Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

badan ya cutar da itaba......

Itakuwa munu kullun tunaninta bai wuce taga komai yadawo hanunta ba kamar yanda suka tsarah Amma haryanzu basu hadu da bassam ba barantana taji ina suka kwana kwata -kwata yanzu shi bata wannan yake yiba tunanin sa kawai yaga ya samu karbuwa matar shi dan haka ma yake kin rabuwa da hajiya salma kullun suna tare da ita babu yanda ta iya saidai kalloh........

Bayan sun gama hutun amarcin su suka koma office duk wasu kadarorin ta, tadankawa *BASSAM* su office din baban manajan kamfani yadawo hanun bassam yasamu guri sosai hakan ya dan ragewa munu radadin rashin bassam a kusa da ita yanzu burinta ta karbo takardun su dawo hannunta sauran kadarorin kuma tabi ta karkashin kasa wajen ganin ta karaba cikin ruwan sanyi"







________________ "A yau za'a sallamo su asibiti Amma saboda rashin gata mahaifiyar su bata ma san suna asibiti ba ta manta dasu shaf arayuwar ta....... Asharab tana zaune tayi tagumi hawaye suna zuba a idanuwanta baba direba ya shigo yana ganinta ahaka tausayinsu ya kama shi janyo kujerah yayi ya zauna yadanyi gyaran murya sannan ya soma magana cikin nuna kulawa kuyi hakuri Asharab hakika nasan kuna cikin jarabawa Amma kuma hakuri shine maganin komai duk kan tsanani yana tare da sauki kuyi hakuri ku cigaba da addu'a insha Allah bazaku tabe ba Allah shizai zama gatan ku........... Ta shafe hawayen da suka gangaro mata tace "bakomai yake damuna baba illah rashin kulawar mahaifiyar mu garemu kada kamanta baba bamuda kowa aduniyar nan sai mum itace ta ragemuna itace farincikin mu mahaifin mu ya rasu mahaifiyar mu ta yada mu ba ruwanta damu ya zamuyi baba me mukayiwa mum dazata koremu daga cikin gidan da mahaifin mu ya gina da gumin sa mun koma yan ai'ki ma sun fimu matsayi a cikin gidan mu.......... Ya zamuyi da wannan bakin cikin, wallahi baba ji nakeyi kamar zan mutu saboda yanda nakejin zuciyata tana mun"

"Ashsha Asharab ki daina fadar haka kiyi hakuri komai zai wuce........ Allah yasa baba Amma yaushe zamu kara samun kulawar mum anan gaba kana ganin fa ko kallon mu bata son yi ta nisanta damu, baba direba yayi shiru na wani lokaci sannan yace ba komai akwai Allah shine zai kawa muku dauki cikin gaggawa....... Ya mike suka fara hada kayan su ya fita karbo takardar sallama sukuma suka karasa had a kayan ita da delu Farha tana kallon su hawaye suka gangaro mata.........

Bayan baba ya dawo suka fito zuwa gida

Sun koma gida delu tacigaba da kula da su tamkar mahaifiyar su ba wanda yasan suna gidan sai delu da baba haka Asharab ta cigaba da kula da kanwar kamar yanda tasaba doctor deen wanda yake duba su asibiti tun da ya ga Asharab yafara sonta shakuwa mai karfi ta shiga tsakanin su hakan ta Sanya kusan kullun sai yazoh ganin su dan ya fuskanci yaran suna bukatar kulawa

Kulawar da suke samu agurin doctor deen yasanya suka rage yawan damuwa...........


