Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata kira ™udundunewa tayi cikin kayan wankin mamanta dake gefe , koshi da yake Wakin bai san tana ciki ba , ashe tayi bacci ma .
Koda yaya Zakari ya shigo , Wakinsa ya nufa domin cin abinci , shima yana ganin aikin da akayi yasan aikin na manya ne , ko magana baiyi ba ya fice waje,
Sallama mama tayi tana cewa ina ´ar albarka harta gama aikin ?
Malam dake Waki ba™inciki ya isheshi ko kulata beyi ba yahau jan carbi , shigowa Wakin tayi tana sallama amma shiru , ganin yana jan carbi yasata Waukar kofin ruwa tasha tahau gado ,
Ajiye carbin yayi a gefe yafara bal bala masifa yana cewa " kinbar ™ara fita da magriba tunda huWubar da kikayi mata kenan , maman bata fahimci inda ya dosa ba tace " malam ban fahimceka bafa , eh ai bazaki fahimta ba naba Aisha Wari huWu kuWin cefane nazo nasami tuwo da ™uli .
dariya ce taso suSucewa mama sai ta waske tare da cewa dama ciko nakeyi ita tayimaka na dai dai kuWinka ne , ta inda malam ya shiga ba tanan yake fita ba , gashi an rasa Aisha , mama ta hangota sbda karta ja mata duka yasa batace ta ganta ba ,
Washe gari da safe malam yayi sammako zuwa jos kasancewar wani aiki da aka kirashi yi na malinta , ran Aisha fess cikin sauri ta shiga wanka tana fitowa ta le™a ta katanga tace " Ummi na shirya ke nake jira , Ummi dake wanke kwanuka saura tukwane tace " nima koda ruwan sanyi zanyi wanka yanzu na fito wanan tukwanen sun sha ruwa , ta tsallake ta wuce gurin rijiya , wucewa Waki Aisha tayi tare da shafa hoda da pink Win janbaki sbda mama akwaita da ™o™arin siya mata kayan kwaliya kuma babu laifi ta iya kwaliyar , doguwar riga tasa ta atamfa Winkin ba ™aramin kyau yayi mata ba , mama jeki duba akuyoyi sun shigo , da sauri mama ta mi™e sbda tana gudun Sarna ta fice da sanda .
Jin mama ta zauna a waje yasa Aisha Wauko wata ™aramar breziya da suka sato a gun mai gwanjo ta cikata da safar makaranta ta cire rigar tasa , Wauko dogon hijab tayi tasa takuma yafa gyale ta fice da uban gudu , bata tsaya ko ina ba sai gidansu Ummi , tun daga zaure take ™wala mata kira , cikin sa'a Ummi ta fito ita kuma da riga da wando na shadda babu laifi tayi kyau itama harda breziyar tasa tayo waje da gudu , mamanta na ™wala mata kira amma duk a banza ko juyowa batayi ba.....!

Da nayi muku al™awarin zan ™ara read more jiya banga comments ba , da bazanyi typing Win yauba tunda litrafin baiyi muku ba raina ya Sacci zan tafi hutu inhar babu comments wlh.

Tofa manyan mata sun fice ko ina zasu dosa oho kubiyo da shar'hi domin jin cigaba >ØpÝ

*MOM ISLAM*
[14/07, 7:53 am] Mom Islam Ce=؃Ü: *YARINYA MAI TAARGAZA*


Typing
'þ.

STORY AND WRITING
BY
*Zainab Habib [Mom Islam]*

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*

Telegram links https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Wattpad momislam2020

FREE BOOK>ØpÝ

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*.

Page 11 & 12

Suna tafiya suna yanga wai su a dole ´an mata lolz fans kuji fa ´an shekara goma da wanan lamarin .
Wani saurayi dake zune a kan dakalin da zasu wuce ya kallesu ya tintsire da dariya harda tafawa , Aisha da takai ™ololuwa gurin jin haushi ta juya zatayi gurinshi , janyota Ummi tayi tare da cewa " kinsan fa inda zamuje karki kulashi gabama zamu haWu sai mun zubar masa da ha™wara munyi masa wawulo suka kwashe da dariya sukayi gaba.
Gidan wata amarya da aka kawo satinnan suka nufa .
Gidane mai Wauke da Wan madai daicin get dakuma flawoyi masu kyau yanayin tsarin gidan yasa baza'a kira mai gidan talaka ba amman yanada rufin asiri , amaryar a layinsu take kusa da gidan su Ummi hakan yasa yau zasu kai mata ziyara .
BuWe get Win sukayi kana suka shige , zaune suka sami amaryar mai suna Sudat tana kallo a tv tana sanye da doguwar riga ta atamfa , gaisheta sukayi cikin ladabi kana suka mai da hankali ga tv .
Mi™ewa tayi naga ta nufi wata ™ofa , sai gata ta dawo da plet cike da cin cin da cake ,dakuma jug mai Wauke da haWin fresh a ciki , da ´a´an jug Win .
Zuba musu tashiga yi tana gamawa ta mi™e ta shige ciki .
Aisha ce ta kalli Ummi tace " musha ruwan lemu ga leda mu Wura cincin , haka kuwa akayi suka juye cincin duka .
Aisha ce tace "wa Ummi zokiji kawo kunnenki bansan mai ta gaya mata ba naji sun sa dariya .
Saudat na fitowa sukace zasu tafi har sunyi kamar zasu wuce suka dawo tare da cewa " wlh anty mijinki bin mata yakeyi jiya muka ganshi da wata budurwa yana gyara mata sa takalmi wani uban ihu Saudat tasa tare da cewa ˜amalu......yau akwai bala'i .
Da gudu suka fice suna maida nunfashi basu tsa ko ina ba sai ™ofar gidan su , a zauren gidan su Ummi suka tsaya aka raba cincin kowa ya shige gida .
tun magrib yaya Zakari ke shirin zuwa gurin Fiddausi anayin isha'i ya na dawowa daga masallaci ya nufi gurinta ,
zaune yake a kan dakalin ™ofar gidan su yana jiran yaga yara ya aika kasancewar bai samu ya siya mata waya ba , cikin sa'a wani yaro yazo wucewa .
kai dan Allah shiga gidannan kace ana sallama da Fiddausi cewar yaya Zakari .
Ba musu yaron ya shiga nanda nan sai gashi ya fito tare da cewa" wai gatanan zuwa , to nagode yaya Zakari yace " mintuna ™alilan sai gata nan cikin sanyin jiki , tun daga tahowarta yagane kamar batada lafiya amma baiyi magana ba sai da ya bari ta zauna sannan yace " lovely y kwana biyu ya su mama , lafiya lau tace " kanta a sunkuye .
Meke faruwa ne naga duk kinyi wani iri ,
Cewar yaya Zakari .
Su baba ne sukace nafito da miji nanda kwana uku , zaro ido Zakari yayi yana nazarin maganarta .
Hmm yaya Zakari ya nisa kana yace " gaskiya ina sonki Fiddausi amma maiyasa suke gaggawa ?" anan kam maganar tafara yiwa Fiddausi nauyi cikin dakiya tace " sha'a ...sha'a Zakari ya kasa ganewa ita kuma sauran kalmomin sun ma™ale a bakinta ta mi™e da gudu tana kuka .
Babu inda ya iya ya mi™e tare da komawa gida , dama baici abinci ba ya tafi gashi yaci karo da tashin hankali gashi ba wani kuWi yake dashi masu yawa ba , juyi yakeyi yana tunanin duniya dakuma abubuwan cikinta bashi yasamu bacci ya Waukesa ba sai waje ™arfe uku na dare .
Washe gari malam na fitowa ya le™a Wakin kwanan Aisha kasancewar tun jiya ya dawo da daddare bai sameta ba .
Ko sallama baiyi ba yafara kai mata duka da carbi da gudu tayo waje bata tsaya ko ina ba sai zauren gidansu Ummi .
Jiyo kururuwar kuka yasata tsagaita nata kukan tana saurarar mai kukan , tabbas Ummi ce.
Ji tayi maman Ummi na cewa " dan ubanki tun baki tafasa ba zaki ™one uban wa yabaki breziyar da nagani cikin kayanki , babu kowa mama Ummi tace " tana zabga ihu .
Jin saukar bulala yasa Aisha waigawa malam ne har zauren gidansu Aisha ya rufeta da duka.
Saida yayi mata lilis sanan ya koma gida inbaku manta ba dama yatafi da haushin gayan tuwo da ™uli ,haka taja ™afafuta ta koma gida , kai tsaye gurin kayanta ta nufa ta janyo breziyar data cire jiya ta ™udundune a leda ta taje ramin wani bulo ta Soye .
Bayan duka ya baje mama ko uffan batace ba sbda itama yawon ya isheta , wanka Aisha tayi ta janyo kayan kwaliya tasa hoda da janbaki ta ciro atamfarta ta sallar bara ta sanya , Winkin yayi mata kyau sosai kasancewarta mai Wan ™iba kaWan , Matsowa tayi gurin katangar gidansu Ummi tace " Ummi fito muje , Ummi dake sanya hijab tace " kifito ganinan .
Niko nace wai su basu gajiya ne ..
a tare suka fito kowanne mamansa na Wakinta shiyasa suke samun damar ficewa , suna cikin tafiya kowacce na bada labarin dukan dayasha .
Ganin mai sai da kwakwa yasasu cewa tsaya zamu siya mai kwakwa da fara'arsa ya sauke yana cewa ´an mata kunyi kyau sosai dazaku amince dani kowacce zan bata ™walon kwakwa bi biyu .
Sun gano mai yake nufi kasancewarsu masu shegen wayo kuma iyayensu na yimusu nasiha tun ba yau ba , mun anince bamu , kun amince fa kukace ?
Eh su Ummi sukace cikin haWin baki , to kuzo muje Wakina na gaban mai siyarda shayin cikin kasuwa , Aisha ce tace amma babu mutane ko ? eh ba kowa ma gurin .
to muna zuwa bari mu zo , suka nufi zauren gidansu Aisha tare da Wauko wani abu a ba™ar leda da basa rabo fashi komai runtsi .....!


Shar'hi yayi low>ØpÝ


*MOM ISLAM*
[14/07, 7:54 am] Mom Islam Ce=؃Ü: *YARINYA MAI TAARGAZA*





Typing
'þ.


STORY AND WRITING
BY
*Zainab habib [mom islam]*

*[AREWA WRITER'S ASSOCIATION]*

Telegram links https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Wattpad momislam 2020

FREE BOOK>ØpÝ

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Page 13 & 14

Da wowa sukayi gurinsa suka Wunguma zuwa Wakinsa , ganin sunja sun tsaya yasa mai kwakwa cewa " kushigo man babu kowa , shigewa yayi da tiren kwakwarsa ya fara cire riga yana shirin cire wando Aisha ta kutso kai tana ri™e da hanun Ummi sai da suka bari ya cire wando saura gajere yana yimusu dariya suka fesa masa ™arara wato wanan abin mai ™ai ™ayi , wani razanannen ihu mai kwakwa yasa tare da cewa " ubanku dan uwarku yana susa yana rawa , Aisha ganin abin yafara aiki yasasu kama yin rawa suma , har kwanciya yayi a ™asa yana birgima amma babu wanda yasan yanayi bare a kawo masa agaji , yayi nan da gudu yayi can da gudu kamar sabon kamu .
Shigewa gurinda ya ajiye tiren kwakwa sukayi yanaji yana gani suka kwashi ™walo uku manya , sai yayi kamar zai hanasu sai ™ai ™ayi yayi masa sallama .
suna cin kwakwa suna cewa oya shoki shoki suna jefa ™afa , nufosu yayi da gudu suma suka Wiba da gudu suna haki . basu tsaya ko ina ba sai a ™ofar gidansu .
Ummi ce ta jiyo hayaniya daga gidansu , Aisha zomuje ana faWa a gidan mu
Suna shiga sukaga maman Aisha da maman Ummi ke faWa , maman Ummi ce tace " wlh yarinyarki kesa Ummi yawo kuma anyi na farko anyi na ™arshe tunda bazaki jawa yarinyarki kunne ba ,
Fitowa sukayi da gudu Aisha ta nufi gidansu Ummi ma binta tayi ganin Aisha ta Wibo ruwa a bokiti yasa Ummi cewa mezakiyi Aisha ?" Aisha dake kuka tace " raina ya Saci Ummi meyasa zasu dinga faWa ruwa zan kwara a katifarsu , kema jeki kwara a ta mamanki .
Cikin azama Aisha ta she™a ruwan a katifar tana haki , zuciya ce ta Wibi Ummi itama taje ta faki idonsu ta she™a a katifar mamanta wai a dole ransu ya Sacci lolz.
fitowar maman Aisha ne yasa Ummi shigewa gidansu , tana shiga mamanta tahauta da masifa wai yanzu ta Saci da yawo tana biyewa Aisha , ha™uri Ummi tashi ga badawa harda ´ar ™wallah , shiru maman nata tayi alamun ta ha™ura hakan yasa Ummi shigewa ta zauna tana tuno mai kwakwa , kwashewa tayi da dariya harda tafawa ta fito da gudu kamar wacce aka zabura ta le™a gidansu Aisha ta katanga tana cewa Aisha ya mai kwakwa , she™ewa da dariya sukayi suna ™arawa .

*WASHE GARI DA RANA*
Zaune yaya Zakari yake gaban iyayensa yana gaya musu yanason yin aure , malam dake jan carbi yace " wato kai ka ri™a harda iya zuwa mana da zancen auranka?
Mama ce ta katse malam da cewa " yaronnan fa inza 'ayi adalci to abin abinda yakeso shiru malam yayi batare da ya ™ara bi takan mama ba , ya janyo buta ya kuskure baki yayi gaba .
Mama ce ta dubi yaya Zakari tace " kayi ha™uri zani ™auye gurin yayana inyimasa magana karka damu , kan yaya Zakari a sunkuye yace " to mama.

*ISLAMIYA*
Kowa ya sansu walau malami ko Walibi ko sunyi latti ba'a dukansu babu ma mai kulasu .
Suna shigowa cikin islamiyar suka tarar anyi sabon malami zasu wuce ya daka musu tsawa tare da cewa " ku tsuguna ku Waga hannu sama tsabar baku da kunya zaku wuce kai tsaye .
Wata uban hajijiya Aisha tayi sai ga........!

Muje zuwa fans

More comments more typing
'þ.

in naga shar'hi zakuga sabon update anjima>ØpÝ

*MOM ISLAM*
[14/07, 7:55 am] Mom Islam Ce=؃Ü: *YARINYA MAI TAARGAZA*





Typing
'þ.


STORY AND WRITING
BY
*Zainab habib [mom islam]*

*[AREWA WRITER'S ASSOCIATION]*

Telegram links https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Wattpad momislam 2020

FREE BOOK>ØpÝ

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Page 15 & 16

Jin saukar duwatsu yayi a jikinsa, Aisha na tabbatar da yaji zafi tace " Ummi ga naki .
Ganin zasu yi masa illa yasa shi binsu da gudu su kuwa suka fice waje , suna gudu malam na gudu .
Ummi ce tace " Aisha taro mai ayaba aikuwa cikin ankara ta janyo tiren mai ayaba dama da akwai Sararun Sawo ta wurgawa malamin cikin sa'a ya taka ya sule , sukuma suka yi hanyar gidan su kowacce na maiyar da nunfashi .
Zaune malam yake yana aikin nasa wato jan carbi, duban mama yayi yace " a ina aka tsaya ?" mama da bata fahimta ba tace " ban gane ba , ai bazaki gane ba cewar malam.
Shiru mama tayi dan ance faWan da yafi ™arfinka sai ka maidashi wasa . sai da malam ya gama jan carbinsa sanan ya juyo yace " ba yaronki yace " aure yakeso ba ? uhm mama tace " tana nazarin irin maganar da zata faWawa malam.
Amman kasan ba yabon kai ba Zakari ya mallaki hankalinsa bugu da ™ari yanada gini nasa na kansa bayan haka kuma yanada zuciya dan wanan aikin garejin da kake rainawa yana temakonsa bama shi kaWai ba har mu .
To to to naji zabiya mai yabo inhar ya tara kuWin aure yazo zanyi masa amma nikam banida kuWi .
Shigowar Aisha da gudu ne ya katse musu zance ta shige Wakin da yake a mazaunin nata da gudu tana haki .
Kingani ko wlh da yarinyar nan zata sami miji aurar da ita zanyi .
zaro ido mama tayi cikin mamaki tace " wanan wace irin magana ce ? yarinyar da ko shekara goma sha Waya bata cika ba kace aure zakayi mata ?" to wlh bazan lamunta ba ehe wane marar lissafin ne zai aureta , jin mama tahau masifa yasa malam jan baki yayi shiru amma cikin zuciyarsa har ga Allah Aisha ta ishe shi yanzu .
Ta taro takalmansa yayi ya fice yana mita , mi™ewa mama tayi ta shiga gurin Aisha , samunta tayi zaune tana maida nunfashi .
Keda waye ? cewar mama
Babu kowa mama rige rige mukayi shine na riga Ummi zuwa gida , janyota mama tayi ta kwantar da ita kan cinyarta tace " ´ar albarka , na'am Aisha cewar Aisha .
Maiyasa kikeson ganin Sacin raina ? ko kinfiso indinga kuka kullum .
HaWe rai Aisha tayi kana tace " mama ki yafe min nadena in Allah ya yarda .
Cikin farinciki mama ta rungumeta tanajin son autar tata a cikin zuciyarta .
Aslamu alaikum mama ta jiyo sallama .
Wa'alaikumussalam cewar mama kashigo man.
Shigowa yayi Zakari yayi yana kallon Aisha dake kwance a jinyar mama , mama ina wuni cewar yaya Zakari.
Lafiya lau ya aiki,
yaya Zakari ne yace " aiki alhmdulilh ya kukayi da malam?
Bayanin da malam yayiwa mama tayi masa dariya yaya Zakari yasa , abin yaba mama mamaki amma sai ta tambayesa tace " lafiya kuwa ?
lafiya mama wato malam tun yanzu ya fara karaya kenan ikon Allah mahaifinka ma kenan yayima haka bare wani , to yasha kuriminsa na tanadi komai jiya aka yiwa gidana fenti ansa komai , kuma na gayawa ogana yace " duk abinda nake bu™ata kar naji nauyinsa in gaya masa Wazu ma yabani kyautar dubu Wari da hamsin yace " inkai sadaki , wasu hawayen farinciki ne suka ziyarci kumatun mama tare da Waga hannu sama tana yiwa Allah godiya ,
Aisha dake kwance tace " wlh kudena yarda malam yanada kuWi masu yawa a Wakinsa shiyasa baya bari kowa yana shiga .
Ina ne Wakin nasa da ya wuce na mama ?" yaya Zakari ya katse ta .
Ka mance Wakin dabobinka da ya mayar Wakinsa ku jirani .
Binta kawai sukeyi da kallo babu wanda ya tambayeta ina zataje suna zaune sunyi jugum.....!

Nagode na ™in yin comments wlh badan ha™uri da aka bani ba nadena typing Win book Winnan raina yana mugun Sacci shiyasa ko nayi tunanin ™ara yawan rubutun nake fasawa tunda bakusan maiyi muku ba typing Win littafin kuWi nakeyi na ajiye shi nake yimuku wannan shima kuma ina yinsa duk baku godemin ba , am sorry to say gobe da jibi da gata kai har one week bazaku sami typing ba nabarku lafiya =ØMÜ.



*MOM ISLAM*
[14/07, 7:55 am] Mom Islam Ce=؃Ü: *YARINYA MAI TAARGAZA*





Typing
'þ.


STORY AND WRITING
BY
*Zainab habib [mom islam]*

*[AREWA WRITER'S ASSOCIATION]*

Telegram links https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Wattpad momislam 2020

FREE BOOK>ØpÝ

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Page 17 & 18

Suna zaune sai gata da wata jaka mai kamada algara ra an Waure bakinta da zaren lilo , buWe baki mama tayi tace " Aisha a ina kika samo wanan abin haka ? Aisha da gumi yafara rufeta tace " wanan fa kuWi ne a ciki kuma wlh masu yawa ku kunce ku gani , a tsorace mama ta Wagawa yaya Zakari hannu dan yana shirin karSar jakar , karka sake ka karSi wanan jaka itama tazo ta mayar inda ta Wauko , haWe rai Aisha tayi kana tace " tsoronsa ku keyi ne ? taSS kunce jakar tayi ta zazzage duka kuWin a ™asa da mamaki mama ta dubi yawan kuWin da a kinta tawa zai kai sama da dubu hamsin tace " Aisha ban isa dake ba ko amma me na gaya miki ? bakida gudun magana ko ? shidai yaya Zakari kansa na ™asa bai ce komai ba kuma bai Wago ya dubi kuWin ba , ana haka suka jiyo sallamar malam , ba Aisha da ke tsaye ba harsu mama gaban su na dukan uku uku tabbas sun shiga uku yau kam , girgiza kai malam ya shiga yi tare da cewa " a lallai ashe dama bincike kuke yimin a Waki in bana nan ? Aisha na shirin magana ya zula mata carbi tare da sunkuyawa ya tattare kuWaWen ya tura a jakar da Aisha ta fito da ita , to wlh karkuga ko dan kunga kuWinnan kuce nerata zatayi ciwo hukuncin masu bincike kenan munafukai daga haka ya wuce da kuWinsa zuwa Waki .
Gumm Aisha tayi tana zaro ido kuma taci alwashin Waukar kuWin ankon bikin yaya Zakari a ciki koda za'a kasheta.

Šan uwan mama yazo daga ™auye sunje sun tambayo auran Fiddausi mahaifinta yace " inda hali bayason bikin ya wuce wata Waya , wata uwar zufa ce ke karyowa malam sbda a tunaninsa shine zai yi komai .
Ji yayi Wan uwan mama yace " karku damu a shirye muke , wanan karon malam shiru yayi , sai rarraba ido ya keyi , bayan sun gama tattaunawa aka yanke lokacin biki nanda wata Waya bayan an bada dukiyar aure.
Tun a hanya da suka fito malam yafara masifa yana nuna Wan uwan mama da carbi , kasancewar tafiyar ™afa zasuyi yasa Wan uwan mama yin gaba bai kula harkar malam ba.
labari yayi wa Fiddausi daWi zata auri masoyinta , zaune suke ita da yaya Zakari suna hira , bayan shiru ya biyo baya yaya Zakari yace " inason in munyi aure ™anwata ta dawo gidan mu da zama , kasancewar Fiddausi batasan ™anwar tasa ba yasata cewa aiko danaji daWi sosai wlh , nan suka ci gaba da hirarsu wacce rabi ta maganar bikin su ne.

Biki saura 2 weeks anata shirye shirye ta kowane Sangare amarya tasha gyara ,su mama anata ™o™arin ganin an haWa akwati malam ko baya magana ya zuba musu ido.
Aisha ce zaune a gaban mama tace " mama ni wai baza ayi min anko bane ?" dariya mama tasa tace " nima fa yayanki ne ya kawo min a Winke dan haka ki kwantar da hankalinki inada atamfa ragowar guda Waya sai ayi miki riga da zani .
kuka Aisha tasa tana ta turje turje tana cewa " wlh sai nayi anko wlh sai nayi , shigowar Ummi ne ya sata tsagaita kukan ta dubi Ummi tace " Ummi yau rabon mu da fita kwana uku kenan zomuje gidan dilaliya in kai mata wanan ™yalen atamfar ko za'a samu a gidan ta .zaro ido Ummi tayi kana tace " Aisha a ina kika sami kuWi ? ban sani ba in bazaki rakani bane to ki barshi .
Aisha ko da wasa kar inga ™afarki ta taka waje dan zanyi miki duka ,
Dan ™awa Ummi ™yalen tayi tace " kije ki cewa dilaliya in akwai inaso wlh inhar bakije ba ko na siya bazan haWa dake a Winki ba kuma kinsan sauran ,
Kasancewar a hankali Aisha ke maganar yasa mama bata jiyosu ba, ficewa Ummi tayi cikin rawar jiki ta doshi gidan dilaliya sallama tayi ,
Cikin sa'a ta sami dilaliya zaune a tsakar gida da bahon kaya a gabanta......!


*MOM ISLAM*
[14/07, 7:55 am] Mom Islam Ce=؃Ü: *YARINYA MAI TAARGAZA*





Typing
'þ.


STORY AND WRITING
BY
*Zainab habib [mom islam]*

*[AREWA WRITER'S ASSOCIATION]*

Telegram links https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Wattpad momislam 2020

FREE BOOK>ØpÝ

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Page 19 & 20

Ina wuni an aikoni cewar Ummi , dillaliya ce tace " lpy daga ina ? cewa akayi in tambayo ko akwai wanan atamfar ? eh kin koyi sa'a saura tirmi Waya, nawa ce Ummi tace "jikinta na rawa .
Dubu uku da Wari biyar cewar dillaliya , to Ummi tace " bari inje in gayawa wacce ta aikoni Ummi ta fice da gudu zuwa gidansu Aisha,
Ganin Aisha a tsakar gida yasata cewa " Aisha wai dubu uku da Wari biyar , ™araso ki zauna babu kowa a cikin gidan mama ta tafi kasuwa , zama Ummi tayi tana rarraba ido , mi™ewa Aisha tayi ta nufi Wakin ajiya , bata wani jima ba sai gata da dubu biyar a hanunta , zaro ido Ummi tayi tace " Aisha sata ? shittt kiyi shiru kuWin malam ne bayaci sai tari zomuje suka fice ammafa gaban Ummi na dukan uku uku, kai tsaye gidan dillaliya suka nufa Aisha ta mi™a dubu huWu aka basu canjin Wari biyar , suna fitowa suka wuce gidan mai Winki Aisha ce tace " ayi mana mu biyu , mai Winkin ce ta dubesu tace " bazai isheku ba sai dai ayi muku ™ari da wani abun , sun yarda a hakan, mai Winki ta bu™aci dubu Waya , mi™a mata Aisha tayi suka fice , idanun Ummi cike da hawaye tace " Aisha bakyajin tsoron malam ko ? nidai babu ruwana , tsaki Aisha tayi kana tace " ina ruwana nida zan koma gidan Yaya Zakari zaku dena ganina , dan Allah can zaki koma ? cewar Ummi eh man sai ma ranar tazo .

Yau kwana goma da Waukar kuWin Aisha kasancewar malam ba duba kuWin yakeyi ba yasa bai san abinda ya faru ba , biki saura kwana huWu ba™i sun fara cika gidan su Aisha yaya Zakari yayi bakin ™o™arinsa gurin yiwa Wakin mama fenti .
Bayan sun karSo Winkin ta wuce dasu Wakin mama , mama na zaune tana duba kayan akwati taji an jefo mata leda , duba ledar tayi tana ganin anko ta Wago kai tare da cewa " na waye ? dariya Aisha tasa tace " nawa ne mama zokiji , dai dai kunnen mama taje tayi mata raWa wanda nima banji me akace ba ,
FaWa mama ta hauta

Please Login or Register in order to submit comment