Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

¶KARAGAR MULKI¶
Littafi Na Daya (1) Part A.

Abdul'aziz Sani Madakin Gini.

A•Haleefah-Physicist.

¶A wani zamani can baya mai tsawo daya shude a kasar Hindu.Anyi wani gawurtaccen Sarki wanda ya shahara akan KARFIN MULKI da kuma karfin SIHIRIN TSAFI wanda masana da masu bincike suka tabbatar da cewar a wannan zamani babu wani matsafi daya kaishi karfin sihirin tsafi a duk fadin duniya. Komai ba jin dadin duniya Allah ya baiwa wannan Sarki wanda ake kira da suna Kanzal face rashin haihuwa.
A wajen mahaifinsu su tara ne kuma gaba dayansu maza ne babu mace ko daya. Sarki Kanzal shine DAN AUTA a GIDAN SARAUTAR. Lokacin da mahaifinsu ya kwanta ciwo sai gaba dayansu su Taran kowa ya kwallafa ransa akan Sarautar har ya zamana cewa suna ta kaiwa junansu hari domin su hallaka junansu.
Bisa dole kowannen su ya nemo hayar DAKARU na waje domin tsare lafiyarsa da rayuwarsa. Amma duk da haka saida kowannen su yasha BAKAR WAHALA ya kusan rasa rayuwarsa saboda MUGUN TANADIn da sukewa juna. Wadannan yan uwa guda tara suna yin tsananin gaba, babu wanda yake son yaga wani a raye.
Babu wanda yafi shan wahala a cikinsu sama da Sarki Kanzal domin a wannan lokacik shine mafi kankanta a cikinsu. Sau uku ana sassarashi ayi masa DUKAN KAWO WUKA ana zaton ya mutu, kai akwai lokacin ma da aka daddaure shi tamau da Igiya aka the sashi a cikin buhu aka kulle buhunwkuna aka jefashi cikin teku. Anna bayan sati biyu sai gashi ya dawo fada a raye. Duk jikinsa yasha dinki na saran takobi.
Koda ragowar yan uwansa su takwas suka ga Kanzal a raye sai suka firgice kuma suka kamu da tsananin mamaki saboda a gaban idanunsu aka sassarashi aka sashi a ckkin buhu aka jefa shi a teku.
A wannan rana ne da Kanzal yazo fada ya iske mahaifinsu ya mutu kuma ya iske za'a fara gabatar da GASAR HAWA KARAGAR MULKI a tsakanin Yayyansa su takwas, dama a wannan lokaci hankalin fadawansa Sarki wato yan majalisa masu zaben sabon Sarki a tashe yake saboda tsawon sati uku ana neman Yarima Kanzal ba'a ganshi ba kuma ko duriyarsa ba'a ji ba. Tuni a wannan lokaci ya zamana cewa Mahaifiyar Yarima Kanzal ta saduda cewa an kashe danta duk da cewa ba'a ga gawarsa ba. Sai tayi ta kuka DARE DA RANA har ma tasa aka shirya bikin mutuwarsa.
Da gawa daga cikin yan majalisar kasar Hindu sunfi son ace Yarima Kanzal ne ya zamo Sarki saboda shi kadai ne yayi gadon mahaifin nasu a halaiya ta kirki. Kanzal yana da tausayi, jin kai da taimakon talakawa sabanin ragowar yan uwan nasa wadanda babu abinda ya shige musu gaba face MULKI, DUKIYA da kuma ZALUNCI. Shi kansa mahaifinsu Yarima Kanzal tun yana da rai ya nuna tsananin Soyayyarsa akan Yarima Kanzal saboda kyawawan halayensa kuma yafi son ace shine ya gaje shi amma saboda dokar MASARAUTAr itace Sarki bashi da ikon bayar da karagar ga wani 'da nasa face anyi gasa. Dole ya hakura da batun bawa Yarima Kanzal karagar.
A ranar da Sarki zai mutu ma yini yayi yana kuka gami da ambaton sunan Yarima Kanzal saboda bakin cikin rashin ganinsa. Al'amarin da yasa ciwon nasa ya kara tsamari kenan har zuciyarsa ta buga sanandin ajalinsa.
Lokacin da Yarima Kanzal ya shigo cikin fadar birnin Hindu a lokacin da fada ta cika ta batse babu masakar tsinke saboda yawan bil'adama sakamakon anzo kallon 'DAN SARKIn da zai lashe gasar hawa karagar mulki.Sai fadar tayi tsit tamkar mutuwa ta gifta.Ba komai yasa fadar tayi tsit ba face ganin shigowar Yarima Kanzal cikin fadar tare da wata Mace JARUMA a cikin shigar YAKI wacce ke sanye da fararen tufafi Tana take masa baya. Ta rufe fuskar ta da farin rawani idanunta kadai ake gani kuma ta rataya wata zabgegiyar takobi a bayanta, babu wanda ya taba ganin wannan Jaruma a NAHIYAR gaba daya don haka mamaki biyu jama'a sukeyi. Musamman ma yan uwan Yarima Kanzal.
Mamaki na farko shine ganin Yarima Kanzal a raye. Tunda kowa ya dauka cewa ya mutu. Mamaki na biyu kuma shine na ganinsa da wannan bakuwar Jaruma kuma a Ina Yarima Kanzal ya samota.
Wannan sune tambayoyin da gaba dayan mutanen dake cikin fadar suke yiwa kansu a cikin zukatansu Amma kuma babu wanda ya iya baiwa kansa amsa. Bayan kowa ya mike tsaye a cikin fadar sakamakon ganin Yarima Kanzal an kama kallon kallo a tsakanin Yarima Kanzal da yan uwansa guda takwas sai Kanzal ya durfafi inda alkalan gasar suke fuskarsa cike da murmushi. Koda yazo daf dasu saiya risina ya gaishe su cikin girmamawa yace Ubangijinmu Zakur ya dawo dani gida lafiya bayan batana na tsawon sati uku, gashi na dawo daidai ranar da za'a fara wannan gasa don haka maimakon ayi gasar ta tsawon kwana takwas sai a kara kwana guda ya zamo kwana tara. Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube gaba dayan jama'ar dake filin fadar, kalilan daga cikin yan majalisar tare da 'ya'yan Sarki su takwas ne suka kamu da tsananin bakin ciki gami da takaici saboda tsananin mamaki da firgici na ganin Yarima Kanzal, basu san sa'adda gumi ya fara karyo musu ba. Take shugaban alkalan gasar ya mike tsaye wanda shine Wazirin Marigayi Sarki ya dubi jama'a fuskarsa cike da annuri yace yaku mutanen kasar Hindu kuyi sani cewa Ubangiji Zakur ya dawo mana da Yarima Kanzal lafiya bisa batan da yayi na tsawon sati uku don haka lallai shima yanzu ya shigo wannan gasa. Koda jin haka sai fadar ta rude da shewa gami da tafi aka shiga yiwa Yarima Kanzal kirari ana kodashi anace masa MURUCIN KAN DUTSE baka fito ba saida ka shirya. Wasu kuma suma rinka cewa dashi lale Marhaban da gagarau, kangarau, kai haka akayi ta yiwa Yarima Kanzal kirari iri iri ya zamana cewa fadar ta rude da hayaniya har saida Waziri ya daga hannu ya daka tsawa sannan akayi tsit tamkar mutuwa ta gifta. Waziri yayi gyaran murya yace kamar yadda kuka sani yanayin wannan gasar shine ana yiwa kowane dan Sarki tambayoyi ne guda goma akan ILMIN MULKI da sha'anin harkokin kasa dake tafe. Idan har ya amsa tambayoyin dai dai ya haye zagayen farko na gasar kuma zagaye uku kadai akeyi.A zagayo na karshe ne za'a fitar da zakaru biyu su amsa tambayoyi na karshe wanda duk ya amsa tambayoyin dai dai bai fadi ko guda daya ba shine zai zamo Sarki gaba daya. Tambayoyin za'a yi ne guda dari ba daya kuma kowanne Yarima da kansa zai zabi lambar tambayar da za'a yi masa. A cikin tambayoyi goma da za'a yiwa Yarima a zagaye na farko idan ya fadi a tambaya daya koda kuwa ta farko ce to ba zai shiga zagaye na biyu ba, don haka kowane Yarima saiya kula da kyau kuma ya nutsu sosai don kada ya amsa tambaya ba daidai ba. A kullum mutum biyu za'a yiwa tambayoyi don haka yanzu za'a ajiye lambobi a cikin akushi, lambobin guda tara ne maimakon takwas amma wadanda zasu sami damar amsa tambayoyin yau zasu dauko lamba ta farko ne ma'ana mutum biyu da suka dauko lambar daya sune zasuyi gasa a yau. Koda waziri yazo nan a zancensa saiya daga hannunsa ya yiwa wani hadimi inkiya take wannan hadimi ya shigo tsakiyar filin fadar dauke da akushi rufe ya ajiye gaban alkalan gasa. A cikin akushi an sanya wadansu dunkulallun takardu guda tara. Nan take aka umarci yayan SARKIn su tara dasu zo daya bayan daya su zabi lamba. Nanfa idanun yayan sarkin ya zazzaro kowannensu hankalinsa ya tashi zuciyoyinsu suka fara bugawa da karfi saboda kowannen su a cikin fargaba yake, idan har zai dauko lamba daya, babban abin fargabar shine zai iya amsa tambayoyi guda goman da za'ayi masa a yau? Idan ya fadi tambaya daya jal daga cikin goman ya fita kenan daga cikin gasar bashi ba hawa KARAGAR MULKI saidai waninsa. Gaba daya ya'yan sarki su tara suka nufi inda wannan akushi yake sai suka far noke noke suna jajja da baya mutum biyu ne kadai daga cikinsu suka durfafi inda akushin yake ba tare da shakkar komai ba. Ba wasu bane face dan autan cikinsu Yarima Kanzal. Shidai Yarima Kanzal mutum ne mai tarin ilmi akan karatun sarauta ta kasar har dama ta sauran kasashen dake makota don tun yana da shekara biyar a duniya ya haddace Littattafai na tarihin sarautar kasar kuma daya shekara goma sha daya sai ya bazama izuwa sauran kasashen dake nahiyar yana neman ilmi akan MASARAUTAr saboda yin tanadin wannan rana. Tunda Yarima Kanzal yabar gida bai dawo birnin Hindu ba sai bayan shekara tara a sannan ya cika shekara ashirin daidai a duniya. A wannan lokaci an zata ya hallaka a wani wuri cikin YAWON DUNIYAr tasa amma sai gashi ya dawo gida a cikin gagarumin shiri na neman Sarauta saida ya zama gawurtaccen matsafin da babu kamarsa a nahiyar. Yana sauka a gida ya far nunawa mutane abubuwan AL'AJABI na sihiri kuma ya rinka bayar da labarai na sihiri iri iri wanda tsofaffi da masana tarihi ma na kasar basu San dashi ba. Wannan al'amari ne ya tayar da hankalin sauran yan uwan Yarima Kanzal su takwas. Ba shiri suma suka bazama cikin duniya don neman ilmin da Yarima Kanzal yaje ya samo. Yarima Kanzal ne kadai bai tafi neman wannan ilmi ba. Sai ya zauna a gida ya cigaba da yiwa mahaifin sa hidima a lokacin baifi shekara tara ba. DARE DA RANA Yarima Kanzal na tare da mahaifinsa kai hatta Kwanciyar baccin ma bata raba su, saboda tsananin shakuwa saida takai cewa hatta abincin da abin sha wanda Sarki zaiyi amfani dasu Yarima Kanzal ne ne dafawa da shirya su saboda yadda idan kuwa wani ya kawo Sarki bazai ko kalle su ba.
Matan Sarki su goma sha daya ne saida suka zamo basu da kishiyar da tafi mahaifiyar Yarima Kanzal. Babu wacce take kaunar Yarima Kanzal a ciknsu face mahaifiyarsa Lamisa. A cikin matan Sarki akwai wacce bata taba haihuwa ba ana kiranta da JALILA. Jalila ta kasance amaryar Sarki don haka itace matar da Sarki ya aura a karshe kuma itace mafi kankanta a duk cikin matan na sarki domin shekarunta sun haura sha takwas. Jalila ta kasance kyakkyawar budurwa abar kwatance kuma a wannan lokaci da shekara uku kacal Yarima Kanzal ya girme ta. Asalin mahaifiyar Jalila Sarki Kairus ya baiwa mahaifin su Yarima Kanzal auren Jalila ne ba don komai ba sai saboda tsohon wani buri dake karkashin zuciyarsa wanda ya gagari iyayensa da kakanninsa cikawa. Burin kuwa shine a cikin yankin kasar Hindu akwai wani SIHIRTACCEN KOGI wanda ba'a shiga Cikinsa domin Su ko debo ma'adanan kasa dake karkashin sa sana da shekaru dari uku baya ko tsuntsu ne ya shiga cikin kogin take zai mutu. Babu daga inda ba'a gaiyato bokaye ba domin su karya asirin da yake kashe mutane da dabbobi da tsuntsaye a cikin wannan kogin amma abu ya gagara. Gaba daya sarakunan da suke mulki a kasar Hindu sun kasa gano asalin wanda ya sihirice wannan kogi bare su sami hanyar da zasu Karya asirin don haka bisa dole aka kewaye kogin kuma aka rufe shi aka hana kowa da komai rabarsa domin sama da dakaru Dubu uku ne suke gadin wannan kogi.kafin a asirce kogin masana albarkatun kasa sun gano cewa inda za'a shekara dubu ana hako dukiyar dake cikin sannan kogi ta nau'in Zinare da lu'ulu'u ba zata kare ba duk sarkin daya hau KARAGAR MULKI a birnin Hindu da wannan bakin ciki yake mutuwa na rashin samun damar debo wannan dukiya dake cikin kogin wanda aka yiwa lakabi da BAHAR LAHIRAM. As he ba wani bane ya asirce wannan kogi ba ba bahar Lamiram face Kakan Gimbiya Jalila na hudu. A dalilin kogin yayi yaki da kasar Hindu sau tara domin ya sami damar shiga kogin ya debo dukiyar dake ciki amma bai sani nasara ba saboda duk sa'adda akayi yakin KARE JINI BIRI JINI akeyi saidai ya hakura bisa dole ya hada ragowar MAYAKANsa ya koma gida. Bayan anyi yaki na taran ne wanda shine na karshe sai CIWON ZUCIYA ya kama Sarkin Kasar Ramhaz ya kwanta CUTAR AJALI. Kafin ya mutune ne ya baiwa Hadimansa dukiya mai yawan gaske suka bazama a duniya neman bokan da yafi dukkan bokayen duniya KARFIN SIHIRIn Tsafi. Saida suka shekara shida suna yawo a duniya sannan suka riski wani boka wanda ake kira da suna Daibul Usara. Wani akasi da sukayi shine Hadiman sun riski Boka Daibul Usara shima a kwance yana kan cutar AJALI, bayan sun gabatar da bukatar sarkin nasu ga boka Daibul Usara kuma suka ajiye masa jakunkunan Dinare manya guda tara a gabansa sai boka Daibul Usara ya yunkura da kyar ya mike zaune ya leka cikin jakunkunan kudin. Koda yayi arba da makudan Dinaren da aka kawo nasa saiya bushe da dariyar farinciki daga can kuma saiya fashe da KUKAN BAKIN CIKI.Al'amarin dayai matukar baiwa Hadiman sarkin mamaki kenan har daya daga cikinsu ya dube shi yace Ya kai Mafificin Bokayen Duniya Ina dalilin wannan KUKA DA DARIYA taka duk a lokaci guda haka? Sa'adda Boka Daibul Usara yaji wannan tambaya sai ya kawo gwauron Numfashi ya ajiye sannan ya dubi hadimin da yayi nasa wannan tambaya yace...............

Abubakar Haleefah physicist.

Via:-Triple Abubakar Hausa Books
KARAGAR MULKI
LIttafi Na Daya(1) Part B.

™Abdul'aziz Sani Madakin Gini.™

A•Haleefah--Physicist

*Sa'adda Boka Daibul Usara yaji wannan tambaya sai ya kawo gwauron Numfashi ya ajiye sannan ya dubi hadimin da yayi masa wannan tambaya yace, ba wani abu bane ya sani wannan dariya ba face ganin na mallaki adadin dukiyar dana dade ina mafarkin mallakarta amma ban samu ba sai yau. Duk da cewa nafi kowa karfin sihirin tsafi a wannan nahiyar. Dan gane da dariyar da kaga inayi kuwa Ina farin ciki ne akan zan mutu na bar wani abu guda daya wanda zai gagari gaba dayan sarakunan da za'a yi a kasar Hindu, har kasa ta nade babu wani Sarki daya isa ya amfani dukiyar dake cikin karkashin kogin Bahar Lihiram duk duk bakin cikin hakan zai rinka zama sanadin Ajalin Sarakunan. Ku sani cewa a cikin binciken da nayi a duk fadin duniya babu inda yafi kasar Hindu yawan dukiya ya Zinare, Lu'ulu'u da Jauhari kuma kaso ba saba'in na wannan dukiya tana cikin karkashin kogin Bahar Lihiram. Ni ma babu yadda banyi ba akan na debo wannan dukiya amma abu ya gagara har dakarun aljanu na tura izuwa Kogin amma sun kasa dauko Koda Dinare daya saboda karfin sihirin aljanun dake rayuwa a cikin kogin na Bahar Lihiram. Tunda dai ba zamu iya debo wannan dukiya ba shike nan zamuyi asirin da babu wanda ya isa ya moreta har abada. Ku koma Ku gayawa Sarki Kairuz cewa ni da shi duk kukanmu iri daya ne amma ya sani cewa ba zamu mutu da bakin ciki ba mu kaidai ba. Duk Sarakunan da za'a yi a kasar Hindu sai sun mutu da bakin cikin rashin amfanar dukiyar cikin kogin Bahar Lihiram. Ku tashi kuyi tafiyarku kafin Ku isa gida ma na gama wannan aiki. Aikuwa daga wannan rana dukiyar dake cikin kogin Bahar Lihiram ta gagari kowa a kasar Hindu walau yan gari ko baki kuma ya zama haramun ga duk wata halitta mai rai.
Kafin wannan hadimai su baro wajen Boka Daibul Usara saida dayansu ya dube shi yace yakai sarkin Bokayen duniya yanzu kana nufin kace babu yadda za'a yi Sarkin mu ya sami damar amfanar dukiyar cikin kogin bahar Lihiram har abada? Sa'adda Boka Daibul Usara yaji wannan tambaya saiya bushe da dariya yace ku gayawa Sarkin ku cewa idan har yana son ya amfani dukiyar cikin kogin bahar Lihiram to saidai ya aurar da 'yarsa ga Sarkin kasar Hindu. Duk ranar data sami haihuwa da Sarkin to a dauke jinin haihuwar tata digo daya a diga a cikin cibiyar ruwan data hade da kogin bahar Lihiram ya zama mallakinsa.
Lokacin da Jalila ta cika shekara uku da auren Sarkin kasar Hindu taga bata sami juna biyu ba sai hankalinta ya DUGUNZUMA ainun ta kamu da tsananin bakin ciki bisa wannan dalili ne tasa likita ya binciki lafiyarta data Sarki inda ya tabbatar mata da cewar ita lafiyar ta kalau take amma shi Sarki ya daina Haihuwa. Koda jin wannan batu sai Gimbiya Jalila ta sulale kasa Sumammiya. Ba komai ne yasa Jalila ta suma ba face tsananin bakin ciki gami da nadamar yin aurenta saboda kafin ayi auren saida tayi rantsuwa da girman abin bautarsu, ta daukar wa mahaifinta alkawari cewar lallai sai ta cika masa burinsa ta share masa hawaye. Daga wannan rana Jalila ta fara tunanin hanyar da zata bi ta kawar da gaba dayan ya'yan Sarki da dukkanin matansa na aure domin ya kasance itace zata haye kan KARAGAR MULKIn kasar. A bisa wannan niya ce tayi ta hada munafunci da rigima kala kala a tsakanin ya'yan sarkin har ta haddasa MUMMUNAR GABA a tsakaninsu.Kafin azo wannan gasar hawa KARAGAR MULKIN akwai wani mummunan abu daya faru.Yarima Yunus wanda shine Babban dan Sarki yana da wata budurwa mai suna Umaira wadda yake tsananin Kaunarta kuma tun suna yara suke SOYAYYA. Ita dai Umaira ta kasance 'Ya ga wani Bawan Sarki mai kula da wani gidan gona. Kawai sai aka wayi gari an kashe Umaira a cikin harabar gidan gonar.Lokacin da aka tsananta bincike domin a gano wanda ya kashe Umaira sai akaga wani abin Hannu na Zinare na Imran a cikin aljihun Umaira. Imran wanda shine na biyu a cikin ya'yan sarki wato shine ke bin Yarima Yunus. Shi dai abin hannun na Yarima Imran duk duniya shi kadai yake da irinsa duk da cewar sauran ya'yan sarki suna dashi amma ya bambanta dana wani saboda kowane abin hannu anyi shine da kalar karfe daban. Abin hannun Yarima Imran anyi shine da Zinare, na Yunus kuma a lu'ulu'u. Na sauran da kuma Jauhar, Zubar daji,Farin Yakutu, Tagulla, Dutsen Safata kore da kuma dutsen Sapaya shudi.Sarki Margayi wato Mahaifinsu Yarima Kanzal shine ya raba musu wadannan ababan hannu guda tara. kuma yayi amfani da girma ne wajen raba ababan hannun. Ma'ana yawan shekarunka shine darajar abin hannun da za'a baka. Abin hannun da aka bawa Yarima Kanzal shine mafi kaskantar daraja, wato dutsen Sapaya shudi amma kuma akwai wani babban sirri cikin wannan abin hannun wanda aka bawa Yarima Kanzal kuma shi kansa bai san da sirrin ba. Babu wanda ya san sirrin dake cikin wannan abin hannu na Yarima Kanzal face mahaifinsa Sarki Margayi. Bayan Sarki Margayi ya rabawa su Yarima Yunus wadannan abubuwan hannu saida ya kira Yarima Kanzal a sirrance ya dubeshi cikin wani irin yanayi na tausayawa Kamar zai zubar da hawaye yace yakai 'Dana kayi sani cewa a cikinku ku tara kai ne kadai nasan cewa yana Kaunata bil hakki kuma kai ne kadai zaka iya sallama rayuwarka don kare tawa, amma gaba dayan yan uwan ka sun kagu ma suga na mutu su mallake karagata. Bani da karfin da zan iya doraka akan karagar mulkin nan walau a yanzu ko bayan mutuwa ta tunda dole sai an bi ka'ida da gasar hawa KARAGAR MULKI. Gaba dayan wadannan yan uwa naka takwas sun fika damar hawa kan wannan karaga amma idan ka kiyaye wasu abubuwa da zan gaya maka yanzu sai kazo ka zama kaine da karagar mulki. Abu na farko shine ka kula da abin hannun ka wanda na raba muku ku tara. Duk wuya duk rintsi, komai dare komai Rana ya kasance kana tare dashi. Kada ka kuskura ka bari ya subuce daga hannun ka koya nisanta da kai. Abu na biyu ka zamo mai Juriya da kuma hakuri bisa duk irin yanayin daka tsinci kanka a cikinsa. Abu na uku wanda shine na karshe ka zamo mai fadin gaskiya bisa duk abinda zaka fada. Idan kayi Alkawari lallai ka cika shi. Idan aka baka Amana kada ka ci yakai 'Dana. Indai ka kiyaye wadannan abubuwa dana lissafo maka babu irin hadarin da zaka shiga baka fita va. Kuna duk abinda kasa a gaban ka sai kayi nasara. Lokacin da Sarki yazo nan a zancensa sai hawaye ya zubowa Yarima Kanzal ya rungumeshi yana mai fashewa da kuka har izuwa tsawon yan dakiku.Daga can kuma ya janye jikinsa daga cikin nasa suka fuskanci juna ya dubeshi yace yakai Abbana kayi sani cewa yadda na shaku da kai kuma nake tsananin Kaunar ka ko mahaifiyata bana Kaunarta haka. Idan har mutuwa zakayi ka barni a cikin wannan duniya to zan so a ce mu mutu tare. Koda jin haka sai Sarki yai sauri ya rufe bakin Yarima Kanzal da tafin hannunsa kuma ya dubeshi cikin murmushi yace, yakai 'dana Ina so ka rayu domin ka zama Sarki ba don komai ba sai saboda kana da kishin kasar nan da al'ummarmu. Cikin ya'yana duka kai kadai kake da irin wannan kishi wanda nake dashi. Kai ne kadai zuciyarka take da adalci irin nawa. Tabbas indai ba kai ne ka zamo Sarki ba komai na kasar nan sai ya dagule, karshe na ana ji ana gani wata kasar zata zo ta mamaye mu. Ina son kayi mini alkawari guda biyu bisa cewar idan

Please Login or Register in order to submit comment