Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

biyu da rabi suka shude Yarima Yunus da Yarima Kamzal basu shigo cikin fadar ba har ya rage saura rabin sa'a kacal wa'adin da alkalan gasa suka dibar musu ya cika.Ashe ba wani abu bane ya janyo makarar zuwan su ba face duk su biyun basu sami isasshen bacci ba a jiya da daddare sakamakon kasancewa kowannensu burinsa shine ya hau kan wannan karagar mulki.Shidai Yarima Yunus har gari ya waye bai sani ba har saida rana ta kwale sannan hasken rana ya doki fuskarsa ta cikin tagar dakin baciinsa.Yana bude idanu ya mike zaune zumbur a firgice ai kuwa sai ya kwalawa kuyanginsa kira sai gasu su uku sun rugo da gudu izuwa gabansa.Yunus ya rufe su da fada kamar zai doke su saboda sun barshi ya makara.Nan dai ya shiga bandaki da sauri yayi wanka sannan ya fito yasa tufafinsa ko kalaci bai tsaya yayi ba ya wuce izuwa fada.

Al'amarin Yarima Kamzal kuwa shi bai makara ba domin asubar farko ya farka daga bacci.Cikin hanzari ya shiga kewaye yayi wanka sannan ya fito ya tsala ado.Yana gam kimtsawa ya fito falo da nufin ya tashi Jaruma daga bacci domin su tafi izuwa dakin mahaifiyarsa yayi kalaci.Yana fitowa sai idanunsa sukayi arba da rabin fuskar Jaruma wajen matsin kwanciya ne mayafin dake kan fusktar ya dan kwaye.Koda Yarima Kamzal yaga kyakkyawar fuskar tata sai ya dimauce jikinsa ya kama tsuma bai san sa'adda ya durkuseh kasa ba bisa guiwoyinsa kuma ya kura mata idanu saida ya shafe sa'a hudu cif yana kallonta yana durkushen ko kyakkyawan motsi baiyi ba saida yayi kamar zai kwaye rabin fuskar ya gani sai ya kasa.Yana cikin wannan hali ne yaji anzo ana buga musu kofar dakin.Karar bugun kofar ne yasa Jaruma ta farka a razane ta mike zaune zumbur.Koda taga Yarima a zaune daf da ita sai ta murtuke fuskarta kuma tayi sauri ta gyara mayafin nata ta rufe fuskar sosai.Ta dubeshi cikin kallon mai nuna alamun zargi tace mene ne ya kawo ka daf dani har da zaka kura mini ido.Shin kai ne ka yaye mini mayafin fuskata?Cikin alamun tsoro Yarima yace na rantse da gemun mahaifina hannuna bai taba komai ba,haka na fito na same ki.Yake Jaruma kiyi sani cewa mun makara kuma na san cewa kuyangar mahaifiyata ce tazo take buga mana kofa saboda ganin cewa mun makara.Koda jin haka sai Jaruma ta mike tsaye da sauri ta nufi bakin kofar bata bude kofar ba saida takobinta don tabbatar da tsaro kuma a hankali ta bude kofar tana dan lekawa kadan.sai taga kuyangar ce sannan ta bude kofar sosai ta dubeta tace ki koma ki gayawa Ummu Kamzal cewa mun makara amma dai gamu nan zuwa.Nan take kuyanga ta juya da baya,ita kuma Jaruma ta maida kofar ta rufe.Sannan ta ruga izuwa kewaye ta tsala wanka.Bata shiga kewayen ba saida ta dauki tufafin da zata sauya.A shirye tsaf ta fito daga wanka sannan tasa Yarima a gaba suka fice daga turakarsa suka nufi turakar mahaifiyarsa.Shiga sukayi suka iske mahaifiyar Kamzal zaune a gaban wani dogon teburi a falon wanda aka cika shi da abincin kalaci.Koda mahaifiyar tasa ta gansu sai ta mike tsaye da sauri cikin murna da durfafo Kamzal da nufin ta rungume shi amma sai Jaruma tayi wuf ta shigo tsakiyarsu ta dube ta tace ki gafarce ni yake Ummul Kamzal,kiyi sani cewa bazan iya barinki ba ki rungumi wannan 'da naki saboda tsaro.Kada kiga laifina ina kan aikina ne.Nasan cewa ke bazaki cutar dashi ba.Amma makiya zasu iya amfani da jikinki wajen kokarin cutar dashi.Idan ba zaki damu ba zan so na dan duba rigar jikinki yanzu.Duk da cewar ran mahaifiyar Kamzal ya sosu amma saita dubi Jaruma cikin murmushi tace ai kome kika bukata zanyi don tabbatar da lafiyar 'da na da rayuwarsa,maza ki aiwatar da duk abinda kike son yi.Koda jin haka sai Jaruma ta zura hannunta a cikin aljihun rugarta ta dauko wata siririyar sandar tsafi ta taba rigar mahaifiyar Kamzal sai ta juya kala zuwa ja kuma sai rigar ta dauki mugun zafi har hayyaki da tiriri na tashi a jikinta.Babu shiri Ummul Kamzal tayi wuf ta cire rigar ta yarda ita kas,a take rigar ta kama ci da wuta ta kone kurmus sai toka.Al'amarin daya yasa Kamzal da mahaifiyarsa kenan suka ja da baya a tsora.Jaruma ta dubi konanniyar rigar sannan ta dubi Ummu Kamzal tace inda kin rungumeshi a yanzu da tuni ke dashi kun 'kone kurmus kamar yadda wannan riga ta kone ko kasusuwan jikinku baza'a samu ba da tuni kun zama toka.Wannan wani mugun sihirin tsafi ne da musamman kuma ba wani ne ya sashi a jikin ba face kuyangarki wacce kika tura ta dazu ta kirawo Yarima,kuma itama Gimbiya Jalila ce ta bata sihiri ta umarceta data sa a jikin rigarki in kuma taki abakacin ranta.Koda jin wannan batu sai jikin Ummul Kamzal ya kama tsuma ta dubi Kamzal a lokacin da hawaye ya zubo mata tace yakai dana tabbas ni da kai duk rayuwarmu na cikin mugun hali koyaushe zamu iya hallaka.Kafin Kamzal ya budi baki yace wani abu sai Jaruma ta tari numfashinsa tace zaki iya tsira da rayuwarki da lafiyarki idan zaki iya amfani da shawarwarin dana baki.To da farko dole ki sallami duk kuyanginki da hadimanki.Ki yarda a samo miki sababbi wadanda suka kasance amintattu kuma baki ba yan gari ba domin ko a bayan nadin sarauta ne makiya ba zasu daina kokarin hallaka ku ba.Koda jin haka sai Ummul Kamzal ta gyada kai tace ai dole ne ma yanzu nayi amfani da duk shawarwarin da kika bani tunda farko tunda gashi yanzu naga zahiri da idanu na,yanzu dai tunda kun makara sai ku zauna ku hanzarta yin kalaci.Nan take Yarima ya zauna ita kuwa Jaruma saida ta debi abincin ta bawa mage taci taga babu abinda ya same ta sannan ta bar Yarima da Mahaifiyarsa suka fara cin abincin sannan itama ta ci.Saida suka kammala cin abincinsu cikin nutsuwa sannan suka dunguma su ukun suka nufi fada dakarun dake tsaron lafiyar Ummu Kamzal su hamsin suka take musu baya.Wadannan dakaru amintattu ne domin tun margayi Sarki na raye ya bawa Ummu Kamzal su.Kuma ba'a taba kama dayansu da wani laifi na cin amana ba.Lokacin dasu Yarima Kamzal suka nufi fada suna tafiya a cikin harabar gidan sarautar sai sukayi kicibus da tawagar Yarima Yunus shida dakarunsa na musamman masu tsaron lafiyarsa su dari biyu suna take masa baya.Koda aka hadu sai ka tsaya cak ana kallon kallo.Yarima Yunus ya dakawa Yarima Kamzal harara cikin kallo mai nuna tsantsar kiyayya a lokacin da yaga Kamzal ya durfafo shi fuskarsa cike da annuri.Tun kafin ya karaso daf dashi ya tsaida shi da hannu yana mai daka masa tsawa yace kai Kamzal me zaka zo wajena kayi?Ko kuwa wani makircin ka kulla domin cutar dani?Koda jin wannanbatu sai Yarima Kamzal ya tsaya cak a inda yake ya dubi Yunus cikin alamun takaici da damuwa yace yakai dan'uwana................

Ni barar adduarku akan wasu bukatu na.

Ayyuka ne sukayi min yawa shi yasa bana posting everyday. Sannan bana jin dadi ne. ยถ๐™†๐˜ผ๐™๐˜ผ๐™‚๐˜ผ๐™ ๐™ˆ๐™๐™‡๐™†๐™„ยถ
๐™‡๐™ž๐™ฉ๐™ฉ๐™–๐™›๐™ž ๐™‰๐™– ๐™๐™ ๐™ช (3) ๐™‹๐™–๐™ง๐™ฉ C.

โ„ข๐‘จ๐’ƒ๐’…๐’–๐’'๐’‚๐’›๐’Š๐’› ๐‘บ๐’‚๐’๐’Š ๐‘ด๐’‚๐’…๐’‚๐’Œ๐’Š๐’ ๐‘ฎ๐’Š๐’๐’Šโ„ข.

๐˜ผ๐™—๐™ช๐™—๐™–๐™ ๐™–๐™งโค๏ธ๐™ƒ๐™–๐™ก๐™š๐™š๐™›๐™–๐™โค๏ธ๐™‹๐™๐™ฎ๐™จ๐™ž๐™˜๐™ž๐™จ๐™ฉ.

โ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขKoda jin wannan batu sai Yarima Kamzal ya tsaya cak a inda yake ya dubi Yunus cikin alamun takaici da damuwa yace yakai dan'uwana sa'adda idanunsa suka ciko da kwalla yace kayi sani cewa ya kamata mu ajje duk wani batu GABA DA KIYAYYA a tsakaninmu. Ka tuna cewa saura ni da kai a cikin gidan wannan sarauta, Yarima Imran kuma an kore shi. Inaso mu hada kanmu mu mulki kasar nan tare. Idan kaine ka zama Sarki inason na zama wazirinka. Idan kuma nine na zama Sarki kaine Waziri na.Muyi Kokari mu gano makiyanmu mu kawar dasu dan tsare martabar gidan nan da kuma zuri'armu saboda kada a shafe mu daga KUNDIN TARIHI. Kafin Yarima Kamzal ya gama rufe bakinsa tuni Yarima Yunus ya tari numfashinsa yana mai daka masa tsawa a karo na biyu yace kai shashasha mara tunani da hankali ta yaya kake tsammanin zan yarda dakai Alhalin kasan cewa har dani aka hada kai aka sassara ka aka saka a cikin buhu aka jefa a teku. Har abada kiyayyata a cikin zuciya ka ba zata taba gushewa ba. Nasan cewa kullum a cikin tanadin DAUKAR FANSA kake. Kayi sani cewa gaba daya yan'uwanmu mutum shida da suka mutu kai muke zargi ka kashe su. Hatta Yarima Imran da aka kora daga cikin gidan nan yana tanadin hanyar da zaiga bayanka. Saboda ya san cewa shima bazaka daina FARAUTAR RAYUWArsa ba. Ina mai tabbatar maka da cewa yau idan na zama sarki saina san hanyar dana bi na hallaka ku kaida mahaifiyarka domin kune kadai nake kallo a matsayin bakin kumurci dake shirin sara na a koyaushe. Tsakanina dakai babu sulhu ko zumunci har abada sai YAKI. Koda gama fadin hakan sai Yarima Yunus ya wuce gaba dakarunsa gaba daya suka bishi aka bar Yarima Kamzal tsaye yana mai binsa da kallo cikin tsananin damuwa da bakin ciki. Nan take Jaruma ta dafa kafadar Yarima Kamzal tace saidai kayi hakuri da duk yan'uwanka domin har abada ba zasu iya rungumarka ba a matsayin dan'uwa, shige mu karasa fadar. Ba tare da gardamar komai ba kuwa Yarima yabi Jaruma a baya, mahaifiyarsa da dakarunta suka rufa musu baya. Yarima Yunus tare da dakarunsa na shigowa cikin fadar sai aka kaure da shewa masoyansa da maroka suka kama yi masa kirari da tafi har saida Yarima Yunus yaje ya zauna a in da aka tanadar masa kusa da alkalan gasa sannan fadar tayi tsit. Faruwar hakan keda wuya sai fadar ta sake rudewa ainun a karo na biyu fiye da karo na farko. Mafi yawan jama'ar dake cikin fadar suka mimmike tsaye suka kama ihu, kirari da kururuwa. Koda alkalan gasa da yan majalisa suka dubi bakin kofar sai sukaga ashe Yarima Kamzal ne ya shigo. Jaruma, mahaifiyarsa da dakarunta na take masa baya. A wannan lokaci Yarima Kamzal yayi kyau saboda ya caba ado na kwatance, abinka da kyakkyawa sai kyawun nasa ya karu ainun. Nan take yan mata da zaurawa na garin suka kama rudewa da dimaucewa burin kowacce daga cikinsu kawai ta hada idanu da Yarima Kamzal ko ya zabe su a matsayin matansa domin gani suke kamar ma ya zama sarki. Bayan Yarima Kamzal ya isa inda alkalan gasa da yan majalisa ke zaune sai ya durkusa har kasa bisa guiwoyinsa ya gaishe dasu cikin ladabi sabanin Yarima Yunus wanda ko kallon kirki baiyi musu ba bare batun gaisuwa. Wannan abu da yayi ne yasa talakawa suka kara kaurewa da shewa suna masa kirari gami da fatan samun nasara.Al'amarin daya fusata Yarima Yunus, yan majalisa da masoyansa kenan. Ba tare da bata lokaci ba Yarima Yunus yaje ya zauna a kujerar da take fuskantar ta Yarima Kamzal. A sannan ne fadar tayi tsit alkalin gasa mai gabatar da tambayoyi sai yazo gaban su Yarima Yunus ya zauna sannan yayi gyaran murya, nan take ya fara gabatar da tambayar farko ga Yarima Yunus. Ba tare da wata gardama ba ya amsa tambayar daidai sannan ya juya kan Yarima Kamzal tayi masa tasa tambayar shima ya amsa daidai, nanfa fadar ta rude da shewa gami da tafi. Saida aka yiwa Yarima Yunus da Yarima Kamzal dukkanin tambayoyin da aka tanada har cikon tambaya ta tamanin da takwas suna amsawa daidai. Ya zamana cewa saura tambaya dai dai a kansu. Nanfa hankalin jama'a ya kama tsuma saboda fargaba da tsoron yadda karshen wannan gasa zai kasan. Su kansu su Yarima Kamzal sai gumi ne ke tsattsafowa akan fuskokinsu. Saboda sun san cewa wannan itace dama ta karshe da suke da ita tunda duk Wanda bai amsa ta daidai ba duk amsoshin daya bayar a baya sun zama na banza. Shi kansa alkalin gasar saida yayi dan shiru tsawon yan dakiku a lokacin da fadar tayi tsit fiye da koyaushe sannan ya dubi Yarima Kamzal yace yakai Yarima yanzu zan yi maka tambaya ta karshe wacce Idan ka amsata daidai ka haye idan kuma baka amsa taba daidai ka fadi wannan gasa Yarima Kamzal ya gyada kai yana mai ajiyar zuciya yace nasan da duk sharadin wannan gasa Don haka Ina sauraronka. Alkalin gasa yace tambayar itace.

"Akwai wani abu guda daya a cikin duniya wanda duk wanda ya ganshi sai yaji tsoro haka kuma idan ya rasa shi sai ya shiga garari, mene ne wannan abu? Koda jin wannan tambaya sai Yarima Kamzal yayi shiru tamkar ba zai iya cewa komai ba. Gaba daya mutanen dake cikin fadar ma sai tambayar ta rikita su kowa ya shiga tunanin amsarta. Kwatsam sai akaji Yarima Kamzal yayi gyaran murya sannan yace a cikin wannan duniya gaba daya babu wani abu wanda duk wanda ya ganshi sai yaji tsoro kuma duk wanda ya rasa shi sai ya shiga garari face JINI.Koda jin wannan amsa sai alkalan gasa suka dubi takardun dake hannuwansu Don ganin ko daidai ya amsa tambayar. Cikin hadin baki gaba dayan alkalan gasar suka bude baki suka ce gaskiya ne ka amsa daidai. Nan fa fada ta rude da shewa jama'a, makada suka cikawa mutane kunne, maroka suka kama yin kirari. A wannan lokaci fuskokinsu Yarima Yunus kuwa a turbune suke kuma zukatunsu a cike suke da bakin ciki domin so sukayi Yarima Kamzal ya kasa amsa wannan tambaya daidai koda shi kansa Yarima Yunus bai amsa tasa daidai ba shike nan suyi kunnen doki saidai akara musu wasu tambayoyin. Saida alkalin gasa mai gabatar da tambayoyi ya daga hannunsa sama sannan akayi tsit tamkar mutuwa ta gifta.Alkalin gasa ya dubi Yarima Yunus yace ya shugabana na dawo gare ka fatan..... Caraf sai Yarima Yunus ya tari numfashin alkalin gasar yace nasan komai ba sai kayi min bayani ba kawai ka gabatar mini da tambaya ta karshe. Alkalin gasa yayi gyaran murya yace shugabana tambayar itace akwai wani abu guda daya wanda farkonsa yana wanzuwa a guri mai zafi kuma bashi da rai amma idan rai ya shige shi da sanyi da zafi zasu iya hallaka shi. Koda jin wannan tambaya sai Yarima Yunus yayi shiru ya fada cikin kogin tunani,nanfa hankalin masoyansa ya DUGUNZUMA suka rasa abinda yake musu dadi saboda sunga alamar cewa Yarima Yunus baisan amsar wannan tambaya ba. A daidai wannan lokaci ne Jaruma ta dubi Yarima Kamzal tayi masa murmushi sannan tayi masa rada a kunne tace amsa wannan tambaya tafi shan ruwa sauki shin kasanta? Yarima Kamzal ya gyada kai cikin alamun karayar zuciya yana mai nuni da cewar bai sani ba. Jaruma tayi dariya tace gashi dai ka amsa tambayoyi da yawa wadanda suka fi wannan wahala sosai amma ka kasa gano mai sauki.
Nan fa Yarima Yunus ya kama muzurai yana kallon rufin saman fadar. Al'amarin daya sake karya guiwar masoyansa kenan. Mahaifiyarsa kuwa take ta fara kuka dama ta riga kowa zuwa fadar saboda doki da kuma murnar zuwan wannan rana amma sai gashi TA LEKO TA KOMA. Dama ka'idar wannan gasa da zarar an yiwa mutum tambaya za'a fara buga wata ganga idan aka buga gangar sau ashirin mutum bai budi baki ba yai magana shike nan ya fadi tambayar. Saida aka buga gangar sau goma sha takwas Yarima Yunus ya kasa motsa bakinsa ana buga na sha tara ne ya budi baki yace Shaho ne amsar.Nan take alkalan gasa suka dubi takardun dake gabansu sannan gaba dayansu suka dubi Yarima Yunus a cikin hadin baki suka ce amsar ba daidai bace. Koda jin haka sai Yarima Yunus ya takarkare ya kwarara uban ihu kuma ya fashe da matsanancin kuka na bakin ciki. Mahaifiyarsa kuwa yanke jiki tayi ta fadi a kasa sumammiya sai kuyanginta ne suka rugo da gudu suka dauketa suka ruga da ita izuwa turakarta sannan aka ruga neman likita. Su kuwa su Yarima Kamzal da dukkanin masoyansa sai suka rude da ihu gami da shewa, kade kade da raye raye. A wannan rana talakawan garin kwana sukayi suna kade kade da raye raye kowane lungu da sako na garin birni da kauye saboda sun san cewa sun sami adalin sarki wanda zai jibanci lamarinsu. Yarima Yunus dai kasa tashi yayi daga inda yake ya zube kasa yana kuka sai dauke shi akayi aka kaishi turakarsa inda ya cigaba da kuka yana farfasa duk kayan kawar dake cikin dakin, kai saida aka kamashi da karfin tsiya aka danne shi likitansa ya dura masa maganin bacci don kada ya yiwa kansa lahani.Ita kuwa mahaifiyarsa daga wannan suma da tayi sa'adda ta farfado da cutar mutuwar rabin jiki ta tashi.

Kashe gari kuwa da safe aka shiga shagalin bikin nadin sarauta na Sarki Kamzal a wannan rana an zuba dakarun tsaro a ko ina a cikin birnin da kewaye. Sarakuna kuwa na duk kasashen dake makwabtaka saida suka halarci wannan biki. Tun safe aka shiga shagali iri iri har yamma tayi amma duk abinda akayi ba'a ga Yarima Yunus ba da dukkanin masoyansa ba. Amma gaba dayan yan majalisa saida suka halacci wannan biki har na da wadanda basa son Yarima Kamzal saboda tsoro kada a gane kiyayyarsu a zahiri. Duk wannan abu dake faruwa hankalin Sarki Kamzal baya kan kowa face Jaruma burinsa kawai shine ya kebance da ita a cikin turakarsa domin ta cika alkawarinta na bude fuskarta ya gani kuma ta bashi labarin rayuwarta amma babu damar hakan saboda duk inda ya shiga dakarun manyan baki na tare dashi. A wannan rana talakawa sun ci sun sha sun more rayuwa a cikin gidan sarautar kuma sun sakata sun ji dadin da basu taba ji ba a tarihin masarautar. Kyaututtuka kuwa na tufafi da kudi saida maroka da talakawa suka gaji da diba. Saida dare ya raba sannan aka watse baki suka tafi masaukinsu, yan gari suka tafi izuwa gidajensu. A wannan lokaci Sarki Kamzal ya gaji ainun kuma idanunsa har lumshewa suke saboda jin bacci gashi yayi shaye shaye, ita kuwa Jaruma bata yarda tasha komai ba a wajen bikin kuma ko yaushe idanunta akan Sarki suke da duk mutanen dake kusantarsa. Ko yaya taga wanda hankalinta bai kwanta dashi ba sai tasa a hana shi zuwa wajen sarki komai matsayin sa da mukaminsa kuma duk inda Sarki Kamzal ya dauke kafarsa nan Jaruma ke sa tata. Kuma dakaru kimanin dubu hamsin ne a kewaye dasu suna basu tsaro. Bayan taro ya watse sai Jaruma ta raka sarki Kamzal har can cikin kuryar turakar marigayi Sarki ta kwantar dashi akan gado sannan ta janyo mayafi ta lullube shi kamar yadda ta saba yi masa Koda yaushe. Koda ta juya da nufin ta fice daga cikin dakin sai kawai taji ya riko hannunta. Cikin tsananin kaduwa da mamaki ta juya ta dube shi tace ya shugabana ka hanzarta sakin hannuna kayi sani cewa kaifa yanzu Sarki ne bani da ikon kwanciya a inda kake. Babu wata mace data isa ta kusanceka face matarka ko kuyangarka. Koda jin wannan batu sai Sarki Kamzal ya Mike zumbur ya dubi Jaruma cikin alamun damuwa yace saboda me zaki guje ni a yau alhalin tunda na hadu dake bamu taba rabuwa ba. Ki sani cewa a halin yanzu duk duniya babu mutumin dana shaku dashi sama dake. Rabuwa ta dake da dakika daya daidai take da gana mini azaba ta tsawon kwana arba'in. Ina mai yi miki tuni cewar yau ne ranar da kikayi alkawarin cewa zaki bude mini fuskarki na gani kuma yaune zaki bani labarin rayuwarki. Na rantse da irin kaunar da nake yiwa mahaifina idan har banga cikakkiyar fuskarki ba a yanzu kuma banji labarin ki ba bazan iya bacci ba. Koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke Jaruma tace kai kuwa mene ne dalilin da yasa ka kagu kafa fuskata kuma kaji labarina? Sarki Kamzal ya numfasa yace saboda na dade da kamuwa sa tsananin son ki da begenki. Ki sani cewa ko Ina tare dake zuciya ta a cikin tunanin ki take. Koda Jaruma taji haka sai hawaye ya zubo mata ta zauna daf dashi takai hannunta izuwa fuskar ta domin yaye mayafin.

WANE IRIN HALI SARKI KAMZAL ZAI SHIGA IDAN YAYI ARBA DA KYAKKYAWAR FUSKAR JARUMA?

KUMA YAYA SOYAYYARSU ZATA KASANCE?

MENE NE AINIHIN LABARIN JARUMA DA ASALINTA, KUMA WAYE BABBAN MAKIYINTA WANDA TAKE SON DAUKAR FANSA A KANSA?

WANE MATAKI YARIMA YUNUS DA MASOYANSA ZASU DAUKA AKAN SARKI KAMZAL?

SHIN KUWA INA JALILA?

A WANE HALI YARIMA IMRAN YAKE BAYAN AN KORE SHI DAGA BIRNIN GABA DAYA?

Mu Hadu A Littafi Na Hudu Domin Jin Cigaban Wannan Kasaitaccen Labari.

Kar ku jjni Shiru.
My system battery got damaged.
Amma insha Allah zan sami wani very soon. ยถ๐™†๐˜ผ๐™๐˜ผ๐™‚๐˜ผ๐™ ๐™ˆ๐™๐™‡๐™†๐™„ยถ
๐™‡๐™ž๐™ฉ๐™ฉ๐™–๐™›๐™ž ๐™‰๐˜ผ ๐™ƒ๐™ช๐™™๐™ช(4) ๐™‹๐™–๐™ง๐™ฉ ๐˜ผ.

โ„ข๐‘จ๐’ƒ๐’…๐’–๐’'๐’‚๐’›๐’Š๐’› ๐‘บ๐’‚๐’๐’Š ๐‘ด๐’‚๐’…๐’‚๐’Œ๐’Š๐’ ๐‘ฎ๐’Š๐’๐’Šโ„ข.

๐˜ผ๐™—๐™ช๐™—๐™–๐™ ๐™–๐™งโค๏ธ๐™ƒ๐™–๐™ก๐™š๐™š๐™›๐™–๐™โค๏ธ๐™‹๐™๐™ฎ๐™จ๐™ž๐™˜๐™ž๐™จ๐™ฉ

โ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขLokacin da Sarki Kamzal yaga Jaruma ta dora Hannunta akan mayafin kanta don ta bude masa fuskarsa ya gani, sai jikinsa ya fara tsuma idanunsa da bakin sa ma suka kama motsi hatta hancinsa ma rawa yake tsabar kaguwa da son ganin Fuskarta ta. A hankali a cikin jan rai Jaruma ta kwaye fuskarta ta gaba daya.koda Sarki Kamzal yayi arba da kyakkyawar fuskarta sai ya mike zumbur kamar wanda aka tsira da allura ya kura mata idanu yadda ko kiftawa ba yayi.Tunda Sarki Kamzal yazo duniya bai taba ganin mace mai kyakkyawar fuska ba irin ta Jaruma tamkar saida aka zana ta iya yadda ake so ta kasance sannan aka halicceta. Gaba daya numfashin Sarki Kamzal daukewa ya yi yaji a ransa cewa duk irin bakin cikin da zai shiga a rayuwarsa indai zaiyi arba da wannan kyakkyawar fuska to fa bakin ciki zai juye ya koma farin ciki. Lokacin da Jaruma taga sarki Kamzal ya dimauce kuma ya fita daga hayyacinsa sakamakon ganin kyawun fuskarta wacce ta kasance mai haske tamkar wata dare na sha biyu. Sai ta mike tsaye ta cire rigar yakin dake jikinta, faruwar hakan ke da wuya sai taga sarki Kamzal ya fadi kasa tamkar an kwarfe kafafun.Ashe ji yayi kafafun nasa ba zasu iya daukar nauyinsa ba saboda ganin tsananin kyawun surar jikin Jaruma wanda ya baiyana a cikin rigar dake jikinta wacce ta kasance fara sol kuma mai shara shara. Koda Jaruma ta tabbatar da cewar Sarki Kamzal ya gama ganin duk irin baiwar Allah yayi mata ta kyau. Sai tayi sauri ta dauki rigar yakinta ta sanya sannan ta zauna a kasa dirshan ta fuskanci Sarki Kamzal a lokacin da tazarar dake tsakaninsu bata wuce taku shida ba. Kuma a sannan ne hawaye ya zubo mata tace yakai wannan Sarki kayi sani cewa ban bayyana fuskata da jikina a gareka ba domin komai ba sai saboda ka gasgata labarin da zan baka a yanzu wanda shine sanadin bukatar da nake nema a wajenka kuma shine asalin tarihin rayuwata. Koda Jaruma tazo nan a zancenta sai Sarki Kamzal yayi dogon ajiyar numfashi tamkar wanda ya farfado daga dogon suma a sannan ne ya dawo cikin hayyacinsa kuma ya kara nutsuwa yana mai kura mata idanu. Jaruma tayi gyaran murya sannan tace:-
๐˜ผ๐™—๐™ช๐™—๐™–๐™ ๐™–๐™งโค๏ธ๐™ƒ๐™–๐™ก๐™š๐™š๐™›๐™–๐™โค๏ธ๐™‹๐™๐™ฎ๐™จ๐™ž๐™˜๐™ž๐™จ๐™ฉ
Ni dai na fito ne daga wata nahiya dake kusa da dajin nan wanda nayi jinyarka a cikinsa. Shi kuwa wannan daji yana cikin yankin kasar da mahaifiyata ke Mulki wacce ake kira da suna Madinatul Sauwab. Birnin Madinatul Sauwab ya kasance babbar daula wacce ta tara kabilu sama da kala bakwai. Kuma gari ne mai cike da bokaye iri iri. Fiye da shekaru dari uku zuri'ar mahaifina ke mulki a wannan kasa ta Madinatul Sauwab kuma kabilar su itace mafi rauni da karancin al'umma Amma kuma sune mutane na farko da suka fara zama a kasar tun wajen yana kungurmin daji. Sunan kabilar mahaifina Banu Amzad. Amzad shine kakana na saba'in da tara kuma shine Sarki na farko daya fara mulkar birnin Madinatul Sauwab. Daga kansa wannan sarauta ta cigaba habaka tana bin iyaye da jikoki bata taba fita daga gidan ba. Gaba daya zuri'ar mu mun kasance gawurtattun sadaukai don haka jinin sadaukantaka ne yake bibiyarmu

Please Login or Register in order to submit comment