Wata rana doctor ya zoh gun Asharab suka fito zata rakashi munu tana zaune a gurin shakatawa tana ganin doctor saida gabanta ya fadi ta mike tsaye haka kawai ta tsinci kanta cikin matsanaciyar fargaba yana kallonta ya dasa A yar tambaya akanta jikinsa yabashi abubuwa da yawa game da ita"

Tana tsaye suka wuce ta gaban ta suka fita daga gidan suna fita doctor yace dear wannan wacece? .....yar kanwar mum ce ya akayi yace naga kamar batada gaskiya kamar yaya? Yayi dariya ba matsala amma inason nasan tarihinta dan tabbas inada shakku akanta



Toooooo=Ø(Þ munu wata kila watan kunyarki yakusa tsayawa

Allah dai yasa karshen wahalar kune ya zoh

KUYI HAKURI DA WANNAN =ØOÞ

TAKUCE A KULLUN



LAURAT M BELLO


SHARE& COMMENT...............




=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ



BANGARE NAH
(part of me)


=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ



STORY& WRITING
BY
LAURAT MUH'D BELLO

DAGA MARUBUCIYAR LITTAFIN
SUKHAINAH
ALKAWARI
AND NOW
BANGARE NAH
(part of me)






Ina farawa da sunan Allah mai rahma mai jikan



........4þã 1þã é#4þã 5þã .......



______________________"jikinta yana bari tabar gurin haka kawai take jin wani irin tsoro da shakku akan wannan mutumin........"

"Asharab! Tayi murmushin yake tace kada kadamu zan sanar da kai insha Allah...."


Munu ta shiga cikin gidan hankalin ta tashe jinta take kamar me saboda fargaba..... To wannan waye me yazoh yi anan gidan Anyah wannan mutun ne kuwa? ban taba ganin mutumin da ya tayar mun da hankali ba gani guda kamar shi, yazama wajibi nasan koshi waye nasan abunda yazoh yi agidan nan dole ne. nasan koshi waye da abunda yazoh yi anan gidan"

Har kofar gidan Asharab ta raka shi ya tsaya yana murmushi ya janyo hannun ta kanwata ki rage yawan damuwa please na gaya miki matukar muna tare bazaki koma shiga damuwa ba..... Asharab tayi murmushi tace insha Allah zanyi kokarin yin haka sukayi sallama ya ja motar sa yatafi"

Yana hanya yana tunanin Aunty su Asharab haka kawai yaji yana da shakku akanta tabbas akwai wani wani boyeyyen al'amari atare da ita kuma yazama wajibi ya gano ko menene...... Har zai nufi asibiti ya juya motar shi yanufi gidan kakan sa malan imam babban malamin ne anan yana matukar taimakawa jama'a....... Yana isa ya taddashi tare da mutane ya shiga gida hajiya ruma matar malan tana ganinsa tasoma dariya a'a a'a lallai yau muna da babban bako a gidan nan yau babana ne a gidan namu yayi murmushi yace eh hajiya yau dinnan na kawo muku ziyarah ta musamman wuni cur zanyi a tanadar mun fura da nono tayi dariya aikuwa yau fura har sai kaji ta isheka..... Yayi dariya ta shimfida masa tabarma ya zauna suka gaisa sosai tace ya su hajiya habiba suka nan qalau hajiya sunce a gaida ku dake ba daga gida nakeba naso muzoh da humairah tanata korafin sai na kawota gunki Ayyah kishiyata amma kuwa baka kyauta ba ai da ka, kawota inyaso idan muka gama zumudin juna sai mu farah fadan da muka saba dariya yayi yace humairah sarkin rigima ke nan zan kawota insha Allah cikin satin nan....... Ta kawo masa ruwa masu sanyi da Abinci suka cigaba da hirah har izuwa lokacin da malan ya gama da bakin shi.... Yaga motar shi, hakan yasanya yashigo gidan shima suna zaune a tsakar gida yayi sallama cike da barkwanci yace a'a lallai yau kace muna da manyan baki a gidan nan naga motar ka awaje to ina tare dabaki ya can gurin iyayenka? sunanan lafiya kalau malan"....... Yadan russunah ya gaida shi cikin girmama wa bayan sun dan taba barkwanci jika da kaka ......daga nan deen yace malan dama nazoh ne akan wata yar matsala wallahi malan ya dago ya kara gyarah zaman shi ya fuskance shi sosai matsala kuma deeni daga gun aiki ko kuwa...a'a


Wallahi wasu yarah ne suke tare da matsala kuma basuda wani wanda zai taimake su inajin tausyin yaran shine nazoh gunka koda akwai taimakon da zaka iya yimusu...... Malan imam yayi shiru na tsayin lokaci kana ya nisa yace Akwai wani abunda yake damun su ne? Eh malan wallahi yaran suna cikin matsala babba saboda ita kanwar yanzu haka a kujerah take kuma ayanda yayar take bani labari lalurar ta sameta ne haka siddam batar da hadari ko wata gagarumar faduwa ba suna zaune kawai sai ta farah yin wani abu kamar mai shafar jinnu daga nan sai kafa da hannu suka shanye bakinta ya rufe ayanzu haka ta kai kimanin shekara uku acikin wannan lalurar....... Ga yaran basuda wani mai taimakon su suna bani tausayi sosai shine nace zan sanar da kai koda akwai abunda zakayi akai"

"Tabbas suna cikin wani hali insha Allah za'a taimaka gobe kazoh dasu sai muga yanda za'ayi Amma tabbas acikin lamarin da akwai saka hannu aciki ansaka yaran agaba Amma insha Allah komai zai zama kamar ba 'ayibah...... Doctor yayi dariyar farinciki nagode malan Allah ya kara rufa asiri na gode. Malan yayi dariya ja'iri kodai da akwai surukata ne acikin su naga fah rawar kanka tayi yawa dariyar maganar malan tabawa deen dosai yasosa kansa batare da yace komai ba sai bayan la'asar yayiwa malan sallama yanufi gida......

Yana isa gida bai shiga cikin gidan ba ya wuce bangaren shi yadan watsa ruwa tukunnah ya shiga gun mahaifiyar shi..... Suna zaune a palour dukan su har mahaifin sa yayi sallama ya shiga a tare suka amsa fuskokin su akasa yakara sa shiga ciki humairah tana ganinshi ta rugo aguje ta rungume shi dady oyoo yoo dady oyoo cikin shagwaba tace dady ina icream dina dafa kansa yayi kashhhhh aikuwa na manta bansiyo miki ba yau shazumami sarkin kwadayi..... Ta turo baki agaba tace mukwance daga yau ni ba kawar ka bace dariya sukayi gaba dayansu ummah tace ashsha yau dai mungan ku aranah Abbii yace dama ni haka nake so zoh ga alawah nabaki tunda yau baki samu dan sadar taki ba...... Ta shagwaggwabe fuska zatayi kuka dady da gaske baka siyo mun ba ya janyota jikinsa da wasa nake dama nayi haka ne saboda naga yanda su Abbii zasuyi ne kuma na gani yafito da robar ice cream yace surprise aikuwa ta hau tsalle tana murna ta karba tayiwa su ummi gwaloh tace badai ansiyo mun ba Abbii yace kamomin ita nan ja'irah namafasa auren baturiya nake so bake ba wanka tarwada ai kuwa kamar jirah take tafara kuka ta kwashi robobin ice cream dinta ta bar falon dama idan akace ita baka ce to angama wasa =ØÞ yace rabuda Abbii ke baturiya ce tayi gaba abunta... "

"Ummi tana dariya tace humairah rigima bansan yaushe zata girmaba yarinyar nan deen yayi dariya yacezata daina sai nan gaba Abbii yace naga yau bakaje hospital ba lafiya?
Yace wallahi Abbii naje gidan su Ashraba ne bayan na dawo shine naje gun malan akan matsalar tasu acan ma na wuni..... Yace na gaidaku sosai Abbii yace masha Allah hakan yayi dama nima inason nace dakai matsalar yaran yakamata a dan saka malamai aciki a dinga addu'a.... Ai shine yasanya naje gunsa kuma Abbii malan fa ya tabbatar mun da sa hannun kamar yanda kace yayi dariya yace ni dama tunda kasanar dani mahaifiyar su tana raye amma ba ruwanta dasu nasan akwai wani abu
Yanzu yaushe zaka kai su..... "Yace gobe na tafi dasu Amma Abbii bana son yan'gidan nasu su sani fah banzan yanda zan fito dasu ba"....... "Wannan ba matsala bane Allah yakaimu goben za'a sanyanda za'ayi... Ya mike ummi bara naje na kwanta inason gobe na tashi da wuri zan dan shiga asibiti kafin naje daukar su.... "Bazaka ci komai ba yep am ok kinsan waccen tsohuwar bazata barni haka ba karamin fulon da yake hanun Abbi ya jefowa deen yace mamar tawace tsohuwa suka saka dariya gaba daya..... Yayi gaba yana dariya"
Yana shiga dakin sa yalalibo wayar shi ya soma kiran lambar Asharab tana kwance rungume da yar'uwar ta takasa bacci kwata-kwata rsyuwar duk ta isheta dama zasu mutu su huta da wannan bakar rayuwa sun rasa gata sun rasa madafah basuda wani tudun dafawa Abu daya yarage musu ayanzu sai deen shine kadai yanzu yake tausaya masu Farha tana daga nade a katifar su tayi shiru hawaye suna zuba tana tausayawa kanta da yar'uwar ta tabbas ta fahimci dan'uwa yanada matukar tasiri"

DAGA ALKALAMIN LAURAT M BELLO=ØŠÝþ


*idan kina bukatar cigaba da karatun wannan littafin zaki turo kudi naira 100 kacal ta wannan Account din RAMLATU BELLO MUHAMMAD 1381724404 ACCESS BANK idan kuma kati zaki/ zaka turo Katin MTN ta wannan lambar 08164949554*

*yanzu ne zanga irin soyayyar da kuke nuna mun*







COMMENT.....................






=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ



BANGARE NAH
( part of me)

=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ



STORY&WRITING
BY
LAURAT MUH'D BELLO

DAGA MARUBUCIYAR LITTAFIN
SUKHAINAH
ALKAWARI
AND NOW
BANGARE NAH
( part of me)




________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*=ئÜ{Arewa ginshi™in al'ummah}=ئÜ*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com




ALHAMDULILLAHI ALAH KULLI HALIN AMEEN>Ø2Ý




4þã 6þã ......é#......5þã 0þã




=ØÖÜ____________________=ØŠÝþ" Ta dago tana kallon fuskar ta tana jin matukar tausayin ta ahankali tace kiyi hakuri yar'uwa ta Allah kadai ne yasan irin yanda nakeji idan naganki acikin wannan halin dan kawai banida abunda zan iya yimiki ne....."


" *FARHA* da bata iya cewa uffan ta kalleta idanuwanta cike da kwallah yawunda ya dararo mata Asharab ta sanya tsumma ta goge mata cikin tausaya wa..... Tana murmushin karfafa gwiwa tace bana son naganki cikin damuwa yar'uwa ta kiyi hakuri...... Kinji insha Allah zaki warke kidawo kamar yanda kike ada ta kalle ta batare da ta iya cewa komai ba saboda bakinta baya iya furta komai saidai idoh.......

"Haka suka kwanta tanata tofawa yar'uwar ta addu'oin da baba direba yabata yace da ita taringa yimata kullin idan zasu kwanta....... Har sun fara bacci taji ringing wayar ta da kyar ta iya mikewa ta dauko wayar ganin mai kiran yasanya ta mike zaune cikin sauri doctor lafiya yake kirah irin wannan lokacin.... Ta daga wayar cikin girmawa tace hello cikin muryar bacci,

" Ayyah sweet heart na tada ke koh?"

Tayi murmushi kamar yana gabanta kada kadamu, ya kk?

" Shima murmushin yayi normal ya kanwata?"

Tadan juya ta kalli bangaren da take a kwance tace bacci take"

Good ina fatar dai tana samun sauqi Eh insha Allah hawaye suka cika idanuwan ta yanda yaji tayi shiru yasan kuka take yayi ajiyar zuciya mai karfi yanda zata iya jiyo sautin shi acikin wayar hummmmm!!

Zakifara koh ta langwabar da kanta kamar yana ganinta tace wallahi akullun ina kara jin jikina yayi sanyi idan naga yar'uwata acikin wannan halin..... Ya lumshe idanuwan shi yace kada ki damu insha Allah zata samu sauqi nan bada dadewa ba, ahankali tace inafatar haka doctor wallahi akullun sai nayi mafarkin yar'uwata ta jisauki tadawo normal kamar yanda take a da...... Yayi murmushi yace lokaci yayi kusa insha Allah,"

Yace gobe ki shirya da wuri zamuje wani guri insha Allah.......tayi shiru har saida yace Asharab kina jina kuwa?.......eh tace ahankali yace naji kinyi shiru tace ina tunanin yar'uwata ne wazan bari tare da ita kasan fah ni nake taimaka mata kayi hakuri bazan iya tafiya nabar yar'uwata ba........murmushi yayi yace kada kidamu da wannan tare zamuje har ita hasalima tafiyar saboda ita zamuyi...... Ina zamuje ne?

Idan muka je zaki gani, please ka gayamun dan Allah naki wayon sai goben kishirya da wuri idan naje asibiti zan biyo na dauke ku..... To Allah ya kaimu tace asanyaye sukayi sallama a tare suka ajiye wayar........


Kwanciya tayi shiru a zuciyarta tunanin yanda zasu fita daga gidan nan take..... Soronta daya ne kada Aunty munu ta ganta haka kawai tanajin shakku akan hakan......


Saida ta kara tofah addu'a tukunnah ta kwanta bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita......



Abangaren su hajiya salma kuwa suna ta cin amarcin su kamar ba gobe ta manta kwata-kwata da wasu yaranta abu daya takan zauna ita kadai cikin zurfin tunani amma kuma bata iya tuna komai *Bassam* kuwa yakasa aiwatar da komai akan su Asharab duk lokacinda zaiyi wani abun yakasa amma zuciyar shi tana son taimakon yaran.....





...................munubiya kuwa tun lokacinda sukayi ido biyu da doctor deen takasa samun nutsuwa tsoron yaron take matuka haka kawai idan ta tunashi sai ta tsinci kanta cikin faduwar gaba mai tsananin gaske.......tana son taje gun bokanta ta kasa zuwa jinta take kamar an daureta kwata-kwata batada wani kuzari...... Kai har kwaryar tsafinta ta kasa dubawa baranta taga sbunda ake ciki ita dai kata nan gata nan dai kamar marar lafiya........ Babban bakin cikin bassam ya daina wani kulata duk wasu kadarorin da take hari ta gurinshi ba wan I abunda yabada kullun idan tayi masa magana sai yace yana kan hada takardun ne......... Dan saukinta daya satar da takeyi a company itace kawai zatace tana dan rage mata radadi"

_____________Ayau duk suna gida kasancewar ba aiki weekend ne hajiya salma tana kan cinyar bassam kawai ta mike tsaye kamar mahaukaciya tayi waje cikin sauri munu tana zaune tana kari itama ta mike tana kwallawa hajiya kirah mum lafiya ina zakije batare da ta juyo ba tace naji kamar ana kirana ne ina zuwa gaban munu yayi wata mummunar faduwa darammmm!! dammmmm!!! A firgice tace kitsaya ba wani mai kiranki bara naje na gani a'a ni zan je da kainah hankalin munu atashe jikinta har wani rawa yakeyi saboda firgici.......

Alokacin su Asharab da doctor sun fice daga gidan bayan motar su kawai ta gani tashiga kwallawa baba direba kirah baba ummaru waye can yafita da mota yayi tsaye can yace hajiya bakonane lafiya hankalinta atashe tace wallahi kirana naji anayi kuma jikina yana bani a cikin motar can ne ka tsayar dashi dan Allah,

Baba direba da kansa yagama kullewa yace Ayyah ai ya tafi bana tunanin ma kinsan shi hajiya kawai dai kunnenki yake miki gizoh kamar ana kiranki arude tace baba ba gizoh bane tabbas naji ankirah ni har lekawa tayi get din gidan amma wayam ba kowa hakan nan ta juyo jikinta asanyaye jinta take wani iri yaudin nan"


Itakuwa munubiya har cikinta yafara kugi saboda firgici ahankali ta sulale tabi ta baya ta window ta leka tagani ko su Asharab ne hajiya tagani fuloluwan da baba direba yajerah ya rufe da zanin gadon ta gani kamar mutun akwance dan idan dai ba angaya maka filo bane bazaka taba ganewa ba ajiyar zuciya tayi mai karfi tare da murmushi mugunta tace wai Allah na gode maka ashe ba su tagani ba yau da na shiga uku......

Ta fito daga bangaren baba direba yana ganinta a zuciyar shi yace kifi naganinka mai jarkomah tare dayin murmushin samun nasara cikin nuna kulawa ta karaso mum muje ciki dama na gayamiki ba kowa Amma duk kin tashi hankalin ki....... Bassam dayake atsaye ya kai dubanshi kan munu ya wurga mata wani irin kallo yaja hanun matar shi suka shiga ciki suna shiga ta fashe da kuka mai karfi tarungume shi kam.......zuciyar shi a raunane ya soma magana kukan na menene ta dago jikakkun idanuwanta tace ji nake kamar narasa wani bangare a atare dani......munu datake shigowa alokacin ta wutsila kamar zata fadi saboda faduwar gaba..... Jikinta yana bari tabar gun tana shiga ta nufi kwaryar tsafinta jikinta na rawa......



Comment...................






=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ
BANGARE NAH
( part of me)
=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ



STORY& WRITING
BY
LAURAT MUH'D BELLO

MARUBUCIYAR LITTAFIN
SUKHAINAH
ALKAWARI
AND NOW
=ØžÜBANGARE NAH=ØžÜ
part of me


&BISMILLAHIR& RAHMANIR& RAHEEM&



________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*=ئÜ{Arewa ginshi™in al'ummah}=ئÜ*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


5þã 1þã é#5þã 5þã




&&&&"Jikinta yana mazari ta karasa gun ta dauko kwaryar tsafinta ta bude wani bakin abu ne ya mamaye cikin kwaryar babu wani abunda take iya gani aciki hankalinta atashe tasoma magana cikin razani tace meyake faruwa ne wai?




"Nashiga uku banga ta zama ba yazama wajibi na je gun boka tamike cikin hanzari ta shirya a gaggauce ta bar gidan ta nufi gun boka bawanda ma yasan tafice daga gidan"




"A bangaren su Asharab kuwa suna fita daga gidan basu zame ko inaba sai gidan malan cikin wasu daga cikin yaran malan ne suka dauko Farha aka shigar da ita cikin gidan Asharab da doctor kuwa suna biye dasu abaya har suka shiga ciki"




"Ganin halinda Farha take ciki yabawa mutane da dama tausayi yarinya karama tana cikin jarabawa haka, matar malan ma ta tausayawa Farha matuka an karbe su hannu bibiyu sun dan taradda layi sai da suka dan jirah tukunnah layin yazoh kansu atare suka shiga tare da doctor malan yana zaune rike da carbin sa yadan jima tukunah ya dago ya jima yana kallon Farha kafin daga bisani ya soma magana........ Yace zakiya tuna abunda yafaru tun daga farkon faruwar matsalar? Yake tambayar Asharab.



Daga kanta tayi tace Eh malan yace menene mafarin abun, ta kalli farha hawaye masu zafi suka fara zubo mata tace bazan manta ba muna zaune adaki muna hirah nida yar'uwa kwatsam wannan matsalar ta faru da ita haka kawai ta kwallah kara ta zube akasa shike nan ta koma haka yau ta kai kimanin shekara hudu je anan acikin wannan lalurar.



"Jijjiga kansa yayi yace kintaba saninta da aljanu A'a gaskiya banta'ba sanin tanada aljanuba abokin fada fah babu gaskiya mutun daya ce nasan basa shiru itace Aunty munubiya wacece kuma munubiya yar' sister mum din ce to ita nasan farha bata shiri da ita kwata-kwata........ Yayi shiru na tsayin lokaci sannana yabude alkur'ani mai tsarki yajima yana karatu daga bisani ya dago yace ciyon yar'uwarki ba haka siddan bane yi mata akayi.



=Ø(Þido a waje Asharab ta dago tare da mamakin maganar malan bakinta yana rawa tace yanzu dama ciyon nan ba haka kawai bane wani ne yayi...... Jijjiga kansa yayi yace tabbas wannan ciyon yanada nasaba da wani kuma najikin ku ne dafe kirjinta tayi tace nashiga uku malan waye wannan murmushi yayi yace kada kidamu da son sanin kowaye ayanzu ranar zata zoh kiwaye zai fada da bakinsa amma tabbas duka gidan ku yana cikin matsala kuma matsalar tana jikin ku har abunda mahaifiyar ku take yimuku ayanzu yanada nasaba da hakan"




Kuka ne ya subucewa Asharab tace me mukayiwa mutane mukuwa da suke kokarin tarwatsa mana gida ya dago komai ya kusa zuwa karshe insha Allah daga nan yasoma jero addu'oi yana tofawa a jikinta tana kwance agaban shi bayan yagama ya basu wasu ruwa galan yace wannan ruwan za'a dinga shafa mata duk dare idan zaku kwanta wannan kuma hayaki ne shikuma sau uku arana kidinga daura mata alwala duk lokacin da kika fuskanci ta karye alwalar dan gaskiya aikinda akayi mata bana wasa bane tsafi ne da siddabaru ba matsafa dole sai anyi da gaske dan kuwa maiyin aikin har yanzu yana kanyi bai fasa ba"




Son samu dama zaku bar gidan na wani lokaci dan tabbas aikin zai iya samun matsala idan har kuna gidan doctor yace to malan ko zan iya tafiya dasu can gun ummi inyaso idan tasamu sauqi sai amayar dasu can gidan nasu Asharab ta dago kaunar doctor tana kara shiga cikin jikinta kimar shi takara karuwa acikin zuciyar ta babu abunda Asharab tace malan yace hakan yayi yarinyar ma zata kara samun kulawa bakamar idan yayar kadai bace ai tama yi kokarin jinyar sun kai yammah agidan sannan ya dauke su zuwa gidan ummin sa"



" Ita kuwa munu tana fita ta hau taxi tanufi kauyen da bokan yake tafiya akeyi amma ganin take kamar direban baya sauri saboda a matse take dan haka suna tafiya tana zazzagawa direba masifar baya sauri har sun kusa isa motar ta tsaya cak yayi yayi amma mota kememe taki tashi gashi da sauran tafiya ran munu biya a matukar bace tasoma yiwa mai motar masifa Amma wallahi bakada mutunci dama kasan motar taka batada lafiya amma shine zaka daukoni kasan uzurin da nake dashi ne da zaka kawo ni nan ka jibge sai kace kayan wanki.... Ran dan taxi ya ka kololuwar baci yadago afusace yace ke malama daka ta mun bafa haifata kikayi ba tun dazu sai rashin mutunci kike yi dan kinga ban kula kiba kibarni da takaicin mota ta tsaya mun mana wallahi idan kika kara magana agun wallahi sai nayi maganin ki anan bakuma abunda zaki
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment