Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bishiyoyi daga can nesa
suna gani.
Sai da su sarki larbusa suka yi nisa
da tafiya suka bace sannnan su
Humairu suka fito daga cikin sakon
da suka buya suka karewa sansanin
kallo suka ga ragowar dakarun da
aka bari sun kai su dari.
Koda ganin haka sai hankalin
Humairu ya dugunzuma suka rasa
dabarar da zasu yi su shiga cikin
sansanin bare har su binciko inda
aka tsare iyayensu mata da kuma
masoyansu su Laila.
Cikin tsananin damuwa Hashlar ya
dubi Humairu yace, ya kai abokina
yanxu ta yaya zamu iya afkawa
cikin wannan sansanin har mu ceto
rayuwar iyayenmu da masoyanmu
tunda gashi Kimanin dakaru dari ne
ke zagaye da wajen.
Idan muka ce zamu taresu gaba
daya ba zamu iya hallakasu ba
tunda mun jarraba dasu a baya
mun gani.
Da kyar da sidin goshi muka kashe
irin su mutum uku.
Koda jin haka sai Humairu yai shiru
yana mai sunkui da kansa kasa
kuma ya shiga tunani mai zurfi.
Daga can sai ya dago kai ya dubi
Hashlar cikin murmushi yace,
dabara ta fado mini muyi kokari
mu shiga cikin sansanin cikin labiya
da sumame mu kashe mutum biyu
kacal daga cikin masu tsaro
wadanda ke daf da farkon sansanin
sai mu janye gawarsu mu boyeta
sannnan mu cire tufafin jikinsu mu
sanya.
Sai dare yayi sannnan zamu koma
cikin sansanin muci gaba da yi
musu dauki dai,dai muna kashesu
har sai mun karar dasu sannnan mu
binciko inda mutanenmu suke mu
kubatar da rayuwarsu.
Koda Humairu yazo nan a zancensa
sai Hashlar yai ajiyar zuciya
sannnan yace "Na yarda da
wannnan shawara taka, amma wai
shin ka manta ne cewa wadanan
mutane sun fimu tsawo da kauri
sossai? "
Ai koda mun sanya irin tufafin
jikinsu suna ganin kankatarmu zasu
gane cewa mu ba nasu bane.
Humairu yace, "Na da hakan amma
kada ka damu akwai dabarar da
zanyi mana.
Koda gama fadin Hakan sai
Humairu ya zare wata sharbebiyar
wuka a jikinsa sannnan ya kwanta
a kasa da rub da ciki ya kama tafiya
akan ciyawa kamar kadangare.
Cikin hanzari shima Hashlar yayi
koyi dashi.
Haka dai Humairu da Hashlar suka
ci gaba da tafiyar rub da ciki a cikin
ciyawa har suka iso farkon sansanin
inda wadansu dakaru biyu ke tsaye
suna ta kallon gabas da yamma
kudu da arewa suna muruzai,kuma
sun dafe kubben takubbansu.
Jira kawai suke suji motsi a wani
wurin su kai hari, tsakaninnsu
Humairu da wadanan dakaru biyu
bai wuce taku uku ba.
Kai inba don yanayin suturar dake
jikinsu Humairu yazo daya da tarin
ciyawar dake dajin ba da lallai sai
dakarun sun gansu.
Ko kyakkyawan numfashi su
Humairu suka yi sai wadanan
dakaru sunji.
Koda Humairu yaga sun kusanto
daf da dakarun biyu sai ya dubi
Hashlar yayi masa inkiya.
Nan take su biyun suka daka tsalle
sama daga kwancen tamkar yan
biririka suka dira akan wuyan
dakarun suka shaftare
makogwaronsu da wukake.
Take dakarun suka zube kasa
matattu
Sai suka janye gawarwakin
dakarun can baya nesa da sansanin
sannnan suka cire tufafin jikinsu
suka watsasu a wani rami.
Kafin Humairu da Hashlar su sauya
tufafin dakarun sai suka cusa ganye
a cikin tufafin mai yawa ya
kumburo sannnan suka sanya, sai
gashi girman jikinsu ya karu ainun,
ya
Kai irin na dakarun, nan dai suka
sake labewa a cikin duhuwar har
sai da dare ya raba sannnan suka
mike suka sami wadansu dogoyen
itatuwa masu gwafa suka zurasu a
cikin wadandunansu ya zamana
cewa tafin kafarsu akan gwafar
itatuwan suke suna takasu sai
gashi sun kara tsawo kai kace
tabbas sun kasance
Samudawa irin dakarun sarki
larbusa.
