Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaskiya nima anan naba da goyan bayan tafitar da miji kafin nan da tagama secondary school

Hajiya rukayya tace wannan ba abin muwabane
Abamu nan wani lokaci saurayinta zaizo dakanshi yagaisheku aitana dashi


Alhaji abubakar yace to alhamdullila Dan Allah komai ya wuce

Ke Laila ba wa mijinki hakuri
aikuwa hajiya rukayya tace ya za ace tabashi hakuri bayan shiyakamata yabata hakuri daya dauki hanu ya tsinka mata mari acikin mutane


Ganin abinda hajiya rukayya takeyi yasa Hakeem barin falon yayi sashinsa

Yana fita suka hadu da Ahmad
Hakeem yace ango

Ahmad yace komaidai yakoma dai dai ko Hakeem yace barin shiga nashirya nazo muwuce

Muje musallami friends dinmu na nesa

Ahmad yace karka damu nagama komai

Hakeem yace yanzu har ka rakasu airport Ahmad yace kwarai

Hakeem yace amayar fa Ahmad yayi murmushi yace ai andade da tafiya da amarya

Dan dazu nakirata harsun huta ma

Yan uwanta ma sun kamo hanyar dawowa

Hakeem yace to ai sai musamu mushirya muwuce muma ko karnayi laifi dayawa agurin Madam Aisha

Ahmad yayi murmushi yace a haba aitasan komai

Idan taga bamuzo ba tasan abinda yatsare mu

Hakeem yace yau zaka shiga dakin amaryar ka

Barima kagani Hakeem yashige sashinsa

Yafada bathroom yayi wanka
Yana gama shiri cikin shadda marun colour ya balain masa kyau kamar danshi akayi shaddar

Yana fesa turare Laila tashigo
Tace daddyn meenat naga kaman tafiya zakayi baka sallamemuba

Hakeem ya watsa mata wani kallo

Yace mekuke bukata tace kayan abinci da na amfanin gida yace kizauna kirubuta duk abinda bukata zansa driver yakawo muku

Daga yau nabar baki daman da kikesamu harkike ganin kaman kinfi karfina sai yadda kikayi dani ko

cikin tashin Hankali Laila tace Dan Allah karkamin wannan horon kasan nasaba sayan abinda nake bukata da kaina


Hakeem yayi murmushi mugunta yace nawa nakebaki dama

Laila tace dubu Dari uku duk wata

Hakeem yace hakane ko ta ce a hakane

Yace kedawa nabari agidan nan tace nikadai

Yace good yanzu duk wata zanturo miki dubu hamsin

Kekadai dai nasan zasu isheki

Yana gama fadan haka yayi waje da brief case dinshi



Haukane Kane kawai Laila batayi ba
Amma hankalinsa yatashi sosai nan tadauki gyalanta tayi gurin mahaifiyarta hajiya rukayya


****
Bayan wata shida professor Hakeem zaune kan kujerar office din shi

Yadauki wayarshi yakira yaya shamsu

Ya shamsu yashigo yace Barka dai yallabai sannu da aiki Hakeem yayi murmushi yace yauwa malam shamsu

Yace ga wannan ya shamsu yakarba yace ina zankai yallabai

Hakeem yayi murmushi yace nakane malam shamsu zaka kaiya dubawa kagani

Ya shamsu yabude Aikuwa ya shamsu ya dago ido yakalli PROF Hakeem

Yace admission fa nake gani yallabai

Hakeem yace yes nasan kana da burin karatu a rayuwarka

Iyakacin zamana da kai na lura kai mutum ne mai son karatu

So yanzu ga dama nan malam shamsu zaka iya farawa nagama komai har registration da komai sai dai ka kai credentials dinka asa maka a file

Kuma daga Level two zakafara nariga nayi komai

A department of business administration


Ya shamsu baisan lokacin da tashiba yace yallabai gaskiya ba abinda zance da sai dai Allah yabaka abinda kake nema duniya da lahira
Allah ya jikan mahaifanka ya ramaka zuria

Hakeem yace ameen malam shamsu na gode kwarai da adduarka a gareni

Sai dai ni har yanzu baka taba tambayata wani Abu da yashafi rayuwata ba malam shamsu koba bukatar sanin daga ina nafito ne

Ya shamsu yayi murmushi yace zanso sanin tarihinka dakuma tarihin nagartarka a rayuwar alumma


