Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

makiya .

amma wallahi wannan aure na Hakeem bai kwanta minba kokadan

Haka dai sukayi ta tattaunawa tsakaninsu .



HAKEEM bayan yakoma dakinshi yashiga duniyar tunani yace tabas gaskiyar mummyn shine auren manufa zasuyi ,

Dan yadade da gane 'yan uwan mahaifinsa basa kaunarshi koka dan ,

Inba haka zasuce wai za a hadashi aure da yarinyar da bata da mutunci batada tarbiya ,

Nifa idan asona nane sai nan da shekara goma sha nayi aure ,

Dan sai tsaya na zaba matar da ta dace da rayuwata ,

amma idan tasake tashiga rayuwa ta a yanzu zan nuna mata waye ABBULHAKEEM

zata San koni waye duk wani shige da ficen dangin mahafin nasa yasani sarai


Dan haka yadauki aniyar yiwa mahaifinsa biyayya

Sai zai nuna musu shidin namijine wato dangin mahaifinsa kenan

Haka dai Hakeem yayi ta sake da warwara


Washagari da safe bayan Hakeem yagama break fast ne yadauki phone dinshi yakira Ahmad
Abokinsa yace kana inane ahamad yace ganin agida

Hakeem yace OK ganin nan shigowa gidan """"'

Ahmad abokin Hakeem kud da kud dan tare sukayu primary da secondary school

Kuma tare sukatafi makaranta a Saudi Arabian tare suke dawowa Hutu ,

Hakeem da Ahmad basa boye wa juna sirrinsu kokadan

Komai nasu tare sukeyi dalilin hakan yasa iyayensu sanin juna har ake zumunci sosai ""


HAKEEM yayi parking a harabar gidansu Ahmad

Kai tsaye ya wuce part din Ahmad yana shiga yafada kan kujerar falon Ahmad din

Ahmad yace ya man yanaga duk kayi wani iri meyake faruwa ne

Hakeem yaja dogon numfashi yace kaidai bari man wallahi so ake a hada min zafi agida

Ahmad yace zafi kuma kaman yaya
Ahmad yakwashe komai yafada wa Ahmad

Ahmad yayi dariya sosai yace to ai kai Allah ya kashe yabaka tunkana very young dinka zaka angonce ni wallahi banga abinda damuwa Ba


Tunda Ahmad yafara magana Hakeem yake kallonshi dan yabashi haushi sosai

Yace wato dariya ma nabaka ko
Ahmad yace dariya kabani mana kaida za ama auren gata


Ahmad yace amma fa ina tausayawa yarinyar saboda by the time din kake cikin samartakarka by then itakuma bayadda takaraji fa dan tazama baba


Hakeem yace kai man har ka mata lissafi kasan ko yar ten years za abani

Ahmad yace ai nasan baza a tabaka yarinyar da bata wuce goma Ba

Kaga kuwa may be 16 to 17 years haka
Kagakuwa ai kafin nan da wani lokaci tazama mama

Hakeem yace duk ma baka zogunba
Todai yarinyar shekara daya nabata a duniya


Ahmad yace cab wallahi hartabani tausayayi dan nasan bayadda za ayi kazauna da ita kadai a lokacin da samartaka yazo maka


Hakeem yace kaji dan rainin hankali yanzun wanene idan ba saurayin Ba


Ahmad yayi dariya yace sau dai baka kai rayi dinba

Hakeem yadauki trowing pillow ya jefeshi dashi


Yace kaiko nazo nafada maka damuwa ta memakon kakwantar min da hankali sai kuma bige da da yimin shiririta ko

Ahmad yace to naji abikona yanzu dai kasan muhimmancin bin umarnin iyayeko dan haka kawai kabi maganar daddy insha Allah komai zaizo dasauki


Ya da amaryar zamuwuce ne Hakeem ya yatsina fuska yace Allah yasauwake natafi da ita akanme


Ahmad yace ya hakuri maida wukar

Yanzu dai katashi mushiga cikin gida kugaisa dasu mummy


Sai muwuce sallar azahar ko dan naga time yayi .



Alhaji abubakar yasamu mahaifinsa alhaji shuaib akan maganar dasukayi da hajiya suwaiba

aikuwa alhaji shuaib yace baisan San zance Ba
Yace waini abubakar sai yaushe za abarka kayi abun kankane

Kai an baka mata batareda son rankaba ka karba sakamokon biyayyar da kayi Allah yasa kadace da mata tagari

Sai kuma yanzu andawo kan danka
Wanda shi ko auren ma bai isaba ance za abashi mata

Hajiya suwaiba tafito daga dakinta tana cewa haba alhaji ai nagani yaran nan fa duk jikokinkane daga ita lailar har Abdulhakeem din

Idan akayi wannan aure sai munfi kowa farinciki

Kaga ai tuwona maina kenan

Alhaji shuaib yace yanzu Nagano kekika kitsa komai suwaiba

Hajiya suwaiba tace a nice alhaji ganinayi da abubakar da rukayya ai duk 'ya'yanane
To ina laifi dan nace suhada yaransu aure tunda sauran numfashin mu muga hakan

Alhaji shuaib zaiyi magana abubakar yace dan Allah Abba maganar yawuce kawai ka amince kawai da bukatarta

Alhaji shuaib yanisa yace yanzu Abdulhakeem din ya amince

Abubakar yace namishi magana tunjiya kuma ya amince

Alhaji shuaib yace banyardaba katuromin shi idan bayason auren ba maiyi mashi dole ..


Bayan kwana biyu Hakeem yayi shiri tsaf ya wuce gidan kaman nasa alhaji shuaib

Yana shiga falon gidan yasamu kakan nasa yana zaune yana kallon sunna TV

Sai yace a a tsoho mairan karfe an kura wa TV ido kaman kanagani da gaske

Alhaji shuaib yace aikuwa dai idona yafinaka naka karfi dan tar nakeganin ka

Hakeem yayi dariya yace fadi gaskiya dai kakus

Alhaji shuaib yace yanzu dai Ba wannan
Maganar da kuka yi da mahaifin ka nakeson naji ka amince ne ko baka aminceba idan baka amintaba Ba zanbada goyon baya amaka doleba amma idan ka amince shikenan Allah yasa albarka

Hakeem yayi shiru dan dai kawai yariga yayi wa mahaifinsa alkawarin amincewa ne

Nan yace na amince kakus
Alhaji shuaib yace Allah yasaka albarka

Sannan kuma ina maka albishir da cewan duk lokacin da zuciyarka yabaka kanason auren zabinka kana da dama yin hakan

Dan wannan aure ne kawai na hadi nasu na daban

Harcikin ran Hakeem yaji dadin maganar tsohon yayi wata dariya Allah yakara maka Nisan kwana kakus dina na kaina kaga irin wacce zanzabo a matsayin mata


Kakan yace Ameen dan albarka Allah yasa muna raye muga wannan rana

Hajiya suwaiba tashiigo taji duk abinda suke fada

Cike da isa tace wa alhaji shuaib aidai kabari ayi wannan din kafin afara zancen wata

Hakeem ganin shigowar hajiya suwaiba yasa yadaure fuska yakoma Hakeem dinsa

Danshi Sam jinin bai hadu da matar kakan nashi Ba

Ganin haka yasa yace sai anjima kakus zan dawo muyi hira na musamman

Batareda yakalli inda hajiya suwaiba take ba

Yace ina wuni hajiya
Baijira amsawarta Ba yayi hanyar waje

Tabishi da harara tace inan daku ai
Zamu hadu a karo na biyu ne


Laila da mahaifiyarta sunan suna ta murnar samun nasara
Dan ansa sati nan sati daya saboda komawar Hakeem school


Mummyn Hakeem kam batayi wani gayya Ba dan ita wannan auren ba aure bane agurinta

Duk lokacin da yakawo matar da zai aura alokacin ne zata yi nata bikin

Zata nunawa dunniya sai a lokacin dan yayi aure


Next page

Your comments is needed fan's====
Much love to your comments<ؗ<ؗ<ؗ<ؗ<ؗ<ؗ<ؗ<ؗ<ؗ
[30/04, 5:46 PM] UMMU AFAN <9: BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


<ؗHAKKIN MALLAKA NA UMMU AFAN <ؗ



I DEDICATE THIS PAGE TO MY LOVELY MOM
MUCH LOVE TO YOU MOM
NO ONE LIKE YOU IN THIS WORLDd'd'd'



<GORGEOUS WRITERS FORUM <

<G.W.F<


HOME OF GORGEOUS, INTELLIGENT AND EXPERTS WRITERS WE ARE THE BEST AMONG THE REST




<ؗAKWAI LOKACI <ؗ




<ؗPAGE 16 to 20<ؗ




Hajiya suwaiba da hajiya rukayya kadai suke kidansu kuma suke rawar su

Abin yana basu haushi ganin Ba Wanda yake shiri akan bikin
Sai dai dayake suna ganin dazarar anyi auren shikenan

Zuriar alhaji abubakar sundawo hanunsu dan sai yadda suka juyasu


amarya laila ta gayya ci kawayenta sosai dan halartar bikinta


Maman amarya hajiya rukayya  
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~ 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~ 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~ 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~ce tazaunar da ita tace wai ke yau saura kwana biyu biki amma baki tambayi shi Hakeem din kudin dazakiyi hidima dasu Ba


Laila tace hmm mama kenan to ina managanshi ballantana har na tambayeshi kudi

Hajiya rukayya tace lalle ma yaron nan ya raina wa mutane hankali amma zai shigo hanunmu ne ai

Yanzu abinda nakeso dake kitashi kidauki kawarki daya tarakaki zuwa gidan su Hakeem din
Kikarbo kudin dazakiyi Hidima dasu

Laila tace wannan ma shawara ne mamana yanzu kuwa zan tafi

Haka laila tadauki biky daya daga cikin kawarta taraka zuwa gidan su Hakeem

Laila shiga tayi cikin wasu Riga da wondo parkistan Wanda siririn gyalenta tayafashi akan gashin dokinta dayazubo mata har gadon bayanta

Ga farce da akasa musu duk ita da kawar tata kana ganinsu kasan dai Ba tarbiyya

Laila tana parking cikin gidan su Hakeem tashiga direct zuwa falon gidan
Tana shiga ta tarar da hajiya hafsat mom din Hakeem zaune kan two sitter tana kallon tasharta na MBC 4

Mummy hafsat kawai ganin mutane tayi tsakiyar falo batare da sunyi sallama ba
Tadaga kai takallesu suka hada ido da laila

Laila cikin rashin gaskiya tace mummy ina wuni wallahi banganki bane nazo gurin Abdul Hakeem ne

Mummy hafsat tamusu wani kallon takaici tace Ku wasu irin marasa tarbiyar yarane dazaku shigo gida Ba sallama ko haka aka koya muku agidajenku

Cikin in ina laila tace sorry mom please ina Hakeem yake muna sauri lokaci na kurewa

Cikin tsanin mamaki mummy hafsat take kallonsu laila da suke tsaye kikam kaman andasasu suna karkada jiki

Mummy hafsat tace nikuke wa rashin kunya laila ankuwa fada miki halina
To kikoma kitambayi uwarki wacece ni idan ita ta turoki kimin rashin ni ina dai dai da lokacinku


Kuma kije kifada wa uwarki dan tana yar mijina hakan bazai bata dama hakan bazai bata damar saku kuzo harcikin gida kuna min dibar albarka Ba
Ita tasan wacece ni niba kanwar lasa bace


aikuwa daga Laila har biky kawarta sun tsorata da yanayin mummy hafsat

Mummy hafsat tace kubace min daga gida yanzun nan insake ganin kafarki agidan nan kiga abinda zaifaru

Da gudu suka fice agidan kuwa harsuna tun tube

Suna zuwa parking space
Zasu shiga mota sai ga motar abdulhakeem aikuwa Laila washe baki tayi tace biky Gashi nan fa biky tace waw wannan
Zazzafar motar shice

Laila tace kadan ma kika gani indai Hakeem ne kinga zomuje musameshi karyashiga


Hakeem kuwa shida Ahmad ne
Ahmad yace wa Hakeem ya kaman kunyi baki Hakeem yace maikagani

Ahmad yanuna mashi su wurinsu laila
Hakeem yakai idonshi gurin
aikuwa yana ganin sun nufosu yadaure fuska

Ahmad yace kai harda bakin ma zaka nunawa halinka ko
Hakeem dai baice komai

Laila suka karaso gurin su Hakeem din
Sai Ahmad yadan durkusa yace anty ina wuni

Cikin tashin hankali Laila tace wace ce antyn taka
Ahmad yakalleta cikin rashin mahimta danshi yadauka yayar Hakeem ce dangin su

Danshi baitaba sanin laila Ba tunda Hakeem bazuwa yakeba

Abin yaba wa Hakeem dariya amma yaci fuska sosai dan kar laila taga hakorinsa da sunan dariya

Yarufe motarshi ya kalli Ahmad yace mujeko

Laila ta tari gabanshi tace haba Abdul kasanfa gurinka nazo ko

Hakeem yakalleta ya watsamata wani mummunar kallo yace gurina kikazo namiki me

Abin yaba Laila haushi dan ya tsinkata agaban babbar kawarta

Ta daure tace naga har yanzu baka zo gida munyi maganaba kuma baka kuma tambayeni abinda nake bukata na game da harkar bikinba shine mama tace nazo nakarbi kudin dazan yi hidima dasu


Sai a lokacin Hakeem yayi wani killer smile yace lalle kuwa bazakiyiba
Kikoma gurin wacce ta hada abin sai tabaki
Nikam kwandala ta bazaiyi ciwo akanki Ba

Nan ya wuce ta Ahmad yabi bayansa suka shiga cikin gida


aikuwa da gudu Laila tafada mota
Dan tunda take Ba a taba wulakantata irin wannan Ba

Kawarta biky tayi ta rarrashinta kasa driving tayi biky ce tayi


Hakeem da Ahmad suna shiga falon mummy
Suka ganta zaune kan kujera
Hakeem yasaki murmushi yace mummy na yadai naga kaman antaba minke

Ahmad yanemi guri yazauna yace mummy an wuni lafiya

Cikin fara a mummy hafsat tace lafiya qalau Ahmad ya su hajiyartaka
Ahmad yace lafiya qalau tace zata zo anjima

Mummy hafsat tace aikuwa kaman tasan inason ganinta Allah yakawo ta lafiya

Hakeem yace mummy shine wato kinga Ahmad ina miki magana kina wani basarwa ko


Mummy tayi murmushi tace ai matarka ce taba tamin rai shiyasa

Hakeem yadaure fuska yace daliba zakifara ko

Mummy tayi murmushi takalli Ahmad tace Ahmad katayini da abokinka dan Allah matarshi tazo ta bata min rai dan Allah basai na huce akanshi Ba

Ahmad yayi dariya yace kinyi dai dai mummy

Tace a to kaima kafada dai

Hakeem ya harari Ahmad ya kalli mummy yace daliba bazaki daina kiran wannan Mara kunyar yarinyar da mata ta bako

Mummy hafsat tace toya zamuyi komunki ko munso sai anyi

Nan tabasu labarin yadda sukayi da su Laila dasuka shigo
Hakeem yatashi ya suri key din motarshi yayi hanyar fita

Mummy hafsat tace dagata dan albarka ina zaka yace mummy kibarni naje naci ubanta har tana da gost da zata zo gidan nan tasaki magana haka


Mummy hafsat tace kalesu nima din ai sunsan wacece ni zata je tafada wa uwarta

Zasu sake sabon shiri mu basusan shirinmu yafi nasu dan muda Allah muka dogara

Hakeem yace wai mummy maiyasa daddy yakasa gane mutanen basa kaunarshi Ba sonshi suke ba fa

Mummy hafsat tace nima abun yana damuna wallahi hakurin mahaifinka yayi yawa wallahi


amma bakomai duk mai hakuri wataran yana tareda riba

Mummy tace kutashi kushiga kuci abinci

Suka tashi zuwa part din HAKEEM

Suna shiga dariyar dayake cin Ahmad yafito dashi

Yayi sosai Hakeem yace wai kai kuma wakake wa dariya

Ahmad yace wallhi matarka da nacewa anty

Hakeem yace karkasake cewa matana kace kawai matar kaddara


Ahmad yace narki gaskiya man na tausaya ma wannan yarinyar wallahi kokadan wallahi bakuyi marching ba kokadan

Da zanbata shawara data nemi mijinta a wani wajen tabarka

Hakeem yayi dariya yace akai man shine wannan dariya haka amma nima naso nayi dariyar Dan bakaramin dariya abin yabani ba
Kawai dai banson rainine yasa na make kawai

Ahmad yace oh baruwana fa randa zaka angonce ina ina Dan haka nayishiru Allah yabada zaman lafiya

Tsaki Hakeem yayi yace katashi muje muci lunch idan kuma baka gama surutun ba to

Nan dai sukayi hira amma Rabin hirar tsokanane Ahmad yakewa Hakeem


***
Bayan komawar su Laila gida tana kuka tana bawa mamanta labarin abinda mummyn Hakeem da Hakeem din suka mata

Ran hajiya rukayya yabaci
Tadauki waya takira uwarta hajiya suwaiba ta fada mata komai abinda Laila tafada mata

Nan itama hajiya suwaiba ranta yabaci tace bakomai ai sunkusa shigowa hanunmu

Tayi hidimarta da kudinta kawai zata fanshe ai

Hajiya ruakayy tace amma hajiya kinsan wallahi bakudi a hanu na sosai

Hajiya suwaiba tace kwantar da hankalinkki
Kituro min ita jikallen sai nabata wasu kudi

Nan hajiya rukayya tayi godiya ga mahaifiyarta kafin takashe wayar takalli 'yartata dake kukan wulakancin da akamata

Tace kidaina kuka kitashi kitafi gidan hajiyata zata baki kudi konawane sai kufara hidimarku na kawaye

Nan Laila ta washe baki tace kai Allah yabarmin kakallena yanzu ita zata bani kudin

Hajiya rukayya tace kwarai kuwa aiba abida bazatayi miki ba kece fa jikarta tafarko


Nan dai Laila suka tashi suka tafi karbo kudin """"



Ranar daurin aure dasafe hajiya suwaiba takira alhaji abubakar tace mishi yau daurin aure amma haryanzu basuga kayan lefe ba

Alhaji abubakar yace ai mun sha afa ne hajiya kaman nawane za a hada lefen dashi

anzo inda takeso tace million biyu sun isa

Alhaji abubakar yayi signing a cheque yabata tace yauwa Allah yayi albarka

Alhaji abubakar yace Ameen hajiya

Nan yatashi yashige wajen mahaiginsa alhaji shuaib

Yanashiga yasameshi yagama shirin daurin auren ne ma

Yace a a abubakar kaine tafe kohar kafito gurin daurin auren ne

Alhaji abubakar yayi murmurshi yace
ai hajiya ce takirani akan maganar kayan lefen Daba akawo ba

Alhaji shuaib yayi dariya yace wargi ma guri yakesamu

Tamin magana nace tawa angon magana shine taki kai dayake sunga kana da hakuri shine suka bita kanka ko

Alhaji abubakar murmushi kawai yayi baice komai ba

Alhaji shuaib yace yadda yaron nan yake yana burgeni suna mugun shakkarsa

Dan ina mata maganar ta tambayi Abdul Hakeem dakanta bakaga yadda ta yiba

Alhaji abubakar yace ai yaron nan nima yana bani mamaki wlh gashi karamin yaro amma koyanzu nasake mishi komai zai riqe sosai

Alhaji shuaib yace ai Allah ne yama sakayyar biyayyarka gareni da wannan d'anaka ABDULHAKEEM

Zakayi alfahari da haihuwar Abdul Hakeem saboda kaima nayi alfahari da haihuwarka Allah yajikan mahaifiyarka amina

Alhaji abubakar yace ameen Abba

Nan sukayita hirarsu har lokacin daurin aure yayi suka fita zuwa gurin daurin auren



Hajiya suwaiba ta kira yarta hajiya rukayya tafada mata yadda sukayi da alhaji abubakar

Wani irin ihu hajiya rukayya tayi tacikin waya tace million biyu fa kika ce hajiya

Hajiya suwaiba tace to meza afasa

Hajiya rukayya tace aikin ki nakyau hajiya ta
Kinga munfara bambara tun yanzu ko

Hajiya suwaiba ta ce kidai bari yarinya dai Allah yakashe yabata





****

Bayan andaura auren Abdul Hakeem da Laila usman



Daddyn Hakeem ya dawo gida bayan yazauna
Mummy hafsat takawo mishi abinshi yaci sannan yabata labarin yadda sukayi akan kudin lefe

Mummy hafsat tayi murmushi tace a lalle sun wankeka

Yanzu zasuga kaman shirinsu yafara aiki kenan

Murmushi Daddyn Hakeem yayi yace Hafsat mata agurin abubakar maman Abdul Hakeem

Rigimar ki yana bandariya kefa baki yarda dawannan auren bako

Mummy hafsat tayi murmushi tace ai Dana baiyi aureba

Dan banmasan anyiba wallahi kawai dai za aiya kiran aurn da kaddara

Daddyn Hakeem yayi murmushi yace zanso kimishi fatan dacewa kamar yadda nadace dake
Dan ko zabin kaina nayi ba lalle nayi dacen danayi akankiba hafsat


Next page

Your comments is needed fan's =؋=؋=؋

=====
<ؗ<ؗ<ؗ<ؗ<ؗ<ؗ<ؗ<ؗ<ؗ<ؗ<ؗ<ؗ<ؗ<ؗ<ؗ<ؗ
[30/04, 5:48 PM] UMMU AFAN <9: BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


<ؗHAKKIN MALLAKA NA UMMU AFAN <ؗ


DEDICATED THIS PAGE TO LOVELY SON AFAN
d'd'd'd'd'd'd'


<GORGEOUS WRITERS FORUM<

<G.W.F<


HOME OF GORGEOUS INTELLIGENT AND EXPERTS WRITERS WE ARE THE AMONG THE REST




<A KAWAI LOKACI<




<PAGE 21 to 25 <



Ankai amarya Dan kararen part dinta dake gidan su Hakeem .

Mummy hafsat kam a ranar ma gidansu taje wa wuni
Saboda batason damuwa """"'


HAKEEM suna zaune shida Ahmad

Ahmad yace kai kasan karfe nawa yanzu katashi muje narakaka dakin amarya fa .

Cikin halin ko inkula Hakeem yace lalle kuwa su amarya manya bari ma kagani

Ya kashe phone din shi ya gyara kwanciyarsa akan bed din Ahmad .

Ahmad yace banganeba mekake nufi badai anan zaka kwana ba

Hakeem yayi banza dashi yayi baccinsa Ahmad yace OK halin ya motsa ko

ai wannan amarya taja wa kanta data waye. Hakeem da bata kanta wahala ba wajen auranka ba


Nan shima yakwanta abinshi Dan yasan duk yadda zaikai ga magiya Hakeem bazai tashi ba .




Amarya Laila tana ta zuba ido taga ango yashigo shiru kakeji malam yaci shirwa kawayenta ma sun gaji suntafine


Idonta biyu har wajen karfe uku ba ango
Tadauki waya takira Maman ta Maman tace yadai laila naga kiranki yanzu


Kingane dai yadda akace kiyi anfani da maganin ko karfa kiyi wani abin da zaisa yaki kusantarki kinsan maganin na yau ne kawai

Duk hanyar da zakibi yakusance ki
Kiyi shi karmuyi asara makudan kudaden da muka narkar wajen karboshi

Laila tace yanzu dai dakin tsaya na fada miki abinda zanfada miki

Hajiya rukayya tace inajinki meyafaru

Laila tace haryanzu fa bai shigo gidan ba ma

Cikin tashin hankali hajiya rukayya tace munshiga uku
Yanzu soyake muyi asarar makudan kudaden nan

Ki kirashi a waya mana
Laila tace ina naga numbarsa

Hajiya rukayya tace shikenan munyi asarar kudinmu

Dan malam yace maganin kwana daya yakeyi idan yakusanceki zai zaima rakumi da akala bazaiji maganar kowa ba sai abinda kikace mishi


Kuma zai tsani iyayensa

To gashi Hakan su bai comma ruwaba

Har kuka sai da hajiya rukayya tayi Dan maganin nan naira million daya haka suka caske wa malam


Gashi yanzu wannan Dan ban zan yaron yaja musu asara


Daga laila har uwarta basuyi bacci ba


*********

Washagari da misalin karfe goma Hakeem yafito daga wanka daga bathroom din Ahmad

Yashirya cikin wasu kananun kaya sun balain mishi kyau ya fesa turare

Kafin nan yakalli Ahmad da yariga yashirya Dan yariga Hakeem tashi tunda suka dawo daga sallar asuba shi Hakeem sai yanzu yatashi


Hakeem ya kalleshi yace yace muje mukarya zanje naga dalibata fa

Ahmad yace to ango muje dining din ko
Suka wuce zuwa dining area na Ahmad

Sukayi break fast
Kafin suka dauki hanyar zuwa gidan su Hakeem

Suna hanya kafin sukai gidan su Hakeem sai daddyn Ahmad yakirashi akan yazo zai aikeshi

Ahmad yace man sauke ni kawai nakoma gida idan na dawo daga aikan dad zan shigo mugaisa da amarya

Hakeem bai kalleshi yajuya da motar yamaida Ahmad gida kafin shikuma yakoma gida yanazuwa yayi parking a gurin parking dinsu """"


Laila tana jin shigowar mota tabude labulen window din ta
ai kuwa taga shine
Harfitowarsa tagani

Yamata kyau kuwa Dan Hakeem mai kyau ne bakarya
Da badan son kudin dayamusu yawaba ai Hakeem miji ne na nuna wa sa a

Hakeem ya kulle motarsa yayi part din mummy
Yanashiga yaga bata falo ya haura bedroom dinta

aikuwa tana can tana ninkin kayan ta tana jerawa a sif

Yashigo yace assalamualaikum mummy na

Cikin murmushi mummy tace Dan mummy yakake

Dafatan dai katashi lafiya ko

Hakeem yace lafiya qalau daliba kawo kiga ni koma kawai kizauna muyi hira

Mummy hafsat ta nemi gefen bed din ta tazauna

Tsaf Hakeem yagyara wa mummy kayan ta yasake gyara mata bedroom din kafin yace mummy kinci abinci kuwa

Mummy tayi dariya tace kaima dai tsokanata kake yaushe zankai har wannan time ban ci abinciba "'''

Hakeem yayi dariya yace acici
nasan ai dama agurinki na dauko ci

Mummy tayi dariya tace a a nikarka min sharri

Mummy tace ba wannan ba ma
Dama inason magana dakai

Hakeem yadawo da hankalinsa kanta

Tace Dan albarka jiya ba agida ka kwanaba hakane

Hakeem yace hakane mummy a gidansu Ahmad na kwana


Mummy tace ai baka kyauta ba
Tunda anriga andaura dole zamu rungumi kaddara
Yanzu dai Laila tariga zama matarka
Dan haka ina umartarka da karka wulankanta aure

Aure ba abin wasabane duk kuma wani sharrinsu zai koma kansune da izinin Allah bazasu taba tasiri akanmu ba

Hakeem yace ai mummy ki kwatar da Hankalinki adduoi na tsarin jiki ba Wanda bamayi agidan nan dai
Dan haka ba abinda zasu iya mana

Mummy tace Allah yasa Dan albarka acigaba da kula da addua Dan ina tsoron sharrin mutane """"""


Bayan sun gama magana yace Mum zanje wajen Daddy a office Dan kinsan jibi mukeson dagawa fa Hutu yakare zamuje mutattauna


Mummy tace kadage dai sai katafi ajibinko

To da amaryar zakatafi Hakeem yace Allah yasauwake tayi zamanta ba inda zantafi da ita

Mummy tace bazan maka doleba amma ka tabbatar komai kabari a kafin tafi

Hakeem yace insha Allah mummy

Yace barinje gurin daddyn

Mummy hafsat tace a a kafara shiga kaduba yar mutane tukun ko
Koba komai fa yar uwarkace

Yace to mummy sai na dawo
Tana jin dadin inda Dan nata baya mata musu

Hakeem yashiga part din shi
Direct bedroom din shi yawuce
Yaje yadauko wani file kafin yasake fitowa

Laila kuwa basan shigowarshi ba fitanshi tagani
aikuwa kafin yakarasa fita tasha gabanshi

Yace lafiya kuwa zaki sha gabana haka

Laila cikin yanga tace Haba Abdul ya kake min wasu Abu kaman ba mijina kuma Dan uwana ba Dan Allah kadawo muzauna kona minti biyar ne .

Hakeem ya watsa mata wani kallo Wanda dakanta tabashi hanya yawuce abinshi zuwa office din dad dinsa

Hankalin Laila yatashi tace anya kuwa wannan
Mutum """


********
Da daddare bayan daddy da Hakeem sundawo sunci abinci can wajen karfe goma
Mummy tace Dan albarka tashi katafi kabar Laila ita kadai

Badan yasoba yamusu sai safe ya wuce part dinsa ,
Yana shiga falon Laila ta na kashe wayarta dasukaga gama da gawarta

Ko kallo bata isheshiba ya wuce abinsa zuwa bedroom dinsa

Yanashiga wanka yafada

Yana fitowa sukayi ido hudu da Laila cikin wasu arnar kayan bacci wato sleeping dress kenan

Kallo daya yamata yakau da kanshi
Danshi idan ya raina kasuwa ko sauto baya mata

Ya goge jikinsa yashafa mayukansa masu kamshi kafin yasaka night Wear din shi

Ya kwanta tare da kashe wutar dakin """""


ai kuwa Laila tafashe da kuka
Tun abin na bashi haushi har yagaji yace dalla malama kitashi kifita min adaki

Cikin kuka tace Haba

2 Comments On AKWAI LOKACI
avatar
musa-6-3-2

1 year ago

Reply

Akwai lokaci

avatar
oumara-wassai

1 year ago

Reply

Replying to musa-6-3-2

17866

Please Login or Register in order to submit comment