Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Abdul yanzu wannan shine zumuncin da iyayenmu suka hada muyi kenan

Hakeem yayi wani uban tsaki kafin yajuya ya kwanta abinshi

Can tace ai idan kai baka bukatata ni ina bukatarka

Bai kamata kahanani hakkina da Allah yarataya a wuyarka ba """"'

Tabbas yasan hakane kuma mummynshi ma ta mashi tuni akan haka
Koba komai gwamma yafita a hakkinta


Yajuya yace mata damuwarki kenan yasa aka miki aure ko
Kafin tayi magana ya bajadda ita akan bed din

Yacire sleeping dress din nata yayi wurgi da shi bako romance

Sai dai adduar da akeyi lokacin da miji zai sadu da iyalinsa

ai kuwa dai Laila tafada musu

Tagane shayi ruwane

Yanagama abin da zaiyi ya tureta ya kwanta abinshi

Ita kuwa Laila tana cikin farin ciki Dan ita yadda taji din ne kuma bazata iya hakuriba """""


Kullum zata kawo kan nata indai zai biya mata bukatarta kafin ta shekashi lahira taci dukiya

Nan itama ta kwanta bacci ya dauketa cike da farincikin kasancewarsu da Hakeem a Daren nan .


Washagari Hakeem kota kanta baiyiba yana gama shirinsa cikin wata yadi mai tsadar gaske iri daya ma sukayi da Ahmad

Yadin ash colour ne sai yasa bakin takalmi da hula Wanda akekira da senator

Duk Wanda yakalli Hakeem sai yasake kallonsa Dan ya hadu iya haduwa

Yana fitowa Laila ta tareshi tace abdul ga break fast dinka fa mai aiki tagama ,

Wani matsiyacin kallo yamata yace kinga nayi miki kama da mai cin abincin masu aiki """

Ban guri nawuce ni
Tabishi da kallo tace aikuwa sai dai idan bazaka ci abinci agidan nan ba Dan ko kwai ban iya soyawa tayi dadi batare da ya kone ba """



Hakeem suna break fast daddy yace mishi
Shi Ahmad din yashirya kuwa Dan naga kaman kai ka matsa kutafi

Hakeem yayi dariya yace bahaka bane dad kasan fa I want to be come professor like you kaga yakamata indage ko dad

Daddyn Hakeem yace hakane but please son take care of your self sosai kaji ko banda harka da mutanen banza """




Mummy tayi murmushi tace kai daddyn Hakeem duk komawarshi school saikayi mishi wannan nasihar yanzu fa babban mutum ne tunda ya ajiye iyali

Daddy yayi murmushi yace wai haka son
Shidai Hakeem baice komaiba

Daddy yace nifa wallhi ina mantawa yarinyar nan tana cikin gidan nan
Ya bara kace tazo akarya da itaba .

Hakeem yace daddy ai tana da mai aikinta har tagama komai sunci abincinsu

Daddy yace duk da hakadai ai itama yar gida ce

Mummy tace kasan alamarin yara sai a hankali
Kawai kabarsu nan dai mummy ta canja magana

Tace jirgin safe zakubi ko

Abdul Hakeem yace da asuba makuwa mummy tace aikuwa kaman nasani nagama hada ma komai

Mummy Allah yasa kinmin wanna cake din naki medadi

Tace ai duk abinda kasan ina maka ba abin da na rage

Cikin jin dadi Hakeem yace that's my mom Allah yabar minku iyayena

Daddy da mummy sukace ameen Allah yamaka albarka



Yauma da daddare sai da Laila takai kanta gurin Hakeem

Tun karfe uku yatashi yagama shirinsa tsaf bai Dade da gamawa ba Ahmad ya kira yace man kataho tafa nigani a air port ma

Hakeem yace OK gani nan
Yadauki cheque ya rubuta dubu Dari biyar yasama Laila akan bed
Da kuma short note


Yafita daddy da mummy shi kawai suke jira suka rakashi



Next page
Your comment is needed fan's

=ØÖÜ=ØÖÜ=Ø‹Ü=ØÝÜ=ØÝÜ=ØÝÜ
[30/04, 5:49 PM] UMMU AFAN <Ø9ß: =ØÖÜ=ØÖÜ=Ø‹Ü=ØÝÜ=ØÝÜ=ØÝÜ
<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß
BISSIMILLAHI RAHMANIR RAHIM

<Ø—ßHAKKIN MALLAKA NA UMMU AFAN<Ø—ß



DEDICATE THIS PAGE TO MY ONE AND ONLY HUSBAND
ABU AFAN (DOCTOR SULEIMAN)d'=Ø‹Ü




<ØßGORGEOUS WRITERS FORUM<Øß

<ØßG.W.F<Øß

HOME OF GORGEOUS INTELLIGENT AND EXPAERT WRITER'S WE ARE THE BEST AMONG THE REST



<ØßAKWAI LOKACI<Øß




<ØßPAGE 26 to 30 <Øß



Laila ta tayi taga ba Hakeem
Sai ta tashi tashiga tayi wanka tana fitowa idonta yakai kan takardar da ya ajiye mata

Tadauka ta duba taga cheque ne na kudi """""

Nan da tawashe baki tace kai tun yanzu bata gama rufe baki ba taga wani guntun takarda .

Tadauka taduba
Cewa yayi Nina wuce ga kudi nan

Idan kina bukatar wani Abu zaki iya samun mummy


Laila na gama karantawa ta wurgi da takardar tace kutuman uba Ashe tafiya yayi yabarni anan ,

Nida nake ta burin tafiya Saudi
Ashe ma badani zaitafiba """

Tadauki wayarta takira hajiya rukayya
Tanadawa Laila tafashe da kuka

Hajiya rukayya tace Lafiya kike kuka Laila cikin kukan Laila tace mama kinsan
Abdul Hakeem yakoma Saudi yau """


Maman tace yakoma fa kika ce
Lalle ma yaron nan wato badake zai wuce ba kenan """"

Laila tace ai niban Masan yatafi ba rubuta min yayi
amma yabarmin dubu dari biyar yace kuma idan ina bukatar wani Abu na sami mummynshi ,


Hajiya rukayya tace aikuwa sun ja wa Kansu
Nan da jibi kice kina bukatar kudi
Kinga sai musamu mufara shiri kafin yadawo ,

Laila tace to mama wallahi amma naji haushin rashin tafiya dani din nan dayayi ,

Hajiya rukayya tace kwantar da hankalinki zai dawo ne ai zai shigo hanunmu daga shi har iyayensa .

Yanzu zanzo gidan naki nakarbi kudin na ajiye su a wajena

ai gwamma ma da yatafi abinsa kinga matara kafin yashigo hanu mu kawar dashi banza"'''''


******
Bayan kwana biyu Laila taje gidansu daga nan itada mahaifiyarta suka wuce gidan hajiya suwaiba wato kakan Laila kenan ,

Suna isa hajiya suwaiba takira hajiya larai kishiyar suka shige can dakin hajiya suwaiba
Laila ta kwantar da kanta akan cinyar kakarta

Nan hajiya rukayya tafada musu komai abin da Hakeem ya ma Laila

Hajiya suwaiba tashafa kan rukayya tace hakuri kinji jikalle zai shigo hanun mu ne kinji ko ,

Dazaran yashigo hanun mu sai yadda kikayi dashi kinji ko
Cikin jin dadi Laila tace Allah yasa haka kakalle na

Dakuwa kinga gata Dan sai na canja maki gida kekadai basai da wannan tsohon ba

Hajiya rukayya tace a lalle ma uban nawa ko

Hajiya larai tace Dana dashi aka ware

Hajiya suwaiba tace a dinta ji anwarekun

Nan dai suka ta kulla tsiya

Sai can wajen karfe goma na dare kafin Laila ta tashi tayi hanyar gida
Dan dama ita tasaba da driving din dare ,


tana shiga maigadi yabude mata gate din yana gaisheta ko ta amsa mai .

Tana parking sai daddyn Hakeem yafito yace Laila daga ina a wannan Daren haka
Laila tace daddy daga gidansu alhaji nake a can na wuni .

Daddy yagane wani alhaji take nufi wato alhajinsa,
Yace kin tabbata tace a daddy kakira ma katambaya

Yace a a shikenan karkisake kai dare a waje haka kinji ko tace naji Daddy

Yace maza wuce dakin kin dare yayi
Namishi saida safe

Tana shiga falonta tayi wurgi da gyalenta tace nifa bana son sa ido haka kawai mutum yafita amma ana gadinsa



*****
Bayan wata biyu Laila ce kwace cikin lallausar kujerun falon Hakeem tana kallo
Sai tafara jin tashin zuciya

Ta tashi tayi hanyar bathroom tafara amai sosai take amai kaman zata fitar da kayan cikin ta

Kanwarta suby wacce taci sunan hajiya suwaiba ce tazo
Tana ta sallama amma shiru
Dan tunda Hakeem ya tafi suby tadawo gidan gurin yarta ,

Itama dai duk halin nasu dayane da yaruwarta

Taje siyo wa Laila balangune a bakin titi

Taduba bedroom din Laila bata ganta ba tace anty Laila da karfi

Can ta duba bathroom din falon Hakeem aikuwa nan taganta tayi sharaf ,

aikuwa suby ta rude ganin yar uwar tata a kasa jiki ba karfi tadauki waya takira uwarsu hajiya rukayya tafada mata tace gatanan zuwa


Can dai taga karfa Laila ta mutu Dan haka sai ta
Tashi tayi hanyar part din mom din Hakeem

Mummy hafsat tana kitchen Dan daura abincin rana sai taga suby kaman anjifota

Tace lafiya kuwa suwaiba zakishigo ba sallama
Suwaiba tace kiyi hakuri mummy anty laila ce balafiya ,

Mummy hafsat tace meyasameta tace wallahi bansaniba nima naje aika kafin nadawo nasameta a haka

Mummyn Hakeem tace wace muje naganta
Wannan shine farkon shigowar mummy hafsat part din Dan nata

Kusan atare suka iso da Maman su Lalai hajiya rukayya

Mummy hafsat tace a a yaya ashekema kinzo

Hajiya rukayya tace a gani nan ai

Mummy hafsat tace bara na dauko mota akaita asibiti ko

Hajiya rukayya tace duk yadda kikayi

Mummy hafsat tace afito da ita mutafi ko

Hajiya rukayya ta kalli mummy hafsat wato ita bazata kamata afita da ita ba sai dai tabasu command

Hajiya rukayya da suby suka kama Laila zuwa mota

Mummy hafsat ita taja motar zuwa hospital

Bayan gwaje gwajen da aka wa Laila likita yagano tana da cikin wata biyu

aikuwa hajiya rukayya da suby dama ita kanta Lailar murna suka hauyi sosai ko kunyar mummy hafsat basaji


Itadai mummy hafsat tunda doctor yace Laila cikine da ita

Bata ce komai ba tausayi kawai danta yabata hada zuria da irin hajiya suwaiba

Nan dai tana ta tunanin zuci

Hajiya rukayya tace hafsat bakice komai ba zamuyi jika mummy hafsat tayi murmushi kawai tace Allah yaraba lafiya

Yanzu dai bari na sami doctor nabiya komai sai muzo muwuce gida

Hajiya rukayya tace ai inaganin zan wuce da ita gida kawai idan tasamu lafiya sai ta koma dakinta


Mummy hafsat tace badamuwa hakan ma yayi zama Ku iya bari saita haihu sata dawo

Hajiya rukayya maganar mummy hafsat yamata zafi sosai wato subasa ma bukatar zaman Lailar agidan kenan

Hajiya rukayya tace tokuma idan mijinta yadawo fa

Mummy hafsat tayi dariya tace ai daga har ta haihu son bazai sami damar zuwa ba

Hajiya rukayya tace duk karatun ne zaisa yaki dawowa gida

ai yanzu idan kika kirashi kikafada mishi zai iya samin lokaci yazo yaga matarahi kafin yakoma ko

Mummy hafsat tace sai dai nabaku numbar nashi ita lailar saita kira tafada mishi

Cike da jin haushi hajiya rukayya tace ai ashikenan takira tafada mishi da kanta


Mummy hafsat tace dayafi dai bara na biya kudin nazo mutafi ko

Hajiya rukayya tace a a kibarshi kawai driver na zaizo yanzu yamaida mu gida

Mummy hafsat tace to Allah yabata lafiya ni na wuce


Laila tayi saurin cewa mummy baki bani numbar abdulhakeem dinba

Mummy tace OK kawa wayar taki na samiki

Laila Tamika wa mummy hafsat wayar
Nan tasamata numbar HAKEEM

Laila tace thanks mom

Mummy Hakeem tawuce abinta


aikuwa tana fita hajiya rukayya tace zanyi maganinkine

Muza ayi wa wulakanci duk abin mutaum dai
Ciki dai sai an haife shi tsaf
Ta kalli Laila tace kekuma harda wani godiya Dan anbaki numbar mijinki

Suby tayi dariya tace kai mama kaman Bakisan halin anty Laila ba
Tasan metakeyi fa

Laila tayi dariya tace Haba mama anfada miki Dan Allah nayi godiyar caf

Nan dai sukayi gidan hajiya suwaiba suka shaida mata abin farin

aikuwa harda gud'a hajiya suwaiba tayi Dan murna tace kaman muzuba ruwa a kasa musha Dan dadi

Hajiya rukayya tace kinga yanzu saimuyi addua ta haifi namiji Dan mukasa mutsare gidan

aikuwa hajiya suwaiba tace ai namijin ne ma zata Haifa kuzuba ido kugani

ai tunada wuri zamuje gurin malamin nan yabamu taimako

Haka dai sukulla wannan su kulla wancan


*****

Mummy hafsat bayan daddy ya dawo gida ta shaida mishi abin dake faruwa

Daddyn Hakeem yace kai amma naji dadi Allah yaraba lafiya

Kice son dina yagirma fa
Harda da d'a

Mummy dai bata ce komai ba
Yace ai sai a tura musu kudin dazai ishesu kula da ita abin da kecikinta

Mummy hafsat tayi murmushi tace hakane


Nan daddy yakira yayarshi wato hajiya rukayya maman laila

Tana ganin kiran daddyn Hakeem tasan sunwarke Dan tasan zai jikasu da kudi

Nan da nan tadaga wayar daddyn Hakeem yafara gaisheta kafin yace yaji abin farinciki Allah yaraba lafiya

Sannan kuma inason kuturo da account number dazanturo muku da abinda zatayi anfani dashi
aikuwa farinciki Yakama hajiya rukayya tace yanzu kuwa zanturo
angode fa Allah yakara arziki

Tunda yake bai taba jinta tamishi godiya ba sai yau yace bakomai
Mudai fatanmu dai Allah yarabasu lafiya

Ameen hajiya rukayya tace takashe wayar nan da nan taba wa suby wayar tace ta tura wa daddyn Hakeem account number din Laila


aikuwa suby bata Dade da turawaba sukaji alert din dubu Dari takwas cas

aikuwa murna awajen su kaman me

Hajiya rukayya tace wanna ma ai kadanne ne

Dan nasan nan da wani lokaci zai kara mana

Nan dai Laila ta dauki wayarta takira Hakeem sai da yayi ta ringing kafin yadauki
Tare da sallama cikin kwarewa da harshen larabci Dan bazaka kadauka bahaushebane

Can yace dawa nake magana please

Cikin sauri Laila tace Laila ce
Hakeem yace inajinki ya akayi

Nan tafada mishi what's kina da ciki
Laila tace a mummynka cema takaini asibiti

Hakeem yaja numfashi yace Allah yasauke ki lafiya daga haka baikara cewa komai ba yakashe wayarsa

Laila tabi wayar da kallo ta kalli mahaifiyarta tace mama kodai shima baya farinciki da cikin ne

Suby tace kai bahaka bane kinsan halin ya Abdul yanzu hakama murna ne yasa yakashe wayar

Hajiya rukayya tace komai dai menene shine dai uban d'a

Da su so da karsu so duk uwa ubansu daya can ta matse musu


*****
Hakeem bayan ya kashe wayar ya kalli Ahmad dake fire musu doya
Dan basa cin abincin waje

Yace man kasan meye kuwa
Ahmad yace saika fada

Hakeem yace wai Laila cikine da ita har na wata biyu

Cike da farinciki Ahmad ya ajiye wukar yadaga hanu sama
Yace Allah mungode maka
Wai mune zamu baba

Hakeem ya watsa mishi harara
Yace dadina da kai Ahmad yarinta wallahi

Ahmad yace nayarda yarinta nedan gaskiya kam yanzu fa ka girmeni tunda gashi kana shirin ajiye baby

Hakeem yace please man muyi maganar arziki mana
Nifa harga Allah banso samun da daga jikin lailaba
amma tunda Allah yabani Allah ya albarkaci abinda za a Haifa

Ahmad yace adduar kenan kawai
Allah yashige mana gaba
Nan Hakeem yace ameen



*******
Bayan wata bakwai
Abubuwa da dama sunfaru

Su hajiya dai an tatsi Daddy Dan abin kadan zasuce a turo kudi

**
Yau laraba Laila ta tashi da nakuda
Sukayi da ita hospital
Nan da nan aka shiga da ita labour room

Mummy hafsat itama ana fada mata tazo asibitin daddy ne yasauketa kafin yawuce office bayan kaman awa hudu da shigarta

Ta haifo yarinyarta maikama da ita sak

Aka gyarasu itada babyn kafin akazo sanardasu mummy

ana ce ta haihu sukayi cikin dakin dasauri banda mummy hafsat
Tace wa likitar me akasamu likita taçe mace

Mummy Hafsat tace Allah yaraya

Takira daddy tafada mishi
Yace gashinan zuwa

Su hajiya kuwa ganin Allah baicika musu burinsuba yasa sukacika tam kaman zasu fashe

amma ganin yadda daddy yake farinciki da samunjika yasa suka kwantar da hankalinsu kadan


Nan daddy yakira Hakeem yafada mishi Hakeem yace Allah yaraya Daddy yace Ameen Ameen

Yakamata kasamu lokaci kazo kaga yarinyar da ita Lailar ko

Hakeem yace ai daddy bayanzu Dan karatu yafara zafi sosai sai dai mumsami time zanshigo


Daddy yace Allah yamuku albarka inashi Ahmad din
Hakeem yace yashiga wanka

Nan sukayi sallama da daddy


Ranar suna yarinya taci sunan maman daddy wato amina

Mahaifiyar daddyn Hakeem kenan marigayiya

Alhaji shuaib yasaka sunan da kanshi ba ma daddynba


Haka Laila tacigaba da rainon yarta Amina



*********"********

Tofa
Yanzu akafara kubiyo ummu afan

Your comment is needed fans=ØÞ=ØÞ=ØÞ=ØÞ=ØÞ



=ØÝÜ=ØÝÜ=ØÖÜ=ØÖÜ
[30/04, 5:51 PM] UMMU AFAN <Ø9ß: =ØÝÜ=ØÖÜ=ØÖÜ
<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß
BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM




<Ø—ßHAKKIN MALLAKA NA UMMU AFAN<Ø—ß


DEDICATE THIS PAGE TO MY ONE AND ONLY HUSBAND ABU AFAN (DOCTOR SULAIMAN)d'=Ø‹Ü



<ØßGORGEOUS WRITERS FORUM<Øß


<ØßG.W.F<Øß

HOME OF GORGEOUS INTELLIGENT AND EXPERT WE ARE THE BEST AMONG THE REST



<ØßAkWAI LOKACI <Øß




<ØßPAGE 31 to 35<Øß



Laila kwance take tana danna wayarta
Yayinda hajiya rukayya takeba wa Amina cerelack

Hajiya rukayya tace kinga wasa wasa fa watan meenat shadaya amma amma haryanzu mahaifinta baizoba


Suby tace wai Ku meye kuka damu sai yadawo ne bakusan idan yadawo Baku basamun abinda kuke samu yanzu ba """""


Laila tace nimadai haka nagani
Nifa wallahi tunda acikamin jaka da abinda nakeso yashekara goma ma baizoba ba abinda yadameni


Hajiya rukayya tace duk kurinta ne yake damunku inba yarinta ba ai wallahi idan yashigo hanu zamufi yadda muke yanzu

Dan sai abinda tace zaibata komai ta tambaya zaiyi jiki na bari

amma hakan bazaiyu ba sai
Yaci abinci da maganin har na wajen wata daya inji malam

To ta yaya hakan zaifaru idan bata jawo shi jikinta ba

Laila tace kuma fa hakane mama yanzu manene shawararki mama


Hajiya rukayya tace yauwa anzo gun danakeson azo

Kinga yanzu abinda zakiyi ke Laila kisamu Daddyn Hakeem kice kizakibi mijinki can saudin


Nasan shi da hangen nesa bazaiso shiga hakkin waniba

Idan kikaje can duk wani Abu na biyayyya ki kirkiro kiringa mishi inda zamusamu yasaki jiki dake sosai inda har zaki bashi abinci kuma yaci


Laila tace to mama yanzu dai zanshirya na tafi gidan mummy hafsat
Zanfada wa daddy komai

Hajiya rukayya tace yauwa yar gari tashi maza kishirya kiyi kama hanya

Suby tace anty Laila zanrakaki
Lailatace shirya muje

Hajiya rukayya tace kuje kawai kubar min yarinyar

Laila tace dama bazamu jeda itaba



****
Laila sukayi sallama a falon mummyn hafsat tana zaune tace a a

Laila kune atafe

Laila tace a mummy Allah yasa daddy na nan
Munzo gurinshi ne

Mummy hafsat idan da sabo tasaba da zuwa Neman daddy agunsu Laila

Mummy tace yanan yanzu zaishigo ya fita sallah ne

Nan su Laila suka zauna zaman jiran daddy

aikuwa daddy shigowa suka gaisa
Yace Lafiya kuwa Laila kokuna bukatar wani abunne

Laila tafada mashi damuwarta nason bin mijinta

Daddy yace wannan ba wani abinda damuwa bane

Kishirya kawai kije kiyi passport agama komai kafin jibi sai kitafi

Laila tace To daddy Allah yakara girma yace Ameen
Ina amaryar tawa

Suby tace tana wajen hajiya

Yace to ace angonta na gaisheta

Nan suka wa mummy sallama suka fita


Daddy ya kalli mummy yace Lafiya kuwa mummyn Hakeem

Mummy tace wallahi alhaji mutanen kotata ban yarda dasuba
Mezaisa tabishi har can yabari mana ai komai daran dadewa zadawo

yanzu haka uwartace ta kitsa mata komai

Daddy yayi murmushi yace insha Allah ba abinda zaisamu Hakeem
Kokin manta Dan naki
Ma abocin riko da addini ne
Dakuma yawaita adduoin tsarin jiki

