Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

wunin ranar duka ba inda taje office dinma kasa tafiya tayi haka tayita tunanin mafita".....

"Karfe 5:00pm dai-dai BASSAM yayi parking a kofar gidan hajiya salma a lokacin baba direba yana zaune shi kadai agurin yayi mamakin ganinsa a gidan yataso saboda ya murza masa rashin mutunci yace malan dakata gurin wa kazoh Bassam ya dago cikin kallon rainin wayo yace gurin masoyiya ta Salma nazoh ko kanada matsala da hakan..... "Gaban baba ya fadi ya yadago da sauri wace Salma"

"Yace wacce kasani bani guri kajikoh kana bata mun lokaci ya bangaje baba yayi shigewar shi ciki kansa tsaye tana zaune a palourn tana kallon wata tasha kamshin sa ne yafara ziyartar hancinta ta lumshe idanuwanta a tunaninta ko gizo ne kawai batayi auneba tajiyo sallamar sa cikin sassanyar muryarsa mai dadin sauraro ta jiyo a cikin sauri sukayi ido biyu da juna"............


"Dan Allah kuyi manage dashi zaman yana bani wahala yanzu"



TAKUCE A KULLUN

LAURAT M BELLO

SHARE
VOTE

COMMENT................




________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*=ئÜ{Arewa ginshi™in al'ummah}=ئÜ*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü


BANGARE NAH
(part of me)



=ØžÜ=ØžÜ=Ø•Ü =ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü



STORY & WRITING
BY
LAURAT MUH'D BELLO


Daga MARUBUCIYAR LITTAFIN
SUKHAINAH

AND NOW
BANGARE NAH
part of me



BISMILLAHIR~RAHMANIR~RAHEEM.


ina godiya sosai masoyanah masoyan littattafainah ILOVE U SO MUCH=Ø“Ü

Allah ya bar mu tare.....


Wannan shafin nakune yaranah kune rabin jikinah Allah ya raya mun ku AMEEN YA ALLAH.




________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*=ئÜ{Arewa ginshi™in al'ummah}=ئÜ*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com











..........2þã 1þã é#2þã 2þã ..........














"Cikin hanzari ta mike cike da mamakin ganin shi yana mai yi mata killer smile dinsa da yasaba ji take kamar kafarta bazata iya daukarta ba yakaraso gunta ya zauna"

"Cikin rashin kuzari ta zauna zuciyar ta tana bugawa cikin sauri ya, kula da hakan yayi gyaran murya ya soma magana"

"My soul" yakirata cikin sansanyar muryar shi" ta dago batare da tace dashi komai ba"

"Haka kawai idan yana tare da ita bata samun nutsuwa kwata-kwata, kwarjinsa yana yimata yawa sosai,...... "Gunda yake a zaune ya taso ya dawo daf da ita ahankali ya kirata"

"Meyasa bakya sakin jikin ki idan muna tare akullun bana son naga kina yin haka nafison ki saki jikin ki dani inason mu gina rayuwa mai dadi mu fahinci junan mu kafin mu zama abu daya,.... "Ta runtse idanuwan ta gam tana jin kalamansa suna shiga cikin jikinta tamkar kibiya!....... "Ina ma zata iya sakin jikinta kamar yanda yake bukata to kuwa da tayi hakan amma kash hakan ba mai yuyuwa bane agareta tana duba da makomar ya'yanta"

" Batayi aune ba taji ya kai hanunsa gefen fuskarta wani irin yanayi ne ya ziyarce ta na daban tayi saurin ja da baya hakan kuwa yayi dai-dai da shigowar Farha"

"Kirjin hajiya salma yayi mummunar faduwa rassssss!! rassss!! Haka kirjinta yacigaba da lugude tabbas idan farha ta ganta hakan kuwa zai zamar mata jin kunya marar misaltuwa"

" Tashigo palourn fuskarta cike da mamaki da kuma tuhuma ta daure fuska bako gaisuwa mum waye wannan?"

Ashrab da munu suma shigowar su kenan sukayi cirko-cirko a tsaye, "mum tambayar ki nake? kinyi shiru ta dago "bako ne tabata amsa bakon wa?"

"Ashrab! tace ke farha ya isa haka ta gaya miki bako ne ina ga ya wadatar ko"

"Ta dago a'a ni ban gamsuba sai anyimun baya ni saboda ayanzu idan da akwai abunda na tsana naga wani ya ra'bi mum bana son ganinta da kowa dan haka ina bukatar bayani"

"Ashrab ta dago cikin mamaki tace ai kema kinsan mum bazata taba soyayya da wannan karamin yaron ba, haba ai sai yazama abun kunya garemu da ita dakuma abun fade a unguwa"..... Jikin hajiya salma ya kara sanyi da jin kala mansu yayinda BASSAM ya kalli munu ta daga masa kai wanda hakan yana nufin wani abu"

"Ya karaso gaban Farha ya soma dafa hannayensa "wow Kin bani mamaki da kalamanki abun boye yau zai fito fili ni Bassam ba abunda zaku raina bane saboda ni zan zama baban ku nan da dan kan kanen lokaci"

"Kinga kuwa na wuce raini a tare suka dafa kirji me??=Ø(Þ "wannan ba abunda zai yuyu bane kana hauka ne, mum ce fah yakama ka bude idanuwan ka sosai ka tashi daga baccin da kake saboda na kula hankalin ka ya fara gushe.......

"Farha cikin tuhuma tajuyo mum ki sanar damu wannan ba gaskiya bane ni nasan wannan bazai zama gaskiya ba"

"Haba mum kada ki bar mana abun kunya ki rasa wanda zaki so sai wannan yakamata kiyi duba na tsanaki mum ta fashe da kuka mai ratsa zuciya ta bar gun a guje"

Hajiya salma ta dago zatayi magana Ashrab ta daga mata hannu bana son jin komai shirunda kikayi ya tabbatar mana da amsa ta share hawayen da suka gangaro mata ta shige ciki ,cikin sauri..


Munu ta karaso gunda hajiya take a tsaye kiyi hakuri kibisu ahankali kinsan har yanzu yara ne dama dole zaki fuskanci hakan daga garesu

Ta dago cikin damuwa tace har ga Allah na hakura dama ni kaina naga hakan bai kamata ba Bassam ba sa'an aure nah bane ba

Ta gado ta kalleshi yana harde da hannayensa a kirjinsa ya kura mata ido ahankali tace kayi hakuri aure na dakai bazai yuyu ba na zabi farincikin ya'yanah na hakura da nawa

Ta juya ta barsu anan tayi shigewar ta ciki

BASSAM dayaji maganar kamar saukar aradu cikin kirjinsa hankalinsa ya tashi matuka ya kalli munu yace ya kike ganin za'ayi dan naga kamar muna da sauran aiki babba a gaban mu

Ta ja ajiyar hummmm!! zuciya tace nima na ga haka kabani lokaci zanga abunda zamuyi amma ai idan sunsan wata basu san wata ba ni munubiya dani suke zancan......

"Duk abunda akeyi a kunnen baba direba da delu mai aiki suka kalli junah baba direba yace kinga abunda nake gaya miki ko dama nasan hadin baki ne

"Wannan yarinyar na tabbata da akwai abunda take shiryawa yazama dole mu dakatar da su kada su cutar da hajiya da yaran ta.... "Delu ta yi shiru can tace to yanzu ya zamuyi kenan"

"Yazama wajibi musaka ido sosai akan akan duk wani motsinta agidannan inaga ta wannan hanyar ce kawai zamu san abunda zamuyi"


"Delu ta fito daga maboyar su karab sukayi ido biyu da munu cikin izzah tace zo nan mekikeyi anan munafuka delu data tsure tace a'a ni ba abunda nakeyi dama tun safe nake aikin gyaran gurin

"Wani abu kika gani ne?"

'Munafuka ban yarda dake ba amma nasan maganin ku wallahi dan ni ba'a shigarmun hanci ban fato mutun ba, ya kamata ki kiyaye dan wallahi bani imani komai zan iyayi"

"Kirjin delu sai dakan uku-uku yake dan wallahi tasan sarai zata iya cutar da ita"

Bassam yana zaune ya dora daya kan daya yana nazarin abunda zaiyi dan ya ci alwashin bazai taba hakura da hajiya salma ba =Ø(Þtabdijam lallai akwai kura kenan....



*************** "BANGAREN Ashrab da Farha kuwa suna daki suna aikin kuka Farha ta dago ta kalli yayarta ta soma magana cikin shshekar kuka yanzu dan Allah mum ta kyauta kenan ni ina ganin idan tayi haka kamar ta nemarwa kanta tozarci ne a gurin ja'ama

"Ashrab tace ni bama wannan ba kankantar shi zaki duba anya ba da wata manufa kuwa yakeson mum ba zuciyata tafara zargin akwai wani abu acikin al-amarin"

"Saboda a ganina shi kansa yasan mum tafi karfinshi....

"FARHA! ta share kwallar da ta gangaro masa tace cikin tsiwa ai kuwa idan haka ne wallahi bazai taba cimma burinsa akan mum ba matukar ina raye"

"Me zakiyi akai?"

Ashrab" ta tanbaya,

"Idan har dole sai yayi shisshigin shigowa gonar mu to kuwa zamuyi maganin sa"

"Munubiya! ta da take kofar dakin a labe tanaji tayi murmushin mugunta ta bar gun tana shiga dakinta ta kulle ta nufin can bayan gadonta ta janyo wata a kwati babba ta bude sai ga wasu baby roba guda biyu babba da karama tayi murmushi tace

Babu wurin gudu babu gurin tsirah Farha dama na dade da sanin kece babbar matasala ta, dan haka zanyi maganin ki zaki gani idan har zaki iya dakatar dani daka cikar burinah kina gani za'ayi auren hajiya salma da Bassam batare da kin iya aikata komai ba..... A lokacin babu wani wanda zai iya furta komai"

"Nasha gaya miki kidaina shigarmun hanci"

"Babu abunda bazan iya yiba indai akan muradi nane dan haka kijirah ki gani zaki kare a kujerah bazaki kara moruwa ba har abada zaki tabbata zaune kuma babu abunda wani ya isa ya iya yimiki na taimako,..... "Ta kwashe da wata irin dariya karamar baby ta dauka ta karya wuyanta da kafar dama da hannun hagu ta sanya bakin tsumma ta toshe bakinta dashi acikin kasar da suke tayi rami ta cusa rabin jikin yar tsanar aciki tasanya makulli tarufe ta mayarda akwatin ma'ajiyarta ta gyarah gun bawanda zai iya sanin da akawai wani abu agun.........=Ø(Þ


"Mum tana shiga dakinta ta fada kan gadon ta zuciyarta tayi nisa cikin tunani tabbas yaranta sun fadi gaskiya Bassam ba 'sa'an aurenta bane yazama dole tayi gaggawar fitar dashi daga cikin zuciyar ta"

"Ta ja dogon ajiyar zuciya hummm!!