A haka suka shiga cikin sansanin
suka rinka yiwa dakarun kissan
mummuke.
A haka suka sami nasarar kashe
Kimanin dakaru tamanin da biyar.
Wadanda suka rage mutum goma
sha biyar ne kacal.
Abinda ya sa su Humairu basu sami
Damar kashe mutum goma sha
biyar din ba shine, sun ware kansu
sun zauna a tsakiya sansanin sun
kunna wuta sun kewaye wutar
suna jin dumi suna hira.
Har su Humairu suka gama kashe
Dakaru tamanin da biyar din
wadanan guda goma sha biyar
basu san abinda ke faruwa ba,
kuma shugaban dakarun wanda
aka baiwa ajiyar sansanin a
hannunsa yana cikin masu jin
dumin... DUGUNZUMA!!!
LITTAFI NA BIYU
PART 4
LITTAFIN YAKI
NASEER SHEHU TEARLOW
******
Abinda ya sa su Humairu basu sami
Damar kashe mutum goma sha
biyar din ba shine, sun ware kansu
sun zauna a tsakiyar sansanin sun
kunna wuta sun kewaye wutar
suna jin dumi suna hira.
Har su Humairu suka gama kashe
dakaru tamanin da biyar din
wadannan guda goma sha biyar
basu san abinda ke faruwa ba
kuma shugaban dakarun wanda
aka baiwa ajiyar sansanin a
hannunsa yana cikin masu jin
dumin.
Bayan su Humairu sun sami nasarar
kashe wadanan dakaru sai suka
hango inda aka zuba 'yan uwansu
mata a cikin wani katon keji duk an
zuba musu sarkoki a hannayensu
da kafafunsu, gasu a kwance suna
ta faman shara barci.
Humairu ya kare musu kallo daya
bayan daya gaba dayansu amma
sai yaga babu buduwarsa laila a
cikinsu sai mahaifiyarsa, mahaifiyar
Hashlar budurwа Hashlar da sauran
iyayen abokansu da kuma 'yan
matan abokan nasu.
Al'amarin da ya matukar
dugunzuma hankalinsu kenan ya
dubi Hashlar cikin tsananin
damuwa yace, ya kai abokina kayi
sani cewa idan muka ce sai mun
ceci rayuwar gaba dayan matan
nan asirinmu ne zai tonu a
hallakamu.
Na duba gaba dayan matan dake
barci a cikin wancan keji babu
masoyiyata laila a cikinsu.
Abinda nake so da kai shine, ka
lallaba cikin sanda kaje ka bude
kejin ka kwance sarkokin da suka
daure uwata da mahaifiyarka da
kuma masoyiyarka hulaiza sannnan
ka tashesu daga barci ba tare da
sauran 'yan uwansu sunji ba.
Ni kuma zan tafi neman
masoyiyata a cikin wadancan
tantunan.
Mu hadu da kai a can karshen
wannan sansanin inda dakarun nan
suka daure giwayensu.
Na gama akwai dawakai guda biyu
a wajen sai mu gudu a kansu "
Koda jin wannnan batu sai murna
ta kama Hashlar, nan take ya
durfafi inda wannan keji yake yana
sanda shi kuma Humairu sai ya nufi
inda sauran tantunan sansanin
suke ya leka su daya bayan daya
har ma ya wuce ta bayan wadanan
dakaru goma sha biyar masu jin
dumi basu ganshi ba.
Yana zuwa tantin dake gaban
wadanan dakaru ya leka cikinsa sai
ya hango masoyiyarsa laila da
matar sarki larbusa a zaune suna
hira.
Zuraiha ta dubi laila tace, yake
wannnan budurwа kiyi sani cewa
na ceci rayuwarki ne daga hannun
mijina ba don komai ba sai domin
ina kishin ya tara da wata 'ya mace
in ba ni ba.
Tuni na gane nufinsa cewar so yake
ya tara dake.
Na sani cewa keda yan uwanki duk
kuna cikin bakin ciki marar
misaltuwa gamida tsananin
fargaba da tashin hankali domin an
kashe dukkanin mazajenku, an
kone kauyenku kurmus ya zama
toka kuma yanzu gashi kun zamo
bayinmu zaku ci gaba da yi mana
bauta daga nan har Izuwa karshen
rayuwarku.
Zan iya kubatar da rayuwarki ke
kadai ki gudu daga wannan nahiya
gaba daya amma sai idan zaki
daukar mini alkawari guda daya. "
Koda jin wannnan batu sai mamaki
ya kama laila ta dubi zuraiha tace,
ke kuwa wane irin alkawari ne
haka kike son na daukar miki?"
