Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mulkin birnin Hindu amma zan iya sanar dakai muhummancin wannan karagar mulki dana zauna aanta da kuma wannan takobi dana dauko a cikin kogon dutsen.Ita dai wannan karagar mulki babu mahalukin daya isa ya iya zama a kanta face ya kasance duk duniya babu wani sadauki daya fishi karfin damtse kuma dole ne ya sami nasarar kashe zakuna guda dari ba daya da hannunsa ba tare da yayi amfani da karfin sihiri ko makami ba.Yakai Yarima kayi sani cewa tun ina yarinya karama yar shekara tara nake kashe zaki da hannuna amma sai a yau ne na kashe zaki na ciko dari ba daya.Don haka a yau ne na cika sarauniyar sadaukan duniya shi yasa na sami ikon zama akan wannan karagar mulki ta saudakantakar duniya,kuma har na iya daukar wannan takobi.Ita kuwa wannan takobin asalinta mallakin sarkin sadaukan duniya ce na farko wanda ba'a taba samun kamarsa ba sai bayan shekara dubu daya da dari shida da arba'in da hudu.Jarumin da ya sake amfani da takobin shima yau shekararsa dari da goma sha hudu da mutuwa.Bayan shi mutum biyu ne kacal suka sake samun damar mallakar wannan takobi sannan ni a yau na mallaketa.Ka sani cewa duk abinda wannan takobi ta sara saiya rabe gida biyu komai kwarinsa kuma duk takobin datayi karo da ita saita balle.Bayan haka kuma duk Jarumin daya rike wannan takobin indai ya zaro ta daga cikin kufenta,tofa ko gaba dayan MAYAKAN DUNIYA zasu yi masa rubdugu ba zasu iya hallaka shi ba.kuma saiya karar dasu.Koda za'a shekara dubu yana yaki dasu.Duk irin mugun tanadin da za'ayi masa ba za'a iya cutar dashi ba.Koda Jarumar tazo nan a jawabinta sai Yarima ya sake kamuwa da tsananin mamaki fiye da koyaushe yai shiru yana jinjina al'amarin daga can kuma saiya dubeta yace to menene batun wadannan halittu wadanda suka sauko daga sama sukayi miki sujjada?Koda jin wannan tambaya sai Jaruma tayi murmushi tace wadannan halittu daka gani aljanu ne kuma wakilai ne na gaba daya sarakunan aljanun duniya,sunzo ne gare ni domin mika mubay'arsu kuma su shaida cewa na tabbata shugabar sadaukan duniya.Nice ta biyar a cikin sarakan duniya wadda har abada baza'a taba mancewa da ita ba a cikin KUNDIN TARIHIN jarumai.Koda gama fadin hakan sai Jaruma ta wuce gaba ta nufi hanyar da zata kai su can inda bukkarta take,cikin hanzari yarima ya bita suka cigaba da tafiya har suka iso.Bayan sun huta dare ya soma sai Yarima ya dami Jaruma da yawan tambayoyi wasu ta bashi amsar su,wasu kuma sai taki idan har sun shafi sirrin matsayinta.Koda taga tambayoyin sunyi yawa sai ta daka masa tsawa tace kada ka sake yi min wata tambaya a yau sai kuma gobe,yanzu lokaci yayi da zaka tashi mu fita daga wajen bukkar nan domin na fara koya maka yaki kamar yadda na dauki alkawari.Koda jin wannan batu sai Yarima ya dubi jaruma cikin alamun tsananin damuwa yace haba ya jaruma shin yanzu ba kya ganin cewa ina cikin tsananin gajiya bisa dadewar da mukayi a daji muna farauta kuma gashi mun dade a tsaye a cikin kogon nan da kika dauko takobi.Caraf sai Jaruma ta tari Numfashinsa tace kwana biyar ne kacal suka rage mana na mayar dakai kasarku kuma lallai a cikinsu ne nake so ka kware a iya yaki kamar yadda nayi alkawari.
Don haka yau ma ina ganin sai mun kwana ina baka HORON YAKI.Tana gama fadin haka sai ta bude wata tsohuwar akwatinta wacce tun da suka zo dajin tsawon kwana tara da sukayi tare bata taba budeta ba.Take ta dauko wata takobi kirar mutanen Siriya gami da wata Garkuwa ta mikawa Yarima tace wannan takobi da garkuwa suna da matukar muhimmanci a wajena amma daga yau na baka su kyauta.Ka rike su da kyau kamar yadda zaka rike karagar ka ta mulkin Birnin Hindu.Koda gama fadin hakan sai Jaruma ta fice daga cikin bukkar tana fita sai ta zaro tsohuwar takobinta daga cikin kufenta,shi kuma Yarima Kamzal yana rike da wannan takobi da garkuwa data bashi.Ba tare da bata wani lokaci ba Jaruma ta dubi Yarima tace yake ni.Da yake Yarima ya koyi yaki a wajen mahaifinsa tun yana yaro saiya yunkura ya kaiwa Jaruma sara aka in ba don tayi sauri ta kaucewa saran ba da tuni ya cire mata kai.Al'amarin daya bata mamaki kenan ta gane cewa lallai ya dan san wani abu a yaki.Nanfa Yarima ya cigaba da kaiwa jaruma SARA DA SUKA da takobinsa amma sai ta rinka gocewa da kaucewa ba tare da ta kare harinsa ko daya ba da takobin hannunta.Har saida Yarima ya gaji likis ya fara haki.Koda ganin haka sai Jaruma ta gyadar da kai kuma tayi tsaki tace yakai wannan dan sarki ai ko ruke takobin ma baka iya ba.Nan take Yarima ya dubeta cikin mamaki yace ban iya rike takobin ba amma na kusan cire miki ka dazu,in badon kinyi sauri kin goce ba.Jaruma tayi murmushi tace ba zaka gamsu da maganata ba sai nan gaba idan ka kware da iya sarrafa takobi.Na sani cewa tun kana yaro Karami mahaifina yake koya maka yaki kuma abinda ya koya maka tamkar somin tabi ne a cikin koyan yaki.Domin ka iya kare kanka daga harin kananun dakaru.Ka nutsu ka kalle ni ka lura da yadda nake rike takobina da yadda zan rinka sarrafata tana gama fadin haka sai ta fara kaiwa iska sara da suka tana tsalle a kwance wani lokacin har alkafira takeyi a kasa tana yin katantanwa ko kuma ta tashi sama kamar tsuntsuwa tana shawagi a saman Yarima.Tun yarima yake kallon jarumai a birnin Misra sa'adda suke nuna jarumtakarsu walau a filin gasa ko kuma filin yaki bai taba ganin mai irin wannan jarumtakar ta ba.Tabbas tunani ko hasashen mutum ko kadan babu aikin sihiri a cikin al'amarin.Bayan jaruma ta shafe kusan dakika dari uku tana yakar iska a gaban yarima sai ta tsaya cak ta dubi yarima tace ma kayi irin duk abinda kaga nayi.Ba tare da wata gardama ba kuwa Yarima ya fara sara da sukan iska yana kwaikwayin irin abubuwan da jaruma tayi sai gashi yana matukar kokari amma dai bayi yadda ita tayi sosai ba.Saida shima ya dauki tsawon yan dakiku yana kaiwa iska saran.Yana cikin haka ne kawai sai yaga Jaruma ta dako tsalle ta dira a gabansa ta kawo masa sara,nan fa suka kacame da azababben yaki tamkar sun kasance abokan gaba masu neman hallaka juna.Da farko Yarima ya dauka abin kamar wasa amma da yaga Jaruma yakarsa takeyi da dukkan karfinta tana neman yi masa illa sai shima ya jajurce iya karfinsa don kara kansa.Amma cikin kankanin lokaci ta galabaitar dashi tun yana iya maida martani har ya kasa ya zamana cewa da kyar yake iya kare harinta kuma wani lokacin har faduwa yake a kasa amma saboda yana da zafin nama yana da naci sai taga yayi wuf ya mike zumbur ya cigaba da yaki.Lokacin da jaruma ta sake kuntata shi ainun sai takobin hannunsa ta subuce ta fadi a kasa kuma ta tsira shi da tata takobin a lokacin ne idanun Yarima suka raina fata ya rasa yadda zaiyi.Jaruma ta dube shi cikin murmushi tace yayin da kake cikin yaki da abokan gabarka idan takobinka ta subuce ta fadi kasa me zakayi domin ka kare kanka?Cikin alamun karayar zuciya yarima yace ai babu abinda zan iya yi tunda babu makami a hannuna.Koda jin haka sai Jaruma ta gyada kai tace ba haka ne ana da zabi,zaka iya amfani da karfin damtsenka ka kwaci kanka ko kuma kayi amfani da kwarewarka gami da dabararka ta iya yai.Yanzu zan numa maka hakan a zahiri.Nan take ta dauki takobin dake kasa tace dashi ya tsirata.Koda Yarima ya tsira ta da takobin sai tayi wuf ta shammace shi ta doki hannunsa mai rike da takobin aikuwa sai takobin tasa tayi masa lokaci guda duk su biyun suka daka tsalle sama domin su cafo takobin.Koda Jaruma taga Yarima zai rigata riko takobin sai ta doki kirjinsa da kafarta guda,saboda karfin dukan saida yayi baya da gudu tamkar an janye shi da majaujawa ya fado kasa tim yana aman jini.Ita kuwa sai ta cafe takobin tasa ta diro kasa bisa kafafunta.Koda taga Yarima yana aman jini sakamakon dukan kirjinsa da tayi sai hankalinta ya dugunzuma ta ruga gareshi ta kama kafadunsa ta rike a karo na farko kenan data taba jikinsa tun sanda ya warke daga raunikan nan.Kawai sai taga Yarima ya dubeta ya bushe da dariya.Al'amarin daya sa tayi sauri ta saki jikinsa kenan ta mike tsaye.Yarima ya dubeta yace ain tun da nake jarraba yin gumurzu da mazaje ban taba jin anyi min naushi mai karfi da mugun zafi ba kamar naki domin ji nayi kamar kirjin nawa ya fashe.Tabbas kin cika sarauniyar SADAUKAN DUNIYA.Gaskiya ba karamar juriya nayi ba da har na iya mikewa yanzu.Amma na zata zaki tausaya min.Jaruma tayi ajiyar zuciya tace a rayuwata ban san wani abu wai shi tausayi ba Amma bisa mamaki a yau sai naji tausayinka ya shige ni a dazun dana nausheka a sama ka fado kana aman jini kuma sai naji nadama tazo mini bisa abinda nayi maka.Amma dai ba tausayi ne ya janyo nadamar ta ba kawai tsoro naji kada nayi maka lahanin da ba zaka zama sarki ba har ni ma na sami damar cika babban burina na duniya.Koda jin wannan batu sai Yarima ya bushe da dariya yace ai tunda dai ina da muhummanci.............

Naga low response Shekaranjiya.
Ban San why ba.
Amma

Mu hadu a part C.

Abubakar Haleefah Physicist ยถ๐™†๐˜ผ๐™๐˜ผ๐™‚๐˜ผ๐™ ๐™ˆ๐™๐™‡๐™†๐™„ยถ
๐™‡๐™ž๐™ฉ๐™ฉ๐™–๐™›๐™ž ๐™‰๐™– ๐˜ฝ๐™ž๐™ฎ๐™ช (2) ๐™‹๐™–๐™ง๐™ฉ ๐˜พ.

โ„ข๐‘จ๐’ƒ๐’…๐’–๐’'๐’‚๐’›๐’Š๐’› ๐‘บ๐’‚๐’๐’Š ๐‘ด๐’‚๐’…๐’‚๐’Œ๐’Š๐’ ๐‘ฎ๐’Š๐’๐’Šโ„ข.