"Tamike ta nufi dakin yaran nata tana isa ta jiyo ihun Farha

"Da gudu ta karasa shiga dakin tashin hankali Farha ta koma tamkar aljanah kai ya juye kafa da hanunta sunjuya tamkar ba jikin bil'adama ba bakinta ya rufe ruf hajiya salma ta karasa gun cikin matsanancin tashin hankali Ashrab da abun yafaru a gaban idanuwan ta ba abunda take sai kuka Tana kiran sunan yar'uwar ta farha ki tashi dan Allah kiyi magana dan Allah ina

"Babu abunda yake fita daga bakinta sai yawu dan ya gagarah tsayawa fita kawai yakeyi idanuwanta sunyi ja kamar gauta ta nade wuri guda kamar tsummah=Ø-Þ

"Hajiya salma ta rugume yarta tana wani matsanancin kuka mai shiga zuciya"

"Kukanta delu ta jiyo tayo dakin cikin sauri tana zuwa taga halinda take ciki itama sai kuka munu datake daki a kwance tana jiran abunda zai biyo baya ta fito cikin hanzari ta nufi dakin"

Tana shiga dakin ta dorah hanu aka ta kurma ihu tanufi Farha lafiya meyasa meki haka ta fashe da kuka mai karfi.............




Takuce Akullun

LAURAT M BELLO


SHARE
VOTE
COMMENT.........................



=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ



BANGARE NAH
(part of me)


=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ




STORY&WRITING
BY
LAURAT MUH'D BELLO



DAGA MARUBUCIYAR LITTAFIN
SUKHAINAH
ALKAWARI AND
NOW
BANGARE NAH
(part of me)



Bismillahir~Rahmanir~Raheem....

Ina farawa da sunan Allah mai rahma mai jinkai....




________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*=ئÜ{Arewa ginshi™in al'ummah}=ئÜ*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com





.............2þã 3þã é#2þã 4þã ............







"Mum lafiya meya same tane tafada cikin matsanancin tashin hankali
Cikin kuka hajiya salma tace nima ban saniba shigowata kenan na taddata ahaka nashiga uku menene kuma haka zai faru da ya'ta"

"Delu mai aiki tana kuka ta soma magana ku tadata mana sai naga kamar wuyanta ya juye inaga fa aljanune suka shafeta kukan Ashrab yakara tsananta muna zaune fah haka kawai naga tafara wani abu kamar na masu al-janu shinefa ta fadi mum mutafi asibiti"

"Delu kira mana baba direba a kaita asibiti, cikin sauri tafita daga dakin kamar zata fadi baba yana zaune yayi nisa atunanin duniya delu ta iso cikin tashin hankali tana kuka baba! baba!! baba!!! Kazoh inji hajiya"

"Yamike lafiya meyake faruwa cikin kuka ta labarta masa abunda yake faruwa ya nufi cikin gidan da sauri "

"Yana shiga dakin hankalinsa yayi mummuna tashi hajiya yakamata muje asibitin kada a bata lokaci ta share hawayen fuskarta ta mike suka dagata tamkar wata karamar yarinya suka fita da ita"

"Idan ka gani abun tausayi ta koma kamar wata halitta ta daban cikin kankane lokaci"

" suka fito zasu tafi asibitin hajiya salma ta dago tana sharar kwalla tace ke munu ki zauna agida kada kuma a bar gidan ba kowa"

"Cikin jimami tace da kin bari mun tafi tare idan ina zaune anan bazan sami nutsuwa ba, a'a bai kamata abar gida haka ba kiyi hakuri ki zauna ta daga kai to mum zan zauna amma nasan ba zan taba samun nutsuwa ba.... ,,

"Baba direba yace hajiya ki hanzarta muje"

"To tace tashiga suka bar gidan acikin matsananci gudu"

Asibitin da suke zuwa can suka nufa suna isa aka dorata a gadon tura marar lafiya suka shigar da ita emergency a kofar likitoci suka tsayar da hajiya, ki dakata anan hajiya

Tana kuka ta tsaya Ashrab tazoh gunta ta rungume ta sukacigaba da kuka mai ban tausayi.....

"Baba direba ya matso kusa dasu yafara magana cikin rarrashi, hajiya ba kuka zakuyi ba addu'a za'ayi domin kinsan itace takobin mumini, insha Allahu abun zaizoh da sauki addu'a za'a dage da ita ta share hawayen fuskar ta, zanyi addu'a baba zanyi tafada cikin kuka kawai dai zuciyata ce nakejin tayi rauni, ina tsoron na rasa Farha kamar yanda na rasa daddyn ta zuciyata bazata iya dauka ba baba ta karasa maganar cikin matsanan cin kuka",

"Ta bashi tausayi matuka yayi kyaran murya yace insha Allahu bazaki rasa Farha ba ai cuta ba mutuwa bace ba zata tashi insha Allah"

"Ashrab da take zaune agurin tana sharar kwallah ta dago mum insha Allahu yar'uwata zata tashi bazamu rabu yanzu ba ki kwantar da hankalin ki"

"Har tsahon awa likitocin basu fitoba hankalin hajiya salma yakara tashi ta koma kofar dakin ta kifa kanta tasoma magana cikin rashin nutsuwa na shiga uku Allah kasa ya'ta tana raye ya Allah ka tausaya mun ina matukar kaunar yaranah Allah, bana son wani abu yafaru da Farha"

"Ashrab ganin mum dinta duk ta rikice yakara Tayar da hankalin ta ta fashe da kuka mai karfi baba diraba shi kansa dauriya kawai yakeyi Amma zuciyar sa a karye take

"Tunda likitoci suka shiga da farha aikin ceton ranta suke amma sun gagara gano bakin zaren duk wani abunda yakamat suyi amatsayinsu na kwararrun likitoci sunyi shi amma sun kasa gane komai

"Hasali ma biciken su ya tabbatar musu babu wani abu da yake damun ta Rass take komai na jikinta lafiyar sa kalau

"Su kansu sun kasa fahimtar abunda ya hana numfashinta ya dai-daita dan duk abunda yakamata suyi sun rigada sunyi daga karshe dai sun daura mata ruwa kawai saboda babu wani abunda zasu iya yi akan matsalar"

"Doctor yafito yana sharar gumi dan baima san abunda zai gayawa hajiya salma ba dan yasan ta tanada matukar rudewa akan abu, suna ganinsa suka taso dukan su saida ya dai-daita nutsuwar shi sannan ya soma magana kada ku damu ta farfado amma yanzu mun yimata allurai mun kuma saka mata ruwa insha Allahu idan ta farka zata samu sauki sosai..... "Allah sarki hajiya salma tayi murmushi tace Alhamdulillah yanzu zamu iya shiga mu ganta yace a'a bama bukatar haya niya saidai zuwa wani lokaci tukunnah,

" Ba damuwa likita Amma menene matsalar gabansa saida yafadi yace har yanzu bazamu iya cewa ga inda matsalar take ba saidai idan result din test din da mukayi ya fito tukunah"

"To shikenan likita mun gode ya wuce baba direba kazoh akwai wani magani da zaka je kasiyo bamuda shi a pharmacy kuma muna bukatar shi yace to yabiyo bayan likita........"

"Kai tsaye office dinsa suka nufa ya bashi izinin zama ya zauna doctor yayi shiru na dan lokaci can ya nisa yace baba direba nasan kai namiji ne so nasan zuciyar ka ba irin ta mata bace zaka iya daurewa baba direba yace Allah dai yasa ba wani abun ne yafaru da Autar hajiya ba.

"Idan ba abunda yafaru mu kanmu zamuyi farin ciki da hakan Amma baba maganar gaskiya ban gayawa hajiya komai ba munyi iya binciken da yakamata muyi amma mun kasa gano inda matsalar ciyon Farha yake inaganin matsalar kamar ba ta asibiti bace akwai wani abu,...... "Yace wani abu likita kamar yaya ban ganeba?

"Ina nufin A nemar mata maganin gargajiya zaifi inaga"

"Baba direba yayi shiru zuciyar sa a cinkushe hummm!! Babu babban tashin hankalin irin yanda za'a sanar da hajiya wallahi inajin tausayinta likita abunda zai faru ni zan dauki nauyin maganin batare da kowa yasani ba bana son kuma ka sanar da kowa ciki kuwa harda hajiya da duk wani wanda yake gidan koda wani zai tambayeka dan Allah likita kada kasanar da kowa"....