Zuraiha tayi murmushi sannnan
tace, idan mijina ya gama kama
sauran tsirarun kasashen da ke
wannan nahiya zai zamo DODON
MAZA a duniya ya zamana cewa
gaba dayan nahiyoyi suna tsoronsa.
A sannnan ne duk abinda ya bukata
daga kowacce nahiya dole ne a
bashi don tsoron kada ya kai
FARMAKI.
A sannnan ne mulkinsa da
dukiyarsa zasu bunkasa ya kai
babban matsayin da ya dade yana
mafarkin kaiwa.
Yayi mini alkawari cewar idan ya
kai wannan matsayi zai bani
shugabancin kasuwanci nahiyar
gaba daya domin ni banida burin
da ya fi na zamo sauraniyar
attajiran duniya a wannan zamani.
A takaice ina son na tara dukiyar da
babu mai yawanta.
Banida tabbacin mijina zai iya cika
mini wannan alkawari.
Ni kuwa a cikin zuciyata na yanke
hukuncin cewa idan har bai cika
mini wannan alkawari ba na
nakasashi ya zama kamar mace a
cikin maza kuma yana ji yana gani
zan gaje karagar mulkinsa nayi
yadda duk naso.
Bazan iya samun nasarar nakasta
mijina ba ya rasa komai nasa face
na mallaki jinin dan da matar sarki
Aryan ta haifa ba ya cika shekara
goma sha takwas a duniya.
Na gano hakan ne a cikin binciken
tsafin da nayi.
Bukatata dake shine, bayan na
tserar da rayuwarki nan da cikar
shekara goma sha takwas ki samo
mini jinin wannan yaro ki kawo
mini.
Koda mijina ya cika alkawarin dake
tsakaninmu ba zan fasa ajiye jinin
ba don babu mamaki a gaba ya
tashi alkawarin namu."
Lokacin da zuraiha tazo nan a
zancenta sai laila tayi shiru tana
tunani da nazari domin tasan cewa
abinda zuraiha ke son tayi dai-dai
yake da cin amanar matar sarki
Aryan wato diban jinin danta ba
tare da ta sani ba.
Kafin laila ta gama tunani tace wani
abu sai kawai suka ga Humairu
tsulum! Ya shigo cikin tantin ya
sawa zuraiha kaifin takobinsa a
wuyanta sannnan yace,
"Ba zan bar masoyiyata ta dauki
irin wannnan alkawari ba na cin
amana."
Cikin tsananin farin ciki da mamaki
laila ta mike tsaye zumbur zata
taho wajen Humairu sai zuraiha ta
daka mata tsawa ta tsaida ita
sannnan ta juya ta dubi Humairu
cikin murmushi ba tare da shakkar
komai ba.
Kawai sai ta danna kaifin takobin
tasa akan wuyanta amma sai kaifin
ya kasa yankata.
Al'amarin da ya matukar razana
Humairu da laila kenan.
Zuraiha ta sake duban Humairu tayi
murmushi tace, ba za ka iya
kasheni ba kuma yanzu idan nayi
maka ihu ragowar dakarun da baku
kashe ba kai da abokinka Hashlar
zasu rugo nan har su hallakaku.
Idan har buduwarka ta daukar mini
wannan alkawarin yanzu lallai zan
fatar daku daga sansanin nan lafiya
ba tare da dakaru sun ganku ba.
Ku nake sauraro, yaya kuka gani? "
Koda jin haka sai hankalin Humairu
dana laila ya dugunzuma suka
kama kallon juna kuma suka rasa
abinda za su ce.
Daga can sai laila ta dubi Humairu
tace, ya kai masoyina kayi sani
cewa bamu da wani sauran zabi
face mu dauki wannan alkawari in
ba haka ba kuwa ni da kai da
Hashlar da iyayenku mata babu
wanda zai tsira da rayuwarsa.
Tabbas na san cewa abinda ya
kawoku kenan domin ku tserar da
rayuwarmu"
Koda jin wannnan batu sai jikin
Humairu yayi sanyi ya dubi laila
yace, shikenan sai ki ki daukar mata
alkawari ".
Nan take laila tayi rantsuwa da
darajar iyayenta cewar lallai bayan
shekara goma sha takwas in dai
tana raye zata nemi gimbiya
zuraiha a duk inda take ta kawo
ma ta jinin dan sarki Aryan
Koda jin haka sai farin ciki ya
lullube zuraiha ta dubi Humairu da
laila tace, "ku saki jikinku ku biyoni
a baya kawai "
Koda gama fadin Hakan sai zuraiha
ta mike tsaye ta fice daga cikin
tantin, Cikin sauri Humairu da laila
suka bita a baya.
