Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haba yarannan fa sunyi aiki Wazu girki ma yana neman ga gararki taS ku koma ku zauna barin yi muku girkin , tana kallonsa ya shiga kitchen ya haWa komai yai sanwar taliya harda ja jjage ya gama ya fito , ruwa na tafasa yasa taliya ya juya ya dawo waje yana ™arewa Fiddausi kallo da mamaki a fuskarsa , amma baiyi magana ba .
Tun a mota Ammi ta fara faWa tana cewa "ashe kai yarinyar da kake nema ™arama ce kasa naketa ´ar murya to inka aureta ya zakayi da ita ? kokuma za'akai ajiyar dukiyar aure ne ? da sauri Khamis yasa a'a Ammi wlh inhar ban kasance da wanan yarinyar ba zan iya mutuwa , Ammi kam kunyar zancen nasa taji amma shi ko a jikinsa, suna isa gida Ammi ta shige ta barshi a mota ranshi in yayi dubu ya Saci inda batason Sacin ransa haka shima baya son nata , da gudu ya fito ya nufi part Winta ganin bata nan yasa shi juyowa ya dawo palo tare da haWa kai da guwaiwa ya rasa me ke yi masa daWi , fitowar Ammi ne yasa shi saurin mi™ewa ya kamo hanunta cikin murya ta mai shirin yin kuka yace " Ammi na ki gafarce ni na ha™ura da maganar Aisha , hawaye na sintiri a fuskarsa , hankalin Ammi a tashe taya za'ayi Khamis ya yarasa wacce zai nemo sai ´ar 11yrs ina bazai yuwu ba ,Ammi ta faWa a fili , jin tace bazai yuwu ba yasa Khamis mi™ewa ya nufi bedroom Winsa ya sa key ya faWa gado yana mai sakin marayan kuka.
Washe gari har ™arfe tara shiru babu labarin Khamis bai fito ba kuma Ammi ta gwada wayarsa shiru , hankalinta ya tashi sosai tama rasa dabara , ™ara zuwa bakin ™ofar Wakinsa tayi ta bubuga amma shiru ta kira sunansa yafi a ™irga bai amsa ba , Ammi tayi ficiki ficiki kamar mai ciwo ga gida ita Waya , rashin extra key beyi ba Ammi ta faWa tana share hawaye , da wowa palo tayi ta zauna tare da rafka uban tagumi tana jiran tsammani , takai awa Waya zaune a gurin babu motsin fitowar Khamis kodai ya mutu ne ? Ammi ta tambayi kanta .
bayan yaya ya gama girkin ya ™walawa su Aisha kira , a kasalance suka fito kasancewar sun galabaita da yunwa maza kuje kuci yaya ya faWa , Wauka Aisha tayi sukaje suka fara ci suna hira , zubawa anty Fiddausi yayi ya shige Wakin ya mi™a mata kasancewar ta koma Waki, da sauri ta karSa da alamu yuwa takeji amma tayiwa kanta na ™in yi girki , ba tare da ta tambayesa yaci ko baici ba ta fara kaiwa cikinta , zama yayi yana ™are mata kallo darajar cikin dake jikinta yasa yake tausaya mata badan haka ba bata isa ba.
bayan sun kammalah cin abinci sukayi sallah suka kwanta.
Kwanan Khamis biyu a kulle idanun Ammi sun ™an™ance tsabar kuka agajin drivers da masu gadi ta nema akazo aka fara buge ™ofa , cikin sa'a ™ofar ta buWe, wani uban wari ne ya ziyarci hancin su Ammi toshe hanci Ammi tayi tana dube dube , hangosa tayi can ™ar™ashin gado kamar wanda ya shekara yana ciwo da salati ta ™arasa gurinsa tana kiran sunansa , baya iya magana sai Wago hannu da yakeyi , cikin azama Ammi ta kama hanunsa tana shirin mi™ar dashi , mai gadi ne ya temaka mata ta mi™ar dashi ta nufi toilet dashi tace " suje ta gode , wanka Ammi tayi masa da brush ta shafa masa mai ta temaka masa ya sanya kaya ,ta zaunar dashi bakin gado , baya iya zama hakan yasa tana zaunar dashi ya Singire a gurin kasancewar jikin babu ™wari , da™yr Ammi ta iya fito dashi palo ta ™walawa ´ar aikin gidan kira ,da sauri tazo ta tsuguna gaban Ammi , Fati maza ki gyara Wa™in son kar inga datti cikin ladabi tace " to ta mi™e ta nufi Wakin nasa , driver Ammi ta kira tace " hospital zai kaisu , a ga gauce suka fito dashi aka sanya a mota suka nufi hospital, da isarsu aka fara bashi kulawar gaggawa ruwa aka ™ara masa da alurai bacci yai nasarar Waukarsa , zuwa 12:pm ya buWe ido fuskarsa ta ciko babu laifi sunan Ammi ya kira hawaye na zuba ta gefen idonsa , na'am Ammi tace " taja kujera dan taji mai zaice, Ammi na ki yafe min bazan ™ara yin abinda zai Sata miki rai ba na ha™ura da Aisha Ammina na ha™ura .Ammi ce taji maganar kamar wasiyya hakan yasa hankalinta kuma tashi tace "my son insha Allah sai ka auri Aisha koda arzi™in da muka mallaka zai ™are ta hanyar nemanta ni Amminka zan temaka maka da yardar ubangiji , murmishi Khamis yayi ya na shirin sau™owa daga gado fuskarsa Wauke da fara'a sai dai ramar da yayi sosai ta baiyyana , mayar dashi Ammi tayi tace " bakaga drip a hanunka bane my son ? naji sau™i Ammi na sami lafiya , cewar Khamis naji Ammi tace " koma ka kwanta yakusa ™arewa ma komawa yai ya kwanta yana ganin fuskar Aisha nayi masa yawo .
Zuwa yamma aka biya komai aka sallamesa suka dawo gida , duk da jikin nasa babu ™wari amma yana maganar zuwa gurin Aisha , Ammi mamakin wanan irin so takeyi , dole ta la llaSa shi gudu karya ™ara yin irinna jiya , sun samu Fatima wato ´ar aikin gidan ta gama abinci dining kawai suka nufa ,sai da Ammi da Khamis suka cika cikinsu sanan suka mi™e kowa ya nufi part Winsa , jin ana kiran mgrib yasa Khamis fitowa bayan yayi alwalah ya nufi masallacin gidan , Ammi ma alwalah tayi tayi sallah , jin wayarta na ring yasa ta Wagawa bayan ta duba sunan , aslamu alaikum Ammi tace " daga cab Sangaren akace wlkslm Ammi na gode da kikabar Afnan ta dawo batada lafiya , a zabure Ammi ta tashi daga zaman da tayi tace " aiko lafiya ta taho ni banma san musababin tahowarta ba , nima ta™i gayamin damuwarta amma ya kamata ke dakin matsa mata Ammi , mom Afnan kiyi ha™uri muma Wazu muka dawo daga hospital son babu lafiya , innalilahi mom Afnan tace " maiya sameshi ? zazzaSi wlh Ammi ta bata amsa , Allah ya ™ara lafiya mom Afnan tayiwa Ammi sukayi sallama.
bayan yayi isha'i ya dawo gida sbda bacci dake idonsa da alamu aluran da akayi masa basu gama sakesa ba , sallama yayi ganin Ammi a palo yace " Ammi yau da wuri zan kwanta bacci nakeji , tom Ammi tace " kasancewar likita yayi mata bayanin hakan ,kayi adu'a my son , insha Allah Khamis yace " ya nufi bedroom Winsa , sai da ya shiga toilet yai brush kana ya kwanta dan babu halin wanka bacci na idonsa .
Aisha da Ummi ne zaune bakin katifa suna shirin zuwa islamiya , wata ba™ar leda Aisha ta karSa a hanun Ummi tace " wlh yau sai malaminnan yayi dana sani , suka fito suna jiran yaya , bayan yaya ,ya fito ya samesu fuskarsu cike da annuri ,to yaya yace " ayi dai karatu ba wasa ba , to sukace cikin haWin baki , anty Fiddausi na Wakinta tana sana 'ar tata wato bacci , ko sallama beyi mata ba ya fice dasu , suna shiga ya tada mota suka nufi islamiya ana suwa bakin get Win ya sau kesu tare da bawa kowacce nera hamsin yace " in suna son wani abun , godiya sukayi masa kana suka shige ciki , hango malam Umar na taron latti kuma shine malamin su yasa Ummi cewa " wlh Aisha jeki hura masa nikuma zan kareki , da ™warin guwai wa Aisha taje dai dai saitin kunnensa ta hura masa cikin ikon Allah babu wanda ya ganta bare yai mata magana , suka wuce suna tafiyarsu kamar ba suba , koda suka shiga aji babu malam babu alamarsa Aisha ce ta le™a ta window ta hango malam Umar yanata susa malamai sun taru a kansa ya sosa nan ya sosa can ,ganin duka Waliban makarantar na fitowa ganin abin da ke faruwa yasa su Aisha suma suka fito , wani uban ihu da malam Umar ya zabga kai kace anyi masa alura ,sai surutai yake ,yana cewa " kuzo mu cashe kuzo ´an yara wayo bayana ku Wibo ruwa kuyimin wanka , dama ya gama cire kayan jikinsa duka yana shirin cire gajeren wandonsa malaman sukayo kansa da gudu sun rasa musababin sashi hakan sun fara tunanin anya ba haukacewa yayi ba , tsalle yayi ya hau bishiyar mangwaron dake makarantar ga ™ai™ayi kamar ana ™ara masa ,ganin abin baya baya yasa shi fara wurgo mutane da Wanyun mangwaro yana ihu , wata malama ce tace " anya ba hauka malam Umar ya fara ba ? dauran malaman ma haka suke faWa , gashi ya hau ™ololuwar reshe kaf cikin malaman babu mai iya sauko da shi , malaman ne suka kalli Waliban sukace akwai mai iya temakawa malam a cikinku ku sauko da shi , babu wanda ya Waga hannu sai Aisha , waro ido sukayi suna cewa " kece zaki iya ? eh Aisha tace " wani malami dake gefe yace " ku barta ta gwada basirarta , aiko suka barta ta hau bishiya tana zuwa saitin malam Umar ta karyo reshen itace ji kake timmm malam Umar ya faWo , da sauri aka yo kansa ana yi masa sannu a zabure ya mi™e ri™e da kafaWarsa yana kiran wayo zan mutu waiyo ™ai™ayi susa yake kamar zai cire fatar jikinsa, sudai yau suna ganin ikon Allah wata malama na shirin yiwa Aisha faWa malamin dake gefenta yace "ai ta fimu hikima kuma tayi ™o™ari ,barta kawai malamar zatayi magana taji wani azababben ™ai™ayi na shigarta da gudu ta yarda hand bag Winta tana gudu tana susa ta fice daga makarantar , inalilahi malaman suka shiga mai maitawa aka bi malama da gudu aka kamota aka sanyata a office suka kulle shima malam Umar da keta kewaye makarantar sun kasa kamashi badan haka ba kullesa za'ayi malam sai ihu take tana zage zage tare da cewa " kuzo kuyimin wanka da ruwa mai Wan Wumi Wumi ko zan warware , babu wanda ya kulata sai ma kewaye makaranta da sukeyi gurin kamo malam umar abin ya citura , Aisha da Ummi suna haWa ido sai su sakarwa da juna murmishi , da™yar aka kamo malam Umar aka kulleshi a aji......!


Ina jiran comments>Øpİ


*MOM ISLAM*
[14/07, 8:21 am] Mom Islam Ce=؃Ü: *YARINYA MAI TAARGAZA*





*Zainab Habib [Mom Islam]*



*Wattpad @momislam2020*


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*


*Page 48_49*


Bayan sati biyu , tunda aka sallamo sa daga asibiti bai kuma batun Aisha ba sai yau gudun kar ya Satawa Ammi rai duk da yasan tace " masa ta amince da maganar auran , cikin shiri ya fito yana sanye da farin boyel wanda ya fito da ainihin kyansa , dur™usawa yayi gaban Ammi yace " Ammi zani gurin Aisha ki tayani da adu'a ,insha Allah my son Ammi tace " cike da kulawa , jirani ina zuwa Ammi ta cewa " Khamis , samun guri yayi ya zauna yana jiran Ammin , fitowa tayi hanunta ri™e da wata farar leda mai ™yali ta mi™a masa tace " wanan na my suruka ne , farinciki fal zuciyar Khamis yana ganin Amminsa zata kula masa da rainonsa , tom Ammi aiko zan kai mata ya fice yana shirin buWe mota drivers suka fito , Waga musu hannu yai tare da cewa " ba nisa zanyi ba ya shige tsarariyar motarsa ™irarar lexus ya harba titi tafiya yake cike da nishaWi yana jin inama Wauko ta zaiyi ta dawo gidansu ai da abin yafi armashi amma bazai yarda a jima ba'ayi biki ba , duk cikin zuciyarsa yake wanan batun , yana zuwa ™ofar gidan ya faka motarsa tare da ciro wayarsa ya danna number yaya Zakari , yaya Zakari dake bacci bai ma san ana kiran ba anty Fiddausi ce ta tashesa ta mi™a masa wayar , bai duba mai kiran nasa ba ya amsa , sallamar da yaji anyi ne ya tabbatar masa da mai kiran duba screen Win wayar yayi yaga sunan da yasa no. wlkslm yaya Zakari yace " ina yini ya iyali , lafiya yaya yace " yana jiran abinda zai kuma cewa " Aisha na gida ne ? bata nan yaya Zakari ya faWa muryarsa babu yabo babu fallasa , nunfasawa Khamis yayi yasan dawan garin yace " to na gode ya ja motarsa ya dawo gida , yana shigowa ya tarar da Ammi zaune da jarida a hanunta , tana ganinsa ta mi™e tare da cewa " lafiya my son? murya kamar ta mai shirin kuka yace " Ammi wanan brothern nata ya hanani ganinta pls Ammina ki temakeni , da kallon tausayi Ammi ta bishi tasan wanan lamarin banda ™addara da ta riga fata ina Khamis ina Aisha anguwarsu ma abin kallo ce ga Wanta kyakyawa ´an mata na rubibinsa amma ya Sige da ´ar ficika , janyo hanunsa tayi ta zaunar tare da cewa " come down my son kabi komai a hankali mai ha™uri zai ci riba ina lefin kabar yarinyar nan ta gama secondary in yaso sai kaji power zuwa gurinta , no Ammi dan Allah kice susa rana tunda sun amince , zaro ido Ammi tayi cike da tsoro take kallonsa ikon Allah Ammi ta faWa a fili kai kuma kalar taka soyayyar kenan ? kwata kwata bakajin kunyata ?" rufe ido Khamis yayi yana cewa " my lovely Ammi ayimin afuwa bana sanin lokacin da nake surutan suka sa dariya dukkan su , Ammi wa zaki tura maganar tambayowa ? kawunka na anguwar rimi mun fara waya dashi jiya , wow my Ammi kina sona , ya wuce bedroom Winsa cike da farinciki , sbda duk wanan Sacin ran da ya dawo dashi ya goge , faWa bed Winsa yayi kamar ™aramin yaro ya fara tsalle harda rera wa™a , kin zamo farinciki na, masoyiya ke nake soo..lol.
Anty Fiddausi dake kan kujera a zaune ta sakko ta zauna kusa da yaya Zakari tace " my blood waye yake kiranka kwana biyu ? naji sai ka dinga cewa"batanan waye bata nan? mi™ewa yayi daga kwanciyar da yayi , ya bata labari tundaga haWuwarsa da Khamis har zuwanshi na yau, dan ™ari anty Fiddausi tace " Aisha yarinya ce ™arama bugu da ™ari batasan halin rayuwa ba taya za'ace za'ayi maganar aure ? hmm Khamis yace " batare da ya ™ara kula zancen ta ba.
Washe gari ™arfe 10:am kawun Khamis ya iso , Ammi ce tayi masa kwatancen anguwar ba tare da Sata lokaci ba driver ya kaishi kasancewar ya bar motarsa a nan gidan , suna isowa anguwar ya tura yaro acewa mai gidan yayi ba™o , yaron ne ya fito tare da cewa" wai yana zuwa ,to kawu yace " ya jingina jikin mota , fitowar malam ce ta sashi faWaWa fara'arsa ya mi™awa malam hannu suka gaisa , nine wan mahaifiyar Khamis ,washe ha™ora malam yayi kana yace " mu shiga daga ciki , malam na gaba kawu na baya suka shige , gidan shiru mama bata nan hakan yasa malam hamdala na zai zartar da hukunci cikin sau™i , bayan malam ya shimfiWa tabarma suka sake gaisawa , kawu yace " maganar yara ce ta kawoni Khamis yaga Aisha yana so muna ro™on arzi™i da a yanke mana dukiyar aure bamason bikin yaja lokaci , masha Allah malam yace " banason yi mata auran dole amma bari zuwa gobe shi yaron yazo suga juna zansa yau a kawota , to kawu yace " ya yiwa malam godiya tare da ajiye masa kuWi masu yawa ya fice , kawu na fita malam ya tura kuWin a aljihu ya nufi Wakinsa , wayarsa ya Wauka ya danno lambar yaya Zakari , da mamaki yaya Zakari ke kallon mai kiran yaushe rabon da malam ya kirasa Allah dai yasa lafiya ba jikin mama bane , gudun karta tsinke yasa shi kamawa tare da sallama , bayan malam ya amsa yace " maza ka kawo Aisha gida yau , gaban yaya Zakari ne ya yanke yana tunanin baya wuce wanan mai nacin kuma malam a ™arfin halinsa sai yace " zai yiwa Aisha aure yanzu , malam suna makaranta fa , faWa malam ya fara yana cewa " ni ban isa dakai ba kenan dahar zan gaya maka magana kayimin kunnen uwar shegu , zan kawota yaya Zakari ya faWa , kashe wayar malam yayi ya fara zance shi Waya , zanga samu inga rashi fitinaniyar yarinyar ashe mai ™ashin arzi™i ce wlh bazanyi wasa da wanan damar ba muddun ina nunfashi, mi™ewa yaya Zakari yayi ya nufi Wakin su Aisha samunta yai zaune sun haWa kayan wasa sunayi , da kallo ys buita na tausayi can yace " Aisha Wauko hijabi kizo Ummi kema taho kuje gida inaga kwana zakuyi , Aisha ce ta kalli fuskar yaya Zakari tace " lafiya dai yaya ?" eh lafiya yace " mata ya juya ya nufi mota , suna shiga suka fara tsalle a dole zasu gida, cikin ™an ™anin lokaci sai gasu a ™ofar gidan su da sauri suka buWe ko wacce tayi gidansu cike da murna , lokacin mama ta dawo , sallama Aisha tayi ta faWa jikin mama tana cewa " mama ai nadawo kenan na gaji da zaman gidan yaya , dariya mama tayi tace "oh nikam mai ake yimiki ne bakida dama Aisha , ina malam Aisha tace " tana kallon ™ofar Wakinsa , bayanan mama tace " koda na dawo ban samesa ba , taSSa barin le™a Aisha ta mi™e ta nufi Wakin malam, hangoshi tayi zaune kan tabarma yayi nisa da ™irga kuWi baima san tana tsaye ba , a hankali Aisha ta koma ta kirawo mama , mama bata Wauka wani abin bane ta biyo Aisha suka le™a Wakin , Wago kan da malam zaiyi sukayi ido biyu , na shiga uku malam yace " yana kallon Aisha hanyarki da sheda inkikazo sai kin Satamin rai banda dole mezai sa in sa azo dake , kekuma ya nuna mama , meya kawoki ? taSe baki mama tayi ta juya batare da ta bashi amsa ba, dariya Aisha tayi tace " aheeee malam ka fiya son kuWi inka mutu Wakinnan zan shiga inyita kuka kambun uba wlh yarinyar nan kin rai nani babu abinda zai hana banyi miki aure watan gobe ba , dariya Aisha ta kuma sawa tace " wlh da naji daWi , ware ido malam yayi daganan yaja baki yai shiru gudun kar bakin nasa yaja masa matsala , mama dai na jinsu bata maida zancen nasu gaske ba , ta fara haWa wuta sbda Wora abincin dare,
™in shiga gidan yaya Zakari yayi ya juya zuwa gareji , yana tafiya sai ga motar Khamis tayi parking Allah baisa zasu haWu ba , amma Khamis Win ya gansa , yaro ya aika yace " masa kace ana sallama da Aisha ,sai da yaron yasa dariya kana ya shige cikin gidan ya faWi aikan , malam dake Waki yace " kace tana zuwa , mama zatayi magana malam ya dakatar da ita yace " babu ruwanki irinku ne masu toshe hanyar alkairi maza Aisha fito kinyi saurayi , da gudu Aisha ta fito tare da rufe fuska tana dariya tana tsalle a dole ta girma , maza kije Khamis ne yazo ina jiranki zamuyi magana , a'a malam ya za ayi ka tura yarinya kamar Aisha gurin mai mota ? duniyar nan fa ba abin yarda bace , to malama kicigaba da yimin wa'azi shine fa mijin da zai aureta banison shishigi da ba™in ciki , saboda kinga kaf zuri 'arku bakuda attajirai shine Allah ya kawo mana har gida kike neman gurguWewa maza Aisha ta jeki Allah ya dawo min dake lafiya, a guje Aisha ta fice ta nufi waje ganinshi da ita sau Waya amma zai iya ganeta , Aisha Khamis ya ™wala mata kira , turo bakinta na tsiwa tayi tace " dallah malam kaine me kirana ? eh Khamis yace " yana murmishi , shigo man yace " mata tare da buWe murfin mota , yasin bazan shiga ba kalan ace min ´ar iska kome zaka faWa ka faWa ni banason gulma , zaro ido Khamis yayi yana mamakin surutu irinna Aisha , to my Aisha ina sonki kina sona ? Khamis ya faWa tare da ™ara sakar mata murmishi , tsayawa kallonsa tayi sai yanzu ta tuno inda ta gansa , oh ashe kaine wanan baturen kai gaskiya kanada kyau sosai , daWi ne ya kama Khamis ya shafa sajensa yana jin ™aunar Aisha na shigarsa, Ammi na tace " in gaishe ki , ina amsawa Aisha tace " tana kallon fuskarta ta mudubin motarsa ,baki bani amsa ba Aisha na , wlhi ina sonka sosai ma tahau tsalle kaine na shirin fim Win da muka kalla jiya ka iya tsalle kana ta kaiwa wasu naushi tana shirin naushinsa ya kauce tare da sa dariya , ga chocolate Ammi tace " in kawo miki , da dariya Aisha ta karSa tace " na gode rabona da inci tun sallah da mukaje muka samo kuWi yaya ya karSe ya siyo mana , dan Allah kace ina gaisheta sosai zanzo gidanku amma inhar zata yimin wainar fulawa da Wanta malele, dariya yasa yace " meye wanan ? ni banma san sunansa ba amma naga Afnan na yin wainar fulawa , aiko na fasa zuwa Aisha tace " tana tafa hannu , gyara ri™on ledar tayi tace " ka tafi gidanku inma jira kake in baka baza kaci ba , ta faWa tana hararar sa shiko dariya ma ta basa ya dinga ™yal™yalewa ,Allah na ganoka irinku ´an sa rani ne Aisha ta faWa tare da shigewa gida da gudu tayi masa gwalo,
shikam wanan nishaWin da Aisha ta sanya shi yau zaiyi bacci mai daWi tare da mafarkinta , ya daWe a tsaye daga ™arshe ya tada mota ya bar anguwar , driving yake cike da nishaWi , yana isa gida yai horn mai gadi ya buWe tare da Waga masa hannu , mi™awa mai gadi 1k yayi cikin rawar jiki mai gadi ya dur™usa yana yi masa godiya , batare da ya kulasa ba ya nufi ciki yana jefa keys Win hanunsa yana cafewa, da sallama ya shiga palon yana cewa " my Ammi am very happy suruka ta amince Ammi na kina ina ya hau dube dube.....!


*godiya nake masu comments karkuga bana kulaku ina ganin irin soyayyar da kuke nunamin iya wuya ana tare>Øİ*



*MOM ISLAM*
[14/07, 8:21 am] Mom Islam Ce=؃Ü: *YARINYA MAI TAARGAZA*





*Zainab Habib [Mom Islam]*



*Wattpad @momislam2020*


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*


*Page 50 _51*

Da sauri Ammi ta fito fuska cike da fara'a tace " masha Allah yarona yayi farinjini kai amma fa naji daWi , kace sai maganar sadaki da sa rana , tsalle Khamis ya buga yana rawa da gudu ya ruga Waki yana cewa Ammi am so sorry nayi rawa a gaban ki , murmishi Ammi tayi sbda farincikin Wanta shine burinta , koda kawu yazo gidan su Khamis ya faWawa Ammi abinda malam yace " Ammi ce tace " ai yanzu ma ya dawo bai daWe da fita ba ka shigo sun dai daita , ok tom masha Allah kawu yace " sintiri fa ya gammu dole mu zage yanzu gidan zan kuma komawa , godiya Ammi tayi masa ya fice , kai tsaye gidan su Aisha kawu ya koma , sawa yayi yaro yayi masa sallama da malam fitowa yaron yayi yace " wai ga shinan , malam na fitowa ya hau washe baki yace " wa kawu ya shiga , kawu na shiga sai ga baban Ummi nan ya shigo nan aka gaisa , malam ya kira Aisha cikin zumuWi tazo ta zauna tana wasa da ledar dake

Please Login or Register in order to submit comment