Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

maitsoka nasan zamu huta sosai


Yace ameen yar kanwata jeki karkiyi latti


Tafita abinta tana murmushi


Umma ta sauke ajiyar zuciya tace wa yaya shamsu

Kasan wani Abu kuwa shamsu deen yaya shamsu yace a a umma saikin fada


Tace wato akullum na kalleku kaida kanwar ka ina wa Allah godiya daya mallakamin 'ya'ya nagari

Dan ba abinda zance wa Allah sai godiya kawai

amma duk inda ake neman 'ya'ya nagari nasamu
Abba dayake shirin fitowa daga dakinsa yace munsamu dai zakice zainaba

Tunda Allah yasa shamsu yakawo kwari fa shiyake dawainiyya damu agidan

Shine komai na kanwarsa shine namu aiba abinda zamuce sai muce shima Allah yabashi mai mishi

Umma tace Ameen malam

Malam sulaima yace babban damuwata shine inga kasamu aiki kayi aure Dan shine cikar mutuncin mutum


Umma tace hakane ai baki yayi tunda yana da wacce yakeso khadija yarinyar kirki taki kowa saishi take jira
Ko a yanzu aka tura za ayi komai tunda iyayen ma sun komai

Malam sule yaja numfashi yace hakane kam to Allah yabamu yadda zamuyi


Ya kalli shamsu da tunda suka fara zancen auranshi yashiga duniyar tunani


Dan yana matukar son budurwarshi khadijat wacce akekira da kubra kitama tana son yaya shamsu sosai Dan

Shekarar ta daya kenan dagama secondary school
Manema sunzo Neman aurenta taki ita sai shamsu
Haka iyayen suka hakura suke zaman jiran shamsu yakawo sadaki a daura aure



Malam sule yakalli shamsu yace karka damu akwai Allah

Shamsu yace barinje Abba sai na dawo ya ma umma ma sallama ya wuce zuwa Neman abinda zasuci


YAYA SHAMSU daga secondary bai kara gaba ba saboda rashin kudi daya musu katutu shida mahaifansa

Dan haka kawai ya hakura yake Dan buga bugansa dahaka kuma har Allah yasa aka haifi kanwarsa husna saiya yaci burin Husna zatayi karatu tunda shi Allah baisa zaiyi mezurfiba


Sai kuma gashi Allah yafara cikawa shamsu burinsa inda husnah taci scholarship


**
Husnah tana isa school tasamu anfara assembly
Ta tsaya daga bayan 'yan mate dinsu suna sauraron jawabi daga bakin principal dinsu



Can sai vice principal yace yace zamufara kiran new prefect dinmu daya bayan daya

Principal tace a fara da head girl ko

Sai copper bash yace am sorry ma
Gwamma afara da sauran kafin head girl
Zaifi Jan ra ayin su

Principal tace OK afara kira kawai


Nan akafara kiransu ana samusu hula da kuma belt
Dansu prefect din hula suke sawa green gabadayansu na head girl ce kawai ya banbanta Dan nata read cap take sawa


Can taji ance social prefect AMINA HAKEEM ABUBBAKAR




Nan aka dau tafi raf raf raf ana murna


Can sai vice principal yayi gyaran murya yace yanzu zamu Kira me gayya me aiki wato our head girl

Nan aka kira sunan ASMAU SULAIMAN SHAMSU

cikin gigicewa Husnah tadago kanta aikuwa tana dogowa sukayi ido hudu da Copper bashir

Ya kashe mata ido daya

Cikin tashin hankali Husnah ta daga kafa dakyar tana zuwa ta hau kan stage

Principal ta rungume Husnah tare da
Da samata hulan head girl dinta read cap

Ta daura mata belt dinta read shima
aikuwa daga students har malaman dake wajen aka dautafi Dan sunburge kowa ga read cap din yawa Husnah kyau sosai kaman Dan ita akayi hulan


Nan dai aka rantsar dasu Husnah a matsayin new prefect


***
Copper Bash ya tsare Husnah alokacin dazata wuce gida itada meenat


Copper bash yace asmau
Ya naga kina ta shan kamshi ne Yau

Meenat tafashe da dariya
Tace uncle ai Husnah fa batasan za abata prefect ba ballantana Head girl

Copper bash yayi murmushi yace ai kuwa ta yaudari kanta

To inba a bata ba waza aba wa
Meenat tace aifa dai kam


Husnah dai tana jin su batace komaiba

Nan driver din meenat yazo daukarta

Husnah kuma dama da kafa take zuwa take komawa

Meenat tace Dan Allah Husnah kizo musaukeki a gidan kinga sai naga gidanku ko

Husnah tayi murmushi dimple dinta suka lotsa

Copper bash ya tsaya kawai yana kallon Husnah komai nata cikin aji takeyinsa da nutsuwa shiyasa takeda farinjini a school din


Husnah tace wallahi meenat idan ya shamsu ya ganni a mota zai min fada sosai .

Meenat tace kedai kawai bakyason kibimu sai kiyi tayiwa yaya shamsu sharri


Copper bash yace kinga kuyi sauri kutafi gida kar anemeku kuntsaya surutu


Meenat tace to shikenan sai mun hadu goben idan munzo ko

Husnah tace to meenat Allah yakaimu kigaida gidan
Nan sukayi sallama

Copper bash yace wa Husnah muje nakaiki gida da kaina

Tunda kinki kawarki takaiki

Husnah tace Dan Allah uncle kayi hakuri wallahi yayana yaganni da kai zaimin fada

Copper bash yace mezaisa yamiki fada baki kai a rakakin bane ko yaya

Husnah tayi shiru tace kayi hakuri Dan Allah

Yace wato har yanzu Husnah kinkasa yarda da sonda nake miki ko

Kibani dama nasan gidanku da iyayenki wallahi dagaske nake auranki zanyi Asmau

Husnah tace Dan Allah malam kayi hakuri kar yaya yasan da wannan maganar

Dan ya hanani kula koda kawace ballantana

Maganar soyayya tun yanzu

Da kyar yabani dama kawance da Àmina Hakeem ma



Copper bash yace OK na fahinceki
Ba wai nidinne bakyaso ba umarnin yayanki kikebi ko


Husnah ta rufe ido tana murmushi tayi hanyar fita daga gate din school din


Copper bash yayi murmushi tunda ya gano yafara shiga zuciyar Husnah

Zaisan hanyar da zaibi Dan yasan iyayenta da yayanta shamsu



Bashir Dan wani hamshakin maikudi ne sosai acikin garin kano

Bautar kasa wato NYSC yakaishi school dinsu Husnah
Tunda yadora idonshi kan Husna yaji yakamu da son ta

amma takibashi daman hakan



Next page
[05/05, 11:05 AM] UMMU AFAN <Ø9ß: <Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


<Ø—ßHAKKIN MALLAKA NA UMMU AFAN <Ø—ß


<Ø9ß<Ø9ßFIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATION<Ø9ß<Ø9ß

<Ø9ßF.C.T.W.A<Ø9ß



<Ø9ßHOME OF QUALITIES AND TRUSTED WRITERS OF THE NATION<Ø9ß



<Ø—ßDEDICATE THIS PAGE TO UMMY =Ø
Þ KINA KOKARI WAJEN GANIN NOVELS DINA SUNA KARBUWA A KOWANI GROUP ALLAH YABAR KAUNA =ØÞ=ØÞ=ØÞ=ØÞ=ØÞ




<Ø—ßAKWAI LOKACI<Ø—ß




<Ø—ßPAGE 41 to 45 <Ø—ß




ABDUL HAKEEM THE YOUNG PROFESSOR

kwannansu biyu da dawowa daga saudiya dashi da madam laila


HAKEEM yana shirin zuwa sashen iyayensa ne don yagaishesu

Yafito daga wanka ne yashirya cikin wani farisol din jallabiya ya faffesa turarruka masu kamshi Dan akwaishi da son kamshi sosai

Har yagama shiransa zaifita Laila bata tashiba

Ya kalleta kawai ya girgiza kai yayi gaba abinsa zuwa part din su mummynshi


Yanashiga yasamesu akan dining da mummy da daddy


Daddy yace Dan halal kaki anbato yanzu nace baka shigo break fast ba mummyn ka tace ai tasan kana hanya

HAKEEM yayi murmushi cike da kaunar iyayensa

Yace ai mummy tafadi gaskiya Dan bazan taba karyawa a wani waje ba matukar muna tare da mummy

Mummy tace yauwa son fada mishi dai

Nan mummy tayi serving din HAKEEM abinci yafara ci


Bayan sungama break fast ne mummy zata kwashe kwanukan Hakeem yace haba daliba yazakimin haka kuma

Kezaki kwashe kayan zuwa kitchen nikuma meye anfani na

Mummy hafsat tace nabari tashi ka kawashe

Daddy dai dariya yake musu yakoma kujerar falo yazauna

Hakeem bayan yagama kwashe kwanukan zuwa kitchen saiya dawo falo Dan hira da iyayen nasa


Daddy yace wai acikin makarantu biyu dasuke bukatarka wanne kazaba kayi lecturing din agun

HAKEEM yayi murmushi yace ai daddy daga ni har Ahmad munzabi muje BUK kano


Daddy yace Allah yasa haka shine alkairi

Mummy hafsat tace amin

Daddy yace kace kuna tare da amaryata kenan

Mummy hafsat tayi murmushi tace MEENAT ko rigima

Yakama ta ma suturota tazo tagaida iyayenta ai

Daddy yace karkice komai tunda basuyi hakan ba shi saiyaje yaganta


Kafin Hakeem yayi magana wayar daddy yadau kara

Daddy yadaga sai sukaga daddy yace subuhanallla a wani asubiti

Mummy da Hakeem suka maida kallonsu kan daddy

Bayan daddy yakashe wayar ne suka tambayeshi abinda kefaruwa

Yace Abba na aka kai hospital

HAkeem yace subuhanalla muje kawai daddy

Mummy hafsat tace nima bazaku barniba muje tare

Suka he asibitin Hakeem ne me driving dinsu

Suna isa suka sami alhaji shuaib bayadda yakara ji

Dan yanajin jiki sosai

Alhaji shuaib yarike hanun Dan nashi wato daddy
Yace Allah yamaka albarka abubakar da kai da zuriarka

Ba abin da zance dakai sai Allah yàmaka sakayya da gidan aljanna duk inda akeneman yaro nagari ka kai abubakar

Ya kamo hanun Hakeem yace jikallena ga mahaifinka nan nabar maka amanarshi duniya da lahira

Kabishi kamar yadda yabini

Ya kalli mummy hafsat yace kema Hafsatu Allah shizai biyaki akan yadda kika nuna kaunarki ga abubakar

Duk yadda aka kai cutar dashi kinki bada damar hakan

Allah yamiki albarka

Tunda alhaji shuaib yafara magana suke kuka musamman daddyn Hakeem

Da mummy

ABDUL HAKEEM ne kawai ya daure amma shima idonshi yayi ja sosai


Can dai likitoci sukace sufita zasu samishi
Oxygen Dan numfashinsa yafara kasa

Alhaji abubakar ne kawai akabari a dakin


Can wajen La asar 'yan kano suka iso asibitin

Kuma harda meenat

Hajiya rukayya itama a rikice tazo jincewa jikin mahaifin nasu ya tashi

amma anhanata shiga taganshi

Hakan kuma ya bata mata rai sosai

Amina kuwa tana ganin daddynta Hakeem tare da mummynshi takarasa wajensu cike da murnar ganin uban nata

Bayan tagaida Hakeem ne take tambayarsa dad ina mummyna yace tana gida yanzu zata zo itama

Amina ta kalli mummy hafsat tace wato ma bazaki kimin magana ba ko

Mummy hafsat tace kaga jaira kinga babanki bakima San ina wajenba zaki ce ban miki maganaba

Sannu uwata mummy hafsat takarasa maganar tana tsokanarta

Amina tace ai wallahi duk abin kidai saina auri mijinki sai naga yadda zakiyi

Mummy hafsat tayi murmushi tace kishigo mana kigani da tabarya zan koraki ai nan mummy Hafsat tana jikinta ajiki sukata Dan hirarsu amma cikin jimamin rashin lafiyar alhaji shuaib


Ahmad yakaraso hospital din shima cikin jimami

Hakeem na ganin Ahmad yace Man ka karaso kenan

Ahmad yace ai kana kirana nace wa mummy zanzo hospital namata bayani

Itama zasu zo tanason gama abincine sai ta taho dashi

Hakeem yace Allah yakawota Lafiya

Ahmad yace barinje na gaida su mummy suka karasa harwajensu mummy

Yagaishesu yamusu ya maijiki

Amina tace daddy Ahmad ina wuni yace Lafiya qalau daughter ya mummyn ki

Tace banganta ba mu yanzu mukazo daga kano

Kafin Ahmad yayi magana daddyn Hakeem yafito daga dakin yana goge hawaye

Hakeem da Ahmad suka karasa dasauri Hakeem yace daddy yajikin alhajin

Daddy abubakar yace Hakeem Allah ya yi wa mahaifina rusuwa
Alhaji yatafi yabarni Hakeem

Yanzu bani dakowa dama bansan mahaifiyata ba shikadaine min aduniya

Shima yatafi

Duk matan dake gun sukasa kuka


******

Bayan arbain din alhaji shuaib

ABDUL HAKEEM da aminin sa suka fara lecturing B U K

Dan karakaran gidaje makaranta tabasu a matsayinsu na professional akan aikin su

Yanzu Haka suna shirye shiryen auran Ahmad kuma a kano zaitare da matarsa

Itakuma Laila tayi tayi yabarta tadawo kano yaki

Sai dai yazo masu Hutu yakoma

Yanzu haka bikin Ahmad saura sati biyu cas a daura auren Ahmad




*****

Yaya shamsu zaune akan kujera yar tsugune umma kuma na hada zobo Dan duku gidan suna azumin Monday da alhamis

Itakuma Husnah tana kan hada musu abincin buda baki a kitchen

Kanin kubra budurwar yaya shamsu ne yayi sallma yashigo ya tire

Ya gaisheda umma kafin ya ajiye abincin yace yaya shamsu gashi anty kubra

Kafin shamsu yayi magana umma

Tadauko naira hamsin tace zoka karba ko kace mata angode Allah yasaka da alkairi

Yaron yaki karbar kudin umma yaya shamsu yace haba kanina karba mana ai ba roka kayiba

Yakarba yayi godiya zaifita kenan
Husnah ta tace sani kace wa anty kubra gobe zanzo kitso
Sani kanin kubra yace to zanfada mata


Umma tace kajita kaman wani kitson takeso
Yanzu zatace maka zata kitso taje tadawo da kalba

Husnah tayi murmushi tace umma wallahi banason kitso nafison dai amin kalban kawai


Tagama kwashe komai ta ajiye musu akan taburma

Jelouf din taliya ta musu Wanda ya shamsu yakawo dazu yace a dafa yasan tana son taliya sosai

Umma tace wallahi yarinyar nan kubra akwai kokari
Bata gajiya da aiko maka da abinci duk Monday da alhamis


Husnah tace gaskiya kam wallahi anty kubra Nada kirki

Yaya shamsu Allah yabaka kudi wannan sallar dai kasamu kamata kayan sallah

Umma tace amin gaskiya kam ta cancan hakan


Shamsu yaja numfashi yace kuma wallahi umma kubra bata jin dadin gidansu
Indai ba abbanta yana gidaba

Kishiyar mamanta tana matsa mata sosai
Yanzu fa wai akwai Wanda yamata magana yanson kubra shine tadage sai kubra ta amince da auran wani baniba

Dan taki amincewa shine take bata wahala
Kuma abbanta yace bazai mata auren doleba
Sai Wanda takeso zaibata

Shine tayi bakin jini agidan


Umma tace Allah sarki marainiyar Allah

Allah yabaka abinda zaka auro yarinyar nan karabata da gidan nan

Shamsu yace amin umma
Husnah ma tace amin

Yaya shamsu yace barinje sallar magriba indawo muyi buda baki



Shamsu yana fita Husnah tace wallahi ummu yaya shamsu yana bani tausayi

Dan wallahi shima yana son kubra sosai

Umma tace bakomai AKWA LOKACI

watarana sai labari Husnah tace Allah yanuna mana lokacin amin ummu tace

Suma tashi sukayi Dan gabatar da sallah



**
Bayan kwana biyu wani abokin shamsu yabashi
Shawarar mezaihana yakai takardunsa Neman aiki B U K koda masinja aka bashi zai rage zafi ai

Shamsu yace gaskiya naji dadin shawarar nan daka bani kabiru
Allah yabar zumunci

Kabiru yace bakomai ai zaman taren kenan

Kaga ni a secondary school nake masinja amma alhamdulilla ina samu

Ya shamsu yace hakane yanzu zanyi wanka nakai kuwa

Bayan ya shamsu yashirya zuwa kai application dinsa

Saiya wa umma sallama Yakama hanya



Bayan yakai akace za anemeshi idan yasamu idan kuma baisamuba zaiji shiru

Yabasu number dinsa

Yatafi gida yana ta aduar samun nasara

Idan Allah yasa yasamu aikin nan zaiyi kokarin raba kubra da gidansu tazo suyita maneji yasan kubra zatayi hakuri da abinda zaibata umma kuma bata da matsala zasu zauna Lafiya


*****

Professor Abdul Hakeem zaune a office dinsa yana duba wasu takardu sai wata mata tashigo tagisheshi

Tace wai itace sabuwar sakatariyarsa


Abdul Hakeem yace OK zaki iya tafiya sai na nemeki

Tafita
Tana fita Hakeem yakira management din makarantar

Suna ganin wayar office dinsa
Aka je dasauri Dan yanakirane

Manager nashiga yagaishe da professor Hakeem

Hakeem yace ina buka tar a canza min secretary ma ana bayason mace

Namiji yakeso akawo mishi

Manager yace angama sir

Hakeem yabashi izinin tafiya

Sukaje suka zauna meeting

Nan akayi shawarar daukar SHAMSUNDEEN SULAIMAN a matsayin secretary na THE YOUNG PROFESSOR ABDUL HAKEEM



Yaya shamsu yana kofar gidansu kubra yaje zance
Sai yaga kira da bakuwar number

Yayi picking call din

aikuwa kubra taga yana ta fara a yana godiya
Bayan ya kashe wayar ne

Ya kalli kubra yace kiyimana murna munsami aiki kinga kenan burinmu yakusa cikako

Cikin tsananin farinciki kubra tace alhamdulillahi
Gobe zafara azumina kenan

Da mamaki shamsu ya kalli kubra yace azumin mekuma zakiyi

Kubra tayi murmushi tace aina wa Allah alkawarin cewa duk randa kasamu aiki sainayi azumi uku cas

Shamsu yace aikuwa bazakiyi kekadaiba tare zamuyi

Nan dai yamata sallama ya wuce gida Dan yasanar wa umma


**
Umma tayi farinciki sosai haka ma mahaifinsa

Husnah kuwa tsalle taringa yi tana murnar ankusa kawo musu anty kubra gidansu

Mahaifinsa yace gobe zaka fara zuwa kenan
Yaya shamsu yace a daga gobe sukace wai karfe takwas zandinga zuwa
Sainaje ma zasubani dokokinsu

Nan iyayen sukayi ta albarka


Washagari yaya shamsu yashirya zuwa wajen aiki

Bayan yayi sallama da su umma

Ya wuce gidansu kubra itama tamishi adawo Lafiya



Yana isa aka gama komai aka turashi office din PROFESSOR HAKEEM


yana zuwa yayi nocking akace yashiga

Professor Hakeem yanakan kujerar shi yana fama da wasu takardu

Shamsu yashiga yagaisheshi professor Hakeem ya amsa batare da kalleshiba

Yace ta akayi malam

Shamsu yace daman nine sabon secretary din da aka turo office dinka

Professor Hakeem yace OK dafatan zamuyi da gaskiya malam

Shamsu insha Allah sir

Sai alokacin professor Hakeem yadago kai ya kalli ya shamsu

Yace ko zan iya sanin sunan malamin
Yaya shamsu yayi murmushi yace Shamsuddeen

Hakeem yace malam shamsu Allah yatayaka riko za iya tafiya

Shamsu yayi godiya yace nagode sir


Ya wuce abinshi professor Hakeem yacigaba da aikinsa

Can wajen shabiyu da rabi professor Ahmad yashigo office din Hakeem yace ya man muje muyi lunch kasanfa bana jure yunwa

Hakeem yayi murmushi yace wai damma ka kusa shiga daga ciki
Aisha Nada aiki wallahi sai dai ta ringa samaka wani flask



Ahmad yayi dariya yace ai dani dakai duk jirgi daya yakwàso mu

Nan dai Hakeem ya tattara suka fito tare Hakeem yakalli shamsu dake kan kurarshi yace

Abokina zamufita ga key din office din take care

Shamsu OK adawo Lafiya



Suna zaune a gurin cin abinci Ahmad yace waini wannan Dan gayun ne sakatarenka

Hakeem yace kaima kaji mamaki ko

Da naso namishi tambayoyi sai naga rashin dacewar hakan gwamma nagama fahimtarshi kafin

Naji tarihinsa

Ahmad yace hakan ma yayi
amma mutum very responsible person kaman wannan ace yana sakatare


Shamsu yashiga office din maigidan nashi yaga kudi a kasa
Ya dauka ya ajeye mishi a saman tebur



Bayan su Hakeem sundawo yashiga office din sa
Sai ya kalli inda ya zubar da kudi yaga babusu
Dan dama da gangan yayi hakan Dan ya gwada shamsu ne kawai

Yazauna akan kujerarshi aikuwa idonshi yakai kan kudinshi da shamsu ya ajiye mashi su

Professor Hakeem yayi murmushi akaro na farko
Yaya shamsu yashiga ranshi


Karfe hudu dai dai Hakeem yatashi a office dayafito yaga kujerar da shamsu yake yaga yana waya ne amma yanaganin fitowar Hakeem yawa kubra sallama

Hakeem yayi murmushi yace hala kaida uwargida kuke wayar kuma ka kashe

Yaya shamsu baice komai ba sai murmushi kawai

Hakeem yace natashi kaima zaka iya tafiya

Shamsu yace aisunce wai sai time din tashi yayi zantashi

Hakeem yace no zan musu magana kaje kawai abinka

Hakeem har yayi gaba ya dawo yace sunbaka kudi kuwa
Ya shamsu yace wani kudi kuma nida nafara aiki yau sir yakarasa yana murmushi

Hakeem yayi murmushi yace yakamata subaka kudin daukar aiki

amma zanbaka aro idan anbaka sai ka dawo mundasu ko

Ya shamsu yayi dariya kabarshi kawai sir kar azo basu baniba

Hakeem yayi murmushi yace idan basu baka na barma

Kuma banason musu yashiga tsakaninmu malam shamsu ka karba kawai karmuyi haka dakai

Shamsu yakarba yace nagode yallabai


Yace karka damu

Sai gobe kayi kokari ka koma gida


Shamsu yasake baki kawai yana kallon Hakeem

Yaduba damin kudin da Hakeem yabashi

Nan dai yayi wa Allah godiya cike da farinciki shamsu ya kulle kofar office din su

Yayi gida

Yana zuwa Husnah ta tareshi da murna oyoyo yaya na sannu da dawowa

Shamsu yayi dariya yace yauwa yar kanwata ina umma

Ummu ta fito daga daki tana daura dankwali tace a a dawuri haka

Yaya shamsu yace wallahi Allah ne ya hadani da shugaba nagari yace karfe hudu ma ina iya tafiya


Umma ta ce alhamdulilla ai haka akeso
Yaya shamsu yace umma ina Abba tace yanzu zaishigo sunje gaisuwar Mara Lafiya shida malam tanko

Kafin tarufe baki ma sai ga Abba yayi sallama yace a a Dan albarka har andawo

Nan suka zauna kan ta Burma yafito da kudin ya ajiye gaban mahaifinsa

Nan yamusu bayanin komai

Abba yayi gyaran murya yace to yanzu idan akazo ba a baka kudin daukan aikin bafa

Ya shamsu yace nima haka nagani dai
Na nuna yabar kudinsa kawai yace aishi yabani

Umma tace to kaidai duk inda kake ka tabbatar karike gaskiya kazauna da kowa zuciyarka daya

Ya shamsu yace insha Allah
Zankiyaye

Nan dai Abba da umma sukace baza a taba kudinba harsai

anbaka angani koba hakaba yaya shamsu yace hakan ma yayi gaskiya

Husnah tace Abba kawai da yaya shamsu yayi anfani da kudin gurin kai sadakin anty kubra

Koba a bashi tunda yana aiki saiya biyashi a hankali

Abba yayi murmushi yace uwatakenan ke yarinyace har yanzu bakisan duniyaba

Indai aure ne ai zaiyi insha Allah

Suka ce Allah yasa


Bayan kwana biyu ranar alhamis ya shamsu yaje wurin aiki aka kirashi akabashi kudin daukar aiki naira dubu goma shabiyar

Da yadaqo gida yace wa ma haifinsa ambashi yanuna musu

Abba yace alhamdulilla kaga gobe saika mayar mashi da kudinsa

Allah yayi albarka ya shamsu yace ameen Abba

Abba yace yakabar kudin kuma anan
Ya shamsu yace Abba kayi abinda yadace kawai

Abba yace wa umma tadebi kudin ta ajiye agunta



Washagari ya shamsu yasami professor Hakeem a office yamishi bayani yamayar mashi da kudinsa

Hakeem shi har ya manta ma yaba wa ya shamsu kudi

Ba karamin burgeshi ya shamsu yayi ba
Yace
Gashi kasiya wa yara sweet

Ya shamsu yayi dariya yace ai banida aure

Hakeem yakalleshi yace

Malam shamsu idan bazaka damu zanso jin labarinka




Next page

Your comments is needed
Fan's

=ØÖÜ=ØÖÜ=ØÝÜ=ØÝÜ
[05/05, 11:08 AM] UMMU AFAN <Ø9ß: <Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


<Ø—ßHAKKIN MALLAKA NA UMMU AFAN <Ø—ß


<Ø9ß<Ø9ßFIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATION<Ø9ß<Ø9ß

<Ø9ßF.C.T.W.A<Ø9ß



<Ø9ßHOME OF QUALITIES AND TRUSTED WRITERS OF THE NATION<Ø9ß



<Ø—ßDEDICATE THIS PAGE TO UMMU HANIF <Ø—ß



<Ø—ßAKWAI LOKACI<Ø—ß



<Ø—ßPAGE 46 to 50<Ø—ß



PROFESSOR HAKEEM yace ina sauraronka malam shamsu

Ya shamsu yayi murmushi nan yabashi kadan daga cikin tarin rayauwarsu

Hakeem yace kace kai din dai har yanzu dai gaurone murkusheshen gaurone

Ya shamsu yayi murmushi yace a nakusa fita a layin gaurayen tunda nasamu abinyi

Hakeem yace hakane

Ya kalli kudin da ya shamsu ya ajiye mashi akan tebur

Yadauko wani rafar ya hada mashi dasu yace

Kadauki wannan kudin kaje kamuku cefane

Sannan kuma ka Isar min da gaisuwata wajen Abba da umma
Da kuma yar kanwarmu

Ya shamsu yace amma ai kudin sunyu yawa yallabai

Hakeem yayi murmushi yace karkadamu

Malam shamsu kana da sha awar cigaba da karatu ne

Shamsu yayi murmushi yace
Zanyi kokari bayan aure na ga nasamu ko degree na samu insha Allah

Hakeem yace Allah ya nuna mana ya shamsu yace nagode Allah yasaka da alkairi


Hakeem yace godiyan yana yawa kuma.banason godiya malam shamsu

Ya shamsu yayi murmushi yace ai ka canci hakan ne yallabai

Nan dai suka Dan taba hira har lokacin tashin Hakeem yayi suka tafi shida Ahmad

Ya shamsu kuwa yana fita yaje kasuwa yamusu cefane sosai har kaji da lemuka masu sanyi


Yana isa kofar gidansu mai adai daita sahu ya tsaya yabiyashi yafito da ka yansa

Yashiga cikin gidan da sallaman shi


alokacin Husnah tana alolar La asar

Tana ganinshi ta karasa wanke kafarta ta zo takarbeshi tana mishi sannu da zuwa

Yace alolar mekikeyi tace LA asar ya shamsu yace haba Husnah yazaki bari lokacin sallah ya wuce kina da lafiyanki

Kafin tayi magana umma daga kitchen tace ai yau Husnah bataji dadiba ne

Tun da tadawo daga makaranta take kwance kanta naciwo


Ya shamsu yace ashsha barin je nasiyo miki magani
Yanzu zandawo

Husnah ta rike rigar ya shamsu tace wallahi naji sauki yaya

Dama abin da ya haddasa min ciwon kan ma

Wani taro akayi a school dinmu kuma nice presenter

Hayaniya ce yasani ciwon kan amma Dana dawo gida umma tabani magani nasha na kwanta yadaina

Ya shamsu yace kinta tabbata
Husnah tadaga kai alamun ta tabbatar


Abba ne yayi sallama yashigo
Da Leda a hannunsa Husnah ta ajiye Wanda ya shamsu yakawo akan taburma tayi saurin karbar na Abba alkamace Abba ya auno Dan Abba akwai son tuwon alkama dashida ya shamsu


Bayan sun zauna ne ya shamsu yace Husnah dauko kayan can kiraba mana

Husnah ta tashi ta dauko

Plate guda uku da tasawa Abba kajin da kuma Irish potato wato dankalin turawa
Ta ajiye mashi maltina Dan tasan zaifi sonshi

Kafin tasawa umma itama maltina tamata

Sai ta hada musu itada ya shamsu ta

2 Comments On AKWAI LOKACI
avatar
musa-6-3-2

1 year ago

Reply

Akwai lokaci

avatar
oumara-wassai

1 year ago

Reply

Replying to musa-6-3-2

17866

Please Login or Register in order to submit comment