Ta gaban wadanan dakaru goma
sha biyar masu jin dumi su zuraiha
suka wuce amma dakarun basu
gansu ba kuma basu ji motsinsu ba
har zuraiha ta kaisu Izuwa bayan
sansanin inda suka tarar da
dawakai guda biyu, suna zuwa
wajen suka ga Hashlar tare da
mahaifiyarsa, mahaifiyar Humairu
da kuma hulaiza.
Ba tare da bata wani lokaci ba suka
dora iyayensu mata akan doki
daya, dayan dokin kuma suka dora
laila da hulaiza suka yi gaba.
A sannnan ne ya dubi zuraiha yayi
mata godiya sannnan ya dada
tabbatar mata da cewa lallai
masoyiyarsa laila zata zamo mai
cika alkawarin dake tsakaninsu.
Nan take Humairu da Hashlar suka
yiwa zuraiha sallama suka juya
suka falfala da matsanancin gudu
kafin cikar wani lokaci mai tsawo
tuni sun riski iyayensu da 'yan
matansu dake gudu bisa dawakai.
****
A can kofar birnin LURHAJ kuwa,
tuni su sarki Aryan sun gama shirin
jiran isowar abokan gaba, wato su
sarki larbusa amma su sarki larbusa
basu iso ba sai da rana ta take.
Tun daga nesa karar sawayen
giwayensu ya tashi hankalin
mutanen birnin LURHAJ.
Su kansu su sarki Aryan da suka
jeru a sahu sahu a gaban kofar
birnin sai da suka firgita domin
kasa ce ta kama rawa tamkar zata
dare duk abinda ke kanta ya rufta
ciki.
Sa'adda rundunar su sarki Barham
ta matso kusa suka yi arba da
rundunar sarki Aryan suka ga suma
suna da yawan gaske sai suka cika
da murna domin sun san cewa yau
takubbansu zasu sha jini su more.
Cikin tsananin kaguwa dakarun
sarki larbusa suka kama zare
makamansu tun gabanin a basu
umurni suka fara ihu da kururuwa.
Shi kuwa sarki larbusa sai ya fara
kyakyata dariyar mugunta
musamman da ya yi arba da sarki
Aryan ya kare masa kallo yaga
girmansa bai wuce na dan tsako ba
a gaban shirwa in aka dangantashi
da nasa girman.
Nan take sarki larbusa ya zare tasa
takobin ya zunguri giwar da yake
kai, ta fita da gudum ta tunkari
sarki Aryan a Lokacin da sauran
mukarrabansa suka rufa masa baya
suna a guje bisa giwayensu.
Koda ganin haka sai shima sarki
Aryan ya zaburi dokinsa kuma ya
zare takobinsa yayi kan sarki
larbusa tare da tasa rundunar suna
biye da shi.
Koda rundunar biyu ta hadu sai aka
ruguntsume da azababben yaki.
Ihun mazaje, rurin giwaye da
haniniyar dawakai ta cika dodon
kunne, jini ya rinka fantsama da
malala yana cukuduwa da kasa.
Al'amarin su Humairu kuwa, koda
suka shafe sa'a uku suna tafiya sai
suka yada zango a bakin wata
korama domin su huta.
A sannnan ne mahaifiyar Humairu
ta shiga basu labarin wata
sarauniya wacce wani almajiri ya
shigo fadarta yana bara.
Take sarauniyar ta mike daga kan
karagarta tazo wajen almajirin ta
kama sandarsa ta rike ta dubeshi
tace, "zan baka abinci kaci ka koshi
yanzu ya kai wannan tsoho, amma
ba zaka iya biyana ba da komai
domin ni bana bukatar abinci ko
dukiya.
Koda gama fadin Hakan sai
sarauniya larbisa ta juya taja taja
tsohon har Izuwa cikin gidan
sarautar.
Al'amarin da ya baiwa kowa
mamaki kenan hatta mutanen gari
da sauran masu fada aji saboda ita
dai larbisa bata kasance mai
tausayi da jin kan talakawa ba
kuma tana da tsananin rowa bata
bayar da abin hannunta face akan
bukatarta kawai.
Lokacin da sarauniya larbisa ta kai
wannan almajiri cikin babban falo
na turakarta wanda girmansa ya
kai na wani gida guda sai tsohon
ya zama cikakken dan kauye ya
kama kalle kalle domin bai taba
tsintar kansa a cikin waje mai
ni'ima da daula ba irin wannnan.
Gaba dayan falon a shimfide yake
da wata irin darduma mai tsananin
laushi da zarar ka taka darduma sai
kaji kamar zaka nutse a cikinta
saboda taushi.
Kujerun dake zagaye da falon gaba
dayan an yi su ne da zinare kuma
sun kai kamar guda dari biyu da
daya.
A tsakiyar falon an ajiye wani katon
gunkin tsuntsun dawisu wanda
akayi shi da karfen jauhar mai
launin kore da rawaya kuma anyi
masa wata hikima ruwa na ta zuba
ta cikin dawisun yana taruwa akan
wani katon faranti na lu'u lu'u abin
dai akwai ban sha'awa da ban
al'ajabi.
A saman rufin falon kuwa wadansu
irin fitilu ne sama da guda dubu
daya wadanda suma da lu'u lu'u
akayi su sai sheki da walwala suke.
Duk inda almajirin ya duba a cikin
falon sai yaga Kuyangi ne tsala
tsala suna ta hidimar goge-goge da
gyare-gyare. Tabbas wannan wuri
ya cika aljannar duniya.
Koda suka iso tsakiyar falon sai
larbisa ta dubi almajirin tace, ya
zauna bisa daya daga cikin kujerun
falon.
Almajirin ya dubi kujerar sai tayi
masa kwarjini ainun, yaga cewa shi
dai bai kasance basarake ba ina shi
ina zama akan irin wannnan kujera.
Kawai sai ya zauna a kasa dirshan
bisa wannan darduma mai taushi.
Koda ganin haka sai sauraniya
larbisa da kuyanginta suka bushe
da dariya domin basu taba ganin
wanda yai irin wannnan kauyancin
ba.
Sarauniya larbisa ta dubi shugabar
kuyanginta wacce ake kira da suna
HULAIRA tace da ita aje a kawowa
bakona duk irin kalar abincin dake
gidan nan.
Hulaira tace,an gama ya
shugabanta "
Nan take Hulaira ta juya ta fice
daga cikin falon, ita kuma
sarauniya larbisa sai ta dubi
almajirin tace, bayan ka huta zan
dawo gareka da yamma domin mu
yi 'yar hira kafin na sallameka ka
tafi saboda kazo mini da bayani
wanda ya jefani a cikin wasi wasi.
Lallai ba zaka tafi ka barni a cikin
duhu ba.
Koda gama fadin Hakan sai
sarauniya larbisa ta wuce Izuwa
can cikin turakarta.
Sai da ta jima tana tafiya sannnan
ta kule almajirin ya daina hangota.
Nan fa almajirin ya shiga sakar zuci
yana mai cewa a ransa, "wai shin
Yaya cikin turakar sarauniya larbisa
zata kasance a kyau da
kawatuwa?"lallai dole ne ya ninka
nan falon a komai.
Jin kadan da tafiyar sarauniya
larbisa sai ga wadansu Kuyangi
dabam su goma sha biyu sun shigo
cikin turakar kuma kowacce na
dauke da katon farantin abinci.
Akan kowanne faranti akwai abinci
kala shida.
Nan take kuyangin suka ajiyewa
almajirin farantan abinci a gabansa
suka juya suka fice.
Ba tare da jiran komai ba almajirin
ya bude kwanukan farantin farko
dake gabansa, kawai sai ya kama
cin abincin hannu baka hannu
kwarya
Cikin dakiku kadan ya cinye abincin
dake cikin kwanuka shida gaba
daya.
Al'amarin da ya firgita gaba dayan
kuyangin dake cikin falon kenan
suka fara tunanin anya kuwa
wannnan almajiri mutum ne? "
A iya zamansu a gidan sarautar
basu taba ganin mutumin da ya
taba cinye koda kwano daya ba na
abinci kasancewar kwanukan
manya ne kuma cike suke taf da
abinci.
Sau tari sai mutane biyar sun taru
suke iya cinye abincin kwano daya.
Lokacin da almajirin ya gama da
abincin farantin dake gabansa sai
ya janyo wani farantin ya
gwamutsa abincin kwano shida
akan farantin duka ya kama ci.
Nan da nan ya karar da abincin ya
janyo faranti na uku.
koda ganin haka sai gaba dayan
kuyangin suka firgice suka ruga
wajen falon a dimauce suna ihu
kuma suka tsaya a can bakin kofar
falon suna leken almajirin.
Abu dai kamar wasa sai da
almajirin ya cinye gaba dayan
abincin dake kan farantan goma
sha biyu.
A sannnan ne almajirin yai gyatsa.
Dama an kawo masa ruwa inibi a
cikin tambulan guda.
Koda ya kafa tambulan din a
bakinsa sai yayi masa kurba uku ya
zukeshi duka.
Shi kansa wannan tambulan din
sau tari idan aka cikoshi da ruwan
inibi komai yawan bakin da suka zo
gida basa shanyeshi gaba daya sai
kaga sun rage wani abu.
Sa'adda kuyangin suka ga ya cinye
gaba dayan wannan abincin kuma
ya shanye ruwan inibin sai suka
kara dimaucewa suka ruga Izuwa
cikin gidan sarautar suna ihu da
fadin cewa, tabbas aljani ne a cikin
alon sarauniya ba mutum bane".
Koda jin wannnan bushara sai
dakarun tsaro na gidan sarautar
suka zare takubbansu suka ruga
Izuwa cikin falon sarauniya larbisa
suka yiwa almajirin kawanya.
Al'amarin da ya matukar baiwa
almajirin mamaki kenan kuma ya
tsoratashi domin bai san laifin da
yayi ba har da a kazo aka
yanyameshi haka.. DUGUNZUMA!!!
LITTAFI NA 2
PART 5
LITTAFIN YAKI
NASEER SHEHU TEARLOW
******
Sa'adda kuyangin suka ga almajirin
ya cinye gaba dayan wannan
abincin kuma ya shanye ruwan
inibin sai suka kara dimaucewa
suka ruga Izuwa cikin gidan
sarautar suna ihu da fadin cewa,
tabbas aljani ne a cikin falon
sarauniya ba mutum bane ".
Koda jin wannnan bushara sai
dakarun tsaro na gidan sarautar
suka zare takubbansu suka ruga
Izuwa cikin falon sarauniya larbisa
suka yiwa almajirin kawanya.
Al'amarin da ya matukar baiwa
almajirin mamaki kenan kuma ya
tsoratashi domin bai san laifin da
yayi ba har da aka zo aka
yanyameshi haka.
Ana cikin wannan hali ne labari ya
riski sarauniya larbisa bisa abinda
ke faruwa. Koda larbisa taji wannan
abin al'ajabi sai itama ta cika da
tsananin mamaki.
Cikin hanzari ta mike tsaye daga
kan kujerar da take zaune ta taho
cikin falon nata.
Da shigowarta cikin falon ta iske
dakarunta sun yiwa almajirin
kawanya suna tsuma ba tare da
sun afka masa ba, ga dukkan alamu
suma sun tsorata ne bisa ganin
gagarumin aikin da yayi.
Nan take sarauniya larbisa ta
dakawa dakarunta tsawa suka jajja
da baya har Ta hango almajirin
zaune a tsakiyarsu yana kyarma
cikin alamun tsananin tsoro har ya
jike sharkaf da gumi.
Al'amarin da ya baiwa larbisa
tsananin mamaki kenan, nan take
ta gamsu a cikin zuciyarta cewa
lallai wannan almajiri ba aljani
bane mutum ne domin inda aljani
ne babu abinda zai sa ya tsorata
bisa ganin dakarunta Izuwa kansa.
Larbisa ta dubi dakarun nata da
dukkan kuyangin dake cikin falon
tace, kowa ya fita barsu "
Cikin gaggawa suka bi wannan
umurni, falon yayi tsit! Tamkar
mutawa ce ta gifta.
A wannan Lokaci ne larbisa ta taka
taje har daf da almajirin ta zauna
tana mai yi masa wani irin kallo na
rashin yarda tace, Ya kai wannan
tsoho bani labarinka ka sanar da ni
komai bisa gaskiya, idan kuwa kayi
mini karya bazaka fita daga nan ba
a raye.
Lokacin da almajirin yaji wannan
tambaya sai yai ajiyar numfashi,
nan da nan idanunsa suka ciko da
kwalla har hawaye ya subuto masa
sannnan ya dubi sarauniya larbisa
yace, yake wannnan sarauniya kiyi
sani cewa ni dai sunana
HUZAILATUL MARWASU kuma na
fito ne daga can kudancin duniya a
wata kasa da ake kira madinatul
sauwaba.
Mahaifina ya kasance kusurgumin
matsafi wanda yai nisan kwana a
duniya domin sai da ya shekara
Dari hudu da arba'in da uku a
duniya sannnan ya mutu a Lokacin
ina da shekara shida kacal a duniya,
kuma nine dan auta kuma tun ina
jariri uwata ta mutu ta barni.
A wannan Lokaci ragowar yan
uwana su hudu duk sun haura
shekara goma sha. Daga mai
shekara Ashirin sai mai Ashirin da
'ya'ya.
Wadanan yayye nawa sun taso da
hikima gamida sauran daukar
ilimin tsafi a wajen ubanmu.
Nan da nan kowannensu ya zamo
shahararren boka, ni kuma sai na
taso da dakikanci, duk abinda aka
koya mini bana iya yi.
Ko karanta mini dalasiman tsafi
mahaifina yayi bana iya biyawa
kamar yadda Ya biya haka kuma na
kasance malalacin gaske bana iya
yin aikin komai koda kuwa sharar
gida ne.
Bisa wannan daliline sauran 'yan
uwana suka tsaneni.
Bugu da kari, sai na taso da
tsananin cin abinci mai yawan
gaske, amma kuma idan naci na
koshi ina iya yin kwana Ashirin da
daya ban kara cin komai ba sai dai
nasha ruwa.
Wani abin mamaki kuma shine, a
tsawon kwana Ashirin da dayan
bana kawar da bukatar bawali ko
bayan gida.
Sai da ta kai cewa na cinye gaba
dayan abincin dake gidanmu
wanda mahaifinmu ya tanada a
rumbu wanda a takaice zamu iya
shekara goma muna amfani dashi.
Duk wannnan halaiya tawa ba ta
taba sa mahaifina ya tseneni ba
face ma yana dada nuna mini
soyayya da janyoni a jikinsa.
Su kuwa 'yan uwan nawa sai haka
yasa suka dada tsanata ya zamana
cewa idan mahaifinmu ya aikemu
cikin gari ko kasuwa sai su yi mini
dukan tsiya akan hanya.
Wani lokaci ma dukan kawo wuka
suke yi mini har sai jama'ar gari sun
kwaceni, sai dai a dawo dani gida
jina-jina.
Kafin a kawoni gida sai yan uwan
nan nawa su rigani komawa suce
da mahaifinmu sun hadu ne da
abokan gabarmu 'ya'yan wani
bokan garinmu an fafata yaki.
Sau uku haka na faruwa, don haka
sai mahaifin nawa ya hanani fita ko
ina.
Ya zamana cewa kullum muna tare
dare da rana.
Ko barci mahaifina zai yi sai ya
tabbatar da cewa ina kwance akan
kirjinsa.
A kullum idan na tuna irin yanayin
hallitar dana taso a ciki na
dakikanci, lalaci da cin tsiya.
Sai na kamu da tsananin bakin ciki.
Nayi ta kuka.
Shi kuwa mahaifin namu sai yayi ta
rarrashina yana mai cewa, ya kai
dana kayi sani cewa akwai ranar da
zaka rabu da duk wadanan
matsaloli,amma sai a bayan
mutuwata bayan kayi wata
doguwar tafiya.
Lallai kafin mutuwata zan sanar da
kai bangaren da zakaje a cikin
duniya domin ka rabu da wannnan
matsaloli.
A sannnan ne zaka sami wata
gagarumar daukaka irin wace ni
kaina ban samu ba.
Kayi hakuri da duk irin
muzgunawar da 'yan uwanka za su
yi maka daga nan har Izuwa ranar
mutuwata domin hakurin naka
shine zai kaika Izuwa kan tafarkin
daukakarka.
Na sani cewa yan uwanka basu da
buri wanda yafi su hallakaka
saboda ya zamana cewa ba zaka ka
mallaki komai ba daga cikin
dukiyar dana tara.
Babu yadda basu yi ba don su
hallakaka amma sun kasa domin
ina baka kariya ta musamman.
Duk abinda ke faruwa a yayin da
kuka fita kasuwa ko cikin gari ina
gani daga nan a cikin madubin
tsafina.
Duk sa'adda kaga jama'ar gari sun
zo sun ceci ranka a hannun 'yan
uwanka to ba mutanen gari bane
ni ne na rikede Izuwa siffar mutane
nazo muku.
Wannan bakar wahalar da kake sha
a hannunsu itace alamun samun
daukakarka ta nan gaba.
A duk sa'adda mahaifin namu yazo
nan a zancensa sai na fashe da
kuka nace,"ya kai abbana yanzu
idan ka mutu waye zai iya ci gaba
da ciyar dani alhalin yanzu ma kana
ciyar dani ne da karfin sihirin
tsafinka?"
Idan baka nan ya za'a yi na tsira
daga shairin 'yan uwana?"
Da jin wannnan tambaya sai
mahaifina yayi murmushi yace,
"nayi maka alkawari ko a bayan
raina baza ka fuskanci matsalar
komai ba, kuma ba zaka sha
wahala ba ta dogon lokaci."
Haka dai mahaifina yaci gaba da
rarrashina yana bani baki a duk
sa'adda nake cikin damuwa ko
tashin hankali.
Wata rana da farkon dare sai
mahaifina ya kamu da tsananin
rashin Lafiya har ya kama kumallon
jini.
Nan fa muka hadu mu biyar din a
kansa,a Lokacin da hankalina yayi
matukar dugunzuma na fara kuka.
Su kuwa sauran yan uwana ko
kadan babu alamar wata damuwa
a fuskarsu kawai sai suka kama
yake.
Mahaifin namu ya dubi sauran yan
uwan nawa yace dasu, ku tafi
Izuwa cikin daji ku nemo mini
ganyen bishiyar suljara.
Shine kadai abinda za'a jika mini na
sami sauki".
Koda jin wannnan batu sai hankalin
yan uwan nawa ya tashi.
Babban cikinsu ya dubi mahaifin
namu cikin alamun matukar
damuwa yace, ya kai. Abbanmu ka
sani cewa ganyen bishiyar suljara
yana da matukar wuyar samu a
duk cikin dazuzzukan garin nan,
zamu iya kwana a daji muna
nemansa "
Da jin haka sai mahaifinmu ya
fusata yace, shin yanzu wahalar da
zaku sha a daji tafi lafiyata
muhimmanci kenan a wajenku?
Idan har baza ku tafi neman
Wannan ganye ba yanzu take zan
lalata dukkan sirrin tsafin da kuka
mallaka kuma na kone dukkan
dukiyata dake cikin gidan nan.
Koda jin wannnan batu sai yan
uwan nawa suka juya suka fice
daga cikin dakin suna guna-guni
cikin fushi.
Sai bayan yan uwana sun dade da
tafiya daji sannnan mahaifina ya
mike zaune da kyar sannnan ya
jany@oni Izuwa jikinsa ya
rungumeni akan kirjinsa.
Kawai sai naji hawayen idanunsa
na zuba akan fuskata.
Cikin karfin hali ya bude baki yace,
ya kai dana ka saurara da kyau ka
natsu kaji jawabin da zanyi maka.
Idan har ka rike abinda zan gaya
maka yanzu lallai zaka sami
daukakar da tafi tawa ma.
Kayi sani cewa na aiki yan uwanka
ne Izuwa can daji domin na sami
damar da zan sanar da kai babban
sirrin dana adana maka a cikin
zuciyata tsawon shekara da
shekaru.
Ka sani cewa tsananin kaunarka da
tausayinka da nake ji bisa yanayin
hallitar daka kasance ne ya sa na
adana maka wannan babban sirri.
A yau kuma nan bada dadewa ba
wa'adina zai cika na bar wannan
duniya. Da zarar ka ga na mutu
kayi sauri ka shiga cikin turakata ka
dafa bakin akwatina na karfe da
hannu na hagu, take akwatin zai
bude.
Zaka ga wata jakar fata a ciki sai ka
dauki jakar ka ratayata a kafadarka
ka fice daga cikin gidan nan.
Kana fita zaka ga gidan nan ya
nutse Izuwa cikin karkashin kasa ya
bace bat tamkar bai taba wanzuwa
ba a wajen.
Daga nan sai ka juya ka nausa
yamma kayi ta tafiya har ka fita
daga cikin garin nan ka nausa daji.
Duk iya tsawon tafiyar da zaka yi
kada kayi waige koda zaka ji
sukuwar giwaye a bayanka.
Duk inda ka gamu da mutum ko
aljan kada kayi masa magana kuma
idan aka yi maka magana kada
amsa.
Kana shiga garin ka bude wannan
jaka taka zaka iske babu komai a
cikinta face dinare mai yawan
gaske sai ka nemi abinci mai yawa
wanda zai isheka har ka koshi ka
siya.
Amma ka tabbatar da cewa a boye
zaka cinye wannan abinci ba'a
gaban jama'a ba.
Kada ka kuskura ka kwana a
wannan gari da zarar ka koshi sai
kayi harama ka sayi doki ka hau ka
cigaba da tafiya.
Ina mai tabbatar maka da cewa sai
ka shekara arba'in da biyar kana
wannan tafiya kana ta keta
dazuzzuka da birane.
A sannnan ne zaka cika shekara
hamsin da daya a duniya, kuma a
wannan Lokaci ne guzurin dake
cikin jakarka zai kare, ka iso wani
babban Birni inda wata
mashahuriyar sarauniya ke mulki.
A sannnan ne yunwa zata
gallabeka don haka ka nemi hanyar
gidan sarauta.
Kana zuwa fada ka wuce kai tsaye
Izuwa gaban katangar mulki

Please Login or Register in order to submit comment