Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko mace ko namiji duk wanda za'a haifa a zuri'armu bama gidanmu ba sai kaga ya taso da gagarumar Jarumtaka da sadaukantaka kuma gashi mun kasance kyawawa na gaban kwatance. Wannan daukaka da muke da ita da kuma nasibi a harkar mulki itace ta sanya tsananin hassada da kiyayya a cikin zuciyar sauran ragowar kabilu na kasar. Tun suna boye hassada da kiyayyarsu a cikin ransu har suka fara bayyanata a fili kuma suka rinka taro na sirri akan yadda za'a kwace mulki daga hannun zuri'ar Banu Amzad a bawa wata kabilar itama ta dana. Sarki Amzad ya kasance tamkar dodo a kasar domin kuwa kowa tsoransa yake yi saboda tsananin karfin damtsen sa da kuma karfin sihirin tsafinsa. Masana tarihi sun tabbatar da cewa tsabar karfin damtsen Amzad da kuma iya yakinsa shi kadai ya yaki birane goma sha biyu dake kewaye da kasar ya cisu da yaki kuma ya dawo dasu izuwa karkashin mulkinsa da karfin tsiya.Bisa wannan dalili ne ma ake yi masa lakabi da DARE GAMA DUNIYA. Komai kaurin gini ko dutse idan Sarki Amzad ya naushe shi saiya ruguje kai ko karfe ya nausa sai ya lauye koya lankwashe ba tare da yaji komai ba. Idan yana yaki kuwa yana iya shafe kwana uku cur yana SARA DA SUKAn mazaje ba tare da ya gaji ba ko ya bukaci ruwa da abinci ba. Kai komai yawan dakarun yaki saidai su gudu su barshi. Don haka ne ma akeyi masa kirari da SA GUDU MAGANIN KI GUDU wasu kuma suce dashi GA DODON MAZA ko DUBU TA TARU ALBARKA. Yana da wani lakanin sihiri wanda KAIFI DA TSINI basa tasiri a jikinsa kuma indai mutum ya tunkaro shi da wata muguwar hanya suna hada idanu zai ga niyarsa da mugun abinda yake dauke dashi. Bisa wannan dalili ne aka rasa hanyar da za'a bi aga bayan Sarki Amzad. Wani abin mamaki kuma a game da Sarki Amzad shine sarkin da yafi kowane Sarki dadewa akan karagar mulki domin saida ya shekera saba'in da hudu akan karagar mulki. Daidai da rana daya bai taba kwanciya ciwon daya kasa fitowa fada ba.Ranar farko a rayuwar kabilu shida ne sukayi taro na sirri akan yadda za'a tunbuke Sarki Amzad daga kan karagar mulki. Anyi taron ne a can wata kasa dake nesa da birnin Madinatul Sauwab wacce ake kira da Baitul Najmas. Birnin Baitul Najmas gari ne dake kan wani tsuburi shi kuma tsuburin akan tsakiyar teku yake. A tarihin birnin Baitul Najmas, gari ne na barayi da masu laifi wadanda ake nema ruwa a jallo.Duk irin laifin da mutum ya aikata a kowace nahiya indai ya sami nasarar guduwa izuwa birnin Baitul Najmas tofa yazo TUDUN TSIRA. Saboda ba a iya shiga garin da mugun nufi saboda wani tsaro na musamman da aljanun wajen ke baiwa garin. Koda niyar yaki akazo komai yawan jiragen ruwa na mayaka basa iya haye tekun face an fitar dasu kuma duk mayakan cikin jirgin sai sun hallaka. Mutum daya bazai tsira da rayuwarsa ba........ .. . . .

Anan zan daka Sai kuma wani lokacin Insha Allah.

Duk wanda zai dauki post dina ya dauka a yadda yake.Bana son editing. Take it the way it is.
Don't edit my post without my permission. ¶𝙆𝘼𝙍𝘼𝙂𝘼𝙍 𝙈𝙐𝙇𝙆𝙄¶
𝙇𝙞𝙩𝙩𝙖𝙛𝙞 𝙉𝙖 𝙃𝙪𝙙𝙪 (4) 𝙋𝙖𝙧𝙩 𝘽.

™𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍'𝒂𝒛𝒊𝒛 𝑺𝒂𝒏𝒊 𝑴𝒂𝒅𝒂𝒌𝒊𝒏 𝑮𝒊𝒏𝒊™.

𝑨𝒃𝒖𝒃𝒂𝒌𝒂𝒓❤️𝑯𝒂𝒍𝒆𝒆𝒇𝒂𝒉❤️𝑷𝒉𝒚𝒔𝒊𝒄𝒊𝒔𝒕

••••••••••••Mutum daya bazai tsira da rayuwarsa ba. Mutumin kirki bai isa ya shiga birnin Baitul Najmas ba saidai mutumin banza wanda babu alheri a zuciyar sa face mugunta da mugun nufi. Wannan shine ka'idar aljanun dake gadin birnin Baitul Najmas. Sau tara Sarki Amzad yana shirya DAKARUN YAKI Amma duk sa'adda yaje baya iya ketare wannan teku kuma duk mayakan dayaje dasu sai sun hallaka. Shi kadai yake dawowa gida a raye. Babu irin binciken da Sarki Amzad baiyi ba a cikin hallarar tsafinsa domin ya gano hanyar da zai isa birnin Baitul Najmas ya share shi daga doron kasa Amma abu ya ggagara. Abin da bai sani ba shine wanda ya bashi sirrin tsafinsa shike da mulkin birnin Baitul Najmas kuma ya kasance wani tsohon boka wanda shekarunsa sun kai dari da arba'in da uku. A nahiyar gaba daya babu tsohon daya fishi yawan shekaru har takai cewa baya ji kuma baya gani sannan baya iya magana. Jikokinsa ne ke kula dashi. Komai saidai ayi masa, a kwantar a tayar. Amma indai batu ne na dukiya da tsaro babu wanda ya fishi a nahiyar gaba daya. Inda Allah ya tauye shi shine rashin lafiya taji da gani da magana. Abinda aka jararbe shi dasu kenan a tsufansa. A na kiran wannan tsohon boka da suna Ukairu Bin Jaddas. Mutanen da suka yi taron sirri a birnin Baitul Najmas masu wakiltar kabilu shida su goma sha biyu ne. Akwai shugabannin kowace kabila da kuma babban boka na kowace kabila. A sirrance wadannan mutane suka iso birnin Baitul Najmas kuma daya bayan daya har suka gama haduwa a cikin wani gida dake can karshen garin. Shidai wannan gida sama da shekaru arba'in baya babu wani mai zama a cikinsa kuma asalin gidan na wani gawurtaccen barawo ne wanda yayi shahara a birnin kuma wanda ake matukar tsoron sa saboda karfin sihirin sa na tsafi. Ance bayan ya mutu ne yabar dukiya mai tsananin yawa a cikin gidansa Amma duk wanda ya taba dukiyar ko yayi amfani da ita saiya mutu. Bisa wannan dalili ne ko tsinke na gidan ba'a dauka ba komai yana nan yadda yake kamar yadda ya barshi. Kai saida takai cewa ma an daina shiga wannan gida saboda TSORON MUTUWA. Duk wanda kaga ya shiga kuwa to ya isa JAN WUYA kuma shima din bazai yi gangancin daukar komai ba a gidan.
Lokacin da wadannan mutane goma sha biyu suka zauna a cikin babban falon wannan gida sai bokayen suka hada hannayensu a waje guda suka karanta wadansu dalasumai na tsafi sau uku sannan kowannen su ya koma inda yake ya zauna. A sannan ne shugaban Kabilar da tafi dukkanin kabilub birnin Madinatul Sauwab yawa wanda ake kira da Shamshaki bini Zallas yayi gyaran murya yace yaku ya yan uwana shugabannin kabiloli da bokayenmu kun sani cewa fiye da shekaru saba'in baya Sarki Amzad ke mulkinmu a wannan birnin namu mai ALBARKA, gashi har ya tsufa Amma mulki bai dawo hannun wata kabila ba. Bincike ya tabbatar da cewa idan har muka bari dan Sarki Amzad ya karbi mulki tofah har abada karagar mulki a hannun kabilarsu da zuri'ar su zata kasance mun sani cewa sune mutane na farko da suka kafa kasar nan Amma a halin yanzu mun fisu yawa. Mun fisu tarin arziki kuma duk arzikin da muke samu hannunsu yake komawa saboda harajin da muke biya mai yawa. Yanzu takai cewa a nahiyar nan kaf babu mai tarin dukiyar Sarki Amzad kuma shine yake juya kowa a wannan birnin na Baitul Najmas ne kadai ya gagare shi mallaka. Bisa wannan dalili ne yasa muka shirya wannan taro domin muyi shawara akan yadda zamu maganance wannan matsala. Kun sani cewa ba zamu iya hallaka Sarki Amzad da KARFIB DAMTSE ba Koda karfin sihirin tsafin. Don haka dole ne muyi tunanin wata hanyar tunda dai masu iya magana sun ce hanyar kashe makahon kare yawa gareta. Sarki Amzad makahon kare ne wanda zai cizon kowa. Lokacin da Shamshaki yazo nan a zancensa sai gaba daya wakilan da kuma bokayen suka yi shuru suna tunani da nazari aka rasa wanda zai ce kala har izuwa tsawon yan dakiku. Koda ganin haka sai Shamshaki ya numfasa yace idan dukkanin ku baku da abin fada ni ina dashi. Ni a ganina idan har muna son mu kawar da Sarki Amzad kuma mu karbe mulki daga hannunsa dole ne mu hada kai da wani shakikinsa ko kuma wani babban hadiminsa amintaccensa wanda zamuyi masa dole yaci Amanarsa. Mu kawar dashi.Ckin sanyayyar hanya kuma mu kashe dansa Yarima Dalzuk. Idan mukayi nasarar kawar da Sarki Amzad da Yarima Dalzuk sai mu raba majalisar kasar tsakanin mu. Sannan a zabi Sarki. Ya zamana cewa muna da iko A cikin fada.Hatta karagar mulkin sai mu shirya gasa a tsakanin kabilun mu duk wanda yayi nasara sai ya hau kan karagar mulkin. Koda Shamshaki yazo nan a zancensa sai farin ciki ya lullube kowa. Amma sai Raihus shugaban Kabilar Banu Zaidur yace yakai Shamshaki yanzu kai a tunanin ka dawa zamu hada kai daga cikin shakikan Sarki Amzad mu sami nasarar kawar dashi kuma ta yaya zamu iya hallaka Yarima Dalzuk (Darzula) da iya yaki gami da karfin sihiri? Ka sani cewa wannan fa aikine mai tsananin hadari wanda idan asirinmu ya tonu gaba dayan mu babu wanda sai tsira da rayuwarsa. Kai bama mu ba danginmu ma da dukkan zuriar mu saidai suyi hijira su bar kasar. Lokacin da Raihus shugaban Kabilar banu Zaidur yazo nan a jawabinsa sai Shamshaki yayi ajiyar zuciya sannan yace yakai Raihus abinda ka fada gaskiya ne, to amma ka sani cewa matsoraci bazai taba zama gwani ba saboda kawai muna tsoron MUTUWA ba zamu zauna mu kwaci yancinmu ba, so kake 'ya'yanmu da jikokinmu su cigaba da zama a cikin BAUTA da bakin ciki har abada?
𝑨𝒃𝒖𝒃𝒂𝒌𝒂𝒓❤️𝑯𝒂𝒍𝒆𝒆𝒇𝒂𝒉❤️𝑷𝒉𝒚𝒔𝒊𝒄𝒊𝒔𝒕

Koda jin wannan batu sai ran kowa ya baci zuciyoyinsu suka kama tafarfasa kamar zasu kone kuma dukkanin tsoro ya kau daga zukatansu. A wannan lokaci ne ran Shamshaki yayi fari sannan ya dubi kowa daya bayan daya yace a halin yanzu nan da sati biyu Sarki Amzad zaiyi sabuwar amarya wata kyakkyawar budurwa wacce ta kasance 'yar talakawa daga kauyen Shammur, za muyi amfani da wannan budurwa da jyayenta domin hakarmu ya cimma ruwa. Ko kadan Sarki Amzad bai taba tunanin wannan hikima tamu ba. Koda jin wannan batu sai kowa ya aminta dashi aka rude da shewa. Tabbas akwai nasara amma kuma akwai wata matsala guda daya wacce suka kasa gano ko ta mecece. Al'amarin daya DUGUBZUMA hankalinsu kenan Amma sai su kace babu gudu babu ja da baya koda kuwa duk zasu hallaka.

A can GIDAN SARAUTAR Sarki Amzad kuwa a ranar da aka daura aurensa da amaryarsa Malina yana cikin tsananin farin ciki kai kace wani matashin saurayi ne alhalin ya kusa shekara tamanin a duniya. A wannan rana Yarima Dalzuk suna cikin tsananin bakin ciki bisa wannan aure domin sun tabbatar da cewar babu wani alheri a cikinsa. Lokacin da Sarki Amzad ya matsa akan cewa sai yayi wannan aure ne matar sa Zuraisa ta same shi a cikin turakarsa inda ta fashe da kuka tace yakai mijina akan wane dalili zaka dage sai kayi wannan aure alhalin kana da kwarkwarori da kuyangi kyawawa wadanda suka fi wannan amarya kyau da komai. Idan har ni kaina kana ganin cewa nayi maka tsufa to su kwarkwarorin fa da kuyangin naka fa wadanda a cikinsu akwai yan kasa da shekaru ashirin. Lokacin da Zuraisa tazo nan A zancenta sai Sarki Amzad ya taso daga kan shimfidar da yake kishingide. Dama a lokacin an zuba abinci da abin sha kala kala a gabansa yana ci yana nishadi da farin ciki. Sarki Amzad ya kama kafadun Zuraisa ya ruke su suka fuskanci juna. A lokacin da idanunsa suka ciko da kwallah yace yake matata ki tuna cewa yau fa kusan shekaru talatin da hudu kenan dayin aurenmu. Ni dake a tsawon wannan lokaci ban taba tunanin yi miki kishiya ba sai yanzu. Lallai kuwa kin sani cewa ruwa baya tsamin banza kuma banza bata kai zomo kasuwa. Ina da wata matsala guda daya jal a duniya wadda ta addabi rayuwata kuma ta jefani cikin tsananin bakin ciki. A kullum idan na tuno da wannan matsala nakanyi kuka har na ZUBAR DA HAWAYE na. Ba komai bane wannan matsala face Bokana Kimbaru bin Alsasi a farkon rayuwata Tun daga kuruciyata kawo zuwa girma na babu mutumin dana aminta dashi sama da boka Kimbaru saboda a gidan su ne asalin bokayen gidanmu suke. Kakan kakana ma da gidansu yayi hulda, kinga kenan nima gadon Kimbaru nayi. Boka Kimbaru bai taba cin amanata ba kuma babu irin taimakon da baiyi mini a rayuwata ba, kuma duk fadin duniyar nan babu wanda yasan sirrin da za'a yi amfani dashi wajen hallakani face shi. Hatta ke dinnan da kike matata kuma uwar 'dana ban taba gaya miki wannan sirri ba. A tsawon shekarun zaman mu abu daya ne ya bani tsoro yasa nake tunanin cewa ko boka Kimbaru bai ci amanata ba yanzu nan gaba magajinsa zai iya cin amanar 'dana har takai cewa wannan KARAGAR MULKI tabar kabilar mu ta koma izuwa wata kabilar. Wannan abu kuwa ba komai bane face wanzuwar birnin Baitul Najmas kuma ya wanzu ne a cikin abinda baifi wata uku ba. Ba kowa ne ya kafa wannan birnin ba face boka Kimbaru. Birni ne na manyan barayin duniya kuma manyan masu laifi wadanda ake nema ruwa a jallo. Saboda me boka Kimbaru ya kafa wannan birnin na mutanen banza?wannan itace tambayar dana yiwa kaina kuma na kasa fitar da amsarta. A tunani na iya dukiyar da nake bawa boka Kimbaru ta ishe shi rayuwa a duniya ashe shi ba haka bane. Kamar yadda na mallaki matar aure guda daya jal gami da 'da daya haka shima boka Kimbaru ya mallaka. Ni dashi sa'annin juna ne. Me zaiyi da dukiya mai tarin yawa alhalin shekarun sa sun taru da yawa kamar nawa. Ko A yanzu iya abinda ya mallaka nan da shekara dubu iyalansa ba zasuyi talauci ba. Bisa binciken da nayi na zahari duk barayin dake cikin birnin Baitul Najmas da dukkanin masu laifin dake garin suna biyan haraji mai tsoka a duk kwana talatin. Wannan birnin na Baitul Najmas Ana shirya makirci, cuta, sace sace, kisan kai da dukkan kowane laifi a cikinsa. Ni kaina ance makiyana suna shirya taro na ganin bayana a cikin wannan birni kuma boka Kimbaru yasan da haka saboda me zaiyi mini haka? Bisa wannan dalili zuciyata ta kasa samun sukuni da kwanciyar hankali har na shirya da kaina na tafi izuwa ga boka Buda na birnin Sin bokan da babu kamarsa a sanin ilmin abinda zai faru a gaba. Na sashi yayi mini bincike akan abinda zanyi na tabbatar da dorewar mulkin kasar nan a hannun kabilarmu. Kuma a cikin gidan mu. Abinda boka Buda ya fara gaya mini shine na kara aure kuma lallai amaryar da zan auro ta kasance daga kabilata. Nasan cewa zata iya cin amanata har makiyana su sami nasara akaina. To amma fa idan har banyi wannan aure ba sai wannan sarauta tabar gidanmu da kabilar mu domin Yarima Dalzuk bazai taba zama Sarki ba.

𝑨𝒃𝒖𝒃𝒂𝒌𝒂𝒓❤️𝑯𝒂𝒍𝒆𝒆𝒇𝒂𝒉❤️𝑷𝒉𝒚𝒔𝒊𝒄𝒊𝒔𝒕

Koda Sarki Amzad yazo nan a zancensa sai hawaye ya zubowa Zuraisa tace yanzu kana nufin kace dana bazai gaje ka ba? Koda jin wannan tambaya sai hawaye ya zubowa Sarki Amzad yace kwarai kuwa domin binciken Boka Buda ya tabbatar da hakan. Zuraisa ta cakumi rigar Sarki Amzad cikin dimauta tace bazai yiyu ba boka Buda makaryaci ne akan me zaka yarda dashi?Koda ganin haka sai Sarki Amzad ya rungume Zuraisa a kirjinsa yana mai kankame ta a lokacin da duk su biyun suka fashe da kuka. Daga can saiya janye jikinsa daga cikin nata suka sake fuskantar juna yace yake matata kin San cewa a duniya babu abinda nake kauna sama da Yarima Dalzuk kuma bani da burin da yafi ace Dalzuk ne ya gaje ni. To Amma yaya zamuyi da kaddara? Abinda zan iyayi kawai shine na tabbatar da cewar wannan mulki bai bar hannun kabilarmu da zuri'ar mu ba. Koda Sarki Amzad yazo nan a jawabinsa sai Zuraisa taja da baya daga gare shi ta dubeshi a fusace tana zubar da hawaye tace to yanzu saboda kawai baka son wannan mulki ya subuce daga zuri'ar mu sai ka auro macen da zamo sanadin ajalinka. Shike nan sai ta raba mu da kai. Yayin da Sarki Amzad yaga Zuraisa ta fusata kuma ta rude sai ya sake kamota ya rungume ta kan kirjinsa sannan yace yake matata ko Ina so ko bana so girma ya kamani kuma MUTUWA a koyaushe zata iya kwankwasa mini Kofa.idan makiya basu kashe ni ba tsufa da cikar lokaci zasu cimmani ko kuma cuta ta zamo sanadin ajalina tunda a halin yanzu liktana ya tabbatar mini da cewa Ina dauke da ciwo HAWAN JINI. Kuma na sami sannan ciwo ne watanni uku baya daga ranar dana gano cewa boka Kimbaru shike da mallakar birnin Baitul Najmas. Ni yanzu bana tsoron MUTUWA abinda nake tsoro kawai shine ta yaya bayana zata kasance tunda har na sami tabbacin cewa Yarima Dalzuk bazai hau karagar mulki ba, dole ne na gaggauta yin wannan aure domin na sami magaji kuma dole ne na sanar da Yarima Dalzuk komai don kada sai bayan raina yaga kamar na ha'ince shi a na boye masa gaskiya.
Koda jin wannan batu sai Zuraisa ta fashe da matsanancin kuka tana mai dada kankame Sarki Amzad tace yanzu wane irin bakin ciki Yarima Dalzuk zaiyi idan yaji cewar bazai gaje ka ba? Shin baka tunanin cewa zaiki amincewa da wannan aure da zakayi kuma zai iya aikata abinda bai dace ba Koda kuwa hakan zai iya janyo rushewar kaunat dake tsakanin ku ta 'DA da MAHAIFI. Sa'adda Sarki Amzad yaji wannan tambaya sai yaja dogon numfashi sannan yace na fiki sanin waye Dalzuk duk da cewa kin fini kasancewa a tare dashi. Ina mai tabbatar miki da cewa ni nasan duk hanyoyin da zan bullo masa yadda zai iya Rungumar kaddara. Abinda nake so dake kawai shine kada kikuskura ki fara sanar dashi komai akan wannan al'amarin. Zan kadaita dashi mu tattauna Amma sai bayan na dawo daga gidan boka Kimbaru. Koda jin haka sai zuciyar Zuraisa ta buga da karfi ta dubeshi cikin alamun tsananin tsoro tace me kuma zakayi a gidan boka Kimbaru? Sarki Amzad ya numfasa yace mahaifina kafin ya rasu ya bar mini wasiyar abu uku akan boka Kimbaru. Wasiyar farko itace kada na kuskura na nunawa boka Kimbaru cewa Ina tsoro sa. Wasiya ta biyu kuma itace duk sa'adda boka Kimbaru yayi min wani laifi kada na boye abin a raina. Na fito fili na nuna nasa. Wasiya ta uku wacce itace ta karshe itace na nemi shawarar Kimbaru bisa duk abinda ya shige mini gaba. Yake matata kiyi sani cewa yau ne za'a kawo mini amaryata Malina Amma sai idan dare ya raba. Bisa al'adar kabilarmu abinda nake so dake shine yanzu bayan na tafi gidan boka Kimbaru ki shaidawa Yarima Dalzuk cewa ya jirani nan da cikar sa'a biyu zan gana dashi a sirrance anan cikin turakarta kafin naje dakin amaryata. Koda gama fadin haka sai Sarki Amzad yaje ya bude dirowar da yake ajiye kayan yakinsa. Nan take ya dauko sulke da damara ya sanyasu sannan ya dauki takobinsa da garkuwarsa ya juya zai fita daga cikin turakar. A guje Zuraisa tasha gabansa ga dube shi a cikin firgici da tsananin tsoro tace yaya kai da kace zaka je gidan boka Kimbaru kuma kayi shigar yaki haka? Shin zaka je kayi yaki da boka Kimbaru ne? Koda jin wannan tambaya sai Sarki Amzad yayi murmushi yace sannan yace ai ko hauka ne ya same ni bazan je na baki Kimbaru ba, ba komai bane yasa kikaga nayi shigar yaki ba face saboda ni kadai nake son na tafi izuwa gidan boka Kimbaru kuma a wannan lokaci da muke ciki rayuwata na cikin hadari domin a koyaushe makiya zasu kawo mini hari duk da cewa na yarda da kaina bazan yi sakaci da rayuwata da lafiya ta ba. Tunda bani da tabbacin cewa baza a iya cin amanata ba. Koda gama fadin haka sai Sarki Amzad ya juya ya fice daga cikin turakar tasa ya nufi inda bargar dawakansa take. Nanfa gaba daya hadimansa suka firgice bisa gani Sarki a cikin shigar yaki aka fara zargin ko harin bazato aka kawo wa kasar. Amma da kaga Sarki ne kadai ya fito a cikin shigar yaki sai aka gane cewa ba haka bane. A guje sarkin yaki ya karaso gaban Sarki Amzad ya zube yana haki yace haba ya shugaba na wane abu ne mai girma haka ya taso wanda har bazaka turani ba nayi maganinsa? Cikin sauri Sarki Amzad ya kama kafadun sarkin yaki ya tashe shi tsaye ya dubeshi yace ai ba yaki bane yazo mana wata unguwa nake son zuwa kuma ni kadai zanje kada ka bari kowa ya biyo ni bare aga inda zanje. Sarkin yaki ya risina yace an gama ya shugabana. Nan take sarkin yaki ya ruga izuwa cikin bargar dawakan ya kamo dokin sarki da sauri ya dora nasa siddi ya kawo masa. Cikin hanzari sarki Amzad ya haye dokin ya zabureshi da gudu ya fice daga cikin gidan sarautar.
........ A can Kauyen su amarya Malina kuwa tun da sassafe aka fara shagalin biki a kofar gidan mai gari Mahaifin Malina. Nan fa mawaka da makada suka taru suka fara........

Sorry for the delay.
Babu abin typing.
Ayyuka sun min yawa. ¶𝙆𝘼𝙍𝘼𝙂𝘼𝙍 𝙈𝙐𝙇𝙆𝙄¶
𝙇𝙞𝙩𝙩𝙖𝙛𝙞 𝙉𝙖 𝙃𝙪𝙙𝙪 (4) 𝙋𝙖𝙧𝙩 🅒.

™𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍'𝒂𝒛𝒊𝒛 𝑺𝒂𝒏𝒊 𝑴𝒂𝒅𝒂𝒌𝒊𝒏 𝑮𝒊𝒏𝒊™.

Abubakar Haleefah Physicist

.... ••••A can Kauyen su amarya Malina kuwa tun da sassafe aka fara shagalin biki a kofar gidan mai gari Mahaifin Malina. Nan fa mawaka da makada suka taru suka fara aikinsu. Maza da mata kuwa sai tikar rawa sukeyi ana ta taya mai gari murnar bikin 'yarsa. Abinci da abin sha kuwa sai fitowa ake dasu daro daro. Mutane suka wanzu suna warwasawa har dare ya fara. Sannan jama'a suka fara watsewa. Ana cikin haka sai sako yazowa mai gari cewa dakarun sarki suna tafe.Sune wanda zasu dauki Amarya Malina izuwa gidan sarauta. Koda jin wannan batu sai mai gari ya cika da tsananin farin ciki. Malina ita ma haka. Nan fa aka shiga shirye shiryen daukar Amarya ana kimtsa kayan ta kuma ta fara yin sallama da yan uwa da abokan arziki. Ta rinka rungume su suna kukan rabuwa.

Kash ashe wadannan dakaru da akace sun taho daukar Amarya ba dakarun sarki Amzad bane. Asalin wadannan dakaru n sarki Amzad wadanda suka taho daukar Amaryar an tare a daji an kawo musu harin bazato an kashe su gaba dayan su. Su dari da arba'in dayansu bai tsira da rayuwarsa ba. Ba wasu bane sukayi wannan mummunan aiki ba face dakarun sauran kabilun shida na kasar bisa jagorancin Sadauki Kan'an babban 'da ga shugaba Shamshaki. Bayan su Sadauki Kan'an sun tabbatar da cewar sun kashe gaba dayan dakarun sarki Amzad masu dauko amarya sai sukayi musayar tufafi dana dakarun suka dau makaman su na yaki suka haye dawakansu suka cigaba da tafiya izuwa garinsu amarya Malina har suka iso. Da isowarsu kofar gidan mai gari sai suka ja linzamin dawakansu sukayi cirko cirko nan take Sadauki Kan'an bin Shamshaki ya sauko daga kan dokinsa ya zube kasa gaba mai gari ya kwashi gaisuwa sannan ya mika masa wata takardar wasikar sarki Amzad. Mai gari ya bude wasikar yaga tabbas rubutun sarki ne a jiki har da hatiminsa mai nuna tabbacin cewa su aka turo su tafi da amarya. Cikin farin ciki mai gari ya karbe su ya shigar dasu aka kawo musu abinci da abin sha na alfarma suka ci suka hantse. Ba tare da bata lokaci ba mai gari ya kirawo gaba dayan matansa da 'ya'yansa har da amarya Malina suka shigo izuwa cikin turakarsa domin su dankawa masu daukar Amarya kuma suyi bankwana da ita. Aikuwa suna gama shigowa sai suka ga dakarun sun kulle kofa kuma sun zare makamansu suna masu yi musu KAWANYA. Al'amarin daya razana mai gari da dukkan iyalan nasa kenan suka firgita ainun. Kawai sai Sadauki Kan'an ya yaye mayafin daya rufe fuskarsa dashi ya dubi Mai gari fuskarsa a murtuke ba kyan gani yace ya kai Baban Amarya

Please Login or Register in order to submit comment