Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

alhalin ka san
cewa yaki akeyi acan? "
Humairu ya gyada kai cikin alamun
tausayi yace, na rigaya na yiwa
sarki ARYAN alkawarin cewar zan
kubatar da rayuwar matarsa da
dansa.
Don haka dole ne na koma birnin
LURHAJ yanzu.
Sarki Aryan ya nuna mini wata
barauniyar hanya da za'a iya fita
daga cikin gidan sarautarsa, kuma
ta can bayan gari za'a shiga.
Babu wanda yasan wannnan hanya
sai shi kadai, sai kuma ni da ya
nuna mini ita, don haka ina son ku
kwantar da hankalinku.
Nayi muku alkawari zan dawo
gareku a raye ".
Koda jin wannnan batu sai hawaye
ya zubowa mahaifiyar Humairu da
laila suka rungumeshi a lokaci guda
suka kama kuka.
Al'amarin da ya baiwa Hashlar,
Huzaila da mahaifiyar Hashlar
tausayi kenan suma idanunsu suka
ciko da kwallah.
SHIN HUMAIRU ZAI SAMU NASARAR
KOMAWA GIDAN SARAUTAR YA
KUBATAR DA RAYUWAR MATAR
SARKI YA DAWO A RAYE? "
YAUSHE SU HUMAIRU ZASU YI GAMO
DA SARKI LARBUSA, IDAN SUN HADU
MAI ZAI FARU? "
Mu hadu a Dugunzuma 4 don jin ci
gaban wannnan kasaitaccen labari.
****** Dugunzuma!!!
LITTAFI NA 4
PART 1
NASEER SHEHU
****
Lokacin da su jarumi Humairu
kuwa, tun da suka kama hanya
suka yi
ta gudu a cikin daji tare da
iyayensu da masoyansu su Laila,
basu
yada zango ba a ko ina har sai da
suka iso iyakar birnin LURHAJ da
wata kasa da ake kira ZAITUN,
sannnan suka tsaya.
A sannnan ne Humairu da Hashlar
suka tsugunna a kasa suna ta
faman haki kamar ransu zai fita
saboda tsananin gajiya, saboda sun
shafe kusan sa'a tara kenan suna
gudu basu huta ba.
Sai da suka dawo cikin haiyacinsu
sannnan suka sha ruwa, suma
iyayen nasu da 'yan matan nasu
suka fito da abinci aka ci aka sha.
Dama a can sansanin su sarki
larbusa sun samu sun debo guzuri.
Bayan kowa ya nutsu sai Humairu
ya mike tsaye ya dubi
mahaifiyarsa da masoyiyarsa laila
yace, "Ni anan zan rabu daku,
dole ne na koma can birnin LURHAJ
yanzu.
Koda jin wannnan batu sai mamaki
da tsoro ya kama mahaifiyar
Humairu da Budurwаrsa laila.
Mahaifiyar tasa ta dubeshi cikin
alamun tsananin damuwa tace,
"akan wane dalili zaka koma Izuwa
birnin lurhaj yanzu alhalin ka san
cewa yaki akeyi acan? "
Humairu ya gyada kai cikin alamun
tausayi yace, na rigaya na yiwa
sarki ARYAN alkawarin cewar zan
kubatar da rayuwar matarsa da
dansa.
Don haka dole ne na koma birnin
LURHAJ yanzu.
Sarki Aryan ya nuna mini wata
barauniyar hanya da za'a iya fita
daga cikin gidan sarautarsa, kuma
ta can bayan gari za'a shiga.
Babu wanda yasan wannnan hanya
sai shi kadai, sai kuma ni da ya
nuna mini ita, don haka ina son ku
kwantar da hankalinku.
Nayi muku alkawari zan dawo
gareku a raye ".
Koda jin wannnan batu sai hawaye
ya zubowa mahaifiyar Humairu
da laila suka rungumeshi a lokaci
guda suka kama kuka.
Al'amarin da ya baiwa Hashlar,
Huzaila da mahaifiyar Hashlar
tausayi kenan suma idanunsu suka
ciko da kwallah.
Mahaifiyar Humairu ta janye jikinta
daga cikin nasa suka fuskanci juna
a Lokacin da itama laila ta janye
jikinta ta sunkui da kanta kasa.
Mahaifiyar Humairu ta dubeshi
sa'adda hawaye ya subuto mata
tace, "Ya kai dana tun da na haifeka
duk abinda ka sa a gabanka kana
samun nasara, ba'a taba samun
akasi ba.
Amma ka sani cewa wannan karon
zuciyata tana rawa, domin na
firgita da Al'amarin sarki larbusa da
dakarunsa, ina ji a jikina kamar
idan muka rabu ba zamu sake
saduwa ba.
Koda gama fadin Hakan sai ta sake
rungume Humairu ta fashe da
sabon kuka.
Da kyar Humairu ya rarrasheta tayi
shiru ya kara tabbatar mata da
cewa lallai komai RINTSI DA
TSANANI sai ya dawo gareta.
Daga nan sai ya matsa gaban laila
ya rike kafadunta, ita kuwa sai ta
dago kai ta dubeshi cikin yake tace,
"Baka taba yi mini alkawari ka saba
ba, don haka wannan karon ma
idan har ka karya mini alkawari
kashe kaina zanyi domin ba zan iya
rayuwa ba in babu kai.
Ka tuna cewa an kashe uwata da
ubana sa'adda aka kawo hari
kauyenmu,
Yanzu ba ni da kowa sai kai, kaine
uwata kaine ubana.
Lallai ta kowanne hali ka cika
alkawari ka dawo gareni a raye
domin muyi aure.
Koda jin wannnan batu sai fuskar
Humairu ta fadada da murmushi
yace, Ai kuwa laila zan kasance mai
cika alkawari a gareku keda
mahaifiyata."
Laila tace "Na baka kwana daya da
yini daya jal ka dawo garemu kafin
faduwar rana.
Idan har rana ta fadi baka dawo ba
sai dai kazo ka riski gawata, ko da
kuwa ka tsira da rayuwarka."
Koda jin wannnan batu sai hawaye
ya zubowa Humairu yace, "kada
kiyi gaggawa ya masoyiyata, lallai
koda mutuwa zanyi sai munyi
bankwana."
Gama fadin Hakan keda wuya sai
Humairu ya karasa wajen Hashlar
ya tsaya daf! Dashi yadda har suna
iya jin numfashin juna, suka tsaya
suna kallon juna kawai har tsawon
'yan dakiku, sannnan suka
rungume junansu.
Daga can sai Humairu ya janye
jikinsa daga cikin nasa ya dubeshi
yace, "Ya kai abokina ka sani cewa
mu biyu ne rak!
Muka rage daga cikin abokanmu
don haka duk yadda za'a yi komai
rintsi da tsanani inason mu rayu
domin mu kai Izuwa zamanin daza
muga dawowar kasarmu.
Idan kun shiga cikin birnin zaitun
ku batarda kamanninku kada ka
bari a shaidaku, kuma kada ka bari
a san masaukinku.
Lallai gobe kuje tsakiyar kasuwar
birnin nan a gabannin faduwar
rana anan zan riskeku.
Idan ka kiyaye hakan lallai zamu
sake saduwa.
Da wannnan furuci nake yi maka
sallama sai gobe idan muna da
rabon sake saduwa."
Koda gama fadin Hakan sai
Humairu yaje ya kama dokin dasu
laila suka hawo yai tsalle ya haye
kansa ya juya da baya ya zabureshi
da gudu Izuwa cikin daji.
Su kuwa su Hashlar sai suka bishi
da kallo kawai cikin tsananin
damuwa da tashin hankali tamkar
su aza hannu aka su fashe da
matsanancin kuka.
Humairu yaci gaba da keta
dazuzzuka akan dokinsa yana ta
tsala uban gudu na gaban
kwatance, amma ji yake kamar ya
sauka daga kan dokin yayi gudun
da kafafunsa saboda gani yake
kamar dokin baya sauri.
Sai da ya shafe sa'a uku cur! A haka
har ta kai cewa dokin ya fara gajiya
yana rage karfin gudunsa a hankali,
kai har ma ya koma tafiyar sauri-
sauri, gudu-gudu, sannnan ya koma
sassarfa.
Al'amarin da ya fusata jarumi
Humairu kenan, domin yana cikin
tsananin sauri ne, burinsa kawai
shine ya isa cikin birnin LURHAJ
kafin su sarki larbusa su sami
nasarar fasa kofar birnin su shiga
cikin gidan sarautar inda su
gimbiya lushairat suke, wato matar
sarki Aryan.
Dama wani boka da ya riska a cikin
wani daji wanda ya fito daga wata
kasa dabam yayi masa bincike ya
gaya masa cewar sarki larbusa zai
karya kofar birnin lurhaj a dai-dai
Lokacin da magariba ta doso.
Humairu ya gama auna cewa zai
iya isa bayan birnin lurhaj a cikin
sa'a biyar dai-dai, a Lokacin da
saura baifi rabin sa'a ba kenan
magarib ta doso.
Koda Humairu yaga gashi yanzu
sa'a uku kadai da fara tafiyarsa
amma har dokinsa Ya sare sai
hankalinsa ya dugunzuma ainun,
Cikin tsananin fishi yaja linzamin
dokin nasa yayi turjiya sannnan ya
duro kasa ya falfala da azababben
gudu Izuwa cikin dajin ko waigowa
bai yi ba bare yaga halin da dokin
nasa ke ciki.
Humairu yaci gaba da tsala gudu ba
sassauci, babu daga kafa, ba gajiya,
tamkar jikinsa bana jini da tsoka
bane na karfe ne,
Sai da Humairu ya shafe sa'a daya
da rabi yana wannnan gudu
sannnan ya fara sarewa.
Gajiya da haki suka isheshi gamida
tsananin kishirwa, inda yaji
makogwaronsa ya bushe kamar zai
mutu.
Bisa dole ya dakata ya zaro battar
ruwansa ya kwalkwala.
Hutun dakika talatin kawai yayi
sannnan ya mike zumbur yaci gaba
da falfala azababben gudu.
Sai gifta bishiyoyi, duwatsu da
kwazazzabai yake kamar giftawar
tauraruwa mai wutsiya.
Saboda da karfi gudun nasa wani
Lokacin ma har tashi sama yake
yana tsalleke abubuwa.
Bayan cikar rabin sa'a dai-dai ya
fara juyo ihun mazaje.
Nan fa yasan cewa ya kusanci
birnin LURHAJ, kuma gashi a
wannan Lokaci yamma tayi sossai
hasken rana ya fara disashewa.
Nan fa hankalinsa ya kara
dugunzuma, ya kara kaimin gudun
nasa.
Wohoho! Kaga maza masu
DAKAKKIYAR ZUCIYA! Wadanda basu
san wani abu ba wai shi tsoro ko
karayar zuci.
Ko yaushe a cikin sa ran samun
nasara suke.
Lokacin da Humairu ya kara
kusantar bayan birnin LURHAJ sai
ya firgita ainun sakamakon hangen
yadda hayaki ya turnuke sararin
samaniya a cikin tsakiyar birnin,
kuma ya rinka jiyo Iface-iface da
kururuwar mata da maza wanda ya
cika daji da amsa kuwwa.
Nan fa zuciyarsa ta kama bugawa
da karfi ya fara tunanin cewa lallai
ya makara, aikin gama ya gama,
wato tuni a wannan Lokaci su sarki
larbusa sun fasa kofar birnin
LURHAJ sun shiga ciki.
Duk da aiyana Hakan a zuciyarsa sai
ya yanke hukuncin ya karasa yaga
zahiri da idanunsa ko da kuwa
shima zai rasa rayuwarsa domin
mutuwarsa itace sauki akan kasa
cika alkawarin da ya daukarwa
sarki Aryan.
Wani katon kududdufi ne a karshen
bayan birnin LURHAJ.
Koda ya iso bakin gabar wannan
kogi sai ya daka tsalle ya fada
cikinsa yayi nutso Izuwa
karkashinsa ya kama iyo yana
karawa gaba.
Sai da yayi 'yar doguwar tafiya
sannnan ya dago sama ya shaki
numfashi ya sake komawa yaci
gaba da iyo.
Sai da yayi hakan sau uku sannnan
ya riski wani dogon bututu na karfe
wanda ya lume a cikin kasan
ruwan.
Ba tare da fargabar komai ba ya
kunna kai cikin bututun sululu!
Kamar tafiyar kifi, yayi ta tafiya a
cikinsa sai gashi ya iso karshensa,
ashe magudanar ruwan da ake
amfani dashi a cikin gidan sarautar
ne.
Tsulum! Sai ga Humairu a cikin
tsakiyar gidan sarautar sarki Aryan.
Yana baiyana yaga ana fafata
kazamin yaki, da dakarun sarki
larbusa nata ragargazar dakarun
sarki Aryan tamkar suna sassabe a
gona.
Cikin hanzari ya zare takobinsa ya
ruga da gudun tsiya Izuwa inda
turakar gimbiya lushairat take.
Ai kuwa sai dakarun sarki ya suka
hangoshi suka yi caa! Akansa da
nufin su gididdibashi.
Wohoho! Idan zuciya ta fusata sai
tsoro ya kauce, kuma jarumtaka ta
ban al'ajabi ta bijiro.
Nan take Humairu ya zamo tamkar
shaidani a cikin wadannan dakaru
ya zamana cewa yana gudu a
tsakiyarsu yana kaucewa saransu
da sukansu, kuma yana mai da
martani.
Yarinka tsalle -tsalle tamkar dan
biri akan bishiyoyi.
Ai kuwa sai ya rinka saransu akai
da wuya suna zubewa kasa yana
kutsawa da karfin tsiya cikin
azababben zafin nama na ban
al'ajabi wanda shi kansa yayi
matukar mamakin yadda akayi ya
sami wannnan jarumtaka alhalin
dakarun sun fishi karfin damtse da
iya yaki.
Shi dai jarumi Humairu abinda ya
sani shine, yana yin wannnan yaki
ne da dukkan karfinsa da ransa da
jikinsa, ko yai rai ko ya mutu.
Kafin dakarun su ankara tuni ya
tsere ya basu tazara mai dimbin
yawan gaske, ya rigasu zuwa inda
kofar turakar gimbiya lushairat
take.
Tun daga nesa da dakarun dake
tsaron kofar suka hangoshi kuma
suka hango abokan gabar dake
biye dashi sai suka yi sauri suka
bude masa kofar,yana shigewa
suka mayar da kofar suka rufe
saboda dama sun san zai zo don
sarki Aryan ya sanar da su.
***
SUNA SHIGEWA NIMA NA MAYAR DA
LITTAFIN NA RUFE, DUGUNZUMA!!!
LITTAFI NA 4
PART 2
LITTAFIN YAKI
NASEER SHEHU TEARLOW
*******
Shi dai jarumi Humairu abinda ya
sani shine, yana yin wannnan yaki
ne da dukkan karfinsa da ransa da
jikinsa, ko yai rai ko ya mutu.
Kafin dakarun su ankara tuni ya
tsere ya basu tazara mai dimbin
yawan gaske, ya rigasu zuwa inda
kofar turakar gimbiya lushairat
take.
Tun daga nesa dakarun dake tsaron
kofar suka hangoshi kuma suka
hango abokan gabar dake biye
dashi sai suka yi sauri suka bude
masa kofar, yana shigewa suka
mayar da kofar suka rufe saboda
dama sun san zai zo don sarki
Aryan ya sanar da su.
Ita kuwa gimbiya lushairat bata
san da zuwansa ba, tana can cikin
kuryar dakinta ta rungume jaririnta
tana ta faman rusa kuka,
Kuyanginta na tayata kukan.
Acan bakin kofar turakar gimbiya
kuwa, dakaru na rufe kofar sai
suma suka ruga da gudu suka tari
abokan gaba aka ruguntsume da
yaki.
Duk da dai cewar anfi karfinsu
amma saboda suna da zuciyar kare
martabarsu da kishin kasarsu basa
mutuwa farat daya sai bayan bakin
gurmuzu.
Lokacin da Humairu ya iso cikin
tsakiyar turakar gimbiya lushairat a
guje rike da takobinsa wacce ta
rine da da jini, sai gimbiya lushairat
da kuyanginta suka firgice suka
kama ihu suna zaton ko abokan
gaba ne suka karaso.
Cikin tsawa Humairu ya dubesu
yace, "Ni dan uwanku ne haifaffen
wannan kasa.
Yake gimbiya kiyi sani cewa nine
jarumi Humairu wanda sarki ya
umarta da ya kubatar da rayuwarki
da ta jaririnki daga cikin birnin nan.
Maza ki goya jaririn naki a bayanki
sannnan nima na goyaki a bayana
mu fice da gudu daga cikin gidan
nan.
Koda jin haka sai lushairat ta
dakawa Humairu tsawa tace, " kai
waye har da zan hada jikina da
naka?"
Bazan ci amanar mijina ba, duk da
cewa nasan cewa ya mutu. "
Humairu ya ruga Izuwa gaban
lushairat da sauri yace, "Bamu da
Lokacin gardama,ai lalura ce ta
janyo hakan.
Ki hanzarta yin abin da na umurceki
da yi in ba so kike keda jaririn naki
ku mutu ba!"
Lushairat tace, "Ai gwara mu mutu
tun da dai mijina ya mutu, bamu da
sauran wani gata, babu mai ka
re...."
Kafin ta gama rufe bakinta tuni
Humairu ya doki wuyanta da
hannunsa, kawai sai ta Sulale zata
fadi kasa sumammiya.
Cikin zafin nama ya tallafota tare
da jaririn na ta.
Cikin dakiku kadan ya goyata a
bayansa. Su kuma kuyangin nata
suka daure masa jaririn nata a
bayanta.
Kawai sai Humairu ya juya da baya
da gudu ya nufi inda ya fito rike da
takobinsa.
Yana isowa bakin kofar turakar
yayi arba da dakarun sarki larbusa
Kimanin su dari biyu, tuni sun gama
karkashe gaba dayan dakarun dake
gadin kofar.
Ita kanta kofar sun ragargazata.
Nan fa aka yi kallon-kallo tsananin
dakarun da Humairu, suka gane
cewa lallai matar sarki Aryan ce da
jaririnta a goye a bayansa, kuma
dama umurnin da aka basu shine
duk inda matar sarki Aryan take da
jaririnta a kamosu a kashesu a
kaiwa sarki larbusa gawarsu.
Shi kuwa Humairu abinda yazo
masa a rai shine, dole ne fa ta
kowanne hali ya kashe gaba dayan
wadanan dakaru da suka yi arba
dashi, in ba haka ba kuwa dayansu
zai iya kai labarinsa inda su sarki
larbusa suke azo a gama dashi.
Nan take jikin Humairu ya kama
tsuma yaji wani irin gagarumin
sabon karfi ya shigeshi,
Kawai sai ya ruga da gudu Izuwa
kan dakarun tun kafin su afka masa
ya kutsa ta tsakiyarsu yana kai sara
da suka ta ko ina, suma suna kawo
masa.
Koda dakarun suka ga sauran kiris!
Ya fita ta tsakiyarsu sai suka yi
dabara suka yi masa kawanya aka
ci gaba da azababben yaki, suna
kokarin gididdibashi shi da wacce
yake goye da ita da kuma abinda
ita take goye dashi (jaririnta)
Kaico! Lallai duk inda jarumi yake
jarumi ne, wanda a kowanne lokaci
jarumtarsa kan iya motsawa yayi
bajintar da ba'a taba tsammani ba.
Koda Humairu yaga MUTUWA
muraran sai ya fara katantanwa a
tsakiyar wadannan dakaru ya rinka
kaiwa kafafunsu sara ya hanasu
kusantarsa, kuma yaci gaba da
kokarin matsawa gaba, ammma sai
abu ya gagara, domin kara matse
kowanne gurbi suke, kuma suna
dada kai masa mugayen SARA DA
SUKA.
Inba don ma Humairu ya sami
sabon gagarumin karfi ba da tuni
wadannan dakaru sun yi gutsin-
gutsin da sassan jikinsa dana
gimbiya lushairat da jaririnta.
A koyaushe kokarinsa shine ya kare
jikin lushairat dana jaririnta, ko
kadan baya son su sami ko
kwarzane a jikinsu.
Sai da aka shafe sama da dakika
dari biyu da saba'in ana wannan
bakin gurmuzu, dakarun sun kasa
cutar dasu Humairu, shi kuma ya
kasa fita daga tsakiyarsu.
Duk tsawon wannnan lokaci
lushairat na kwance a gadon bayan
Humairu a sume bata farfado ba.
A dai-dai wannnan lokaci ne
hankalin Humairu ya sake
DUGUNZUMA ainun, domin ya
fahimci cewar idan aka sake kara
bata wani Lokacin a haka tabbas
zai gaji, da zarar ya gaji kuwa tasu
ta kare, take za'a gama dasu tun da
Sarkin yawa yafi Sarkin karfi. Bare
ma karfin ma anfi shi, juriya ce da
tsantsar sa'a a tare dashi.
Koda gama yin wannnan tunani sai
Humairu ya yanke shawarar yin
wata dabara ta karshe wacce ko dai
ya sami nasarar tsira ne ko kuma
shi dasu lushairat din su hallaka.
BAZATO ba tsammani sai dakarun
suka ga Humairu ya zaro wata
zabgegiyar adda daga cikin
wadonsa ya hada da takobin
hannunsa sannnan ya doki kasa da
hannayensa biyu ya tashi sama
tamkar daga cikin baka aka
harbashi, sai gashi ya dira akan
katanga.
Ai kuwa sai ya kama gudu akan
katangar tamkar akan turba yake
gudun
A dai-dai wannnan lokaci ne
dakarun sarki larbusa dubunai suka
sake tuttudowa cikin gidan, a
cikinsu har da 'yan baka (Gwanayen
harbin kibiya ).
Koda suka hango Humairu akan
katanga sai 'yan bakan nan suka
fara zaro kibiyoyi suna harba masa.
Kibiyar farko ta cakeshi a kaurinsa
na dama ta fasa kafar.
Humairu ya kurma uban ihu
sakamakon tsananin zafi da zogin
da yaji, amma saboda tsananin
juriya bai yarda ya fadi kasa ba, sai
ya ci gaba da gudu akan katangar
goye dasu lushairat, kuma ya rinka
kade kibiyoyin da ake harbo masa
da takobinsa da Addarsa ta gaba da
baya, sannnan yana gocewa tare da
yin tsalle-tsalle kibiyoyin na
wucewa ba tare da sun sameshi ba.
Su kansu dakarun sarki larbusa sai
da suka yi tsananin mamaki yadda
akayi ya iya yin wannnan
gagarumar jarumtaka, amma sai
suka bishi gaba dayansu duu! Da
gudu har ya duro daga kan
katangar yaci gaba da gudu Izuwa
cikin wani surkuki mai siririn lungu
cikin gidan sarautar.
Adaidai wannnan lokaci ne gimbiya
lushairat ta farfado daga dogon
suman da tayi.
Abinda ta fara ji a kunnenta shine
kukan jaririnta wanda ke goye a
gadon bayanta, gashi kuma ita ma
a goye take a bayan Humairu yana
ta tsala gudu dasu.
Koda ta waiga baya ta ga
dubunnan dakarun da suka biyosu
da gudu rike da makamai, sai ta
kwalla ihu cikin tsananin firgita da
dimauta.
Nan fa taga anci gaba da harbo
musu ruwan kibiyoyi, amma sai
taga Humairu ya ci gaba da kade
kibiyoyin ta baya da makaman
hannunsa ba tare da ya waigo
ba,kuma gashi yana dada ci gaba
da gudu.
Nan take ta kamu da tsananin
mamaki, domin a saninta mijinta
ne kadai yake da irin wannan bakin
zafin nama da gagarumar
jarumtakar haka.
Koda ta kalli kasa taga kibiya soke
cikin Kaurin Humairu ga jini na
zuba amma bai fasa gudu ba da
kokarin ceton rayuwarta da
jaririnta sai ta sake cika da tsananin
mamakin dalilin da yasa wannnan
jarumi ya sallama rayuwarsa haka
don kawai ya kubatar da tasu ita
da jaririnta.
Hakika rashin sani yafi dare duhu!
Ashe wannan siririn dogon lungu
da Humairu ya shigo babu komai a
cikinsa face danyen mai acikin
ganguna.
Shi Humairu ya san da hakan,
amma su dakarun da suka biyoshi
basu sani ba.
Sai da ya bari dukkaninsu sun shigo
tsakiyar lungun inda gangunan
man suke a jibge, kawai sai ya cafe
kibiya guda daya daga cikin
wadanda ake harbo masa ya tsaya
cak! Ya daina gudun.
Al'amarin da ya sa gaba dayan
dakarun suka tsaya cak! Suma suna
mamakin tsayawarsa, kuma
tazararsu dashi bata wuce taku
goma ba.
Alokacin ne dakarun suka lura da
yawan gangunan man sun huje
suna ta tsiyayar da mai har
kafafunsu sun jike sharkaf a cikin
man ba tare da sun ankara ba.
Kawai sai dakarun suka sake
yunkurawa da gudu da nufin su
cimma Humairu suyi masa rotse.
Cikin bakin zafin nama ya yagi
tsumman rigar jikinsa ya
nannadashi a jikin wannan kibiya
dake hannunsa, kawai sai ya karci
bangon da kibiyar.
Take wuta ta kama tsumman dake
jikin kibiyar,kawai sai ya wurgo
kibiyar Izuwa inda gangunan man
suke.
Koda ganin haka sai dakarun sukai
turjiya ta bazato, sannnan suka
juya da baya a firgice domin su
ruga da gudu su bar wajen.
Kash! Masu iya magana sunce, idan
ajali yayi kira dole a amsa koda
babu ciwo.!
Kafin dakarun su tsere tuni wannan
kibiya mai ci da wuta ta dira a cikin
gangunan man nan.
Ai kuwa sai gangunan man suka
kama yin bindiga suna tarwatsewa,
wata irin gagarumar wuta ta kama
ko ina a cikin lungun ta rinka
babbake wadannan dakaru suna
ihu suna faduwa kasa.
Koda Humairu yaga wutar ta dawo
da baya zata lullubesu sai ya juya
ya falfala da azababben gudu, ita
ma wutar ta bishi suka kasa tsere.
Saura kiris! Wutar ta lasosu ya sake
daka tsalle ya fada cikin katon
bahon wanka na sarki Aryan wanda
ke cike da ruwa.
Ruwan bahon ya rine da jinin
mutanen da aka kashe a wannan
yaki,
Ashe can kasan bahon hanya ce
wadda ta hade da wannnan katon
kududdufin dake can bayan birnin
LURHAJ.
Kawai sai lushairat ta ga sun taso
saman wannan kududdufi,gashi
tana daure a bayansa tamau ai
kuwa sai nauyinsa ya rinjayesu
suka sake nutsewa kasa.
Koda lushairat taga numfashinsu ya
fara daukewa ita da jaririnta sai ta
yi ta maza ta zare wata wuka dake
daure a cinyar Humairu ta yanke
igiyar da ta daureta a gadon
bayansa. Sannnan ta cafi rigar
Humairu tayi iyo Izuwa saman
kududdufin suka fito tare.
Koda ta dago sama taga jaririnta
bai mutu ba, yana raye cikin koshin
lfy, wannnan karon ma baya kuka
sai murmushi yake yi kawai
sakamakon tsintar kansa akan
ruwa, sai farin ciki ya lullubeta.
Haka dai lushairat taci gaba da jan
Humairu a cikin wannan ruwa
wanda ke sume har suka iso bakin
gabar wannan kududdufin.
