Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hanunta , kallonta baban Ummi yayi yace " kina son Khamis ?" juyawa tayi ta kalli mama , mama da batasan Aishar na kallonta ba.
Tambayarki muke kinyi shiru , eh Aisha tace " idanunta a na baban Ummi , mamaki da tsoro ya cika zuciyar baban Ummi amma babu halin magana tunda iya abinda ya kawosa shi zaiyi ba shida ta cewa " sbda tsoron azabar faWan malam , ganin Aisha yasa kawu zaro ido cikin ransa yace " dama wanan Wan nawa yake so innalilahi wanan wace irin jaraba ce ?" bai bari zancen ya fito fili ba ya ce " to yanzu maganar dukiyar Aure fa , baban Ummi ne yace " kubada dubu Wari ,badan malam yaso haka ba ,a nashi inda shine dubu Wari biyar zai ce gaskiya an kwafsa masa , ya haWe rai , kawu ne ya dire kuWin a gurin sai da aka ™irga dubu Wari huWu ne sukayi wa Allah godiya nan fa malam yaWan fara murmishi , kasancewar Aisha ta wuce Waki yasa kawu cewa " munason asa rana dan Allah bamson akai da nisa , to to malam yace " kana ya kalli baban Ummi ka gaya masa man ,malam yace " baki na rawa a'a malam baban Ummi yace " abi komai a hankali zuwa ™arshen wanan watan a sa ranar kafinnan ´an uwa sun hallara , tunda bazakayi magana ba ni inada bakin magana innasa ´an uwan zasu canza ne ?" malam ya tambayi baban Ummi , shiru baban Ummi yayi dama yasan kafin a tashi dole sai sunyi faWa sbda malam akwai ™in shawara ,ansa biki wata biyu masu zuwa malam ya faWa ranshi fess , masha Allah kawu yace " ya mi™e yana jaddada godiya a garesu yai musu sallama , kawu na tafiya baban Ummi ya mi™awa malam kuWi tare da yi masa Allah ya sanya albarka , amin malam yace " tare da godiya ya tattara kuWi ya mi™e , ficewa baban Ummi yayi zuciyarsa babu daWi, yana shiga gida ya samu maman Ummi zaune a tsakar gida tana tsinke alaiyyahu , sallama yai ta amsa Wago kan da zatayi taga fuskar tasa kamar ta mai shirin yin kuka , lafiya baban Ummi na ganka haka ? inafa lafiya ankawo sadakin Aisha.zaro ido maman Ummi tayi tace " sadaki fa kace wanan Aisha tamu? eh itafa caS amma babu wanda yafi ganganci fiye da malam , hmm baban Ummi ya nisa kana yace " banda yaga ruwan kuWi wanan ai bai dace ba sam , to Allah ya kyauta aikin gama ya riga ya gama tunda gashi har ansa rana , mamaki da tausayin yarinyar duk yabi ya kama maman Ummi ba komai take dubawa ba sai ™an™antar shekaru Allah ya tabbatar da alkairu maman Ummi tace " cikin sanyin jiki .
Le™a Wakin mama malam yayi ya samu tana kuka iyeee ´ar ba™inciki kukan me kike arzi™i yazo mana har gida kuma nasan zakifini morarsa tunda tafi sonki , Aisha da keta jijiga mama tana jin kalamin malam ta kallesa tace " wlh zance na fasa tunda abin haka ne , ubanki nace " dan gidanku ko nine nace an fasa ai nayi ™aranta wlh ko da wasa ,share hawaye mama tayi tace " a gaskiya malam baka kyauta min ba , baka duba nima inada ha™™i a kanta ba ka zartar da hukunci amma sai naga kamar ana shawara kafin haka , ungo dubu ashirin kisi wasu abubuwan nikuma zanji da kayan gado da katifa da kujeru , babu inda mama ta iya haka ta karSi wanan kuWi zuciyarta na tafar fasa inalillahi take mai maitawa ,ganin mama ta™i dena kuka yasa Aisha sakin kuka tace " mama in bakiso nima baniso kidena kuka kinji , babu komai Aisha Allah yayi shine mijinki karki damu duk abinda Allah ya ™addara babu makawa sai ya faru , ta rungume Aisha . shidai malam da ya gama surutunsa ya fice dan tunda mama ta gama faWa masa lefinsa ta barshi tsaye kamar gunki.
Washe gari 8:am kawu ya iso gidan Ammi , Ammi na ganinsa tace " oh yaya munsaka Wawainiya , murmishi kawu yayi yace " ai yiwa kaine karki damu , kinsan jiya naje gidan su yarinyar da Khamis yake nema ,mun gama magana na bada sadaki anma yanke ranar wata biyu , farinciki fal zuciyar Ammi ta dinga yiwa kawu godiya tare da yi masa fatan alkairi , hirar su ta ´an uwa suka shiga yi bashi yabar gidan ba sai sha biyu bayan an zubo masa abinci yaci.
Anty Fiddausi ce a kan cinyar yaya Zakari tana zuba masa shagwaSa amma sam hankalinsa baya gurinta , lura da hakan da tayi ne ta sa masa kuka tare da cewa " kwana biyu baka kula da ni shiyasa nace banison ciki amma ka™i yarda da magana ta ,yasan duk rigima ce takeso da shi shikam a halin yanzu hankalinsa yayi gida yanaji a jikinsa mama bata cikin kwanciyar hankali , kiyi ha™uri Fiddy ba haka bane banajin daWi ne, ina iya bakin ™o™ari na gurin ganin na sakaki farin ciki kiyimin uzuri zani gida dubo mama yanzu zan dawo, ru™osa tayi tana cewa " haba mijina nikam banison kayi nisa dani , afuwan insha Allah yanzu zan dawo yaya Zakari ya faWa tare da haWe hannayensa , to Allah ya tsare anty Fiddausi ta faWa cikin murya mai shirin kuka , amen yaya yace " kana ya fice bai tsaya Waukar motarsa ba ya hau mashin ya gaya masa anguwar da zai kaisa , kasancewar anguwar batada nisa cikin lokaci ™an™ani suka iso , kuWi ya ciro yaba mai mashin Win ya shige gidan nasu da sauri , ganin mama da maman Ummi a zaune yasa shi dur™usawa ya gaishe su , amsawa sukayi cike da kulawa maman Ummi ta mi™e tana cewa " mama Allah ya rufa asiri , amen mama tace " ta kalli fuskar yaya Zakari , lafiya dai na ganka kamar baka cikin nutsuwarka ? lafiya mama meke faruwa a gidannan? me ka gani ? cewar mama gabana nata faWuwa tun Wazu any kuwa lafiya ?" uhm mama tace " lafiyar kenan ashe kaima mahaifinnaka baiyi shawara da kai ba , shawarar me kuma mama ?" yaya Zakari ya faWa , gyara zama mama tayi tace " ka nemi guri ka zauna da sauri ya ja kujera ´ar tsuguno ya zauna yana kallon mama , ansa ranar auran Aisha ,a fusace yaya Zakari yace " aure kuma ? wanan wace irin rayuwa ce ? wlh nasan hakan zata faru menene riba a aurar da Aisha ? sekace mun gaji da ita ?" babu neman shawara haka ya yanke hukunci itama ai Aishar duk da ita Wazu fa da mai bin maganar auran yazo aka tambayeta cewa " tayi tana sonsa , tsaki yaya Zakari yaja kana yace " mama Aisha guda nawa take batasan komai akan so ko ™i ba gaskiya ba'ayi mata adalci ba,
uban adalci ne ba'ayi mata ba kanada hankali kuwa ?" har zan faWi magana ku zauna kai da uwarka kuna neman warwarewa to wlh baku isa ba sbda nayi istahara auransu alkairi ne dan haka babu makawa sai anyi aurannan ,malam ya faWa yana shirin shigowa , buWe baki yaya Zakari yayi zai yi magana mama tayi masa alamar yai shiru , mi™ewa yayi idanunsa na fitar da ™wallah yace " mama zan tafi sai gobe cikin rashin jin daWin yanayin da yake ciki mama tace" ka kwantar da hankalinka insha Allah komai yai tsanani maganinsa Allah adu'a zamuci gaba da yi mata ,tom kawi yaya yace " dan magana ma bazata yiwu ba ya fice , ya daWe a kofar gidan zaune yana ri™e da kai ya rasa meke yi masa daWi ina zaisa kansa , ciwon kan da yaji ne yasa shi runtse idonsa ya mi™e tare da shiga gidansu Ummi yace " ta fito su tafi maman Ummi dake kitchen tana girki tace " yau baza'a da Aishan bane?eh banma ganta a gidan ba , da sauri Ummi ta janyo hijab Winta a jikin igiya ta ri™o hannun yaya suka fito ™ofar gida ya tari mashin , suna isa anguwar suka sauka tare da bawa mai mashin kuWinsa suka shige gida , da shigarsa ya samu anty Fiddausi na kitchen tana soya doya da ™wai Fidy zo man Ummi jeki karSa mata aikin , to anty Fiddausi tace " ta mi™e da Wan cikinta da zai kai wata uku ta nufi Waki , da shigarta ta gansa zaune ya haWa kai da guwaiwa hawaye na zuba a fuskarsa , salati ta fara mekuma ya faru ?"anty Fiddausi ta faWa tana shirin tayasa kukan , wai Aisha ce za'ayiwa aure nanda wata biyu wanan wane irin hukunci ne ? aure kuma ? dai dai kaji kuwa ?"anty Fiddausi ta faWa tana zaro ido , eh man shiyasa tun safe nake jina babu lafiya amma wanan yaron shima ba ™aramin sakarai bane , ubanme zaiyi mata inhar ya aureta anya malam yayi tunani kuwa ?jinjina kai anty Fiddausi tayi tace " tunda anriga an yanke hukunci sai dai mu tayata da adu'a .
Tunda Khamis yaji wanan kyakyawan albishir Win yake ta zumuWi kaf abokansa ya basu labarin auransa sunma koma ce masa na Aisha.
Kasuwa Ammi ta tafi ta siyo akwatuna masu tsada daga ganinsu ma zaka sheda hakan ga wasu kaya da taje jida harda su breziya tofa , atamfofi kam babu na ™aramin kuWi kashe kuWi Ammi takeyi kamar bata san zafinsu ba , ga kayan makeup data haWa a babban akwati akwatunan zasukai kala goma sha biyu , duk da haka ma bata gama siyan kayan ba .
Ni™i ni™i suka dawo da kaya cikin both haka drivers da masu gadi suka dinga shiga da kaya , Khamis da yayi shirin zuwa anguwa jin motsin shigowar Ammi yasa shi dakatawa oyoyo my Ammi ya faWa lokacin da ta ™arasa shigowa, da dariyarta tace " ango ango dariya masu shigoda kayan sukayi tare da cewa" Allah ya sanya alkairi , amen Ammj tace "suka koma bakin aikinsu , zoka gani ba'a gama siyayyar ba ma , inason momyn Afnan tazo gobe muga abinda babu , zama Khamis yayi yana ™arewa kayan kallo cikin farinciki yace " Ammi baza'a ™aro akwatunan ba kuwa ? no a barshi haka amma dai a ™ara yawan kayan Ammi ta faWa tana murmishi......!


Masu yimin magana ta PC karku Wauka wula™anci ne pls adinga yiwa juna uzuri some times post da typing nake kawai afuwan =ĜOÜ.



*MOM ISLAM*



[19/07, 3:29 pm] Mom Islam Ce=ĜƒÜ: *YARINYA MAI TAARGAZA*



*Zainab Habib (Mom Islam)*


*Wattpad @momislam2020*


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*


*Page 52-53*

Harma ya hango ranar auran su kasancewar in zaiyi misali yana ajiye Aisha a matsayin babbar mace , Ammi ni zan fita Khamis ya faWa, to a dawo lpy my son , Ammi taci gaba da duduba kayan sbda taga abinda babu .
Washe gari tun safe Afnan da momynta suka iso kana ganin fuskar Afnan kasan bata cikin kwanciyar hankali ,a palo suka yada zango ´ar aikin gidan ta cika gaban su da kayan ciye ciye , fitowa Ammi tayi cike da farinciki ta dubi momyn Afnan tace " munata shirye shirye ,dariya momyn Afnan tasa tana cewa" munada bidiri ai zuciyar Afnan kamar an buga mata guduma tsabar ba™inciki da tasan wanan maganar zata zo ta tarar da batayi gigin zuwa gidan ba , amma tunda ta faWa wa momynta dalilin dawowarta gida babu damuwa komai zai dai daita amma tasan akwai ™ura a gaba sbda koda sau Waya Khamis bai taSa nuna alamun kulawa da ita ba .janyo akwatunan momyn Afnan tayi ta fara duddu ba kayan kasancewar Ammi tabar gurin yasa Afnan matsowa tace " wlh momy wanan kayan ba ™aramin kashe kuWi sukayi ba ,hmm momyn Afnan ta nisa tare da cije leSe tace " wanan uban kaya kamar wacce ta fito daga gidan wani hamsha™i? indai ko ina nunfashi sai kin auri Khamis wlh wanan al™awari ne na Wauka . farinciki na ya baiyyana a fuskar Afnan ,jin motsin tahowar Ammi yasa su yin shiru sukaci gaba da duba kayan ,Ammi na isowa momyn Afnan tace " oh my sister kinyi aiki fa Allah ya sanya alkhairi amen Ammi tace " kana ta nemi guri ta zauna sukaci gaba da tattauna abinda zai wakana.
Washe gari da yamma Khamis ya shirya zuwa gurin Aisha wani lallausan yadi ya sanya mai tsadar gaske wanda ya fito da ainihin kyansa gashin kannan yasha gyara hannayesa suna Wauke da tsadaddun zobuna wa inda suka ™ara ™awata kyansa fitowa palo yayi yana ™walawa Ammi kira , da sauri Ammi ta fito tana washe baki tace " kai my son karfa kasa Aisha tace " da wancan da wanan akwai ban banci suka kwashe da dariya , Ammi sai ma ranar da na kai mata chocolate kinga murna harda rawa cemin take wai balarabe , dariya Ammi ta ™ara sawa tace " ai kana kama dasu shiyasa , to Ammi ayi min adu'a zan tafi hira ,ya rufe fuskarsa , cike da kulawa Ammi ta dubesa tace " my son Allah ya tsaremun kai a duk inda kake. amen Ammi Khamis ya faWa kana wuce, kai tsaye parking spice ya nufa ya Wauki motarsa ya fice yana jin wani farinciki , driving yake yana murmushi shi kaWai yasan inda yake ji a ransa , yana isowa unguwar yai parking a ™ofar gidan su , yaro ya hango da bazai wuce sa'anta ba ya aikesa ya kira masa Aisha , bayan yaron ya shiga bai kai ga cewa " komai ba sai gata ta fito da uban gudu ta rungumeshi , dariya yaron yasa yace " Aisha wanan Wan uwanku ne? dariya Aisha tasa tace " kai wanan saurayi na ne baka ganshi kamar balarabe ba ,shidai Khamis na tsaye yana jin hirarsu hanunsa a na Aisha gyaWa kai yaron yayi tare da cewa " kinji daWi natafi aikana ya wuce " da gudu , ko ka goyani kokuma in koma gida wlh ,Aisha ta faWa tana cuno baki , murmishi Khamis yayi da har dimple Winsa ya loSa yace " my Esha zan goyaki amma ba yanzu ba ko kinaso mutane suyi miki dariya? girgiza kai tayi tace " to ina tsaraba ta , bugar goshinsa yayi da tafin hanunsa alamar mantuwa ya dai daita nutsuwarsa da cewa" zan siyo miki amma gaya min me kikafi so , alewa da chocolate da tuwon madara ,Aisha ta faWa tana tsalle ,tsayawa kallonta yayi yasan she is very young amma a hakan yake da bu™atarta , tana ta surutanta bai kulata ba dan bai san tanayi ba , taSosa tayi tana cewa " balarabe ciromin waccan ´ar bebin ta cikin motarka , sai a lokacin yaji abinda take cewa" taSS Khamis ya faWa a cikin ransa , me zakiyi da ita? wasa harda goyo kuma in Winka mata kaya , dariya Aisha ta basa dan har ga Allah tana sashi nishaWi , le™awa ta cikin motar yayi ya ciro mata babyn ya mi™a mata ,tsalle ta doka tace " kai balarabe ina sonka sosai ta rungume babyn , wani daWi ne ya kama Khamis a dole kalmar so ta fito daga bakin masoyiya, rugawa gida tayi da gudu ta le™o tace " balarabe in zaka sake zuwa ka taho min da kayan ´ar bebi dan Allah ta ™ara da gudu , ya daWe a gurin yana dariya daga ™arshe ya tada motarsa ya bar anguwar.
Tunda Ummi ta koma gidan yaya Zakari kewar Aisha ke damunta shiko yayan kwata kwata Aisha ta fice masa daga ransa.
Yunwar da ta addabeta ne yasa ta fita kitchen dan bataci abincin dare ba , ™wai ta fasa har guda goma ta tsiyayo mai da maggi da albasa ta hau suya , lokacin yaya Zakari da anty Fiddausi na zaune tana kukan amai ya dameta , jiyo ™amshin suyar ™wai yasa ta tashi daga zaman da take tace " itafa ™wai zataci kuma soyayye, ya fara jin bacci ya fito ya nufo kitchen Win jin kitchen Win ya gaure da ™amshi kuma na ™wai yasa shi dube dube kuma gashi risho da zafi , bai gama shan mamaki ba har sai da yaga babu ™wai ko guda Waya alhalin yasan jiya da ragowar guda goma , a hanzarce ya dawo Wakin anty Fiddausi haskata yai da fitilar wayarsa kasancewar yanzu suka Wauke yace " naga babu ™wai fa ina aka kai ?" wlh ban sani ba nikam, ni da nake Waki kwance ko fitowa banyi ba , mamaki ne ya kuma kama yaya yai ™wafa yace " koma dai menene wataran Allah zai haWani da mai satar nan .
Ummi na Waki zaune ta sa tiren ™wai tana ci tana gyWa kai daga Wakin tana jiyo surutun su yaya amma tayi burus , sai da ta cika cikinta fam sanan ta tura ragowar gefen jakarta , goge hanunta tayi da zanin gado ta haye ranta fesss bacci mai nauyi yai awon gaba da ita.
Washe gari Ummi sai fama da tusa take da ta zauna zataji tusa ,suna zaune da anty Fiddausi taji wani uban wari ,toshe hanci anty Fiddausi tayi tace" haba Ummi kamar kinci ™wai? wuli wuli da ido Ummi ta shiga yi tana shirin tashi ankara da alamun rashin gaskiya yasa anty Fiddausi lura da ita , zo nan anty Fiddausi ta ™wala mata kira , ™in zuwa tayi ta Wauki buta tare da shigewa bayi , tana shirin yin fitsari taji gudawa ta taho , zaro ido Ummi tayi tana cewa" na shiga uku wlh na mance ™wai na sani gudawa , kuka ta fara a bayn gida tare da cewa" yanzu wazai siyamin maganin kashi ?" haka ta mi™e ta ji™e da zufa tayo waje ,anty Fiddausi dake zaune bata tashi daga inda take ba ta daka wa Ummi tsawa , a firgice Ummi ta saki tusa tana jin gudawa na shirin zubo mata tayi bayi da gudu tana kuka , dariya ma abin yaso bawa anty Fiddausi hakan sai ya tuno mata da nasu kashin da sukayi , ganin shiru shiru Ummi bata fito ba yasa anty Fiddausi mi™ewa ta nufi Waki ta kwanta .
Washe gari .
Zaune Aisha take ta haWa kayan wasanta da ™yallaye tana yankawa da reza , mama dake zaune kusa da ita ta girgiza kai dan tana tausayin Aisha kasancewarta yarinya ™arama , lafiya mama kike kallo na ?" Aisha ta faWa tana yiwa ´ar bebinta rawa , lafiya Aisha mama tace " kana ta mi™e hawaye na zuba a fuskarta ta nufi Waki.
Aisha taga kukan da mama ta keyi bata bita ba ta cigaba da zama har shigowar malam , kasancewar yanzu malam basa faWa da Aisha , yawwa malam ga mama can a Waki tana kuka na tambayeta tace " wai tsire takeson ci , Aisha ta faWa tana jujuya ´ar bebi , zaro ido malam yayi kana yace " tsire ko to inma sawa kuWina ido takeyi tun wuri ta fasa dan wlh ba kuWin banza gareni ba , dariya Aisha tasa tace " malam wasa fa nake maka , kinci gidan ku malm ya watsa wa Aisha da™uwa , turo baki Aisha tayi tace " amma fasa auran bazan aureshin ba ta murguWa baki , tsugunawa malam yayi cikin muryar lallashi yace " habba Aisha na karki ™ara faWar hakan banaso zomuje in siya miki tsire kici , da sauri Aisha ta mi™e ta nufi gurin malam ya ri™e mata hannu suka fice , da fitarsu waje wasu tsofaffi suka fara gulmar su malam suna cewa " wlh auran jari zeyi mata dubi ´ar yarinyar da zai aurar taS ,karab a kunnen malam amma burinsa kar Aisha taji duk da ba lallai tasan ko me suke nufi ba , haka dai suka wuce zuciyar malam babu daWi ya nufi gurin mai tsire , Aisha ta mance da sun taSa zuwa satar tsire ita da Ummi, gaisawa malam sukayi da Lawali bayan ya amsa yace " malam kazo siyan tsire ne ?" eh malam yace " na Wari biyar zaka bani jikin lawali na rawa ya fara zuge tsire ,hango Aisha da yayi ne yasa shi tsayawa yana nazarin kamar itace tayi masa sata ita da wata yarinya , tabbas ita ce lawali ya faWa a fili , sarai Aisha ta gano komai amma batada damuwa tunda akwai malam , malam wanan Wiyarka ce ?" Lawali ya tambaya eh malam yace "yana washe baki masha Allah Lawali ya faWa yana yiwa Aisha kallon inna ri™e™i zakisha wuya, bayan Lawali ya gama sawa malam ya mi™a masa , kuWin malam ya basa kana suka wuce , suna isowa gida malam yaba Aisha leda Waya yace " ´ar albarka kici ki ™oshi ki samma mamanki Wan kaWan , ma™e kafaWa Aisha tayi tace " nidai ni kaWai zanci ka bani in kai mata a naka ai inaji kace wa Lawali ya sa naka da yawa , zaro ido malam yayi yace " duk wanda ya aureki wlh ya aurarwa kansa sai kuma yai shiru , mama da ta fito domin Wora girki ta gansu da leda a hannu , ko saurarar su batayi ba tunda Aisha yanzu ba jin maganarta takeyi ba , ko yazo bazan fita ba yasin Aisha ta faWa tana cuno baki , ganin abin zaiyi masa yawa yasa malam shigewa Waki yabar Aisha a gurin.
Ummi ta gala baita bata ma iya fitowa wunin ranar yaya Zakari a gida yayi shi kasancewar baya jin daWi sosai , lura da rashin jin motsin Ummi yasa ya le™a Wakin nasu , ganinta yayi kwance rufe da bargo sai rawar sanyi take ga wani uban wari da yayi masa sallama , innalilahi Ummi Ummi ....ya kira sunan ta da ™arfi , shiru bata amsa yasa shi shafa fuskarta jikinta yayi sanyi ga wani irin nunfashi da take fitarwa da sauri ya fice ya nufi shagon siyarda magani na nan anguwar tasu ya kira mai chemist Win , tare suka taho cikin sauri suna shiga ba'a tsaya Sata lokaci ba aka sanya mata drip, bayan yasa magunguna a ciki yayi wa yaya Zakari sallama yace " in ya ™are ka kira number ta , to yaya Zakari yace " jiki a sanyaye , fitowa anty Fiddausi tayi ta nufo Wakin ranta a Sace babu ko sallama ta bankaWo labule tana ™arewa yaya Zakari da Ummi kallo , cikin masifa tace " andai ji kunya ka rasa wacce zaka so sai ´ar cikinka , da mamaki yayan ke kallonta dan da farko bai fahimci me take nufi ba amma yanzu kam ta fahimta , ki nutsu Fiddausi , bazan nitsu ba kazo ka Worata a cinya kamar wata matarka koni ynzu baka yimin haka , anty Fiddausi ta faWa tana ri™e da ™ugu , dariya ma taso bashi banda hauka da yarinya ´ar shekara goma sha Waya za'ayi kishi aiko sai da ya dara ya kwntar da Ummi yaja hanun anty Fiddausi sukayi waje , kai tsaye Wakinsa ya nufa da ita ya zaunar da ita kan katifarsa , kina nufin son Ummi nake ko me ?" idanun anty Fiddausi na fitar da hawaye tace " eh man inba so ba ai naga ko shiga Wakinsu bakayi , shitttt....ki fahimceni badan larurarki ba babu abinda zai sa na Wauko Ummi tausayinki da nake ji yasa hakan me zanyi da Ummi ? ki kiyaye bana son jin wanan zancen ya ™ara fitowa daga bakinki , kingane ko ?" gallah masa harara tayi ta fice tana magana ciki ciki.....!
[23/07, 8:50 pm] Mom Islam Ce=ĜƒÜ: *YARINYA MAI TAARGAZA*


*SUBSCRIBE*
_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ







*Zainab Habib (Mom Islam)*


*Wattpad @momislam2020*


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*


BOOK 1

*Page 54 -55*

bayan ruwan da aka sa mata ya ™are sai da aka kuma sa mata wani dan ta galabaita sosai , zuwa ™arfe takwas aka cire .bayan yaje ya biya kuWin ™arin ruwan ya dawo kitchen ya Wibi ruwan zafi ya koma Wakinsu ya Wauki lipton da madara da suga ya haWa mata shayi mai kauri ya nufi gurin ta , samunta yayi tana zaune ta rame sosai mi™a

Please Login or Register in order to submit comment