"Inaga abun zaifi tafiya yanda ake so itakuma hajiya kacigaba da karfafa mata gwiwa kuma bana son ka sallamesu yanzu saboda idan a kayi hakan zata shiga wani hali, kada ka damu insha Allahu ba wanda zaiji kamar yanda kabukata......"

"Yafito daga office din cikin hanzari yabar cikin asibitin"


"Munu suna fita daga gidan tamike ta nufi dakinta tana shiga ta fada kan gadon ta sheke da dariya mai karfi"

Hhhhhhhhhhhhhh!! Baby Farha kinyi bye bye da farinki har abada keda jin dadi sai a lahira idan anyi kijishi acan

Ni munubiya ba'a tabani azauna lafiya wallahi hummmm!! Tamike ta kara killace akwatin tayi shirin zuwa asibiti dubo farha da wani ruwa ababban galan =Ø(Þ wai munu ina zaki kai mugunta ne? >ØÝ




TAKUCE A KULLUM


LAURAT M BELLO


SHARE&
COMMENT







=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ



BANGARE NAH
(part of me)


=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ=Ø•Ü=ØžÜ





STORY&WRITING
BY
LAURAT MUH'D BELLO



DAGA MARUBUCIYAR LITTAFIN
SUKHAINAH
ALKAWARI
AND NOW
BANGARE NAH
(part of me)



ALHAMDULILLAHI ALAH KULLI HALIN~



Ina farawa da sunan Allah mai rahma mai jinkai.....







________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*=ئÜ{Arewa ginshi™in al'ummah}=ئÜ*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com









...............2þã 5þã é#2þã 6þã .............









"Ta fito cikin sauri kome ta tuna oho ta koma daki can ta nufi wata katuwar kwarya ta leka baba direba ta hango yanata sauri yanufi wani gurin tayi murmushi tace baba ai ka makara ta sanya hanu ta juyo dashi yadawo ta rufe , tarufe dakinta ta nufi asibitin"

"Delu tana zaune duk batada nutsuwa so kawai take tasan halinda Farha take ciki, amma kuma taji shiru tace bara na kira baba direba naji nasan suna tare yanzu, tana kira ya dauka bayan sun gaisa tace ya mai jikin kuwa naji shiru nace bara na kira naji "

"Maijiki tana nan taji sauki sosai nafito daga asibitin Amma gashi zan koma nama rasa dalilinda yasanya na fito nasan suna bukatata akusa ina hanya zan koma"

"To baba idan kaje ka gaida su dan Allah, Allah ya sau'waka ta kashe wayar ta"

"Samun guri baba direba yayi ya zauna yayi takumi ahankali yafara tunanin to ma wai me nafito yi ne na manta kwata -kwata yayita son yatuna abunda yafito yi amma ya manta haka yatashi ya koma asibitin batare da ya tuna abunda zai yiba.,,

"Doctor yana ganin sa yayi murmushi yace baba har ka dawo muje office koh to kawai yace yabi bayan shi"

"yana shiga doctor yace ya akayi baba kasamu kaje kuwa baba direba daya kasa fahimtar doctor yace naje ina abun yabashi mamaki yace maganar maganin da za'a karbowa Farha yace na Tuna dama magani zan karbo koh bara nayi azama naje dan mantawa nayi kwata-kwata

Doctor yace kamanta? anan fah mukayi magana da kai amma daga fitar ka har kaman ta To Allah ya kyauta..... Ya mike bara naje doctor yamma tana yi yana fita yanemi guri ya zauna yana ji ajikinsa yana son yayi wani abu amma ya kasa kuma baya jin zai iya aiwatar da komai"


"Yana zaune munubiya ta zoh ta wuce yana ganinta saida gabansa yafadi haka kawai yakejin yau yana masifar tsoronta kai tsaye dakin da aka kwantar da Farha ta nufa su Hajiya Salma da Ashrab suna zaune ba mai cewa komai zaune suke abun duniya ya ishesu ta shigo da Sallama suka dago Ashrab ta Amsa Aunty kece tafe Eh Ashrab nakasa samun nutsuwa wallahi dana fito ma harda magani naje na karbo mata zaiyi matukar taimaka mata insha Allahu zata samu sauki.....,,,

"Hajiya Salma ta share hawayen da suka gangaro mata mungode munu da irin taimakon da kike akan mu hakika kedin ta daban ce Kada ki damu mum ai duk yiwa kaine kinsan Farha Cousin dita ce koba komai yar'uwa ce a gareni idan ban yi mataba wazan yiwa Ashrab ta taso ta rungume ta muna kaunar ki Aunty tayi murmushin samun nasara tace nima haka.."

"Ta dago mum ga maganin ki tayar da ita abata tasha hajiya salma tace likita yace kada a tayar da ita a barta har sai tatashi da kanta sunyi mata alluran bacci ne...... "Ohhhh na gane to ba damuwa dama yace a tabbatar an bata acikin lokaci ne amma baida matsala ta dan jima a asibitin sannan tace mum bara naje gida anbar delu ita kadai idan na koma sai itama tazoh ta kawo muku abinci nasan akuci komai ba"

"Ba matsala Amma kice abunda za'a kawo ba mai yawa ba saboda babu wani kwanciyar hankalin cin shi

"Ba damuwa ta mike tabar dakin tana fita suka dan tattauna da doctor sannan ta bar asibitin"

"Kai tsaye gidan ta nufa tana zuwa delu ta fito zuwa asibitin wannan shi yabata damar shiga dakin margayi Tasoma binciken inda aka ajiye takardun kadarorin hajiya salma saida ta duba ko'ina acikin dakin babu taje dakin hajiya salma nan ma ba abunda ta samu taji haushi matuka tafito daga dakin talalibo lambar BASSAM"

"Yana kwance tunanin hajiya salma ya addabi zuciyar shi kiran munu ya shigo wayar shi ya dauka cikin rashin kuzari yace"

"Hellooo Ahankali munu ta lumshe idanuwan ta tace baby ina bukatar ka a kusa dani yayi ajiyar zuciya nima haka Amma kinsan dole yanzu muyi baya-baya da junan mu kada asirin mu ya tonu"

"Haka ne Amma ai suna asibiti ba kowa a agidan ni kadai ce zamu iya haduwa batare da kowa yaganka ba,....... "Ya mike cikin hanzari yace waye ba lafiya tayi dariya tace uwar Giggiwa da rashin kunya mana kasan batada kunya nikuma banida hakuri saboda haka nayi maganin bakin tsiwarta kaga banida wata sauran damuwa da ita..... Yanzu kuma haka zata karasa rayuwar ta har lokacinda ta Allah ta kasance da ita....... Ya rintse idanuwan shi baya son halin munubiya na wannan bakar munguntar amma ba yanda zaiyi ya nisa yace haka yayi dai-dai Amma bakya ganin hakan zai iya zama matsala agaba"

"Idan zakiyi abu ki ringa tunani fah"

"Dakata malan kacire kalmar matsala da kake yimun fata duk a rayuwata ban taba cin karo da matsala ba barantana dan na ta'ba yar'tsakuwa Farha na hadu da wata matsala kada nakara jin wannan furucin yakara fita daga bakinka dan Haka ka kiyaye",,

"Am so sorry my dear ba wani abu nake nufi ba naga kin daui zancen da zafi sosai"

"Na dauka gaskiya, kaga malan kazoh ina da bukatar ganin ka diffff ta kashe wayar ta tana huci kamar
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment