Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mu ba wakilan sarki Amzad bane. Shiga mukayi irin tasu. Inaso kayi sani cewa mu wakilai ne na kabilu guda shida na kasar nan masu adawa da mulkin sarki Amzad kuma masu son kawo chanji. Ka sani cewa rayuwarka data dukkan iyalan ka na cikin hadari amma akwai mutum daya jal wanda zai iya ceto rayuwar taku kuma ba kowa bane face yarka Amarya Malina. Daga nan zamu wuce daku izuwa birnin Baitul Najwas inda za'a tsare ku amma ita Amarya Malina za'a kaita gidan mijinta kamar yadda kuke bukata. Daga yau yarka Amarya Malina zata rinka karbar umarni daga wajen shugabannin kabilu shida duk abinda aka umarce ta da tayi dole yishi akan sarki Amzad. Idan kuma ta kiyi a bakin ranku gaba dayanku. Koda jin wannan batu sai gaba dayan matan mai gari da yayansa suka dimauce suka kama koke koke anna shi mai gari da Malina ko gezau basuyi ba. Mai gari ya dubi Sadauki Kan'an cikin nutsuwa ba tare da alamar tsoron komai ba yace waishin kun manta da waye sarki Amzad har da kuke tunanin cewa zaku iya ganin bayansa ta hanyar amfani da 'yata? Koda jin wannan batu sai Kan'an ya dakawa mai gari tsawa yace bamu da lokacin baka amsar wata tambaya ina mai ja maka kunne da kada ka kuskura kace zakayi wani kokari na guduwa ko tserar da kanka da iyalenka domin idan gaba dayan mazajen kauyen ban naku zasu taran mana ba zasu iya damu ba. Lallai kuyi shiri mu tafi gaba daya yanzu kuna masu nunawa jama'ar gari cewa kuna cikin farin cikin raka 'yarku izuwa birnin gidan mijinta.ku sani cewa ko yaya ku kayi wani motsi wanda bamu yarda dashi ba don tona mana asiri a bakin ranku. Koda jin wannan batu sai mai gari da iyalansa suka firgita ainun suka dimauce. Ita kuwa amarya Malina ko a jikinta kawai ma sai ta kama dariya saboda tasan cewa sarki Amzad ba kanwar lasa bane. Nan dai su Sadauki Kan'an suka tusa keyar amarya da duk mutanen gidansu suka tafi dasu bisa dawakai ana ta bushe bushe da kade kade irin wanda aka sabayi bisa al'ada.wannan shine abinda ya faru ga Amarya Malina bayan an daukota daga kauyen su don kaita gidan angonta.

-Al'amarin Sarki Amzad kuwa lokacin daya fito daga cikin sarautar sa a guje bisa doki kuma cikin SHIGAR YAKI sai ya cigaba da da falfala azababben gudu tamkar zai tashi sama. Burinsa kawai shine yaga ya isa gidan boka Kimbaru cikin kankanin lokaci. Haka dai ya cigaba da wannan gudu har ya zamana cewa yaci rabin Tafiyar. Koda ya shigo cikin wani daji wanda ake kira da Mautul Azaru sai kawai yaji shi da dokin nasa anyi masa dasu ashe cikin tarkon raga suka fada. Kafin ya Ankara an janye ragar izuwa can saman bishiyoyi. Koda ya leko kasa sai yaga ashe wadansu dakaru ne na yaki sama da dubu goma dauke da miyagun makamai suka rabu kaso biyu suna jan igiyar dake sakale da ragar da yake ciki shida dokinsa. Dakarun suna jan igiyar shida dokinsa nasa suna karayin sama. Koda ganin wannan al'amari sai sarki Amzad yayi murmushi kawai sai ya bude hannayensa take ragar data kanannadesu shida dokinsa ta zagwanye ta zama ruwa suka diro kasa bisa kafafunsu. Nanfa dakarun suka ruga gaba dayansu suka yiwa Sarki Amzad KAWANYA suna masu zare makamansu. Maimakon Sarki Amzad ya zare takobinsa sai ya gyara zama akan dokinsa ya dubu gaba dayansu ya fahimci cewar gaba dayansu baki ne na SOJAN HAYA aka dauko su. Sarki Amzad ya dube su cikin takaici yace banason na kashe mutanen da suka kasance baki. Ina mai shawartar ku daku yakice wannan kwangila da aka baku ta kashe ni. Domin ba zaku iya ba. Kuma idan har zaku sanar dani wanda ya baku wannan kwangila zan biya ku ninkin ba ninkin abinda ya baku. Idan kuma kuka ki gaba dayanku zaku koma izuwa birninku a kakkarye domin bani da bukatar kashe ku. Kafin Sarki Amzad ya gama rufe bakinsa tuni shugaban wadannan dakaru ya tari numfashin sa yana mai daka nasa tsawa yace kai tsohon azzalumin sarki wanda ya danne hakkin sauran kabilun kasar sa. Kayi sani cewa mun karbi wannan kwangila ne bisa amana da kuma goyan bayan masu son ganin bayanka. Saboda mun fika gaskiya don haka ba zamu taba cin amanarsu ba. Muna da labarin karfin damtsen ka dana tsafi gami dana iya yakinka. Amma ka sani cewa mai laya ya kiyayi mai zamani. Gama fadin hakan keda wuya sai gaba dayan dakarun suka afkawa Sarki Amzad da nufin zu daddatsa shi. Cikin bakin zafin nama Sarki Amzad ya daka tsalle sama daga kan dokinsa ya kaucewa duk harin da suka kawo masa. Kawai yana saman ya fara gabzar dakarun da hannunsa da kafafunsa, duk wanda ya nausa sau daya walau a hannu ko a kafa saidai kaji karar ballewar kashinsa. Nanfa ihun mazaje ya cika dajin gaba daya. Babu abinda ya firgita Dakarun face ganin irin tsananin zafin naman sarki Amzad da yadda yake kaucewa dukkanin saran su da sukan su. Kuma a duk sa'adda ma dayansu ya sami nasarar saran jikinsa ko sukarsa saidai kawai yaji kara ta tashi tamkar karfe da karfe ne suka hadu. Saida aka shafe sa'a daya da rabi ana wannan bakin gumurzu ko kwarzanar jikin sarki Amzad ba'a yi ba. Kuma Babu alamar zai gaji kuma gashi sai kakkarya dakarun yake suna faduwa kasa suna koke koke da iface iface har ya zamana cewa ya bazar da kaso biyu a cikin kaso ukun dakarun. A lokacin ne dakarun suka firgita ainun bisa ganin irin mummunar barnar da sarki Amzad ya yiwa yan uwansu. Bisa dole suka fara ja da baya ya zamana cewa basu gudu ba kuma basu fasa yunkurin kai hari ba. Shi kuwa shugaban dakarun wanda ya kasance narkeken kato mai kirar mutanen farko mai takama da karfin damtse, iya yaki da karfin sihirin tsafi. Har izuwa wannan lokaci yana tsaye a gefe daya yana kallon duk abinda akeyi zuciyarsa sai tafarfasa take kamar zata kone. Koda yaga cewa dakarun sun fara firgita sai ya daka musu tsawa ya umarce su dasu ja da baya. Nan take kuwa dakarun suka ja da baya suka bar sarki Amzad da shugabansu a tsakiyar filin. Take shugaban dakarun yasa hannunsa guda ya yage rigar jikinsa yayi jifa da jta. Koda Sarki Amzad yayi arba da kirar jikin shugaban dakarun yaga kamar dutse aka cure ga tarin kwanji da jijiyoyi a jikin nasa sai zuciyarsa ta dan kada domin ya tabbatar da cewa kai wannan katon kasa ba wasa bane. Shugaban dakarun ya gyara tsayuwarsa kuma ya zare takubbansa guda biyu daga gadon bayansa ya tunkari inda Sarki Amzad ke tsaye da gudu yana kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa. Koda ganin haka sai shima Sarki Amzad ya zabura ya zare takobinsa kuma ya ruga da gudu ya tari shugaban dakarun suka ruguntsume da azababben yaki. Nanfa suka wanzu suna masu kaiwa junansu sara da suka cikin tsananin zafin nama, juriya da bajinta. Tunda Sarki Amzad yake gumurzu da manyan mazaje a filin daga bai taba haduwa da wani jarumi mai zafin nama da iya yaki ba kamar wannan kato. Domin kuwa nan take karfinsu yazo daya. Amma daya tuna da irin gwagwarmayar daya sha a rayuwarsa da irin nasarorin daya samu sai yaji wani sabon karfi da rashin tsoro sun shige shi. Kawai sai ya kara zage damtse suka cigaba da kaiwa juna mugayen hare hare cikin mugun nufi. Saida suka shafe sama da rabin sa'a dayansu bai sami nasarar komai ba. Kuma duk sa'adda takobinsu ta hadu saidai kaga tarwatsin wuta na tashi. Idan kuwa jikinsu suka sara saidai kaji karar haduwar karafa. Hakanne ya tabbatar wa da junansu cewar karfi yazo daya a komai don haka bisa dole kowannensu yaja da baya sukayi cirko cirko suna haki da kallon juna kamar zakaru. Su kansu dakarun dake wajen sun kura musu idanu kawai suna mamakin irin wannan jarumtaka ta Sarki Amzad. Shi kansa shugaban dakarun bai taba zaton cewa zai kasa kawar da Sarki Amzad ba a cikin kankanin lokaci saboda tun yana da shekara tara a duniya aka fara bashi horon yaki ana tsuma shi a cikin aTSUMIN TSAFI don kawai tanadin wannan rana da zaiyi gaba da gaba da Sarki Amzad ya sami nasarar hallakashi. Kamar yadda wannan barden mayaki keyin tunanin zuci haka shima Sarki Amzad ke ta zancen zucin yana mai cewa ashe akwai jarumi kamata haka a duniya ban sani ba. Kuma boka Kimbaru bai taba sanar dani ba. Koda Sarki Amzad yazo nan a cikin zancen zuciyarsa sai ya fusata ainun musamman daya tuna cewa yau ne ranar da za'a kawo masa amaryarsa a cikin wannan dare kuma gashi mutum daya jal yana neman ya bata masa lokaci. Kawai sai yayi jifa da takobinsa ya takarkare ya kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa irin wanda ke TARWATSA MAZA a FILIN DAGA. Koda ganin haka sai shima shugaban dakarun yayi jifa da takobinsa ya kwarara nasa ihun kai kace rurin zaki ne uban dawa. A tare duk su biyun suka rugo da gudu izuwa kan juna cikin mugun nufi. Koda ya rage saura baifi taku biyar ba su hadu sai kowannensu ya daka tsalle sama tamkar an cillo su daga cikin baka. Suna haduwa a saman sai shugaban dakarun ya kai wa Sarki Amzad kware da kansa da nufin ya doki fuskarsa. Cikin bakin zafin nama Sarki Amzad yayi wata irin katantanwa a saman ya makale jikinsa. Cikin kwarewa a iya gumurzu ya kaucewa harin sannan ya soke idon shugaban dakarun da farcen danyatsan sa. Take dan yatsan ya lume a cikin idon. Sarki Amzad yana zare hannun dan yatsan jini yayi feshi waje a lokacin da shugaban dakarun ya kurma uban ihu sakamakon tsananin zafi da zugin daya ji. Ya rikito kasa a dimauce yana mai dafe ramin idon nasa wanda ya gama tsiyayewa. Shi kuma Sarki Amzad saiya diro kawa a can gaba kadan ya juya yana mai kyalkyalewa da dariya bisa ganin nasarar da ya samu. Lokaci guda kuma saiya takarkare ya kwarara uban ihu sannan ya hade fuska ya dubi shugaban dakarun yace yakai wannan jarumi kayi sani cewa a duniya babu abinda na tsana sama da mutuwar jarumi na kwarai. Kaine jarumi na farko wanda na yaba da jarumtakarsa kuma har zuciyata tayi rawa akan tabbacin samun nasara akansa. Wannna nasara dana samu har na lalata maka idon ka guda daya ba wai tsagwaron karfin damtsena bane. Ba iya yaki na bane, kawai na fika kwarewa ne a iya gumurzu da kuma sanin wayo saboda na fika shekaru a duniya. Amma nan gaba idan shekarun ka suka karu zaka sami irin wannan kwarewa tawa. Ina mai shawartarka da kada ka cigaba da yakata saboda in ka matsa mini zan iya rabaka da hannunka ko kafarka guda. Ka koma gida ka cigaba da baiwa kanka horo idan muna raye nan gaba zaka iya DAUKAR FANSA a kaina. Idan kuma na mutu tunda na fara tsufa saidai ka dauki fansa akan dana ko jikana. Koda Sarki Amzad ya gama fadin hakan saiya nufi inda dokinsa yake ya kama ya hau. A daidai wannan lokaci ne hawayen takaici suka zubowa shugaban dakarun ya dubi Sarki Amzad yace yau shekara ashirin kenan mahaifina yana bani horon yaki kuma yana tsumani a cikin tsumin tsafi domin na sami nasarar kashe ka Amma kuma gashi na kasa. Koda kin wannan batu sai Sarki Amzad ya waigo da sauri ya kurawa shugaban dakarun idanu sannan ya gyada kai cikin MURMUSHIN MUGUNTA yace idan ka koma gida ka gayawa mahaifinka Sarki Barmas na birnin Kisra cewa har ya mutu ba zaiga faduwa ta ba saidai abayan ransa. Ka gaya masa cewa ya cire batun daukar fansa a kaina domin na gaba yayi gaba na baya sai labari. Koda gama fadin hakan sai sarki Amzad ya zaburi dokinsa da gudu ya tasamma hanyar da zata kaishi gidan boka Kimbaru. Shi kuwa Ihham Bin Barmas saiya durkushe a kasa bisa guiwoyinsa yana mai kurma ihu kuma ya fashe da kukan bakin ciki. Cikin tafiyar sa'a daya da rabi Sarki Amzad ya iso gidan boka Kimbaru yana isowa kofar gidan wanda ke tsakiyar daji kuma an kawata shi ainun tamkar ba a cikin wannan duniya ba. Sai yaja linzamin dokinsa ya tsaya cak sannan ya sauko daga kan dokin nasa ya daure shi a jikin wata bishiya. Kai tsaye ya tunkari kofar gidan duk da cewa a kulle take kuma babu mai gadi a bakin kofar kuma babu alamar wani mariki a jikin kofar. Kawai sai kofar ta bude kanta sabanin da can idan yazo saidai ya dafa kofar da tafin hannunsa sannan ta bude. Kofofi tara ne wadanda sai mutum ya wuce ya cikinsu sannan zai isa fadar Boka Kimbaru Amma bisa mamaki wannan karon sai Sarki Amzad yaga kofofin sun karu da guda uku. Kai hatta tsaron dake cikin gidan ya sauya domin ya ninka na da sau uku. Inda ya saba ganin runduna ta aljanu kimanin su dubu yanzu sai yaga sun Kai dubu goma. Hadimai, bayi da borori da kuyangi na gidan ma sun ninka na da sau goma. Haka dai Sarki Amzad ya cigaba da wucewa ta cikin kofofin tamkar cikin gidansa yake shiga. Kuma fuskarsa a murtuke take babu alamar annuri har ya iso fadar boka Kimbaru. Anan ne fa yasha jinin jikinsa kuma ya dan tsorata domin bai taba ganin irin dakarun tsaron da aka da aka zuba a wajen ba irinsu. Dakaru ne na musamman daga jinsin mutane, ajanu, dodanni da dabbobi masu mutukar kwarjini daban tsoro wanda da zarar mutum yayi arba dasu zai iya aiyanawa a ransa cewar zasu iya tashin duniya kaf a cikin kankanin lokaci. Koda ganin Sarki Amzad sai boka Kimbaru ya taso daga kan KARAGAR MULKInsa cikin mutukar farin ciki kamar wanda aka aikowa da albishir na mallakar komai da kowa. Koda Sarki Amzad yaga boka Kimbaru ya durfafo shi a cikin wannan siga sai shima ya saki fuskarsa ta fadada da murmushi suka rungume juna. Nan take boka Kimbaru yaja Sarki Amzad izuwa kan karagar mulkinsa suka zauna tare. Zamansu keda wuya aka kawowa Sarki Amzad kayan shaye shaye iri iri na alfarma. Ba tare da shakkar komai ba Sarki Amzad ya kama shan abinda ransa yake so tamkar a dakin matarsa yake har saida yaji ya wadatu. A daidai wannan lokaci ne boka Kimbaru ya dubeshi cikin nutsuwa a lokacin da idanunsa suka ciko da kwalla yace yakai tsohon aminina kayi sani cewa zamani ya kawo sabani da rashin fahimta a tsakanin mu wanda indai bamu dauki mataki ba hakan na iya warware tsohuwar alaka da zumuncin da iyayenmu suka kulla na tsawon shekaru da dama. Ni bani da wani buri wanda yafi na barwa dana hanyar da manyan kudade zasu rinka shigo masa. Kudaden da har yayansa da jikokinsa ma zasu amfana. Kuma zuri'ar sa ta cigaba da amfana har abada.kudin da aka tara da neman kasuwanci basa yin irin wannan dadewa a duniya. Ka bar ganin tarin dukiyar dana tara a yanzu kayi zaton zata cika min wannan buri. Ko kadan ba zatayi ba. Bisa wannan dalili ne na kirkiri birnin Baitul Najwas wanda a halin yanzu duk duniya kaf babu wani birni wanda ya fishi tarin masu arziki da kuma hada hada ta kudi tsabarsu. Ka sani cewa duk manyan biranan duniya a halin yanzu suna zaune a cikin birnin Baitul Najwas kuma duk dukiyarsa tana cikin birnin suna biyana haraji mai tsananin yawan gaske saboda ina tsare lafiyarsu, rayukansu da kuma dukiyarsu. Ni bazan yake ka ba kuma ba za'a hada kai dani ba a yake ka ba. Amma ka sani cewa makiyanka abokan huldar kasuwancina ne. Kuma ko maganar ka basu isa su zo min da ita ba. Saboda sun san irin alakar dake tsakaninmu tun muna yara ta amana.Tun iyaye da kakanni yanzu kai a iya tunaninka wane hukunci ka dauka don ganin mun cigaba da alaka ta zumunci har abada. Inason ka gaya mini duk abinda yake cikin ranka kada ka boye mini komai. Koda Boka Kimbaru yazo nan a jawabinsa sai hawayen takaici ya zubo wa sarki Amzad yace yakai babban Abokina kuma aminina me yasa ka zabi dukiya akan zumunci? Ka tuna cewa iyayenka da kakanninka basu mutu da irin wannan buri ba. Sun mutu akan cika burinsu na neman suna da daukaka. A zatona iya hakan ya ishi mutum ma rayuwa. Koda jin wannan batu sai Boka Kimbaru yayi murmushi cikin yake sannan yac yakai abokina kayi sani cewa buri yana tafiya ne da zamani. A can shekarun baya zamanin iyayenmu da kakanninmu dukiya ba komai bace.mai dukiya bai damu da ita ba, burinsa ma ya rabar da ita ga masu bukata Amma anan gaba zamanin da zaizo ma idan mutum bashi da kudi to dashi da takardar banza duk daya ne. Bisa wannan dalili ne na yanke shawarar na kafawa dana abinda har abada bazai yi rashi ba, tsafi ko fatauci. Abune wanda zai iya rushewa Amma kadara mai kawo kudi tana dadewa. Bisa wannan bincike danayi anan gaba wani zamani da zai zo mutum ba zai sami manyan kudade ba dole sai ya kaucewa gaskiya da amana. Bisa wannan dalili ne na baiwa barayi da marasa gaskiya dama ta zama lafiya a cikin birnina na Baitul Najwas kuma na kare su daga harin kowa har da kai kanka.ina mai shawartarka da kaje ka cigaba da tsara rayuwarka ta hanyar daka dauka kamar yadda nima na tsara tawa ta hanyar da naga ta dace. Kada muyi gaba da juna domin hakan bazai haifar da komai ba face lalata biyu. Daya bata gyaruwa. Duk abinda Boka Buda na birnin Sin ya gaya maka gaskiya ne kuma kayi amfani da shawarar daya baka. Ni dai na rantse da Gemun ubana har abada ba za'a hada kai dani ba a cutar dakai.kaima kada ka yarda da a hada kai dakai wajen cutar dani. Koda bata shiri na. Yanzu idan ka koma gida ka kirawo Danka Yarima Dalzuk ka sanar dashi komai kamar yadda kayi niyya. Kuma kada kayi yunkurin cutar da amaryar ka koda kuwa ka kamata da laifin cin amanarka. Domin itace uwar magajinka. Idan ka kashe ta tamkar ka rushe mulkin zuri'ar ku ne. Ka sani cewa ni da kai duk kwanaki ne kadai suka rage mana a wannan duniya. Don haka duk yadda za muyi muyi iya kokarinmu muga bayan mu tayi kyau. Abu na karshe wanda baka sani ba shine zan sanar dakai yanzu. Daga kanka ba za'a sake yin Namijin sarki ba a zuri'ar ku. Matane zasu cigaba da hawa karagar mulki kuma kowacce Sarauniya tana kan karagar mulkin za'a kashe ta saidai yar uwarta ta karbeta. Makiyanku ne zasu rinka kashe su kuma babu Sarauniyar da zata iya yin dogon zamani kamar yadda kai ka shekara saba'in akan KARAGAR MULKI. Babu Sarauniyar da zata haura shekara sama da goma akan KARAGAR MULKI. Wannan wani bakin asiri ne wanda makiyanku zasu binne akan wani boyayyen daji dake kasar Hindu.babu mai iya tono wannan sihiri ya lalata shi face mutumin dayafi kowa sa'a da tsawon rai a duniya. Wannan mutumin kuwa bazai bayyana ba sai nan da cikar shekaru dari uku masu zuwa kuma zai kasance sarki na wata babbar kasa a wata nahiyar daban. Lokacin da Boka Kimbaru yazo nan a jawabinsa sai sarki Amzad ya rungumeshi duk su biyun suka fashe da kuka. Da kyar suka saki junansu sukayi bankwana. Daga wannan rana basu sake saduwa ba har kwanansu ya sadu da ajalinsa.
Sarki Amzad ya zauna da amaryar sa kuma ta haife masa kyakkyawar 'ya wacce Yarima Dalzuk yaso fiye da komai a duniya. Kuma shi ya raineta yatsare lafiyar ta da rayuwarta har ta girma. Wannan yarinya tana da shekara tara a duniya mahaifiyarta ta zubawa sarki Amzad guba a lemo yasha. Sanadin ajalinsa kenan. Kuma su shugaba Shamshaki ne suka tilasta mata ta zuba mishi guba in ba haka ba zasu kashe iyayenta da yan uwanta. Bakin cikin mutuwar sarki Amzad ne ya zamo sanadin ajalin Yarima Dalzuk. Wannan yarinya yar amarya Malina itace ta hau karagar MULKI, Amma tana shekara goma kan KARAGAR MULKIn itama ta mutu yarta ta gaje ta. Yau kusan shekaru dari uku kenan haka wannan abu ke faruwa, wato ana kashe kowace sarauniya da zarar ta cika shekara goma akan KARAGAR MULKI saidai yarta ta gaje ta. Kuma babu Sarauniyar data taba haihuwar 'da namiji har yazo kan mahaifiyata. A yanzu saura shekara biyu kacal mahaifiyata ta cika shekara goma akan KARAGAR MULKI. Bisa wannna dalili ne na bazama a duniya ina ta neman ilmin tsafi a wajen bokaye domin na gano sarkin da zai taimake ni ya karya wannan bakin sihiri da aka yiwa mutanen gidan mu domin na tserar da rayuwar mahaifiyata. Da kyar da sidin goshi na gano cewa ba wani bane mutumin da yafi kowane mutum sa'a da nisan kwana a duniya face kai. Kai sarki Kamzal.A cikin bokayen dana ziyarta ne wani daga cikin su ya gaya mini cewa duk ranar da na ceto rayuwar mutumin da aka jefa a teku bayan an daddatsa shi to shine wanda nake nema. Har na shiga cikin wannan teku wacce aka jefa ka ban taba sanin cewa kai zan gani ba. Yakai wannan sarki, wannan shine tarihin rayuwata. A takaice ina fatan zaka cika alkawarin dake tsakanin mu ka taimakeni mu tafi izuwa birnin Hindu domin na gano dajin da aka binne wannan sihiri saboda na ceto rayuwata data mahaifiyata. Lokacin da Jaruma tazo nan a labarinta sai hawaye ya zubowa sarki Kamzal saboda tsananin tausayin ta daya kama shi. Kawai sai ya janyo Jaruma izuwa kan kirjinsa ya Rungumeta yana mai cewa kamar yadda kika taimake ni kika tserar da rayuwata da lafiyata har na zama sarki, nima nai miki alkawarin nan da cikar sati daya jal zamu shirya mu tafi izuwa birnin Hindu domin gano dajin da aka binne wannan bakin sihirin da akayiwa zuri'ar ku. Amma inada tambaya guda daya. Shin bakya zaton cewa a cikin zuri'ar boka Kimbaru babu wanda zai iya taimakon mu akan wannan al'amari.? Domin mu gano inda wannan daji yake a saukake kuma mu iya lalata wannan bakin sihirin. Kiyi sani cewa a halin yanzu na kamu da tsananin SON KI kuma irin son da in babu ke nima bazan iya rayuwa ba a doron kasa. Matsala ta biyu daga Bangarena. Ita matar ubana da Dan uwana wanda mukayi takarar karagar mulki da kuma dan uwana wanda akayi masa makirci aka kore shi daga garin nan. Wadannan mutane uku ba zasu taba daina kiyayya dani ba face sunga karshe na. Yanzu idan mu kayi wannan tafiya a hannun wa zan bar karagata bisa amana yadda zan dawo na karbeta salin alin cikin kwanciyar hankali. Lokacin da sarki Kamzal ya yiwa Jaruma wannan tambaya sai hankalinta ya DUGUNZUMA ainun ta janye jikinta daga cikin nasa tayi shiru tana tunani shima ya fada dogon tunani. Saida suka jima a cikin wannan hali sannan Jaruma ta dago da kai ta dube ta ce. Tabbas kazo mini da babban al'amari Amma zanyi tunani a cikin daren nan. Lallai kafin gari ya waye zan samo mafita.

WATA MAFITA CE JARUMA ZATA SAMO KAFIN GARI YA WAYE?

WACE IRIN BAKAR WAHALA SU SARKI KAMZAL ZASU SHA A CIKIN WANNAN GAGARUMAR TAFIYA DA ZASU YI IZUWA BIRNIN HINDU DOMIN GANO DAJIN DA AKA BINNE WANNAN SIHIRI?

WANE IRIN MATAKI ABOKAN GABAR SARKI KAMZAL ZASU DAUKA BAYAN TAFIYARSA IZUWA BIRNIN HINDU DOMIN GANIN SUN MALLAKI KARAGAR MULKIN SA?
KUMA WANE IRIN DAUKI BA DADDADI ZA'A YI A TSAKANIN SU?

WAI KUWA INA YARIMA IMRAN WANDA AKA KORA DAGA BIRNIN?

Mu hadu a littafi na Biyar don jin cigaban wannan kasaitaccen labari.

Abubakar Haleefah Physicist.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya





Please Login or Register in order to submit comment