Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kana
mai yin bara kana cewa, "waye zai
ciyar da kai yanzu ni kuwa na ciyar
dashi iya rayuwarsa? "
Tabbas wannan sarauniya zata sa a
baka abincin da zaka koshi.
Bayan nan ka tambayeta babban
burinta na duniya, lallai zata zo
maka da barun wani littafi wai shi
TSATSUBA
Lallai kai ne zaka yi jagora bisa
tafiyar da za'a yi ta neman
wannnan littafi. DUGUNZUMA!!!
LITTAFI NA BIYU
PART 6
MR NASSEER
******
Kada ka kuskura ka kwana a
wannan gari da zarar ka koshi sai
kayi
harama ka sayi doki ka hau ka
cigaba da tafiya.
Ina mai tabbatar maka da cewa sai
ka shekara arba'in da biyar kana
wannan tafiya kana ta keta
dazuzzuka da birane.
A sannnan ne zaka cika shekara
hamsin da daya a duniya, kuma a
wannan Lokaci ne guzurin dake
cikin jakarka zai kare, za ka iso
wani
babban Birni inda wata
mashahuriyar sarauniya ke mulki.
A sannnan ne yunwa zata
gallabeka don haka ka nemi hanyar
gidan
sarauta.
Kana zuwa fada ka wuce kai tsaye
Izuwa gaban katangar mulki kana
mai yin bara kana cewa, "waye zai
ciyar da kai yanzu ni kuwa na
ciyar dashi iya rayuwarsa? "
Tabbas wannan sarauniya zata sa a
baka abincin da zaka koshi.
Bayan nan ka tambayeta babban
burinta na duniya, lallai zata zo
maka da batun wani littafi wai shi
TSATSUBA
Lallai kai ne zaka yi jagora bisa
tafiyar da za'a yi ta neman
wannnan
littafi.
Tabbas za'a samu wannan littafi
har bukatar wannan sarauniya ta
biya.
A sannnan ne zaka sami lada mai
tsoka daga wajen sarauniyar kamar
yadda tayi alkawari zata bayar ga
wanda duk ya samo mata littafin
TSATSUBA.
A cikin tafiyar da zaku yi ne zaka
sami daukaka irin wacce babu wani
boka da ya taba samunta har
duniya ta shude baza a manta da
kai ba a cikin tarihi.
Amma ka sani cewa zaku sha
tsananin ukuba a cikin wannan
tafiya kuma zaku ga abubuwan
al'ajabi da yawa.
Sa'adda mahaifina yazo nan a
zancensa sai na cika da tsananin
mamaki na dubeshi cikin alamun
rashin fahimta nace, " ya kai
abbana yanzu ni da nake malalaci,
matsoraci, kuma dakiki ya za'a yi
na iya jagora a cikin wannan
gagarumar tafiya alhalin ma ban
inda za'a je ba bare a samo wani
littafi wai shi TSATSUBA? "
Ya yin da mahaifina yaji wannan
tambaya sai ya yunkura domin ya
bani amsa amma sai tari ya
sarkeshi yaci gaba da aman jini.
Al'amarin da ya dugunzuma
hankalina kenan na dimauce naci
gaba da matsanancin kuka ina mai
kankame mahaifina.
Daga can sai ya daina wannan
kumallon sannnan ya janyeni daga
jikinsa muka fuskanci juna sossai a
Lokacin da idanunsa ke lumshewa
yana budewa da kyar sai ya budi
baki yace,"ya kai dana abin kaunata
kayi sani cewa muddin kana tare
da wannnan jaka ta guzurinka
babu abinda zai gagareka kuma
babu wani tsautsayi da zai sa ka
rasa rayuwarka.
Sai kun yi shekara daya da rabi
sannnan zaku isa inda littafin
TSATSUBA yake,kuma wannnan
jaka taka itace zata rinka yi muku
jagora.
Baza ku sami nasarar zuwa inda
wannnan littafi yake ba sai kun
hadu da wadansu jarumai guda
hudu uku mata ne,daya namiji
ma'abocin wani addini da ake kira
MUSULUNCI.
Wannan jaka taka itace zata kaiku
wajen wadanan jarumai guda
hudu.
Sa'adda naji wannan batu sai na
kara cika da tsananin mamaki bisa
yadda za'a ce jaka zatayi mana
jagora a cikin wannan doguwar
tafiya alhalin bata kasance abu mai
rai ba kuma ba magana take yi ba.
Har na budi baki zan tambayi
mahaifina ta yadda wannan jaka
zata yi mana jagora a cikin tafiyar
sai naji gaba dayan jikinsa ya
sandare kamar gunki,idanunsa
kuwa suka kafe.
Cikin dimauta na girgizashi amma
ko motsi baiyi ba.
Kawai sai na rungumeshi na fashe
da matsanancin kuka.
Cikin sauri na maida shi kan
shimfidarsa na kwantar dashi
sannnan na ruga Izuwa cikin
turakarsa.
Da shigata sai naje na dafa bakar
akwatin mahaifin namu da hannun
hagu faruwar hakan keda wuya sai
akwatin ta Bude nayi arba da wata
jaka wadda akayi ta da fatar
damisa.
Koda na dauki jakar sai naji ta da
dan nauyi.
Kawai sai na rataya jakar a
kafadata na fita da sauri daga cikin
gidan.
Ai kuwa ina fita sai naga gidan
namu ya kama nutsewa Izuwa
cikin karkashin kasa har sai da ya
lume gaba daya.
A dai-dai wannnan lokaci ne
hawaye ya zubo mini saboda na
san cewa shikenan na rabu da
mahaifina, kasarmu da 'yan uwana
har abada.
Yanzu ne zan fuskanci sabuwar
rayuwa irin wacce ban taba tsintar
kaina ba a ciki.
Kamar yadda mahaifina yayi mini
jawabin tafiyar da zan yi da
sharuddan da ya gindaya mini a
cikinta banyi wasa da guda daya
ba.
Haka naci gaba da tafiya babu
waige kuma babu magana.
Hakika naga abubuwan al'ajabi da
yawa a cikin tafiyar tawa kuma na
sami ilimi mai yawa da wayewa
akan sanin mutane da al'adu iri-iri.
Gaba dayan rayuwata ta tsawon
shekaru arba'in da biyar din acikin
tafiya ta kare.
Na shiga dazuzzuka iri-iri masu
mugun hadari, amma duk bala'in
da na shiga da duk masifar da ta
tunkaroni sai na ga na tsira daga
shairinta.
Babban abinda ya bani kariya kuwa
ba komai bane face wannan jakar
sihiri ta abbana.
Sau tari sai naji wani abu mai rai
yana ta motsi a cikin jakar har ma
nakan ji kamar yana magana
amma idan na bude jakar sai naga
babu komai a ciki face tarin
wannan dinare.
Haka kuma idan na kasa kunnena
akan jakar sai naji tsit babu wani
sauti a ciki.
A ranar da na iso nan birnin ne
guzurina ya kare na kamu da
tsananin yunwa na tunkari wannan
gidan sarauta sai naji wani abu na
tsalle a cikin jakar sihirina.
Kawai sai na bude jakar duk da
cewa ina da yakinin ba zan ga
komai ba.
Bisa mamaki sai nayi arba da wani
dan mitsitsin aljani mai rafkeken
kai wanda girmansa bai wuce na
fara ba.
Cikin tsananin firgici na yarda jakar
a kasa na ruga da gudu ina waige,
sai da na iso daf da kofar gidan
sarautar nan sai kawai naga
wannan jaka ta baiyana a gabana
tsaye cikin iska.
Cikin dimauta na yunkura da nufin
na juya da baya kawai sai naji an
rikeni gam-gam na kasa koda
motsa dan yatsan hannuna.
Kawai sai naga wannan dan guntun
aljani ya baiyana a hannuna yana
mai kyalkyala mini dariya.
Wani abin mamaki shine, mutane
nata kai kawo a gabana amma
basa iya ganin aljanin kuma basa
jin dariyarsa.
Daga can sai aljanin ya murtuke
fuskarsa yace, "ya kai HUZAILATUL
MARWASU kayi sani cewa yanxu
kaine ubangijina tunda mahaifinka
ya bar duniya.
Lallai babu abinda zai rabani da kai
face mutuwa.
Sunana SUBAURATU IBNI KIMSASA,
nine jikan Sarkin bokayen aljanu na
farko na dari tara da casa'in da tara.
Nine kadai na san inda littafin
TSATSUBA yake wanda mahaifina
ya rubuta, kuma ni kadai ne na
rage daga cikin zuri'armu gaba
daya.
Daga yau ka saki jikinka dani
domin nine kadai zan sa ka a
tafarkin da zaka zamo gwarzon
jarumi, ka daina mugun cin abinci,
kuma ka sami daukakar da ko
mahaifinka bai samu ba.
Yanzu sai ka mayar da ni cikin
wannan jaka da hannunka domin
idan na haura rabin sa'a a waje
iskar duniya zata zamo sanadin
ajalina saboda tsananin tsufana."
Koda gama fadin Hakan sai nayi
sauri na dauke aljani subauratu da
yan yatsun hannuna biyu ina
karkarwar jiki na mayar dashi cikin
wannan jaka sannnan na rataya
jakar akan kafadata, kai tsaye na
shigo cikin wannan gidan sarauta.
Lokacin da huzailatul marwasu
yazo nan a labarinsa sai sarauniya
larbisa ta cika da tsananin mamaki
da farin ciki.
A karon farko a rayuwata sai ta
kama huzailatul marwasu da
hannayenta biyu ta rungumeshi
tana mai cewa, "tabbas kaine
wanda zaka share mini hawayena.
Sai da larbisa da huzailatul
marwasu suka shafe sa'a bakwai
suna hira a wannan rana tare ma
suka ci abinci dare sannnan tasa
aka kaishi masauki, Kuyangi suka yi
masa wanka aka caba masa ado.
Abinda ya baiwa larbisa mamaki
shine, Lokacin da suka ci abinci
loma daya jal huzailatul marwasu
yayi yace ba zai iya cin komai ba.
Sa'adda huzailatul marwasu ya
tsinci kansa a cikin kasaitacen daki
bisa kan luntsumemen gado na
alfarma ga kyakkyawan Kuyangi
suna yi masa tausa sai ya kama
kyalkyala dariyar farin ciki ba
sassauci tamkar mahaukaci sabon
shiga.
A wannan rana dai bai rintsa ba
saboda tsananin farin ciki.
Kashe gari da sassafe sarauniya
larbisa ta fito fada ta zauna kuma
ta tura aka kirawo dukkanin
fadawanta. A sannnan ne kuma ta
tura aka kirawo huzailatul
marwasu.
Koda aka je sai aka iske huzailatul
marwasu yana ta faman shara barci
bai tashi ba.
Da aka Koma aka shaidawa larbisa
sai tace a kyaleshi yaci gaba da
barcinsa har sai ya farka da kansa.
Al'amarin da ya baiwa kowa
mamaki kenan domin ba'a taba
ganin sauraniya larbisa ta girmama
makaskanci ba.
Haka dai larbisa da fadawanta suka
ci gaba da jiran huzailatul marwasu
har sai da ya farka da kansa daga
barci yayi wanka ya kimtsa
sannnan aka yi masa jagora Izuwa
fadar.
Koda shigowar huzailatul marwasu
sai gaba dayan fadawan larbisa
suka kura masa idanu suka cika da
tsananin mamaki domin basu
shaida shi ba cewar shine wannan
almajiri da yazo yai bara yana
neman abinda zai ci.
Cikin farin ciki larbisa ta mike tsaye
ta taryo huzailatul marwasu ta
jawoshi hae Izuwa kan karagarta ta
zaunar dashi.
Sannnan ta dubi 'yan majalisarta
cikin nutsuwa tace," ya ku yan
majalisar birnin daulatul luharus
kuyi sani cewa wannan almajiri da
yazo ya nemi abincin da zai ci a
wajena shine wanda zai cika mini
babban burina na duniya.
Koda jin wannnan batu sai fadawan
suka sake cika da tsananin mamaki.
Larbisa taci gaba da bayani tana
mai cewa, ya ku 'yan majalisata
inaso ku sani cewa na taraku ne
anan domin na sanar da ku cewa
nan da kwana uku zanyi shiri ni da
wannnan bako nawa mai daraja
domin mu yi tafiya neman abinda
zai biya mini bukatata.
Saboda haka xan bar Amanar
kasata a hannunku Kuci gaba da
tafiyar da mulki kamar yadda nake
gudanar dashi.
Idan akwai wani mai korafi a
cikinku bisa wannan hukunci dana
yanke sai yayi yanzu naji.
Lokacin da fadawan sarauniya
larbisa suka ji wannan batu sai
suka yi shiru suka kama kallon
junansu aka rasa wanda zai ce kala.
Koda ganin haka sai larbisa ta
sallami dukkanin fadawan nata
suka fita suka barsu su biyu kacal
ita da almajiri huzailatul marwasu
Tsawon yan dakiku da fitar
fadawan sai larbisa ta dubi
huzailatul marwasu tace, ya kai dan
boka mai daraja inason ka fito da
aljani subauratu ibini kimsasa daga
cikin jakarka ta sihiri domin ina da
wadansu Tambayoyi masu matukar
muhimmanci da nake son zanyi
masa dangane da wannnan
gagarumar tafiya da Zamuyi.
Koda jin wannnan batu sai
huzailatul marwasu ya fiddo jakar
sihirinsa daga cikin babbar rigar
jikinsa ya ajiyeta a gabansa
sannnan ya bude ya zura hannunsa
a ciki ya dauko aljani subauratu bin
kimsasa ya ajiyeshi akan wani dan
karamin tebir na zinare dake gaban
sarauniya larbisa.
Nan take subauratu yayi sujada ga
sarauniya larbisa yana mai bude
fuka fukansa ya kwashi gaisuwa
sannnan ya yace da ita,
Yake sarauniyar duniya, fadi irin
Tambayoyin da kike son ki gabatar
dasu a gareni koda kuwa adadinsu
ya kai na yawan gashin dake jikin
rago ko Tinkiya.
Lallai zan baki amsoshinsu koda
kuwa zamu kwana dubu a zaune
inayi miki jawabinsu."
Koda jin wannnan batu sai
sarauniya larbisa ta bushe da
dariya sannnan tace, "Ai ni
Tambayoyina guda uku ne kacal.
Tambaya ta farko itace, naji
huzailatul marwasu yace, abokan
tafiyarmu Izuwa inda zamu samo
littafin TSATSUBA su hudu ne.
Kuma ukun cikinsu mata ne, na
hudun kuma namiji ne.
To wai shin menene amfanin
kowanne daya daga cikinsu a cikin
wannan tafiya, kuma a wane
garuruwa zamu riskesu?"
Tambaya ta biyu itace, akan wane
dalili wadanan abokan tafiya tamu
su hudu zasu yarda suyi mana
rakiya Izuwa wannan tafiya mai
tsananin hadari? "
Tambaya ta uku wacce itace ta
karshe, shin kasan dalasiman tsafin
da za'a karanta a lalata gaba dayan
tsafin dake cikin littafin TSATSUBA?
"
Sa'adda aljani yaji wadanan
Tambayoyin guda uku daga bakin
sarauniya larbisa sai yai shiru yana
mai kura mata idanu cikin al'ajabi.
Ba wani abu bane yasa yai shiru ba
kuma ya kura mata idanu ba face
tsananin kyawunta daya
dimautashi.
Koda larbisa ta fahimci halin da
aljani subauratu ya shiga sai ta
daka masa tsawa tace,
Shin zaka bani amsar Tambayoyina
ne ko kuwa za kaci gaba kallona ne
har sai ka gaji?"
Nan take aljani subauratu ya shiga
taitayinsa ya dubi larbisa cikin
nutsuwa yace, ki gafarceni ya
shugabata kiyi sani cewa kinyi mini
Tambayoyi ne masu matukar
muhimmanci a cikin wannan tafiya
tamu, kuma wadanda zasu dauki
dagon lokaci ina yi miki bayaninsu.
Da farko dai, abokin tafiyarmu
wanda zamu fara tafiya nema ba
wani bane face JARUMA SHUMAIRA
'yar mafarauci IMSHAL.
A halin yanzu duk duniya babu
wani mahaluki wanda yafi
shumaira ibn imshal sanin sirrin
daji da iya farauta da kuma juriyar
wahala.
Kafin mu isa kogon KITABUL SIHIR
inda aka ajiye littafin TSATSUBA sai
mun keta ta cikin wadansu
dazuzzuka guda uku.
A cikin Daji na farko sai mun shafe
wata shida muna tafiya sannnan
zamu je karshensa.
A cikin wannan daji wanda aka
yiwa lakabi da SHAJARUL SHALJUMA
akwai mugayen dabbobi da
mugayen tsuntsaye wadanda kaifi
da tsini baya tasiri a jikinsu, haka
ma tsafi baya aiki a kansu.
Babu abinda zai ceci mutum daga
shairrinsu face ya san sirrinsu kuma
ya kware a iya farauta gamida da
jurewa wahala.
Lallai idan babu jagorancin jaruma
shumaira bamu isa mu ratsa ta
cikin dajin shajarul shaljuma ba a
raye.
Abokin tafiyarmu na biyu kuwa ba
kowa bane face jaruma LARIFAT
ma'abiciyar basira da hangen nesa.
Daji na biyu wanda ke gaban dajin
shajarul shaljuma ana kiransa da
suna UJURUL MAJNAN....
Koda mahaifiyar Humairu tazo dai-
dai nan a zancenta sai suka jiyo
takun sawayen giwaye daga can
nesa a guje an durfafo inda suke.
A rude kuma a dimauce su Humairu
suka mike tsaye zumbur suka dora
iyayensu da masoyansu akan
wadannan dawakai biyu suka kada
dawakan suka yi cikin daji da gudu,
suma suka bi bayansu cikin
azababben gudu.
Suna cikin gudun ne suka waigo sai
suka ga ashe ragowar dakarun nan
ne na sansanin sarki larbusa su
goma sha biyar bisa kan giwaye
suka biyo sawunsu.
Nan fa Humairu da Hashlar suka
kara kaimin gudunsu zuciyoyinsu
cike da tsananin fargaba da tashin
hankali saboda tsoron kada
dakarun su riskesu su hallaka
iyayensu da masoyansu.
WANE IRIN MASIFAFFEN YAKI ZA'A YI
A CAN KOFAR BIRNIN LURHAJ
TSAKANIN RUNDUNAR SARKI ARYAN
DA RUNDUNAR SU SARKI LARBUSA? "
SHIN LAILA ZATA CIKA ALKAWARIN
DAKE TSAKANINTA DA ZURAIHA
MATAR SARKI LARBUSA? "
SHIN SARKI LARBUSA YANA CIKAo
BURINSA NA MALLAKAR NAHIYAR
GABA DAYA? "
WACCE IRIN JARUMTAKA DAN SARKI
ARYAN ZAI TASO DA ITA, KUMA ZAI
DAWO BIRNIN LURHAJ NE YA KARBI
KARAGAR MULKINSA? "
Mu hadu a littafin Dugunzuma
kashi na uku don jin cigaban
wannan kasaitaccen labari.

Dugunzuma!!!
LITTAFI NA 3
PART 1
Mr NASEER SHEHU
******
Lokacin da su Humairu suka ci gaba
da falfala azababben gudu a cikin
daji tare da iyayensu da masoyansu
wadanda ke bisa dawakai, duk
sa'adda suka waigo bayansu sai
suga har yanzu wadanan dakaru na
sarki larbusa su goma sha biyar na
nan biye dasu sun kasa tsere musu
kuma tazarar dake tsakaninnsu
bata wuce taku goma sha ba,
alhalin sun yi wannan tseren gudu
na akalla tsawon sa'a guda.
Nan take zuciyar Humairu tayi
bakikkirin yaji dukkan tsoro ya kau
daga cikin zuciyarsa domin ya
fuskanci cewar gudu fa ba mafita
bane,
Domin idan aka kure musu gudun,
biyu babu za'a yi wato za'a kashesu
kuma a kashe iyayen nasu gamida
da masoyan nasu.
Koda gama aiyana Hakan sai
Humairu yaja ya tsaya cak!
Shima Hashlar yana ganin tsayuwar
Humairu sai ya tsaya ya dubeshi
cikin tsananin mamaki da kaduwa
yace, "ya kai abokina me yasa kayi
ganganci ka tsaya alhalin ka san
cewa ba zamu iya ba da wadannan
dakaru su goma sha biyar? "
Humairu yace, gudunmu bashida
wani amfani domin ba zamu iya
tsere musu ba kuma idan suka
riskemu biyu babu zamu yi, babu
mu, babu iyayenmu da
masoyanmu.
Idan kuwa muka tsaya muka yaki
wadanan dakaru kafin su kashemu
iyayenmu da masoyanmu sun yi
nisa a cikin daji sossai sun basu
ratar da baza su iya riskarsu ba.
Abinda nake so da kai shine, mu
tsaya mu yi yakin nan da dukkan
ranmu da karfinmu kuma da
madaukakiyar zuciya yadda koda
zasu kashemu muma sai munyi
musu mummunar barna don haka
kada mu taba cire tsammanin sa'a
da nasara akan abokan gaba.
Koda gama fadin Hakan sai
Humairu ya zare takobinsa ya
dagata sama yana mai kwarara
uban ihu mai tsananin firgitarwa
wanda ya cika dajin gaba daya.
Take shima Hashlar yayi koyi dashi.
A wannan Lokaci wadannan dakaru
guda goma sha biyar sun kara
tunkarosu a sukwane kuma a
fusace suna masu karawa
giwayensu kaimi saboda sun gane
dabarar dasu Humairu ke shirin yi
tason su tserar da rayuwar
iyayensu da masoyansu.
Koda ya rage saura bai fi taku
goma ba dakarun su iso inda suke
sai Hashlar da Humairu suka
yunkura cikin zafin nama suka ruga
suna masu taryarsu.
Kamar hadin baki sai duk su biyun
suka daka tsalle sama Izuwa kan
dakarun.
Duk da cewa Hashlar hannu daya
gareshi sai da yai amfani da daya
hannun lafiyayye ya kaiwa dakaru
uku sara da takobinsa a lokaci
guda, a hammatarsa kuwa ta hagu
bangaren da yankakken hannun
nasa yake yana makale da dogon
mashi.
Cikin bakin zafin nama ya zabtare
makogwaron dakarun biyu da
kaifin takobinsa kuma ya soke
wadansu biyun da mashinsa, duka
su shidan suka rikito kasa daga kan
giwayensu suka kama shure -
shuren mutuwa.
Shi kuwa Humairu yana sama ya
kwashe rabin kwanyar dakaru uku
da kaifin takobinsa kuma ya soki
tsakiyar kawunan dakaru biyu da
wata zabgegiyar wuka tasa, su
biyar din a lokaci guda suka rikito
kasa matattu ko shurawar kirki
dayansu baiyi ba.
A Lokacin Humairu da Hashlar suka
duro can bayan dakarun kafafunsa
suka doki kasa suna masu tayar da
kura.
Cikin tsananin mamaki da takaici
ragowar dakarun bakwai suka yi
tirjiya da giwayensu suka juyo suka
fuskancesu suna tsuma da gurnani
kamar namijin kure.
A wannan Lokaci su kansu su
Humairu sunyi tsananin mamaki
yadda akayi suka yi wannan
gagarumar jarumta wacce basu
taba yin irinta ba.
Abinda basu sani ba shine, ya yin
da zuciya ta hasala kuma rai ya tari
mutuwa, tofa gangar jiki zata iya
aiwatar da abinda baza iya ba.
Bayan anyi kallon kallo na 'yan
dakiku tsakanin wadanan dakaru
bakwai dasu Humairu sai dakarun
suka sauko daga kan giwayensu
suka daga makamansu sama suna
masu gyara tsayuwa.
A wannan Lokaci ne Humairu ya
dubi Hashlar yace, "tunda dai kai
hannu daya gareka ka barni da
mutum hudu kai kuma ka kara da
mutum ukun. Inason mu jajirce iya
karfinmu da kokarinmu har sai
mun ga iya inda karfinmu ya kare.
Ka sani cewa bamu da sauran abin
alfahari face mu ceci rayuwar
iyayen namu da masoyanmu.
Sannnan kada ka manta cewar ina
da alkawari a kaina na kubatar da
rayuwar matar sarki da dan da ta
haifa don haka ta kowanne hali
lallai inason mu tsira da
rayuwarmu. Musamman idan
munason mafarkinmu na sake
kafuwar kasarmu ya tabbata.
Koda Humairu yazo nan a zancensa
sai ya dubeshi yana mai gyada kai
yace, ai kuwa zan jajirce iya karfina
don ganin mun cimma nasara.
Gama fadin Hakan keda wuya sai
Humairu da Hashlar suka yi kukan
kura a lokaci guda suka falfala da
azababben gudu Izuwa kan
wadannan dakaru guda bakwai.
Ai kuwa suma dakarun sai suka
falfalo da gudu suka taresu aka
ruguntsume da azababben yaki.
Kaico! Wuya bata da dadi kuma
tashin hankali ba'a sa masa rana.
Lokacin da aka fara wannan
kazamin yaki sai kowa ya gane
cewa shayi ba ruwa bane.
Domin babu wanda yake da
tabbacin cewa zai iya tsira da
rayuwarsa saboda karfi ya hadu da
naci gamida juriya da zafin nama.
Kiri-kiri gashi dai dakarun sunfi su
Humairu karfi, girma da iya yaki,
amma sai karfi yake naman zuwa
daya domin sun zamewa juna
alakakai, wato kowanne bangaren
yana jin jiki.
Wani abin mamaki shine, dakarun
suna yakin ne da dukkan karfinsu
kuma a fusace, su ma su Humairu
haka.
Nan fa suka ci gaba da kaiwa
junansu sara da suka na hauka ba
kakkautawa.
Tabbas in ba don Allah ya baiwa su
Humairu tsagwaron zafin nama ba
da naci da tuni dakarun sun
hallakasu farat daya saboda
bambancin karfi da iya yakin a
baiyane yake, kuma sannnan Salon
fadan da dakarun keyi yafi nasu
Humairu, saboda sun hada da kai
naushi da bugu.
Tabbas su Humairu suna iya kare
saran dakarun da sukarsu, amma
kuma sai suka kasa tare naushinsu
da bugunsu na hannu da kafa.
Nan fa suka fara hada musu jini da
majina a baki da hanci, amma
kuma basu sami nasarar sarar
jikinsu ba sai dai ga dukkan alamu
idan aka sake dan jimawa a hakan
dakarun zasu sami nasarar
hallakasu farat daya.
Ana cikin haka ne wani badakare
wanda yafi sauran dakarun karfi da
zafin nama ya sami nasarar yankan
Hashlar a gadon baya, take gadon
bayan ya dare, jini yai feshi. Hashlar
ya tsandara uban ihu ya yi baya
taga-taga zai kife a Lokacin da
dakaru hudu suka yi kansa da nufin
su daddatsashi.
Cikin bakin zafin nama Humairu yai
wuf ya janyeshi Izuwa gefe daya
takubban dakarun suka sari kasa,
kasar ta daddare kai kace girgizar
kasa a akayi.
Damar da wannnan badakare mai
karfi da zafin nama ya sake samu
kenan ya sari Humairu a cinya, take
cinyar ta dare, jini yai tartsuwa,
amma saboda tsananin juriya irinta
Humairu bai yarda ya fadi kasa ba
sai ya juyo a matukar fusace yaci
gaba da yaki da wani irin
azababben karfi, duk da cewa jini
na zuba a cinyarsa bai sare ba.
Ba komai ne ya sa Humairu ya sami
wannan gagarumin karfi ba face
tunowa da cewar idan fa basu sami
nasara ba a wannnan yaki lallai
iyayensu da masoyansu ma sai sun
zama gawa.
Cikin sa'a kuwa Humairu ya
shammaci dakarun yayi wata irin
katantanwa a kasa a tsakiyarsu ya
sassare kafafunsu suka zube kasa
su taran a lokaci guda suna
zubarda jini tare da tsandara uban
ihu mai firgitarwa.
Kafin su kara mikewa tsaye
Humairu ya kara dankarawa
kowannensu sara a tsakiyar kai.
Duka su taran sai suka zama gawa,
ya zamana cewa sauran su shida
kacal.
Kuma sai Hashlar wanda ke kwance
a can gefe daya, bayansa yai kaca-
kaca da jini yana ta faman
numfashi kamar ransa zai fita.
Nan fa aka fara kallon kallo
tsakanin Humairu da ragowar
dakarun shida suna masu matukar
mamakin yadda akayi ya sami
wannnan gagarumar nasara har ya
kashe musu mutum tara a lokaci
guda, kuma suna shakkar su
shigoshi.
Shima Humairu duk da cewa ya
sami wannan nasara sai yaji yana
shakkar ya sake tarar ragowar
dakarun shida a Lokacin, domin har
jiri ya Fara dibarsa sakamakon
raunin dake kan cinyarsa mai zubar
da jini.
Dan kallon kallon da aka tsaya yi ne
ya bashi damar da yai wuf ya yagi
rigarsa ya daure raunin dake cinyar
tasa.
Faruwar hakan keda wuya sai yaji
ya daina jin wannnan jiri dake
damunsa
Amma da ya dubi dan uwansa
Hashlar wanda ke kwance face-face
cikin jini sai zuciyarsa ta kama
tafarfasa kamar zata kone, jikinsa
gaba daya ya kama tsuma saboda
tsananin fushi saboda ya tuna cewa
yanxu fa a cikin abokansa su
bakwai su biyun ne fa kadai suka
rage kuma idan bai gaggauta
tsayar da jinin dake zuba ba a
bayan Hashlar shima zai iya rasa
rayuwarsa.
Nan take Humairu ya wangame
bakinsa ya takarkare ya kwarara
uban ihu ya ruga Izuwa kan
dakarun aka sake ruguntsumewa
da sabon yaki.
Wannan karon sai ya sauya salon
fadan ya hada
Da tsalle-tsalle da kwance kwance
yana kai musu hari da gudu ta ko
ina.
Nan da nan kuwa ya fara samun
lagonsu ya rikitasu har ya sami
nasarar dukan kijirnansu sau uku
da kafarsa a sama.
Duk da sadaukantakarsu, karfinsu,
juriya da naci irin na wadanan
dakarun sai da suka yi baya taga-
taga kamar zasu fadi amma kuma
saboda naci sai su mike su ci gaba
da kawo mishi sara da suka.
Al'amarin da ya firgita Humairu
kenan
yana mai ci gaba da kare kansa
gamida mayar da martani har ma
yana hadawa da kai naushi da
bugu.
Duk da hakan sai yaga suma
dakarun sun kara kaimi fiye da
farko ma.
A sannnan ne ya gane cewa lallai
wadanan dakaru ne na musamman
ne wadanda suka sami horo mai
tsanani.
Sai da Humairu ya dage sossai
sannnan ya fara samun nasara akan
su.
Nan fa ya rinka saransu da
yankansu yana bazar dasu a kasa,
cikin kankanin lokaci ya kashe
mutum biyar daga cikinsu.
Ya zamana cewa saura mutum
guda ya rage kuma ba wani bane
face wannan badakare mai karfin
damtse da zafin nama fiye da na
sauran yan uwansa.
Nan fa badakaren yaja da baya
cikin dan alamun tsoro ya tsaya
cak!
Ya zamana cewa shi bai gudu ba
kuma bai afka masa ba.
Humairu ya sake waigawa ya dubi
inda Hashlar ke kwance yaga har
numfashinsa ya fara sarkewa,
kawai sai ya juya ya nufi inda
Hashlar ke kwance yayi kamar ma
ya manta da wannnan badakare
dake tsaye a bayansa.
Koda ganin haka sai badakaren ya
dubi gefensa ya hango wata kwari
da baka a kasa, kawai sai ya nufi
inda kwarin take yana waigen
Humairu da nufin ya dana akan
bakan ya harbeshi.
Abinda bai sani ba shine, humairu
na lura dashi, kuma yana kallonsa
ta wutsiyar ido.
Koda badakaren ya dauki kwarin ya
dana akan bakan. Kafin ya dago
sama ya harbawa Humairu kibiyar
tuni shi Humairu ya zaro wata
sirriyar wuka mai tsawo kaifi da
tsinin tsiya ya wurgawa badakaren,
nan take wukar ta nutse a
makogwaronsa ta fito ta wuyansa.
Kawai sai badakaren ya sandare a
tsaye ya bingire kasa matacce ko
shurawa bai yi ba.
Cikin hanzari Humairu ya karasa
kan Hashlar ya shiga kokarin
tsayarda jinin dake zuba a jikinsa
don ceto rayuwarsa.
Da kyar da sidin goshi Humairu ya
sami nasarar ceto rayuwar Hashlar
ya farfado kuma ya dawo cikin
haiyacinsa.
Koda ganin haka sai farin ciki ya
lullube Humairu ya mike tsaye da
sauri shima ya sawa raunikan
jikinsa magani sannnan ya goya
Hashlar a bayansa ya sake
runtumawa da gudu dauke dashi
Izuwa cikin daji domin su riski
iyayensu da masoyansu.
Wannan shine abinda ya ga su
jarumi Humairu bayan sun yi
mummunan yaki da dakarun sarki
larbusa.
*
A can kofar birnin LURHAJ kuwa su
sarki Aryan sun yi dafifi a cikin
shigar yaki, sarki Aryan ne tsaye a
gaban rundunar dakarun kowa ya
zuba idanu yana kallon Ta inda
abokan gaba zasu bullo.
Sai da aka shafe sama sa'a uku a
tsaye cirko cirko aka yi tsit!
Ba'a jin sautin komai face na iskar
dake kadawa.
Kwatsam! Sai aka hango kura daga
can nesa ta turnuke sararin
samaniya. Daga nan kuma sai aka ji
kasa ta kama rawa da kara tamkar
za'a yi girgizar kasa.
Ashe ba komai bane ya haddasa
hakan ba face tsananin yawan
takun sawun dakarun sarki larbusa.
Al'amarin da ya fara tayar da
hankalin gaba dayan dakarun sarki
ARYAN kenan zuciyoyinsu suka fara
sarewa.
Koda dakarun suka kara matsowa
kusa
Sai dakarun sarki ARYAN suka
dimauce kuma suka firgita ainun,
saboda ganin yawan dakarun,
girman jikinsu da kwarjininsu,
domin sun san cewa ko ba a gwada
ba linzami yafi karfin bakin kaza.
Nan fa dakarun sarki ARYAN suka
fara ja da baya-baya. Suna kokarin
komawa cikin gari.
Koda ganin haka sai sarki Aryan ya
fusata ainun ya daka musu tsawa
mai karfin gaske wacce tasa suka
kara firgicewa fiye da farko
sannnan suka shiga taitayinsu
kowa ya dawo inda yake ya tsaya.
Sarki Aryan ya juya ya fuskanci
dakarun nasa yace, "Ya kai ku
dakaruna shin kuna ji kuna gani
zaku bari ne a yiwa matayenku
fyade a kashe iyayenku, kuma a
kame 'ya ' yayenku a maishesu
bayi?"
Shin kuna ji kuna gani za'a kwashe
dukiyoyinku ne kuma a kone
gidajenku da birninku wanda
iyayenku da kakanninku suka shafe
shekara da shekaru suna faman
wahalar mayarda shi maraya?"
To ku sani cewa dan halak baya
yarda aci zarafinsa dana iyalinsa ko
dukiyarsa sai dai ya mutu akan
kare kimarsa da martabarsa.
Ku tsaya kuyi yaki, ku zubar da
jininku don kare kimarku da
mutuncinku.
Koda sarki Aryan yazo nan a
zancensa sai gaba dayan dakarun
nasa suka ji kamar an cire musu
dukkan tsoro da fargaba daga cikin
zukatansu.
Nan take jikinsu ya kama tsuma
suka ji ma babu abinda suke so
sama da su ga karasowar abokan
gaba a fara gurmuzu. Dugunzuma!!!
LITTAFI NA 3
PART 2
Mr NASEER SHEHU TEARLOW
******
Koda ganin haka sai sarki Aryan ya
fusata ainun ya daka musu
tsawa mai karfin gaske wacce tasa
suka kara firgicewa fiye da farko
sannnan suka shiga taitayinsu
kowa ya dawo inda yake ya tsaya.
Sarki Aryan ya juya ya fuskanci
dakarun nasa yace,
"Ya ku dakaruna shin kuna ji kuna
gani zaku bari ne a yiwa
matayenku fyade a kashe iyayenku,
kuma a kame 'ya'yayenku a
maishesu bayi?"
Shin kuna ji kuna gani za'a kwashe
dukiyoyinku ne kuma a kone
gidajenku da birninku wanda
iyayenku

Please Login or Register in order to submit comment