Mummy tayi murmushi tace hakane daddyn Hakeem
Gaskiya Hakeem kam akwai addua
Sai dai muce Allah yadada tsare mana shi


Daddy yace Ameen

Washagari daddy yagama wa Laila komai nashirin tafiya
Wanda jibi jirginsu zaitashi

Zuwa Saudi

Hajiya rukayya da hajiya suwaiba ne suka sata gaba kan yadda zata yi anfani da magun gunan dasuka karbo daga gurin malam


Komai Laila ta haddace Dan hartafara hango kanta cikin daula



Washagari jirginsu Laila yadaga zuwa Saudi
Inda tabar meenat 'yarta agurin mahaifiyarta hajiya rukayya


Daddy yadauki waya yakira Abdul Hakeem cikin ladabi Abdul yagaida mahaifin nasa
Daddy yace kashirya kaje airport kadauki matarka
Tana hanya

Cikin mamaki Abdul Hakeem yace Laila kuma daddy
Meyasa zata biyoni har nan

Gaskiya takoma gida kawai Daddy

Daddy yace Haba Dan albarka aure fa ba abin wasa bane

Na kusan shekara bakanan
Ta nemi data zo tagan ka ai baza a hanata bako

Hakeem yace amma daddy
Daddy yace karkace komai ka je airport kadauketa kawai kaji ko

Yace naji daddy Allah yakara Lafiya daddy yace Ameen
Allah yamuku albarka Hakeem yace ameen daddy

Suna gama waya da daddy yace ya Allah

Ahmad yace Lafiya kuwa Man naganka haka
Hakeem yasauke ajiyar zuciya yafada wa Ahmad komai

Ahmad yayi murmushi yace kace nakoma dayan part tunda amarya zata zo

Hakeem dai baice komai ba
Yazauna akan kujera

Karfe hudu dai dai yaje yadauko Laila

Tana ta rawar kai shikuwa Hakeem tunda tagaisheshi ya amsa bakaracewa komai

Wannan shine mafarin zaman Laila a saudiya

Dan bata koma ba


*******
Bayan shekara goma shabiyar
PROFESSOR ABDUL HAKEEM ABUBAKAR

Dan shekara talatindashida aduniya
Cikakken saurayine Wanda ya amsa sunan

THE YOUNG PROFESSOR

ko ina haka akeranshi gida da wajen kasan nan

Yayi suna sosai aduniya saboda kudi da kuma ilimin da Allah yabashi

Har yanzu yanazama a sauddiya ne a inda yake koyarwa a jamiar Saudi Arabian

Dashi da babban abokinshi professor Ahmad

Wanda a yanzu suke shirye shirye komawa kasarsu Nigeria

Laila anzama manyan mata koda wasa bazaka kaga Hakeem kace shine mijinta ba

Ba alamun dacewa a tsakaninsu

HAKEEM bashida rowa koka kadan kudi masu sunan kudi yana cika
Laila dasu
Dan yanzu taza business wuman sosai suke kasuwanci da kanwarta Suby

Idan ta saro kaya a Saudi sai ta tura wa Suby Nigeria

Su duk aganin su Hakeem magani ne yake aiki akansa
Wanda abin bahaka bane dai niyya kawai yayi yake mata abinda yake mata


Amina kuwa agurin hajiya rukayya take sun shaku sosai Dan yarinya dai tayi mugun gado

Shiyasa basa shiri da kakarta mummyn Hakeem Dan tana mata wa azin tabi a hankali kartayi mugun gado

Yanzu haka ma basa Kaduna suna can kano nan hajiya rukayya takoma Dan mijinta yayi ritaya sai ya koma garinshi kano

Shiyasa hajiya rukayya tadauki jikarta meenat suka koma can
Yanzu meenat ta Dade a kano

Tana zuwa Hutu Saudi gurin iyayenta

Wannan kenan


KANO

Malam sualaiman yana zaune a wata unguwar talakwa ne dake nan kano

Yana da mata daya da rana biyu

Yaya shamsu shine babba zaikai shekara 36 aduniya

alokacin da umma ta haifi yaya shamsu sai da yashekara ashirin cas

Kafin tasamu cikin asmaullahil husna
Wato asmau kenan

Inda akecemata husnah

Husnah ta taso cikin gata da tattalin uwa Dana uba da kuma Dan uwa rabinjiki wato yaya shamsu

Tunda aka haifi husnah shamsu ne me dawainiya da ita kasancewar yadade baisamu kani ko kanwa ba


A yanzu haka husna tasamu scholarship a wani makarantar masu kudi a inda take s s two a halin yanzu


Husna tana da hankali da nutsuwa ga kuma uwa uba kyau da needed

da Allah ya horemata

Husna yar kimanin shekara shabiyar aduniya

Sun hadu da Amina Abdul Hakeem abubakar

A school lokacin da husna ta samu scholarship tashigo itama Amina alokacin tashigo makarantar

Amina taso husna Dan Abu guda biyu ne na farko iliminta farinjininta da kuma kyau

Dakyar husnah ta amince wa Amina suka zama kawaye sosai duk inda kaji ance husnah to za ace amina


Muje zuwa =ØÞ anfra fa

Fan's kubiyo ummu AFAN

Kawai

Your comments is needed
[30/04, 5:53 PM] UMMU AFAN <Ø9ß: BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


<Ø—ßHAKKIN MALLAKA NA UMMU AFAN

<ØßGORGEOUS WRITERS FORUM<Øß

<ØßG.WF.<Øß

HOME OF GORGEOUS INTELLIGENT AND EXPERT WRITERS WE ARE THE BEST AMONG THE REST


<Ø—ßDEDICATED THIS PAGE TO MY ENTIRE FAMILIES<Ø—ß



<Ø—ßAKWAI LOKACI <Ø—ß



<Ø—ßPAGE 36 to 40<Ø—ß




HUSNA nata saurine saboda tayi latti yau Monday yau ne za a Nada zabin prefect a school dinsu


Ummu tace husnah naga kina ta sauri yau Lafiya kuwa

Husnah tayi murmushi har dimple dinta suka lotsa tace wallahi ummu yau za a nad'a sabbin prefect a school ne shiyasa mukeson muje muga wadda za a ba


Yaya shamsu yace kokuma kije a nad'a kuba
Husnah tace aini bandani yaya Dan an min

Interview ma naki bada amsa a hall din

Duk Dan kar abani damuwar nan

Yaya shamsu yace ai duk yadda kikayi sunsani tunda sunsan dalibarsu
Kokinyi shiru sunsan bawai baki sani bane

Tunda dama sunsan bakyaso
Bakince min saki dole akayi kiyi interview din ba

Husnah tace wallahi wani malaminmu ne copper yace lalle sai nayi interview

Kuma duk abinda suka tambayeni Nace I don't no
Komai I don't no kawai


Yaya shamsu yayi dariya yace kedai jekidawo kiban labarin wadda akazaba


Husnah tace to shikenan yaya
Tajuya ta kalli ummanta tace ummu sai na dawo

Ummu tace Allah yadawo dake Lafiya tace ameen umma na


Har takai bakin kofa yaya shamsu yace husnah kiyi hakuri kinji bakudi ajikina yanzu nakeson zuwa nayi buga buga naga abinda za a samo acigidan

amma namiki alkawari idan nafita nasamu wani abin zana biyo har school dinku

Inbaki Abu mai dadi

Husnah tayi murmushi tace karka damu yaya na wallahi bani da damuwar komai Dan bancika son cin komai a school ba ma

ai kana kokari yayana Allah yakawo maka aiki

2 Comments On AKWAI LOKACI
avatar
musa-6-3-2

1 year ago

Reply

Akwai lokaci

avatar
oumara-wassai

1 year ago

Reply

Replying to musa-6-3-2

17866

Please Login or Register in order to submit comment