Nan professor Hakeem yayi murmushi
Yabashi labarin rayuwarshi kaf bai boye mai komai ba


Ya shamsu yaja numfashi yace yanzu tun kana 20years kayi aure kenan

Hakeem yace kwaraikuwa ina da 17 year old girl yanzu haka


Da mamaki ya shamsu ya kalleshi yace masha Allah
Gaskiya kai kam duk abinda ake nema a rayuwa Allah yabaka


Hakeem yace zakasan daughter nawa ma ai duk sati tana zuwa ranar alhamis

Ya shamsu ko wacce kake cewa amina

Hakeem yace yes ita nake nufi


Ya shamsu yayi shiru yace am sorry sir wallahi duk azatona madam dinkace


Hakeem yayi murmushi yace 'yata ne nacikina

Ya shamsu yace masha Allah wallahi gaskiya labarinka ya burgeni


Bude kofar office akayi Prof Ahmad ne yashigo yace

Kace kuna tare da malam shamsu ne Hakeem yace ai tundazu muke hira anan

Ahmad yabawa ya shamsu hanu sukayi gaisa

Ahmad yace wa Hakeem madam fa tagama abincin rana yakamata muje muyi lunch

Hakeem yace gaskiya dai nima yaka mata nasan abinyi

Kaga madam Aisha sai tadinga hutawa ko

Ahmad yace Aisha ce zagaji wai caf yanzu kasan Allah da zankoma inje cin abinci nikadai sai tambayi ina kake baka biyoni ba
Duk randa kake azumi haka nake fama da ita



Hakeem yace Allah sarki madam tana tausaya wa marayan Allah

Ahmad yayi murmushi yace maraya a kano ba

Ahmad ya kalli ya shamsu yace malam shamsu gaskiya yau Na kamaka sai munje kaci abincin amarya

Hakeem yace aifa dai kam tunda shi yana mana rowan abincin amaryarsa da kuma ladan da zamu samu wajen gaida su umma da Abba


Ya shamsu yayi murmushi yace bahaka bane banyi tunanin inna gayyaceku zakujeba shiyasa

Hakeem yayi murmushi yace saboda gamu aljanu bama cikin jinsin mutane ko

Ahmad yayi dariya yace zamu baka mamaki sai dai kaganmu agidanka

Ya shamsu yace ina zuba ido ,nan dai kyar ya shamsu ya yarda suka je dashi cin lunch



Suna kan dining din Ahmad suna cin abinci itakuma Aisha tana kan two sitter

Tace wa Ahmad honey yaushe zaka kaini yawo kasan fa bansan kowaba a kano kuma inason inga gari

Ahmad yace zan hadaki da kawance da madam din malam shamsu kinga saikije mata itama tazo miki
amma sai malam shamsu ya amince


Ya shamsu yayi dariya yace ina zata iya erea mu ai sai mu

Hakeem yace kaidai kawai malam shamsu kace bazaka bar madam dinka suyi zumunciba


Ya shamsu yayi murmushi yace shikenan Allah yashige mana gaba

Sukace amin


Dazasu tafi ne Aisha tace wa ya shamsu Dan Allah agaisar mata da kawarta kafin suhadu

Ya shamsu yace zataji insha Allah


****

Bayan wata biyu da fara zuwa makarantar shi
Ankawo sadakin Husnah
Harda kayan lefe akwati gomashabiyu cas


Sadaki kuma naira dubu Dari biyu

Yanzu haka ana jiran suyi waec da neco ne kawai asha biki

Shakuwa ce maitsanani da kaunar juna tsakanin copper bash da Husnah


***
Meenat zaune kan carpet dinsu hajiya rukayya tadawo daga tafiyan datayine wajen boka Dan karbowa meenat maganin MALLAKA da zata mallake copper bash yazama nata

Hajiya rukayya tace a abinci zaki zuba mishi idan yaci zai kamu da soyayyarki Wanda ko uwarsa bazai mata Sannan kuma zaiji ya tsani Husnah aduniya

Cikin farincki amina tace kai Allah yabar minke kakus dina


Laila dake gefe tana kallonsu Dan itama jiya tazo

Laila tace hajiya Nifa ba abinda kika karbo min Akan daddyn meenat

Hajiya rukayya tace ai wannan yaro fa asiri bazai kamashi ba sai dai kawai musa a kawar mana dashi
Har lahira kinga masamu dukiya muyi yadda mukeso da shi



Meenat caf daddyn nawa za a kashe wallahi bazaiyi yiwuba
Haka kawai ita mummyn bata San yadda zata karbi kudi a ahanunshi ba sai ankasheshi


Hajiya rukayya tace to ai murasa yadda zamuyi da wannan uban naki ne jikalle

Meenat tace natabbata baza arasa wani hanyar ba kudaiyi tunanin




Husnah zaune a dakin amarya kubra tana asigment dinta

Kubra tace kedai Husnah kinji dadi wallahi wannan irin gashi aikoda shi zaki yaki mijinki balantana ga uwa uba kyau da diri duk

Allah yabaki Husnah tadago manyan idonta ta kalli kubra tayi murmushi

Tace anty kubra kenan sai kace ke

Kubra tayi murmushi tace zakicimin fuska ko ai idan dai kina guri muai saidai muyi shiru


Husnah tace banda zuga fa matar yaya

Husnah ta fashe da dariya ita kadai

Sai kubra tace meyabaki dariya
Husnah tace kawai danku nakeson gani keda yaya wannan irin kyau da kyau ai sai dai kuhaifo mana aljani Dan kyau fa

Kafin Husnah takarasa maganarta kubra ta dauki pilon kujerarta zata kwadawa Husnah

Husnah ta tashi ta gudu dai dai shigowar ya shamsu

Yace lafiya kekuma Husnah tace Lafiya qlw ya shamsu

anty kubra ce ta biyoni

Umma dake kan sallaya a faranda tace o keda kubra dai zanga ranar rabuwanku akwai drama

Ya shamsu yayi murmushi yace sai tabita ai

Umma tayi murmushi tace andawo Dan albarka ya makarantar

Ya shamsu yace alhamdulillah umma bara nayi wanka sai nazo muyi hira umma tace

To banana

Ya shamsu yashiga dakinsa yasami kubra zaune ta tashi tana mishi sannu da da wowa

Yayi murmushi Dan kullum son matanshi karuwa yakeyi saboda yadda take matukar mutunta 'yan uwanshi hakan nasa yana Dada jinta cikin ranshi

Murmushi yasakar mata yace kamu hanunta yace meya hadaki da kanwartaki

Kubra ta yi murmushi tace tsokanata tayi shiyasa tagudu

Wai karmu haifi aljanu Dan kyau fa

Ya shamsu yayi dariya yace ai haka tace
Shiyasa na tambayeta tamin shiru



Washagari da safe bayan anfito break sai copper bash yakira Husnah office din sa Dan ta serving din abinci Dan baya break shima sai goma

Shiyasa daga gida akekawo mishi

Ba kullum yake kiran Husnah ba Dan idan yakirata bata zuwa Dan kare mutuncin kanta
Ba kullum ana ganinta a office din shi ba


Suna zaune itada meenat wayarta yayi kara ta dauka tace aslammu ailaikum

Yace wa alaikumussalam my love

Husnah tayi murmushi tace inajinka ranka yadade

Yace alfarma nake nema kizo Dan Allah ki serving dina break fast

Husnah takalli meenat tace kice to Dan Allah

Husnah tace shikenan ganin nan zuwa

Husnah takashe wayar ta kalli meenat tace meyasa kikasa na amsa mishi

Meenat tace tace haba kekuwa Dan ya roki alfarmar yau dai ai sai kiyi mishi

Husnah tace bazaki gane bane
amma tashi muje kiraka ni dama abinda meenat kesonji


Suna isa office din copper bash

Yace wa amina taje cikin motarahi zataga basket din abinci ta dauko mishi


Aikuwa amina cike da farinciki ta wuce class dinsu ta dauko maganin ta da zata sawa bash

Sai da ta bude flask din ta zuzzuba dama soyayyan doya da kwai ne

Sai ruwan tea

Aikuwa ta zuba ta dauka takai mai
Husnah tayi serving dinshi

Yayi dai dai lokacin komarwar su class

Husnah tace zata wuce class yace ita bazataciba
Tace ai yau alhamis suna tana azumi

Yace yayi kyau kikula min da kanki kinji ko

Tayi murmushi dimple dinta suka lutsa yace I like your smile

Husnah tace thanks

Ta wuce zuwa class Wanda tuni meenat tarigata


Yagama break dinshi tsaf



Washagari jumma a

Dama bashir yasaba zuwa duk Jumma a

Husnah zaune tagama shirinta tsaf bashir kawai take jira

Kubra tace gaskiya dai tunda yasaba kiranki kuma yasaba zuwa yakamata kikarashi kiji kolafiya

Husnah ta yarda da shawarar anty kubra

Takira bashir yakai sau goma amma yaki dauka sai a kiran karshe

Yadauka yace dalla malama me na damuna haka

Kebari nafada miki karkisake kirana daga yau banza Mara mutunci

Na tsaneki Husnah bana son jin sunanki kifita a rayuwata

Sadakina da kayan aurena duk za azo karba kafin yafadi wata magana

Husnah ta yanke jiki ta fadi

Ya yi dai dai da shigowar kubra

Aikuwa kubra tayi ihu umma da abba da ya shamsu suka zo



Next page

Your comments is needed fans

Ina dadin comment din Ku fan's=ØÞ=ØÞ=ØÞ=ØÞ



Ina alfahari da Ku =ØMÜ=ØMÜ=ØMÜ

=ØÝÜ=ØÝÜ=ØÝÜ=ØÝÜ=ØÖÜ=ØÖÜ=ØÖÜ
[05/05, 11:08 AM] UMMU AFAN <Ø9ß: <Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


<Ø—ßHAKKIN MALLAKA NA UMMU AFAN <Ø—ß


<Ø9ß<Ø9ßFIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATION<Ø9ß<Ø9ß

<Ø9ßF.C.T.W.A<Ø9ß



<Ø9ßHOME OF QUALITIES AND TRUSTED WRITERS OF THE NATION<Ø9ß



<Ø—ßDEDICATE THIS PAGE TO MOM IMAN &HANIFA
MUCH LOVE TO YOUR COMMENTS SIS
KEEP IT UP<Ø—ß

Ina alfahari daku masoya novel din AKWAI LOKACI

daya bayan daya zakuji sunanku ina bin comments dinku sosai

Allah yabar zumunci=ØÞ=ØÞ=ØÞ=ØÞ=ØÞ=ØÞ





<Ø—ßAKWAI LOKACI<Ø—ß





<Ø—ßPAGE 61 to 65<Ø—ß





HUSNAH kan cinyar umma ansamata ruwa ta farfado

Ya shamsu yace Husnah kiyi magana meya haddasa miki wannan suman

Husnah ba baki sai kuka
Abba yace ke kubra kukinsan abinda yafaru

Kubra tace gaskiya dai ba abinda yafaru sai takira bashir
Bansan meyace mata ba kuma nasan tabbas abinda yasameta yana da alaka da bashir



Kafin suyi wata magana wasu mata sukayi sallama suka shigo

Umma ta sannunku da zuwa suka yauwa

Umma ta ce sannunku da zuwa sukace yauwa Allah yasa nan ne gidan su Husnah ba bata mukayi ba

Ya shamsu ya kallesu yace nan

Suka shiga yiwa gidan kallon wulankanci suna kebe baki

Dayar tace ni wallahi dama banga gamin kifi da kaska ba da za ace wai bashir yarsa gidan dazai nemi matar aure sai gidan matsiyata


Wato kubran ya shamsu wani takaici ya debeta ta tashi
Ta cakumo wuyar wacce tayi maganar

Ta wanke ta da mari zata kara mata ne ya shamsu yariketa

Kubra tace Dan Allah ya shamsu kabari
Nakara mata
Inbanda cin mutunci kishigo har gidan mu kuce zakuci mana zarafi

To wallahi ubanku yayi kadan

Ita wacce aka Mara tace kika mareni to wallahi sai kinyi da nasanin marina

Kuma abinda yakawo muda ma munzo abamu kayan auren mu da sadakinmu

Mai auren yace bayayi mudama bason gidan matsyata irinku mukeba

Cikin tace kune kuwa babban matsiyata wadda basusan darajan nagaba dasuba

Abba yace wa kubra shiga daki

Kubra tabi maganar Abba tayi dakin

Abba yace wa ya shamsu fito musu da kayansu

Ya shamsu yafito da kayan daya bayan daya

Umma ta ce kuna iya kwashewa kufita mana daga gida ko

Ita wacce aka Mara tace aiko bakuce mufita zamu fita ehe


Ya shamsu yace ke idan kina rashin kunyarki ya tsaya iya kan dai dai ke banda iyayena

