Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikinsa kuma Hashlar
na tsaye akansa sai suka rabu da
Humairu suka rugo da gudu Izuwa
kan Hashlar.
Kafin su iso tuni Hashlar ya zare
takobin daga cikin dan uwansu ya
fadi kasa matacce,
Kawai sai ya taresu suka fara sabon
gurmuzu, a wannan Lokaci ne
Humairu ya kyalla ido ya hango irin
mugun kisan wulakancin da aka
yiwa yan uwansu, shima sai ya
fashe da kuka.
Cikin tsananin fusata ya mike tsaye
zumbur duk da cewa akwai sara a
jikinsa guda uku masu zubarda jini,
kuma jini na yoyo a hancinsa da
bakinsa, kawai sai ya dauki
takobinsa ya ruga da ya kaiwa
Hashlar dauki, wato ya tayashi yaki
da samudawan ya zamana cewa
biyu da biyu ake yakin.
Hakika sau tari tsananin bakin ciki
da asarar masoya tana sa mutum
ya fusata ya sami karfin da shi
kansa bai san yanada irinsa ba.
Lokacin da aka fara wannan sabon
bakin gurmuzu tsakanin Humairu,
Hashlar da wadanan samudawan
biyu sai labari yasha banbam
domin abin mamaki ne ya faru...
Duk da cewar ko a zahiri mutum ya
kalli gurmuzun yasan cewa
samudawan sun fisu karfi, girma da
zafin nama amma sai gashi su
Humairu sun zame musu alakakai
sun kasa kaisu kasa.
Babu ma wanda yafi bada mamaki
face Hashlar wanda ya zama
nakasasshe mai hannu daya.
Da hannu daya ya cigaba da amfani
da wannnan katuwar takobin suka
yi ta taki da dayan basamuden.
Shi kuwa Humairu da tasa takobin
ya tari abokin gwamin nasa sai dai
duk sa'adda ya sami nasarar sarar
jikin basamuden sai yaga baya yi
masa wawan raunin kirki saboda
takobin tasa ta gama dukushewa.
Duk sa'adda samudawan suka
kawo ma su Humairu sara suka
goce duk abinda takobinsu ta samu
walau bishiya ko dutse sai dai kaga
abin ya rabe gida biyu tamkar ansa
wuka an raba tufa.
Sai da aka shafe rabin sa'a ana ana
wannan gurmuzu babban abin da
ya dugunzuma hankalin Hashlar
shine duk da cewa yana saran
abokin gwamin nasa yana yi masa
rauni kuma jini nata zuba a jikinsa
amma yaki faduwa kasa, koyaushe
ma kamar kara kuzari yake saboda
tsananin fushi da taurin zuciya bisa
ganin an kashe musu dan uwan
guda daya.
A bangaren Humairu da nasa
abokin yakin ma abinda ke faruwa
kenan, ana cikin haka ne abokin
fadan Humairu ya doki kirjin
Humairu da kafa.
Saboda karfin dukan sai da
Humairu yai baya a sama da gudu
tamkar an cillashi daga cikin baka
sannnan ya fado akan gawarwakin
yan uwansu su Kaimur a matukar
galabaice.
Da kyar ya yunkura ya mike zaune,
koda ya ga gawarwakin su Kaimur
wadanda akayi gunduwa-gunduwa
da sassan jikinsu, kai dabam,
hannaye da kafafu dabam dabam
ga jini male male yayi wanka a
cikinsa sai ya kwala ihu yai jifa da
takobinsa kuma ya mike tsaye
zumbur ya ruga da gudu Izuwa kan
abokin gwamin nasa.
Ai kuwa shima abokin gwamin
nasa yana ganin haka sai ya yarda
tasa takobin ya rugo da gudu
Izuwa gareshi yana wani irin ihu
wanda ka iya firgita mazaje dubu
daruruwa a filin yaki su dimauce.
Burin wannan basamuden shine su
hada kirji shida Humairu domin ya
tabbatar da cewa idan hakan ta
faru sai kasusuwan kirjin Humairu
sun kakkarye.
Saura kiris su hadu kuwa sai
Humairu yai tsalle a sama cikin
shammace ya kama wuyan
basamuden da kafafunsa biyu, a
saman ya murde masa wuyan, take
wuyan ya karye ya bayar da sautin
karyewar kakakass!
Nan take basamuden ya sulale kasa
matacce karar karyewar wuyan
tasa ce ta janyo hankalin dan
uwansa ya juyo da baya a Lokacin
da shima ya sami nasarar damkar
wuyan Humairu ya daga shi sama
da hannu daya ya shakeshi , sai
gashi kafafun Humairu suna wutsil
wutsil a sama kamar an shanya
busasshen tsumma akan igiya iska
na walagigi dashi, Idanun Humairu
kuwa suka yi bulu-bulu kamar zasu
fado kasa harma ya fara kakarin
mutuwa,
Koda wannan basamuden yaga dan
uwansa ya fadi kasa matacce sai yai
jifa da Humairu tamkar ya yarda
jikakken tsumma sannnan ya
kurma uban ihu ya daga takobinsa
sama ya ruga da gudun tsiya a
matukar fusace Izuwa kan Hashlar,
Shi kansa Hashlar a wannan Lokaci
ya karaya domin bai ma san abinda
zai yi ya kare kansa ba, tunda gashi
babu makami a hannunsa kuma
kafin ya ruga inda ya yarda
takobinsa tuni basamuden ya
cimmasa don haka sai ya tsaya cak
yana tunanin dabarar da zai yi.
Ya rage saura taku daya jal
basamuden ya cimmasa sai kawai
yaga kibiya ta faso ta cikin kwayar
Idon basamuden ya tsaya cak! A
gabansa kamar an binne ice a cikin
kasa.
Take basamuden ya fadi kasa a
sandare ya danneshi suka fadi kasa
tare da kyar Hashlar yasa hannunsa
mai kyau ya ture gawar
basamuden daga kansa sannnan ya
hango cewa ashe Humairu ne ya
dauko kwari da bakan marigayi
ILsam ya harbo basamuden.
Humairu da Hashlar suka tsaya cak
a nesa da juna suna kallon
gawarwakin yan uwansu,
Nan take suka fara zubarda
hawaye, daga can kuma sai suka
rugo da gudu suka rungume juna
sannnan suka fashe da
matsanancin kuka.
Komai rashin imanin mutum idan
dubesu a wannan Lokaci dole ne
yaji tausayinsu musamman idan
yayi la,akari da babbar asarar da
suka yi ta abokansu mutum biyar
wadanda suka shaku da su ainun
tun kurciya kawo Izuwa girma.
Bugu da kari gashi sun rasa
iyayensu maza kuma an rabasu da
iyayensu mata da kuma masoyansu
wato yan matan da suke da burin
su aura. DUGUNZUMA!!!
LITTAFI NA DAYA
PART 3
LITTAFIN YAKI
*******
REAL RAYYANU SAEED
.
Komai rashin imanin mutum idan ya dubesu a
wannan Lokaci dole ne yaji tausayinsu
musamman idan yayi la'akari da babbar asarar
da suka yi ta abokansu mutum biyar wadanda
suka shaku dasu ainun tun kuruciya kawo Izuwa
girma.
Bugu da kari gashi sun rasa iyayensu maza kuma
an rabasu da iyayensu mata da kuma masoyansu
wato yan matan da suke da burin su aura.
Cikin gaggawa Humairu ya cire rigar jikinsa ya
nannade dungulmin hannun Hashlar domin har
yanzu bai daina zubarda jini ba sannnan suka
mike da kyar suka tattaro sassan jikin abokansu
suna ta kuka.
Da kyar suka sami damar haka rami suka binne
sassan jikin abokan nasu suka sa kabarin a gaba
suka ci gaba da kuka har Izuwa tsawon sa'oi
Bayan sun yi kuka mai yawa har sun gaji sai
suka kurawa junansu idanu.
Humairu ya dubi Hashlar yace, " ya kai abokina
kuma dan uwana gudu daya wanda ya rage mini
a duniya yanzu dai kaga irin bala'in da ya same
mu mun rasa komai kuma mun rasa kowa yanzu
menene abinda kake ganin ya kamacemu?"
Koda jin wannnan tambaya sai hawaye sake
zubowa Hashlar yace, " ya kai dan uwana ni a
ganina rayuwa a duniya bata da wani amfani
muddin babu masoyi
Ka sani cewa babu wani abu da zai iya gusar
mana da bakin ciki dake cikin zukatanmu bisa
abinda muka rasa.
Saboda haka ni ina ganin cewa abu mafi sauki a
garemu shine mu kashe kanmu kawai domin mu
tafi Izuwa ga inda masoyanmu suka tafi domin
babu wani jin dadi da zamu samu anan gaba
wanda zamu ji dadinsa.
Wanne dadi ne zai dawo mana da abokanmu?"
Wane dadi ne zai dawo mana da iyayenmu da
kuma matan da muka kamu da tsananin
soyayyarsu?"
Wanne dadi ne zai dawo mana da ainihin
kauyenmu na Garul Aswar da mutanen cikinsa? "
Dukkan burinmu ya ruguje kuma dukkan farin
cikinmu ya rushe."
Sa'adda Humairu yaji wannan batu sai yaji ya
kamu da tsananin bakin ciki fiye da koyaushe don
haka bai san sa'adda ya sake fashewa da
matsanancin kuka ba.
Ba zato ba tsammani sai yaga Hashlar ya zaro
wata karamar wuka a kugunsa ya daga sama zai
kirba a cikinsa cikin bakin zafin nama Humairu
yai wuf ya rike hannunsa yace,
"Haba dan uwana ashe kamanta cewa har yanzu
iyayenmu mata da yan matanmu na nan a raye a
hannun wadanan samudawan azalumai?"
Koda jin wannnan batu sai jikin Hashlar yayi
sanyi yai jifa da wukar hannun nasa ya sake
rungume Humairu, suka ci gaba da kuka tare.
Tsawon yan dakiku suna manne da juna sannnan
Hashlar ya janye jikinsa daga cikin na Humairu
ya dubeshi yace, ka sani cewa ni da kai bamu isa
muje mu tunkari wadanan mutane ba.
Har mu iya kwato iyayenmu da yan matanmu,
tunda gashi da kyar da sidin goshi muka kashe
irin su mutum uku, idan har kuwa baza mu iya
kwato su ba menene amfanin rayuwarmu a doron
kasa?"
Da jin wannnan tambaya sai Humairu ya jinjina
kai yace, hakika ni da kai ba zamu iya wannan
aiki ba.amma ka tuna cewa idan har da rai da
akwai rabo.
Har abada hikima da basira basu karewa ga dan
adam.
Ni a ganina zamu iya karbo jama'armu amma
bata hanyar tarar wadanan mutane gaba da gaba
ba.
Kodai mu nemi taimakon wadansu al'ummar daga
can wata nahiyar dabam ko kuma mubi sawunsu
ba tare da sun sani ba har musan dabarar da
mukayi muka sato jama'ar tamu a cikinsu.
Wannnan shine kadai abinda zamu iya yi a yanzu.
Lokacin da Hashlar yaji wannan shawara da
Humairu ya kawo sai yai shiru yana nazarinta a
cikin zuciyarsa har Izuwa lokaci mai dan tsawo.
Daga can sai ya dago kai ya dubeshi yace, ka
bani kwana biyu nayi tunani akan wannnan
shawara da ka kawo.
Amma yanxu ya zama wajibi mu tashi mubar
wannan wuri domin idan yan uwan wadanan
samudawan suka ji shiru, dole ne su aiko
wadansu jama'ar tasu, suzo suga abinda ya faru.
Humairu ya gyada kai yace, tabbas maganarka
gaskiya ce, amma a yanzu ina yakama mu doso?"
Hashlar yace, ai babu inda ya kamata muje face
babban Birninmu na LURHAJ domin mu sanarda
sarki ARYAN abinda ya faru a kauyenmu saboda
asan matakin da za'a dauka tun karfinsa
wadanan mutanen su isa can.
Ni ina ganin cewa ma acan ya kamata mu tsaya
a yaki wadanan mutane tare damu domin mu
dauki fansa akansu.
Koda jin wannnan batu sai Humairu ya kada kai
yace, " naga alama kana wasa da Al'amarin
wadanan bakin samudawan da baro a wannan
nahiya tamu.
Shin ka manta ne da bayanin da wannnan mutum
yayi mana a bakin kogi?
Cewa yayi fa mutanen yawansu ya wuce kima bai
san adadinsu ba.
Kana ganin yadda uku daga cikinsu suka kashe
mana abokanmu biyar muma da kyar muka tsira
daga hannunsu.
Ina mai tabbatar maka da cewa koda basu fi su
dubu biyu ba zasu iya hallaka gaba dayan
dakarun sarki ARYAN.
Batun ayi fito na fito da wadanan mutane bai
taso ba.
Kuma akwai bukatar muga adadinsu da idanunmu
sai dai a yanzu abu mafi sauki shine mu ruga
Izuwa birnin LURHAJ mu sanarda sarki ARYAN
abinda ake ciki.
Yanzu dai tunda wadanan abokan gaba gabas
suka nufa mu sai mubi ta kudu muyi shatale- tale
mu rigasu zuwa birnin LURHAJ.
Koda jin wannnan batu sai Hashlar ya gyada kai
yace, tabbas na yarda da wannnan shawara taka
dari bisa dari.
Ba tare da wani bata lokaci ba kuwa suka zauna
Humairu Humairu ya kwance raunin Hashlar wato
dungulmin hannunsa ya wankeshi da ruwa
sannnan ya debo garin magani ya barbada
akansa, sai jini ya tsaya cak ya daina diga.
Cikin sauri suka kama dawakansu suka hau suka
zaburesu suka nufi bangaren kudu suna waigen
kabarin da suka binne abokansu suna zubda
hawaye.
* * *
A can bangaren tawagar wadanan samudawan
mutane kuwa, wadanda adadinnsu ya haura
miliyan uku da dubu dari hudu,
sun ci gaba da tafiya ne basu yada zango ba sai
bayan sa'a biyar sa'adda yammaci yayi sossai
sannnan sarkinsu wani mummunan garjejen kato
wanda ake kira LABARUSA ya tsaida giwarsa ta
tsaya cak! Sannnan ya daga hannu sama yana
mai bada umurnin kowa ya tsaya.
Ai kuwa nan take kowa ya tsaya, Dakaru suka
sauko kan giwayensu.
Dama fursunonin da aka kamo an daure
kafafunsu da hannayensu da sarkoki, babu yadda
dayansu zai iya guduwa kuma acikin wani katon
keji aka durasu wanda akayi masa tayoyi na karfe
guda Dari da Ashirin a kasansa, giwayene suke
jan wannan keji ana tafiya dashi.
Koda sarki ya lura da cewa wadanan fursunoni da
aka kamo sun galabaita ainun kuma yunwa da
kishirwa sun addabesu sai ya bushe da dariyar
mugunta, nan take ya dubi badakare wanda shine
Sarkin yakinsa ana kiransa da suna GARBUZA
yace dashi, A bude wadanan fursunoni a kaisu
bakin waccan koramar su sha ruwa a basu abinci
suci domin Banason daya daga cikinsu ya mutu
kasan irin aikin da nake son suyi min nan gaba.
Nan take garbuza ya bada umurni aka bude
wannan katon keji aka rinka fito da fursunonin
ciki wadanda dukkaninsu mata ne, matasa da
tsofaffi sai kuma kananan yara.
Duk wanda ka kalla a cikinsu sai kaga yana
zubarda hawaye saboda tunanin daginsa da ys
rasa.
Nan dai aka tusa Izuwa bakin wannan korama
wanda duk yai gardama sai a zabga masa wata
katuwar bulala mai fasa fatar jiki don haka bisa
dole suka bi umurni.
Daga cikin wadanan fursunoni akwai iyayen sh
jarumi Humairu da kuma yan matansu guda
bakwai wadanda zasu Aura.
Wadanan yan matan bakwai duk sun kasance
kyawawan gaske amma daya daga cikinsu ta fita
zakka domin duk ta fisu kyau nesa ba kusa ba
kuma ana kiranta sa suna LAILA.
Laila itace budurwа Humairu, mai biye ta a kyau
itace HULAIZA itama kuma budurwа Hashlar ce
A koyaushe wadanan yan mstan bakwai suna tare
da juna basu rabuwa kamar yadda samarinsu
suka kasance suma kawayen juna ne tun
kuruciya.
Lokacin da aka kai su Laila bakin korama sai
suka jeru su bakwan suka tsugunna suna shan
ruwan, a wannan Lokaci ne huzaila ta dubi laila
Lokacin da idanunta suka ciko da kwalla tace,
"ya ke kawata ki sani cewa ina cikin alamun
fargaba da tashin hankali domin inaji a jikina
cewar wadanan dakaru uku da aka tura su koma
can kauyenmu lallai sun sadu da masoyanmu sun
kashesu saboda haka ni yanzu banga amfanin
rayuwata ba muddin babu masoyina Hashlar.
*****naku Smart Rayyanu DUGUNZUMA!!!
LITTAFI NA DAYA
PART 4
LITTAFIN YAKI
******
Lokacin da aka kai su Laila bakin
korama sai suka jeru su bakwan
suka tsugunna suna shan ruwan, a
wannan Lokaci ne huzaila ta
dubi laila Lokacin da idanunta suka
ciko da kwalla tace,
"ya ke kawata ki sani cewa ina cikin
alamun fargaba da tashin
hankali domin inaji a jikina cewar
wadanan dakaru uku da aka tura
su koma can kauyenmu lallai sun
sadu da masoyanmu sun kashesu
saboda haka ni yanzu banga
amfanin rayuwata ba muddin babu
masoyina Hashlar.
Abinda na yanke hukunci shine zan
fada karkashin wannan korama na
kashe kaina.
Gama fadin Hakan keda wuya sai
hulaiza ta yunkura zata yi nutso
Izuwa cikin koramar. caraf! Sai laila
ta riketa tace, "saboda me zaki
hallaka kanki alhalin baki da
tabbacin cewa masoyinki ya mutu
"?
Ki tuna cewa dakarun da aka tura
su kashesu har yanzu fa basu dawo
ba, babu mamaki masoyanmu ne
suka sami nasara akansu.
Ni na sani cewa masoyanmu
mazaje ne wadanda mutuwarsu ba
karamin bala'i bane domin sun cika
jaruman gaske, koda kuwa zasu
mutu sai sunyi mummunan barna.
Ni ina ji a jikina cewar har yanzu
masoyina Humairu yana nan a raye
kuma komai rintsi da tsanani sai ya
biyo sawu ya cecemu ni da
mahaifiyarsa. Saboda me ke hulaiza
ba kya jin wannnan abu da nake
ji?"
Koda jin wannnan batu sai jikin
hulaiza yayi sanyi ta fasa kokarin
hallaka kanta, laila ta dubi dukkan
yan matan nan tace,Abin da nake
so da ku shine mu saurara Izuwa
wani lokaci tukunna domin mu
tabbatar da halin da masoyanmu
ke ciki.
Idan har mun tabbatar da cewa
suna nan a raye basu mutu ba to
muma zamuyi kokarin mu gudu. "
Cikin firgici hulaiza ta dubi laila
tace, "ta yaya kike zaton zamu iya
guduwa daga hannun wadanan
samudawan mutane?"
Ta yaya zamu iya kwance wannan
sarka dake daure da hannayenmu
da kafafunmu? "
Kafin hulaiza ta gama rufe bakinta
tuni an gabza mata naushi a fuska,
take ta kife a cikin koramar jini na
zuba ta hancinta da bakinta, cikin
sauri laila ta dago ta sama, ba wani
bane ya naushi hulaiza ba face sarki
labarusa.
Fuskarsa a murtuke ya dubi hulaiza
sannnan ya dubi laila a fusace yace,
na fahimci cewa kune masu hikima
da basira a cikin dukkanin
fursunonin nan kuma kuna
yunkurin guduwa.
To ku sani cewa duk wadda tayi
yunkurin guduwa a cikinku sai nayi
mata mugun wulakanci sannnan
nayi mata kissan gilla.
Koda gama fadin Hakan sai sarki
labarusa ya mike tsaye, har ya juya
zai tafi sai ya sake waigowa ya
dubesu gaba daya yace, " naji kuna
mafarkin cewa masoyanku suna
nan har yanzu a raye, ina tabbatar
maku da cewa dayansu baya
numfashi a doron kasa.
Zamu tsaya anan mu yada zango
domin mu jira dawowar dakaruna
uku dana tura su kashe masoyan
naku domin kuga kawunansu da
idanunku ".
Caraf! Sai laila ta tari numfashin
sarki labarusa ba tare da jin tsoro
ko fargabar komai ba tace, " nasan
ko su waye masoyanmu. Ina mai
tabbatar maka da cewa mutuwarsu
ba karamin aiki bane,
Idan kuwa har sun mutu tabbas
suma yaran naka sai sun mutu,
Kayi nazari yaran naka sun dade
basu dawo ba,
Menene ya hanasu dawowar? "
Ba komai bane face mutuwa?"
Koda jin wannnan batu sai sarki
labarusa ya fusata ainun, jikinsa ya
kama tsuma, wani irin zazzafan
gumi ya fara karyo masa.
Gaba daya fursunonin dake wajen
sai da suka firgita ainun.
Kai ba ma fursunonin ba hatta
sauran dakarun sarki labarusa sun
tsorata saboda sun san cewa duk
sa'adda labarusa yayi irin wannnan
fusata wanda ma bai san hawa ba
bare sauka sai kashin kaji ya
shafeshi.
Ita kuwa laila ko alamar razana
babu a tare da ita,
"kawai ma sai ta juyo ta fuskanci
sarki labarusa ta tsaya a gabansa
tamkar an ajiye kyanwa a gaban
kura, tace, idan maganata ta bata
maka rai ka kasheni ko ka huce
takaici amma ka sani cewa duk
ranar da masoyina yayi arba da kai
sunanka gawa.
Sa'adda laila tazo nan a zancenta
sai kawai akaji sarki labarusa ya
takarkare ya bushe da
mahaukaciyar dariya Al'amarin da
ya matukar baiwa kowa mamaki
kenan, daga can sai ya durkusa
kasa bisa guiwoyinsa yadda
tsawonsa yazo dai-dai dana laila ya
zamana cewa suna daf da juna har
tana jin hucin numfashinsa tamkar
gurnanin zaki yace, "ke yarinya kiyi
sani cewa a cikin duniуаr nan kaf
babu wani mahaluki mai karfin
damtsena da iya yakina in dai ya
kasance bil'adama.
Ta yaya kike tsammani cewa
masoyinki zai iya yi mini wani abu?
"
A rayuwata babu abinda na tsana
sama da zama babu abokin gaba.
Abinda zai hanani na kasheki yanzu
shine, ina son na kama masoyinki a
hannuna nayi masa kisan
wulakanci da karfin damtse a
gaban idanunki. "
Laila tayi murmushi tace, abinda ka
fadi dai-dai yake da mafarki, kuma
mafarkin da ba zai taba tabbata ba.
Kafin laila ta gama rufe bakinta tuni
Sarkin yaki garbuza ya maketa ta
fadi kasa sumammiya, kawai sai ya
zare takobinsa zai datsata gida
biyu caraf sai sai sarki labarusa ya
cafi hannunsa yace dashi, saboda
me kake son kasheta?"
..
A kwashe su gaba daya daga cikin
koramar nan a mayar dasu cikin
keji amma ita wannan marar kunya
a kaita cikin tantina a daureta.
Kai Sarkin yaki ka debi dakaru
hamsin ku juya da baya kuje
wannan gari da muka baro kuga
abinda ya faru tunda mun tura
mutanenmu su uku har yanzu basu
dawo ba "
Sarkin yaki ya risina yace an gama
ya shugabana.
Nan take aka tusa keyarsu hulaiza
Izuwa cikin kejin su aka kullesu ita
kuwa laila a sume wani badakare
ya kwanceta daga cikin sarka yan
uwanta ya sabata a kafadarsa ya
kaita tantin sarki labarusa ya
daureta a jikin dirka.
A wannan Lokaci babu abinda zai
baiwa mutum tausayi face ganin
yadda aka gwamutsa kananan
yara, wato fursunonin da aka kamo
a cikin keji wani kan wani, sai kuka
suke saboda matsuwa ga kuma
yunwa domin abinci da aka basu
suka ci basu koshi ba.
Da yawansu ma iyayensu mata ne
suka rinka jefa musu nasu abinci da
aka basu su suka hakura.
* * *
Al'amarin su Humairu da Hashlar
kuwa, Lokacin da suka kama hanya
suka durfafi birnin LURHAJ sai suka
yi ta falfala gudu kamar zasu tashi
sama.
Abinka da wadanda suka saba da
gudun, sai da suka shafe sa'a
bakwai cif suna gudu basu huta ba.
Ko kishirwa ce ta kamasu sai dai
kaga suna gudun suna daga battar
ruwa suna kwankwada.
Bayan cikar sa'a bakwai dinne suka
iso birnin ARYAN.
Da zuwansu kofar birnin suka sha
mamaki domin sun iske masu
gadin a zaune cikin farin ciki da
nishadi sun gaiyato wani makidi
daga cikin gari ya baje kolinsa har
wadansu karuwai su uku sunyi
shigar banza suna tika rawa su
kuwa masu gadin sai shan giya
suke suna ta kyalkyala dariya.
Koda masu gadin suka hango
mutum biyu a guje sun durfafo
birnin sai suka mike tsaye zumbur!
Shi makadin ya daina kidan,
karuwan suka kame.
Cikin hanzari masu gadin suka zare
makamansu suna jiran ko ta kwana
Koda su Humairu suka kara
matsowa kusa sai masu gadin suka
shaidasu, don haka sai suka mayar
da takubbansu cikin kufe.
Da karasowarsu sai shugaban masu
ya taresu yace, lale marhaban da
manyan ya'yan sarakunan farauta,
shin lafiya kuwa na ganku a
sukwane haka? "
Humairu ya budi a Lokacin da yake
faman haki yace, Babu lafiya, kowa
ya shigo ciki ku rufe kofa akwai
babbar masifa tafe!
Ba tare da gardamar komai ba
masu gadin suka bi wannan
umurni jikinsu na rawa.
Kai tsaye Sarkin kofa ya yiwa su
Humairu jagora Izuwa fadar sarki
ARYAN.
Fadace kasaitacciya wadda akayi
mata ado na gani da fada da kayan
alatu dangin su zinare, lu'u lu'u da
sauransu.
