Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aka basu suka wuce gida ,Khadija na ganin yan zaman makoki tafara tambayar waye ya rasu ,momy ce ta tuno da sharud'an da doctor ya gaya mata akan ta kiyayen 6acin ranta kokuma shiga damuwa ko gani ko jin fargaba ,momy ce tace ”suna hutawa ne kinsan wanan watan dolle sai anyi meeting da ma'ai kata ta gamsu da baya nin momy shiyasa ma bata k'ara d'aga hankalinta ba....



Kai nimafa mom Islam abin ya d'auremin kai 😢meya faru a gidansu Khadija ??waye ya rasu ??? tabb todai kubiyoni danjin inda muka dosa👏.



Kwance take tana wani matsanancin kuka rabonta da abincin kirki tun da wanan abin ya faru ,tarasa ina zatasa kanta gashi Allah ya jarabeta da abubuwa duka biyu ,alwalah ta d'auro tazo tafara nafilfili tana gayawa Allah damuwarta ,washe gari yaune akayi sadakar uku mutane sun ragu sosai ba kamar daba ."

Kale ² takeyi a d'akin tarasa meyafaru bazata iya tunowa ba ihu tafarayi dan razana take koda wane lokaci ,momy da tatashi akan darduma tayo d'akin da gudu ta sami Khadija nata juya kai tana ihu ,wasu zafafan hawayene suka zubowa momy tayi waje da sauri ,driver ta k'walawa kira cikin azama yazo ya drk'usa a gaban momy _momy ce tace ”maza ka fito da mota mu koma hospital ,komawa tayi ta ruk'o Khadija tafito da ita hijab d'inta ta Sanya mata daganan sukayi mota ,dak'ayar momy ta sata a mota suka wuce hospital, sunyi sa'ar ganin doctor ,inda yake sanar musu cewar su dage da adu'a kuma akwai abinda take tunawa yake tsorata ta magunguna ya kuma basu yace ”ku kulla sosai da ganin tasha magani."


Haka driver ya dawo dasu gida ,matane keta shigowa gidan momy suna yimata ya karin hakuri ,wanan su shigo wanan su fita dayake momyn ta mutane ce .



*KAUYE*
Sahura ce ta shigo gidan inna da gudu tana shewa ,had'e fuska inna tayi tace ”fitarmin a gida nace kifice ko ,dariya Sahura tasa tace ” inna ya alelen ranan waya biya kud'in ¿"ubanki ne ya biya kinji ,sahura ce ta zaro ido tace ” ubana fa sirikinki ne ,inna ce ta d'auko sanda tana shirin buga mata wani yaro yai sallama yace ” Aslamu alaikum zakusi kai da kafar kaza ?" tsalle Sahura ta doka tace ”kai yaro kawo nan shigowa yaron yayi ya nemi guri ya zauna ,Sahura ce ta dubi inna tace ” hmm sai na tuna lokacin da mukaje gidansu Ladidi kullum sai naci kaza ,amma yauma Allah yasa inada ragowar kud'in da Humaidu ya bani d'ari biyu na siya ,dajin haka inna ta washe hak'ora tana dariya tace ”yoo ai siyama zakiyi koda na d'ari ne Sahura ce ta tambayi yaron nawa nawa ashirin ashirin yaron yace ”kasiyar uku hamsin ¿"eh kawo .


Kai ta d'iba guda biyu k'afa kuma d'aya duban inna tayi data zuba tagumi tace ”toke bazaki d'auka bane ?inna ce tace ”to masu abin basuce in d'auka ba ni na isa ,dariya Sahura tasa tace ”laaa ina ki d'auki na hamsin ,inna na sid'ar hannu ta d'auka harda zubo romo ,yaron yana zaune har suka gama ci Sahura tace ”ga hamsin d'inka kajira wanan tsohuwar ta baka kud'inta inna na sud'e hannu tace ”kan uban ke kin biya naki hakafa kikayimin ranar sai malam ne ya biya yana fad'a Sahura dake taunar k'ashi tace ” maganin mai kwad'ayi komai mutum saiyyaci ,inna ce ta kunto zaninta gudar d'ari biyar ce a jiki mik'a wa mai kai da k'afa tayi tace ”k'aromin na hamsin ,dan ubanta ni zata rainawa hankali*LADIDIN KAUYE*



funny & love story



51_52
Yaro dai na ganin ikon Allah ya je ya samo canji ya kawowa Inna ,Sahura ce tace ”au kewai inna kina gadarar zaki bani haushi ne aikin 6urr saidai inbaki haushi ta ja gyalena ta d'aura a kwankwaso ta fizge kwanon da inna tasa a dad'o mata naman ta ruga da gudu ,kuka inna tasa tana tsinewa Sahura tana cewa ,shegiya ga kashe d'ari danayi tashi d'aya gashi iya romo na tsaya sud'a ta wafce kwanon ,shidai mai talla gaba yai yabar inna tanata surutunta."


_JOS_

da sallama ya shigo yana cewa momy yau akayi sadakar bkwai to Allah ya gafarta masa kuka momy takeyi sbda inta tuno abinda yafaru amma aikin gama ya gama rayuwar batajin dad'in yinta sbda Khadija har yanzu sai sauk'in Allah yanzu ciwon 'nata ya koma kamar na mai aljanu in ciwon ya tashi to guduwa take burin yi dady abubuwa sunyi mai ywwa sosai duka dai familyn gidan basuda wal wala ,kwance take tana bacci sai kuka takeyi kuma da k'arfi ,momy ce ta shigo d'akin ta sameta tana bacci kuma tana kuka ,adu'oi tashiga yimata tana tofa mata ,yunk'urowa tayi tana gurnani zata hankad'e momy ,cin sallamar Jalal yasa momy k'wala masa kira ,da sauri ya shigo yana cewa momy lafiya kuwa ¿inafa lafiya Jalal ?narasa yaza’ayi da ciwon Khadija kullum abin baya lafawa kullum cikin fad'a muke gashi banda kunu batacin komai y'an aikin gidan suntafi garinsu ,sai kuma tasa wani kuka mai ban tausayi ,hak'ik'a momy mace ce wace batada zalunci batada mugunta kuma bata fifita wani akan wani ,Jalal shima abin yafara damunshi kukan da momy keyi ya kuma tayarmai da hankali ,sukan sunga jarabawa Allah yasa su cinyeta duka."

Washe gari antashi da wani sanyi mai shiga mai shiga jiki tunda gari ya waye khadija keta ihu tana k'ok'arin fitowa wani girgiza d'akin yakeyi ga wasu k'ara dake baiyyana a cikin d'akin ihu takeyi iya k'arfinta ,dady daya shigo yanzu yai d'akin da sauri ,ganin inda jikin khadija keta 6ari yana makyar kyata yasashi cire hular kanshi adu'oi yaketa karanto mata amma sauki sai lokacin da Allah ya nufa ,gefenta wasu abubuwa take gani masu ban tsoro sai nuni take yiwa dady ina shikam bai gani ba ,ihu take kuma yi tana ruk'o hannunshi amma dady babu abinda yagani yarasa wane ciwo ne ke damun khadija , adu oin da yai mata yasamu jikin ya lafa dan har bacci ya d'auketa."


D'akin momy ya nufa zaune ya sameta kan sallahya tana azkar shigowar sa ne yasata shafa adu'a tace ” barka da dawowa mijin kirki ,dady ne ya fitar da wata zazzafar iska daga bakinshi ya d'aga hannu sama yana cewa Allah mun gode da jarabawar da kayi mana Allah ka kawo mana mafita ba yawan arzik'inmu ba bakuma yawan ibadunmu ba Allah ka dubemu ,suka shafa tare da cewa amen.


Wata girgiza sukaji mai firgitarwa momy zata tashi dan taga meke faruwa dady ya tsayar da ita yana cewa kibari in lek'a ,momy na shirin kuka tace ”gaskiya sai dai muje tare ,hannun dady ta rik'e tana kuka suka fita , duk wanan hayaniyar da girgizar duk a part d'in Khadija yake faruwa hatta k'ofar ma girgiza takeyi kuma a bud'e take ,dady na shirin lek'awa momy ta rik'oshi tace muje mu nemo malamai dan Allah ,hankalin dady a tashe damu warshi wane hali baiwar Allah take ciki marainiya ,kutsa kai yayi momy na tsaye ya wuce ,kwance ya sameta d'akinta duk ruwa mai had'e da jan abu mai kamada jini sai wasu surutai takeyi ,kafin dady yace ”bismillah kawai aka d'aukeshi aka gwara da jikin bango ,ihu momy takeyi iya k'arfinta gadai khadija a kwance shikuma dady ,kowaye yayi mai haka oho , mai gadi ne da driver sukayo cikin gidan a tsorace ,momy babu magana sabda kuka yaci k'arfinta saidai nuni da hannu ,hango dady sukayi a mak'ale a jikin bango shi bai sauka ba shikuma bai yi sama ba, wani hayaki ne ke fitowa amma Khadija na kwance tana bacci ,driver ne yace ”anya babu shed'anu a lamarin kafin ya rufe baki yaji an wankamai mari ,ganin basuga kowaba yasa mai gadin da driver da momy suka arce da gudu , d'akinta momy ta koma ta d'auko wayarta ta kirawo Jalal ring d'aya ya d'aga yana sallam momy ko amsawa batayi tace ”Jalal.ka kirawo mai ruqyya dan Allah dadynku tana kuka to yace kashe wayar momy tayi tana adu ar datazo daga bakinta , bayan 30minutes sai gashinan shida wani babban malami sun shigo ."



Gai sawa sukayi da momy daganan tayimai bayanin ciwon Khadija dakuma halin da dady yake ciki ,ruwa ya buk'ata domin alwalah bayan ya idar da alwalar ne yace ”a nunamai d'akin ,momy ce ta shige gaba itada Jalal shikuma malamin na baya da Qur'ani a hannunshi ,da hannu momy tayimasa nuni da d'akin ,lek'awa yayi ya hango dady jingine a jikin bango shi baya k'asa auxubillahi yace ” a lokacin da yake karanta suratul bak'ara ,jikin dady ne ke jijiga yana wani gurnani tsananta adu'a malamin yayi , Allah cikin ikonsa saiga dady ya fad'o yana tangad'i ,malamin ne yace ”asamu yayi wanka kuma ya kwanta ,kan Khadija aka koma daketa bacci ko motsi batayi adu'oli iri _iri malamin yayi amma har yanzu shiru ,d'akin sai fitarda wani hayak'i takeyi mai ban tsoro."



Fitowa malamin yayi yana yarfe gumi yace ”zanje in dawo ,to su momy sukace daganan suka rufo k'ofar khadija ,da fitar malamin gidan duka ya kaure da kururuwa mai firgitarwa daga momy har Jalal sun kasa koda motsi ne ,dama dady bai tashiba tunda yai wanka ,jin girgizar tayi yawa yasa momy shiga bathroom d'inta d'auko buta tana shirin zuba ruwan alwal wasu abubuwa tagani na ban tsoro hakan yasata ficewa tana salati Jalal ne yace ”momy to yanxu ya za'ayi ¿ jin momy tayi shiru yasashi kallon inda take kallo ,wata halitta ce mai abin tsoro da girman ta ya zarce tsawon d'akin a sunkuye take tafiya ,idanuwan momy suk k'afe bataji bata gani ,kafin wanan abin ya iso Jalal cikin tashin hankali ya cici6i momy yai da ita d'aki suna gudu halittar na binsu Allah yabashi ikon rufe k'ofar ba tareda wanan halittar ta shiga ba."




Ruwa yadinga yayafawa momy amma shiru ,a karo na biyu ne ya bud'e ma dai _dai cin fridge d'inta ya ciro ruwan sanyi yana yayyafa mata cikin sa'a ta mik'e tana salati, sallamar malam sukaji babu wanda yai k'ok'arin tashi malamin yace ”yanaga babu kowa Jalal ne cikin d'aga murya yace ” kaje d'akin mara lafiyar ,gamunan momy na ce babu lafiya ,shigewa d'akin malamin yayi daganan yafara adu'oi yana tofa mata yanayi yana tofa mata wata atishawa tayi mai k'arfi wacce tayi dai dai da tashin dady daga bacci ,momy take kira iya k'arfinta ,momy najin muryar Khadija ta fice da sauri tana cewa yaushe rabon da daughter ta kirani, fara'a ce ta baiyyana a fuskarta tashiga d'akin zaune ta sameta ,da shigar momy Khadija tace ” momy maiya faru ne babu komai momy tace ”daganan malamin yace ”hajiya muje parlor inyi miki bayani OK tace suka wuce Khadija tashi tayi ta shiga wanka ,ganin duniyar takeyi kamar sabuwa.*LADIDIN KAUYE*




Page 53 & 54

Malamin ne yace ”dole sai kun kiyaye da shan maganinta to momy tace ”yabasu adu'oi da zasu dingayi a gidan , momy ce tacewa "Khadija ta shirya suje airport itada Khalel , cikin sauri ta nufi d'akinta dan yanzu burinta bai wuce taga mijinta ba , Jalal ne yashigo yana k'walawa khadija kira , fitowa tayi cikin wata shiga mai d'aukar hankali , less ne pink a jikinta sai gyalenta fari takalmi fari jaka pink and wait, wow kuzo kuga Khady , suka shige mota zuwa airport , mutane ne keta saukowa , hango wani had'ad'en saurayi tayi mai kamada Humaid ,tunani tafara kodai humaid ne ?" sanye yake da bak'ar rigar sanyi my adon flawoyi gashi yayi haske sai dai ya rame sosai , da zuwanshi yayi hugging gimbiyarshi , shidai Jalal na gefe yana zaro ido , sunkuceta yayi ya rungumeta yana yimata rad'a a kunne wanda nima banji me suke cewa ba ,Jalal ne yace ”wato ni an manta dani ko ?"dariya Humaid yayi ya doki k'afad'arshi yace ”am sorry kuna raina dukkan ku , mota suka shige ,Humaid da Khadija a Back side ,Jalal yana gaba yana driving,da isarsu gida sukaci karo da anshirya walima gagaruma gurin ya kawatu da flawoyi masu wuta suka shige ciki ."


funny & love story


55_56


Dady da momy suka zauna a kujerun da aka zagaye gurin suna adu'a Jalal ne yace ”bari a yanka cake sai 'intafi gida ,momy ko dariya takeyi farinciki fall zuciyarta ,durk'usawa Humaid yayi ya gaida dady yaje ya gaida momy ya dawo kusada Khadija ya zauna sunci sunsha dan abinci ma daga hotel aka kawo ,misalin k'arfe biyar dady yacewa Humaid ya d'auki matarshi ya wuce ,wanan karon dai Khadija batayi kuka ba, sai da sukayi sallahr isha'i sanan suka d'unguma zuwa gidansu ,hira sukeyi jefi jefi ,da isar su gidan sabon mai gadin da dady 'ya sa musu ya wangale gate d'in yana yimusu sannu da zuwa ,da shigarsu yai parking a ya fito yana mai yiwa Allah godiya ,itama fitowa tayi suka nufi cikin gidan ,kowannensu d'auke da sallama a bakinsu ,da shigarsu parlor suka yada zango Humaid ne ke dariya yana kallon Khadija yace ”baby kingaji ko farr tayi da idonta tace ”yaya mungaji dai cikin sigar tsokana yace ”to gafa tsaraba na kawo miki dan nasan bakya bata kunya tasowa tayi tazo kusa dashi ta zauna wata leda ce mai kyau ya ciro mata gasashiyar kaza ,murna takeyi tana godiya Humaid ne yace ”to yanz mekuma kikeso ,rufe fuska tayi tace ”nakasa tashi d'auko ruwa zansha yana dariya ya mik'e ya d'auko ruwan ,bayan ta cika cikinta ne humaid yace ”to muje muyi alwala yaukam 'zamuyi nafila a sa'a lol."

Hhh wata nafilar aka kumayi akayi adu'oi sosai daganan 'naga Humaid ya sunkuci Khadija yana harara ta ,garin gudu har nakusa fad'uwa 'asbha tagari amarya da 'ango.



Bayan komai ya lafa ne na hango Khadija nata kuka tana cuno baki ,Humaid da fitowarshi daga wanka kenan yace ”haba baby kiyi shiru mana ya marai raice murya kamar mai shirin kuka ,dariyace da kufce mata tace ”kazo ka d'agani 'inka gama tsokanata ,kaya yafara cire mata sanan ya sunkuceta ya kaita bathroom cikin ruwan wankan daya tara mata wani ihu tasa kamar wacce ake shirin cirewa rai can anjima ta lumshe ido sabda zafin ruwan ya ragu ,zubarda wancan yayi yakuma tara wani ,dubanta yayi yace ”to fito inyimiki wanka ,kuka tafara tana yaya dan Allah kaje ka fitomin da kayan dazansa please zanyi da kaina ,zai juya ya hangota ta kwanta kamar wacce ta sami katifa cikin bahon wanka ,dawowa yayi ya fara yimata wankan tana had'ashi da Allah yanayi bai fasa ba."


Nad'ota yayi cikin towel kamar baby hhh ashefa babyn ce ,kwantar da ita yayi a kan gado yafara shafa mata mai , yana gamawa ya d'auko ta ya zaunar da ita gaban dressing mirror ,itadai ta koma kamar photo ko magana batayi powder yafara shafa mata dagan an ya d'auko k'wali ya sanya mata ya d'auko janbaki ya shafa mata hh gurin yin jagira ne yayimata kamar titi fakaceciya dariya sukasa ,gogewa yai yace ”to ainayi mai wuyar ko kinga inda kikayi kyau kuwa hmm kamar sarauniyar kyau , to zomuje kisa kaya ko baby ,kuka zata fara yace ”mai yafaru kuma¿uhm uhm ni yaya bazan iya tafiya ba please help me ,cewa yai uhm uhm nima Ladidi da k'yar nake tafiya ,dariya da kuka ne sukayi nasarar k'wace mata shikuwa yana ganin haka ya sunkuceta ya dirita a gado ,had'ashi ta dingayi da Allah dama ba komai zaiyi mata ba kwai yanason sata yin shiru ne ,cewa yai zonan muyi adu'a ,cikin shagwa6a tace ”yaya kayanfa ?,riga da wando ya ciro mata masu flawoyi a jiki wandon iya gwaiwa ne rigar kuma iya cibiya bayan tasa ne ya kamo hanunta yana sunbatar k'amshin tiraren data fesa yace ”dan Allah ki yafemin Khadija dan Allah ,raahin fahimtar abinda yake cewa yasata kallonshi tace ” yaya ban ganeba ,kukane yayi nasarar kufce masa yace ”nayi miki mumunan zato Khadija asheke cikakiyar budurwa ce nagode da kika kularmin da kanki ,domin duk soyayyar da kuka zuba da buduraka muddin bata tare da budurcin ta to wallahi bazatai daraja a idon mijinta ba ,Khadija ce ta fad'a jikin Humaid tana kuka mai cin rai ,rungumeta yayi yana kwararo mata 'adu'oi akan albarkar rayuwarta ."


Kitchen suka shiga suka had'a breakfast mai rai da lafiya bayan sungama ne Khadija ta zubo musu shikuma Humaid ya shiga wnka ,yana fitowa Khadija ta d'auko wayarshi tafara yimusu photo ,hotuna sukayi kala kala wani ya d'auketa wani kuma tana bayanshi wani kuma ya rungumeta daganan suka zauna cin abinci ,suna gama Humaid yace ”zaije ya dawo insha Allah baze dad'e ba ,rau rau Khadija tayi da ido tana cewa yaya please kaje dane man dariya yasa yace ”to shirya man am sorry sweetheart yanz zandawo afuwan kinji to Allah ya dawo dakai lafiya hubby ,zaro ido yayi yace ”dama inada Suna na musamman shine ake rowar gayamin juyi tayi tace ”yaya kaje ka dawo cikin sauri ya fice sbda Doctor Umar ne yake kiranshi a hospital ."


Misalin k'arfe 1pm Khadija takuma shiga wanka simple makeup tayi ammafa tayi kyau sosai shadda ta d'auko kalar wacce Humaid yasa mai ruwan coffee ba k'aramin kyau shaddar tayi mata ba kasancewar farace sark'a da d'an kunne tasa sai kuma agogon hannu wohuu kamar ka saceta dan kyau, alamar nocking akeyi mai gadi ne ya tambayeta daga ina kike hajiya ? Matar ce tace ”sunanan Rahma to kishiga hajiyanna ciki ,tana isowa part d'in Khadija tafara nocking a nutse Khadija ta fito ganin Anty Rahma ce yasata rungumeta suka shige ciki ,Anty Rahma ce ta kalli Khadija tace ”amarya yakuma k'arin hak'uri alhamdulilh Khadija tace "ta mik'e ta dibowa 'Anty Rahma kayan motsa baki hira sukeyi cikin farinciki tana tabyarta ina yaranta twins dariya anty Rahma tayi tace ”kema ina yimiki fatan hakan rufe fuska Khadija tayi tace ”rainon twins da wahala anty ,sallamar Humaid ce ta katse musu hirarsu wani tsalle Khadija ta doka tatafi da gudu ta dalle bayan Humako.."


Anty Rahma ce tace ”to ni zantafi masoya Khadija na baya ta rufe ido dagan an tacewa anty Rahma bye bye Humaid ne yace ”ina yini ya yara lafiya Lou tace ”daganan tayi gida ,hmm wato khady ko kunya babu 🤭.


Sauketa Humaid yayi yana yimata wani irin kallo afuwan fans gaskiya zaman gidansu Khadija yafi k'arfin mom Islam .

*AFTER TWO MONTHS*

Kwance take kan cinyar Humaid wani amai ne ya taso mata ,kafin yayi yunk'urin mik'ewa ta wankeshi da aman kuka takeyi sosai sbda bak'on yanayin daya ziyarce ta sam batajin dad'in komai a rayuwa ,d'aukarta Humaid yai ya wanke mata jiki ya dawo ya kwantar da ita 'a kan gadonshi ,komawa bathroom yai ya wanka yasakeyi ya shirya ,hijab ya sanya mata ya d'auketa yafice da ita ,bud'e mota yayi yasata 'a back side ya rufe k'ofar ,direct hospital suka nufa da isarsu aka taresu kasancewar halin su kenan kowa na cewa doctor kak'i dawowa aiki hak'uri yaketa basu kasancewar yanzu hankalinshi ba 'a kwance yake ba ,office d'in doctor Umar ya shiga ganin bai ganshi ba yasashi komawa mota ya rik'o hannun Khadija da ta galabaita ya kaita wani d'aki da babu marasa lafiya ,pitsari yasata yi bayan tayi ne yaje wani lamp ya d'auko abin d'iban jini yana d'iba ya fice test yaje yayi zuwa minti talatin result ya fito bud'e baki yayi yana kabbara wani doctor Hashim ne yace ” doctor da kanshi yana awo tsabar farinciki Humaid yace ”Hashim yanzu ma zamuje d'akin awon munsami k'aruwa, kowa sai tayashi murna yakeyi."


Khadija dake kwance tanajin kwad'ayin shan tsamiya ta taso tana shirin fitowa sukayi ido biyu da Humaid cewa yai haba baby yazaki wahalarmin da kanki 'ina zaki ,cikin shgwa6a tace ”tsamiya nakeson sha ,zaro ido Humaid yayi yace ”kekuma naki jarabawar kenan¿zata yimai kuka yace ” come down zomuje ayi awo sai mu k'ar6i magani mu wuce kasuwa ,babu musu tabishi suka wuce ana gama mata ya kar6o magani suka shige mota basu sauka a ko ina ba sai kasuwar farar gada ,kayane gasunan na masu ciki irin su tsamiyar biri malmo ali mai ruwa dakuma tsada da agwa luma lol dama wanda na manta haka yadinga jidar mata kayan tsami hhh yaufa babu sha'awar cin kaza saboda wari takeyi mata lol.


Da isarsu gida ya zuzuba mata wasu a fridge wasu kuma ya wanko mata suka zauna tanata sha ko tayi babu ,hh Humaid da keta k'are mata kallo yace ”Alhamdulilh Allah yabani kyautar mata tagari kuma zata haifamin y'ay'a nagari am very happy wow Khadija bansan da bakinda zankuma yimiki godiya ba please kikula mana da babyn mu ita dai ko kallonshi batayi ba abinda yafi komai dadi takeshi ammafa a gurinta.

TV Humaid ya kunna NTA wani rahoto ne yaja ra'ayinsu gani nayi Khadija ta tashi ta zauna ,shima Humaid d'in gyara zama yai wani matashin yaro aka nuno hannuwanshi a d'aure yana koro jawabi kamar haka.

_Nidai sunana Ammar d'a daya tilo ga Alhaji Atiku dollars nataso cikin gata da kulawa a London aka haifeni iyayena basa zama a Nigeria amma ni a Nigeria nake rayuwa ,wani soja dake tsaye ga wasu kuma dake ririke da last speaker suna yimasa tambayoyi to maiya kaika aikatawa y'ar minista fiyad'e ? tsautsayine yace ”a takaice ,wasu tambayoyin aka kuma jeromasa akan cewar kwanaki ankashe mai gadi agidan yaron Alhaji ABDULL... ko zaka iya bamu cikakkiyar amsa eh ninne na kashe shi ,kuma ba shi naso kashewa ba tsohuwar budurwata naso kashewa kokuma mijin da ta aura ,bayan nan ko akwai wani kisan daka ta6ayi babu nasani tawa ta k'are k'arfin arzik'in mahaifina bazai fitar dani daga hannun hukuma ba_.


Daganan aka wuce gurin .


Kukane ya kufcewa Khadija sbda tayi dana sani akan sanin Ammar datayi amma Alhamdulilh tunda gashi a hanun hukuma .


Suna cikin alhinin Ammar sukaji sallama ,Humaid ne ya mik'e jiki a sanyaye bud'e k'ofar yayi yana k'are mata kallo yace Khairat!!!! momy dake baya ta shigo sanye da hijab tace ” daughter kinga yarinyar da tayi sanadin ciwonki nan ,mik'ewa Khadija tayi ta fad'a jikin momy ta saki kuka mai tsuma zuciya d'ago kanta tayi tace ”momy wanan wacece ?"tsohuwar matar Humaid ce ,momy ce tabata kaff labarin auran Humaid 'dakuma abubuwanda suka faru bayan barinta gida da halin da momy ta shiga ,kuka Khadija takuma sawa ta durk'usa ta rik'e k'afar momy tace ”momy dan Allah ki yafemin,dana zauna da baki dinga zubar da hawayenki ba natuba momy ,d'agota momy tayi tace ” daughter na yafe miki karki damu kowane bawa da tashi jarabawar ,Khairat ce ta durk'usa 'a gabansu momy tace ”dan Allah nima ku yafemin ,nasan na cutar daku gashi ta sanadiyar bin bokaye fuskata ta k'one kowa guduna yakeyi kuma iyayena ma sun tsune min ta had'a hanunwanta biyu tace ”dan Allah Ku yafemin kodan guduna da duniya takeyi ,Khadija ce ta d'agota tace ”na yafe miki Allah ya yafemana ,Humaid da ko kallonta bayason yi sabda fuskarta tayi abin k'yama yace ”indai zaki ficemin a gida to na yafe miki jekiii ya daka mata tsawa momy ma cewa tai ta yafe mata daganan ta fice ,tana fita suka rufo k'ofar d'akin ,jin wani k'ara da wata mota tayi yasasu bud'e get suka fito da gudu ,motace ta kad'e Khairat jini ta baki jini ta hanci ,drivern kuma ya gudu ,cikin azama Humaid yazo ya jijigata jin alamun babu rai a tare da ita yasashi salati momy ma salatin takeyi Khadija kuwa na kuka gidansu ya nufa da ita inda da shigarsu suka tarar da mahaifinta da mahaifiyarta a parlor."

Bayan ya gaishesu ne yake fad'a musu tare da Khairat yazo ,a fusace mahaifin nata ya mik'e yana nuna Humaid yana cewa karta sake ta shigomin gida da k'azamin jikinta mai za'ayi da mazinaciya !!! Kuka Humaid yafara yana cewa dady ku yafe mata motace ta kad'eta kuma babu alamun nunfashi a tare da ita momy a razane tayi waje dady ko ciki ya shige irin ko a jikinshi ,momyn Khairat na ganin ta tafad'i ta suma dady ne ya fito da gudu shima ganin gawar Khairat yasashi nadamar tsa tsauran hukuncin da ya yanke akanta yafa cewa nayafe miki Khairat Allah kayafewa Khairat .


Wayo Allah mutuwa fa ta

Please Login or Register in order to submit comment