Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

→BA NI NA KASHE TABA← PART 1 na bigboy isah
me yasa kakashe ta me tama kane da zaka kashe
musu ita banyi zatan zaka iya kisan kaiba
zaharaddin sannan ta sake shi daga shake mai
wuya da tayi idanun shi sunyi nare nare ta koma
gefe tana kuka a hankali idan shi cike da kwalla ya
durkusa yace momy wllh BANI NA KASHE TABA
cikin kuka ya karashe maganar yace amma nasan
ba wanda zai saurare ni ya fashe da matsanan cin
kuka abun tausayi ji sukayi ana girgiza get din
gidan kamar za'a karya shi Daga ji kasan katti ne
majiya karfi a kofar gidan sai cewa suke wllh a fito
muna da dan mafia nan bazamu yarda ba ya yanka
masoyiyar sa bale yaran mu da kannan mu ay wllh
bazamu yarda ba sai mun kashe shi shima. da
maman deeny da kuma shi kanshi zaharadeen din
duk sun firgita da jin kalaman jama'ar nan na kofar
gida tunani suke ya za'ayi lalai idan ta basu deenyta
kashe shi zasuyi shima tunani yake bazai iya mika
kansa ba idan ya mutu mahaifiyar sa wane hali zata
shiga. suna ta faman saka wannan kwance wancan
su kuwa matasan nan tuni sun gaji kuma sunga
anki bude get hakan yasa aka nemo jarkar man
fetur a cewar su idan suka ji an fara toya gidan sa
fito su kuma sai su kama zaharadeen din su kashe
kamar yadda suke zargin yayi kisan kai. haka suka
fara watsa fetur a gidan su momy suna cikin tunani
sai sukaji ana jika su da ruwan fetur da dai suka
fahimci fetur ne sai duk suka tsorata jikin su ya
fara bari suka rasa abun yi momy cewa take cikin
kuka ay kaga abunda ka jawo mana yanzu gashi
zasu toya mu da rai kamar wasu yan wuta lol.
deeny yace wllh momy BANI NA NA KASHE TABA
momy tace towa ya kashe ta hawaye kawai naga
ya sake zubowa a fuskar shi karan jiniyar motar
police suka ji a waje ana ta koran mutane da ke
kokarin cin nawa gidan wuta dan har an samo
ashana ana kokarin kyastawa police da duka suka
kori mutane suka je kofar gidan cikin murya me
karfi suka ce zaharadeen ka fito ka mika kanka ga
hukuma dan tabatar da rashin laifin ka ko kuma
laifin jikin shi na rawa sai kuka yake yana wallh
BANI NA KASHE TABA2 momy ta kama hannun shi
tace hakuri zamuyi mu rungumi kaddara isha allah
bazaka cutu ba kayi hakuri ka mika kanka ina ga
hakan zaifi sauki. a gare mu ta karashe maganar ta
cikin kuka haka ya tashi yana tafe yana hawaye
yana juyowa kamar ya bude get din kuma kamar ya
bari a cikin zuciyar shi kuwa yace gwara in fita a
kashe ni ma hakan zaifi min sauki ya kalla sama
yace allah ka fitar dani daga zargin nan da ake min
yana bude get wani police yayi carat ya damke shi
gam sannan wani ta kama hannayan shi ya maida
su baya aka samai ankwa a hannayan shi aka tura
kyyarshi har cikin motar police din mutane ne suka
fara jifar shi suna sai mun kashe ka wllh bazamu
barka ba haka yasa police din cikin hanzari ya
warci motar tasu sai police station ana zuwa aka
nufi sel da shi aka rufe ganin an rufe deeny a sel
yasa na tsaya nan ku biyu ni dan jin labarin

→»ku dinga comment
→»yan mata da samari ayi invite
→»dan momy na gaisuwa
↓Yauwa haka nakeso
comment↓
bigboy



→BANI NA KASHE TA BA← PART 2 na bigboy isa
a gidan su halima kuwa ganin su nayi jigum jigum
kowa yayi ta gumi sai hawaye hajja hauwa hawaye
take tana fadin zaharadeen ashe ba san halima
kake ba ashe duk san da kake na kaje ka kashe ta
ne kayi kudi da ita ta karashe maganar da fashewa
da kuka kacuce mu deeny kaci amanar mu ka
kashe muna yar mu wace ita kadai muka haifa. kiyi
hakuri maman halima wllh wllh wllh sai an kwatar
muna hakin mu sai inda karfina ya kare wllh bazai
kashe muna diya a banza ba sai an kashe shi
shima hawaye ne suka gangaro fuskar shi. jikin
fushi ya tashi ya fita hajja hauwa kuwa kanta a
kasa kuka kawai take. momy kuwa tana ji an tafi da
deenyta cikin hanzari ta dakko hajib dinta ta saka ta
fito da sauri ta kulle gidan kunya duk ta cikata duk
majalisar data wuce ana nunata ana cewa ga
mahaifiyar yaran nan da kashe budurwar sa haka
tata wucewa ana nunata har takai gidan su kawun
deeny wanda shine kanin mahaifin deeny da yake
allah ya amshi ran mijin nata wanda shine mahaifin
zaharadeen tana shiga cikin gidan da sallamar ta
aka amsa ta shiga suka gaisa da amina matar
kawo kenan aka zubo mata koko da kosai dama
bata karya ba amma ko kallan shi batayi ba saboda
abunda ke damun ta su kam basu san komai ke
nan ba saboda labari bai kawo musu nan ba amina
matar kawu tace mamar deeny lafiya naga duk
fuskar ki cike da damuwa daidai nan ne kawu ya
fito daga ban daki kallo daya yama matar yayan
nashi yagane ba lafiya ba alamun tasha kuka ya
karaso wajan a lokacin da yake tambayar ta lafiya
kuwa tana kallan shi ta fashe da kuka a lokacin ne
duk sukayo kanta suna menene ya faru mamar
deeny lafiya kuwa. nan ta fara magana cikin kuka
tana deeny ne da maryam ta maimaita3 har sau
uku cikin kuka ta kasa fada.amina ce ta kamata
tana rarashin ta sannan tadan rage kukan kawu
yace me yasama zaharadeen din da maryam
kuma? nan ta fara shesheka tana musu bayani.tace
maryam tun jiya da ta fita islamiya jiya da yamma
to bata sake dawowa ba har yanzu deeny kuma a
yanzu maganar da nake muku yan sanda sun kama
shi sun tafi da shi wai ana zargin shi da kisan kai
nan ta fashe da kuka su kuma duk suka kama
inalilahhiwa ina ilaihir raji'u
inalilahhiwa ina ilaihir raji'u
inalilahhiwa ina ilaihir raji'u
suke fasa
*****************
acan kuma DPO ne yasa deeny a gaba yana
bazaka fada mana gaskiya ka hutar da kanka kuma
ka hutar damu ba yace yalabai wllh wllh BANI NA
KASHE TA BA dpo ya kara kallan shi yace watto sai
jikin ka yayi tsami zaka fada ko?…… tsoran kar a
hada dani ne yasa na tsaya a nan nima
mu hadu a whatsapp→ 08096831009 Group
bigboy
.


→BANI NA KASHE TABA← PART 3
na bigboy isah
a ranar koni da nake gefe na tausayawa
zaharadeen irin dukan da yasha suna dukan shi
suna bazaka fada mana gaskiya ba shidai abun da
yake cewa kawai wllh BANI NA KASHE TABA. BANI
NA KASHE TABA FA. haka akaci gaba da narkar shi
wai yaki fadan gaskiya har saida ya sume.
***************maman deeny kuwa gidan kawu ta
koma da zama kullum cikin kuka tana tunanin halin
da ta tsinci kanta a ciki yaran ta biyu su duka ba
daya har gwara shi deeny ma tunda ansan yana
hannun yan sanda amma ita kanwar tasa maryam
kenan ba'a san inda take ba kawu yayi yawo har ya
gaji ya dawo gida yana yin sallama suka amsa su
mashi da sauri maman deeny ta mike tana fadin
angan ta anga maryam dina kuwa? gani tayi ya
sunkuyar da kanshi kasa alamun ba labari kenan ai
kuwa ta dora hannun wanta akai ta saka uban kuka
matar kawu dake gefe ita ce ta taso ta rungume ta
tana cewa haba maman deeny hakuri zakiyi kuka
ba namu bane adda'u itace ma fita a wannan lamari
ita ma hawayan ne a fuskar ta. salama suka jiyo a
kofar gida da sauri kawu ya fita dan ganin wake
sallama police yagani cikin kayan aikin sa dan
sandar ya mikawa kawo hannun suka gaisa sannan
dan sandar yace kaine kanin mahaifin zaharadeen
ko kawu yace kwarai kuwa nine police din ya ciro
wata farar takar da ya mikawa kawo yace wannan
san maci ne daga kotu ku gaugauta samun lauya
domin gobe gobe zamu shiga kotu a bisa kes din
danku dan yaki amsa laifin sa a hannun mu kawu
ya karba hannun shi har bari yake yace na gode
sukayi ban kwana har ya juya zai shiga gida dan
sandar yace amma fa ku gaugau ta samun lauyan
ku saboda gobe ko baku da wani lauya bazai hana
zamanan ba a gobe haka kawu ya koma cikin gida
cike da damuwa yana ta tunanin shi ba kudi gare
shi ba ga basu dawa kadara da zasu sayar su
dauka lauya. abban aliyu me ya faru maman deeny
ce ta je4 mai wannan tambaya bai ce mata komai
ba kawai takardar dake hannun sa ya mika mata ta
karba tana bude wa ta fara karantawa sai hawaye
tana tunanin a ina zasu sama lauya Barrister
fadilah ta tuna sai sukaji tace alhmdulilah suka juya
suna kallan ta itama juyowa tayi sannan tace inada
kawata Barrister fadilah nasan tabbas zata taimaka
min idan na nufe ta da wannan alamarin sannan
kwarariyar lauya ce itama. gaba daya sukace
alhamdulilah saiki tashi ki shirya maman aliyu ta
rakaki inji kawu.
mu hadu a whatsapp→ 08096831009 Group
bigboy






on-line 14.04 21:00
→BANI NA KASHE TABA← PART 4
na bigboy isah
******************
alamarin maryam kuwa ranar asabar tayi wankan
ta tasaka kayan islamiya tayi ayr kwaliyar ta ta
dauko jakar qura'a nin ta ta fito tace mama zan tafi
makaranta maman deeny tace to maryam adawo
lafiya ayi karatu da kyau tace to momy zamu dage.
har ta fara tafiya tayi taku uku sai kuma ta juyo
tace momy wai har yanzu su yaya zaharadeen
shida halimar basu dawo ba ne momyn tace wllh
kuwa kinga har yanzu basu dawo ba. maryam tace
uhm nidai na tafi karna makara sai na dawo bye
bye tafita tana tafiya tana tilawa dan karta manta
karatun da sukayi jiya sai ji tayi mota ta faka ta
gefan ta da yake dan titin yau weekend ba jama'a
sosai duk ana gida ana hutu wasu kartai biyu suka
fito a motar cikin hanzari suka kamata suka rufe
mata baki sannan suka jefata cikin mota sukayi
gaba da ita sunata tafiya kamar bazasu tsaya ba ita
kuma kuka take har ta gaji tayi shiru sai kuma ta
fara ajiyar zuciya. wayar ogan yan daban ne tayi
kara ya daga ya risina yace oga an cika aiki ga
yarinyar da ka ce mu kamo ta yanzu ma muna tare
da ita. kome ogan yace mai oho jinayi yace ok sir
ya kashe wayar ya mayar aljihu sannan ya juya ya
kalli yarinyar da idanun ta duk sunyi jawur yace
kuba marar kunya ba zaku gane kun tabo wuta mun
kashe dayar sannan kema an bamu umarnin mu
kashe ki amma ba zamu tashi a tutar babu ba sai
mun danaki tukun nan zamu kashe ki. hannu ta
dora a kai ta fasa wani uban iho hade da kuka.
wuka yaciro yace sheet yi mana shiru, kallo daya
zakawa mutumin ka gane bashi da imani gashi baki
ga wasu jaja yan idanuwa fuskar nan tashi ba
annuri sai kace hata damusa maryam kuwa ta kara
kankame jikin ta tana kuka ciki ciki ana cikin tafiyar
ne naga sun faka motar kome ya faru oho sun fito
duk su ukun ba mai fara'a a cikin su dayan naga ya
zagaya baya sannan ya dawo yace oga akwai
matsala fa munyi faci a bayan nan ogan ya daka
masa tsawa maryam dake cikin mota har dan
fitsari ya kufto mata dan tsananin tsora lol. ogan
yace bazaka kunce tayar ka koma baya wancan
dan garin ka wo mana faci ba ka tsaya kana wani
yen yen yen wuce daga nan dallah. cikin hanzari
naga wanda ake kira kumurci yaje ya fara kunce
tayar ya sabe ta akafada ya koma baya wato garin
da suka wuce to gashi dare ya fara yi shi kuma
ogan ya dauki gallan yace wa wanda ake kira da
mugu yace kai zanje wancan gidan man wanda
muka wuce a baya zan je in karo mai dan ina
tunanin wannan bazai karasa damu kano ba
sannan yace ka kula da wannan yarinyar sosai
kuma kasa ido a kanta sosai yace angama oga shi
kuma ya juya ya fice ya bi bayan kumurci suna
tafiya shi kuma ya shiga gaban mota ya kuna
music yana yi yana girgiza kai yana rawa ita kuma
maryam tunanin tserewa take yi sai sake sake take
yi can sai naga tayi a jiyar zuciya ko me ta tuna
oho nima cewa nayi my queen me kika tuna………
Naku bigboy > whatsapp no 08096831009







→BANI NA KASHE TABA← PART 5
na bigboy isah
jakar ta naga ta bude ta ciro wani lacasera mai
sanyi kuma sai naga ta dakko wasu kwayoyi cikin
hanzari ta zuba a cikin kwalbar lacasera din shi
kuma mugu yana can yana jin music din sa har ya
manta tsaron mutum yakeyi can sai naga maryam
din ta dan matso tace bawan allah dan allah zan
sama breadi ko rabi ne zan dan hada shi da
wannan ne ince sai ta dago lacasera haba baaban
yana ganin lemo gashi dama yunwa yake ji ya
kwace kwalbar tare da cewa yar iska waya ce miki
yara suna shan irin wannan miko shi yana amsa
yaji da dan sanyi sanyi kuwa ya kafa kai sai da ya
shanye shi kaf sannan ya yi wurgi da robar
lacasera din waje ya juya ya kalle maryam yace ina
sauran nan take idan shi suka fara lumshe wa
kamar wanda yasha ya bugu. ita kuma a zuciyar ta
karku so kuga farin ciki sai dadi take ji.sai a lokacin
na kula ashe maganin barci ta zuba mai mutumin
ku ya langabe kai ya fara sharar barci hada
minshari. maryam din tana ganin haka sai ta bude
motar da sauri ta fito ai kuwa tace kafa me naci
ban baki ba nan ta ari ta kare tayi cikin daji da gudu
su maryam anga mutuwa saida tayi gudu 5 mint
sannan ta sama wani gidan fulani gari ne karami
duk yan filo ne a garin ji sai daka ake yi can kuma
anyi wa wani daga cikin yaran fulanin biki an dakko
makadi sai cashewa akeyi. alamarin su ogan yan
daba kuwa tare suka taho shida kumurci sai wajan
magari ba suka dawo tun daga nesa suke jin music
na tashi a cikin motar su ogan yace kutt lalai
wannan yaran zai ci uban sa har ya sama damar
kunna waka a motar nan kamar motar uban shi
zaici uban shi bari mu karasa tun daga nesa
kumurci yace oga yarinyar nan fa kamar bata mota
a fusace ogan ya juyo yace zan mare ka dan
ubanka kasan abunda kake fadi kuwa. to ka muna
shiru ai kuwa suna karasa wa sukaga mota wayam
ba maryam sama ko kasa can gidan gaba kuma
mugune sai sharar barcin sa yake tuna ogan yaje
ya bude gidan gaban ya kwada ma mugu mari.
cikin barci ya tashi yana iho yana wllh na tuba
bazan kuma ba. yana ta yan surutan shi dai ogan
ya daka masa tsawa wanda ni kaina saida na
zabura saura kadan in yarda wayar in gudu lol.
amma saboda tsabar juriya irin tawa tsayawa
kawai zan yi anan *************
ku sani wannan abunda ya faru da maryam kanwar
deeny ka sancewar itama tunda ta fita islamiya
bata kara dawowa ba…………Naku bigboy > whatsapp no 08096831009


mu hadu a whatsapp→ 08096831009 Group
bigboy
on-line 15.04 08:12
→BANI NA KASHE TABA← PART 6
na bigboy isah
tsawar da ogan ya mai ita ce ta dawo da shi
hayyacin sa ogan jikin murya mai kara yace ina
wannan yarinyar?. nan fa mugu ya fara kame kame
yana. dama uhmm uhmm ogan yace dama me
bazaka fada ba saina rabama kai biyu ogan ya fiddo
wukar shi yace wllh kayi wasa zan raba maka kai
biyu. jikin mugu na rawa yace oga inaga sayan
lacasera ta biku baku hadu a hanya ba ni dai na san
na kwace mata lacaseran ta ina shanye wa barci
ya kwashe ni ban farka ba sai ynz wllh oga. nida
nake gefe dariya na kama yi ma mugu. tsawar da
ogan ya sake yi ita tasa na kama baki na nayi
shiru. ogan yace kasan me kake fada kuwa kana
nufin ta tsere yanzu kasan ko asarar nawa ka jawo
mana kuwa ga asarar yarinyar sannan ga na 3m
naira ogan ya jingina kai jikin mota yana wani huci
kamar zaki. shi kuma kumurci da yake gefe ji
sukayi yace alhamdulilah su duka suka kalle shi
yace oga yadda zamuyi kawai muhau motar mu
muyi gida tunda dama mai gida yace a kashe ta to
kaga kawai sai mu koma muce angama aiki duk
mun kashe su tunda kaga wannan yarinyar dai
bazata iya tafiyar da zata sama gari a cikin wannan
daji ba nasan zatai ta yawo ne har yunwa ta kashe
ta kaga mun cika aiki kenan HAHAHAHAHAHA
dariyar mugun ta ogan yayi sannan kamar hadin
baki su duka suka dauka HAHAHAHAHAHAHAHAHA
sai dariyar suke *************
maryam kuwa zuwa tayi wajan masu kade kadan
nan ta zauna ta fara tunanin maganar ogan yan
daban nan da yace mata mun kashe dayar saura ke
ita a tunanin ta to wacece dayar? amsar data kasa
bawa kanta kenan ta dago kanta sai kalle kalan
yaran fulani take can ta hangi wani bakin maciji ya
doso wajan wasu yan mata su biyu dake zaune a
gindin wata bishiyar bedi da gudu ta nufi wajan su
tana kutashi maciji maciji suma da gudu naga sun
watsa suna iho aradu mashiji aradu mashiji kafin
kace me samarin fulanin nan sun rufe macijin da
duka dama kunsan basa rabuwa da sanda ga kuma
wuka. ita kuma yar fulanin zagayo wa tayi tana
neman maryam data taimaka musu can ta hango ta
a inda take zaune da ta kuma yin tagumi abunta a
hankali yar filo ta matsa wajan ta a tsorace tace
hannuka ko maryam ta dago kai tace yauwa
sannun ki sannan yar fulani tace amma naga
kamar kai bako ne anan ko ko zaka iya fada min
sunanka? ita kam maryam abun ya daure mata kai
an maidata namiji bata san haka suke maganar su
ba mace a maida ta namiji namiji kuma a maida shi
mace. can dai maryam ta dago kai ta kalli bafula
tana tace nifa macece ba namiji ba kuma sunana
maryam. sai bafulata nan ta kwashe da dariya tace
kayi hakuri haka maganan mu take. taci gaba da
cewa ni sunana aneesat amma mutanan rigga nan
suna cemin anne. maryam tace gud nice name
aneesat. ita kuma anne budar bakin ta sai cewa
tayi kice naman aneesat lol. maryam ta kwashe da
dariya tace cewa nayi nice name. ina nufin sunan
yayi dadi sannan annee tace ohho hk kike nufi
kenan. haka dai suka ci gaba da hira tamkar
kawaye. wanda suka saba da juna can dama. dan
itama anne har waje ta samu ta zauna sai labari
suke maryam na mata dariya yanayin hausar su ta
fulani. anne tace………
mu hadu a whatsapp→ 08140027062 Group
maman sabir
on-line 15.04 14:45
mungode
mu hadu a whatsapp→ 08096831009 Group
delete
bigboy
on-line 15.04 15:27
→BANI NA KASHE TABA← PART 7
na bigboy isah
anne tace wai shin gidan suwa kika zo ne awannan
riggar tamu?. maryam ta sunkuyar da kai sannan
sai hawaye suka kwararo mata. tace sato ni akayi.
nan ta kwashe labarin duka ta fadawa aneesa.
anne tayi mamaki dajin wannan labari. ta gyada kai
tace tabb aradu kinyi gudun mutuwa. ko kin san
daga nan zuwa bakin titi tafiyar wuni guda ce kuwa
gamu wanda muka saba ma kenan. maryam ta
bude baki tace wuni guda fa kika ce?. annee tace
kwarai kuwa. maryam tace allah ne kawai ya cece
ni daga sharin su. anne tace yanzu kinga dare yayi
tashi mu tafi gida sai mu kwana tare. maryam tayi
godiya ta tashi suka tafi.**************
acan kuwa gidan kawu, kawu ne yake cewa wai ni
shin da ake cewa deeny yayi kisan kai wa ya
kashe?. hawaye ne suka biyu ta kan fuskar maman
deeny sannan tace gawar halima aka gani a motar
shi sannan gawar halima aka samu a cikin nan ta
kara fashewa da kuka. maman aliyu ce ke rarashin
ta tace kiyi hakuri yanzu tashi mu tafi gidan br
fadila din dakyar aka samu tayi shiru ita dai abun
ya mata yawa ba maryam ba zaharadeen din ta
tasa mayafi suka fita suka tsaida nafen sai gidan
barrist fadila. sunyi sa'a tana gida kuwa da yake ba
wani aiki suna isa ta tare su hannun bibiyu tasa mai
aiki ta kawo musu abinci da ruwa da lemo haka
kuwa aka kawo musu abinci aka girke a gaban su
ga lemoka kala kala. su duk hankalin su ba'a akan
abince yake ba su brfadila suke su ta fito su mata
bayani kawai. can after 5mnt sai gata ta fito daga
daki fuskar ta cike da murmushi tace a su maman
deeny manya ba'a ko ganin ku yanzu yaushe rabo
mu hadu. maman deeny kuwa murmushi ta nema
ta rasa duk batada sukuni. tace ai kune manya
bakwa ko neman mu. kallo daya brfadila tawa
maman deeny ta fahimci ba lafiya ba. taga duk ta
wani canza. tace maman deeny lafiya kuwa. haba
sai hawaye kamar jira suke dama nan ta kwashe
labarin duka ta fada wa barrist fadila sannan tace
yanzu haka sunce gobe gobe za'a shiga kotu
saboda baban halima ya kai kara. brfadila wani a
jiyar zuciya ta saki sannan tace tabdi babbar
magana. tace yanzu bari in shirya inje mu gana da
deeny inji kan lamarin ankama deeny ai bamuga ta
zama ba. maman deeny ta dan share hawaye
sannan ta kalla brfadila tace yanzu saiki fada mana
abunda zamu kawo dan allah ki ceci yaran nan
nasan bazai iya kisan kai ba kuma shike daukar
dawai niyar mu yanzu in bashi ya zamu yi gashi
maryam din ma bamu san inda tayi ba. cikin sauri
fadila ta dago kai ta dafe kirji tace maryam ta bata.
maman aliyu ce ta bata amsa tace kwarai kuwa tun
jiya data fita islamiya bata dawo ba har yanzu.
maman deeny kuka take sosai. fadila ta kalle su
cike da tausayawa ta taso daga kujerar ta ta dawo
kusa da maman deeny ta rike hannun maman
deeny sannan tace. ki kwantar da hankalin ki
isha'alahu zamuyi nasara kuma kibar maganar kudi
deeny ai dana ne sannan ta kara dacewa in allah
yayarda deeny zai fito ki bar komai a hannun na
yanzu zanje na sama deeny. maman deeny da
maman aliyu godiya suke kamar me sun rasa kalan
godiyar da zasu mata ma. tace ba komai muje
driver ya kai ku idan ya dawo sannan na shirya sai
mu wuce da shi station wajan deeny…………
mu hadu a whatsapp→ 08096831009 Group
bigboy
on-line 15.04 15:28
→BANI NA KASHE TABA← PART 7
na bigboy isah
anne tace wai shin gidan suwa kika zo ne awannan
riggar tamu?. maryam ta sunkuyar da kai sannan
sai hawaye suka kwararo mata. tace sato ni akayi.
nan ta kwashe labarin duka ta fadawa aneesa.
anne tayi mamaki dajin wannan labari. ta gyada kai
tace tabb aradu kinyi gudun mutuwa. ko kin san
daga nan zuwa bakin titi tafiyar wuni guda ce kuwa
gamu wanda muka saba ma kenan. maryam ta
bude baki tace wuni guda fa kika ce?. annee tace
kwarai kuwa. maryam tace allah ne kawai ya cece
ni daga sharin su. anne tace yanzu kinga dare yayi
tashi mu tafi gida sai mu kwana tare. maryam tayi
godiya ta tashi suka tafi.**************
acan kuwa gidan kawu, kawu ne yake cewa wai ni
shin da ake cewa deeny yayi kisan kai wa ya
kashe?. hawaye ne suka biyu ta kan
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment