Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

mata dauki cikin gaggawa emergency aka nufa da ita saboda asamu a ceto ranta".............
"Yayin da yaran abun duniya ya ishesu Farha ta karasa gurin da daddy yake akwace kamar kace dashi tashi ya tashi cikin shesh shekar kuka take magana daddy nah nasan kana jina dan Allah ka tashi kada ka manta da alkawarin da ka daukar mun kace zaka rayu tare damu bazaka taba rabuwa damu ba me yasa zaka karya alkaqwarin da kayi
Muna matukar bukatar ka a kusa da Allah ka tashi ta fada jikin gawa ta cigaba da kuka kamar ranta zai fita
Ashrab t matso kusa da ita cikin kuka ta janyota jikin ta Kiyi hakuri autar daddy duk irin alkawarinda mutun ya dauka baya ta'ba cika shi saida izinin Mahaliccin sa dan haka kiyi hakuri daddy ya tafi kuma bazai ta'ba dawowa ba saidai muyi masa addu'a Allah ya sadashi da rahma"
Ta janye daga jikinta a'a Ashrab kada muyi haka dake da bakinsa ya gayamun haka dan haka ki bari naje na tayar dashi ninasan yana sona zai tashi
Wallahi ina son daddy bazan iya jure rashin shi ba shi isa bazan bari zuciyata ta sabu da yarda da yatafi ba jikina yana bani da daddy na yana nan da ransa doguwar suma yayi
Kuka mai karfi ya subuce mata katashi daddy dan Allah katashi gidan mu zai zama kamar kango idan har baka tare damu kada ka manta da yanda muka shaku muke rayuwa mai dadi cikin so da kaunar junan mu daddy dan Allah ka tashi......
Likitoci suka shigo farha na ganin sun doshi gurin daddy ta cikin sauri ta taso cikin daga murya tace kada ku kuskurah kuce zaku taba mun daddy daya daga cikin su ya masto kusa da ita kiyi hakuri Farha daddy ya rigada ya rasu abunda zai zamar masa gata ayanzu a kai shi makwancin shi kiyi hakuri ki fawwalawa Allah komai saiki ga ya sanya miki sassauci acikin ranki
Ta dago jajjayen ida nuwanta tace kana tunanin na yard da daddy ya mutu, to idan ma kana tsamanin haka tunanin ka yagayamaka ba dai-dai ba dan ni nasan yan nan da ransa......
Tausayin yarinyar yagama cika zukatan su domin kuwa sukansu sun san irin shakuwar da family yayi amma ba yanda aka iya hakan nan za'ayi hakuri
Baba direba ya kasa cewa komai tausayin yaran ya gama dabaibayeshi ya matso kusa da Farha da ta kankame gawar daddy ta hana kowa yaje kusa da ita har Ashrab tsaye take tana kallon yar'uwarta tana kuka ta kasa aiwatar da komai....... Cikin dabara ya matsa kusa da ita ya tausasa muryar shi yace yarinyar daddy ni nan ina bayanki bazan bari atafi da daddy ba saboda nima ban yarda da ya mutuba kinga karbi kisha ya mika mata lemo mai sanyi kamar jira take take ta karba ta sha sosai kafin yan mintina tafara ganin mutane dishi-dishi can kuma ta sulale kasa bacci mai nauyi yayi gaba da ita
Baba direba ya taimakawa Ashrab suka daurata agadon da yake kusa dana gawar Alhaji cikin sigar rarrashi yace kiyi hakuri hakan da akayi shine kawai mafita saboda idan har tana gani bazata yarda ayi komai ba bada wata manufa nayi hakan ba hasalima banyi hakan ba saida umurnin likita Ta dago na fahimta baba nikaina nasan hakan shine kadai mafita
Ta ja dogon ajiyar zuciya tace ya jikin mum ya jijjaga kansa jiki kam ba'a cewa komai saidai addu'a amma hajiya tana cikin wani hali
Ta share hawayen da suka gangaro mata tace baba direba wannan wace irin jarrabawa ce tazoh mana alokaci daya.
Kada ki damu Allah yana iya sauya rayuwar kowane bawa alokacin da yaso yakuma ga damar hakan ita jarrabawa Allah yakanyiwa bayinsa ne saboda ya gwada imanin sa idan kayi hakuri ka jure sai Allah ya buda maka ta inda bakayi zato ba
"Ta kara goge hawayen da suka gangaro mata wallahi baba direba dauriya kawai nake ji nake kamar nima mutuwar zanyi, ......."haka mutuwa take ya'ta musamman ta iyaye sai dai hakuri amma akwai d'aci ya mike bara naje likitoci suna jirana ya fice daga dakin yana goge hawaye"..... 'Kafin kace meye wannan duka yan'uwa da abokanan Alhaji musaddiq sunji rasuwar sa na kusa da na nesa kowa ya zoh ba'a samu yin jana'izar saba sai washe gari alokacin hajiya salma ta farfado Farha ma haka sadai ita hajiyar zaune kawai take bata cewa da kowa uffan sai hawaye dasuke zuba tamkar fanfoh......
Bayan an kammala shiryashi aka kawashi gurin iyalansa suyi bankwana hajiya salma ta kasa cewa komai sai kuka da takeyi farha tayi zaune kamar mutun butumi itama dai kamar bata cikik hayyacinta dan maganganun da take kadai sun isa su tabbatar da hakan..... Kusan kowa da yake gurin saida ya zubar da hawaye domin kuwa iya tausayi wad'anan iyalan sun bawa mutane tausayi matuka haka aka dauke shi aka fitar dashi domin sadashi da makwancin sa na gaskiya........
Gidan yayi shiru mutane sai kaiwa da kawowa suke yan zuwa gaisuwa.... Mahaifiyar munubiya itama tana gidan saidai wani abun mamaki da daure kai duk wannan abun da akeyi munu bata sani ba domin kuwa tun jiya bata gidan tana can hotel tare da abokin sha-shancinta suna sheke ayarsu tun adaren jiya maman ta take neman wayar ta amma akashe
Haka uwar takwana acikin kunci da kuma Allah wadarai da halayyar munu ace gidan da kake zaune ayi rasuwa amma kai bakada ko labari Allah dai ya kyauta.....


"Washe gari sai 10:00 pm na dare ta dawo gida tun a gate din gidan taso ta gane akawai abunda ke faruwa amma saboda batada mutunci ta share da baba direba tafara haduwa tayi masa kallon wulakancin da ta saba tayi shigewar ta ciki batare da tayi masa magana ba kamar ya sanar da ita amma kuma yanda yake cike da jin haushinta sai ya fasa yaga to meye amfanin hakan dama ita hakan zata soh tunda dama ba wani jituwa sukayi ba.... Ta baya tabi saboda bata son kowa ya ganta baran tana a dameta da tambayar ina ta kwana tana shiga ta yi wanka tabi lafiyar gado kafin yan mintina bacci yayi gaba da ita".....

Wannan ke nan

Tun asuba maman munu ta nufi dakinta tajima tana buga kofar amma shiru zuwa yanzu hankalin ta yafara tashi anya munu tana da hankali kuwa..... Can taji anbude kofar cikin masifar da tasabayiwa delu amamakinta taga maman ta ta tsaya cike da mamakin ganinta lafiya tace da ita kekuma yaushe a gari me kika zoh yimun da sassafe daki...."maganar ta kona mata rai matuka ta dake ta dannah kanta cikin dakin batare da tace da ita komai ba,..... "Tana mai jin haushin maman zata takura mata tace wai yaushe kika zoh ne kuma ma me kika zohyi nifa wallahi bana son takurawa nan dinma bazaki barni na huta ba sai kinbiyoni ki takura mun"....
"Ta dago jajayen idanuwanta tace bazaki taba gyarah rayuwar ki ba kenan munu banzoh gidan nan dan na takura miki ba hasalima dalili ne ya kawoni ta share hawayen da suka gangaro mata tace,
" Kina da masaniyar abunda yafaru kuwa? ta dago tana mata kallon raini tace ni ki gaya mun kawai sai wani janrai kike yi me kuma yafaru? "
" Allah yayiwa Alhaji Musaddiq rasuwa yau kwan biyu kenan
Babu kunya ba tsoron Allah munu ta daga hanu tasoma magana Alhamdulillahi nayarda kwallon mangwaro na huta da kuda"
" Kan Aisha yayi mugun kullewa da zantukan munu me kike nufi da hakan me kike nufi dayin hamdallah rasuwa fah nake gaya miki amma naga kamar ma hakan kikaso

"Ta dago bazaki ganeba bantaba tsintar kaina afarin cikin da na tsinci kaina ba yanzu zanbaki goron Albishir ta bude baki zata kara magana ta dakatar da ita ya isa haka sarkin zuba ki tafi inason zan kara yin bacci kafin na zoh naga iyalan ALHAJI MUSADDIQ...... naga kuma waye yakamata yazama next targate"


"Ta sheke da dariya kamar wata boss"

"Tooooooo=ØDÞwannan family's kun hadu da bala'i sadai addu'ace zata fiddaku daga tarkon munubiya"

"Kuyi hakuri zan dinga yimuku kadan saboda zaman typing din yana yimun wahala yanzu"




TAKUCE AKULLUN

LAURAT M BELLO

SHARE
VOTE

COMMENT.................. ..




=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ



BANGARE NAH
(part of me)

=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ



STORY & WRITING BY
LAURAT MUH'D BELLO
(Maman khairat)


MARUBUCIYAR LITTAFIN
*SUKHAINAH*


AND NOW
....BANGARE NAH
part of me




~ALHAMDULILLAHI ALAKULLI HALIN~

~WANNAN SHAFIN NAKI NE KIYI YANDA KIKE SO DA ABUNKI SHUGABA TA GARI
WATO AUNTY HAU'WA MAMAN USMAN ALLAH YAKARA MIKI HAKURI DA JURIYAH~
~AMEEN YA ALLAH~





________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*=ئÜ{Arewa ginshi™in al'ummah}=ئÜ*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

¶BISMILLAHIR¶ RAHMANIR¶ RAHEEM¶" " " " " "


*A'UZU BIKALIMATILLAHI TAAMATI MINSHARRI MA KALAQ*
*AMEEN*



1þã 7þã é#1þã 8þã








"Sai da tasha baccinta tukunah ta fito zuwa bangaren hajiya salma tana zaune dai kamar kullun bata iya cewa komai sai sharar kwallar da take wacce ita ta zamar mata tamkar abinci yaranta suna kusa da ita a zaune kowa zuciyar sa ba dadi, ta shiga cikin nutsuwa kamar ta kirki hawaye suna zuba kamar fanfoh".....
"Tunda ta shigo farha ta sakar mata wata uwar harara, ji take kamar ta shaketa dan takaici, haka kawai takejin matukar kiyayyar ta aranta munu bata zame ko'ina ba sai kusa da hajiya salma tana zuwa ta rungumeta ta kara fashewa da kuka mai shiga zuciya,......

"Hajiya salma ta kara rungumeta sosai tana kuka mai tsuma zuciya

Farha datake kusa da ita ta mike a fusace ta finciko ta gefe bama bukatar kukanki na munafurci,

"Yau daddy kwanansa biyu da rasuwa amma sai yau kike kuka sai yau kika san da rasuwar shi sai yau kikasan da iyalansa"

"Wallahi na tsane ki inajin tsanarki acikin zuciyata ta bar gurin cikin kuka"

"Hajiya salma ta kalleta tace kiyi hakuri kada maganganunta su tasiri a zuciyar ki Farha har yanzu ita yarinya ce kara"...

"Tayi wani shu'umin murmushi ba damuwa mum nasan dacin mutuwar ne bai gama sakin taba hakan bai wani dameni ba".....

"Haka rayuwa tacigaba da tafiya agidan margayi Alhaji musaddiq zaman kadaici darashin wallawa yacigaba da gudana agidan ..yayinda munu tacigaba ta kulle-kullenta na ganin tasami babban mukami a kamfanin su hajiya salma"

"Sai bayanda hajiya tagama takabar ta takoma aiki amma kana ganinta kasan bata tare da wallawa tunanin Alhaji ya gagarah barin zuciyar ta komai takeyi sai ya fado cikin ranta"

"Haka yaranta Ashrab da munu dukansu suna aikin a kamfanin yayinda Farha taciga da karatun ta"

"Tunda munu ta fuskanci ana samun makudan kudi akamfani ta kudira aranta duk yanda zatayi sai kamfanin ya dawo hanunta saidai wannan lokacin tana bin abunne cikin hikima gudun kada ayi saurin gano shirinta......















____________________________________
BAYAN WANI LOKACI MAI TSAHO
____________________________________




"Tun bayanda Alhaji musaddiq ya yarasu yau kimanin shakara uku ke nan amma hajiya salma ta gagarah yin aure gani take tamkar idan tayi aure ta ci amanar kaunarda take masa ne


Wata ranar lahadi suna gida kasancewar ta week end ne tana zaune ita kadai adaki tayi zurfi acikin tunani munu tayi sallama tashigo dakin

Ta sauke ajiyar zuciya tare da amsa sallamar murmushi tayi a'a munu fita zakiyi ne ta tambaya?

A'a gunki nazoh da akawai maganar da zamuyi ne

To bismillah ina jinki tayi shiru tana tunanin ta inda zatafara hajiya salma

Tace da matsala ne naga kamar kina cikin damuwa

Taja ajiyar zuciya mai karfiii hummmm!

Mum dama ba wani abu bane dama wani ne yazoh gunki yana palourn kasa yana jiranki nayi kokarin ganin na hanashi amma saida ya shigo

Hajiya salma ta yatsine fuska mamaki karara ya bayyanah afuskarta tasoma magana tace wani kuma to daga ina?

Banida wani wanda mukayi dashi zaizoh nemana

Amma kice dashi ina zuwa just give me five minit ina futowa.......


To tace tafice daga dakin zuciyarta tana dakan uku-uku dan bata san yanda hajia zata karbi abun bah

Cikin yan mintin ta fito sanye cikin wani pink din material mai matukar santsi da sheki fuskarta ba kwallaiya amma tayi matukar kyau dama hajiya salma badai kyau ba sai dai yar rama da tayi kadan wannan kuma bayada nasaba da yawan tunin tsohon mijinta uban ya'yan ta..... dayazamar mata tamkar ibadah....


Yana tsaye rungume da hannayensa ya juya bayansa baza a iya hango fuskarshi ba amma zaka iya hango tsantsar kyan surarshi dakuma kuriciya

Tana dosar gurin gabanta yafadi sakamakon jin kamshin turaren sahibitinta kuma abun kaunar ta Alhaji musaddiq da sauri ta karasa gurin da yake tare da yin sallama

Yajiyo ahankali tare da amsa sallamar kyakkyawa ne na ajin farkon fari ne tas dogo ne mai yalwataccen fadin kirji sajenda yake kwance a gefen fuskarshi yakara sanya asalin kyansa ya fito sosai

Saida tayi da gaske ta iya dai-daita kanta sannan ta ce dashi bismillah kazauna mana

Shikansa baiyi zaton haka take da asalin kyau ba tabbas yau ya samu dame akala dan agaskiya yanda munubiya take gaya masa hajiya sai yaga kamar ba abunda ta fada acikin rabin kyanta

Aransa yace lallai yasan zai kwashi rabonsa dan ya tabbatar da sauran ta....... Jikinta ya tabbatar masa da hakan

Haka zuciyoyinsu suka fada kogin tunani alokaci guda

Can hajiya salma takatse shirun da tsambayar dan saurayi ban ganekaba ko su Ashrab za'ayi maka magana dasu....... Yayi murmushin gefen baki wanda ya kara futoda kyansa karara ya nisa yace

Gunki dai nazoh

Yabata amsa yana mai yin kayataccen murmushi abun yabata mamaki matuka ni kuma?

Yes yace nazoh ne da kokon barata agareki ma'abuciya kyau da kwarjini

Kalaman sa sun soki zuciyarta matuka amma ta share

Tace nayi mamaki kuwa duba da ganinka yaro matashi kyau ace yarinya kaje gareta bani ba

Kada kiyi saurin yanke hukunci nike nakeso kuma ke nakeson takasance mun wani bangare nah tabude baki zatayi magana ya dakatar da ita

Zanbarki kiyi tunani idan kin gama ga kati na nan akwai duk wasu bayanai na aciki *SUNANA BASSAM ASIM* na barki lafiya ya fice daga palourn cikin tafiya ta kasaita........



Hummmmmmmm!!! Lallai akawai kwakwakiya kenan

Toko yaya za'ayi da su Farha iyayen rigima

Dan tabbas idan har tasumu labari akwai babbar matsala


Takuce. AKULLUN


LAURAT M BELLO



IDAN HAR BANGA RUWAN COMMENT BA TO ZAN AJIYE ALKALAMIN NAH NA HUTA DAN BAZAN DINGA WAHALA BAH


COMMENT YA GAGARAH



INA BUKATAR GANIN CANJI DAKA GAREKU............




=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ



BANGARE NAH
(part of me)

=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ



STORY&WRITING
BY
LAURAT MUH'D BELLO
(maman khairat)


MARUBUCIYAR LITTAFIN
SUKHAINAH

AND NOW

BANGARE NAH
part of me




Bismmillahir rahmanir Raheem



Ina farawa da sunan Allah mai rahma mai jikai......

Wanna shafin nakune masoyan littafin BANGARE NAH.... ALLAH YABAR KAUNA AMEEN YA ALLAH........





________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*=ئÜ{Arewa ginshi™in al'ummah}=ئÜ*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com







... ... ... ... 1þã 9þã é#2þã 0þã









"BASSAM ASIM! shine sunan da taketa mai-maitawa a zuciyarta hakika abun yazo mata a bazata"

"Yaron tabbas yayi saidai kuma yarintar shi itace abar dubawa tayaya zata iya tarayyah da yaronda ta kusa haifa wannan dacewar shi Ashrab shine dai ba ni ba"


"Tayi zurfi atunani Farha ta shigo palourn bakinta dauke da sallama ta mai-maita sallamar har kusan sau uku amma hajiya salma bata ma santana yiba hakan sai ya bawa Farha mamaki matuka"


Kusa da ita takarasa tare da dafa kafadar ta mummy lafiya inata sallama amma naga kamar hankalinki yana wani gurin firgigit!! tayi ta dawo cikin hankalinta,

Na am Farha baby kin dade ne ban jiba ta zauna akusa da ita ta janyo hanayenta mummy nah lafiya? Meyake faruwa ne kinsan fah bana son damuwar ki

Hajiya salma taja dogon ajiyar zuciya tace bakomai yarinya ta damuwar tana da nasaba da office ne kada hakan yazama damuwa agareki kinji yarinyar dady takarasa maganar cikin sakakkiyar fuska tamkar ba wani abun da yake damunta.......

"Haka ta zauna cikin tunani tsahon dogon lokaci batare da ta sanarda yaranta komai ba



"BASSAM yana fita daga gidan ya kirah munubiya tana murmushin samun galaba hello tace cikin narkewar murya yace my sweet heart every things is don kuma ga alama komai zai tafi yanda aka shirya shi"

"Ta sheke da dariyar samun nasara tace dama na gaya maka ai bana tunanin dama rashin samun nasara saboda ban taba farawa nakasa karasawa ba"

"Ya lumshe idanuwan sa yace ai na fahimci ta fada fah"

Tayi dariya tace dama nasan zata fada bana tunanin akwai macenda zata kasa fadawa komar ka BASSAM kaidin na daban ne ni nasani

Saidai kuma inason kasani wannan auren na manufa ne ban amince kasaki jikin ka sosai ba dan Wallahi banida kyau kuma kai ma kasan da haka

Ya lumshe idanuwan sa kamar tana ganin sa yace kada wannan yazamar miki damuwa ai bana tunanin akwai wata matar da zata fiki matsayi a gurina"

Yanda yayi maganar har wani yarrrrrrr taji jikinta yayi ta lumshe idanuwanta ina fatar haka BASSAM saboda bazan iya sharing dinka da kowa ba kaidin na musamman ne agareni ina sonka sosai...... Ko wannan zan daure ne kawai saboda inada abunda nake nufi da hakan amma idan ba haka ba babu gangan cinda zai sanya nayi wannan danyen aikin"

=ØDÞtabdijam"......


BANGAREN HAJIYA SALMA


Tunani kyakkyawar fuskar shi ya gagarah barin zuciyar ta yayinda sunan sa yake yawo acikin zuciyar ta bayan ko wacce dakika kala mansa sunyi matukar tasiri azuciyar ta

Ta ja dogon hajiyar zuciya hummmmmm!!

A hankali take tambayar kanta me hakan yake nufi ya kamata ki nutsu Salma wata zuciyar take sanar da ita

Kada kyau da kuruciyar shi yayi tasiri azuciyar ki, ki ajiye wannan shirmen gefe zuciyar ta takara sanar da ita.....

Ta kwanta sosai a kan gadon ahankali tace me yake shirin faruwa dani ne ta runtse idanuwanta gam... Tabbas yakamata na dawo cikin hankalina.. Soyayya ba tawa bace abun kunyar ma da yaro sa'an kanina mtssssss taja dogon tsaki wannan ai abun kunya ne"

Har karfe 12:00am na dare tana abu daya can wayar ta tashiga neman taimako tayi matukar mamakin ganin waya awannan lokaci ta sanya hanu ta dauka number an boye ta abun ya kara daure mata kai ta share har saida ta tsinke aka kara kira karo na biyu nan ma taki dauka kirrrrrr taji shigowar sako yashigo da har ta share shi wata zuciyar tace ki duba mana ta janyo wayar ta bude

My soul shine rubutun farko a sakon
Gabanta yafadi shine sunan da Alhaji musaddiq yake kiranta dashi a mafi yawancin lokaci.

"Tunaninki yaki barin zuciyata tsahon dogon lokaci soyayyarki taki barina sukuni
Ina neman sassauci daga ma, abuciya kwarjini da kamshi hakika kedin haske ce wanda baya ta'ba disashewa

Ki tausayawa zuciyar masoyinki mai matukar kaunarki ............

Akwance take amma saida ta mike zaune ta maimata karanta sakon yafi akirga

"Kalamansa taketa mai-mai tawa taja ajiyar zuciya mai karfi na shiga uku....

"Ta furta ahankali ya zanyi,..... "Yayita kira amma takasa samun sukunin dauka saboda zuciyarta tagama rauni...,,

"A nasa bangaren murmushi yayi na gefe baki yace a fili salma yanzu muka fara bazan taba kyaleki ba har sai na cika burin zuciyata akan ki"

"Soyayyar gaskiya nake miki ba wai son yarjejeniya ba dan Haka bazan taba hakura ba =ØDÞtabdijam lallai akwai tashin bama-bamai kenan idan har munu tagano manufar ka".....


"Ashrab da Farha sun gama fahimtar mum dinsu tana cikin damuwa amma abun mamaki taki ta sanar dasu komai sunyi tambayar duniya amma amsarta bata wuce ba komai"

"Hakan nan suka hakura badan sun yarda ba ,.. Munubiya kuwa farinciki fal zuciyarta dama haka takeso domin kuwa hakarta ta fara cimma ruwa saida Farha tatafi school tukunnah ta nufi dakin hajiya salma, tana zaune kamar kullum tana aiki wato tunani munu tayi sallama ta shigo dakin tundaga nesa tasaki murmushi sannan ta karasa gurinta ahankali ta dafa ta mummy lafiya naga kamar kinada damuwa,..... "Ta dago tare da jan dogon ajiyar azuciya kana tace"

"Ba kama bace munu ina tare da damuwa wallahi tun lokacin da bassam ya bayyana cikin rayuwata banida sauran sukuni har yau...... Cikin rashin fahimta tace waye kuma haka mum ta dago wannan bakon mana tajim alamar tunani can tace aw wannan yaron na kwanaki ta jinjina kai shi munu...... Kece kike ganinsa yaro amma zuwanshi yana da tattare da abubuwan al-ajabi kamar yaya mum?

"Hakika yazoh da babban al-amari munu ta dago nifah ban ganeba har yanzu mum ta rigo hanunta sona yake munu.. Kalmar so da ta furta Bassam yana yimata ya yi matukar kona zuciyar munu ta rintse idanuwanta wata zuciyar tace ki nutsu munu ta yi murmushi tace....

"Ni aganina wannan ba abun damuwa bane ki amince mana inaganin yafi zaman ki ahaka kada ki manta shekarun ki karuwa suke zamanki ba miji inaga baiyi ba"

"Na sani munu ba abunda nake tunani sai ya'yanah matsalar ta yarana ce bansan ya zan sanar dasu ba abun kunyar ma ni yaron yayimun kankanta wallahi inajin kunyar sanarda Ashrab da Farha gaskiya"

"Kan uba Bassam dina ne karami ta fada azuciyar ta a fili tayi dariya tace nifa har yanzu banga wata damuwa ba inaganin ki amince kawai tunda naga kamar kina son shi,....... "Tayi shiru na yan dakiku kana tace bansani ba har yanzu ban tantanceba kaina yashiga caji na rasa tudun dafawa"

"Munu ta dafa ta tace kiyi abunda zuciyar ki ta yarda dashi kada kibari damarki ta kubuce miki yaranki bazasu zama silar rugujewar farin cikin ki ba ta mike wannan itace shawarata..... "Tana gama magana ta fice zan wuce office sai kin fito"......

"Bata samu damar amsawa ba saboda kanta ya kulle matuka ahankali tace tabbas inajin wani abu gameda Bassam tokuma ya zanyi da yarah nah,....... "Wani bangare daga cikin zuciyar ta yace ki hakura Salma inaganin zaifi kiso farincikin ya'yanki"

"Wata killa yaron yanada wata manufah akan ki KIRJINTA yayi wata mummunar faduwa RASSSSSS!!! .sai a lokacin tafara wani tunani na daban"

"To idan haka nefa ya kenan
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment