Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kakanninku suka shafe
shekara da shekaru suna faman
wahalar mayarda shi maraya?"
To ku sani cewa dan halak baya
yarda aci zarafinsa dana iyalinsa ko
dukiyarsa sai dai ya mutu akan
kare kimarsa da martabarsa.
Ku tsaya kuyi yaki, ku zubar da
jininku don kare kimarku da
mutuncinku.
Koda sarki Aryan yazo nan a
zancensa sai gaba dayan dakarun
nasa suka ji kamar an cire musu
dukkan tsoro da fargaba daga cikin
zukatansu.
Nan take jikinsu ya kama tsuma
suka ji ma babu abinda suke so
sama da su ga karasowar abokan
gaba a fara gurmuzu.
Nan take suka kama kiran sunan
sarki ARYAN cikin hada baki suna
cewa ransa ya dade.
A dai-dai wannnan lokaci ne
rundunar sarki larbusa ta kara
kusantowo wacce saboda tsananin
yawanta har ba'a iya hango
karshenta,
kai kace ta tokare da sararin
samaniya.
Koda su sarki larbusa suka yi arba
da rundunar sarki Aryan wadanda
basu fi kaso daya ba cikin kaso
ukun tasu rundunar, kuma suka
gansu 'yan kanana a gabansu
amma ko gezau ba suyi ba bare suji
tsoronsu, har ma ihu suke yi suna
yiwa Sarkinsu jinjina, sai suka cika
da mamaki.
Shi kansa sarki larbusa sai da ya
tsayar da giwarsa ya tsaya cak!
Suka kurawa juna idanu shi da sarki
Aryan wanda ke kan dokinsa.
A wannan Lokaci tazarar dake
tsakaninnsu bata wuce taku Ashirin
ba,
Sarki larbusa ya karewa sarki Aryan
kallo sama da kasa, ya lura da irin
kirarsa ta karfi da sadaukantaka,ku
ma ya dubi cikin kwayar idanunsa
yaga cewa tabbas wannan sarki ya
cika JAN GWARZO,wanda zuciyarsa
ta kekashe.
Lallai bai san tsoro ba, kuma da
gani kasan babu tambaya domin
indai akwai dan shi akan kasa to a
karkashinta ma ba za'a rasa ruwa
ba.
Abin nufi anan shine lallai alamar
karfi tana ga mai kiba! Duk da cewa
sarki larbusa ya tabbatar da cewa
yafi sarki Aryan karfi da iya yaki a
zahiri, amma sai zuciyarsa ta raya
masa cewa babu mamaki fa sakon
da Sarkin yakinsa ya zo dashi ya
tabbata.
Koda sarki larbusa ya gama aiyana
wadannan al'amura a cikin
zuciyarsa sai ya sakarwa giwarsa
kaimi ya nufi inda sarki Aryan ke
tsaye shi kadai.
Har wadansu manyan
mukarrabansa sun yunkura zasu
biyoshi sai ya daga musu hannu ya
tsaida su.
Koda sarki Aryan yaga sarki larbusa
ya nufoshi gadan-gadan ba tare da
zare makami ba sai shima ya
sakarwa dokinsa linzami ya nufeshi
suka tunkari juna har sai da ya
zamana cewa tsakaninsu bai wuce
taku uku ba sannnan kowannensu
ya tsayarda abin hawansa suka
sake yiwa juna kallon nutsuwa na
'yan dakiku kadan.
Sarki larbusa ya dubi sarki Aryan
yace,
"Ban taba haduwa da sarki mai
DAKAKKIYAR ZUCIYA ba kamarka!
Kuma ban taba ganin jarumin da ya
burgeni ba irinka! Saboda ko kadan
baka da tsoro tun da gashi ka
tabbatar da cewar anfi karfinka
amma saboda kishinka akan
mulkinka, jama'arka da kasarka
kaki mika wuya.
Inaso ka sani cewa kune jarumai na
farko a nahiyar nan kaf wadanda
suka sami nasarar kashe wasu daga
zakwakuran dakaruna.
Lallai ina bukatar GWARZON JARUMI
irinka! Shin me zai hana ka yi
MUBAYA'A a gareni na baka Sarkin
yakina ko don ka ceto rayuwar
matayenku, 'ya'yayenku da
tsofaffinku.
Idan har ka mika wuya a gareni
digon jini daya ba zai zuba ba a
cikin wannan birni naka.
baza a rushe gidajenku ba,ko a
konasu, kuma ba za'a karbi koda
kwayar hatsi ba a wajen
talakawanka da kai kanka.
Sai dai kasarka gaba daya zata
dawo karkashin ikona!
Kuma wanda naso daga cikin
jama'ata shi zan nada ya hau kan
karagarka!!!"
Lokacin da sarki larbusa yazo nan a
zancensa sai ran sarki Aryan ya
sosu ainun, zuciyarsa ta kama
tafarfasa kamar zata kone, bai san
sa'adda ya tari numfashin sarki
larbusa ba a fusace ya daka masa
tsawa yace, "kai tsohon azzalumi!
Kayi sani cewa ba zan taba siyar da
jama'ata ba da kasata ba saboda
tsoron MUTUWA!
Da dai na bari azzalumi irinka ya
shugabanci jama'ata gwara a
shafemu daga doron kasa.
Tsakanina da kai sai ya yaki!
Babu Aminci sai matsanaciyar
gaba!!
Kaifin takobine kawai zai rabamu ".
Koda jin wannnan batu sai sarki
larbusa ya takarkare ya bushe da
mahaukaciyar dariyar mugunta,
lokaci guda kuma ya turbune fuska,
har fuskar tasa ta kama yin gatsine
ita kadai, ya kuma cewa,
"Ai kuwa sai kayi babbar nadamar
da zata zamo abin misali ga duniya
gaba daya!
Daga yau sai na kashe Duk wani da
namiji a birninka wanda ya kai
shekara goma a duniya!!
Dukkan 'yan matanku da
matayenku na aure sai anyi musu
fyade! Kuma na maishe su bayina!
Sai na tabbatar da cewa an yiwa
gidajenku da kasar birninka ado da
jini kafin a kwashe duk abin amfani
a cikinta a koneta kurmus ta zama
toka!
Sai na baje wannan kasa yadda ko
a tarihi baza a iya tunowa da
wanzuwarta ba....
Kafin sarki larbusa ya gama
wannan furuci tuni sarki Aryan ya
sake tarar numfashinsa a karo na
biyu yace,
"Ni kuma nayi maka alkawari
cewar kafin ka kasheni sai na fitar
da jini a jikinka! Na bar maka tabon
da har abada ba zai bata ba.
Kuma sai na yiwa dakarunka
mummunar barna da ba a taba yi
maka ba.
Inda babu kasa anan ake yin
gardamar kokawa, mu zuba mu
gani!!"
Koda gama fadin Hakan sai sarki
Aryan ya kada linzamin dokinsa ya
juya da baya ya nufi cikin tawagar
dakarunsa da sauri ya bar sarki
larbusa a tsaye bisa giwarsa jikinsa
na tsuma da karkarwa saboda
tsananin fushi.
Ji yake kamar yabi sarki Aryan da
gudu ya sareshi.
Kawai sai aka ga sarki larbusa ya
sauko daga kan giwarsa ya juyo ya
dubi dakarunsa masu jiran umurni.
Sarki larbusa yasa hannunsa na
dama ya zare zabgegiyar takobinsa
ya dagata sama ya zabga kururuwa
gamida yiwa dakarun nasa inkiya a
afkawa abokan gaba!
Kafin su zare takubbansu da sauran
mugayen makamansu na yaki tuni
shi sarki larbusa ya juya ya falfala
da gudu Izuwa kan rundunar sarki
Aryan.
Koda sarki Aryan ya hango sarki
larbusa a tsiyace a fusace ya
durfafosu sai shima ya ruga Izuwa
gareshi domin ya tareshi da sauri,
saboda ya san cewa idan bashi ne
ya tareshi ba zai iya yiwa
dakarunsa mummunar barna cikin
kankanin lokaci.
Ai kuwa suna haduwa sai suka
kacame da masifaffen yaki mai
tsananin ban al'ajabi da ban tsoro,
domin suna kaiwa junansu sara da
suka ne cikin tsananin zafin nama,
juriya da jarumtaka ta musamman,
irin wacce idanu bai saba gani ba.
A wannnan lokaci ne sauran
dakarun sarki larbusa ma suka rugo
da gudu Izuwa cikin filin yaki suna
ihu da kururuwa mai firgita mazaje.
Ba tare da shakkar komai ba kuwa
suma dakarun sarki Aryan sai suka
ruga suka taresu aka ruguntsume
da azababben yaki a filin gaba dai
ya zamo babu abinda mutum zai
iya ji face ihun mazaje da karafkiyar
karafa.
Wohoho! Bala'i ba a sa masa rana!
Haka ma wutar masifa idan taxo
babu mai yayyafa mata ruwa face
Allah!!
Inda ace mutum na tsaye a filin
wannan yaki yana ganin yadda ake
gididdiba jikin bil'adama tamkar
yadda ake sarrafa nama a mahauta
da komai rashin imaninsa sai yaji
zuciyarsa tayi rauni.
Idan kuwa yana da dan guntun
tsausayi ko da baifi kwayar zarrah
ba sai ya zubar da hawaye.
Duk inda mutum ya hanga ko ya
waiga sai dai yaga sassan jikin
bil'adama a zube tsubi-tsubi cikin
ruwan jini tamkar bolar yayi da
takarda, ko kuma ya gansu a sama
suna shawagi suna zubowa kasa,
kai kace biki ake yi na tsuntsayen
duniya.
Abin dai babu kyan gani, babu
dadi!
Sai da aka shafe kusan sa'a uku cur!
Ana wannan BAKIN ARTABU, amma
sarki larbusa da sarki Aryan na ta
fafatawa dayansu bai sami nasarar
koda kwarzanar jikin abokin
gwaminsa ba.
Al'amarin da yai matukar baiwa
sarki larbusa mamaki kenan domin
gashi dai a zahiri yafi sarki Aryan
tsagwaron karfin damtse, amma sai
zafin naman su ya kusan zuwa
daya.
Nan fa ran sarki larbusa ya baci
ainun, zuciyarsa ta kama tafarfasa
kamar zata kone, saboda shi yasan
cewa shi kadai yake tarwatsa
runduna guda ta manyan mazaje
ababan tsoro amma yau gashi
mutum daya jal! Yana neman ya
zamo masa alakakai.
Nan take sarki larbusa ya sauya
salon yaki, ya rinka kaiwa sarki
Aryan hari da makami biyu a lokaci
guda da dukkan karfinsa, wato
bayan takobin dake hannunsa
kuma sai ya zaro wata lafceciyar
adda yaci gaba da kai masa
mugayen hare-hare.
Saboda karfin saram na sarki
larbusa sai sarki Aryan ya kasa
tsayawa a gabansa, bisa dole ya
rinka ja da baya-baya, kuma ya
rinka zille-zille da kauce kauce.
Inda ba don yanada zafin nama
gamida juriya da kwarewa ta yaki
da tuni sarki larbusa ya gama dashi
farat daya! Duk da haka sai da ta
kai cewa da kyar! Yake iya kare
hare-haren da yake kawo masa har
ta kai cewa ya fara kuntatashi.
Kwatsam! Sai sarki larbusa ya sami
nasarar yankar sarki Aryan a gadon
bayansa take wajen ya dare jini yai
tartsuwa.
Sarki Aryan ya kurma uban ihu
sakamakon tsananin zogin da yaji
Sai yai sauri yayi alkafira da baya
sau uku, ya diro akasa a matukar
galabaice a Lokacin da jini ke zuba
a gadon bayan nasa, kuma ya fara
ganin mutane dishi-dashi.
A hakan ne ya dubi gabas da
yamma kudu da arewa yaga
abinda ke faruwa a filin yakin.
Nan take hankalinsa ya sake
dugunzuma ainun fiye da
koyaushe, domin gani yayi kawai
ana ta ragargazar dakarunsa
tamkar ana sassabe a gona.
Al'amarin da yasa zuciyarsa ta
kama tafarfasa kenan ya tuno da
alkawarin da ya dauka cewar kafin
a gama wannan yaki sai ya fitar da
jini a jikin sarki larbusa.
A wannan Lokaci sarki larbusa yana
tsaye kawai yana faman kyalkyala
dariyar mugunta bisa ganin nasarar
da yasamu ta yiwa sarki Aryan
wannan mugun rauni a gadon
bayansa.
Duk sa'adda wani badakaren sarki
Aryan ya gifta ta gabansa kuwa
sara daya yake yi masa ya gama
dashi.
Nan take idanun sarki Aryan suka
kada suka yi jawur tamkar gasa
dan buda a cikin wuta saboda
tsananin fushi.
Kwatsam! Sai aka ga sarki Aryan ya
falfalo da azababben gudu daga
inda yake yana ihu yana kade
dukkanin abokan gaba dake
gabansa ya nufi inda sarki larbusa
ke tsaye bada fargabar komai ba.
Shi kansa sarki larbusa sai da ya yi
mamakin irin wannnan azababben
gudu da sarki Aryan keyi da kuma
yadda ya tunkaro shi gadan-gadan
ba da shakkar komai ba.
Ai kuwa shima sarki larbusa sai ya
yunkura ya ruga domin ya tareshi
yana mai yin wata kururuwa mai
tsananin ban tsoro, wacce ita kadai
ta isa ta sa kananan dakaru su
dimauce su kama sakin fitsari a
wando.
Irin gudun da suke yi su biyun a
wannan Lokaci kai kace akan iska
suke saboda karfinsa.
Lokacin da ya rage saura bai fi taku
uku ba su hadu sai kowannensu ya
daka tsalle sama kai kace daga
cikin baka aka cillasu, suna haduwa
suka kaiwa juna mugun hari.
