Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

waya difff ya kashe wayar sa


Ta mike kamar mahaukaciya bazai yuyuwa wallahi, wallahi bazai yuyuba ta fashe da kuka mai tattare da bakin ciki da takaici

"Wallahi saina samu abunda nake nema agidan man kota halin kaka ban taba neman abu bansamu ba dan haka zan sake shiri wallahi bazan hakura ba"


"Toooo=Ø(Þaiki ya sameki kuwa munu"....


Taci gayu na fada aji tafito kaitsaye bangaren mum ta nufa suna zaune ita da *FARHA* mum ki gaya mun meya sami dady kinki

Suna cikin haka tashigo dakin farha tana ganinta ta hade girar sama data kasa tamkar bata taba dariya ba ta karasa gunda suke tace mum
Dan Allah zanje gidan kawata najwa jiya ne sukayi bikin zagayowar haihuwarta bansamu naje ba

Hajiya salma tayi murmushi tace kada kidamu munu kije amma kada ki dade kinsan dear baya son yawo

Tana murmushi bazan dade ba

Takalli farha sister ba magana, "farha ta dago tayi mata wani kallon raini tace sai kin dawo"

Yanda ta kalleta sai taji wani iri ta fuskanci farha kanta yana hayaki ba kamar Ashrab ba

"Sai na dawo tace tana yake"

"Mum tace to Allah ya tsare, ki gaida ta, zataji tace tafice daga dakin zuciyarta tana kara hura mata wutar tsanar *FARHA*

tana fita mum tace baby nah na fuskanci bakwa jituwa keda munu meyasa yar'uwar ki ce fah

Tadago mum wallahi bansan abunda yasanya nakejin bana son ganinta akusa da muba tun zuwanta gidan nan naji hankalina yakasa kwanciya da ita

Jikina yana bani kamar akwai wani abu datake boyewa

Dafata tayi tasoma magana ahankali kada ki zargi komai *FARHA* bawani wanda yakeda masaniya akan abunda yake boye sai Allah shi isa nake kyautata zato na akullun dan Haka ki nutsu ki ajiye zuciyarki guri daya kidaina zargin komai kinji ko

domin mazon Allah yasanar damu cewar

Mu kiyayi zato domin shi zato shine mafi karyar zance

Ta daga kanta alamar taji amma fa zuciyarta ta gagara jin zata yarda da munu dan tabbas jikinta yana sanarda ita akwai wani Abu.....

Munu tana fita tasami baba direba yana hutawa tayimasa wani kallon raini muje ma'aikatar Alhaji musaddiq

Yayi mamaki sosai ina kika ce? aikaji kada ka raina mun hankali..
Ya janyo mota ba yanda ya iya... Tashiga tana wani yatsina kamar taga kashi

Suna fita kaitsaye ma'aikatar su Alhaji ta nufa suna isa ma aikatar munu takara rikicewa taga tamfatsetsen guri katon gaske har rawa jikinta yakeyi saboda rudewa

Baba direba yana kallonta yayi murmushi aransa yace indai Alhaji ne kigama abunki yarinya

Tashiga tana tafiya mai jan hankali kusan kowa idonsa yana kanta yanda take tafiyar kamar mai gasar sarauniyar kyau kai tsaye office dinsa ta nufah ba neman izini ba komai ta dannah kanta ciki

Yana zaune ya lumshe idanuwansa sanyi air condition yana ratsa shi yagaji matuka

Kamshin gurin ya canja yaji bai bude idanuwansa ba yasoma magana wayace ashigo mun ba neman izini

Asanina duk dan musulmi yasan mahimmancin sallama dan Haka koma kiyi sallama

Taji kunya sosai ta koma tayo sallama tashigo

Ya bude kyawawan idanuwansa gabanta ya yi mummunar faduwa jikake damm! dammm!! Fatt! Fatt!!

"Alhaji barka da ranah"

Tana ininah jitake kamar zata saki fitsari a wando saboda kwarjinin da yayi mata

Idonsa yana kanta duk sai ta dabar barce inajinki

"Meya kawo ki?"

Nan ma saida hanjinta ya kada

"Ba komai dama nace bara nazoh na gaida ka ne"

"Saboda wane dalili ya katseta?"

"Ba komai saboda zumunci"

Gida daya muka kwana mukayi break a table daya duka bai isaba har sai kin biyoni nan

Ya mike yana tafiya cikin kasaitar sa dan Alhaji musaddiq badai ajiba ko mace albarka

Ya tako har gunta ke!! "yace cikin daga murya ta dago cikin sauri
Ya nuna mata hanya tashi ki fita Alhaji katsaya ka saurare ni dan Allah"

"Babu wata magana dazaki iya sanar dani ayanzu nasan nufinki dan ni ba karamin yaro bane ba na dade da fahimtar manufarki"

"Ki sa azuciyarki ni musaddiq babu wata macenda zata taba tasiri azuciyata kamar Salma, "saboda itace kadai muradin raina itace wacce zuciyata ta Aminta da ita bazan taba son wata ya'mace ba sai ita dan haka ina son ki saka azuciyarki bazan taba sonki ba har karshen numfashi nah dan haka ki tashi ki fice mun",,

Banza marar aji wallahi koda mata sun kare bana tunanin zan soki dan ke ba sa'an tafiya ta bace

Mace irin Salma itace muradin zuciyata kuma zabina ta har abada

Ta mike zuciyarta tana kuna duk abunda zaka ce kace wallahi ina sonka

Soyyayarka tana zagaye acikin jinin jikina bazan iya rayuba matukar zan ganka da wata macen nayi Alwashin sai na dauki mataki kajirah ka gani

Kije kuma kada ki fasa akan hajiya salma raina fansa ne agareta


Har takai kofa tajuyo zakaga abunda zai biyo baya wallahi sai kasan wa kataba

"Ni munubiya ba'a tabani akwana lafiya wallahi! Wallahi!! Wallahi!!!
Sai nayi sanadin ranka nida ita salman dakake tutiya da sonta kowa ma yarasa wannan shine Alkawarinda na dauka"

"Ayau basai gobe ba zaka gani tafice daga office din zuciyarta a matukar fusace...............!!!


Tabdijam=Ø(Þ>ØÝmunu mikike son aikatawa ne?

Allah dai yatsare

Muje zuwa dai

Kuyi manage da wannan bana jin dadi







TAKUCE A KULLUN


LAURAT M BELLO


COMMENT
VOTE




SHARE PLSSSSSSSS



08164949554



=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ



BANGARE NAH
(part of me)


=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ




WRITING BY



LAURAT MUH'D BELLO


DAGA MARUBUCIYAR LITAFIN

SUKHAINAH
AND NOW
=ØGÜ

BANGARE NAH
(part of me)





________________________________


*AREWA WRITES ASSOCIATION*
_________________________________
*=ئÜ{Arewa ginshi™in al'ummah}=ئÜ*
_________________________________

https://www.facebook.com/104534761033461/posts/119016616251942/?app=fbl


*BISMILLAHIR~RAHMANIR~RAHEEM*
*ALHAMDULILLAHI ALAH KULLI HALIN*>Ø2Ý


*jan hankali garemu yan'uwa musulmi duba da yanayin da muke ciki na wannan jarabawar ya ku yan'uwa musulmi mu sani Allah dole ya jarabce mu domin kuwa munkasance masu tsallake iyakokin ubangiji duk wani abu da Allah ya hanemu ayanzu ana aikatashi zinace-zinace yayi yawa shaye-shaye yayi yawa madigo yinsa ake luwadi yinsa akeyi cin dukiyar maraya*
*Tayaya Allah bazai jarabcemu ba yakamata muyi hankali wannan cutar kadai tazama iznah agaremu mukomawa Allah mukiyaye hakokin ubangiji mu yawaita istigifari ga Allah ko zamu samu sassauci agurin Allah domin shine kadai zai tsallakar damu muna tawassali da sunayenka kyawawa Allah ka karemu da wannan cutar ta duniya kayafe mana karamana lafiya ka*
*tausaya mana Allah dan tausayinka ga bayinka Ya Allah kaini Allah muna rokon ka da kokon baran mu ya hayyu ya qayyum Allah ka karemun da wannan cutar kaka re dukanin yan'uwa musulmi baki daya ka kawamana karshe wannan itila'in daya saukar mana Dan dai-daituwar Al-arshinka ya mahaliccin mu AMEEN YA ALLAHU YA RAHMAN WANNAN SAKON TUNATARWANE DAGA YA*



*ASTAGFURULLAH WA'ATUBU ILAI*=Ø-Þ>Ø2Ý *Ameen ya Allah*












<ØÝ<><><><><><><><><><>1ã 1ã é#1ã 2ã







<><><><><><><><><><><><"Idon ta yana kan hajiya da abunda take boyewa sai dai ba abunda take iya hangowa"

Tana shiga doctor yana shigowa hakan yakara dakatar da ita gurin son ganin abunda take son ta hango.

doctor yace hajiya dama jikin yayi tsanin haka eh tace a raunane ya karasa gurinsa yafara dubashi
Ya juyo hajiya da an dan ragu ko, "akwai tanbayoyin da zanyi masa munubiya ta dago karaf tace kaga doctor duk nan we are family so I think you don't have any problem to do what you want to do

Hajiya Salma tace a'a mey be he want do something which is personal da bai kamata wani yajiba
Ya daga kansa upcouse kinsan duba marar lafiya Abu ne na daban kada kuyi mun mummunar fahimta
Farha tace kada kadamu Aunty mu je ko doctor kayi aikinka muje aunty munu tsayuwar me kikeyi tana tsaye so take sai taji abunda yake damun sa dakuma adadin kwanakin da yarage masa ya mutu
Wai tunanin me kikeyi ne ta turata gaba muje nace taja ajiyar zuciya mai karfi tukunnah ta fita daga dakin
hajiya da doctor kowa yayi mamakin tsayuwa ta amma banda Alhaji musaddiq dan shi yagama fahimtar ta tuni, salma tana gefe azaune doctor ya ake ciki

Ya dago a gaskiya hajiya bazan boye miki ba kamar yanda yake boye miki yazama dole na sanar dake Alhaji musaddiq ya dago yana girgiza kansa doctor na gaya maka mubar zancen nan hajiya Salma ta mike wane zance doctor dan Allah idan kasan wani abu game da wannan jinyar ta dear ka gaya mun dan Allah

Yan da ta rude sai ta kara bashi tausayi ya katse ta zan sanar dake amma sai kinyi mun alkawarin bazaki sanar da Iowa ba kuma zaki kwantar da hankalin ki

Ta daga kai alamar amincewa insha Allahu doctor nayi maka Alkawarin ba wanda zai sani ko kuma yaji koda su Ashrab ne....

Yayi shiru kana yace hajiya wannan cutar ta Alhaji tabbas da sahun wani ta waro ido =Ø(Þ kamar yaya ban ganeba yace ina nufin wani ne yake shirya salwantar da rayuwar Alhaji ta hanyar zuba masa guba acikin abinci ko kuma a abun sha

"What" tace da karfi bakinta yana rawa tace waye wannan hawaye suka ringa sintiri akan fuskarta... Likita yace kiyi ahankali shi'isa Alhaji yaki yasanar dake tuntuni yana zuwa asibiti kuma yana karbar magani amma maganar ta gaskiya gubar tayi masa illah sosai saboda ayanda na fuskanta yasha ta sosai batare da yasani ba


Amma insha Allah zamu san abunyi kuma yazama wajibi ki saka ido sosai akan duk wani motsin yan gidan nan da ma'aikatan ku, tabbas mai son cutar daku yana tare daku

Tadaga kai cikin jimami insha Allahu likita za'a kiyaye sosai yanzu likita menene abunyi

Yanisa zan dauke Alhaji zantafi dashi asibitina acigaba da bashi kulawa acan

Kuma bama bukatar vitors saboda dakile koma waye, to doctor to ya maganar jinya kuma? "kada ki damu zan kula da komai"

Wannan ba matasala bace....

Suna fita su munubiya Farha ta janyeta saida suka bar bangaren baki daya tukunah tace Aunty ki zauna mujirah fitowar doctor bandan tana soba ta zauna amma jinta takeyi kamar saman kaya sotake kota halin kaka taji abunda likita zaifada..... ..

Ashraba tana zaune bata ce dasu uffan ba ita kawai rashin lafiyar dady ce agaban ta

Delu tafito cikin damuwa tace Ashrab ya ake cikin jikin yallabai tabude bakinta kafin tace wani abu munu tasoma magana tayaya zata sani wancen dan iyayin likitan yakiyabari muji abunda ke damun sa Farha tace A'a kada ki ga laifin likita fah ai baizama lallai sai munji abund yake damun saba Addu'a zamuyi koma menene Allah yabashi lafiya

Haka ne kam munu ta dago ta gallamata harara ta dauke kanta daga kallonta tace bari na cigaba da aiki nah rana tana Dada yi tace baba delu mun gode da kulawar ki

Haba ranki ya dade ai anzama daya bakin ciki duk yakara mamaye zuciyar munu

Tamike bara naje na duba Farha ta dago

Waini Aunty munu na rasa gane miki duk kinbi kin wani damu kamar kece ma marar lafiyar tayi dariyar yake wallahi dole na damu jin Alhaji nakeyi kamar babana na cikina bana son na rasa shi kamar yanda na rasa baba nah

To wayace dake za'a rasashi yakamata ki san abunda zaki fada ai wallahi ina tabbatar miki har abada muna tare da dady dan ba inda zaije kima daina yimana fata e eh hee=ØÞ

'A'a ki fahimce ni kwarai kuwa ai nagama fahintar ki sokike dady ya mutu to wallahi ta Allah bata mutunba wallahi

Ashrab tace ke farha Aunty kike gaya wa magana haka ya isheki haka
Aunty kiyi hakuri kinsan har yanzu yarinya ce batada cikakken hankali

Tayi yake wanda yafi kuka ciyo kada kidamu nasan bata fahimceni bane ba....... Wallahi na fahimceki sarai

Tamike ta bar gurin tana cika tana batsewa

Ashrab ta matso kusa da munu tace Aunty kiyi hakuri dan Allah kinsan dai halin farha idan ranta yabace

Nasani kuma zanyi maganin abun insha Allah Ashrab tadago
Banganeba kamar yaya

Ina nufin zan kiyaye agaba insha Allah=ØÞ. Tayi dariya

Nan kuwa ita tasan mugun kudirinda tayi aranta

Tamike bara naje daki ko naga likitan bai fitoba haryanzu... To Aunty munu nima tashi zanyi

Sunmike kenan saiga su Alhaji sun fito tare da doctor Ashrab takarasa gurin dady ta sannu dady ya daga mata munu ta karaso tana wani shu'umin murmushi tace sannu dady ko kallonta baiyi ba barantana tasamu ya amsa Farha tace dady sannu ya amsa yana murmushi Auta tace na'am dady yace zamuje asibiti Ayimana addu'a kinji ko

dady zaka dawo yau ya jinjina kansa A'a sai na sami sauki dady zan bika tafada cikin shagwaba A'a utar dady ki zauna gida ga mum dinki nan munu tace doctor tafiya zakuyi da gaske?"

Yayi mamakin tanbayar sosai Eh yace ciyon nasa har yakai aje asibiti akwanta

Aa kada ki damu muna dan wani bincike ne gabanta yafadi rassss!!
bincike kuma bincike me kuma doctor nifa duk ban gane ba wane irin rashin lafiya ne wai

Kada ki damu zazzabin cizon sauro ne ba wani abu babba ba... dan haka ki kwantar da hankalin ki

Hajiya salma tace na gode munu da irin damuwar da kikayi da mijina kedin kinada matsayi babba azuciyata..

Tayi dariya ba komai mum jinsa nake kamar yanda kike jinsa azuciyar ki kinga kuwa damuwa dashi tazama dole

Hajiya Salma bata san kwanan zancenba tayi murmushi na gode da kulawa munu suka wuce Alhaji musaddiq ya gallah mata wata uwar harara har saida hanjin cikinta ya kada

Ya kalli matar sa ina kaunarku Ahalina kamar yanda nake son rayuwata duk runtsi duk wahala bana tunanin akwai wata yar tsakuwa da zata ruguza farincikin gidan nan insha Allahu

Yayi murmushi ya wuce yana jin jiki amma ya daure saboda kada munu ta fahimci yana jin jikin nasa maganar Alhaji musaddiq ta tsayawa doctor arai da kuma yaran Sa amma ita hajiya ba abunda ta sanya aranta.


Sororo tayi agurin azuciyarta tace mutun sai shegen taurin ran tsiya komai dai daurin ranka sainaga bayan ka tajuya ta nufi dakinta

Tana shiga ta dannawa *BASSAM* kira ya dauka muryar sa ciki ya akayi sweet heart bacci ma kakeyi to tashi bacci bai same is ba

Ya zauna kamar tana ganinsa wani abu ne yafaru

Abubuwa bama daya ba wai kasan dan iskan nan yana nan daram nifa wallahi bazan kyaleshi ba yaza'ayi kasamo mana poison mai karfi ne wanda yana sha yayi masa bugu daya kowa ma yahuta

Na biyu na fuskanci inada wata damuwa, "wace damuwa kuma

*FARHA* na fuskanci koda na kawarda Alhaji to *FARHA* itace my another problem dan haka ita ba kasheta zanyi ba kassarata zanyi na zaunarda ita takoma batada wani Amfani ba'a kawomun raini. nabar mutun ya zauna lafiya

Munu dan Allah kada ki taba wannan yarinyar kefa da kanki kikace yarinya hankali bai gama ratsata ba

Dakata mun *BASSAM* aikin ka nasaka kayi dan haka kada ma ka bata bakinka ka ganni nan wallahi zuciyata kamar ta fir'auna nake dan haka ina fada ne tare da cikawa ina jiranka da sakonah.... Ta katse kiran

Tajefar da wayar ai wallahi tunda na kashe mahaifina to banga wanda zan bari ba

Ai kuma wallahi sai na koyawa *FARHA* hankali=Ø(ÞALLAH sarki farha na tausaya miki

*BASSAM* ya rike wayar jikinsa asanyaye shi bai taba ganin zuciya irin ta munubiya ba rama Alkhairi da cuta

Allah ya shirye ki

Yamike ya fice daga hotel din zuwa neman poison dan yazarmasa dole ya nemo

Su Alhaji musaddiq suna zuwa asibitin likita yabashi gado daga nan suka fara kulawa ta musamman saboda yana bukatar kulawar

Hajiya salma ta dade a asibitin sannan ta dawo gida domin bin umurnin likita....tundag lokacin kuma gidan yazama wani iri yakoma ba dadi ita kuwa muguwar tana nan tana kullah yarda zatayi taga ta karasa shi

Saidai wani abu tarasa sanin awace asibitin aka kwantar da Alhaji barantana ta samu nurse ta cigaba dayi mata aiki

Kuma tanajin nauyin tanbayar mum kada ta zargi wani abu gashi bata shiri da baba direba ta rasa Tudun dafawa


Haka ta hakura tana jiran tasamu wata dama

To masu karatu laifin dadi karewa anan zan dakatar da wannan littafin sai mun hadu bayan sallah idan Allah ya kaimu



Ina mana fatan shiga Azumi lafiya


TAKUCE AKULLUN



LAURAT M BELLO


COMMEN
VOTE
SHARE


08164949554





=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ



BANGARE NAH
( part of me)


=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ



WRITING BY

LAURAT MUH'D BELLO

DAGA MARUBUCIYAT LITTAFIN
*SUKHAINAH*





________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*=ئÜ{Arewa ginshi™in al'ummah}=ئÜ*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com




ALLAHUM AAJIRNII FI MUSIBATI WA'AKLIFNI KAIRAN MINHA.
AMEEN>Ø2Ý


Helloooooooooooo my fan's barkamu da sake saduwa=Ø
Þ



<><><><><><><>1ã 3ã é#1ã 4ã <><><><><><><><>












<><><><><><><><><><>"Haka ta wuni batare da tasan abun yiba jikinta kwata-kwata bayada wani karfi taso matuka ta kawar da Alhaji musaddiq daga doron kasa saboda ganinsa tamkar wani tabo ne azuciyar ta yazama dole tanemi mafita"

"Hajiya salma! kullun cikin kulawa take daga dukanin wani movement na yan gidan kamar yanda likita ya umurceta amma kwata-kwata ta kasa gano komai sai tafara zargin toko a wani gurin ne Alhaji yaci wannan gubar ba anan bane"

Tana zaune adaki kanta yadau zafi, *FARHA* tashigo dakin tare dayin sallama ahankali ta dago tare da amsawa takarasa kusa da ita ta dafata mummy na fahinci kwanan nan kina tare da damuwa ta ja ajiyar zuciya tare da kirkiro murmushin da baikai zuciyar ta ba ta janyo yarta ajikin tace kada wannan yazar miki wata damuwa rashin lafiyar daddy ce take damuna amma ba komai kinji koh"

Humm! tace mummy nasan ni yarinya ce amma ina kula da idan wani yana tare da damuwa to baran tana damuwar da ta dameki mummy ni nasan akwai wani abu ba iya damuwara rashin lafiyar daddy bane ba"

Kawai dai kina boyewa ne bazan matsa da sai naji abunda yake faruwa bane amma dan Allah mummy ki rage addu'a inaga sai tafi ba yawan tunani ba

Ta dago ina mamakin yanda kike tsara zance *farha* kamar wata babba dariya tayi mummy ai nima babbace farha bata bar dakin ba har saida taga mummy dinta ta rage damuwar da take shinfide a fuskarta

"Allah sarki ya'ya rahma ne"

" munu ta fito cikin kwalliya ta kece raini. Cikin tafiyarta ta kasaita ta karasa gurin mum ta sunkuya kamar da gaske mum zan fita hajiya salma ta dago tana murmushi tace sai ina munu aka caba kwallaiya haka gidansu wata kawata zanje dubiya Ayyah to sai kin dawo amma dan Allah ka dawo da wuri kinsan bana son yawo

Insha Allah zanyi kokarin ganin na dawo da wuri mum tayi dariya tace yaw'wa dan Allah ki kiyaye kinga Alhaji baya son yawon shi isa nake kokarin kiyaye dokar sa

Azuciyar ta tace zan kuwa yi maganin sa indai nice

"Ta dago tana murmushin mugunta tace b komai mum za'a kiyaye insha Allah ai dake komai yazoh karshe dan nayi kusan karasa aikin

Ba abunda hajiya salma ta kawo azuciyar ta tayi murmushi tace kije kada ki makara ta mike tana yauki ta fita........

Tana fita gidan baba direba shi kuma yana ficewa daga gidan dan haka ba wata motar da zata fita da ita hakan nan ta fita ta tare adai-adaita sai hotel ahankali baba direba yake bin bayanta har suka isa hotel din akan idonsa ta biya mai adai-adaitar kudinsa yasamu guri yayi parking ya fito cikin shigarda bata taba ganeshi ba saboda ko ni da kyar na iya gane shi yana binta har dakinta da zata hadu da *Bassam*

"A kofar yatsaya na wasu dakiku kafin daga bisani ya bar gurin zuciyarsa cike da tsoro da firgicin abunda kunnuwansa suka ji masa"..

"Yajima zaune a acikin motar yarasa abunyi sai tufka yake yana warwara ya jaaa dogon numfashi yace yazama dole nasan abunyi bazai yuyu nabar wannan yarinyar ta aikatawa iyalan Alhaji musaddiq abunda ta kudirah ba koda zan rasa numfashi na yafada cikin daga murya idanuwansa ya kada yayi ja tamkar wani zakii!....

Da karfi yaja motarsa yabar harabar hotel din zuciyar sa acunkushe

Kai tsaye asibitin da aka kwantar da Alhaji musaddiq ya nufa bai wanisha wahalar ganin saba kasancewar sa sanenne a asibitin

"Har dakinda aka kwantar da Alhaji yashiga, "ganinsa yasanya shi shiga wani hali dan gaskiya jikin ba'a cewa komai saidai godiyar Allah
Kwance yake kamar wata gawa dan yakara week sosai

Tausayinsa da na iyalinsa suka kara dabaibaye zuciyar baba direba hawaye masu zafi suka gangaro masa yakarasa gurin gadon da yake akwance ahankali yasoma magana"

"Sannu yallabai ya karfin jikin?"

"Daga kansa yayi yabude bakinsa cikin matsanan cin jinjiki ahankali yace Alhamdulillah"

"Baba direba yace Allah ya kara sauqi Alhaji Allah yatashi kafa dunka ya mayarda kai cikin iyalinka...,,

Ya dago jajayen idanuwansa yasoma magana baba direba jikina yana bani bazan tashi ba inajin rabuwar mu ta kusa saboda yanda nakeji nikadai na sani

Ya karasa kusa dashi ya janyo hanuwan sa Alhaji kadai na fadar haka insha Allah zaka tashi zaka koma rayuwa kamar da cuta ba mutuwa bace....

Ya lashi busassun lebunan sa yace kaje ka dauko mun hajiya da yarah na inason muyi sallama tunkafin ruhina yabar gangar jikina

"Hankalin baba direba yakai kololuwar tashi, jikinsa yayi matukar sanyi yana kuka haka yafice daga asibitin ya nufi gida dauko su hajiya....

"Tana daki azaune jinta take wani iri haka kawai jikinta yake yimata nauyi, *FARHA* ta shigo dakin tareda *ASHRAB* azaune suka tadda ta tayi tagumii cikin sauri suka karaso gunda take mum lafiya suka fada lokaci guda....

"Ta dago bakomai haka kawai nake jin bana jin dadi hawaye suka gangaro mata jikina yana bank wani abu zai faru damu marar dadi ya'yanah inajin tsoron abunda zai faru"

"Jikinsu yayi matukar sanyi mum menene yafaru Ashrab tafada a raunane?"

"Jikina ne yake sanar dani something bad is going to happen"

"Mummy kisanar damu idan a kwai wani abu dan Allah"....

"Suna cikin haka delu ta shigo tare da yin sallama ranki ya dade baba direba yana magana,

"Ta dago to kawai tace kice dashi ina zuwa,

"Suna fitowa paloun ayanda ta hango baba direba tasan tabbas akawai wani abu ta karaso cikin sauri baba lafiya dai koh? "naga kamar kana cikin damuwa"


"Yayi kokarin saita nutsuwar shi yace insha Allahu hajiya Alhaji ne yace nazoh na dauke ku yana son ganin ku.... "Gabanta ya yayi mummunar faduwa bakinta yana rawa ta soma magana baba direba kada fah hasashena yazama gaskiya dan Allah kace dani zato kawai nake ba gaskiya bane........ "Jikinsa yakara sanyi yace babu wani abu kada ki sanya komai aranki Alhaji yasami sauqi sosai........ Tamike muje baba bazan sami nutsuwa ba matukar idanuwana basu ganemun shiba bazan ta'ba samun nutsuwa ba".....

"Gaba dayansu suka fita suka nufi asibitin"........

"Kirjin ta sai bugawa yakeyi babu sassauci saboda fargaba zuciyarta a tsinke take ahankali ta tura kofar dakin tare da yin sallama arufe yake har kansa da farin mayafin da ganinsa kadai ya isa ya sanar dakai tabbas akwai wani mumman al-amarinda ya faru"

"Jikinta yana rawa ta karasa gurin ahankali ta daga mayafin kwance yake tamkar kace tashi ya tashi amma ina rai yariga da yayi halinsa wata razananniyar kara tasaki tare da sulalewa kasa a sume"


"Allahu akbar=Ø-Þ

Kumuje zuwa my fan's kuyi hakuri kunjini shiru kwana biyu nayi nauyi ne

I love you all my fan's



Daga laurat m bello


Share
Vote


Comment.............




=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ



*BANGARE NAH*
*(part of me)*


=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ



*WRITING BY*
*LAURAT MUH'D BELLO*


*DAGA MARUBUCIYAR* *LITTAFIN*
*SUKHAINAH*

*AND NOW*
*BANGARE NAH*
*(part of me)*



~BISMILLAHIR~RAHMANIR~RAHEEM~& & &


~ALLAHU AKBAR KABEERAN~






________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*=ئÜ{Arewa ginshi™in al'ummah}=ئÜ*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com



*1þã 5þã é#1þã 6þã *







<><><><><><><><><>"Tim kawai sukaji hajiya salma ta danfara a tayil dinda yake shimfide a dakin cikin gaggawa sukayo kanta suna kuka mummy ki tashi, haka likitoci suka kawo
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment