Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚 LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA*🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀











*NA*


_BINTA UMAR ABBALE_
~*®BINTU BATULA👄*~



*MARUBUCIYAR*

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```

_*LOODING:*_
_*{LADIDI K'WADAG'A🌚}*_




_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_





_BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM_




_*NA FARA DA SUNAN ALLAH ME RAHAMA ME JIN K'AI ALLAH KAYI DAD'IN TSIRA GA ANNABI MUHAMMADU (SLW) DA ALIHIN SA DA SAHABBAN SA BAKI D'AYA*_




_*TSOKACI*_


_*WANNAN LITTAFIN K'IRK'IRAR RE NE DAGA NI MARUBUCIYAR BAN YI DAN WANI KO WATA BA, WANDA YAGA YAYI DAI-DAI DA RAYUWARSA TO A RASHIN SANI NE*_



*_KUNA INA DUBUN DUBAN MASOYA NA, A DUK IN DA KUKE INA MUTUK'AR ALFAHARI DAKU WALLAHI KUNA DA DA BABBAN MATSAYI A CIKIN ZUCIYA TA, HAKIKA BANA RAINA MASOYI DUK INDA YAKE INA MUTUK'AR K'AUNAR KU SOSAI DA SOSAI_*




*_MACE MAI KARAMCI MACE MAI AMUNCI MACE ME MUTUNCI MACE MAI KIRKI MACE MAI DATTAKO MACE ME KYAWUN ZUCIYA MACE ME SON CIGABAN WANI MACE ME AIKI DA ILIMINTA_*
_________________________
*_HAUWA S ZARIA MAMAN USUWAN_*
_________________________

_*HAK'IKA WANDA BAI SANKI BA SHINE ZAI MIKI MUMMUNAR FAHIMTA, INA ROK'ON ALLAH YA SHIGA LAMURAN KI YA DAFA MIKI A DUKKANIN ABUNDA KIKA SA A GABA, UBANGIJI ALLÀH YA RAYA MIKI ZURI'AR KI*_



_*ALHERIN ALLAH YA ZO IN DA KIKE ZAINAB ABDULLAHI REAL SHAXXI KIN IYA KIN HUTA INA MIKI FATAN ALKAIRI A RAYUWAR KI PEGE D'IN FARKO NA SADAUKAR MIKI DASHI KIYI YADDA KIKE SO DASHI*_




_*ALLAH MAI MUTANE ALLAH D'AYA GARI BAM-BAM HAKA KURUM SAI UBANGIJI YA HAD'AKA DA MUTUM ME KARAMCI ME SONKA DA SON ABUNKA ALLAH NA GODE MAKA DA SAMUN KI K'AWATA TA KAINA INA MIK'O GAISUWA TA GARE KI*_
________________
*FAUZIYYA MU'AWUYA*
________________

_ALLAH YA SHIRYA MIKI ZURIA YA BAKU ZAMAN LAFIYA DA MIJIN KI_




_*BAZAN TAB'A MANCE ALKAIRIN KI BA*_
_________________
*RAHAMA ALIYU*
_________________
*WANNAN MA NAKI NE INA YINKI IYA WUYA ANA TARE*🤝🏻❤




*🅿1*




*Misalin k'arfe biyar da rabi na yamma*


Wasu yara na hango sun
yanko da gudu suna ihu! tare da fad'in "Ladidiya me kwarkwata a tab'a kad'an ta sosai kai, a tab'a ta kad'an ta ce kwarkwata ta dame ta a tab'a ta kad'an ta ciro kwarkwata,ladidiya me kwarkwata yeeeee!!! Ladidiya me kwarkwata!!! Da k'arfi suke fad'a suna gudu sosai dukanin su da allo a hannunsu da alama daga makarantar allo suka taso.

Can na hango wata yarinya " yar kimanin shekaru tara zuwa goma ta yanko da gudu, daga kwanar da suka futo,hannunta rik'e da allo take gudu tun k'arfin ta k'okari kawai take ta riske su ta samu na duka ta daka babu abunda ya dame ta.



D'aya bayan d'aya suka dunga shigewa gida ba tare da ta kama ko d'aya ba, ya rage saura mutum biyu,, dukan su "yan hanyar sune,, gudu suke tana gudu, har ta riske su, rai a b'ace ta fuzgo hijab d'in d'aya daga cikin su, ta maka ta da k'asa,d'ayar kuwa ganin an kama " yar uwar ta ya sa ta k'ara k'aimi gurin gudu sai da tayi nisa sosai ta tsaya ta tsinci dutsina ta dunga jefo wa Ladidi su, ko a jikinta, tunda Allah ya sa ta kama guda ta taki sa'a, hawa tayi kan "yar mutane ta shak'o wuyanta tace" Dan ubanki wa kuke tsokana kuna gudu kuna cewa me kwarkwata,, Alawiyya ta fara k'ifk'ifta ido saboda tasan halin bak'ar muguntar Ladidiya sai kace me aljanu haka take da mugun k'arfi sosai take faffasa wa mutane baki,, cikin inda-inda tace"Wallahi bani nace su Shatu ne da Habiba suka fara tsokanar ki, don Allah kiyi hakuri" Ko a jikinta ta kai mata duka a baki tana cewa"Da dai ban ganki bane yarinya ni zaki rainawa hankali wallahi yau he na lahira ya fiki jin dad'i kin tab'owa kan ki bala'in....k'aik'ayi da taji kanta na damun ta dashi ne yasa ta daki kan da hannunta ta sosa sosai gami da dukan in da yake mata k'aik'ayi,, sai da ta tabbatar ta daina jin sosar ta dawo kan Alawiya ta kai mata mari a fuska, tace"Wallahi kika sake CE min me kwarkwata sai na ciro guda goma na sa miki a kanki"


Alawiyya tace"Kiyi hakuri bazan k'ara ba"duka ta kai wa bakin tana fad'in ki k'ara mana sai na zubar miki da hak'ora shegiya mummuna kawai"


Alawiyya tasa kuka ganin yadda jini yake zuba daga bakinta, ga hakurin ta guda na girgid'i kuma na gaba ne, hakuri kawai take bata.

Sai da ta gama dukanta iya son ranta sannan ta d'aga ta, ta gyara d'aurin zanin ta Wanda ya d'angale sama har kusan cinyar ta ana hangowa ta d'auki allon ta ta k'ara gaba ta bar Alawiyya kwance a gurin,, Can ta hango gefan Hijab d'in Habiba ta b'uya a wani lungu da alama b'uya tayi ganin ta wowar LADIDI, sad'af-sad'af ta k'arasa gurin ta jawo hijab d'inta sai ga Habiba kwance a k'asa ihu ta kurma ta mik'e a sittin ta ranta ana kare Ladidi ta rufa mata baya.




Tun daga nesa Lado me icce yace"Ga sababbiya nan fitanniya me k'arfin jinnu ta biyu maka "yar zata daka"


Da Sauri Malam Harisu ya kalli inda Lado yake kallo aikuwa ya hango "yar sa Habiba na gudu Ladidi na bin ta a baya, mik'ewa yayi da sauri yana fad'in " Wallahi Ku bushiyar kuka ce a kan yarinyar nan bata Isa ta dukar min yarinya na na k'yaleta"


Kai tsaye gurin babanta ta nufa tana baki! Tasan k'aryar Ladidiya ta k'are tunda ga ta ga Babanta bata Isa ta dake ta ba,, kafin Malam Harisu ya an kara kawai yaji an in gije shi guri guda saura kad'an ya fad'i LADIDI tayi kukan kura ta dura kan Habiba ta kwantar da iita k'asa gami da haye wa ruwan Cikin ta ta kama dukan kayanta.

Cikin k'arfin Hali Lado me ice ya k'arasa gurin yana fad'in "Ke Ladidi me tayi miki kike k'okarin raunata ne, d'aga musu yarinya Dan ubanki in kin kashe ta Kakar ki me koko kika sa a bala'in"

Hannun guda tasa ta daddaki inda yake mata k'ai k'ayi ta Sosa ta sosa yadda ya kamata. Ta cire hannun ta tana fad'in "Kai lado me ice babu ruwanka kuma kar ka k'ara zagin Ubana idan ba haka ba zaka fuskanci hukunci .........Lado ya zare ido yana kallon ta da jin abunda tace wai zai fuskanci hukunci Lallai Ladidi kunyar ta ragaggiya ce, yace"Au! Nima zaki zage ni ne mara kunyar banza da wofi"


K'unk'uni Ladidiya ta fara yi tana fad'in "Wallahi ni ba mara kunya bace,shikkenan dan suna da gata sai su tsokane ni su gudu su masu iyaye nima ai ba daga sama na fad'o ba, Allah ne ya amshi ran iyaye na"


Sam! Lado bai ji abunda take cewa ba,yasan dai bazai wuce zaginsa take ba, sai yaja bakin sa yayi shiru gudun ta zage can gurin sana'ar shi ya koma ya zauna,, yana kallo Malam Harisu ya nufi gurin yana zagin Ladidi aikuwa ta hau dukan "yar sa tana rama zagin akanta, fad'i take" Haka kawai ai uba bai fi uba tana dukan Habibu tana ambato sunan Harisu tana zagi babu abunda ya dame ta, ya k'araso gurin gami da Kai mata duka ta goce ya samu "yar sa,dariya ta kwashe da ita mik'e daga kan Habiba ta d'auki allon ta sai dariya take k'yalk'yalawa ta mayar dashi mahaukaci tace" Wai shi dole sai yayi irin dukan su Salman Khan da Ashe kumar mutanan hindiya hahahahaha, Habiba Baban Ku Ashe d'an hindiya ne"" Malam Harisu kamar ya d'ora hannu aka don bak'in ciki, yana kallon ta wuce bagaz!-bagazan! Tana tik'ar dariya.



Lado yana gefe shima dariya kamar ta kashe shi fad'i yake"Kad'an daga iya shegen Ladidiya ta gidan Iya me koko kenan shiyasa na k'yaleta nayi zamana,, hahahaha" ya k'arashe maganar yana dariya


A fusace Harisu yace"Ai wannan yarinyar dole ne ma inje in ja mata kunne gaban kakar tata me koko idan ba haka ba wallahi sai na kai k'arar ta gurin me gari"
Ya k'arashe maganar yana d'ago Habiba dake kwance tana rik'e da bakinta inda leb'an ta na sama ya kumbura suntum!


Lado yace"Ko kaje gurin me gari babu abunda za'ayi mata, kawai ka jawa "yar ka kunne ta daina shiga sabgar ta,, su daina tsokanar ta,Iya me koko tana da fada a gurin me gari wallahi babu wani hukunci da za'a d'auka kan Ladidiya"





*COMMENT VOTE AND SHARE*
[9/21, 8:18 PM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀*


*NA*
_BINTA UMAR ABBALE_
~*®BINTUBATULA👄*~



*MARUBUCIYAR*

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```

_*LOODING:*_
_*{LADIDI K'WADAGA🌚}*_




_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_

______________________
```We are here to educate motivate and entertain aur reades```
_______________________



_*DEDIGATED*_
*TO*
_RAHAMA ALIYU_




_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_




*🅿2*



Harisu yace"Dole ne fa naje na fad'awa Iya mai koko domin ta ja mata kunne kar watarana ta jiwa yarinya ta rauni, ta barni da siyan magani, ko ka manta ne ko wata uku ba ai ba, yarinyar ta karya "yar gidan Tanimu Harira,, yarinya sai kace k'ashi saboda da rama, sai mugun k'arfin tsiya malam, anya kuwa babu aljanu a tare da ita"?
Ya k'arashe maganar yana goge gumi dake tsattsafo masa a goshi.


Lado yace" Ka iya bakin ka dai in kaje gurin me koko kasan halin Masifar ta, domin kuwa ta tsani ace da Ladidi tana da jinnu"


Harisu ya kama hannun "yar sa Habiba sukayi gaba, sai mita yake.

Shiko Lado redio ya kunna abunsa yana sauraron dawowar shi yaji ya suka kwashe da me koko.

Iya na tsaye da abun tata a hannun ta, tana gyarawa gefe guda kuma wata k'atuwar tukunya ce,cike da mark'ad'an gero da ruwa a gefe cikin wani duro,, tun d'azu take jiran dawowar Ladidi tazo ta taya ta zuba kullun gasara domin ta tace, saboda kokon gobe da safe, ko guntuwa bata da ita, gashi tun asubah ake mata layi na siyan koko. Gajiya tayi da jiran Ladidi ya sa ta mike tana mita taje ta fara gyara matacin tata,, kawai sai ga ta ta afko gidan babu ko sallama.


Cikin mamaki ta kalle tace"Yau ba arzk'i kenan kin shigo babu ko sallama"?

Zumb'ura baki tayi ta wuce bagazan-bagazan ta d'auki buta, ta duba taga babu ruwa a ciki wata tsohuwar rijiya ta nufa ta zura guga na gwangwani, ta jawo ta zuba a ciki ta jefar da gugan kan jar k'asar dake jik'e a bakin rijiyar ta shige ban d'aki abunta.

Tunda Iya taga haka tasan da walakin goro a miya yau za'ayi kwanan masifa kenan in ba Allah ne ya rufa asiri ba, aikuwa tana tsaka da zan can zuci ne taji sallama daga can waje.


Abun tatar ta rataye kan Igiya ta d'ora mayafi aka tana tafe tana amsa sallamar. Malam Harisu ta gani tsaye shi da "yar sa Habiba sai muzurai yake, Gyara fuska tayi ta sha kunu sosai tace" Amun wa'alaikassalamu da Harisu wannan sallamar fa kuma? Sai ka wacce taci bashi"


"Ba dole in zabga Sallama iyi,, Ladidi tana nema ta rauna ta min yarinya dubi yadda ta fasa mata baki ya kumburi har leb'an kasa ya Tsage,shine Nazo na fada miki ki ja mata kunne wallahi ta kiyaye ni, kuma ta daina dukar mi " yata domin ni ba Tanimu bane ehe"!


Wani kallo iya ta watsa masa tace"Kaji ka da wani zance Harisu, ni dai na san haka kawai Ladidi baza ta doki Habiba sai da dalili watak'ila tsokanar ta sukayi, ayyo! Shiyasa naga ta shigo gidan a fusace"!



Harisu yace"Ai dama nasan baza ki yadda ba,, kullum idan an kawo miki k'arar ta sai kice tsokanar ta akayi to ni daina wallahi na fada miki ki ja mata kunne gudun abunda zai biyo baya "


Mai Koko tace"To gatanan ga kanan Harisu, kun bi gun addabi marainiyar Allah ta'ala komai tayi a unguwa sai a hau zaginta da ai bata ta, nace Harisu ga Ladidiya nan ga kananan Ku zuba mugani tunda dai ka k'i ka tsaya balle in baka hak'uri"


Katangar band'akin had'e take da ta soran gidan Duk abunda ake Ladidi naji ko gama kashin bata yi ba ta d'auraye jikinta ta futo jefar da butar tayi ta futa da sauri
Tsayuwa tayi a tsakiyar su,, tana sosa kanta gami da duddukan sa,, da sauri Harisu ya matsa da baya domin baiyi tsammanin ta a gurin ba, tsidig! ya ganta, ita kan ta Mai koko ganin ta kawai tayi kamar an jefo ta,, Habiba ta rakub'e a bayan Baban ta tana zare ido..

Fashewa tayi da dariya, har yanzu hannunta na kanta tana sosawa tace"Harisu Dan Hindiya Hahahaha yanzu ma k'ara gwada naushi na ka gani ko zaka same ni,, Hahahaha ta cigaba da k'yalkyala dariya, ta kalli Mai koko dake b'oye dariyar ta tace"Kinga Iya wai Babansu Habibu ne d'azu ya kawo hannu zai naushe ni, sai na kauce da sauri ya naushi bakin "yar sa,, wai dole ga Ahe kumar wannan me k'arfin nan na hindiya"


Iya ta sa dariya tana fad'in"Yo Ashe kaine ma ka fasawa d'iyar ta ka baki amma saboda neman magana ka kawo k'ara"

Tsabar bak'in ciki bai bar Harisu yace Komai ba yaja hannun "yar sa suka wuce gida yana cizon ya tsa.


Iya ta gimtse da dariyar da take tana kallon Ladidiya tace" Ina raba ki da kiwon kyalla kina kyalla ta haihu,, ki sani fa baki da wani gata a cikin wannan garin , ni da kike tunk'awo dani bani da k'arfi nema nake kullum duk a kanki, hakanan wannan k'aramin uban naki D'alha da yake fad'i tashi duk akan ya in gan ta miki rayuwa ne, kullum ina fada miki babu ruwan ki,, da yara unguwa ki daina dukan "yayan mutane kada watarana ki jawo mana masifar da baza mu iya ba, Yo in badan ma me gari yana daure miki gindi ba, ai da nasan mutanan garin nan sunyi k'uli-k'ulin kubura dake saboda yadda kika addabe su babu yara babu manya"


Kartar kanta kawai take hannu bibbyu tace"Iya wallahi kin san halina bana barin bahi duk hegiyar da ta tsokane ni sai na zane ta,, da Alwayya da Habiba da Fainusa da Abule da Mariya ne, suke tsokana ta a makarantar allo sunayi min ihu bayan an tashi Wai me kwarkwata, to na kama biyu saura uku billahil lazi sai na zane su suma"


Tsaki Iya taja tana fad'in "Kece ai ko ina sai ki ta sosa kai in ta kama ma ki d'auko ki kashe dan shashanci,, ni narasa wace irin kwarkwata ce wannan me mugun naci sai kace iska sam bata jin magani"


"Tabd'ijam kin San yadda take cizo na kuwa iya wallahi in ina sosawa har dad'i nake ji" Ta k'arashe maganar tana dukan kanta gurin da yake mata k'yayk'ayi.



Iya tace"Ni wuce muje ki d'auraye hannun ki k'azama ki tayani tatar kullu, ga magariba ta gabato"


Ladidi ta tsani a kira ta da k'azama, haushin Iya ya kamata, tw zumb'aro baki gaba,, hanya futa daga gidan tana nufa


Iya tace"Ina kuma zakije"


"Ki samu wanda zai taya ki tatar tunda ni k'azama ce"
Tayi fucewar ta.

Mai koko tabi ta da kallo da baki a sake.






*COMMENT VOTE AND SHARE*
[9/22, 10:03 AM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀*




*NA*
_BINTA UMAR ABBALE_
~*®BINTUBATULA👄*~



*MARUBUCIYAR*

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```

_*LOODING:*_
_*{LADIDI K'WADAGA🌚}*_




_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_

_______________________
```We are here to educate motivate and entertain reades```
_______________________



_*DEDIGATE*_
*TO*
_RAHAMA ALIYU_



_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_




Da sauri ta biyo bayanta tana k'wala mata kira tayi mata banza,, ko juyo wa ba tayi ba, hanyar dandali ta nufa, girgiza kai kurum tayi ta koma cikin gida tana fad'in "Ubangiji Allah ya shirya min ke Ladidi"


D'alha ne yake tafe yana tura baro dake d'auke da goba da mangwaro d'ata,, duk sunyi saura da alama yau kasuwa tayi kyau, can Ladidi ta hango shi ya karyo kwana, zai shiga gida, da sauri ta shige soron wani gida tana lek'en shi, har ya wuce, tai sauri ta futo da gudu ta bar gurin.


A mutuk'ar gajiye ya shiga gidan, Mai koko na tsaye tana aikin tata sai sauri take saboda magari ba tayi,, guri ya samu ya aje abun sana'ar tashi,, ya zauna kan tabarma cikin gajiya, yace"Iya sannu da gida da aiki"

"Yawwa Sannu ka dawo kenan"?
"Eh Wallahi Allah yayi mana dawowa"
"To masha Allah" Iya tafad'a ta cigaba da abunda take
Kishingid'a yayi yace"Iya ina Ladidi take ne? Yau naga aiki yayi miki dare, ko ta futa yawon da tasaba ne"?

Ajiyar zuciya ta sauke tace"Yanzu ta futa ashe ba ka ganta ba, tana futa kana shigowa"

K'wafa yayi cikin b'acin rai yace"Wato yarinyar nan bata jin magana ko Iya"?

"To yaya zakayi ne, sai kayi mata addu'a k'uruciya ce take damunta"

"Nifa Iya babban bak'in ciki na da Ita rashin kamun kai da wasa da maza da take in taje dandali babu shirmen da bata yi wallahi"


"To wai yaya zakayi ne D'alha, nifa bana son kana takura mata, nasan duk abunda take k'uruciya ce watarana zata daina"

Shiru yayi ya daina wahalar da bakinsa domin yasan duk surutun da zaiyi Iya sai ta kare Ladidi duk wani iyashege da yarinyar take itace take daure mata gindi.
Mik'ewa yayi ya d'auki buta ya futa waje domin ya d'aura alwala.


Suna zauna gidin wata k'atuwar bishiyar mangwaro, sun kai su Tara zuwa goma duk sun kewaye ta itace shugaba,, duk sun mimmik'e k'afafunsu suna wasan *nanje na gidan gona* in an cinye mutum sai su kwashe da dariya har da burgima,, ihu! Suke suna fad'in Ladidiya don Allah yanzu ki sauke a kaina,, muga wa za'a kad'awa barbad'in tusa"
"Ku tsaya!Ku tsaya kuji! Ku tsaya kuji"! Ladidi ce take fad'in haka.
Tsit! Sukayi suna sauraron ta,, k'aykayin da taji kanta nayi ne ya katse mata abunda take so tace, cire d'ankwalin tayi ta jefar k'asa ta sanya hannuwan ta biyu ta dunga kartar kan tana lumshe ido,, dad'i take ji sosai in tana sosawa, shiru sukayi kowa yana jin tsoro kar yayi dariya ta doke shi,, tafi minti biyar tana aikin sosa kanta sannan ta cire hannuta tana muzurai,, kallonsu take ta sha kunu domin shaf ta mance a inda take idan tana Sosa kai kwata-kwata mance komai take,, so take taga ko akwai wanda zai mata dariya a cikin su, sai taga duk sun nutsu,, ba tare da ta mayar da d'ankwalin nata ba tace" Ku san me"? Had'a baki sukayi gurin fad'in "A'a sai kin fad'a"

Dariya ta kece da ita tace"Wallahi duk wacce k'arshe ya sauka a kanta to ta saddak'ar da cewar sai anyi mata ihu an k'ada barbad'in tusa kuma har gida za'akai ta anai mata ihu! Kun yarda ko"?

Ihu! Suke suna fad'in "Mun yarda" Mun yarda"

"To kowa ya mike k'afarsa a sako daga farko"

Mik'e k'afafun su sukayi, ta fara yi musu,, duk wacce ta futa sai ta koma gefe tana murna ya rage saura mutum biyu Murja da Indo kenan duk sunyi tsuro-tsuro dasu,, ita ko Ladidi sai dariya mugunta take musu,, Nan je na k'arshe ya sauka a k'afar Indo ta mike da sauri tana murna,, Murja ta mik'e da sauri zata gudu,, Ladidi ta tad'o k'afar ta, tafad'i gurin ,sai suka dauk'i ihu!!!!! Yeeeee!! "Murja warin wando Murja mai wari tusa,akad'a mata barbad'in tusa, a kad'a mata bar bad'in tusa!!!! Su ka ture Murja suna yi mata ihu!! Suna ja mata k'afafu saurin muryar Ladidiya yafu na kowa tashi a gurin.

Hankalin masu sai da nama fura da nono da duk wani mai sana'a gurin ya dawo Kansu,, Mutari me nama yace " Wannan yarinya baza ta tab'a barinmu mu huta ba wallahi duk itace shugaba" Haliru me fura da nono ya nufi gurin a fusace yana fad'in "Bari naje nayi maganin su" Yana zuwa gurin ya d'aga murya yana fad'in "Ke " yar gidan mai koko, zan ci ubanki wallahi idan baki ja zugar ki ba kun bar gurin nan ko an fad'a miki kowa mahaukaci ne irin ki"?

Tsittt! Sukayi jin abunda Halliru yake fad'a, Ladidi ta kura masa ido tana jin takaicin zagin da yayi mata, amma tasan abunda zata yi masa,, ganin sun daina ja mata kafa yasa ta mike da sauri zata gudu, Ladidi tayi saurin damk'e ta tana fad'in " Murja me warin wando Murja me warin tusa yeeee! a kad'a mata barbad'in tusa!!! Aikuwa sauran suka d'auka gurin ya k'ara kacamewa da ihu!! Halliru ya gama b'ab'atun sa ya hak'ura ya tafi domin ko sauraron sa ba suyi ba, haka suka tasa Murja suna ihu! gami da dungure mata kai, har suka kai ta gida,, sai kuka bak'in ciki take,,nan ta basu umarni tafiya kowacce ta kama hanyar gidan su, ita kuwa dandali ta k'ara komawa domin ta aiwatar da k'udirinta. Kan Halliru a ganinta tana raye babu wanda ya isa ya zagar mata iyaye ba ta hukun tashi ba,,

Ta bayan gatangar da suke zaune ta bi,, sosai gurin yake da kwazazzabai gami da ra muka katangar ta d'ane sosai ta hau ta dura, a hankali ta tsuguna tana tattaro k'asar gurin,, zanin ta ta kwance ta zuba k'asar a kai ta nufi inda suke zaune,, Halliru na can gurin wani mai rake suna magana, shi kuma Mutari mai nama kasuwa ta bud'e ana ta cini ki,, da sauri ta bud'e doguwar robar dake cike da nono ta zazzage wannan k'asar me uban yawa da ta d'ebo ta cikin zaninta, ba tare da ta d'aura zanin ba ta bar gurin kamar walk'iya.
Halliru ya dawo gurin da sauri hannunsa rik'e da wata roba me kamar kwanon sha, da ledoji a hannun sa,, wasu matasa na bin bayan sa, da sauri ya bud'e robar nono sa ya zura k'aton ludayi da yake motsa wa,, sai yaji gurin-gurin d'in dutsina da k'asa a ciki,, salati ya rafka da sauri ya zaro cocilan d'insa daga cikin aljuhu yana haskawa, innallahi wa'inna ilahi raji'un , nono ya rine! Ya koma jajazur
DOWNLOAD
DOWNLOAD

1 Comments On LADIDI KWADAGA
avatar
north

1 year ago

Reply

dadi

Please Login or Register in order to submit comment