โ€ขโ€ขโ€ขKoda jin wannan batu sai Yarima ya bushe da dariya sannan yace ai tunda dai ina da muhimmanci a gareki na tabbata da cewar ba zaki nakastani ba cikin wannan horon yaki da zaki bani.Jaruma tayi dan guntun murmushi na mugunta sannan tace tabbas bazan lahanta ka ba amma zakasha bakawar wuya kuma dole ne kasha wahalar da indai kana son ka koyi yakin da zaka iya kare rayuwarka daga kowanne irin hari na ABOKAN GABA musamman hari na MAMAYAR BAZATO.Haka dai jaruma ta cigaba da koyawa Yarima horon yaki kala kala har da fadan hannu da kai naushi da bugu da hannu da kafa.A wannan rana saida Jaruma ta hadawa yarima JINI DA MAJINA kuma saida ta sumar dashi sau uku ta tara masa muguwar gajiya.Ta kumbura masa fuskarsa da sassan jikinsa idanunsa sukayi luhu luhu tamkar yayi gasar dambe.Saboda tsananin jigatar da yarima yayi kasa mikewa yayi tsaye ya taka da kafafunsa.Saida jaruma ta goya shi a bayanta sannan taje ta kwantar dashi kan shimfidarsa a cikin bukka.Cikin gaggawa ta kunna wuta ta dora tukunya don dafa ruwan dumi.Bayan ruwan dumin yayi dumi sai ta dauko kyalle mai tsafta daga cikin suturunta ta shiga tsoma shi a cikin ruwan dumi tana gasa sassan jikin Yarima inda ya kumbura.Bayan hakan ne ta dura masa wani ruwan magani a bakinsa yasha.Adaidai wannan lokaci ne alfijir ya keto kuma a sannan ne bacci ya dauke yarima.Jaruma ta kurawa Yarima idanu.Koda taga yadda ta kumbura masa kyakkyawar fuskarsa sai nan take tausayinsa ya turnuketa har hawaye ya zubo mata.Tana cikin kallonsa ta langwabe akan kirjinsa ta kama shara bacci bata sani ba.Saida gari ya waye har rana ta take sannan Yarima ya farka daga bacci yana bude idanunsa sai yaga Jarima a kwance akan kirjinsa tana bacci.Al'amarin dayai matukar bashi mamaki kenan.Nan take ya aiyana cikin zuciyarsa cewa yau fa ga dama ta samu wacce zai iya cire rawanin da jaruma ta rufe fuskarta dashi domin yaga irin kyawunta da kamanninta.A tsawon kwanakin da sukayi tare bai taba ganin jaruma ta cire wannan rawanin daga fuskarta ba ko sau daya kuma ko wana zatayi saidai ta debi kayan da zata sauya ta nausa wani wuri a cikin dajin.Saidai yaga ta dawo a cikin sauyin tufafinta.Har Yaroma yakai hannunsa ya kama wannan rawanin dake fuskar jaruma sai kawai yaji ta motsa cikin sauri ya janye hannunsa.Aikuwa sai ta bude idanunta.Koda taga kanta a bisa kirjin yarima kuma ta fahimci cewa akan kirjin nasa tayi bacci sai ta mike zumbur cikin alamun kunya.Cikin hanzari ta mike tsaye ta shirya musu abin kalaci.Bisa mamaki sai Yarima yaga ya iya mikewa zaune alhalin a zatonsa ko motsin kirki ba zai iya ba sakamakon bakar wahakar da yasha a jiya da daddare da kuma mugun duka da yasha a wajen Jaruma.Bayan sun gama kalaci ne sai kawai yaga Jaruma ta dauko takobinsa da garkuwarsa ta mika masa sannan ita ma ta dauki tata takobin.Abinda ya daure masa kai shine wannan farar takobin wacce ta dauko a cikin wannan kogon dutsen da ita ta kwana a goye a bayanta kuma da ita ta tashi ko sau daya bata cire ta daga jikinta ba.Yarima yana son ya tambayeta dalilin yin haka amma saiya hakura kawai sai ji yayi jaruma tace mu fita waje mu cigaba da yaki.Cikin kaduwa da matukar tsoro Yarima ya dubi jaruma kamar zai fashe da kuka yace haba jaruma indai ba so kike ki kashe ni ba ai ya kamata a hakura da koya mini yakin nan haka.Koda jin haka sai Jaruma ta bushe da dariya tace ai in da so nake na kashe ka da tun a jiya zan kashe ka ba zaka kawo yau ba.Kada ka manta cewa ba'a zama a banza,sai nan gaba zaka gane cewa ba karamin gata nayi maka ba.Tashi mu tafi ko kuma na fitar dakai da duka.Koda jin haka sai Yarima ya mike da sauri ya fice itama ta bishi da gudu ta afka masa suka ruguntsume da azababben yaki.Aikuwa suna fara wannan gumurzu ne Yarima ya gane cewa lallai ya sami horon yaki ninkin wanda yake dashi a da.Domin a wannan rana ta biyu sai gashi yana iya kare hare haren jaruma har ma yana iya maida martani duk a lokaci guda.Kuma saida suka shafe kusan rabin sa'a suna gumurzu ba tare da ta sami nasarar taba jikinsa ba.A sannan ne ta sami nasarar dukan bayansa da kafarta ta hagu.Cikin shammace ya tafi taga taga zai kife da ruf da ciki amma saiyayi gwaninta ya dafa kasa da hannunsa mai rike da garkuwa ya taso sama kamar sifirin suka cigaba da gumurzu kamar ba zasu daina ba.Babu yadda yarima baiyi ba akan ya rama dukan da jaruma tayi masa koda sau daya ne amma saiya kasa.A wannan rana na dai itace ta sami galaba akansa takaishi kas har sau uku tana tsira shi da takobi kuma tana kade takobin hannunsa tana faduwa kasa saida suka yini suna wannan gumurzu tun daga safe har izuwa faduwar rana sannan suka koma cikin bukarsu suka kwanta domin huce gajiya.Haka dai Jaruma ta cigaba da baiwa Yarima horon yaki har izuwa tsawon kwanaki uku ya zamana cewa sun sami sati biyu a cikin dajin kuma tsawon kwanaki uku kullum yarima kara samin horon yaki yakeyi gami da kwarewa ainun.A ranar karshe ma saida ya sami nasarar naushin jaruma sau daya a kirjinta tayi taga taga da baya kamar zata fadi amma sai ta tsaya kyam kawai sai ta bushe da dariyar farin ciki kuma ta kama yi masa tafi saboda ya burgeta daya sami wannan nasarar.Aikuwa a wannan rana sukayi shirin tafiya birnin Hindu.Bayan sun kimtsa sai Jaruma ta shafi wannan takobin tata wacce take yaki da ita koyaushe take takobin ta rikide ta zama wannan katon tsuntsun tsafin nan nata.Kawai sau suka hau kan tsuntsun ita da yarima ya tashi sama yana mai kada fukafukansa ya luluka dasu cikin gajimare ya nufi birnin Hindu.Wannan shine asalin yadda yarima Kamzal ya hadu da bakuwar jaruma har ta dawo dashi izuwa birnin hindu ya shiga gasar samun karagar mulki.

LOKACIN da Yarima Kamzal tare da Jaruma suka shiga cikin daji don yin farauta sai kawai suka rinka jin motsin takun sawaye daga gabas da yamma,kudu da arewa ana tunkararsu.Koda jin wannan motsi sai Jaruma sai jaruma ta riko hannun Yarima ta tsaida shi suka tsaya ca a inda suke kuma ta jingina bayanta da nasa.Lokaci guda shida itan suka zare takubbansu suna kallon gabas da yamma,kudu da arewa domin taga ta inda za'a kawo musu hari.Kwatsam sai ga dakarun kisan kai a cikin shigar bakaken tufafi sun rugo da gudu bisa kan tsaunikan da suka yiwa dajin KAWANYA.Fiye da kaso daya cikin ukunsu na rike da KWARI DA BAKA.Take suka ritsa Yarima da Jaruma kawai jira suke a basu umarnin yin harbi.Koda Yarima yaga wadannan dakarun Sumame kuma gashi sun ritsa su da kibiyoyi a sama bisa tsaunika sai hankalinsa ya DUGUNZUMA shida Jaruma.Adaidai wannan lokaci ne shugaban dakarun ya matso kan gaba ya dubi jaruma yace yake wannan bakuwar jaruma kiyi sani cewa umarnin da aka bamu na kashe wanda kike tare dashi ne kawai zamu cika.Don haka idan kina son ki tsira da rayuwarki ki sulale ki bar shi damu.Kafin shugaba dakarun ya gama rufe bakinsa tuni jaruma ta tari numfashinsa tana mai daka masa tsawa tace kai karamin kwaro karyarku tasha karya,kayi sani cewa idan har kaga na bari kun hallaka yarima to tabbas bana tsaye a doron kasa.Don jaka idan kuna ganin zaku iya hallaka mu to ku jarraba ku gani.Koda jin haka sai shugaban dakarun ya fusata nan take ya bayar da umarnin a sakarwa su Yarima harbi.Koda dakarun sukaji wannan umarni sai suka saki kibiyoyin a lokaci guda saida ya rage saura kiris kibiyoyin su taba jikin Yarima da Jaruma sai suka tsaya cak a sama cikin iska sannan suka juya da baya sukaje suka soke wadanda suka harbo su duk suka zube kasa matattu.Koda ganin haka sai gaba daya dakarun sumamen suka gangaro kasa daga kan tsaunikan suna zare takubbansu suna kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa.Ai kuwa sai suka afkawa Yarima da Jaruma aka ruguntsume da azababben yaki.Duk da tsananin Jarumtaka irin ta jaruma da kuma sabon horon yakin da yarima ya samu saida wadannan dakaru suka zame musu alakakai saboda suna da tsananin iya yaki gami da tsantsan juriya da kuma mugun naci sannan ga karfin sihirin tsafi.Gashi dai jaruma da yarima suna tarwatsa su da karfin tsiya kuma suna samin nasarar saransu da sukarsu amma da zarar sun sare su wajen ya dare jini yai tsartuwa ko feshi sai kaga raunikan sun koma sun manne tamkar ma ba'a taba saran su ba.Kuma koda sun zube kasa matattu sai su mike tsaye rayayyu su cigaba da yaki.A hakan ne harma dakarun Sumamen suka sami nasarar yankar yarima a damtsen hannunsa na hagu take ya tsandara ihu sakamakon tsananin zafin zugin dayaji a lokacin da jini ya fara zubwa a hannunsa ya durkushe a kasa.Koda ganin abinda ya faru ga Yarima sai jaruma ta fusata ainun ta soke takobinta a cikin kasa sannan ta zaro wannan sharbebiyar farar takobin dake rataye a bayanta ta afkawa dakarun ta hau su da dara da suka.Duk badakaren data sara take yake rabewa gida biyu kuma ya baje a kasa matacce baya kara sake tashi.Cikin dakiku kadan ta kashe sama da kaso biyu na dakarun sumamen.Koda dakarun dukaga irin mummunar barnar da jaruma tayi musu sai suka firgita ainun suka yar da makamansu suka ruga da gudu izuwa daji.Shugabansu ne kadai ya tsaya aka fara KALLON KALLO tsakaninsa da jaruma a lokacin daya dafe kufen takobinsa yana shirin zaro ta.
WANE IRIN BAKIN GUMURZU ZA'AYI TSAKANIN JARUMA DA WANNAN SHUGABAN DAKARUN SUMAMEN?
TA YAYA YARIMA KAMZAL ZAI LASHE GASAR KARAGAR MULKI HAR YA ZAMA SARKI?
YAUSHE NE ASIRIN GIMBIYA JALILA ZAI TONU BISA KISAN MUMMUKEN DA TAKE YIWA 'YA'YAN SARKI?
MENE NE BABBAN BURIN JARUMA,KUMA WACECE ITA,MENE NE ASALINTA?
Mu hadu a karagar Mulki littafi na uku don jin cigaba wannan kasaitaccen labari.
Daga mai debe muku kewa Abdul'aziz Sani Madakin Gini.

Abubakar Haleefah Physicist
ยถ๐™†๐˜ผ๐™๐˜ผ๐™‚๐˜ผ๐™ ๐™ˆ๐™๐™‡๐™†๐™„ยถ

๐™‡๐™ž๐™ฉ๐™ฉ๐™–๐™›๐™ž ๐™‰๐™– ๐™๐™ ๐™ช (3) ๐™‹๐™–๐™ง๐™ฉ ๐˜ผ

โ„ข๐‘จ๐’ƒ๐’…๐’–๐’'๐’‚๐’›๐’Š๐’› ๐‘บ๐’‚๐’๐’Š ๐‘ด๐’‚๐’…๐’‚๐’Œ๐’Š๐’ ๐‘ฎ๐’Š๐’๐’Šโ„ข.

โ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขLokacin da aka fara kallon kallo tsakanin Jaruma da shugaban dakarun kisa sai Yarima Kamzal ya zama dan kallo kawai don haka saiya zuba idanu domin yaga yadda zata wakana.A wannan lokaci hannun dama na shugaban dakarun na bisa kan kufen takobinsa shima bai zaro ba.Amma idanunsa car a kan jaruma,ita ma haka kuma sai suka kama zagaye juna,kai da gani kasan cewa KAR TA SAN KAR ce.Kuma kowannensu nazarin abokin gwaminsa yakeyi,ko zai gano lagonsa.Takobin jaruma sai digar jini takeyi.Sai dai wannan shugaba na dakarun kisa ya kasance narkeken kato mai kirar mutanen farko domin kuwa dogo ne zabgege ga kaurin jiki gami da murdewa ga tari gwanji,kallo daya zakayi masa kasan cewa sadaukin gaske ne,duk da cewa Jaruma zabgegiyar mace ce doguwa amma sai ta zamo yar karama a gaban shugaban dakarun.Take ta zare sharbebiyar takobinsa ya kaiwa Jarima mummunan sara a wuya da nufi ta fille mata kai,amma sai ta goge cikin bakin ZAFIN NAMA tana mai sunkuyawa gami da kare saran da wannan sihirtacciyar takobi.Takubban na haduwa sai wata gagarumar muguwar kara ta cika dodon kunne,tarwatsin wuta ya tashi.Maimakon takobin shugaban dakarun ta balle ko ta lalace sai tayi wani irin haske na ban mamaki.Al'amarin dayai matukar girgiza Jaruma kenan ya bata tsananin mamaki.Ba shiri Jaruma taja da baya taku biyar ta dada kurawa shugaban dakarun idanu.Ba komai ne ya bata mamaki ba face a saninta babu wani abu da zai hadu da wannan takobi tata ba tare da ya lalace ba.Ya akayi takobin wannan katon bata yi komai ba?Wai shin ma wane irin sihiri gare shi kuma waye ya daure masa gindi a cikin BOKAYEN DUNIYA?Nanfa zuciyar jaruma ta kama tafarfasa kamar zata kone cikin tsananin fushi ta ruga da gudu izuwa kan shugaban dakarun suka sake ruguntsumewa da azababben yaki ya zama cewa suna kaiwa junansu sara da suka cikin tsananin zafin nama,juriya da bajinta taban mamaki.Duk sa'adda dayansu ya kaiwa dayan hari ya goce toh fah duk abinda takubban nasu ya sara koya soka take wannan abu yake ragargajewa komai kwarinsa.Take jaruma ta gane cewa lallai takobin wannan shugaban dakarun tana da irin sihirin da tata takobin take dashi.Saida jaruma da shugaban dakarun suka shafe rabin sa'a cif suna bakin gumurzu ba tare da dayansu ya sami nasarar koda lakutar jikin daya ba.Koda ganin haka sai jaruma ta sake fusata ainun ta tuna cewa a halin yanzu fa itace sarauniyar sadaukan duniya don haka dole ne ta nunawa wannan barden matsayinta.Tana gama aiyana hakan a cikin zuciyarta sai ta shammaci katon ta daka tsalle sama ta doki hannunsa wanda ke rike da takobin tasa tayi sama taje ta cake a jikin wani dutse ta fasa dutsen ta dan nutse a cikinsa.Koda ganin haka sai itama jaruma ta cilla tata takobin izuwa inda tasa takobin take,ai kuwa sai ita ma tata takobin taje ta nutse a cikin dutsen daf da tasa.Kawai sai jaruma ta dubi shugaban dakarun cikin murmushi tace yanzu ne zamu fidda raini muyi fada da iyakar tsagwaron karfin damtsenmu ni da kai.Idan na sami nasara akanka zan mallaki takobinka da tawa.Idan kuma kai ne ka sami nasara a kaina kaga kenan zaka mallaki takobina da taka saboda na fahimci cewar takubban namu duk suna da dangantaka da sihiri iri daya.Lallai inason na gano ta yadda akayi hakan ta faru.Koda jaruma tazo nan a zancenta sai Yarima Kamzal dake tsaye a gefe daya yana kallonsu hankalinsa ya DUGUNZUMA ainun saboda yana ganin cewa wannan hukunci data yanke ba karamin ganganci bane tunda babu yadda za'ayi ta sami nasarar fadawa kan wannan basamuden kato mai kirar saudakai wanda ya ninka ta sau uku a girma,kwarjini da kirar karfi.Lokacin da shugaban dakarun yaji jawabin jaruma saiya takarkare ya bushe da mahaukaciyar dariya mai tsananin firgitarwa wacce ka iya sa mai ciki tayi bari.Lokaci guda kuma ya turbune fuska ya dubi Jaruma yace ke karamar kwaruwa tabbas kin tafka babban ganganci har da kike tunanin cewa zaki iya gwada sadaukantakar ki akan tawa saboda baki san koni waye ba.Ki bar ganin cewa an baki sarautar sadaukan duniya a can kogon Darul Kinzaz ba,sannan kiyi zaton cewa babu wanda zai iya da ke,to ki sani xewa komai sammakon ki wani a rafe ya kwana.Ni tun kafin a haife ki na shiga cikin kogon Darul Kinzaz domin ban samu abinda kika samo ba amma kuma na tsallake duk hadarin dake

Please Login or Register in order to submit comment