Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dauki lacasera

Ta dauka wa ya shamsu fanta dantasan abinda kowa yakeso

Umma ta ce yau fa shagwaban yatashi Abba yace a din tayi baruwanki ai sunfi kusa yakarasa maganar yana dariya

Husnah tace yauwa Abba fada mata dai

Ya shamsu yayi murmushi Dan yanason yadda suke rayuwarsu cikin son juna acikin gidansu

Suna gamawa Husnah ta tashi tadauko Dan karamin kula tasaka naman da komai yadda sukasha sai wannan lemu sunkai uku

Tasaka a Leda tace ya shamsu wannan na anty kubra ne idan kaje kace mata inji sweet kanwarta


Umma tace kai wannan soyayya da Husnah takewa kubra

Inba auren nan akayi ba hankalin Husnah bazai kwanta ba ba


Abba yace ai soyayyar Dan uwantane yashafi khadijan

Husnah tace gaskiya Abba kana da ganewa wallahi yadda anty kubra takeson ya shamsu yasa na ke ganin girmanta

Shidai shamsu inbanda murmushi ba abinda yakeyi

Nan yawa mahaifinsa da ummansa bayanin yadda sukayi da maigidansa

Abba yace Allah yasa hakan shine mafi alkairi

Kaga girman alkawariko

To haka akeson mutum aduk inda yake ya rike gaskiya

Ya shamsu yace hanekam
Nan yabawa mahaifin nasa kudin gabadaya yace ya ajiye agunsa


Ya tashi yashiga wanka Wanda Husnah ce takai mai yana fitowa yayi alwala zuwa sallar magriba


Bayan ya dawo daga isha ne yadauki kayan da Husnah tabashi yakaiwa kubra

Ya fesa turarensa mai Dan arha duk da talaucin su ya shamsu baya rabuwa da turare danshi mutum ne mai tsafta sosai Dan gado sukayi a wajen iyayensu

Saikuma Husnah tace matsa kaban guri akan tsafta kokadan Husnah bata son datti


Yana isa gidansu kubra ta fito da hijabinta dogo

Duk yadda takai taboye abinda aka mata agida kubra takasa sai da yagane

Yace Lafiya naga fuskarki haka kubra

Kubra tayi yake tace bakomai wallahi abune yafada min a idona amma nacire

Kafin ya shamsu yayi magana wata kanwarta wadda suke uba daya tazo tace wai kizo inji mama kicigaba mata da abinda tasaki

Kubra tace kice inzuwa yarinyar tajuya takoma zuwa cikin gidan

Tausayin kubra Yakama shamsu sosai yace kiyi hakuri kinji watarana sai labari nasan duk akaina kikaganin wulakanci Dan kin ki bada hadin kai


amma namiki alkaqarin komai yazo karshe insha Allah

Yace karbi wannan inji kanwarki tace nakawo miki

Kubra tace Allah sarki Husnah Dan Allah kace mata nagode sosai

Yaciro dubu uku a aljihunsa yace karbi wannan kirike a hanunki

Kubra ta kalleshi ta kalli kudin tace haba sahibina ya daga samun aiki zaka fara barna da kudi kawai kabarshi

Yace ai duk abinda zansamu kina da kaso aciki kikarba kawai kubra idan baki karba ba zaki bata min rai


Cikin sanyin jiki kubra ta karbi kudin
Tace nagode Allah yakara budi yace amin

Maza koma gida kikarasa abinda aka saki karkiyi laifi ko

Tace to sai anjima ko kuma saigobe ba inji ya shamsu



Washa gari dasafe ya shamsu yagama shirin zuwa aiki bayan sun karya

Yafito yace wa Husnah muje ko

Husnah tace to yaya suka wa umma sallama

Suna futa kuwa suka yi sa ar keke napep yaya shamsu yatare musu sukashiga

Suna tafiya suna hira yace inga jakanki tabashi bata kawo komai a ranta ba

Ya shamsu kuwa yafaketa yasaka mata 1000 a ciki dubu daya kenan

Suna zuwa dai dai gate din su Husnah ya shamsu yace wa driver tsaya ta sauka nikuma kayi dani BUK Husnah tasauka tana daga wa ya shamsu hanu

Yayi dai dai dannowar motar copper bash

Yaji lokacin datace ya shamsu kanan ya shamsu ne acikin keke napep din nan
Inkuwa shine zanbisa namishi bayanin komai


aikuwa copper bash yayi ta bin yaya shamsu abaya har yasauka a gate din BUK

Bayan ya shamsu yabiya kudin yayi gaba abinsa

Copper bash yayi parking yafito
Yabi bayan ya shamsu
Har yaje yayi signing yazo kafin yaje can kujerashi kofar

PROFESSOR HAKEEM yazauna

Copper bash yamishi sallama ya shamsu ya amsa yace kozan iya taimakonka

Copper bash yace a daman taimakon nazo nema

amma a gurinka ya shamsu

Yadda copper bash yakirashi ya shamsu yasan duk yadda akayi yasanshi ne

Ya shamsu yanuna mishi kujera
Nan copperbash yafada wa yaya shamsu irin son da yake wa kanwar shi

amma taki bashi dama hakan

Ya shamsu yace bazata ta taba amince maka har sai nabata izini

Umarni nabata nima kuma bazan taba amincewaba har sai nayi bincike akanka kafin nan kuma na tabbatar tana sonka na uku kuma zakamin alkawarin barin ta tayi karatu bayan kinyi aure amma wannan zaizone bayan nayi bincike nagar tarka


Copper bash yace wallahi ya shamsu indai akan asali ne bana shakku aje ayi bincike fata na kawai idan kabincika bani da matsala ka amince min nakawo sadakina gidanku shikadai ne zaisa hankalina yakwanta

Ya shamsu yayi murmushi yace karka damu Allah yashige mana gaba

Nan yawa ya shamsu sallama yatafi



*******

HUSNAH zaune kan kujerar class dinsu teacher din dazata shiga musu ta haihu shiyasa suka samu Free time

Meenat tace gaskiya Husnah baki da kirki yanzu kakan dad dina da mummy na ya mutu amma kikasa Neman gidan mu kije kiwa kakata ta aziyya


Husnah tace afuwan aminyi insha Allah ranar asabar zanzo gidanku nawa kakanmu ta aziyya

Meenat tace kai amma danaji wallahi har na matsu asabar tayi

Hajiya ta taganki labarinki kawai takeji agurina


Husnah tace aikuwa zanzo nagaisheta

Tace amin Allah yasa daddy ma yazo sai kigaisheshi

Kinsan tun yadawo kano aiki duk Saturday yake zuwa yaganni

Husnah tace to Allah yakaimu ranar

Suna haka wata junior tashigo tace anty husnah wai kizo inji uncle bash

Husnah tace OK kice ganinan zuwa

Meenat ta kebe baki tace wai meke tsakaninku da copper bash ne

Husnah tace sirrine amma zakiji nan gaba tashi muje kirakani kawai

Meenat ta tashi jiki a sanyaye tabi Husnah zuwa office din uncle bash

Suna shiga suka gaishe da bash ya amsa idonsa akan Husnah

Takaici Yakama meenat

Dan ita ba namijin datakeso irin copper bash
Tayi shishigin amma bata samu karbuwa ba

Ya kalleta yace zaki iya jiranta a kofa magana zamuyi

Meenat cike da bakin ciki ta fito

Copper bash ya kalli Husnah yace munhadu da ya shamsu

Cikin sauri husnah ta dago kanta da sauri tace meyace maka shikenan nasan yaya zaiyi fishi dani

Copper bash yace karkidamu ba abinda zai miki shima naga alama yana da fahimta
Nan yafada mata yadda sukayi da ya shamsu

Cike da jin dadi Husnah ta tashi tayi hangar waje

Yana kiranta amma taki juyowa saboda kunya

Tana shiga sukacikaro da meenat

Kuka shabe shabe a fuskar meenat

Husnah cikin tashin hankali tace lafiya kuwa meenat cikin rashin sanin mezatace tafara in inna

Tace wallahi bansan menayi wa copper bash ba ya tsani yaganni aguri sai yakoreni

Husnah tace kiyi hakuri zanmishi magana kuma I sha Allah zaiyi dai dai

Meenat ta share hawayenta tace Husnah na tambayeki meketsakaninku da shi baki fada min ba


Husnah tayi murmushi tabata labarin komai

Meenat tace yanzu kinaso kice min kun Dade kuna soyayya da shi

Husnah tayi murmushi tace a
Amma ni banbashi daman zuwa gidan mu ba

Shine yanzu yake cemin ya wa yayana magana


Meenat tarike kai alamun jiri nason yarda ita

Husnah ta taimaka mata tazauna tace Amina Hakeem anya lafiyarki kalau kuwa

Gaskiya kitashi mu dispensary
Abaki magani

Meenat tace gida ma zantafi tai maka min da phone dina acikin bag

Husnah tabude jakar meenat taga wasu hadaddun wayoyi masu tsadar gaske kuda biyu aciki

Ta kwaso duka tace gasu meenat ta karbi daya takira driver din ta

Taba wa Husnah wayar ta mayar mata dashi jaka



******

Bayan kwana hudu ankai sadakin yaya shamsu gidansu kubra

Sannan kuma Abba yasai block da yashi ma aikata sukafara aikin gyaran inda ya shamsu zai zauna acikin gidan ne amma ciki da fall da bayan gida acikinshi

Har Dan karamin kitchen dinta basai ta fito tsakar gida ba


Komai nasu aciki yake

Umma da Husnah sukaje kasuwa suka nemo akwatunansu masu kyau guda uku

Aciki akafara zuba kayan lefe

Wanda yanzu kusan duk asabar sai sunfita kasuwa


Dai dai gwargwado dai aka hada lefen ya shamsu

Aka kai gidansu kubra

Nan da sati biyu za adaura auren



Dubu ashirin ya shamsu yaba wa kubra tayi hidiman biki dashi



*****
Hakeem zaune kan kujerar yana hada wani muhimman file

Sai Ahmad yashigo yace wai baka gama ba har yanzu kasan time kuwa

Hakeem yace nagani ai nan da Kaduna dai insha Allah komai dare

Ahmad yace Allah yasa nidai kai nake jira kawai nagama shirina


Hakeem yayi dariya yace bantaba ganin ango merawankai irinka ba Ahmad

Ahmad yayi dariya yace ai gwamma ni kai inkatashi karawa ai bansan dokin dazakayi ba


Hakeem yayi murmushi dayake kara fito da zallan kyanshi

Yace tabbas kuwa lokaci yakusa zuwa inji ajikina nakusa samun choice dina sai dai bansan a inabane


Ahmad yace kai amma fa akwai rigima Dan madam Laila zatayi rikici bakadanba

Hakeem yayi murmushi yace zatawa kanta danzan iya komai akan matata da zan aura Dan itace zabina
Kaga kuwa ta taka a sannu


Ahmad yace wallahi man I like your style gaskiya zanso Gina gidana kaman yadda kake handling naka


Hakeem yayi murmushi yace banbaka shawarar hakanba
Dan na tabbatar Aisha ba halinsu daya da Laila ba

Kagakuwa ba za amusu hukunci iri dayaba ko

Ahamad yace gaskiya Dan hankalin Aishat nagani yasa har nayi shaawar aurenta



Ya shamsu yashigo ya musu sallama suka amsa suka mika mishi hanu suka gaisa


Ya shamsu yace wa Hakeem gani yallabai

Hakeem yace dama zanfada maka ne zamu tafi Kaduna

Sai nan da sati daya zamu dawo

Hakeem yadauko invitation card na auren Ahmad

Yabawa ya shamsu yace muna gayya tarka daurin aure

Ya shamsu yayi murmushi yace masha Allah
Allah yabasu zaman Lafiya

Sai dai ranar yazo dai dai danawa auren


Hakeem yakalleshi yace har ansa rana baka fada minba malam shamsu

Dama bakayi niyyar gayya tarmu bakenan kokana ganin inka fada ma bazamu bane

Ya shamsu yayi murmushi kawai yace aikuna kokari ma da aiki
Kuma har ga Allah bani tunanin inna Baku invitation zakuzoba

Saboda matsayinmu badayaba

Hakeem da Ahmad suka kalli juna

Ahmad yace haba malam shamsu karkace haka saikasa muga kaman mu ba mutane bane

Ya shamsu yace to afuwan

Nayi kuskure

Hakeem yace to yanzu dai bazamu samu zuwaba amma muna maka fatan alkairi


Tace ban account number din ka inbada nawa gudumawar asiyawa amarya kaji

Ya shamsu yace wannan yana daga cikin dalilin dayasa naji fada muku zamanin yanzu kowa yana fama da kanshi

Dan Allah kabarshi karka damu kanka


Hakeem yace karka damu ni nayi niyya kuma kasan bakyau maida hanun kyauta baya

Ya shamsu yace hakane yakaranto wa Hakeem number account din

Shima Ahmad yanaji kuma ya kwashe number.



Hakeem yace zakaji alert Allah yabada zaman Lafiya

Ya shamsu yace ameen nagode

Sukayi sallama har wajen mota



*****

Da daddare suna zaune tsakar gida ya shamsu yace Abba da ina son ba wa manemin auran Husnah dama yaturo iyayensa

Kaga tana gama makaranta sai aiyi aurenko

Baban yace ai nalura yaron nan bashir kaman da gaske yakeyi

Umma ta ce sau biyu yana kawo mahaifiyarsa muna gaisawa

Shamsu yace alhamdulillahi gaskiya konina yaba da bashir

Kara shigowar sako yaji a wayarsa yaduba yaga alert ne na dubu Dari biyardaga professor Ahmad


Kafin yayi magana wani alert din yasake fadowa daga boss dinshi a office

Wato professor Hakeem

Shima dai dubu Dari biyar dinne yaturo

Sun hada mishi 1 million NIRA cas su biyu suka bashi

Nan shamsu yakalli mahifinsa yafada musu


Abba yace kai amma wannan uban gida naka Allah yasaka mishi da alkairi
Umma tace ameen wallahi ko a mafarki bamutaba tunanin samun dubu Dari nan kusaba

Ballantana har million daya Allah yasaka musu da alkairi

Kai kuma saika kazauna dasu da zuciya daya

Nan dai ya shamsu yakira Hakeem a waya yace ga Abba na zai muku godiya

Hakeem yace haba shamsu yanzu saboda kyautar da baitaka kara ya karya ba zaka wahalar da Abba wajen gode mana

To gaskiya indai Dan inbari Abba yagode min ne zankashe wayata

Insha Allah idan nadawo zanzo nagaisheshi da ka ina amma banda godiya tsakanin malam shamsu

Ka gaida umma da kanwarmu

Sai da safe
Dif
Hakeem yakashe wayarsa


Dama wayar ya shamsu a handsfree take duk su Abba sunji komai

Abba yace gaskiya duk inda akeneman shugaba nagari wannan yaro ya kai
Allah yarabashi da sharrin duniya Lafiya

Ameen Ameen gaskiya dai bantabajin mekudi hakaba da Jan talakawa ajikinsa kamar wannan uban gidan naka

Nan dai suka ta tatattaunawa akan yadda za ayi da kudin

Abba da umma dai suka barmai zabi

Ya shamsu yace shikenan Allah yakaimu gobe aga yadda za ayi

Itakuwa Husnah Allah Allah take safiya tayi taje school taba wa aminiyarta labari

Za a ba copper bash daman turowa gidansu



Washagari Husnah da meenat suna zaune a inda suka saba zama

Husnah tabata labarin za a ba copper bash daman turowa gidansu

aikuwa gaban Meenat yatsinke ras

Wani tashin hankali ya ziyarceta
Tarasa meyake mata dadi

aikuwa har aka tashi daga school meenat batadawo dai dai ba

Tana kallo copper bash ya budewa Husnah gaban motarshi zai kaita gida

Dan tunda aka sanshi yaroki alfarmar zai dinga dawo da Husnah gida idan antashi


Da kyar aka yarda mashi Dan saida yahada da mom dinshi

Husnah tana daga wa meenat hanu Ina AMIN ABDUL HAKEEM kam batasan tanayiba

Ta Lula dunitar tunani



**
MEENAT tana zuwa gida tafada cinyar hajiya rukayya kakanta

Tafashe da kuka maitsanani

Hankalin hajiya rukayya yatashi Dan ta dauki soyayyar duniya ta daura akan 'yar jikan nata bakaramin so takewa Amina ba

Nan dai dakyar tasamu meenat tayi magana

Tace hajiya nashiga uku nakusan mutuwa

Wallahi idan ban auri copper bash hajiya zaku iya rasani dan mutuwa zanyi

Nan hajiya rukayya tace kwantar da hankalinki kimin bayanin komai

Nan meenat ta kwashe komai tafada mata

Ba abinda yafi burge Hajiya rukayya a labarin sai jin cewan

Bash Dan hamshakin mai kudine a kano


Tace kwantar da hankalinki kaman yazama naki ma anfama

Aure shida Husnah kuma yazama tarihi

Zanje Kaduna aiko
Zan baki mamaki bash da bakinshi zaice yanasonki


Next page

Your comments is needed fans

Kamar yadda nayi typing metsayi haka nakeson

Comments dinki da tsayi

Wallahi comments mai tsayi yana burgeni
Sosai

Ina yinku masoya AKWAI LOKACI=ØÞ=ØÞ=ØÞ=ØÞ=ØÞ=ØÞ



=ØÝÜ=ØÝÜ=ØÝÜ=ØÖÜ=ØÖÜ
[05/05, 11:08 AM] UMMU AFAN <Ø9ß: <Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß<Ø—ß

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


<Ø—ßHAKKIN MALLAKA NA UMMU AFAN <Ø—ß


<Ø9ß<Ø9ßFIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATION<Ø9ß<Ø9ß

<Ø9ßF.C.T.W.A<Ø9ß



<Ø9ßHOME OF QUALITIES AND TRUSTED WRITERS OF THE NATION<Ø9ß



<Ø—ßDEDICATE THIS PAGE TO adda khadija and shamsu ina yinki over sister
Dik ina ganin comment din ki akan novel di na
Wato AKWAI LOKACI=Ø‹Ü=Ø‹Ü=Ø‹Ü=Ø‹Ü

Daya bayan daya zakuji sunanku masoya AKWAI LOKACI FANS GROUP =Ø‹Ü=Ø‹Ü keep comments kawai =ØÞ




<Ø—ßAKWAI LOKACI<Ø—ß




<Ø—ßPAGE 51 to 60<Ø—ß





Ya shamsu ya yagyara wa iyayensa gida dai dai gwargwado

Har anyi fenti sabo gida sai kamshin sabon fenti yakeyi da sabon siminti


Ya zuba wa umma sabbin kujeru dai dai karfinshi

Sannan shima ya zuba a dakinsu shida kubra

Yasai TV guda biyu dayasa wa iyayensa daya kuma yasa a sashinsa

Sannan kuma yama umman shi dinkuna kala biyar na fitan biki sai yama abbanshi ma kala biyar shima masu kyau shadda da kuma yadi

Umma har da hijab uku da ta kallamansu
Uku


Sai Husnah kuma yamata kusan kala bakwai dai dai karfinsa
Ya hada mata da mayafai guda biyar da takalman ta hudu

Sai kayan kwalliya da dai sauransu

Yafi kashe wa Husnah kudi acewanshi ita tafi bukatar hakan


Yama kubra ma kayan fitan biki yace kartayi amfani Dana lefenta

Sannan kuma yasa wa abbanshi kaya a shago Dan dama Abba yana shawa ar sana ar awu na hatsi



*****

Yauce ranar daurin auren shamsu da amaryarsa khadija
Komai yatafi yadda akeso

ankai amarya dakinta dake cikin gidan su shamsu



****

an daura auren Ahmad da amaryarsa Aisha
Suna shirin zuwa dinner ne Wanda PROFESSOR HAKEEM ya hada wa babban abokinsa


Hakeem da Ahmad sunyi shiga iri daya wani hadadden suit suka saka ango yasaka baki nacikin ja

Sai Hakeem kuma yasaka brown colour na cikin sa fari

Duk Wanda ya kalli PROF HAKEEM sai yasake kallonshi


'Yam mata sai rawankai suke musam man kawayen amarya


Laila ma taci ado cikin wani tsadadden less Wanda tayi order daga malesia

Tayi kyau kan nan yasha gashin doki
Fuska kuma yaci bleaching kana ganinta dai kasan anci duniya

Ango yashiga mota zuwa gurin dinner

Hakeem yabude mishi bayan mota Laila kuma ta babbar kawar amarya kuma ta bude wa amarya dayan gefen tashiga


Hakeem ne zaija motar ahmad yace Man please kamin wata alfarma mana
Hakeem yace ina sauraronka malam ango

Ahmad yace kasan idan muisa wajen babbar kawar Aisha ce zata bude mata kofa tunda kai kadaine a gaban motar ta shiga muje kawai

Hakeem yayi shiru alamun ya amince kenan

Shine rahma kawar amarya tashige gaban mota tana gaida Hakeem ya amsa a dakile kaman bayaso



Suna isa kuwa bayan Hakeem yayi parking aikuwa har 'yan gulma sunje sun sanar da Laila cewan ga Mijinta ya dauko budurwa a gaban mota


ai kuwa tafito kaman wata mahaukaciya dai dai lokacin da rahma kawar amarya take fitowa daga motar Hakeem


aikuwa rahma batayi tsammani ba sai taji mari kau sannan kuma akasa kafa aka kwasheta

aikuwa yazo da tsautsayi rahma tabuga kai sosai take kuwa ta suma

aikuwa cikin tsannanin bacinrai Hakeem yadauki hanu ya zabga wa Laila mari yasake kwasheta da mari

Nan fa mutane aka taru ganin wannan Abu da Laila ta aikata
Nan da nan 'yan uwan rahma dama suma suna gun sukace basu yarda bayan ansa mata ruwa ta farka


Hakeem yace kinayin abin kika dama ina kyaleki idan zanyi aure kin isa kiha nanine

To barin fada miki daga yau kikasake min dabban ci irin haka wallahi zanyi maganin ki ban wawaiya kawai

Wasu da basusan suwayeba

Wata 'yar dattijuwa ta matso tace haba 'yar nan Kinsan fa yaran yanzu ba a hanasu auren abinda sukeso koda kuwa iyayensu ne
Ballantana keda gani dai baki haifeshi saidai kizama yarshi aisai hakuri

Tajuya kan Hakeem tace haba d'ana da hankalinka zaka mari yayarka a cikin mutane akan mace

Wasu abin dariya yabasu wasu kunya wasu kuma haushi

Musammam meenat cikin gatsali tafito daga cikin taron

Tacewa matar nan dalla malama kirufemana baki
Wayafada miki kanintane dazakisa mutane agaba da surutu to banana ne itakuma mamana ne Dan haka kikama gabanki bamason muna furci

Wato cikin tsananin bacin rai Hakeem yadanko Amina yayi mota da ita ya wurga ta ta tashi motar sai gida

aikuwa Laila tace shikenan zaikashe min 'yartawa Dan zata kwacewa uwarta 'yanci
Tana ihu tana kokarin shiga mota sai saiga motan police nan sunzo tafiya da ita 'yan uwan rahma kawar amaryace suka dauko 'yansanda aikuwa suka tafi da Laila


Hankalin Ahmad yatashi yace wa Aisha amarya tayi hakuri bari yakira akawo mishi mota subi bayan Hakeem Dan komai zaiya faruwa



Hakeem na isa gidansu yayi sashen sa Meenat ya dauki belt dukanta yasoma

Kuka sosai meenat take tana bashi hakuri

Wayyo Allah daddy kayi hakuri wallahi bazan sakeba yace Ashe baki da mutunci kikalli kaman wannan matar kimata rashin kunya ko

Abinda uwarki da kakanki suka koya miki ko
To ba agidana ba Dan ubanki

Mummy hafsat ce yashigo da kyar ta karbi meenat agurin uban

Hakeem ya kalli mummy yace mummy Dan Allah bana son yarinyar nan ta koma gurinsu
Kwatata sunbata wa yarinya tarbiyya

Mummy hafsat tace wai meyafarune nan Hakeem yafada wa mummy hafsat komai harda dabbancin da uwarta tayi a wajen dinner


Mummy hafsat tayi salati tace yanzu wadan nan mutane bazasu canja haliba gashi harsuna Neman bata mana jika


Kaman daga sama kuwa suka ance sannu masu tarbiyya
Dana nasan ba Wanda yake haddasa fituna saike hafsat

To wallahi anzo gurin da banzan bariba dan me zaudauki hanu yata dukan matarshi acikin bainar jama a


Mummyn Hakeem tace aini abinda Hakeem yayi amin dai dai duk abinda Laila takeyi tasamu daurin gidinkine yaya rukayya


Hajiya rukayya tace wato kekikabashi daman yadauki karuwa a mota ko

Mummyn Hakeem tace ya isa haka yaya rukayya wallahi zanyadda da komai amma banda mummunan kazafi akan Abdul Hakeem

To wai ma da kuke wannan haukan wayace muku Hakeem bazai kara aure ba

ai Karin aure akan Hakeem wajibine Dan wallahi koshi baiyi niyya ba nizansashi aure dolene


aikuwa hajiya rukayya tafashe da kuka tace yanzu hafsat nizaki cewa mahaukata ina matsayin yar mijinki kidubi tsaban idona kice muna hauka

Mummy hafsat tace duk abinda yafaru kokuka janyo
Kuma wannan yarinya da kuka sangarta bazata koma wajenkuba

Zanriketa har Allah yasa tagane gaskiya tadawo hanya bakaman Ku da kuka bata ba



Hajiya rukayya tace wannan kuma baki isaba hafsat kinyi kadan kirabani da jikata

Mummy hafsat tace zancen kikeso

Tana amina fuuuuuu suka bar falon



Hakeem kuwa barin falon yayi zuwa dakinsa

Sukabar hajiya rukayya kaman tafashe dan bakin ciki

Wayar hajiya rukayya tayi kara taduba taga Suby ce kanwar Laila tace kekuma ya akayi

Suby cikin tashin hankali tace mama gamunan a police station ankulle anty Laila

Hajiya rukayya tace wani station din kuke

Nan tafada mata tafita zuwa police station din

Hakeem yana shiga bedroom dinshi wanka yashiga

Kafin yafito yadan kwanta yana tunanin bakin hali irin na Laila da 'yan uwanta


**
alhaji abubakar yana office din shi azaune saboda yayi baki daga India

Sai yaji kiran yayarshi hajiya rukayya

Yadauka tare da sallama
Hajiya rukayya tafashe da kuka tace duk inda kake kazo gida ba Lafiya

Matarka da 'danka zasukashemin 'yata da jikata

alhaji abuabakar yace subahanalla ganin zuwa yaya kidaina kukan Dan Allah


Ya kashe wayar yadau hanyar gida

Yana zuwa yasamu yayansa hajiya rukayya a kofar gidanshi
Yafito amota da sauri yace mekefaruwa ne haka

Nan dai ta kwashe karya da gaskiya tafada mashi yace yanzu kishiga mota muji police station din ayi belinta
Inyaso sai mudawo gida a yi magana


Hajiya rukayya tashiga mota suka nufi can police station din
Suna isa tun kamin ayi parking suka ga Ahmad da Laila

Ahmad yaga motar daddyn Hakeem sai yakaraso gurin motar yagai da daddy

Daddy yace sunbaka belin kenan
Ahmad yace a amma dakyar suka bayar sai da nasa hanun zata je har gida tabawa yarinyar data sumar hakuri

Daddy yace Allah yarufa asiri kaima kayi kokari Ahmad Allah yabaku masu yimuku

Ahmad yace ameen daddy barin karasa gidan

Daddy yace wa Laila tashiga bayan motar sutafi tabude bayan tashiga

Ta madubi hajiya rukayya tace Dan Allah kalli yadda suka mayar min yarinya saikace wacce bata da gata


Alhaji abubakar dai baice komai har suka isa gida


Duk yatarasu a falo Hakeem na zaune daddy yace banji daddyn abinda yafaruba naji komai

amma ina insan kai Hakeem wace mata kadauko agaban mota nan Hakeem yawa mahaifinsa bayanin

Hajiya rukayya tace karya kakeyi kana nufin Laila Karya zata maka

Mummyn Hakeem tace to ita Lailar uwarshice dabazata mishi karya ba

Daddyn Hakeem ya ce ban baki iznin maganaba hafsatu kiyi shiru

Mummy hafsat tayi kwafa

Nan dai daddy yayi musu nasiha meshiga jiki

Hajiya rukayya tace sai maganar yarinya sunce wai bazan koma da Amina ba

Daddy ya kalli Hakeem yace yazakayi haka bayan kuma yarinya dasu tasaba

Hakeem yace daddy idan har yarinyar nan zata koma to ta gaggauta fito da miji tana gama secondary school kawai aiyi aure

Dan wannan da irin tarbiyyar dasuka bata nan gaba zata iya fin karfin mutane

Mummy hafsat tace wannan shawarar taka tayi dai dai
Dan bazanso jikata ta acikin wannan rayuwar da ba asan nagaba ba

Hajiya rukayya tace kaga abubakar kashiga tskanina da matarka

Daddy Hakeem yace wa mummy hafsat Dan Allah karkisake cewa komai sai na baki dama


Nan alhaji abubakar yace zata koma amma

2 Comments On AKWAI LOKACI
avatar
musa-6-3-2

1 year ago

Reply

Akwai lokaci

avatar
oumara-wassai

1 year ago

Reply

Replying to musa-6-3-2

17866

Please Login or Register in order to submit comment