Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har ka zamo Sarki zaka cika mini su. Daya daga cikin alkawarin zaka iya yinsa tun gabannin ka zamo Sarki. Alkawari na farko shine kace dani daga yau rashi ko bakin ciki ko azaba ba zasu sake saka ka zubar da hawayenka ba. Ka sani cewa rashin zubar da hawaye alamace ta Sarkin da zai iya hawa karagar mulki a cikin kowane irin kangi. Sarkin da baya zubar da hawaye dole ne makiyansa da masoyansa suyi shakkarsa. Domin ya cika NAMIJIN DUNIYA ko za'a sami galaba akansa sai DUBU TA TARU.Alkawari na biyu da nake so ka daukar mini shine idan ka zama Sarki zaka cigaba da tsaron Kogin Bahar Lihiram, ya'yan ka da jikokinka ma zasu gaji tsaron Kogin Kamar yadda nakeyi yanzu. Ka sani cewa bawai dakarun da muke zubawa a bakin gabar kogin sune suke iya tsareshi ba, akwai wani babban sirri na tsaron Kogin Bahar Lihiram wanda ba zan iya gaya maka shi ba. Amma nan gaba bayan ka zama Sarki zaka San shi kuma kaima ba zaka iya gayawa danka daya gaji karagar mulki a hannunka ba saidai ya sani a karan kansa. Shin zaka iya daukar mini wadannan alkawarurruka guda biyu. Sa'adda Yarima Kanzal yaji wannan tambaya sai yai ajiyar zuciya cikin kwarin guiwa ya dubi Sarki yace lallai na daukar maka alkawari zan cika wadannan muradi guda biyu Kamar yadda ka umarce ni. Koda jin haka sai fuskar Sarki ta fadada da murmushi kuma ya cika da dimbin farin ciki ya janyo Yarima Kanzal ya rungumeshi akan kirjinsa sannan yace ai tun yanzu ma ka nuna mini cewa lallai zaka iya cika wannan alkawari guda biyu. Koda jin haka sai Yarima Kanzal ya dubi Sarki cikin mamaki yace menene dalilin da yasa kace zan iya cika wannan alkawari? Sarki yace gashi tun yanzu ka daina zubar da hawaye. Ban taba zaton cewa maganar nan ta karshe da kayi zata fito daga bakin ka va tare da hawayen idanunka sun rako ka ba. Wannan shine abin daya faru a yan shekarun da suka gabata a baya.

•••Lokacin da Yarima Yunus yaga gawar Masoyiyarsa Umaira take ya tsandara uban ihu kuma ya fashe da matsanancin kuka, sannan ya rungume gawar Umaira a kirjinsa a zaune saida ya kwana ya yini a hakan yana kuka da kyar aka banbare gawar Umaira daga hannunsa sannan aka je aka binneta. Da yake Yarima Yunus ya kasance Gawurtaccen matsafi saiya shiga HALWAR TSAFI domin ya gano wanda ya kashe Masoyiyarsa amma saida ya kwana uku yana bincike amma sai ya kasa gano wanda yayi kisan. Dama ya hana a binne gawar Umaira sai bayan ya gama bincikensa don haka a cikin kankara aka adana gawar.
A ranar kuwa na ukun ne ya fito daga halwar tsafin yasa aka cire gawar daga cikin kankara domin aje a binneta a lokacin yana ta faman shara kuka. A kokarin fito da gawar ne tsulum akaga abin hannun Yarima Imran ya fado daga cikin gawar. Koda idanun Yarima Yunus suka kai kan abin hannun saiya sunkuya ya sauka ya dubeshi da kyau ya tabbatar da cewar na Yarima Imran ne saiya takarkare ya kwarara uban ihu yana mai ambaton sunan Yarima Imran. Nan take ya zare takobinsa ya nufi gidan SARAUTAR yana kwalawa Yarima Imran kira. Nanfa gaba dayan jama'ar dake cikin gidan SARAUTAR suka firgice ba'a sami wanda yasha gabansa ba saboda tsananin tsoransa da ake ji. A gaba dayan kasar Hindu babu SADAUKAN JARUMAI wanda ake takama dasu akan iya yaki gami da TARWATSA MAZA sama da Yarima Yunus da Yarima Imran, domin ko yaki za'a fita sune akan gaba kuma basu taba Jagorantar yaki an rasa nasara ba. Sannan ba'a taba kai dayansu kasa ba a FILIN YAKI. Labarin Jarumtakarsu ya bazu ko ina a nahiyar takai cewa saboda su biyu kacal duk kasashen dake nahiyar suna tsoron suyi yaki da kasar Hindu.
Yarima Imran na zaune a cikin Lambun gidan SARAUTAR yana shakatawa tare da kuyanginsa ana debe masa kewa kawai sai yaji gidan sarautar ya hargitse, bayi da borori, hadimai har da dakarun ma sai guje guje suke suna neman inda zasu buya. Cikin tsananin fushi Yarima Imran ya mike tsaye zumbur ya tari wani bawa daya taho da gudu ta gabansa zai wuce ya cafke shi da hannu daya sai gashi kafafunsa na reto a sama tamkar dan shila ya daga. Yarima Imran ya dakawa bawan tsawa yace lafiya, menene yake faruwa ake ta guje guje haka a cikin gidan nan? Muryar bawan na rawa yace ya shugabana ai Yarima Yunus ne ya zare takobi ya shigo gidan nan da gudu yana ta kwala maka kira ga dukkan alamu dai yana zargin ka ne akan mutuwar budurwarsa Umaira. Koda jin wannan batu sai Yarima Imran yayi jifa da bawan dake hannunsa sannan shima ya zare tasa takobin cikin tsananin fushi ya ruga gudu izuwa hanyar shigowa cikin gidan sarautar yana mai kwalawa Yarima Yunus kira. Faruwar hakan keda wuya sai gasu sun hadu a wata babbar farfajiya ta gidan sarautar kuma tazarar dake tsakaninsu bata wuce taku goma ba. Nan fa kowannensu yayi turjiya har kura ta tashi suka fara kallon kallo suna muzurai da huci kai kace bakaken macizai masu mugun dafi suka dana domin kai sara. Cikin alamun tsananin fushi, hawayen takaici ya zubowa Yarima Yunus ya dakawa Yarima Imran tsawa yace akan wane dalili zaka kashe mini Masoyiyata wacce tun ina yaro karami nake sonta, shin kana ganin cewa hakan da kayi shine zai dasa min CIWON ZUCIYA na mutu a banza domin ka gaji karagar mulki. Kafin Yarima Yunus ya gama rufe bakinsa tuni Yarima Imran ya tari numfashinsa yana mai daka masa tsawa yace kai wawa mara tunani ya za'ayi na kashe maka Masoyiya alhalin nima Ina da Masoyiyar kamar taka wacce idan na rasata zanyi bakin cikin da kake yi, menene hujjarka da zakace nine na kashe Umaira? Koda jin wannan tambaya sai Yarima Yunus yayi MURMUSHIN TAKAICI sannan ya zura hannunss a cikin aljihu ya fiddo da abin hannun Yarima Imran wanda akayi shi ds Zinare yace wannan abin hannun waye? Koda ganin abin hannun sai Yarima Imran ya cika da tsananin mamaki, cikin kaduwa ya dubi Yarima Yunus yace na rantse da girman Ubangijinmu har izuwa safiyar yau Ina tare da wannan abin hannu nawa, ni ban san sa'adda ya bar jikin hannuna ba har yazo hannunka. Koda jin haka sai Yarima Yunus ya tari numfashin Yarima Imran yana mai daka masa tsawa yace karya kake munafiki yanzun nan zan kashe ka da hannuna tunda dama nasha turo DAKARUB SUMAME a sirrance domin su kashe ka basu sami nasara ba Yarima Imran yayi dan guntun murmushi yace ai nima nasha turo maka dakarun sojan haya don su kashe ka basa samun nasara, kaga yanzu kenan sai muyi ta ta kare. Nan take duk su biyun suka rugo izuwa kan junansu suna kwala ihu mai tsananin firgitarwa suna haduwa sai suka kacame da AZABABBEN YAKI ya zamana cewa suna kaiwa junansu SARA DA SUKA cikin tsananin bakin ZAFIN NAMA, JURIYA da BAJINTA kuma kowannensu yana yaki ne da dukkan karfinsa da zuciyarsa kawai burinsa shine yaga ya hallaka dan uwan nasa. Nan da nan suka tashi haikan komai da kowa dake cikin gidan sarautar hankalinsa ya dugunzuma aka rasa wanda zaije ya shiga tsakaninsu ya raba wannan fada. Duk sa'adda suka kaiwa juna sara suka goce to fa duk abinda suka samu walau gini ko bishiya ko wani abu saidai kaga sun tsarge shi saboda tsananin kaifin takubban nasu wadanda suka kasance na musamman. Saida suka shafe kusan rabin sa'a suna wannan BAKIN ARTABU sannan kowannensu ya sami nasarar yankan dan uwansa. Duk su biyun suka kwala ihu a lokaci guda sakamakon zafi da zogin daya shige su a lokacin da jini yayi tsartuwa daga cikin raunikan nasu. Kuma ba shiri kowannensu yaja da baya. Shi dai Yarima Yunus a kafarsa ta hagu Imran ya yanke shi, shi kuma Yarima Imran akan kirjinsa bangaren dama aka yankeshi. Faruwar hakan ne tasa suka gane cewa idan fa suka ce zasu cigaba da yakar juna to saidai fa ayi biyu babu ma'ana zasuyi RAGAS. Ya zamana cewa duk su biyun babu wanda ya sami KARAGAR MULKI. Koda gama aiyana hakan sai Yarima Yunus ya shammaci Yarima Imran ya watso masa kibiyoyin tsafi. Kibiyoyin sunfi guda dubu kawai sai suka tafi da gudu a sama cikin iska zasu tsire Yarima Imran. Koda ya rage saura baifi kamu daya ba tsakanin jikin Imran da kibiyoyin sai akaga kibiyoyin sun tsaya cak a cikin iska sannan kuma sai gaba dayansu suka kama da wuta suka kone kurmus suka zama toka. A daidai wannan lokaci Yarima Imran ya dubi Yarima Yunus ya bushe da dariya yace yakai dan uwana kaje ka sake yin shiri wai dan ka rigamu shigo duniya ba lallai bane ka rigamu samun ilmi ba. Sai mun hadu a filin Gasar KARAGAR MULKI sannan ne za'a bambance tsakanin Zare da abawa. Kaje ka nemi wanda ya kashe Masoyiyarka amma bani ba. Shin zaka iya bani abin hannuna? Wanda ya sace wannan abin hannu nawa tabbas shine ya kashe Masoyiyarka kuma na fuskanci cewar lallai ya cika MURUCIN KAN DUTSE domin bai fito ba saida ya shirya ba don haka ba da tuni ka gano ko waye tunda sa'adda ka shiga HALWAR TSAFIn ka.sa'adda Yarima Imran yazo nan a zancensa sai jikin Yarima Yunus yayi sanyi kadan ya jefa masa abin hannunsa ya cafe amma duk da haka saiya dubeshi a fusace yace kada ka dauka cewa na gamsu cewa bakai bane ka kashe Masoyiyata ba, zan cigaba da bincike tunda bani da abin zargi sama da kai. Idan har na tabbatar da cewar kai ne lallai saina DAUKI FANSA Koda kuwa ace kaine ka sami nasarar hawa KARAGAR MULKI. Koda gama fadin haka sai Yarima Yunus yai sauri ya cire rawanin kansa ya daure raunin dake jikinsa don tsaida jinin dake zuba ya nufi bangaren da turakarsa take shima Yarima Imran saiya dafe nasa raunin ya nufi inda tasa turakar take.

•••Lokacin da Yarima Kanzal da Yarima Yunus suka zo gaban wannan akushi mai dauke da lambobin gasa sai duk su biyun suka zura hannayensu a cikin akushin a tare kowannen su ya dauko tasa takardar, mutum na uku daya dauko takardar shine Yarima Imran, sannan ragowar ya'yan sarki su shida. Su duka taran sai aka umarce su dasu zo gaban alkalan gasar su bude takardunsu......

Abubakar Haleefah Physicist.

Via:- Dandalin Triple A Hausa Books 📚 ¶KARAGAR MULKI¶
Littafi Na Daya(1) Part C.

™Abdul'aziz Sani Madakin Gini.™

A•Haleefah--Physicist.

•••Lokacin da Yarima Kanzal da Yarima Yunus suka zo gaban wannan akushi mai dauke da lambobin gasa sai duk su biyun suka zura hannayensu a cikin akushin a tare kowannen su ya dauko tasa takardar, mutum na uku daya dauko takardar shine Yarima Imran, sannan ragowar ya'yan sarki su shida. Su duka taran sai aka umarce su dasu zo gaban alkalan gasar su bude takardunsu. Nan take kuwa suka jera su taran kowannensu ya bude takardsrsa, kwatsam sai akaga Yarima Kamzal da Yarima Yunus sun bude lamba dai dai. Take ragowar yan uwan nasu su Yarima Imran sukayi ajiyar zuciya cikin murna saboda ganin ba dasu za'a fara wannan gasa ba. Kuma fuskokinsu suka cika da murmushi. Koda ganin haka sai Yarima Yunus ya dubi su Yarima Imran yayi musu MURMUSHIN MUGUNTA yace wai shin murnar me mukeyi alhalin hutun jaki da kaya zakuyi.Tunda dole ne kuma tambayoyin su zo kan ku. Nan take aka kai Yarima Kamzal da Yarima Yunus izuwa kan wadansu kujeru biyu dake fuskantar alkalan gasar aka zaunar dasu. Zamansu keda wuya sai Yarima Kamzal ya hango mahaifiyar sa Zarina zaune a inda sauran matan sarki suke. Ta kura masa idanu tana ZUBAR DA HAWAYE. Kawai saiya dubeta yayi murmushi yai mata nuni data kwantar da hankalinta. A wannan lokaci fadar tayi tsit kowa ya kasa kunne domin yaji irin tambayoyin da za'a yiwa ya'yan sarki. Mai gabatar da tambayoyin ya fito daga inda yake zaune yazo gaban su Yarima Kamzal ya tsaye. Koda da hada idanu da wannan Jaruma wacce ke tsaye a bayan Yarima Kamzal sai yaji zuciyarsa ta buga da karfi. Al'amarin daya bashi mamaki kenan domin shi kansa bai san dalilin da yass zuciyarsa ta buga ba. Shin ganjn ganin kyawawan Idanuwan Jarumar ne ya janyo haka ko kuwa Kwarjinin tane da KYAWUN SIFFAr jikinta ta 'YA MACE? Amsar daya kasa baiwa Kansa kenan don haka sai yayi sauri ya kau da idanun sa ga barin kallonta ya dubi Yarima Kamzal yace ya shugabana zamu fara tambaya ta farko, itace WADANNE ABUBUWA GUDA UKU WADANDA DOLE SAI IDAN SARKI YANA DASU SANNAN ZAI IYA SHUGABANCIN AL'UMMARSA? Koda jin wannan tambaya sai Yarima Kamzal yayi murmushi sannan ya dubi mai tambayar yace
*Abu na farko shine dole sarki ya zamo da Kwarjini da kuma Siffa ta shugabanci.
*Abu na biyu dole sarki ya zamo mai tunani da nazari akan duk al'amuran da suka zo masa kafin ya yanke hukunci.
*Abu na uku shine dole ne sarki ya zamo mai hankali ya kasance bashi da tabin kwakwalwa. Wanda duk bashi da wadannan abubuwa uku bai cancanci ya hau KARAGAR MULKI ba. Gama fadin haka keda wuya sai mai tambaya ya dubi alkalan gasa yace shin Yarima Kamzal ya amsa tambayar sa daidai? Cikin hadin baki alkalan gasar suka ce ya masa dai dai. Da jin haka fadar ta rude da shewa ana tafi. Mai tambayar ya daga hannunsa sama akayi tsit sannan ya juya ya fuskanci Yarima Yunus yace yakai Yarima Yunus na juyo gareka. WADANNE ABUBUWA NE GUDA UKU WADANDA SARKI ZAI KIYAYE DON KARE TALAUCI, FARI DA CUTUTTUKA A KASARSA? Koda jin wannan tambaya sai Yarima Yunus yayi ajiyar numfashi yayi shiru na yan dakiku kadan sannan yace
*Mataki na farko da sarki zai dauka shine Kyautata harkokin noma ta hanyar samar da ruwa, irin shuka da tallafi ga manoma.
*Mataki na biyu shine samar da Sana'oi ga masu ZAMAN BANZA gami da inganta Sana'oin.
*Mataki na karshe wanda shine na uku tabbatar da tsabtar muhalli da kuma bayar da horo ga sababbin Likitoci domin Wadatar dasu ko ina cikin kasa gami da yawaita shuke shuke na ya'yan itatuwa wadanda ake sarrafasu ayi magunguna. Koda jin wannan amsa sai mai gabatar da tambaya ya dubi alkalan gasa yace yaya shin Yarima Yunus ya amsa tambayoyin dai dai? Cikin hadin baki alkalan gasa suka ce ehh ya amsa daidai. Take Yarima Yunus da masoyansa suka rude da ihu gami da shewa har saida aka daga hannu sannan suka nutsu. Haka dai aka cigaba da yiwa Yarima Kamzal da Yarima Yunus tambayoyi har aka yiwa kowannensu tambayoyi goma goma kuma cikin sa'a suka amsa daidai babu wanda ya fadi ko tambaya daya.
Kashe gari kuwa da aka zauna a don cigaba da wannan gasa tsakanin Yarima Imran da Yarima Zainur da kyar Yarima Imran ya amsa dukkanin tambayoyinsa guda goma shi kuwa Yarima Zainur tambayoyi uku kacal ya amsa daidai amma duk ragowar tambayoyin guda bakwai faduwa yayi. Haka dai aka cigaba da yin wannan gasa har tsawon kwana tara. Kuma Yarima Imran ne kadai ya samu nasarar zuwa zagaye na uku ya kafsa da Yarima Kamzal da Yarima Yunus amma sauran ya'yan sarkin tun a zagaye na biyu aka zubar da su. Suka kamu da tsananin bakin ciki sukayi ta rusa kuka.Kai wasu ma daga cikinsu saida suka kusan zautuwa saboda sambatu da iface iface suka kama yi suna zage zage da doke doke har saida aka kama su aka kulle su cikin daki. Da yake saura kwana biyu ayi zagayen karshe na gasar sai hankalin Yarima Yunus ya DUGUNZUMA ainun domin yana ji a jikinsa cewar lallai Yarima Kamzal zai iya kashe wannan gasa saboda la'akari da yayi yadda yake amsa duk tambayoyin da akeyi masa. Tunda ake yiwa Yarima Kamzal tambaya a cikin wannan gasa bai taba yin tunani ba ko bata lokaci kafin ya bayar. Kai tsaye yake amsa tambayoyin kamar da ma can ya haddace amsoshin a cikin kwakwalwarsa. Bisa wannan dalili ne Yarima Yunus ya fara tunanin hanyar da zaibi ya hallaka Yarima Kamzal ya zamana cewa bai sami damar halattar gasar ta karshe ba da za'a yi ba. Cikin sirri Yarima Yunus ya tura izuwa Birnin Romaniya dauko hayar wadansu zakakuran DAKARUN SUMAME mutum dubu biyu bisa shirin cewa ana I gobe gasar karshe wadannan dakarun sumame zasu mai MAMAYAR BAZATO izuwa turakar Yarima Kamzal su hallaka shi. Yarima Yunus na cikin yin wannan shiri ne matar sarki Jalila ta sami nasarar kashe ya'yan sarki guda biyu ta hanyar sa musu guba a cikin abincinsu. Al'amarin daya hautsuna gidan SARAUTAR kenan aka shiga bincike mai tsanani domin gano wanda ya hallaka ya'yan sarki amma duk wadanda suke da hannu a cikin al'amarin da zarar an kama su kafin a fara binciken su sai kaga sun kashe kansu ko kuma an kashe su a sirrance ba tare da ansan wanda ya kashe su ba. Abu dai kamar wasa mutuwar ya'yan sarki ta cigaba da faruwa ya zamana cewa saura su uku kacal wato daga Yarima Kamzal sai Yarima Yunus da kuma Yarima Imran. Iyayen ya'yan sarkin da aka kashe kuwa mata da yawansu zuciya suka hadiya suka mutu saboda tsananin bakin ciki. Wasunsu kuwa suka kwanta matsananciyar rashin lafiya. Kai a tarihin wannan gidan sarautar ba'a taba ganin tashin hankali da masifu ba akan karbar mulki irin wannan ba. Babu abinda Jalila batayi ba domin ganin ta kashe Yarima Imran amma ta kasa. Sau bakwai tana sawa ana sa masa guba a cikin abincinsa amma yaki yadda ya ci.Burinta kawai shine ya rage Yarima Kamzal da Yarima Yunus kadai a gabanta in yaso ko bayan daya daga cikinsu ya hau kan karagar mulkin zata san yadda zatayi ta kawar dasu daya bayan daya a saukake ba tare da asirinta ya tonu ba. Har ya zamana cewa saura kwana daya ayi gasar karshe tsakanin Yarima Kamzal, Yarima Yunus da Yarima Imran Jalila bata sami damar kawar da Yarima Imran ba. Al'amarin da yayi matukar dugunzuma hankalinta kenan ta kasa zaune ko tsaye kuma ta kasa ci da sha tun daga safe har rana tayi. Nan fa ta kama kai kawo a cikin turakarta tana ta tunani. Tana cikin wannan hali ne wata dabara ta fado mata nan take ta tura aka kirawo wata kwarkwara ta margayi sarki wacce ake kira da suna Shamila. Shamila kyakkyawar budurwa ce ta gaban kwatance wacce shekarunta basu haura ashirin da daya ba. Allah ya hore mata kyab diri na jiki wanda babu wani 'da namiji da zai ganta bai rude ba. Lokacin da Shamila taji cewar Gimbiya Jalila na kiranta sai hankalin ta ya dugunzuma ainun jikinta ya kama tsuma saboda dama gaba dayan matan dake cikin gidan sarautar suna matukar tsoron Gimbiya Jalila kamar yadda bera ke tsoron kyanwa. Hatta yantattun matan sarki tsoron Jalila suke saboda ko kyakkyawan musu ne ya shiga tsakaninsu da Jalila to za'a iya wayar gari aga mutum ya zama gawa. Kuma duk irin tsananin binciken da za'a yi ba za'a iya gano wanda yayi kisan ba. Sa'adda Shamila ta gabata gaban Gimbiya Jalila sai ta zube a gabanta ta kwashi gaisuwa sannan tace ya shugabata gani na amsa kiranki me kike bukata daga gareni? Koda jin wannan tambaya sai Jalila ta bushe da dariya lokaci guda kuma ta turbune fuska kamar wadda aka aikowa da SAKON MUTUWA tace, na kirawo kine domin na baki umarni. Idan kin bi wannan umarni zaki tsira da rayuwarki kuma zaki sami dukiya mai tsananin yawa da hatta danginki ma ba zasu taga yin talauci ba a doron kasa. Amma idan kika bijirewa umarnina lallai zaki rasa rayuwarki kuma iyayenki da duk zuri'arki ma kin shafa musu kashin kaji don sai na bisu daya bayan daya na karkashe su daga doron kasa. Gama fadin hakan ke da wuya sai Gimbiya Jalila ta yiwa Shamila rada a kunnenta ta gaya mata bukatarta. Koda jin bukatar sai jikin Shamila ya cigaba da karkarwa sosai fiye da farko amma sai ta risina tace an gama ya shugabata. Nan take farin ciki ya lullube Jalila ta sallami Shamila. Tun sa'adda su Yarima Imran suka ga an kashe gaba dayan yan uwansu mutum shida kuma an kasa gano wanda ya kashe su sai suka shiga taka tsantsan da rayuwarsu ya zamana cewa sun daina yarda da kowa hatta ruwan sha basa yarda wani hadimi ya basu su sha. Kuma suka daina zuwa ko ina daga fada sai turakarsu. Cikin gidan sarautar kuwa ko ina zagaye yake da dakaru masu tsaro don haka basu da shakkar shiga ko ina a gidan. Ana I gobe za'ayi gasa ta karshe tsakanin Yarima Kamzal, Yarima Yunus