Kwarjinin ya shamsu ya musu suka kasa mishi rashin kunyar


Nan da nan suka fara jidan kayansu suna fita dashi

Ya shamsu yashiga daki yadauko musu sadakinsu yakai musu har gurin mota

Yace gashi sai Ku hada basai wani yasake zuwa mana gida

Suka karba shiru Dan sunkasa magana ma



Ya shamsu yashiga gida yaga yadda Husnah take kuka yace kiyi shiru kidaina kuka kinji yar kanwata


Allah zai miki canji da mafi alkairi

Umma tace gaskiya yaron nan yabani mamaki yanzu memuka mishi da zai mana wannan cin mutunci


Abba yace ai sai agode wa Allah ba akaiga aurenba

Da anyi auren ne ya wulakanta mana yarinya ai bazamu ji dadi ba

Ya shamsu yayi ajiyan zuciya yace shiyasa ba kuwani maikudi ake yarda da soyayyrashi akan talaka ba

Yayi amfani da talaucin mu ne yasa har ya iya yin abin da yayi

Amma bakomai watarana sai labari

Shiyasa ni kwatata yanzu bazan sake wa Husnah auren mai kudi Ba

Gwamma ta auri dai dai ita sayi arzikin tare zaifi ganin mutuncinta

Umma ta ce wallahi na goyi bayanka
Dari bisa Dari

Abba yace muna namune kuma Allah na nasa Allah yazaba mana abinda yafi alkairi

Sukace amin

Nan akayi ta rarrashin Husnah da kyar tasamu tayi shiru


***

Satin Husnah biyu bata je makarantaba school ba saboda rashin Lafiya datayi

amma yanzu jikin alhamdullila
Dan tana ma shirin zuwa school gobe insha Allah


Washagari Monday da safe Husnah tashirya cikin sabon uniform dinta Wanda ya shamsu yadinka mata


Tayi kyau sosai tasaka read cap dinta da belt dinta na head girl

Bayan ta fito tayi wa umma sallama umma tace Allah miki lbarka kinje Dan kicire komai aranki

Tace umma namiki alkawari cire damuwa daga raina

Tawuce bangaren ya shamsu
Ta Dan bubbuga kofar ya shamsu tace ya shamsu nagama mutafi yace OK daman kenake jira

Suka fito tare da kubra tana rataye da jakar mijinta

Ta kalli Husnah tace kai tawan wallahi kinyi kyau sosai

Husnah tayi murmushi tace anty kubra kenan ya Shamsu

Mutafi kasan anty idan tafara sai tasa muyi latti

Kubra tayi murmushi tace to Dan Allah kisayo

Wannan kunun ayar da kike kawo min

Husnah tace karki damu
Zantaho miki dashi
Kubra yauwa kanwata


Nan dai ya shamsu da Husnah suka fita yatare musu keke napep




Yabata dari biyar tace kai yaya shamsu yamin yawa ai

Ya shamsu yace ai nasan bakya azumi Dan haka kiyi amfani dashi kiyi break karkizauna da yunwa

Husnah tace wallahi umma ce ta hanani yin azumin wai saina warke

Ya shamsu yace ai gaskiyar tane
Gwamma yar kanwata tayi katuwa

Husnah tayi murmushi tace nagode yaya

Ta shige cikin school dinsu

Tana shiga an buga assembly nan ada sauran prefect din suka tayata
Shirya yara Assembly

Nan dai Husnah ta hau kan stage tafara control din data sabayi


Bayan angama assembly principal ta aika akira mata head girl dinta Husnah

Tace mata nakiraki ne nabaki hakuri akan kinyi rashin Lafiya har natsawon sati biyu school bataje tadubokiba

Husnah tayi murmushi tace mummy ai an wakilta prefect sunje sun dubani

Mummy principal tayi murmushi tace ai duk da haka yakamata a hada da malamai

amma dai muna Neman afuwa
Husnah tace wallahi mummy bakomai aikema bakya gari da kinje

Nan mummy principal tace bata wani envelope tace ga wannan kikai gida

Husnah tace to mummy

Nan principal tabata daman ta koma class


Husnah nazuwa class taga meenat sai alokacin take zuwa

Husnah tayi murmushi tace ai wallahi aminyi bakida kirki
Banda Lafiya kokije kidubani ko

Amina ta kalleta sama da kasa tace Allah yabaki Lafiya

Abin yaba wa Husnah mamaki
Har zatayi magana sai Ku ma tafasa

Dagana kuma malamin su na
Math's yashigo

Ana cikin musu teaching wata daliba tayi excuse sir copper bash yana kiran anty amina Hakeem

Sir yace amina Hakeem
Meenat tace yes sir

Yace oya tashi kije
Kafin amina ta fita sai da tajiyo taga ko Husnah tana kallonta

Itakuwa Husnah batasan tanayi ba
Dan ita kosunan bashir bata son ji tatsaneshi sosai



Har aka fita break amina batadawo ba




******
Yauce su Husnah suke graduating a school dinsu

Aka kawata hall dinzasu yi taron aciki

Principal bata ba da damar graduating students Susa kayan gidaba wato personal wear's kenan

Shiyasa duk inda kaga SS 3 zaka gansu sunsha guga sunsha kyau

Dan ba hana suyi make up ba

Duk prefect kowacce da hulanta akanta sunjeru a kujera na musamman sai kuma sauran graduated students dinsuma suna nan akujera ta musamaman


Husnah ma duk 'yan gidansu sunzo mata Abba ne kawai baisamu zuwaba amma ya shamsu da anty kubra da umma duk sunzo

Amina Hakeem dakyar tasamu daddynta Hakeem yace zaizo

Ahmad da amaryarsa sai Hakeem sukazo sai mamanta da kuma hajiya rukayya duk sunzo

Hakeem tunda yazauna yake ta fama da wayarsa

Dagowar da Ahmad zaiyi yaga ai anzauna kusadashi
aikuwa dai ya shamsu ne da anty kubra umma kuma tanacan bangaren dattijai mata

Ahmad yace kaga ikon Allah malam shamsu kai ne anan kokuma wa

Ya shamsu yajuyo jin ankira sunanshi
aikuwa yaga su Ahmad da Hakeem
Hakeem ma jin an ambaci sunan malam shamsu

Yasa yadago mai suka yi murmushi gadayansu

Nan ya shamsu yabasu hanu suka gaisa

Yace wasuka zowa Ahmad yace daughter dinmu ai nan take karatu

Kaifa yace nikuma kanwata ce anan

Kubra tace ina wuninku Hakeem da Ahmad suka amsa

Ahmad yakalli inda madam dinshi Aisha take yatashi yaje yarada mata magana akunne aikuwa Aisha ta task da sauri

Tana zuwa ta kama hanun kubra tace alhamdullilahi yau dai nima na hadu da kawata

Kubra ma dayame wayayyiyace tace nima naji dadin haduwata dake

Nan Aisha taja hanun kubra suka koma gurin su daban


Nan kuma ya shamsu da Hakeem da Ahmad suka can gaba wajen special guest


Nan akafara taron da addua

Can principal tafara jawabinta kamaryadda aka saba

Daga can kuma ta ce itada kanta zatakira best student of the year

Wanda duk shekara akeba principal dama tazaba da kanta ta kuma bata kyauta duk karshen shekara haka akeyi


Wani daga cikin teachers dinsu ya tashi yakarbi Mike din hanun principal da list din hanunta


Yafara kiran suna kaman haka

Best student of the year
Kowa ya kasa kunne

ASMAU SULEIMAN SHAMSU

aikuwa duk student aka dauki tafi raf raf raf

Dan daga malamai har student sunsan Husnah ta cancanta sosai

Cikin nutsuwa Husnah ta tashi ta isa gurin principal
Nan principal tace wazata kira ya tayata karba
Husnah tace wa principal ya shamsu za akiramin

ya shamsu suna zaune duk hankalinsu yakoma kan head girl
Shi ya shamsu baifada musu wacece kanwar tashiba

Sai jisukayi ankira ya shamsu yatashi cike da alfahari da 'yar kanwarshi bata bashi kunya kokadan


Ahmad da Hakeem suka hada ido
Ahmad kaddai itace kanwar tashi

Hakeem yayi murmushi yace ga zahiri amma fa yarinyar taburgeni matuka
Yayi maganar yana kallonsu Husnah

Cike da mamaki Ahmad yakalli abokin nashi
am I dreaming ?
Man what are you saying

Hakeem bai kalleshiba murmushi kawai yayi ya dauke idonshi daga gurin su Husnah ya mayar da kanshi kan wayarshi


Murmushi Ahmad yayi dai dai lokacin ya shamsu yadawo yazauna

Ahmad yace kanwarkace ya shamsu yayi murmushi yace yar karamar kanwata kenan

Yace masha Allah
Allah ya albarkaci rayuwarta

Ya shamsu da Hakeem suka ce ameen

Daga nan kuma sai akafara ba wa prefect satificate dinsu ya rage sauran na social prefect da Head girl

Aka kira social prefect AMINA HAKEEM ABUBAKAR

Nan akabata sertificate dinta da kuma gift dinta maman Laila ita tayata karba

Hakeem kallo daya yamusu yacigaba da abinda yakeyi

Can akakira me gayya mai aiki wato head girl

Husnah taje ta karba itada yaya shamsu principal Tamika kyautar aka musu hoto

Duk wani kyauta da akerabawa Husnah ita takarbi na farko abin yaburge kowa ana karshen

Husna ta tashi zata karba sai kawai tafashe da kuka Dan tasan koba komai yayanta zaiyi alfahari da ita

Principal ta rungumeta tana share mata hawayen

Tace asmau Allah ya albarkaci rayuwarki

Ya shamsu yaji dadin adduar principal

Yace Ameen hajiya mungode Allah yabar zumunci


Nan fa students sukayi tazuwa suna daukar hoto da Husnah suna mata fatan alkairi

Masu bata gift nabata kai gaskiya Husnah tayi farin jini sosai har malamai suna tururruwar hoto da ita


Meenat zaune abin duniya yadameta tana matukar jin bakin ciki abin da kefaruwa da Husnah

Laila tace wai ita wannan yarinyar fa saikace aljana komai ta handame ita kadai

Meenat tace kyaleta dama yunwa ne yakawota school din Dan dama 'yar matsiyata ce

Scholarship taci tashigo

Hajiya rukayya dole ai yanzu naji batu


Motar school ce ta kaiwa Husnah gift dinta har gidan




****

PROFESSOR HAKEEM yana zaune cikin falonshi kusan sati kenan da graduation dinsu Husnah amma kullum da ita yake kwana da itayake tashi aranshi

Kuma tunda yake a rayuwarshi bai taba saka 'ya mace a rayuwarahi ba

Kuma a yadda ya fuskanci zuciyarshi takamau son 'yar baby nan

Shida kanshi yake wa kanshi dariya

Ya duba agogo yaga sai yanzu 8:30 nadare tayi
Yaje ya hada Kofi

Yanasha kadan yana tunanin Husnah

Abinda baisaniba shine Ahmad yadade a bakin kofa yana kallon abokin nashi daya fada shauki


Ahmad yayi gyaran murya hade da sallama

Hakeem yajiyo suka hada ido da Ahmad

Ahmad yace abokina wai meyake faruwa ne
Kwana biyu naganka kaman akwai wani Abu

Hakeem yayi murmushi tareda kurbar copee yace shine kabar matarka kazo gulma ko



Ahmad shima dariyar tare da dauko lemu maisanyi a fridge

Yadawo yazauna

Ahmad yace inkarashida gulma kaikaso

amma dai ni bazan bar nan ba sai kafada min


Hakeem yatashi yakoma bayan kujera yace
Ahmad am in love


Ahmad yayi dariya yace daman nasani


Duk wannan boye boyen naka duk kallonka nakeyi

amma gaskiya idan har kasamu yarinyar nan kayi sa a wallahi

Hakeem yace wace yarinya kenan tunda nidai ban fada wacce nakeso da bakinaba

Ahmad yayi dariya yace karka rainawa wa kanka hankali mana

Kawanwar shamsu koba hakabane

Hakeem yayi murmushi yace amma ya akayi kagane hakan dawuri

2 Comments On AKWAI LOKACI
avatar
musa-6-3-2

1 year ago

Reply

Akwai lokaci

avatar
oumara-wassai

1 year ago

Reply

Replying to musa-6-3-2

17866

Please Login or Register in order to submit comment