Koda ta kara hancinta dai-dai dana
Humairu sai taji babu alamar
numfashi.
Nan fa hankalinta ya DUGUNZUMA
ta shiga kokarin ceto rayuwarsa
tana danna kirjinsa saboda zargin
ko ruwa ne ya cika cikinsa,amma
shiru bata ga ruwa ya fito ba ta
cikin bakinsa ko hancinsa.
Nan fa ta kara dimaucewa bata san
sa'adda tasa bakinta ba a cikin nasa
ta hura masa iska.
Faruwar hakan keda wuya kuwa
sai Humairu ya farfado yana mai
yin tari.
Koda bude idanunsa ya tsinci kansa
a bakin gabar wannan kududdufin
kuma yaga gimbiya lushairat tare
da jaririnta a raye a gabansa sai ya
bushe da dariyar farin ciki. Amma
da ya yunkura don ya mike tsaye
sai ya kasa sakamakon kibiyar dake
cikin kafarsa.
A wannan Lokaci kafar tasa ma ta
kumbura suntum! Kuma bata daina
zubarda jini ba.
Kawai sai ya sake kama rigarsa ya
yageta gaba daya sannnan ya
cusata a cikin bakinsa.
Nan take ya kama wannan kibiya
dake cikin kafarsa ya dinga zareta
yana ihu da kururuwa saboda
tsananin zafi da zogi.
Tabbas in ba don ya toshe bakinsa
ba da wannnan tsumma na rigarsa
da har a cikin gidan sarautar sai an
jiyo ihun nasa.
Humairu yana gama zare wannan
kibiya ya kare sumewa, kuma jini
yaci gaba da bulbulowa ta cikin
ramin da kibiyar tayi masa.
***** DUGUNZUMA!!!
LITTAFI NA 4
PART 3
LITTAFIN YAKI
NASEER SHEHU TEARLOW
*****
A wannan Lokaci kafar tasa ma ta
kumbura suntum! Kuma bata daina
zubarda jini ba, kawai sai ya sake
kama rigarsa ya yageta gaba daya
sannnan ya cusata a cikin bakinsa.
Nan take ya kama wannan kibiya
dake cikin kafarsa ya dinga zareta
yana ihu da kururuwa saboda
tsananin zafi da zogi.
Tabbas in ba don ya toshe bakinsa
ba da wannnan tsumma na rigarsa
da har a cikin gidan sarautar sai an
jiyo ihun nasa.
Humairu yana gama zare wannan
kibiya ya kare sumewa, kuma jini
yaci gaba da bulbulowa ta cikin
ramin da kibiyar tayi masa.
Cikin hanzari lushairat ta yage
gefen rigarta mai tsada ta sarauta
ta daure inda jinin ke zuba, tayi ta
nannada rigar akan kafar har sai da
taga jinin ya daina zuba sannnan ta
kama yiwa Humairu fifita.
Humairu bai farfado ba sai bayanp
Kimanin dakika dari uku da arba'in.
A dai-dai wannnan lokaci ne suka
daina jiyo ihu da kururuwar
mutane daga cikin gidan sarautar,
amma hayakin wutar nan data
tashi a cikin gangunan mai bai
daina tsiri ba a sama cikin gajimare,
hasken wutar na binsa.
Humairu ya bude idanunsa da kyar
ya dubi lushairat sannnan ya dubi
kafarsa wacce har yanzu a kumbure
take ya gyada kai cikin takaici ya
sake duban lushairat yace, taimaka
ki samo mini sandar da zan dogora
muyi sauri mu bar wajen nan mu
nausa cikin daji don dakarun sarki
labarusa zasu iya zuwa bincike
anan.
Ba tare da gardamar komai ba
kuwa lushairat ta mike tsaye da
kyar ta ruga taje ta karyo reshen
wata bishiya mai dan kauri ta kawo
ya karba ya dogara ya mike tsaye
da kyar, amma duk da haka sai ya
kasa yin tafiyar.
Koda ganin haka sai lushairat ta
karbe reshen bishiyar daga
hannunsa ta yi jifa dashi sannnan
ta tallafo kugunsa da hannayenta
biyu yana dingisa kafar tasa mara
lfy suka nausa cikin dajin.
Al'amarin da yai matukar baiwa
jarumi Humairu mamaki kenan,
yace a ransa.
"Ya ya akayi matar da tace bazata
hada jikinta da nasa ba amma
yanxu ita ce ma take kama jikin
nasa da hannayenta, kuma tana
sane take aikata hakan? "
Amsar da bai sani ba kenan.
Ba tare da Humairu ya dago kai ya
dubi lushairat ba sai yace, "Mu ci
gaba da tafiya har Izuwa iya yadda
zaki gaji sannnan mu nemi inda
zamu buya mu kwana kafin gari ya
waye."
Lushairat tayi shiru bata ce komai
ba, taci gaba da jansa suna tafiya.
A Lokacin ne duhun dare ya
mamaye dajin ya zamana cewa ko
gabansu basa iya gani, sai Humairu
ne yake gane musu hanya ta
hanyar yin amfani da takobin
hannunsa yana sare ciyayi da
kayoyin dake gabansu.
Haka dai suka ci gaba da tafiya har
Izuwa tsawon sa'a guda sannnan
suka riski wani kogon dutse.
Da zuwansu bakin kogon dutsen
sai suka zauna suna haki, sai da
suka dan huta sannnan jaririn
lushairat ya fara kuka.
Cikin hanzari ta kwantoshi daga
Bayanta sannnan ta juyawa
Humairu baya duk da cewa a cikin
duhun dare suke ta fara shayar
dashi.
Take jaririn ya yi shiru kuwa.
Tsawon 'yan dakiku dayansu baice
uffan ba. Daga can sai lushairat tayi
gyaran murya tace, "Tsawon wane
lokaci zamu bar wannan dajin? "
Humairu ya numfasa yace, Da ina
da niyyar mu kwana amma yanxu
na sauya shawara.
Zamu huta ne anan tsawon sa'a
uku kacal sannnan mu tashi muci
gaba da tafiya saboda ina zargin
cewa sarki labarusa zai iya turowa
a biyo sawunmu.
Baya ga haka kuma na yiwa
masoyiyata Alkawarin cewar gobe
kafin rana ta fadi zan riskesu a can
wata kasa da ake kira ZAITUN. "
Koda Humairu yazo nan a zancensa
sai lushairat ta ji zuciyarta ta buga
da karfi, kuma wani irin kishi mai
karfi ya shigeta.
Al'amarin da yai matukar girgizata
kenan, kuma ya bata mamaki,
domin ba ta ga hujjar da za ta sa
tayi kishi akan wani da namiji ba
face mijinta marigayi sarki Aryan
gwarzon jarumin da babu kamarsa
a gaba daya Nahiyar a fagen Kyau,
Jarumtaka, Arziki da daukaka.
Tabbas sarki Aryan yasha gaban
Humairu a komai, don haka babu
hujjar da zata sa lushairat taso shi."
Lushairat na cikin yin wannnan
zancen zuci ne Humairu ya katseta
yace, "Yaya naji kinyi shiru kina
tunani, ko kina da wata shawara
ne?"
Lushairat tayi firgigit! Kamar wacce
ta farka daga barci ta dubeshi da
sauri tace, "Eh.....abinda nake tunani
shine, ci gaba da tafiyarmu da
wannnan rauni naka da kumburin
kafar taka ba a zai yiyu ba dole ne
na fara yi maka magani.
Koda jin haka sai Humairu ya dago
kai da sauri ya dubeta yace, "shin
dama ke likita ce?"
Lushairat tayi murmushi sannnan
tace, ai duk matar jarumi dole ne ta
san magunguna iri-iri, kuma dole
ne itama ta kasance jaruma koda
kuwa a zuci ne ba'a zahiri ba.
Mijina ya koya mini yadda ake
rayuwa a daji da yadda ake farauta.
Kai har yakin ma ya koya mini na
iya abinda na iya dai-dai
gwargwado.
Yanzu zan kunna fitilar ice naje na
nemo wani ganye da wata saiwa
wacce zanyi maka magani dasu."
Tana gama fadin Hakan sai ta
yunkura da nufin ta mike tsaye,
cikin sauri Humairu ya ruko
hannunta yace,
Akan wane dalili zaki bata
Lokacinki akan talakanki?"
Shin kin manta ne cewar ke matar
Sarkin lurhaj ce, kuma uwar Sarkin
lurhaj na gobe?
Ai ni talakanki ne " cikin sauri
lushairat ta zare hannunta daga
cikin na Humairu ta mike tsaye
sannnan ta dubeshi tace, " Talakan
da ya ceci rayuwata da ta dana ya
sami babban mukami a zahiri da
badini.
Har abada masauratar lurhaj baza
ta taba mantawa dashi ba, kuma
dole ne ta girmamashi tayi masa
sakayya"
Humairu yayi murmushi yace, Ai
har yanzu ban sami nasarar
kubatar da rayuwarku ba har sai na
ga mun isa cikin birnin zaitun.
Yanzu na baki kankanin lokaci kije
ki samo ganyen da saiwar.
Amma ina mai shawartarki daki
nemo ganyen bishiyar raihas da
saiwar bishiyar julus, domin sune
masu saukin samu a wannan daji,
kuma sune zasu sa nayi saurin
samun lafiya.
Cikin mamaki lushairat

Please Login or Register in order to submit comment