Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

anan gaba bazai iya sarautar kasar ba saboda yayi abin kunyar da dama can hukuncinsa kenan a cikin kundin Shari'a na masarautar.

WANE IRIN BAKIN HUKUNCI YARIMA IMRAN ZAI DAUKA?
TSAKANIN YARIMA KAMZAL DA YARIMA YUNUS WAYE ZAI CINYE WANNAN GAGARUMAR GASA?
WANE IRIN BURI BAKUWAR JARUMA TAKE SON SAMU DAGA YARIMA KAMZAL?
SHIN MUGUN KUDIRIN GIMBIYA JALILA ZAI CIKA KUWA?
SHIN DAKARUN SUMAME ZASU SAMI NASARA AKAN YARIMA KAMZAL KO KUWA?
Mai son jin karshen wannan labari ya samu Littafi KARAGAR MULKI na biyu domin jin cigaba.

โ€ขAbubakar Haleefah physicistโ€ข ยถ๐™†๐˜ผ๐™๐˜ผ๐™‚๐˜ผ๐™ ๐™ˆ๐™๐™‡๐™†๐™„ยถ
๐™‡๐™ž๐™ฉ๐™ฉ๐™–๐™›๐™ž ๐™‰๐™– ๐˜ฝ๐™ž๐™ฎ๐™ช (2) ๐™‹๐™–๐™ง๐™ฉ ๐˜ผ
โ„ข๐‘จ๐’ƒ๐’…๐’–๐’'๐’‚๐’›๐’Š๐’› ๐‘บ๐’‚๐’๐’Š ๐‘ด๐’‚๐’…๐’‚๐’Œ๐’Š๐’ ๐‘ฎ๐’Š๐’๐’Šโ„ข.

โ€ขโ€ขโ€ขKoda Yarima Imran yaji hukunci da ake yanke masa sai ya kwarara uban ihu ya daka tsalle daga inda yake ya cafi makoshin Shamilat ya shaketa yana mai cewa ta gaya masa wanda yasa tayi masa wannan sharri.A guje dakaru da yawa suka rugo izuwa kan Yarima Imran suka fara kokarin cire hannunsa daga wuyan Shamilat a lokacin da tuni ta fara KAKARIN MUTUWA.A wannan lokaci Gimbiya Jalila na tsaye a gefe guda idanunta sun zazzaro hankalinta ya DUGUNZUMA ainun sannan zuciyarta ta fara dukan uku uku saboda tsoron kada Shamilat ta tona mata asiri.Koda dakaru sukaga sun kasa cire hannun Yarima Imran daga makoshin Shamilat sai suka rufe shi da duka har saida suka sumar dashi sannan suka sami damar banbare hannunsa daga wuyan Shamilat.Tuni a wannan lokaci Shamilat ta suma saida aka yayyafa mata ruwan sannan ta farfado shi kuwa Yarima Imran sai aka tattara nasa ina sa aka jefa shi a cikin wani a kurki kamar kaza aka dora a akurkin sannan aka ja.Yarima Imran na kuka mahaifiyarsa na kuka tana bin keken shanun da gudu har tana faduwa tana daddaujewa.Haka dai ta hakura aka tafi dashi tana gani aka kule dashi ta daina hango shi.Komai rashin tausayi,da rashin imanin mutum idan yaga yadda aka wulakanta Yarima Imran haka aka raba shi da mahaifiyarsa da kuma sarautar gaba daya dole ya tausaya masa.Tun kafin wannan al'amari ya faru wato farkon yammaci Yarima Kamzal ya fita FARAUTA DAJI tare da Jaruma mai tsaron lafiyarsa su biyu kacal.Ashe tuni Gimbiya Jalila ta sami labarin wannan fita da yayi.Nan take farin ciki ya lullubeta saboda dama ta dade tana hakon wannan dama wacce Yarima Kamzal zai fice daga gidan Sarautar domin kuwa tuni ta dauko hayar wadansu zakwakwaran MAYAKA daga birnin Kisra su dari bakwai sunyi kwantan bauna a cikin daji.Kuma ta biya su kudade masu yawa akan cewa sai sunyi kwana arba'in a daji suna fakon Yarima Kamzal ko Yarima Yunus domin su ashe su.Su dai wadannan Mayaka na Birnin Kisra sun kware wajen iya kisan manyan mutane masu mukami a duniya ko masu fada aji kuma musamman aka basu horo na shekara shida domin kwarewa wajen KISA.Don haka basu taba yin kuskure ba bisa irin aikin da aka tura su sama da shekara hudu da suka gabata.Ba wani ne yasa ka tanadi wadannan mayaka ba kuma aka basu horo na tsawon shekara shida face wani gawurtaccen attajiri dake birnin Kisra ana kiransa da suna Abu Yazid.Ba don komai ya kirkiri wadannan mayaka ba sai don samun kudi mai yawa wajen sarakai da manyan attajieai na duniya masu son su kashe ABOKAN GABArsu.Tunda suna iya biyan kudi ko nawa ne akan hakan.Babu wata hanya da take kawowa Abu Yazid kudi sama da wannan DAKARUN KISAN KAI.Saboda duk sa'adda aka zo ka nemi hayarsu ana biyan shi makudan kudade fiye da tunanin mutum don haka shima yana kula ainun da lafiyar dakarun kuma yana kyautata musu ko kuda bai son yaga ya sauka a jikinsu.

ยฐยฐยฐAsalin yadda Yarima Kamzal ya hadu da wannan Jaruma mai tsaron lafiyarsa.Abin ya faru ne a ranar da yan'uwansa su Takwas suka sa aka sassara shi da takobi tamkar ya mutu ashe dogon suma yayi.Sannan aka sanya shi cikin buhu aka kulle bakin buhun sai aka je dashi har tsakiyar teku a cikin jirgin ruwa sannan aka jefa shi cikin ruwa ya lume izuwa can karkashin tekun.Ashe duk wannan abu dake faruwa wannan BAKUWAR JARUMA tazo zata gifta ta saman tekun bisa wani tsuntsunta na tsafi,har ma ta gifta wadanda suka jefa Yarima Kamzal a cikin tekun sai taji karar faduwar Yarima Cikin tekun.Al'amarin da yasa ta fahimci cewa lallai wani abu aka jefa don haka sai ta zunguri tsuntsunta na tsafi ya dawo da baya.Amma kafin su iso tsakiyar tekun tuni wadanda suka jefa Yarima cikin tekun sunyi nisa da tafiya har ma sun kule a hango su.Nan take Jarumar tayi nutso izuwa cikin tekun bisa tsuntsunta.Abina da mai amfani da KARFIN TSAFI tana shiga coin tekun ta hango buhun da aka sa Yarima a ciki yana dada nutsewa izuwa can kasa.Take ta sake zungurin tsuntsunta na tsafi yabi buhun da guda har suka riske dashi.Da hannu daya ta cafo buhun sannan tsuntsun nata ya taso sama izuwa saman tekun sai gasu a jike sharkaf ita da tsuntsun da kuma buhun data dauko ruwa na diga a jikinsa.Cikin hanzari ta kwance buhun saiga mutum a ciki duk jikinsa sara yai kaca kaca da jini.A cikin dimauta Jarumar ta umarci tsuntsun nata daya hanzarta kaita gida.Ai kuwa sai tsuntsun ya juya ya nufi yamma yana mai tsala azababben gudu a cikin sararin samaniya.Cikin abinda bai wuce dakika dari uku da ashirin ba.Tsuntsun ya iso cikin wani kyakkyawan daji mai fadi gami da tsawon gaske,akwai dogayen bishiyoyi ababen sha'awa a cikin wannan daji kuma ga koramai da tsirrai iri iri,ga dabbobin daji kanana da manya birjik sai harkinsu sukeyi.Kallo daya zaka yiwa wannan daji ka gane cewa akwai ni'ima a cikinsa.Wata buka ce guda daya jal a tsakiyar wannan daji wanda babu gida gaba ko baya a cikinsa.Kai tsaye tsuntsun tsafi ya sauko kasa ya dira a gaban bukka.Cikin dimauta da gaggawa Jarumar ta sauka daga kan tsuntsun dauke da Yarima Kamzal a kan hannayenta ta ruga izuwa cikin turakar.Faruwar hakan ke da wuya sai wannan tsuntsun tsafi ya rikide ya zama takobi tsaye a cake a cikin kasa.Lokacin da jaruma ta shiga da Yarima Kamzal izuwa cikin wannan bukka sai ta shimfida shi akan shimfidarta sannan ta dauko zare da allura ta dinke duk raunikan dake jikinsa kuma ta shafa masa magani akan raunikan duka.Har ta gama yi masa wannan kokari bata ga ko alamar numfashi ba a tare dashi.Al'amarin da yai matukar DUGUNZUMA hankalinta kenan ta fara tunanin cewa lallai wannan kyakkyawan saurayin ya mutu.Babban burinta shine ta ceto rayuwarsa kuma taji daga bakinsa abin da yasa aka yi masa wannan mugun sara aka daure shi cikin buhu aka jefa shi a teku don hallaka shi kuma taji wanda yasa akayi masa hakan.Lokacin da Jaruma taga ko kadan babu alamar rai a tare da Jarima Kamzal sai bakin ciki ya turnuke ta don haka sai ta mike tsaye da nufin taje ta haka kabarin da zata binne shi.Kwatsam bazato ba tsammani sai taji Kamzal ya kawo gauron nunfashi sakamakon farfadowar da yayi daga dogon suma.Koda Kamzal ya bude idanunsa da kyar sai yayi arba da Jaruma zaune a gabansa cikin fararen tufafi kuma ta rufe fuskarta da rawani idanunta kadai ake gani sai ya cika da tsananin mamaki kuma ya firgita yaja da baya a tsorace yana mai kallonta yace ina ne nan?Ta yaya akayi nazo nan?Koda jin wannan tambaya sai Jarumar tayi murmushi ta dubeshi cikin wata irin ZAZZAKAR MURYA wacce bai taba jin irinta ba sannan tace kwantar da hankalinka dan samari,a duniya kake ba lahira ba,nice na kawo ka nan kuma na tsamoka ne daga cikin tsakiyar teku bayan an sassara ka an saka a cikin buhu an daure buhun.Ni kaina ban yi zaton kana da rai ba domin har ma nayi niyar haka kabari na binneka bayan na gama duba raunikan jikinka nayi maka magani kuma sai naga ka farfado,wai shin wane ne kai?Daga ina ka fito kuma ya akayi ka shiga wannan hali.Lokacin da Yarima Kamzal yaji wadannan tambaboyi sai hawaye ya zubo masa sa'adda ya kurawa idanun jarumar kallo yana mai aiyanawa a cikin ransa cewa lallai dole ne wannan macen ta zamo kyakkyawa ta misali domin kyawun idanunta kadai ya tona asirin kyawun fuskarta.Kamzal yayi ajiyar zuciya yace sunana Yarima Kamzal kuma na kasance 'da ga Sarki Urdut na birnin Hindu.Wannan hali da kika ga na shiga ba wasu bane suka jefa ni a cikinsa ba face yan uwana su takwas wadanda muke uba daya saboda kawai ganin yadda mahaifinmu yake tsananin KAUNATA kuma sue tsoron kada ya bani KARAGAR MULKInsa ta kowace hanya koda kuwa zai saba dokar masarautar tamu.Nan dai Yarima Kamzal ya kwashe labarin kaf ya zaiyanewa Jarumar har da wasiyar da sarki Urdut ya bar masa tun kafin ya shiga wannan hali.Bayan Yarima Kamzal ya gama bata wannan labari sai ya dube ta yayi godiya bisa ceton rayuwarsa datayi sannan yace yake wannan Jatuma Mai ABIN AL'AJABI mene ne sunanki kuma mene ne naki labarin!Saboda me kike zaune a cikin wannan kungurmin daji ke kadai?Sa'adda Jaruma taji wannan tambaya sai ita ma hawaye ya zubo mata ta dubeshi tace yakai wannan dan sarki,kayi hakuri nayi alkawarin bazan baiyana kaina ga kowa ba har sai bayan na cika wani babban buri nawa a wannan duniya.Zan taimaka maka daga yanzu na tsare lafiyarka da rayuwarka har izuwa lokacin da zaka kau kan karagar mulki ta birnin Hindu amma bisa sharadi guda,sharadin kuwa shine ni ma zaka biya min wata bukata tawa guda daya wacce bazan furta maka ita ba sai bayan naka burin ya cika,wannan shine alkawarin da nake so ka daukar mini.Koda jin wannan batu sai Yarima Kamzal ya kamu da tsananin mamaki kuma ya shiga wasi wasi don haka sai ya dubi Jarumar cikin mamaki yace haba yake wannan bakuwar Jaruma saboda me zaki sa na dauki alkawari akan abinda ban san me zanyi ba,idan kuma abin da kike son nayi bazan iya shi ba fa?shike nan sai ki zarge ni da laifin yi miki butulci ko cin amana!Koda jin wannan batu sai Jarumar tayi murmushi tace ai abinda zan nema a wajenka darajarsa bata kai a tsoma silin gashi a cikin tandun mai ba a ciro shi,dan abin da ka laso shine abinda zaka bani a cikin tarin arzikinka saidai bazaka taba biya min wannan bukata ba face ka hau kan karagar mulkin birnin Hindu.Ina so ka sani cewa hawanka kan wannan karagar mulki ba karamin aiki bane domin daidai yake da Jarumi daya jal daya tunkari Mayaka dubu dari a FILIN DAGA.Koda zan rasa rayuwata zan tsaya tsayin daka na tabbatar da cewar ka zama sarkin birnin hindu,burina kawai shine ka zamo mai cika alkawari a gare ni.Sa'adda jaruma tazo nan a zancenta sai Yarima Kamzal yayi shiru yana tunani da nazari.Daga can kuma sai ya dago kai ya dube ta yace na amince da wannan sharadi da kika zo mini dashi,amma ina neman alfarma guda biyu a wajenki.Alfarma ta farko itace inason ki bude mini fuskarki da jikinki domin naga baiwar ki ta tsananin kyau saboda alamar karfi tana ga mai kiba.
Alfarma ta biyu itace ina son ki fada mini sunanki na gaskiya wanda iyayenki suka rada miki domin bansan dame zan rinka kiranki ba. Koda jin wannan batu sai Jarumar ta kyalkyale da dariya. Al'amarin daya bawa Yarima Kamzal mamaki kenan sannan ta dube shi tace.Magana daya itace alamun mutumin kirki. Bana yin magana biyu don haka bazan taba baiyana maka ko ni wace ba sai bayanzama zama sarki.Zan zauna tare da kai anan har tsawon sati biyu. A sannan ne raunikan fake jikinka zasu warke. Sannan na dauke ka na mayar dakai birnin ku. Zamu iske ana gasar hawa Karagar mulki a tsakanin yan uwandon don haka lallai bazan bari wandama dama ta wuce ka ba. Dole ne kai ma ka shiga cikin wannan gasa. Koda jin wannan batu sai idanun Yarima Kamzal suka zazzaro hankalinsa ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe ya dubi Jarumar cikin alamun tsananin mamaki yace ta yaya zamu je mu iske ana yin wannan gasa alhalin mahaifinmu yana raye. Kuma ya yaya zan shiga wannan gasa har nayi nasara alhalin ni bani da ilmin komai akan irin tambayoyin da za'a yi akan gasar. Koda jin wannan tambaya sai tausayin Yarima Kamzal ya kama Jarumar tayi shiru tana mai sunkui sa kanta kasa. Kuma ta juya masa baya tace zamuje birnin ku mu iske mahaifinku ya rasu sakamakon kwanciyar da yayi ta CUTAR AJALI. Dangane da ilmin sanin tambayoyin da za'a yi muku kuwa ni zan koya maka su a cikin sati biyun nan. Kuma zaka haddace komai a cikin kwakwalwarka tamkar akan takarda aka rubuta da tauwada. Koda jin wannan batu sai Yarima Kamzal yayi shiru bai kara cewa komai ba yana mai zargi da wasu wasi a cikin zuciyarsa dangane da wasu al'amari na wannan bakuwar Jaruma. A karshe dai sai zuciyarsa ta aiyana masa cewa lallai wannan Jaruma tana amfani ne da karfin sihirin tsafi don in ba haka ba babu yadda za'a yi ya iya yin duk abubuwan da tayi yanzu da kuma fadin abubuwan da zasu faru nan gaba. To wai shin abinda ta fadi gaskiya ne cewar mahaifinmu zai mutu nan da cikar sati biyu. Koda yazo nan a tunaninsa sai hawaye ya zubo masa ya tuno da irin tsananin shakuwar dake tsakanin sa da sarki da kuma yanayin da zai kasance idan babu shi. Nan take zuciyat Yarima Kamzal ta sake karaya hawaye ya cigaba da surtowa a kumatunsa. Ya juyar da fuskar sa can gefe daya don kada Jaruma taga halin da yake ciko. Daga wannan rana Jaruma ta cigaba da jinyar Yarima Kamzal ya zamana cewa a kullum itace ke bashi abinci da abin sha a bakinsa da hannunta. Yana daga kwance saboda ko mikewa zaune ba zai iya yi ba. Kai ko daga hannunsa ma ba zai iya ba.Ko kawar da bukata zaiyi ita take taimaka masa yayi a cikin wani akushi kuma ta tsarkake shi ta kawar masa da najasa. Tun yana jin kunyarta saida ya saba da ita Yana mamakin yadda take yi masa wannan wahala ba tare da kyama ko gajiyawa ba. A kullum tana biya masa karatun ilmin sarauta da sauran ilmin na al'amuran rayuwa sau uku, safe da rana da dare. Bayan nan sai su cigaba da hirar duniya wani lokacin saboda dadin hirar har dare ya raba basu sani ba.Babban abinda yake daurewa Yarima Kamzal kai shine tsawon satin biyun da sukayi a cikin wannan daji babu wata muguwar dabba data taba kawo musu hari ko ta gifta ta kusa da bukkar su. Babu wani mugun aljani ko yan fashi da suka taba baiyana a gare su. A ranar kwana na tara ne Yarima Kamzal ya sami lafiyar jikinsa sosai har ya mike daga kwance. A wannan lokaci ne Yarima Kamzal ya lura da duk irin raunin dake Jikinsa yaga irin manyan saran da akayi masa domin a hallaka shi. Take idanunsa suka ciko da kwallar takaici bisa tunowa da cewar yan uwansa nefa na jini suka aikata haka a gare shi saboda kawai su raba shi da Karagar mulki. Bai ankara ba sai yaji hawayen bakin ciki ya zubo masa. Adaidai wannan lokaci ne Jaruma ya shigo cikin bukkar ya dube shi cikin murna yace yakai Yarima dama zuwa nayi ka rakani mu tafi izuwa farauta saboda nasan cewa a rayuwarka babu abinda kake sha'awa sama da farauta a cikkn daji. Koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke Yarima Kamzal ya dubi Jaruma yace haba yake wannan Jaruma ta yaya kice na raka ki farauta alhalin yanzu ma ne na sami saukin da har na iya mikewa daga kwance. Jaruma tayi murmushi tace ai kuwa a yanzu mikewa zakayi kuma yaune zan fara koya maka yaki saboda ka iya tsare kanka. Idan mun shiga wani halin da bazan iya kare kai na da kai ba a lokaci guda. Tana fadin haka sai ta kamo hannunsa ya finciko shi da sauri suka fice da gudu daga cikin bukkar. Nanfa Yarima Kamzal ya cika da tsananin mamaki bisa ganin yadda yake iya taka kafafunsa har yaketsala tsala gudu alhalin a zatonsa saiya shafe sama da wata uku nan gaba kafin ya iya taka kafafunsa saboda saida Jaruma ta gyara masa karaya biyu a kafarsa ta hagu. Amma gashi yanzu yana gudu da kafafunsa tamkar wani abu bai taba samun sa ba. Saida Yarima da Jaruma suka yini a daji suna farauta anan ne Yarima Kamzal ya sake tsinkewa da al'amarin Jaruma yaga tayi gagarumar jarumtakar data shallake tunaninsa. A gaban idanunsa tayi BAKIN GUMURZU da wani rikakken zaki da KARFIN DAMTSEN ta ba tare da tayi amfani da makami ba ko karfin sihirin tsafi. Da farko saida tayi DAUKI BA DADI da zakin suna kokawa a kasa yana turmushe ta tana turmushe shi kuma Tana gabza masa naushi shi kuma yana yakusar jikinta da faratan hannunsa kuma yana kokarin kafa hakoransa akan jikinta amma ya kasa samun ta domin da zarar zakin ya danneta sai kaga ta juye dashi ta ture shi kuma ta take wuyansa da kafa guda tana gabza masa naushi da hannu. Nan da nan zakin ya karkarce mata jiki da faratan hannunsa jini ya rinka zubowa. Ita kuwa a garin naushin sama ta fasa masa ido guda. Nanfa ita da zakin duk suka fusata ainun suka kara kaimi wajen ganin sun hallaka juna. A wannan lokaci ne zakin ya shammaci Jaruma ya dako tsalle a sama ya bangaji Jaruma da kirjinsa take Jaruma tayi sama bayanta ya gwaru da jikin wani dutse ta fado kasa a matukar galabaice. Ai kuwa sai zakin ya dako tsalle da nufin ya dira a kanta saboda a zatonsa ko motsi ba zata iyayi ba. Ba zato ba tsammani sai gani yayi Jaruma ta mirgina can gefe daya faratan kafafun zakin sun karci kasa. Kafin zakin yayi wani yunkuri tuni Jaruma ta daka tsalle sama ta dira a kan gadon bayan zakin kawak sai tasa hannayenta biyu ta tale bakin zakin da karfin tsiya kuma ta turmushe shi a kasa. Wohoho! KARFI SAI ALLAH ya isa. Tabbas sadaukantaka baiwa ce daga Allah. Nanfa zakin nan yayita murkususu a kasa ya ka sa kwatar kansa daga hannun Jaruma yana ji yana gani har saida karfinsa ya kare ta bare masa baki sannan tayi jifa da gawarsa. Ai kuwa ita ma saita zauna a kasa dirshan tana ta numfashi saboda tsananin gajiya tamkar ranta zai fita.saida ta huta sosai sannan ta yanke kan zakin kuma ta fede shi ta gashe namansa. ๐Ÿ˜‹. (Raina ya biya).
Nan suka zauna suka ci naman suka koshi suna hirarsu har saida rana ta fadi sannan sukayi guzurin naman suka bar sauran kafin su tafi sai Jaruma ta dauki kan zakin data kashe tayi gaba. Koda ganin haka sai Yarima Kamzal yace yake Jaruma me kuma zakiyi da kan wannan zakin? Koda jin haka sai Jaruma tayi murmushi yace dadina dakai ka cika garaje. Kayi hakuri ka zuba ido zakaga abinda zanyi da kan wannan zaki. Tana gama fadin hakan sai tayi shiru ba kara cewa komai ba har saida suka iso bakin kofar wani kogon dutse suna zuwa sai Yarima Kamzal yaga Jaruma ya cire takalmin fatar dake kafarta ta ajiye shi a gefe daya sannan sai ta juyo ta dubi Yarima Kamzal tace kaima cire takalmin ka. Ba tare da gardamar komai ba kuwa sai Yarima ya cire takalmin nasa sannan yabi bayan Jaruma a baya suka shige cikin kogon. Da farko kogon dundum yake da duhu amma Jaruma nasa kafarta a cikinsa saiya haskake da wani irin haske na ban Al'ajabi wanda ko allura ce ta fadi a kasa sai idanu sun gani. A can karkashin kogon daga sama jikin dutsen kogon wani gunki ne na batoyi wanda akayi shi da karfen Zinare sai sheki da walwali yake. Wannan gunki ya sassaku sosai tamkar zai iyayin motsi wato tamkar akwai ruhi a Jikinsa. Nan take Jaruma ta durkusa bisa guiwoyinta biyu a gaban wannan gunki tayi masa sujjada. Shi kuwa Yarima Kamzal saiya tsaya cak a tsaye daga bayanta yana kalle kalle da dube dube a cikin kogon. A sannan ne ya hango kawunan Zakuna guda casa'in da takwas rataye a sama jikin dutsen kogon a bangaren yamma nan fa ya cika da mamaki mene amfanin kawunan Zakunan a wajen. Kuma yayi mamaki yadda akayi basu rube ba sun zagwanye tunda kawuna ne na gaske bawai kerasu akayi ba daga kasa ko karfe. Saida Jaruma ya shafe kusan dakika dari tsugune a kasa cikin yin wannan sujjada ga gunkin batoyin sannan ta daga kai ta mike tsaya tana rike da kan wannan zaki data kashe ta nufi inda aka rataye wadannan kawunan Zakuna guda casa'in da takwas. Isarta daf da wajen sai ta daga kan zakin sama, take kan yabar hannun ta yai sama yaje ya manne a kusa da dan uwansa na casa'in da takwas ya zama guda casa'in da tara kenan, wato dari ba daya. Faruwar hakan keda wuya sai wata kofa ta wanzu a jikin bangon kogon dutsen bangaren yamma kuma kofar ta bude kanta. Cikin murna Jaruma ta yafuto Yarima Kamzal da hannun ta ya bita a baya suka shige cikin wannan kofa suna shiga suka tsinci kansu a cikin wani daki mai fadi. A tsakitar dakin an ajiye wata dankareriyar KARAGAR MULKI wacce aka kerata da zallan karfen lu'ulu'u. Akan hannun Karagar kuma an ajiye wata zabgegiyar Takobi wacce itama anyi ta ne da farin lu'ulu'u.Kai tsaye ta durfafi wannan karagar mulki wacce aka........

Mu hadu a part B.
Abubakar Haleefah Physicist ยถ๐™†๐˜ผ๐™๐˜ผ๐™‚๐˜ผ๐™ ๐™ˆ๐™๐™‡๐™†๐™„ยถ
๐™‡๐™ž๐™ฉ๐™ฉ๐™–๐™›๐™ž ๐™‰๐™– ๐˜ฝ๐™ž๐™ฎ๐™ช (2) ๐™‹๐™–๐™ง๐™ฉ ๐˜ฝ.

โ„ข๐‘จ๐’ƒ๐’…๐’–๐’'๐’‚๐’›๐’Š๐’› ๐‘บ๐’‚๐’๐’Š ๐‘ด๐’‚๐’…๐’‚๐’Œ๐’Š๐’ ๐‘ฎ๐’Š๐’๐’Šโ„ข.

โ€ขโ€ขโ€ขโ€ขKai tsaye Jaruma ta durfafi wannan karagar mulki wacce aka lullubeta take da yana kai da gani kasan cewa tafi shekarata arba'in a wajen a haka ba tare da wani ya tabata ba.Koda Jaruma ta iso daf da karagar mulki sai gaba dayan yanar dake jikinta ta nannade kanta tayi sama.Jaruma ta zauna akan karagar mulkin sannan ta dauki wannan zabgegiyar takobi dake kan hannun Karagar ta rike ta da hannun biyu,koda ta janyo takobin tuni saman rufin dutsen ya yaye gaba dayansa tamkar an dauke murfi daga kan tukunya saiga wadansu halittu suna durowa daga sararin sama sune zubewa kasa gaban jaruma suna yi mata sujjada.Saboda tsananin girman halittun gami da kwarjininsu da kuma shigar da sukayi ta yaki saida Yarima ya firgice ainun yaji fitsari kamar ya kubuce masa.Gaba dayan halittun sunyi sujjada ga Jaruma sai ta mike tsaye sannan tayi ruku'u ga halittun kuma ta mayar da wannan takobi cikin kufenta kuma ta rataya ta a gadon bayanta.Faruwar hakan keda wuya sai wadannan halittu suka tashi tsam gaba dayansu kamar tsuntsaye suka fice daga cikin wannan kogon suka luluka izuwa cikin gajimare suka bace bat.
A sannan Jaruma ta sake zuwa gaban gunkin wannan batoyi tayi masa sujjada,wannan karon sai batoyin yayi motsi yana mai wangame bakinsa ya furzar da gagarumar wutaAl'amarin da yayi matukar razana Yarima Kamzal kenan ya yunkura zai fita da gudu amma sai Jaruma tayi wuf ta riko hannunsa amma duk da haka sai ya takure jikinsa a bayanta yana kyarma.Take batoyin ya sake kamewa ya zama gunKi.Kaiwa sai Jaruma ta kamo hannun Yarima ta jashi suka fice daga cikin kogon dutsen suka fita kuwa sai kogon dutsen ya dusashe cikin tsananin duhu da mutum ko tafin hannunsa ya daga ba zai gani ba.Fitowarsu keda wuya daga cikin kogon dutsen sai Yarima yayi ajiyar zuciya kamar wanda ya tsallake rijiya da baya ya dubi Jaruma cikin alamun tsananin kaduwa yace yake Jaruma mene ne alakar ki da wannan kogon dutse da kuma duk abinda naga ya faru a cikinsa,Mene ne amfanin wannan karagar mulki wacce kika zauna a kanta kuma mene ne amfanin wannan farar taobi da kika dauko daga cikin kogon dutsen?Sa'adda jaruma taji wadannan tambayoyi sai tayi murmushi sannan tace bazan iya gaya maka alakata da wannan takobi ba ko abubuwan da ke cikinsa saboda tamkar na baiyana ko ni wace ce ne a gareka.Kada ka manta cewa nayi alkawari bazan sanar dakai wannan sirri ba sai bayan ka hau kan karagar

Please Login or Register in order to submit comment