Girman fadar ya wuce karamin
misali sai abinda ido ya gani.
Sarki ARYAN saurayi ne matashi
kuma kyakkyawan gaske.
Sannnan ya kasance gawurtaccen
jarumi wanda bai san tsoro ba
kuma gwarzo ne mai dakawa maza
gumba a hannu.
Yana da wata kyakkyawar mace
guda daya mai tsananin kyau ana
kiranta da suna LUSHIRAT na dauke
da tsohon cikin haihuwa yau ko
gobe.
Tsananin farin ciki dake tare da
sarki ARYAN da matarsa lushirat a
halin yanxu bisa ganin tana daf da
samun haihuwa ya wuce misali
domin basu da wani buri a duniya
wanda yafi na ganin sun haifi
magajinsu.
Ba komai ne ya haddasa hakan ba
face ganin sun shekara goma sha
uku da yin aure ko batan wata
lushirat bata taba yiba.
Babu irin neman maganin da basu
yi ba kasa-kasa nahiya-nahiya
amma shiru sai a wannan shekara
ne a wata na biyu rana daya aka
wayi gari akaga lushirat ta tashi da
laulayin ciki.
Yanzu tsawon wata takwas kenan
da samun juna biyu amma dai-dai
da rana daya ko dakika daya sarki
ARYAN bai yarda ya rabu da
lushirat ba saboda farin ciki da
kansa yake kula da lafiyarta kuma
ko ciwon kai yaji ta ambata sai ya
tara dukkan likitocin garin a kanta.
Yauma kamar kullum sarki ARYAN
na zaune a fadarsa bisa karagar
mulki, gimbiya lushirat na zaune a
damansa ya rike hannunta suna
duban juna cikin murmushi.
Makada da mawaka suna debe
musu kewa.
A wannan Lokaci fadar ta cika makil
ga fadawa da sauran mutanen gari
har da ma baki daga ketaren
kauyuka da birane saboda rana ce
ta kasuwar birnin.
Kwatsam! Sai akaji an busa algaita
alamar cewa baki sun shigo fada.
Nan take jama'a suka dare suka
samar da hanya a tsakiyar fadar
kowa ya juyo ya dubi kofar
shigowa kuma akayi tsit kamar
mutuwa ta gifta.
Sarkin kofa ne tare da Humairu da
Hashlar suka shigo.
Koda hangosu sai sarki ARYAN ya
mike tsaye ya sauko daga kan
karagarsa ta mulki ya taho garesu,
Al'amarin da ya baiwa kowa
mamaki kenan domin ba'a taba
ganin sarki ARYAN ya sauko daga
kan karagar mulkinsa ba domin ya
tarbi wani bako ba,
Komai muhimmancinsa saboda izzа
da jin kai sakamakon girman
kasarsa,karfin mulki da dimbin
dukiyar da ya mallaka.
Abinda ya kara daurewa mutane
kai shine, bakin ma da sukazo ba
wadansu masu muhimmanci bane,
kauyawa ne kuma mafarauta
wadanda basa zuwa fada sai sau
daya a kowanne wata domin su
kawowa sarki kyautar abubuwan
gwaninta da suka farauto a daji
don nuna jarumtakarsu.
Yanzu gashi mafarauta sunzo a
farkon wata kuma su bakwai ne
suka saba zuwa amma yanzu su
biyu ne jal.
Su kansu su Humairu sunyi matukar
mamaki da suka ga sarki ARYAN ya
sauko daga kan karagarsa ya
tarbesu da kansa.
Cikin hanzari sarki ARYAN ya riski su
Humairu ya kama hannun Humairu
fuskarsa cike da annuri tamkar
wanda yaga dan uwansa na jini
wanda suka dade basu sadu ba.
Kawai sai ya rungume Humairu
yayi masa rada a kunne yace, duk
sakon da kazo dashi kar ka fadeshi
anan fada sai mun Kebe."
Koda gama fadin Hakan sai sarki ya
kama hannun Humairu dana
Hashlar ya jasu Izuwa can inda
karagar mulki take.
Maimakon su zauna sai ya dubi
fadawansa yace, zanje na gana da
bakina don haka na sallami kowa.
Nan take yan majalisarsa suka mike
tsaye suka fara fita daga fadar
kowannensu yana mamakin dalilin
da yasa sarki ya tashi fada a yanzu.
Sarki ARYAN ya dubi wani
hadiminsa yace, a kai Humairu da
dan uwansa masauki abasu abinci
suci su huta tukunna.
Nan take hadimin ya jasu Humairu
suka fice daga fadar.
Humairu na waigen sarki ARYAN
kamar yaki bin hadimin, kai da gani
kasan cewa hankalinsa a tashe
yake kuma lallai akwai sakon
gaggawa a bakinsa wanda yake
son ya isar ga sarki.
Shi kuwa sarki ARYAN sai yaje ya
kama gimbiya lushirat ya taimaka
mata ta mike tsaye da kyar saboda
nauyin jikinta,ta dora hannunta
bisa kafadarsa suka tafi Izuwa cikin
gidan sarautar.
Lokacin da aka kai su Humairu
dakin bakin aka kawo musu abinci
da abin sha na alfarma sai suka
kasa cin komai suka yi tagumi
domin su kadai ne suka san irin
tashin hankalin da suke ciki.
Ai kuwa suna cikin wannan hali ne
kofar dakin ta Bude sai ga sarki
ARYAN da kansa ya shigo.
Humairu da Hashlar suka mike
tsaye don girmamawa a gareshi a
Lokacin da suka ga alamun
tsananin tashin hankali karara akan
fuskarsa,
sarki ARYAN janyo kofar dakin da
hannunsa ya rufeta don kada wani
yaji abinda zasu tattauna sannnan
ya dubesu daya bayan daya yace,
nasan sakon da kuke dauke dashi.
Tabbas kuna dauke da mummunan
labari ne na baiyanar bakin
samudawa a wannan nahiya tamu
wadanda suka je kauyenku suka
kashe dukkan mazajenku kuma
suka kame matayenku
Daga baya kun dawo daga farauta
kuka iske wannan bala'in
Ihun da kuka yine mutanen suka
jiyo aka turo mutum uku kacal
daga cikinsu kukayi babakin yaki
dasu har suka kashe yan uwanku
mutum biyar.
Da kyar da sidin goshi kai Humairu
da Hashlar kuka kashe wadanan
mutane uku.
Haka ne ko ba haka bane?"
Cikin tsananin mamaki kuma cikin
hadin baki Humairu da Hashlar
suka ce, yaya akayi kasan wannan
Al'amari? DUGUNZUMA!!!
LITTAFI NA DAYA
PART 5
LITTAFIN YAKI
NASEER SHEHU TEARLOW
*******
sarki ARYAN janyo kofar dakin da
hannunsa ya rufeta don kada
wani yaji abinda zasu tattauna
sannnan ya dubesu daya bayan
daya
yace, nasan sakon da kuke dauke
dashi.
Tabbas kuna dauke da mummunan
labari ne na baiyanar bakin
samudawa a wannan nahiya tamu
wadanda suka je kauyenku suka
kashe dukkan mazajenku kuma
suka kame matayenku
Daga baya kun dawo daga farauta
kuka iske wannan bala'in
Ihun da kuka yine mutanen suka
jiyo aka turo mutum uku kacal
daga cikinsu kukayi babakin yaki
dasu har suka kashe yan uwanku
mutum biyar.
Da kyar da sidin goshi kai Humairu
da Hashlar kuka kashe wadanan
mutane uku.
Haka ne ko ba haka bane?"
Cikin tsananin mamaki kuma cikin
hadin baki Humairu da Hashlar
suka ce, yaya akayi kasan wannan
Al'amari?
Sarki ARYAN ya sami wuri ya zauna
sannnan yayi ajiyar zuciya yace,
"Duk na ga wannan Al'amarin ne a
cikin madubin Bokana KURHAS
IBINI LAMRAS a yau din nan da safe.
Yanzu haka boko kurhas ya hada
nasa-inasa ya gudu ya bar wannan
nahiya tamu gaba daya domin yace
wadanan mutane da suka zo sai
sun shafe gaba dayan kasashen
dake wannan nahiya tamu.
Yaya za'a yi na gudu na bar
jama'ata kasata da dukiyata?"
Nan ce mahaifata babu abinda zai
rabani da ita face mutuwa.
Bana son jini na ya zuba a ko ina
face akan kasar mahaifata.
Na yarda zan mutu amma ba zan
mutu rago ba, kuma sai dai na
mutu akan tafarkin tsare
mutuncina dana jama'ata.
idan naso zan iya guduwa nida
matata muje muyi sabuwar rayuwa
a wata nahiya dabam.
Amma ai abin kunya ne ace ni sarki
mai cikakken iko kamata ace na
gudu na bar jama'ata da mulkina.
Ba zan iya guduwa ba na

Please Login or Register in order to submit comment