da Yarima Imran. Bayan magriba tayi a lokacin da duhu ya soma. Yarima Imran ya fito daga turakarsa ya nufi hanyar da zata kaishi inda turakar mahaifiyar sa take domin acan ne kadai yake yadda yaci abinci, idan ta fara girki bata gusawa daga wajen har sai ta kammala, tana kammalawa zata zuba abincin a kwano ta tafi dashi har cikin turakar ta ta ajiye shi a gabanta ba zata sake motsawa ko ina ba har sai Yarima Imran yazo ya ci abinci a gabanta. Koda Yarima Imran yazo giftawa ta kofar turakar kwarkwara Shamila sai ya jiyota tana rera waka a cikin sheshshekar kuka da muryarta mai dan karen zaki gami da daukar hankali. Baitocin da take biyawa a wakar bana komai bane face na begen mahaifinsa mariyi sarki. Nan take Yarima Imran ya tsaya cak a kofar turakar Shamila yana sauraron wakar da takeyi alhalin bai taba tsayawa ba a wajen tun mahaifinsa ma yana raye. A hankali sai dadin sautin muryar Shamila ya fara daukar hankalinsa kuma yaji tausayinta ya kama shi ainun saboda abubuwan da take lissafowa a cikin wakar wadanda ta rasa ne sakamakon rashin sarki. Tun Shamila nayin wakar har saida muryarta ta dakushe ta fashe da matsanancin kuka. Al'amarin da yasa Yarima Imran ya kasa hakuri ya wuce izuwa inda ya nufa kawai dai ya tura kofar turakar ta Shamila ya kunna kai ciki ba tare da shakkar komai ba. Yana shiga falon ya iske kuyangin Shamila sama da goma a zaune amma ko kallonsu baiyi ba ya wuce ta gabansu ya shige har cikin dakin barcinta. Cikin sauri shugabar kuyangin ta sha gabansa da nufin ta hana shi amma saiya mangareta ta fadi kasa. Yana shiga ya iske Shamila kwance kan gado cikin wata farar riga bacci shara shara wacce ke bayyana komai na surar jikinta kuma ga hawaye na zuba daga cikin idanunta. Nan take Yarima Imran ya dimauce ya fita daga hayyacinsa cikin karfin hali ya juya da baya da nufin ya fice daga cikin dakin amma sai yaji Shamila ta kira sunansa a cikin murya mai taushi. Kafin ma ya fuskanceta ta tastaso daga kan gadon tazo ta rungumeshi. Nan fa Yarima Imran ya sake dimaucewa baisan sa'adda zuciyarsa ta rinjaye shi ba yayi abinda bai dace ba. Yana cikin tsakiyar wannan hali ne kwatsam sai yaji Shamila ta kurma uban ihu. Kafin ya mike ya tambaye ta abinda ya sameta tuni dakaru da yawa sun rugo izuwa cikin dakin baccin. Suna shigowa sai Shamila ta fashe da kuka tana mai cewa Yarima ne ya shigo dakinta yayi mata fyade. Nan take kuwa dakaru suka kama Yarima aka fice dashi da karfin tsiya daga cikin dakin yana ihu gami da zagin Shamila bisa sharrin da tayi masa. Nan da nan labari ya bazu a Birnin gaba daya cewar Yarima Imran ya yiwa matar mahaifinsa margayi fyade.Ai kuwa sai aka kirawo taro na gaggawa majalisa ta zauna domin ayi bincike da shari'a akan wannan al'amari. Bayan Majalisa ta zauna sai aka tsayar sa Yarima Imran a tsakiyar fada akayi masa tambayoyi akan abinda ya faru. Itama Shamila aka yi mata tambayoyi. Koda Shamila tazo da hujjojinta gami da shaidu sai laifi ya tabbata akan Yarima Imran. Take aka yanke masa kora daga garin gaba daya kuma aka haramta masa matsayinsa na Dan Sarki wanda ko

Please Login or Register in order to submit comment