Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

kawanansu dady biyu da yin maganar auran su Humaid, dady ne yatarasu a parlor'nshi saboda ya gaya musu,halin da 'ake ciki ".

Tunda Humaid yaji wanan kyakyawan albishir ,yadinga farinciki .
Ladidi dajin hakan taji tsoro ya shigeta, saboda tana tunanin,halin da zata shiga ".

Washe gari dady ,yace" ansa biki sati biyu,momy ce tazaro ido tace"sati biyu fa alhaji? dady cikin tuhuma yace "kina nufin yayi kad'an ko¿" eh momy tace.

Dady ne yace"muyi fatan Allah ya kaimu kawai , Ladidi ce kwance a d'aki tana tunanin halin da tashiga, Allah ma yatemaketa Ammar d'in beyi mata komai ba,tunowa da wayarta tayi kukane ya k'wace mata ,tadinga cewa"wlh nayi nadamar saninka Ammar ".
Bayan sati d'aya ,yau biki saura sati biyu ,momy ce take ta shirya Ladidi musamman takira wata k'awarta daga Maiduguri".

Tunda tazo aka fara yiwa Ladidi dilka dasu magunguna ,tun Ladidi nashan 'na marmari har tadawo k'in maganin,se momy tayi da gaske take sha .
Tadena fita ko da harabar gidan'ne , daga d'aki se sallah ,wani haske Ladidi tayi ,dama fara ce gashi kuma ankuma gyarata.
Tunda akasa biki ango Humaid ya dena zama ,shikuwa Jalal kulum cikin siyayya yake".

Yau biki saura sati d'aya, bak'i ne suka fara zuwa na kusa dana nesa ,Inna hauwa ma ta iso itada malam Adamu ,se dangin momy da suka iso saboda shirye shiryen biki".

A yaune lahadi wata k'awar Ladidi tazo tayi mata make up saboda tanada shago, kwaliyar hausa day akayi mata ,duka k'awayen sunsa" farar riga dakuma zanin atamfa da suka fitar anko ,DJ' Jalal ya d'auko musu ,kasancewa gidan yanada fili ".

Bayan Amarya da ango sun fito ne DJ yace " ga Amarya nan itada angon ta ,please kutafa musu "bayan angama tafinne D J ,ya sake wakar da akayi musu ,Humaid 'da baki yak'i rufuwa ya ruk'o hannun Ladidi suna rawa ,sauya wak'ar akayi suka nemi guri suka zauna .
DJ ne yace munason muga nera biyar a gurinnan Jalal yaje yasa dubu d'aya, ana cikin haka ne momy ta fito taja Ladidi tace asa musu wak'ar da 'akayi musu ,Ladidi kanta a sunkuye suke rawa da momy ba k'aramin kud'i momy ta zuba ba.

Ana cikin rawa y'an uwan momy suka fitoda ,su goruba magarya taura aduwa se fate wanda yaji kashi a takeaway dakuma dambu ,kai kowa ya yaba wanan shiri da akayi ,anyi taro lpy an tashi .
Washe gari kuma za,ayi ,kumbo day fans kuzo kuga k'ayatuwa da gurin yayi ,tunda aka fara kumbo ake jiran amarya ,tana can anayimata kwaliya material ne a jikinta me tsada sekuma head d'in data d'aura kasancewar milk ne material d'in ,ta d'aura pink head sekuma takalmi shima pink and milk ,woo gaskiya 'amarya tafito sosai ga k'afar tasha lalle ".
Humaid ne yashigo yasa shadda pink hula milk wow shimafa 'angon ya had'u .
Momy da takejin farinciki tashigo da turare a hannunta ta fesawa Ladidi takuma fesawa Humaid sega y'an uwan momy nan sun shigo suna gud'a.....✍️✍️

Mom Islam ce✍️✍️✍️
*LADIDIN K'AUYE*


Funny & love story.

*Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa*



*NA*

*MOM ISLAM*
*ZAINAB HABIB*


*MARUBUCIYAR:*

*ZAINABU ABU*



*AND NOW*

*LADIDIN K'AUYE*



*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


*Episode:* 19_20


_____wata kakar su Humaid ce ta shigo tana sanye da wata tsaleliyar atamfa, daka ganta kasan nera tayi kuka sawa tayi aka kirawo Ladidi ,Ladidi tana kuka 'aka shigo da ita ,lokacin ta canza kaya 'atamfa ce Holland me tsadar gaske ,riga da skirt ne mai adon stone a jiki ,tunda 'aka fito da ita take kuka mai cin rai y'an uwan momy ne suka rik'ota suka wuce da ita part d'in momy, lulu6eta naga 'anyi daganan kuma 'aka d'auko turaruka masu k'amshi aka fara fesa mata sosai take jin zafin rabuwar ta da iyayen ta gashi kuma yanzu wanda sha'awar ta yakeyi shi za'a 'aura mata kuma tsanan ta kukan tayi saboda zuciyar ta d'aci take yimata , jiyo muryar mutane suna rangad'a gud'a yasata dawowa daga duniyar tunanin da ta tafi, momy ce ta janyo ta jikin ta kana tace" Khadija duk abinda zance na fad'a miki tun jiya , sai dai zan kuma yimiki tuni da ki rik'e mijinki da 'amana kuma kiyi biyayya 'a gareshi kibi duk wani abu da yakeso inhar bai sa6awa shari'a ba ,wani kukan 'ne yakuma ku6uce mata saboda wanan nasihar ba k'aramin shigar ta sukayi ba ."


Bayan momy ta share hawayen da suka zubo mata tace"wa wasu mata da 'alamu k'annen ta ne tace"musu su raka Khadija d'akin dadyn su , k'afar momy Ladidi ta rik'e tana kuka mai tsuma zuciya ,kowa na gurin saida ya zubda hawaye saboda tausayi, bayan sun kaita d'akin dady ne yafara yimata nasiha bayan wa inda suka rakota sun kauce yafara sanya mata 'albarka daganan yafara da ina 'alfahari dake Khadija kibi mijinki karkiyi k'ok'arin sa6a mai kuma yakamata kisani karki kasance mai d'aga murya 'akan ta mijinki kibi umarnin mijinki , karki sa6a masa indai umarnin bai sa6awa addinin musulunci ba ,kanta 'a k'asa tace Dady nagode ,wani small box Dady 'ya d'auko wasu keys ne na mota ,mik'awa Khadija yayi duk da 6acin ran datake ciki saida ta dara saboda tsabar farinciki har k'yal k'yalewa da dariya take,hak'ik'a dady 'yaji matuk'ar farinciki tare dakuma sanya mata 'albarka,kira yayi akan azo a tafi da Khadija ba'adau wani long time ba saiga wasu mata nan suka d'agota kiran sunan dady takeyi amma inna shima baiyi magana ba ,hawayen da suka zubo mai yashere batare da kowa yagani ba ."

Humaid ne zaune a d'akin abokanan shi yana hutawa ,wani abokin shine yace "abokina wallahi ka huta saboda wanan babyn taka tagama had'a maka komai ,Humaid ne ya gyara zama yana kallon abokin 'nashi yace" banason irin wanan wasan, daga nan ya gyara zama ,jiyo k'arar wayar shi ne yasa shi duba gurin da ya 'ajiye wayar ,ganin 'number babu suna yasa shi jinkirta d'aukar wayar ,saida 'akayi 6 miss call sanan ya d'auka ,jin muryar wani yasa shi gyara zama k'irjinshi na dukan uku_ uku,ji nayi yace"what!!!. "


Wata razana nniyar k'ara yasa yana cewa no_no wlh ba ita bace kana ya mik'e yana layi ,abokin 'nashi yace "Humaid akwai problem ne ?" idan Humaid da ya sauya launi ya juyo yace"babu komai zan dawo anjima,abokin baiji dad'in jin hakan ba 'amma sanin halin Humaid yasa shi yin shiru da bakinshi.

Bayan Humaid ya isa gida ne ya hango Khadija ita da k'anwar momy suna magana ,wata muguwar tsanar ta yakeji acikin ranshi, wucewa part d'inshi yayi ba tare da k'ara kallon gurin da 'amaryar tashi take ba?"direct parlorn dady 'ya nufa kafin ya shiga saida ya tsaya sosai yana tunanin kalmar dazai fad'awa dady ,ganin bashiga mafita yasa shi, shigrwa kai tsaye ,bayan yayi sallama ne yasami dady zaune da laptop a hannun shi ,dady ne ya cire farin glass d'in da yake manne a idonshi kana ya juya ya kalli d'an 'nashi ,kan Humaid na k'asa saboda bayason su had'a ido da dady ,bayan sun gaisa ne dady 'yake cemai lafiya ko naga kayi shiru ?"dady ne ya d'ago kai ganin mood d'in Humaid ya sauya sosai yasashi cewa to me kuma ya faru ?idanun Humaid sunk'ara kad'awa ya d'ago kai yana duban dady 'yace"dady dan Allah dan darajar manzon Allah ka fahimceni ,dady dai baisan inda Humaid ya dosa ba saboda babu abinda ya fahimta ,Humaid ne yace"dady nafasa auran Khadija!!!,sauran kalmar ta mak'ale a bakin shi ganin wani mugun kallo da ,dady ke jifanshi dashi."



Dady da yakejin ranshi yana yimai d'aci ya dubi Humaid 'da jikin shi ke rawa yace"wallahi wallahi ko bayan raina ban yarda 'ace ka fasa 'auran Khadija ba ,da ubanwa yasa kace" kana sonta, kodan kanaso ka wulak'anta mu ?"girgiza kai Humaid yayi saboda yana ganin dady bazai fahimceshi ba ,dady ne yace"tashi ka ficemin marar kunya da bakasan mutunci ba ni zakazo kacewa wai kafasa 'auran Khadija to dama gobe juma'a 'aure babu fashi wallahi sai anyi ,Humaid ne yayi saurin ficewa daga part d'in dady saboda kar momy tasan halin da 'ake ciki ,komawa bedroom d'inshi yayi ya hau makeken gadonshi juyi yakeyi saboda zuciyar shi ji yakeyi kamar zata fashe , yafara tuno kalar tanadin da yace"zai yiwa Khadija 'amma yanzu gashi komai ya rushe ,yafara kuka kamar k'aramin yaro ,sai kuma ya tuno cewa gobe nefa d'aurin aure dafe kanshi da yake faman ciwo yayi yana salati ,akwatin shi da yacika shi da d'inkuna ya kalla saboda kayak shiki zasukai kala talatin amma gashi komai ya rruguje."


Khadija ce zaune kusa da umma tana k'ara tunatar da ita 'akan zaman lafiya dakuma ibada da hak'uri ,wata gora babba momy ta d'auko tabawa Khadija tace"kinga wanan daga saudiya 'aka kawo min kuma dan ke nasa'aka taho dashi saboda ba ,a ko ina 'ake samunshi ba , ita dai Ladidi ta kasa gane me momy take nufi ,momy ce ta dubi Ladidi kana tace"zuma ce ta mata kullum zakidinga sha 'amma fa yanada k'arfi,2 small spoon zaki dinga sha ,Ladidi ce take mamakin momy da take zayyane mata maganin mata."




💍 *WEEDING*💍

Yau juma'a yaune dubban jama'a suka shaida daura auran *KHADIJA MUSA DA HUMAID ADAM*
Akan sadaki dubu d'ari lakadan ba 'ajalan ba 'abokanan su Humaid basu ji dad'in ganin yanayin angon ba kasan cewar baya cikin 'nutsuwar shi saboda 'a inda yake basu labarin shagalin da zasuyi a gun bikin dakuma garar daze kwasa 'amma sunga yanzu ko sunan amaryar baya son ji ."


Kowa ka gan yana cikin farinciki a yau saboda biki yayi biki amma banda mutum biyu wato Khadija da Humaid , wata k'awar Khadija ce tace yakamata mu tambayi Humaid saboda musan a inda za 'ayi dinner Khadija ce tace"hmm kuna iya zuwa bazan hanaku ba ,babbar k'awar ce mai suna ramsy ta d'aga waya tana lalubar number Humaid 'dan kab k'awayen sunfi shiri sosai ,jin takira wayar tanata ringing ba'a d'aga ba yasata dad'a gwa dawa cikin k'araji yace" wai waye ne please banason takura ,Ramsy ce tace"Humaid baka ganin 'number tane nice fa ,Humaid ne yace"to inna gani sai me yanzu mezan miki hak'ik'a Ramsy taji zafin hakan amma sai ta daure tace"dama maganar dinner ne shine nace kafin a tafi ne za'ayi kokuma sai ankai amarya, jin ya daka mata tsawa yasata zabura tace"daga tambaya saika nemi firgita ni ,to kasani ko a gidan mu babu mai yimin tsawa ka kiyaye ,ko kulata baiyi ba yaja waya ya kashe ,Khadija ko kuka takeyi dama tasan za'ayi hakan ,tafara magana da k'arfi tana cewa"daman wlhi na kawo wanan ranan saboda yaga 'an d'aura 'aure nazama mallakin shi shine ya keson wulak'anta ni."✍️✍️✍️.





*MOM ISLAM CE*✍️✍️✍️..
*LADIDIN K'AUYE*


Funny & love story.

*Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa*



*NA*

*MOM ISLAM*
*ZAINAB HABIB*


*MARUBUCIYAR:*

*ZAINABU ABU*



*AND NOW*

*LADIDIN K'AUYE*



*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


*Episode:* 21_22



____Kashe wayar yayi gaba d'aya dan bayason jin duk wani abu daya shafi Khadija saboda 'a halin yanzu wutar k'iyayyar ta ce take ruruwa 'acikin zuciyar shi, da misalin k'arfe tara na dare saiga motocin angwaye sun zo d'aukar amarya ,bayan angama yimata makeup dasu nasiha 'aka ce tafito su tafi , tunda taji haka ta k'ank'ame momy sosai tanajin zafin tafiyar da za'ayi da ita saboda tayi nadamar auran Humaid amma babu inda zatayi dole ta yarda kodan soyayyar da su momy suka nuna mata gashi dady harda bata mukullin mota,tana cikin tunani ne taji muryar momy na cewa , ina Khadija tayi share hawayen ta tayi kana ta gyara yafa gyalen ta ,jin alamun shigowar umma yasata dai_daita nutsuwar ta , bayan momy ta shigo ta ganta 'a zaune ta takure gefe d'aya , cikin azama tace"taso taso muje kiyi wanka kinga masu mota sun iso."


Jiki babu k'wari Khadija ta tashi ta rufawa momy baya , bayan sun wuce toilet d'in momy ne momy tace "zonan suna shiga momy ta had'a mata wasu turaruka dakuma magun guna ta shige wanka , bayan ta fito ne momy tasa 'ayi mata makeup aka fito mata da kayan dazata sa , fans kuzo kuga Khadija kamar tauraruwa kowa sai mararin ganinta yakeyi, bayan sungama ne aka fito da ita tana sanye da swiss lace mai ruwan ganye ,fito da ita sukayi aka fara rangad'a gud'a Khadija kuka takeyi sosai kamar 'ranta zai fita, momy juyawa tayi saboda bazata iya ganin Khadija 'a yanayin kukan da takeyi ba ,wata kakar su Humaid ce tace" zo yarinya kiyi bismillah ki shiga ,haka Khadija tashige mota tana kuka mai tsuma zuciyar mai saurare , tunda suka tafi momy ta koma bedroom d'inta tana ta sharar hawaye , ganin ai yau ranar farinciki ce a gurinta yasata murmushi da yau Humaid ya auri wacce take so adu'a tayi musu kana ta haura sama gurin dady ,samunshi tayi kwance yana duba wani file na business d'inshi yana ganinta yafara sakin murmushi k'arasawa tayi ta fad'a saman k'irjin shi tana shafa mai kai ,cikin jin d'ad'i dady yace ,lovely na menene ?"🤭momy ce tafashe da kuka tana cewa shikenan yanzu zan dena ganin Khadija 'a kusa dani."

Gyara musu kwanciya dady 'yayi kana yafara share mata hawayen fuskar ta daganan'na rufo musu k'ofa ."



*GIDAN AMARYA KHADIJA*👰.


Zaune take tana ta gurshek'en kuka babbar k'awar ta Ramsy ce tazo kusa da ita tana cewa habba Khady maiyasa saikace ba 'auran soyayya ba ,share hawayen ta tayi batace komai ba ,dan a halin yanzu batajin zata iya wata magana tunda babu mai fahimtar ta, wanka ta sake yi ,kana suka k'ara yi mata make-up wanda yafi na d'azu aka sauya mata kaya zuwa wani material mai laushi suka feshe ta da turaruka masu k'amshi wow koni danaga Khady saida na yarda 'alk'alami na , shirin tafiya suka farayi ai kuwa Khadija na ganin hakan tafara gurshek'en kuka mai tsuma zuciya mai saurare ,zuciyar ta bata gama tsinkewa ba sai lokacin da taga sun yafa mayafi suna shirin fita ,durk'usawa tayi tana cewa kuyi hak'uri ku tafi dani ,nikuwa nace aure fa kikayi hhh yarinya ki gane aure yafi gaban wasa ."



Haka tanaji tana gani suka wuce suka barta ,komawa tayi ta haye makeken gadon ta daya k'awata d'akin, kwanciya tayi can kuma tafara jin tsoro na shigar ta ,misalin 10:pm taji alamun shigowar mota, wani tsoron takuma ji tana 'adu'a 'a cikin zuciyar ta mik'ewa tayi ta lek'a ta window hango shi tayi shi kad'ai yana shirin fitowa daga mota, sanye yake da shadda mai kalar brown wace ta k'ara fito da ainihin kyan shi ,bayan ya rufe motar ne ya d'auko wata leda ya yi hanyar shigowa parlon ,Khadija ce ta koma ta gyara rufe fuskarta da mayafin jikin ta 'takoma tsakiyar gado ta zauna ,da sallama 'a bakinshi ya shigo zama yayi a d'aya daga cikin kujerar d'akin kasancewar bedroom d'in 'nata kujeru biyu ne ammafa sun k'awata d'akin ,bayan ya zauna ne yace"inkinyi ra'ayi zaki iya bud'e fuskarki ,wanan maganar ba k'aramin dukan Khadija tayi ba ,amma batace komai ba ,kuma d'ago kai yayi yakuma cewa to mekuma zaki 6oyemin bayan angama tallarsu a titi ,a firgice ta mik'e tana nuna Humaid 'da yatsa abinda bata ta6a yiba kenan ko musu dasu batayi amma yaukan ya kaita mak'ura ".



Cewa tayi duk abinda ka fad'a 'a kaina nayi shiru ban kulaka ba yanzu kuma ka sake jifana da wanan mumunanr kalmar ?" to wallahi bazan lamunta ba ,kafin ta k'arasa ya wanketa da mari jiki na rawa tace"kozaka kasheni wallahi sai Allah ya sakamin ,wurga mata ledar yayi ya fice a fusace , kwanciya tayi tafara gurshek'en kuka gashi babu mai rarrashin ta.


Misalin k'arfe 11:pm ta mik'e ta daddafa bango saboda mugun ciwon da kanta yakeyi bata gani sosai,toilet 'ta shiga ta wanko bakinta tazo ta zauna tana son cin abinci gashi matsanancin ciwon kai na damunta ,ba'a fushi da 'abinci ,janyo ledar daya wurgo mata tayi tana bud'ewa taga mutuniyar tace wato kaza gasashiya da yogurt aiko tafara yagowa tanaci tana shan yogurt d'in ,duk girman kazar saida tayi rabi ,alokacin'ne taji ciwon kan ya ragu ba kamar da ba ,mik'ewa tayi ta cire kayan jikinta ta sauya izuwa sleeping dress sosai kayan sukayi mata kyau ,bayan tayi adu'ar kwanciya bacci ,tana kwanciya bacci mai nauyi ya tasheta tare da mugayen mafarkai masu firgitar wa, washe gari tunda tayi sallahar asbha ta koma bacci ba ita ta farka ba sai misalin karfe 9:am lokacin ma jin alamun 'nocking d'in k'ofa ne ya tayar da ita".


Zumbulelen hijab d'inta tasa kana ta nufi k'ofa ,tana fita parlor takuma ji ana nocking cikin azama ta isa k'ofar ta bud'e ,ganin yar aikin momy ce yasa Khadija washe baki tace"yaushe kika dawo ne Ummi?"Ummi cikin jin dad'i da tarbar da Khadija tayi mata tace"yau kwanana d'aya ,Khadija ce tace"to kishiga mana kamar bak'uwa ,shiga Ummi tayi bayan ta mik'awa Khadija abincin da momy tabayar akawo musu tuwon shinkafa ne miyar shuwaka wacce taji nama kamar zasuyi magana kai dakaga tuwon kasan zaiyi dad'i ,jere kulolin tayi a dining ta dawo ta zauna ,kusada Ummi ,tambayar ta tashiga yi 'inasu momy da yaya Jalal 'lafiya Lou tace"daganan Khadija ta kunna musu kallo ,Khadija ce ta mik'e tace Ummi ki jirani yanzu zanyi wanka in fito ,Ummi data tuna da kashedin da Momy tayi mata yasata cewa to nimafa tafiya zanyi dan momy na jirana ,badan Khadija taso tafiyar Ummi ba 'amma tayi mata godiya sukayi sallama .



Humaid ne yafito parlor lokacin 11:am na safe sanye yake da wani lallausan yadi mai ruwan coffee kasancewar shi farine ba k'aramin kyau yayi ba ,shafa bak'ar sumar datayi luf a kanshi yayi can kuma ya ciro waya kamar mai jiran wani abu ,Khadija ce tafito tana sanye da doguwar 'riga pink mai adon ston black tayi rolling kanta da mayafin rigar ,tana fitowa Humaid yakai dubanshi gareta cikin zuciyar shi kuwa ji yakeyi kamar yaje yai hugging d'inta tunda matsayin da 'a gurinshi yayi kawai sai ya had'e rai ,ya dubeta tana neman gurin zama yace"keee!!saida gabata ya fad'i tashi ki gyaramin d'akina baki iya gaisuwa bane ?"na iya tace"a tak'aice ,Humaid ne yace "to kullum zaki dinga zuwa gaisheni ko sau goma zan fita kuma in dawo ,to kawai tace" ganin yayi hanyar dining ne yasata k'arawa da gudu ta kwashe kulolin tayi d'akinta dasu ,key tasa ta rufe k'ofar.....✍️✍️✍️.




*~MOM ISLAM CE~*
*LADIDIN K'AUYE*


Funny & love story.

*Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa*



*NA*

*MOM ISLAM*
*ZAINAB HABIB*


*MARUBUCIYAR:*

*ZAINABU ABU*



*AND NOW*

*LADIDIN K'AUYE*



*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


*Episode:* 23_24



_____Saida ta tsince naman kaff tukun ta ci tuwon bayan tagama cine ta fito da ragowar parlor, bata lura da mutum a parlorn ba direct ta wuce dining ,saida ta 'ajiye kular ta hango shi yana kan doguwar kujera maicin mutun uku ,zata ruga da gudu ya daka mata tsawa yace"kee!!zonan zataci gaba da tafiya ya mik'e da gudu ya janyota ya wurgata gefe kana yace "wuce ki dafamin dambu,zaro ido tayi kana tace"me kuma mai suna haka?".


" Cewa yayi ubanwa zaki rainawa hankali ¿"cikin jin tsoro da fargaba tace"ni ba rainama hankali zanyi ba ,gani 'nayi ban iya ba shiyasa nake tambayar ka, tsawa yakuma daka mata saida ta tsorata yace"kin zo bariki kin manta da shan garin kwaki ko ?"to kitashi ki goge gidannan kuma kar in dawo insami akasin hakan, haka ta shiga bedroom d'inshi tafara wanke toilet sanan ta dawo gyara bed d'inshi tayo kan TV da sauran kayan kallon ta gogesu kana ta dawo tafara shara tana gamawa tayi mopping, bayan ta gama ne kawai tad'an kishingid'e a gefen bed' d'inshi saboda wata gajiya da tayimata sallama ,bacci ne mai nauyi ya kwasheta 🤭nikuwa nace"anci an k'oshi zaki gane, jin shiru har tayi 1 hour bata fito ba yasashi kashe kallon daya kunna kana ya wuce bedroom, samunta yayi kwance tayi d'ai_ d'ai ,zaro ido yayi kana yafara tunanin irin muguntar da zaiyi mata."



D'auko alurar malaria yayi wacce yake ajiyewa 'a gida saboda koda wata matsalar zata taso, bayan yagama zuba magungunan dayasan Khadija zata bada labari ,komawa yayi kusa da ita yana k'are mata kallo can kuma yaji muguwar tsanarta tana kuma baiyyana cikin zuciyar shi.



Tunda 'akayi bikin Humaid 'da Khadija babu wanda yayi k'ok'arin kiran su momy gashi yau har kwana biyu da wuni saidai momy na 'aiko da 'abinci kullum ,amma hakan bai sata kwanciyar hankali ba , kiran Jalal tayi a waya yana d'auka tace" dan Allah kazo inason ganinka .

"Cewa yayi momy lafiya dai ko ?"lafiya tace masa daganan ta kashe wayar ba'adau lokaci mai tsayi ba saiga Horn d'in motar Jalal nan kasan cewar baya gida ,yana shigowa tun daga parlor yafara k'walawa momy kira yana cewa momy gani na iso, sako tayi daga matatrakar dake tsakiyar d'akin tace"gidan Humaid nakeson kaje inasan kadubo su ko lafiya ,itadai Khadija nasan batada waya , dariya ce taso ku6ucewa Jalal ganin damuwa k'arara 'a fuskar momy sun kuyar da kansa k'asa yayi kana yace" momy lafiya suke saboda da babu lafiya 'ai dakinji , momy ce ta d'ake tana masifa tana cewa yanzu ka nuna ban isa dakaiba kenan ko?"to walhai tun wuri kaje ka dubomin su kokuwa ranka ya 6aci !!Dady dake saukowa daga bene yace"karka kuskura kaje gidan su , nagaya maka d'ago kai momy tayi tana kallon fuskar dady _dady dake magana cikin bada umarni yace "ka koma gurin aikin ka, to Jalal yace" batare da yakalli k'wayar idon momy ba."



"Momy ce takalli dady can kuma tayi k'asa da murya tace"haba habiby maiyasa kayi hakan?" tana dad'a matsowa kusa dashi , dady ne ya kawar da kai alamun maganar da momy tayi d'azu nazuwan Jalal gidansu Humaid ya 6atamai rai, k'arasawa kusa dashi momy tayi kana tace"haba mana mijina banason fushinka ta kuma marai raice fuska kamar zatayi kuka tace" please afuwan habiby, hugging d'inta dady 'yai tare da janyota jikinshi a lokacin da yake k'ok'arin zama akan d'aya daga cikin kyawawan kujerun,dasuka haska parlorn ,dady ne yake rad'awa momy a kunne yana cemata walhai Aisha saboda salonki dakuma siye zuciyata da kyawawan kalamanki yasa nak'i k'aro aure amma badan hakaba da yanzu matana hud'u .



Tunda ya gama had'a komai ya bud'e mata gefen hanunta jitayi abu na shigarta kamar'ruwa kasancewar ko a hospital ne kowa nason alurar shi saboda batada zafi,haka yayi mata 'alura tana bacci ,jin alamun kamar ana tsikarin ta yasata saurin motsawa, Humaid na ganin haka ya koma parlor saboda karta gane ,tun tanajin abin kad'an har tazo tanajin k'ai k'ayi sosai, inta Sosa k'afa saitaji a kunne inta sosa kunne saitaji a baya ,haka tadinga susa kamar mahaukaciya ganin lamarin yafi k'arfinta yasa tafara ihu tana tsalle tana cewa wayo Yadikko,
da gudu ta fice a d'akin tayi d'akinta tana tsalle ,rasa 'abinda yake yimata d'ad'i tayi ganin batada mafita yasata d'auko farar hoda ta cire kayan jikinta duka ta shafe ko ina na jikinta ,ganin abun babu sa'a yasata cewa yaya Humaid!!,
"Kazo ka temakeni walahi narasa inda na kwaso k'ai k'ayi ,shiko Humaid ganin tana magana tana soshe _soshe yasashi sakin killer small yace" to yanzu mekikeso inyi miki nikuma ?"kije wanda yafara ganin komai ,ya baki magani ,tana susa tace"bangane ba sokakeyi kacemin 'ni mazinaciya ce?!!! menayi ma dahar zaka k'ullamin wanan mummunan sharin oho yace"daganan yabarta tana soshe ssoshe.



Tana kuka tana susa wani gurin har yayi rud'u rud'u tsabar susa tausayin da tabashi ne yasashi shigowa ya mik'o mata magani k'waya biyu yace"ta shanye duka ,babu musu ta k'ar6a tanasha ba'a d'au lokaci masu tsayi ba ,bacci ya kwasheta , said a ya koma d'akinshi yadinga dariya yana k'arawa saboda ya 'ajiye CCTV a bedroom d'inshi kuma bakowane zaisan akwai CCTV a d'akin ba ,kusan k'arfe hud'u
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment