Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin kogon Darul Kimzaz,banbancina dake kawai shine matsayin da kika samu na sarauniyar sadaukai.Gama fadin hakan keda wuya sai shugaban dakaru ya sake afkawa Jaruma suka ruguntsume da sabon azababben yaki mai matukar ban tsoro da firgici saboda wannan karon saida duk su biyun suka sauya salon fada suka hada da kaiwa juna naushi da bugu da hannu da kafa gami da tsalle tsalle da kwance kwance irin na manyan jaruman da suka kware.Babu abinda ya bawa Yarima Kamzal mamaki sama da ganin yadda jaruma ke shanye duk irin naushin da wannan narkeken kato keyi mata amma duk sa'adda ita kuma ta naushe shi sai kaga har tangadi yakeyi kamar zai fadi kasa.Tsananin juriya da jarumtaka ne suka sa yaki zuwa kasa.Nan da nan suka hadawa junasu jini da majina sai da suka sake daukar lokaci mai dan tsawo a haka suna fafatawa a hakanne jaruma ra fahimci cewa muddin wannan barde na iya cigaba da kai mata naushi da bugu a haka to fah babu tabbacin zata iya samun nasara a kansa domin ya sami horo na musamman akan jure wuya da duka.Koda gama aiyana hakan sai wata dabara ta fado mata kawai sai ta karawa kanta zafin nama wajen kai bugu da naushi.Faruwar hakan keda wuya kuwa sai ta kara kuntatawa barden ya zamana cewa har yin tsalle take sama tana jera masa luguden bugu da kafafunta a fuska.Nan da nan ta rikita shi kuwa har ta kai cewa baya iya maida martani sai kokarin kare hari.Koda jaruma taga ta sami wannan nasara sai ta kara zage damtse wajen kara masa luguden naushi a cikin barden sai gashi yana furzar da jini ta bakinsa yana durkusewa kasa.Wohoho!Tabbas masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce KARFI SAI ALLAH ya isa tabbas ba wani abu bane yasa jaruma ta sami wannan nasara ba face tsagwaron karfin damtsenta,zafin namanta da kuma kwarewarta a iya yaki da fada gami da tsananin nacinta.Saida jaruma tayi laga laga da wannan barde tago ko motsin kirki bayayi sannan ta kama wuyansa da hannayenta biyu ta shake shi.Nan take barden ya fara kakarin mutuwa.Koda ganin haka sai Yarima Kamzal ya rugo gare ta ya dubeta yace kada ki kashi shi bari na bashi dama.Koda jin wannan batu sai Jaruma ta dan sassauta shakar da ta yiwa barden a lokacin da idanunsa suka juye gaba daya saboda tsabar wuya.Yarima Kamzal ya dubi barden yace idan kana son ka tsira da rayuwarka ka gaya min wanda ya turo ku kashe ni!Koda jin wannan batu sai barden ya bude bakin da nufin yayi bayani amma kawai sai sukaga kibiya tazo ta soke shi a KAHON ZUCIYA.cikin razana Jaruma da Yarima suka kama kalle kalle domin gano ta inda aka harbo kibiyar aikuwa sai suka hango motsin a can nesa cikin duhuwoyi.Take jaruma ta falfala da gudu izuwa inda duhuwar take duk da cewa wani irin azababben gudu takeyi har ta wuce inda suka hango motsin bata ga kowa ba.Ba shiri ta tsaya cak ta dubi gabas da yamma,kudu da arewa ko tattabara bata gani ba bare mutum.Cikin sauri ta ruga da baya da koma wajen Yarima.Tana zuwa ta iske wannan barde ya mutu.Cikin tsananin takaici ta ciza yatsa sannan ta dubi yarima tace yallabai ai tashi mu koma cikin gari zamanmu a nan cikin wannan daji yana da hadari.Ba tare da gardamar komai ba kuwa yarima ya mike tsaye suka jera suka nufi hanyar da zata kai su cikin gari.Da aka wayi gari ranar karshe tayin gasar karagar mulki tsakanin yarima Yunus da Yarima Kamzal sai filin fada ya cika ya batse fiye da kullum da koyaushe ya zamana cewa duk inda mutum ya hanga babu abinda zai gani face kawunan bil'adama rututu babu masaka tsinke,gashi dai gaba dayan alkalan gasa da yan majalisar birnin sun hallara amma babu 'ya'yan sarkin guda biyu wato Yarima Yunus da Yarima Kamza,basu hallara ba a fadar kuma babu wanda ya san dalilin rashin zuwan nasu akan lokaci.Bisa wannan dalili ne alkalan gasar suka yanke hukuncin cewa idan sa'a uku ta shude ba'a gansu ba za'a dakatar da wannan gasa a bawa wani daga cikin yan majalisar rikon KARAGAR MULKI.BA wani abu ne ya kawo rashin hallarar su Yarima Kamzal ba face wani al'amari daya faru tsakaninsu da Gimbiya Jalila wato Amaryar marigayi sarki mahaifinsu.

A daren bayan dawowar Yarima Kamzal da jaruma daga yin farauta daga daji sai sukayi kicibus da Gimbiya Jalila tsaye a harabar cikin gidan sarautar tana kai kawo cikin alamun tsananin damuwa da fargaba.Tana hada ido da Yarima Kamzal sai alamun rashin gaskiya suka bayyana kuru kuru akan fuskarta domin kuwa idanunta ne suka zazzaro suna masu nuna alamun tsoro da mamaki.Koda ganin haka sai Yarima da Jaruma suka kalli junansu.Cikin alamun borin kunya Jalila ta araso gaba Yarima Kamzal tana wata irin tafiya mai jan hankali da yaudara kuma fuskarta cike da murmushi,saida tazo daf da shi yadda suna jin numfashin juna,koda ganin haka sai Jaruma tayi wuf ta shiga tsakaninsu.Cikin alamun tsananin fushi Gimbiya Jalila ta dubi Jaruma tace yake mai tsaron lafiyarsa bani waje ba gana dashi.Jaruma tace,ina son ki sani cewa a cikin sarautar nan babu wanda ya zamo abin yarda,inaso ki sani cewa ko mahaifiyar Yarima Kamzal a yanzu ba zata haanani yin aikina ba tunda ta sani cewa Ke kika kashe gaba daya 'ya'yan sarki su shida tare da Yarima Imran wanda aka kora.Yanzu saura mutum biyu kacal.Koda jin haka sai Jalila ta sake fusata ta dubi Jaruma a wulakance gami da wani irin murmushi na raini tace to yanzu kina zargina akan cewa zan iya kashe Yarima ko kuwa kina zarhina ne akan cewa nice na kashe 'ya'yan sarki?Jaruma ta mai dawa da Jalila murmushi na yadda da kai tace ai abu ne a duhu sai an bincika.Ni dai kawai aikina nakeyi don haka bazan taba yadda ki kusanci yarima ba,idan wata magana zaki fada masa ki fadeta a gabana domin ba batun wani sirri a tsakaninki dashi.Koda jin haka sai Gimbiya Jalila ta juya bayanta a fusace ta dubi dakarun gidan Sarautar masu tsaron lafiyarta kimanin su dubu da daka musu tsawa a fusace tace maza ku kama wannan bakuwar Jaruma ku kaita kurkuku ku kulleta.Take dakarun suka yunkura zasu afkawa Jaruma sai Yarima Kamzal yasha gabansu shima ya daka musu tsawa yace idan har kuna so ku kama wannan Jaruma saidai ku kama mu tare ku kulle mu tare.Nanfa dakarun sukayi tsuru tsuru suka rasa umarnin wanda zasu bi tsakanin Gimbiya Jalila da Yarima Kamzal.Koda ganin haka sai Yarima Kamzal ya kama hannun Jaruma a karon farko tun haduwarsu ya jata izuwa inda turakarsa take suka bar Gimbiya Jalila a tsaye tana harararsu gami da huci kamar KUMURCIN MICIJI.Turakar Yarima Kamzal ta kasance katuwa mai tsawo da fadi kuma ta kunshi babban falo guda daya sai kuma dakin bacci da bandaki guda biyu.Bandakin fako a falo yake sai kuma na biyun dake cikin dakinsa na bacci An kawata wannan turaka ta Yarima Kamzal fiye da dukkanin sauran dakunan dake cikin gidan sarautar face turakar sarki margayi.Ba komai bane ya janyo haka ba face tsananin son da sarki yake yiwa Yarima Kamzal fiye da dukkan sauran 'ya'yansa.Kafin a sami annobar mutuwar 'ya'yan sarki kuyangi arba'in da daya ne suke yiwa Yarima Kamzal Hidima.Amma da zuwan Jaruma duk sai ta kore su ya zamana cewa su biyu kacal suke kwana a cikin turakarsa wato daga ita sai shi.Sa yake dama sun saba kwana waje daya basu fuskanci wata matsala ba.Amma duk da haka Jaruma bata yarda su kwanta tare a kan gadon Yarim.Saidai ko ita ko shi wani ya kwanta akan gado,wani kuma a kasa bisa kilishin da aka shimfida mai taushin gaske.A kullum Jaruma bata kwanciya bacci sai alfijir ya keto saboda tabbatar da tsaro.Wani lokacin ma fitowa takeyi daga cikin turakar ta dinga kewaye harabar wajen.Ko motsin wani kwaro taji sai ta bincike inda taji motsin haka kuma idan ta kwanta ta fara baccin ko tari akayi acan kofar turakar Yarima Kamzal sai ta farka daga baccin.Kuma tana farkawa zata zare takobinta ta mike ta dubi ko ina har sai ta tabbatar da cewa babu wani abu mai rai bako daya shigo cikin turakar.Lokacin da Yarima Kamzal tare da Jaruma suka shigo cikin turakar sai suka zauna a falon sukayi zugum suna kallon juna kawai kamar masu zaman makoki alhalin ka'ida duk sa'adda sukayi irin wannan gajiya suna dawowa gida suke kwanciya domin su huta.Kawai sai Jaruma ta dubi Yarima tace Gimbiya Jalila ce ta kashe gaba daya yan uwanka mutum shida kuma dakarun sumamen da suka kawo mana hari dazu a daji sa'adda muka fita farauta itace ta turo su.Koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke Yarima Kamzal ya dubeta yace to yaya akayi kika san duk wannan al'amari?Dajin wannan tambaya sai ta sunkuya ta dauki takubban data zo dasu guda biyu wato farar takobinta wacce ta samo a can Darul Kimzaz da kuma takobin shugaban dakarun kisa ta dubi takubban da kyau tayi nazarinsu sannan ta dubi Yarima tace wannan takobin shugaban dakarun da nayi gumurzu dashi asalinta ta fito ne daha hannun wadansu kwararrun DAKARUN KISA dake karkashin wani mashahurin attajiri .Musamman attajirin daya kirkiri wadannan dakaru yasa aka basu horo na musamman domin kawai masu mulki su rinka dauka hayarsu suna kashe musu ABOKAN GABAR su.Basa yiwa kowa aiki face wasu mulki.Shi dai wannan attajiri bashi da wata hanya da yake samun makudan kudade sama da wadannan dakarun kisa.Dakarun sun kware wajen iya ashe mutane ta hanyoyi kala kala ba wai saida kaifin taobi ba kawai da ganin irin yanayin mutuwar da yan uwanka keyi aikin wannan muguwar kungiya ce.Yana daya daga cikin burina na duniya na share wannan kungiya daga doron asa.Na fahimci cewar Gimbiya Jalila tana son ta karar da dukkan 'ya'yan mahaifinku.Ina so ka sani cewa tun faro bata auri mahaifinku don komai ba sai don ta cika burin mahaifinta na mallakar dukiyar dake cikin kogon Bahara.Ba zata iya taba mallakar wannan dukiya ba face an diga jinin haihuwarta a cikin cibiyar ruwan kogin,gashi kuma bata sami juna biyu ba da mahaifin naku ta mallake kasar gaba daya.A yanzu ta sami nasarar kashe mutum shida daga cikinku kuma tasa an kori daya daga cikin birnin gaba daya wato Yarima Imran.Tun da ta shirya masa makircin da har abada bazai iya kwatar kansa ba.Yanzu fa saura ku biyu kacal kuma a gobe da safe idan kuka yi gasar karshe kai da Yarima Yunus dayanku ne zai hau karagar mulki.Da zarar hakan ta faru zata mayar da hankalinta akan wanda bai sami karagar ba har saita hallakashi sannan ta dawo kan wanda yake kan karagar.Sa'adda Jaruma tazo nan a jawabinta sai hankalin Yarima Kamzal ya DUGUNZUMA ainun fiye da koyaushe ya dubeta cikin alamun tsananin firgici da mamaki yace yake Jaruma yaya akayi kika san duk wannan al'amarin kuma yanzu wace hanya kike ganin ya kamata nabi domin kare kaina daga sharrin gimbiya Jalila.Koda jin wannan batu sai Jaruma ta kawo gauron numfashi ta ajiye sannan ta dubi Yarima Kamzal tace nasan duk wadannan abubuwa ne ta hanyar amfani da hange akan abinda ke kai kawo .Abinda nake so dakai shine ka kwantar da hankalinka nayi maka alkawarin cewa muddin ina tare dakai babu wani tsautsayi da zai taba lafiyarka ko rayuwarka.Ni kawai abinda nake bukata daga gareka shine ka zamo mai cika alkawarin daka daukar min cewa bayan na taimaka maka ka hau karagar mulki nima zaka cika min nawa burin.Yayin da Jaruma tazo nan a zancenta sai Yarima Kamzal yayi ajiyar zuciya.Kuma ya dubeta cikin alamun damuwa yace waishin mene ne dalilin da yasa ba zaki gaya mini ko menene wannan buri naki bane,Kuma menene ne dalilin da yasa kika cigaba da boye min fuskarki har yanzu alhalin mun saba da juna kuma kin gamsu da cewar ni ba mai cutarwa bane Bazan taba cutar da ke ba ko na tona miki asiri.Koda jin wannan tambaya sai Jaruma tayi murmushi tace ai bana magana biyu tunda na gaya maka cewa sai ka zama sarki ka hau kan karagar mulki sannan zan sanar dakai labarina,Kawai ka jira lokaci.Gama fadin hakan keda wuya sai Jaruma ta dan kishingida akan kujerar da take zaune a lokacin data dubi Yarima cikin nutsuwa tace idan har kana son ka tabbatar da zargin da nake yiwa gimbiya Jalila ka tashi yanzu mu tafi izuwa turakarta muyi leken asiri,zaka sha mamaki.Koda jin wannan batu sai Yarima Kamzal ya dubi Jaruma cikin alamun mamaki yace ta yaya zamu iya zuwa mu jiyo sirrin Jalila alhalin akwai dakaru a ko ina cikin gidan sarautar nan suna gadi kuma itama kinsan cewa ba kanwar lasa bace tana da shiri irin nata ai ba zama a barmu ba mu shiga cikin turakar ta ba.Koda jin wannan batu sai Jaruma tay murmushi take ta mike tsaye ta dubi Yarima tace tashi ka biyo ni a baya abinda nake so dakai shine duk inda na dauke sawun kafafuna ka saka taka.kuma kada ka kuskura kayi magana kai ko tari ma kada kayi har muje mu dawo.Gama fadin hakan keda wuya sai Jaruma ta fice daga cikin turakar,cikin hanzari Yarima ya mike tsaye............

Banyi posting ba saboda wasu ayyuka.
Ina barar adduar ku.

Abubakar Haleefah Physicist
ยถ๐™†๐˜ผ๐™๐˜ผ๐™‚๐˜ผ๐™ ๐™ˆ๐™๐™‡๐™†๐™„ยถ
๐™‡๐™ž๐™ฉ๐™ฉ๐™–๐™›๐™ž ๐™‰๐™– ๐™๐™ ๐™ช (3) ๐™‹๐™–๐™ง๐™ฉ ๐˜ฝ.

โ„ข๐‘จ๐’ƒ๐’…๐’–๐’'๐’‚๐’›๐’Š๐’› ๐‘บ๐’‚๐’๐’Š ๐‘ด๐’‚๐’…๐’‚๐’Œ๐’Š๐’ ๐‘ฎ๐’Š๐’๐’Šโ„ข.

๐˜ผ๐™—๐™ช๐™—๐™–๐™ ๐™–๐™งโค๏ธ๐™ƒ๐™–๐™ก๐™š๐™š๐™›๐™–๐™โค๏ธ๐™‹๐™๐™ฎ๐™จ๐™ž๐™˜๐™ž๐™จ๐™ฉ.

โ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขGama fadin hakan keda wuya sai Jaruma ta fice daga cikin turakar. Cikin hanzari Yarima ya mike tsaye zumbur ya bita da gudu.Kai tsaye Jaruma ta tunkari hanyar da zata kai inda turakar Gimbiya Jalila take ba tare da wata gardama ba.Abinda ya daurewa Yarima ai shine tunda suka fito daga cikin turakarsa suka fara wucewa ta gaban dakarun gidan sarautar amma baiga ko alamar akwai masu ganinsu ba.Kuma ko badakare sun tare musu hanya sai yaga sun wuce ta cikin jikinsu kamar yadda danshi ke tsattsafowa daga cikin kasa.Haka dai suka cigaba da tafiya har suka iso kofar turakar Gimbiya Jalila.Tun daga nesa Yarima yaga cewa cikin turakar an kashe fitilu tamkar Gimbiya bacci takeyi.Amma kuma ana jiyo sautin murya daga cikin turakar kasa kasa kamar anayin ra'da.Maimakon Jaruma ta nufi kofa ta shiga ciin turakar sai ta zagaya bayan kofar ta nufi katanga kawai sai Yarima yaga sun shige ta cikin wannan katanga sai gasu tsulum sun baiyana a babban falo suka hango gimbiya Jalila a tsaye ga wani badakare tsugunne a gabanta cikin shigar bakaken tufafi sama da kasa.Hatta fuskarsa a rufe take idanunsa kadai ake gani.Maganar farko da sukaji badakaren ya fada shine ranki ya dade wannan bakuwar Jaruma ba karamar iblishiya bace tunda har ta sami nasara akan shugaba Manzur kuma in badon na harbe shi da kibiya ba da tuni ya tona asirinki.Koda jin wannan batu sai ran Jalila ta baci ta kama kai kawo a cikin falon tana ciza yatsa kamar wacce ta gamu da sabon hauka.Daga can sai ta dawo kan badakaren ta cakumi kwalar rigarsa a lokacin da idanunta suka zazzaro kamar zasu fada saboda tsananin fushi tace me yasa bakayi kokarin kashe jarumar ba sannan ka kashe Yarima Kamzal din?Jin hakan ne yasa Yarima Kamzal ya dimauce saboda razana da mamaki bai san sa'adda yaja da baya ba har kafarsa ta dunguri wani teburi.Akan teburin akwai kofi na zinare,take kofin ya fado kasa.Karar faduwar kofin ce tasa Jalila da badakaren suka taso da hanzari suka rugo wajen amma tuni Jaruma ta cafke hannun Kamzal ta fincike shi suka fice ta bango.Bisa tsananin sa'a sai ga wata fara mace ta gimbiya Jalila tazo inda wannan kofin zinare ya fado.Koda jalila tayi arba da magen sai tayi ajiyar zuciya tana mai dafe kirjinta ta dubi wannan badakaren tace ai na zata ko wani ne ya shigo ya labe yana jin SIRRI NA.Cikin mamaki badakaren ya dubi gimbiya Jalila yace haba ranki ya dade ta yaya wani mahaluki zai iya shigowa har nan cikin turakarki ba tare da saninki ba alhalin kofa a rufe take kuma dakaru sunyiwa turakar KAWANYA.Jalila tace ai tunda wannan shaidaniyar Jaruma tazo gidan sarautar nan naji bani da kwanciyar hankali da sukuni.Ina mai tabbatar maka da cewa idan har bamu kawar da ita ba hakarmu ba zai cimma ruwa ba.Yanzu ba gashi gobe za'ayi gasar nan ta karshe ba.Da zarar an sami sarki ta hau kan wannan karagar mulki za'a kara tsaro sosai,ni ban jin wanda bai cinye gasar ba domin kawar dashi kamar zare silin gashi ne daga cikin tandun mai.Amma duk wanda ya hau kan karagar tofa ya kice shi daidai yake da tunkarar RUNDUNAR YAKI!Sa'adda badakaren yaji wannan batu sai yayi dariya yace haba ya shugabata shin kin manta ne cewa yau shekara arba'in da biyar a gidan sarautar gidanku.Duk wani tuggu da makirci na sarautar da iyayenki da kakanninki sukayi dani aka shirya su.Ai muddin kina raye a cikin wannan gidan sarautar sai na dora ki akan karagar mulkinsu duk da cewa kuwa ke bajin sarautar tasu bace.Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube gimbiya Jalila ta kyalkyale da dariyar farin ciki tace da kyau Zambaru shi yasa nake alfahari da kai.Wannan shine abinda ya faru a turakar gimbiya Jalila matar margayi sarki wacce ke da burin hawa kan karagar mulki ta kowane hali.

Al'amarin Yarima Kamzal da Jaruma kuwa lokacin da suka dawo turakar Yarima sai sua zauna zugum a lokacin da jikin Yarima yayi sanyi ainun yayi tagumi yana tunani.Nan take idanunsa suka ciko da kwallar takaici har hawaye ya fara sartowa akan kumatunsa.Koda ganin haka sai hankalin jaruma ya tashi ta dubeshi cikin alamun damuwa tace yakai yarima mene dalilin zubar wannan hawaye naka?Sa'adda Yarima waji wannan tambaya sai yayi ajiyar zuciya sannan yace yake jaruma kiyi sani cewa ba komai ne yasa ni zubar da wannan hawaye ba face yadda gimbiya Jalila ta tarwatsa gidan sarautar nan,da yadda mu a tsakaninmu muka tsananta gaba a tsakaninmu saboda mulki kawai.Gashi ma bamu ba hatta wasu daga cikin iyayenmu mata sun rasa rayuwarsu akan wannan TAFARKI.Sai na wayi gari babu sauran mutum daya daga cikin irin jinsin jininmu akan wannan KARAGAR MULKI.Koda yarima yazo nan a jawabinsa saiya fashe da matsanancin kuka.Nan take Jaruma taji ta kamu da tsananin tausayinsa don haka bata san sa'adda taso daga inda take zaune ta dawo daf dashi ta zauna sannan ta kamoshi da hannayenta biyu ta rungume shi akan kirjinta a karo na farko tun haduwarsu ta shiga rarrashinsa.Tana mai cewa yakai Yarima ka kwantar da hankalinka ka sani cewa muddin ina numfashi a doron kasa bazan bari wannan mulki yabar hannun zuri'arku ba.Na sani cewa babu wata doka data bada ikon a kori Jalila daga wannan Masarauta taku amma ka sani cewa Jalila annoba ce a gare ka.Muddin ka sami nasarar hawa kan wannan karagar mulki dole ne musan hanyar da zamu bi mu fitar da ita daga cikin garin nan,koda zuwa zamuyi muyi amfani da irin dabarun da tayi akan Yarima Imran ta kulla masa sharrin da bashi da mafita.Koda jin wannan batu sai zuciyar Yarima ta danyi sanyi ya janye jikinsa daga cikin na Jaruma ya dubeta yana mai yi mata dan guntun murmushi yace yake wannan Jaruma kiyi sani cewa tunda na hadu dake nake samun kariya da gushewar dukkan fargaba bisa duk irin masifun dana ke shiga.Kin ceci rayuwata,kin kare lafiyata,kin kula dani DARE DA RANA.Na rantse da darajar kaunar da nake yiwa mahaifina duk da cewa kina taimakona saboda kina da wata bukata a wajen in na hau kan wannan karaga ko mai kike so saina mallaka miki shi indai akwai shi a cikin wannan duniya domin banga abinda zan iya saka miki dashi bisa wanda kikayi min.Koda jin wannan batu sai Jaruma taji farin ciki ya kamata.Haka dai suka cigaba da hira tana bashi shawarwari akan yadda zai tafiyar da harkokin mulki bayan ya lashe gasar dake gabansa.Shidai Yarima Kamzal a wannan lokaci kawai saurarenta yakeyi amma gani yake kamar abu ne mayuwaci ma ya sami nasarar hawa kan karagar.Kuma koda ma ya hau a koyaushe zai iya rasa rayuwarsa.Suna cikin yin wannan hira ne Yarima ya fara gyangyadi sai kuma ya bingire kasa ya kama bacci.Koda Jaruma taga yarima yayi bacci sai ta kura masa idanu kawai ta rinka yin murmushi wanda ita kanta bata san dalilinsa ba.Adaidai wannan lokaci ne taji mayafin data daure fuskarta dashi ya fara damunta sakamakon dadewar da tayi bata kwance shi ba.Bisa wannan dalili ne ta mike tsaye ta shige can cikin turakar ta Yarima ta janyo kofa ta rufeta daga cikin muhalli don gudun kada Yarima ya farka daga bacci ya shigo cikin dakin ba tare data ankara ba.Bayan ta tabbatar da cewa ta rufe kofar saita kwance mayafin dake kanta taje gaban wani katon madubi ta tsaya tana kallon baiwar da Allah ya bata ta tsananin kyau wanda tafi gaba kwatantuwa.Jaruma ta kasance mace mai dara daran idanuwa masu tsananin fari zagaye da baki tamkar an diga tauwada a cikin madarar shanu.Tana da dogon siririn hanci bisa dan karamin baki tamkar yankan wuka.Wuyan ta siriri ne kuma ta kasance doguwa mai matsakaicin kaurin jiki.Tana da faffadan kugu mai tudun gaske daga baya.Kirjinta a cike yake tunjum kuma gashin kanta baki ne sidik mai kyalkyali kuma mai tsawo don ya zubo har kasan kwankwasonta.Koda yaushe kafin ta rufe fuskarta da mayafi sai ta tattare gashin ta daureshi a kasan keyarta.Babu wani 'da namiji da zai iya arba da kyakkyawar surar Jaruma bai dimauce ba yaji babu abinda yake son ya mallaka sama da ita.Lokacin da Jaruma ta shafe kusan dakika arba'in tana kallon kyakkyawar surar jikinta a cikin madubi sai hawaye ya zubo mata sakamakon tunowa da cewar wannan tsananin kyawun nata shine sanadin da yasa ta rasa iyayenta da danginta kuma shine ya rabata da kasar haihuwarta ta shiga duniya inda ta rinka boye kant don dole ta fuskanci wahalhalu da matsaloli iri iri wadanda da kyar da sidin goshi ta tsira da rayuwarta har takai izuwa kan matsayin da take a yanzu.Nan take zuciyarta ta kama ruruwa da wuta tana son DAUKAR FANSA akan wanda ya zamo sanadin rushewar rayuwarta gaba daya,amma inda matsalar take shine bata san a inda zata ga wannan babban makiyi na taba kuma rabon data ganshi a kalla an kai shekaru shida don tun bata fi shekara goma sha biyu ba.Jaruma na cikin wannan hali ne na tunani gami da ZUBAR DA HAWAYE sai taji motsi a can falon data bar Yarima Kamzal,Cikin hanzari ta zare takobinta kuma tayi wuf ta suri mayafinta tana rufe fuskarta dashi sannan ta ruga ta bude kofar dakin baccin ta fada falon tana shiga sai taga ashe Yarima Kamzal ne ya farfado daga baccin ya dauko tambula na ruwa yana tsiyayawa a cikin kofi domin yasha.Koda Yarima Kamzal yaga Jaruma tayi fitar burgu daga cikin daki ga takobi tsirara a hannunta saiya dubeta cikin murmushi gami da mamaki tace shin dama ba bacci kikeyi ba?Aina tura kofa naji ta a rufe don haka sai nayi zargin cewa kin bude fuskarki ne ba kya so na shigo naganki shi yasa kika rufe kofar.Koda jin wannan batu sai Jaruma tayi ajiyar numfashi sannan tace kai ma kasan cewa bazan taba yin bacci a irin wannan lokaci ba.Motsinka danaji shi yasa na fito da sauri tunda bansan meke faruwa ba.Ya kamata ka shiga cikin daki ka kwanta akan gado domin ka sami isasshen bacci tunda gobe da sassafe zamu tafi fada domin halattar wannan gasa ta karshe.Yarima yayi murmushi yace tabbas kinyi gaskiya domin idan ban kwanta da wuri ba zamu iya makara.Nan take Yarima ya shanye ruwan daya zuba a cikin kofin sannan ya mike tsaye ya shige cikin turakar jaruma na biye dashi.Saida Yarima ya kwanta sannan Jaruma ta janyo mayafi ta lullubeshi iya wuyansa sannan ta sake caje ko ina a cikin dakin don tabbatar da tsaro,sannan ta fice tana mai janyo kofar.Haka dai Jaruma ta cigaba da kai kawo a cikin falon kuma tana leka waje ta cikin tagogin falon har saida asuba tayi sannan taje ta kwanta.Aikuwa tana kwanciya bacci ya saceta.Wannan shine abinda ya faru a daren jiya a cikin gidan sarauta bangaren Yarima Kamzal.
A can fada kuwa saida sa'a

Please Login or Register in order to submit comment