yayi yana kwalamai kira. "Aliyu, Son, Gadanga na" fita yayi daga part din yana mamaki to ina yaje yaga motarshi ai, har zai wuce idanunshi suka sauka kan wani fine paint brush dake kasa, tsugunnawa yayi ya dauka yana murmushi yace "yau yan zanen sun tashi kenan jibi ya yarda wanan baima saniba" garden din dake side din Aliyun yawuce dan yasan anan yake zane, garden ne mai kyan gaske an gyara wajen iya gyarawa gawasu kujeru da table da aka jera awajen kaman wurin picnic, hango Aliyu yayi zaune kan wani dan kujera, yana sanye da gajeren wando na Paco Rabanne sai wani dark blue logo t-shirt na Marni kafanshi cikin wani white bedroom slippers, hanunshi rikeda paint brush yana 3D zane dabai riga yagama ba akan babban drawing board, kunenshi makale da head phone, jingina Dady yayi da bishiyar mango dake wurin yay folding hannu a kirji yana kallonshi yana murmushi Aliyu is damn gifted. 1st degree dinshi architecture yayi, 2nd degree dinshi kuma yay law, bai dade dagama masters dinshi ba, dukda first class yake fita, yanzu haka construction company dinshi is ready amma yaki fara zuwa office ko kadan baiso yana takuramai saisa ya barshi yasa wani PA dinshi yana managing wurin kafin Aliyu yay ready finally.



Ahankali ya sanya hanunshi dasuka dan baci da paint ya janye headphone din kunenshi batare daya waigoba yace "Dad why are you looking at me?" ware ido Dady yayi cikeda mamaki kafin yatashi daga jikin bishiyan yakara so inda Aliyun yake ahankali ya dafa kanshi yace "Son yan zanen ne yau suka tashi, mekake zanawa haka?" Dady yay maganan yana janyo dayan stool din dake gefe ya ijiye ata gaban Aliyun ya zauna yana kallon yanda paint din yabata rigan daya saka. "Aliyu" kallon Dady da sauri yayi yana tsayar da zanen jin yanda yakira shi, ajiye paint brush din yayi acikin cup din ruwan dake kan table yace "Dad, wat is it?" gyara zama Dady yayi yace "I want to talk to you" hannu yasa ya kashe headphone din da waka ke tashi daga ciki Aliyu yayi yace "OK, am listening" dan shiru Dad yayi kaman mai tunani, ahankali yace "aure nakeso zan kara Gadanga na" yay dan shiru yana kallon fuskan Aliyun ganin baiga wani chanji ko wani yanayin tattare dashiba yasa yace "Son kasan bana boyema komi ko, kawai sabida na kasance namijin da banso ina yawan sakin mataye nane bazan ma karya ba da tuni na saki duka mata uku nan danake dasu, basuda mutunci, basu da kirki, ga shegen son abin duniya, they've spoilt all my children Aliyu da yau inda zan fadi namutu yaran wanan ba ruwan su da yaran wanan, cikin dukan ku ku 20 daga kai sai Rauda ne Allah ya tsamo min, am worried Son, how many hours nake samu na zauna agida dazan samu nai uniting yarana, y'ay'ana iyye? Na auro jakunan mata babu abinda suka iya sai koyama yarana bakaken hali da tsanan junan su, mata uku amma banda ta arziki ko daya" yadanyi shiru dan ko kadan baiso yana tunawa da matsalolin gidanshi da hawan jininshi zai iya tashi, ahankali yace "I told you shekaran jiya abinda yasa nai latti was because I helped one woman da yarta batada lafiya na kaisu asibiti ne ko" gyadamai kai Aliyu yayi alamun eh, cigaba da magana Dady yayi yace "Aliyu when I saw how caring and loving that woman is towards her daughter I immediately saw myself in her, na yaba da natsuwan matar, sanan na yaba da tarbiyan data bama yarta, she's good, she's educated duka fanin boko da islamiya ahaka banma riga na tambayeta duka abubuwan data saniba tukunna, Ustaziya, kamilan mace, da natsuwa da kamala, ga fikra, all this abubuwan duniyan nan basu dameta ba, sosai naji ina sonta, nama yan uwan ta magana sufada mata tace ta yarda, dazaran an sallami yarinyar daga asibiti nakeso a daura auren, I don't wanna do anything dazai batama rai I need your support Gadanga na, should I go ahead and marry her?" dan shiru Aliyu yayi yana kallon mahaifin nashi deep down ya tsani yanda Dad ke aure but wani zubin baya blaming nashi danko shi kanshi baiga mata tagari acikin matayen ba, he just hope wanan will give his Dad the peace din dayake nema da kwanciyan hankali tunda dai yaga tsantsan son da Dady ke mata a idanunshi, dan murmushi dake karamai kyau yasakin ma Dady yace "marry her Dad, Allah sanya alheri" ajiyan zuciya Dady ya sauke tareda lumshe ido jiyayi duk wani nauyi da zuciyan shi yamai ya sauka baiso yay auren Aliyu bai yardaba saigashi ya yarda, cikeda tsananin farin ciki yace "thank you Gadanga na, zan kira Momman ka tahada min akwati, kaje gidan kuwa tunda kazo?" yatsine fuska yayi tareda girgiza kai, dan batarai Dady yayi yace "kabar zanen nan kawuce ka shirya, bodyguards dinka su kaika kanajina ko" ahankali yace "to" tashi Dady yayi yace "zan kira a gyara the flat that is next to mine, bari naje office" "bye Dady" "bye Gadanga" fita Dady yayi Aliyu yay shiru yarasa mekemai dadi aduniyan nan mugun so yake yaje asibitin but baiso yahadu da Ammi, Abdul yafado mai arai hakan yasa da sauri yatashi yay part dinshi wanka yashiga yafito ya shirya cikin wata hadaddiyar shadda yaja mota ko inda bodyguards din da Dady yace subishi baiyiba yafice abinshi.






Wuraren 3 na rana Dr ya shigo dakin rikeda leda dake cikeda magunguna yana kallon Aneesan data tashi zaune ta jingina da gado tana shan tea da Ammi tahada mata Baffa na zaune kusada ita rikeda plate da soyayyan kwai kekai tanaci, tarame sosai, raman saiya kara karamata kyau, lips dinta sukai pink suka tattare sosai bana wasaba, baki Dr yarike yace "iyye patient dina da bata son allura ne takecin dadi haka, mesa akabata? " dan murmushi Aneesan tayi akunyace, Baffa yace "yo kaiko bazaka barmin diya taci dadi ba, kukenan saiso kuna chakama mutum karfe daku za'a chakamawa da ansha kallo kuka wiwi zaku dinga yi

Please Login or Register in order to submit comment