Kawai sai gani akayi duk su biyun
sun rikito kasa sun tsugunna kasa
sun kasa mikewa tsaye, kuma
kowannensu kansa na sunkuye,
jikinsa na tsuma.
Daga can sai sarki larbusa ya fara
mikewa tsaye, sai ga jini na digowa
kasa ta cikin gefen sulken yakinsa.
Cikin tsananin fishi ya yar da Addar
hannunsa ya yage sulken dake
kirjinsa yai jifa dashi.
A sannnan ne ya yi arba da raunin
da sarki Aryan yayi masa.
Ashe takobi ya soka masa a gefen
kirjinsa, bangaren hagu.
Wajen yayi rami, har a sannnan jini
na dan bulbulowa.
Koda ganin wannan rauni sai sarki
larbusa ya sake kwarara uban ihu a
karo na biyu fiye da wanda yai da
farko, kuma ya kamu da tsananin
bakin ciki da takaici fiye da
koyaushe a rayuwarsa.
Domin wannan ne karo na farko da
aka taba yi masa rauni a rayuwarsa
koda bisa tsautsayi kuwa.
Adaidai wannnan lokaci likitan
sarki larbusa ya rugo da gudu
Izuwa gareshi ya fara kokarin
tsayarda jinin dake zuba a jikin
nasa.
A sannnan ne shima sarki Aryan ya
mike tsaye da kyar yana mai dafe
gefen cikinsa inda jini ke zuba.
Shima wani lacecen yanka ne a
wajen da takobin sarki larbusa tayi
masa.
Tabbas in ban da sarki Aryan ya
kasance gwarzon jarumi mai juriyar
gaske bai isa ya iya mikewa tsaye
ba da wannnan rauni a cikinsa,
domin saura kiris! Yankan ya fasa
fatar cikin gaba daya aga kayan
cikinsa.
Idanunsa kuwa sai lumshewa suke,
jiri na dibarsa yana layi kamar zai
fadi,amma saboda taurin rai sai yai
wuf! ya yagi rigarsa ya daure cikin
nasa tamau, jinin ya daina zuba,
sannnan ya tsaya daram akan
kafafunsa ya dubi sarki larbusa ya
bushe da dariya yana mai nunashi
da Danyatsa sannnan yace,
"Ko yanxu na MUTU burina ya cika
tunda na cika ALKAWARINA na fitar
da JINI a JIKINKA kafin karshen
wannan yaki.
Ina mai dada yi maka ALKAWARIN
cewar yanzu zan sake yi maka wani
RAUNIN a inda zai zamo SHAIDA
yadda sai dai ka MUTU dashi, don
har abada ba zai bace ba a JIKINKA!
"
Cikin tsananin fishi sarki larbusa ya
tari numfashin sarki Aryan yana
mai daka masa tsawa yace,
"Ni kuma nayi maka alkawari
cewar yanzu nan zan yi maka
kissan wulakanci da zarar mun sake
haduwa!!"
Koda jin haka sai sarki Aryan ya
sake bushewa da dariyar karfin hali
yace, "Ai ko ba ka yi mini kissan
gilla ba nasan cewa mutuwa zanyi,
don yankan da kayi mini a cikina
yayi zurfi ainun, ba zan tsira ba.
Dubi jama'ata duk mutuwa suke ta
yi, kuma nasan dayansu ba zai tsira
ba,amma dai nasan cewa ko a
bayan wannan yaki sai ka kwanta
jinya.
Na yarda ka cini da yaki, ka kama
kasata, dukiyata da jama'ata,
amma ka sani cewa iyalina sunfi
karfin duk irin wulakancin da kake
shirin yi musu.
Domin baza ka taba riskarsu ba a
cikin gidan sarautata ba!"
Koda gama fadin Hakan sai sarki
Aryan ya daga takobinsa sama ya
sake falfalawa da matsanancin
gudu Izuwa kan sarki larbusa a
karo na biyu.
Har Izuwa wannan Lokaci likitan
sarki larbusa bai gama sa masa
magani ba akan wannnan rauni
nasa na kan kirji.
Koda sarki larbusa yaga sarki Aryan
ya kusa isowa kansa sai yasa
hannunsa ya mangare likitan nasa
yai sama ya fadi can gefe daya kai
kace janyeshi akayi da majajjawa.
Cikin bakin zafin nama da bakar
zuciya sarki larbusa ya ruga Izuwa
kan sarki Aryan.
Wannan karon ma sai suka sake
daka tsalle a sama suka kaiwa juna
mugayen sara, kawai sai ji akayi
duk su biyun sun kurma uban ihu
sun fado kasa a matukar galabaice
sun kife bisa kasa da rub da ciki! Ko
motsin kirki babu wanda yayi a
cikinsu.
A wannan Lokaci an kashe gaba
dayan dakarun sarki Aryan babu
mutum daya a raye sai dakarun
sarki larbusa ne kawai a tsaitsaye
cikin tsananin tashin hankali sun
kurawa sarki larbusa idanu wanda
ke kwance da rub da ciki ba tare da
sun fahimci halin da yake ciki
ba,kuma an rasa wanda zai je ya
dubashi.
A wannan Lokaci fillin yakin ya cika
da gawarwaki a ko ina a kasa suna
ta iyo a cikin ruwan jini kai kace
teku ce ta balle. DUGUNZUMA!!!
LITTAFI NA 3
PART 3
NASEER SHEHU TEARLOW
*****
A wannan Lokaci an kashe gaba
dayan dakarun sarki Aryan babu
mutum daya a raye sai dakarun
sarki larbusa ne kawai a tsaitsaye
cikin tsananin tashin hankali sun
kurawa sarki larbusa idanu wanda
ke kwance da rub da ciki ba tare da
sun fahimci halin da yake ciki ba,
kuma an rasa wanda zai je ya
dubashi.
A wannan Lokaci fillin yakin ya cika
da gawarwaki a ko ina a kasa suna
ta iyo a cikin ruwan jini kai kace
teku ce ta balle
Bayan kamar dakika dari da Ashirin
sai aka ga sarki larbusa ya yunkura
ya mike tsaye.
Koda ya daga hannunsa na hagu sai
aka ga babu babban dan yatsansa,
don ya guntule, jini na ta
bulbulowa ta cikinsa.
Koda ya dubi dan yatsan nasa yaga
ya guntule sai ya sake kwarara
uban ihu ya ruga Izuwa kan gawar
sarki Aryan.
Koda ya kamo kan sarki Aryan ya
daga sama sai yaga ashe ya tsarge
Gangar jikinsa gida biyu, wato
kugunsa ya rabu da cikinsa tamkar
an sa wuka an yanka tuffa a
tsakiya.
Kawai sai ya jifa da rabin Gangar
jikin sarki Aryan ya tofa mata yawu
sannnan ya dubi wani babban
badakare nasa mai suna ZILGUL
YACE dashi, "maza ka tattara sassan
jikin sarki Aryan kasa ayi masa
kabari a kofar fadarsa, nan gaba
kabarin zai yi mini amfani matuka.
Nan take zilgul ya dauko daya
rabin jikin na sarki Aryan ya hada
da dayan ya saba a kafadarsa.
Sarki larbusa ya nufi kofar shiga
birnin LURHAJ.
Da isarsa bakin kofar sai yasa
kafarsa daya ya banketa.
Duk girman kofar da kaurinta sai ya
zamo na banza, ta fadi kasa rikica!
Wata irin kura mai yawa da karfi ta
tashi, kawai sai sarki larbusa ya
bayar da umurnin a afka cikin garin
a kashe dukkan tsofaffi, kuma a
kame mata da yara.
Nan fa dakarun nasa suka ruga
Izuwa cikin birnin LURHAJ suka hau
ta more!
Kaico!
Komai rashin imanin mutum idan
yaga yadda dakarun sarki larbusa
suka rinka kashe tsofaffin birnin
LURHAJ, sannnan suna kama
matayensu da karfin tsiya suna yi
musu fyade, sannnan su
daddauresu da sarkoki.sai dai kzaji
mata da yara suna Iface-iface da
koke-koke dole zuciyar mutum tayi
rauni har ya zubar da hawaye.
A cikin kankanin lokaci aka yi kaca-
kaca da birnin gaba daya da kuma
mutanen cikinsa aka kwashe
dukkanin dukiyoyinsu aka tare a
waje guda.
Lokacin da aka shiga cikin gidan
sarautar sarki Aryan aka gama da
dukkanin jama'ar dake ciki sai aka
duba ko ina da ina amma ba'a ga
matar sarki Aryan ba da jaririn da
ta haifa.
Al'amarin da yai matukar fusata
sarki larbusa kenan, kuma yayi
matukar bashi mamaki, saboda tun
kafin a fara yakin yayi bincike a
halar tsafinsa yaga matar sarki
Aryan da dan da ta haifa a cikin
gidan sarautar, har Ya kudiri ajiyar
cewar ba zai kashe sarki Aryan
farat! daya ba sai bayan ya
galabaitar dashi ainun sannnan zai
yiwa matarsa fyade a gaban
idanunsa sannnan ya kashe
jaririnsa yana ji yana gani, sai kuma
ya karasashi.
Hakika ba karamin bakin ciki sarki
larbusa yayi ba da yaga babu iyalan
sarki Aryan, kuma dama tun kafin
su fara wannan gurmuzu shi da
sarki Aryan ya shafi madubin
tsafinsa ya ga babu su a cikin gidan
sarautar.
Nan fa sarki larbusa ya sa aka ci
gaba da duba ko ina, a cikin
akwatuna, rijiyoyi da boyayyun
wurare inda ake tunanin ko matar
sarki Aryan da jaririnta sun buya a
ciki.
Amma har dare ya raba ana ta
wannan bincike amma ba a gansu
ba.
A sannnan ne sarki larbusa ya
zauna a cikin tsakiyar turakar sarki
Aryan likitansa ya shiga dinke
raunin dake jikinsa, kuma yana sa
masa magani.
Fuskar sarki larbusa a murtuke take
ko kadan babu annuri, saboda
tsananin fushi, takaici da bakin
cikin rashin ganin iyalan sarki
Aryan.
Nan fa ya shiga tunani. Kwatsam!
Sai tunanin matarsa ZURAIHA ya
fado masa.
Yace a cikin zuciyarsa, " kash!
Amma nayi babban kuskure dana
baro zuraiha a can sansaninmu,
domin inda tana tare dani yanzu,
sai ta gano inda iyalan sarki Aryan
suke tun da ta fini karfin sihirin
tsafi".
Koda gama aiyana Hakan sai sarki
larbusa ya kirawo babban
hadiminsa zilgul ya dubeshi yace,
"maza ka shirya ka koma da baya
Izuwa sansaninmu ka taho da
matata zuraiha
Lallai ina son ganinta cikin
gaggawa ".
Zilgul ya risina yace, "An gama ya
shugabana ".
Nan take zilgul ya juya ya fice daga
cikin turakar yaje ya kimtsa
sannnan ya hau giwarsa ya durfafi
sansaninsu.
Tafiyar sadauki zilgul keda wuya
sai sarki larbusa ya kirawo gaba
dayan fadawansa ya dubesu yace,
"ya ku yan majalisata yanzu dai ga
shi mun ci birnin LURHAJ da yaki,
birnin da babu kamarsa a gaba
dayan wannan nahiya a girma,
yawan arziki da karfin dakaru.
To amma fa ku sani cewa mun
kashe maciji ne bamu sare kansa ba
tunda matar sarki ta gudu tare da
dan da ta haifa.
Wannan da, da ta haifa kuwa ba
karamin annoba bane ga
mulkinmu,domin bincike ya
tabbatar da cewa idan har ya rayu
ya cika shekara Ashirin da biyar a
duniya nan gaba sai yazo ya
shafemu akan doron kasa, ya karbi
mulkinsa da kasarsa.
Bisa wannan daliline yanzu na
tsayar da wannnan yaki don ruguje
sauran kasashen nahiyar wadanda
dama basu kai darajar tsinke ba
akan idanunmu.
Abinda ya kamacemu a yanzu
shine, mu baza dakarunmu masu
yawa Izuwa gabas da yamma,
kudu da arewacin wannan nahiya
Izuwa cikin dazuzzukan birane
domin neman matar marigayi sarki
Aryan da jaririnta a duk inda suke a
kashe su a kawo mini gawarsu.
Wannan ne kadai zai sa mu sami
nutsuwa da kwanciyar hankali.
Kafin a gano inda suke din zanyi
jinyar raunikan dake jikina domin
na sami karfin jikin nawa sossai.
Yanzu zan sa a rubuta wasika
Izuwa ga sauran dukkan kasashen
nahiyar nan wadanda bamu cisu da
yaki ba mu sanarda su cewar mun
kama birnin LURHAJ.
Gama fadin Hakan keda wuya ya
mike tsaye ya fice daga cikin
turakar sarki Aryan.
****
Al'amarin zuraiha kuwa, bayan su
Humairu sunyi mata
Sallama sun tafi zuraiha ta juya ta
nufi inda tantinta yake, inda ta kalli
gawarwakin dakarun dasu Humairu
suka kashe sannnan ta iso inda
ragowar dakarun suke wadanda
suka zauna a gaban wuta suna jin
dumi.
Har ta giftasu zata je ta shiga cikin
tantin nata sai wani tunani ya fado
mata a rai ta tsaya.
Dama su dakarun basa ganinta
saboda karfin sihirin tsafinta, kuma
ba su ga sa'adda ta fito ba.
Kawai sai zuraiha ta dubi dakarun
taMB hura musu iskan bakinta.
Nan take suka bingire a kasa suka
kama barci, sannnan itama ta shiga
cikin tantinta ta kwanta ta kama
barci abinta cikin kwanciyar hankali
tamkar babu wani abu da ya faru a
sansanin.
Kashe gari kuwa, har rana ta kwalle
wadanan dakaru basu farka ba
daga dogon barcin da ya kwashesu
sakamakon iskar bakin da zuraiha
ta buso musu.
Kwatsam! Sai ga sadauki zilgul ya
tunkaro sansanin bisa giwarsa yana
tafiya cikin sauri da takama, sai
huci yake kamar tsohon maciji, kai
kace shi kadai ma zai iya baje
kasashen nahiyar gaba daya.
Tub daga nesa hankalin sadauki
zilgul ya yi mummunan tashi bisa
ganin sauyin yanayi a sansanin,
domin ba kamar yadda suka bar
sansanin yake ba a yanzu.
Sansanin yayi tsit! Tamkar babu
wani mai rai acikinsa.
Babu dakaru masu sintiri don
tabbatar da tsoro.
Ai kuwa yana kara matsowa kusa
sai zuciyarsa ta buga da karfin
gaske, ya tsorata ainun sakamakon
ganin gawarwakin dakarunsu
Kimanin mutum tara.
Cikin dimauta da hanzari zilgul ya
zare takobinsa ya tsayar da giwarsa
ya dure kasa daga kanta, sannnan
ya kama tafiyar sanda yana waige-
waige da dube-dube.
Koda ya iso inda dakarun nan masu
jin dumi suke sai ya iskesu a
kwance suna ta faman shara barci
har suna yin minshari.
Gashi wutar da suka kunna har ta
cinye ta zama toka sai burbushinta
da dan hayaki kawai.
Al'amarin da yai matukar bashi
mamaki kenan, kuma ya daure
masa kai.
Ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa
yace,
"To menene yasa aka kyale
wadanan dakaru ba'a kashesu ba
alhalin an kashe sauran 'yan
uwansu? "
Bashida amsar wannan tambaya da
ya yiwa kansa, kuma babu mai
amsa masa a kusa.
Maimakon zilgul ya tashi wadanan
dakaru daga barci sai kawai ya
wuce gaba ya iso inda bayi suke a
cikin kejin
Nan ma ya gansu a kwance kuma a
daure cikin sarkoki suna ta shara
barci abinsu.
Zilgul ya tasamma tantin zuraiha
matar sarki larbusa zuciyarsa na ta
dukan uku-uku yana fargabar kada
yaje ya tarar da wani abu ya
sameta.
Abinda ya kara bashi mamaki shine,
ko kuyanga daya bai gani ba daga
cikin masu yi mata hidima a bakin
tantin.
Zilgul na shiga cikin tantin gimbiya
zuraiha sai ya isketa a kwance tare
da dukkanin kuyanginta suna ta
faman shara barci da munshari.
Koda ganin haka sai zuciyar zilgul
ta kama tafarfasa kamar zata kone,
bai san sa'adda ya takarkare ya
kwarara uban ihu mai tsananin
karfi da firgitarwa ba.
Cikin firgici da dimaucewa gaba
dayan mutanen dake sansanin suka
farka daga nannauyan barcin da
suke yi.
Gimbiya zuraiha ta mike tsaye
zumbur!
A dimauce tana rawar jiki.
Koda taga ashe sadauki zilgul ne
tsaye a gabanta kuma ta fuskanci
cewar shine yayi wannan ihu sai ta
daka masa tsawa, ta dubeshi a
fusace tace, "menene ya dawo da
kai nan sansanin, kuma akan wane
dalili zaka shigo har cikin tantina ka
kurma wannan uban ihu? "
Koda jin wannnan tambaya sai
zilgul ya durkusa kasa bisa
guiwarsa guda ya sunkui da kansa
kasa cikin biyayya yace, "Ya
shugabana ki gafarceni dole ce ta
sa nayi hakan domin sarki ne ya
aikoni na tafi dake Izuwa can birnin
LURHAJ wanda mun dade da cinsa
da yaki.
A yanzu dana iso cikin sansanin nan
sai na iske an kashe dakarunmu da
yawa, sai kalilan ne suka rage,
kuma sannnan na iske na iske ku
kuna ta yin barci mai nauyi.
Lallai duk yadda akayi abokan gaba
sun shigo mana baku sani ba.
Babu mamaki sun kubatar da
rayuwar wadansu fursunonin "
Koda zilgul yazo dai-dai nan a
zancensa sai idanun zuraiha suka
zazzaro, alamun tsoro ya bayyana
sossai akan fuskarta ta mike tsaye
zumbur! Da sauri ta fice daga cikin
tantin.
***** DUGUNZUMA!!!
LITTAFI NA 3
PART 4
NA KARSHE
NASEER SHEHU TEARLOW
******
A yanzu dana iso cikin sansanin nan
sai na iske an kashe dakarunmu da
yawa, sai kalilan ne suka rage,
kuma sannnan na iske ku kuna ta
yin barci mai nauyi.
Lallai duk yadda akayi abokan gaba
sun shigo mana baku sani ba.
Babu mamaki ma sun kubatar da
rayuwar wadansu fursunonin "
Koda sadauki zilgul yazo dai-dai
nan a zancensa sai idanun zuraiha
suka zazzaro, alamun tsoro ya
bayyana sossai akan fuskarta ta
mike tsaye zumbur! Da sauri ta fice
daga cikin tantin.
A Lokacin ne kuyangin nata su ka
fara mikewa tsaye a razane.
Shima zilgul sai ya biyo zuraiha
baya da sauri.
Zuraiha ta cigaba da yawo a cikin
sansanin cikin sauri da gudu -gudu
tana kallon abinda ya faru.
Bayan taga gawarwakin dakarun
da aka kashe sai ta dubi tsirarun
dakarun da suka farka daga bacci ta
daka musu tsawa tace, kuna ina har
abokan gabarmu suka shigo
sansanin nan suka kashe 'Yan
uwanku?"
Koda jin wannnan tambaya sai
dakarun suka kama duru-duru suna
kallon juna aka rasa wanda zai ce
tak!
Sannnan shugabansu ya risina yace,
"Ya shugabata jiya har dare ya raba
muna nan a gaban wuta muna jin
dumi muna hira ko motsin bera ba
mu ji ba.
Daga sannnan ba mu san abinda da
ya faru ba sai yanzu da muka farka
daga barci sakamakon ihun sadauki
zilgul ".
Ya yin da zuraiha taji wannan batu
sai tayi sauri ta dauko madubin
tsafinta ta shafeshi da hannun hagu
ta kura masa idanu har Izuwa
tsawon yan dakiku sannnan ta
dago kai ta dubi zilgul tace,
Wasu zakwakuran jarumai ne guda
biyu daga cikin kauyen kasar nan
wadanda baku kashe su ba suka
biyo sawun iyayensu da
masoyansu.
Sune suka zo suka kashe
dakarunmu suka sami nasarar
kubatar da bayi hudu.
Kuma sune suka sa mukayi wannan
barci mai nauyi da karfin sihirinsu
na tsafi.
Koda jin haka sai sadauki zilgul ya
takarkare ya kwarara uban ihu a
karo na biyu, sannnan ya dubi
wadanan tsirarun dakarun da basu
mutu ba yace, "sai kuyi shirin
karbar hukunci daga wajen sarki
bisa sakakin da kukayi haka ta
faru".
Caraf! Sai gimbiya zuraiha ta tari
numfashin zilgul tace, " Ba zan bari
ayi musu wani hukunci ba, domin
abu ne wanda yafi karfinsu tunda
ni kaina yafi karfina.
Kawai abinda zamuyi shine, ku
tashi mu tafi Izuwa birnin LURHAJ
yanzu, idan na riski sarki zamu
tattauna musan abinda zamuyi "
Nan take kuwa aka shiga shirye-
shiryen tafiya, sannnan aka fito da
bayi daga cikin kejina aka tusa
keyarsu gaba aka nufi birnin
LURHAJ.
Wannan shine abinda ya faru a
sansanin da aka bar gimbiya
zuraiha bayan sadauki zilgul yazo
da sakon sarki larbusa.
****
Al'amarin su jarumi Humairu kuwa,
tun da suka kama hanya suka yi ta
gudu a cikin daji tare da iyayensu
da masoyansu su Laila, basu yada
zango ba a ko ina har sai da suka
iso iyakar birnin LURHAJ da wata
kasa da ake kira ZAITUN, sannnan
suka tsaya.
A sannnan ne Humairu da Hashlar
suka tsugunna a kasa suna ta
faman haki kamar ransu zai fita
saboda tsananin gajiya, saboda sun
shafe kusan sa'a tara kenan suna
gudu basu huta ba.
Sai da suka dawo cikin haiyacinsu
sannnan suka sha ruwa, suma
iyayen nasu da 'yan matan nasu
suka fito da abinci aka ci aka sha.
Dama a can sansanin su sarki
larbusa sun samu sun debo guzuri.
Bayan kowa ya nutsu sai Humairu
ya mike tsaye ya dubi mahaifiyarsa
da masoyiyarsa laila yace, "Ni anan
zan rabu daku, dole ne na koma
can birnin LURHAJ yanzu.
Koda jin wannnan batu sai mamaki
da tsoro ya kama mahaifiyar
Humairu da Budurwаrsa laila.
Mahaifiyar tasa ta dubeshi cikin
alamun tsananin damuwa tace,
"akan wane dalili zaka koma Izuwa
birnin lurhaj yanzu

Please Login or Register in order to submit comment