Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bar
mahaifata
A Lokacin da nike daf da cika
babban burina na duniya wato
Lokacin da zan ga dana na cikina.
Wanda kullum nake mafarkin
ganinsa akan karagata.
A koyaushe matata lushirat zata iya
haihuwa, burina shine na dauki
jaririn da ta haifa da hannuna na
daurashi akan karagar mulkina.
Idan naga wannan Al'amari na
gama cika burina, ko a sannnan ma
idan na mutu banida asara.
Abinda yasa na hanaku baiyana
zuwan wadanan mutane a fada
shine, jama'ata zasu firgice su fara
kokarin guduwa, a kokarin hakan
kuma zasu iya rasa rayuwarsu da
dukiyoyinsu a dazuzzuka
Sakamakon arangama da 'yan fashi
da mugan dabbobi.
Ni yanzu abinda na yanke hukunci
shine,
Ni da Sarkin yakina zamu jagoranci
gaba dayan dakarunmu mu fita mu
tari wadanan mutane ko mu kosu,
amma zaman gida ba namu bane,
Kai da dan uwanka Hashlar na
yarda da jarumtakarku kuma an
san cewa zaku taka muhimmiyar
rawa a wannan yaki.
Saboda haka sai ku shiga cikin
rundunarmu don kishin kasarmu.
Ko kadan bana son hankalin matata
ya tashi saboda wannan tsohon ciki
da take dauke dashi.
Shine dalilin da yasa bana son
tasan da faruwar wannan yaki.
Lokacin da sarki ARYAN yazo nan a
jawabinsa sai Humairu da Hashlar
suka dubi junansu sannnan
Humairu ya dubi sarki ARYAN yace,
ya shugabana ina son ka sani cewa
yadda duk kake tsammanin
wadanan mutane sun wuce haka.
Ko mu fita mu taresu ko mu tsaya a
gida bamu isa mu hanasu isowa
nan ba.
Idan kuwa sukazo duk yawan nan
namu dakake gani sai gaba dayan
mazajenmu sun fadi kasa.
Ka sani cewa bamu zo gareka
domin ayi shirin yin yaki da
wadannan mutane ba,sai domin ka
sanar da jama'a su gudu mai rabon
tsira ya tsira."
Kafin Humairu ya gama rufe
bakinsa tuni sarki ARYAN ya daka
masa tsawa wacce tasa duk su
biyun suka firgita.
A fusace sarki ARYAN ya zare
takobinsa ya fuskancesu yace, ko
kubi umurnina ko kuma nayi yaki
daku a cikin wannan daki wanda
duk ya sami nasarar kashe wani sai
shawararsa tayi amfani.
Koda jin wannnan batu sai Humairu
da Hashlar suka yi tsuru-tsuru suka
hau kallon juna.
Nan take Humairu ya fada kogin
tunani.
Kimanin shekara uku baya da suka
shude akwai wata rana sa'adda
Humairu da Hashlar, ILsam, Zuraif,
Hashim , Sahal, Kaimur suka zo
fadar sarki ARYAN kowannensu ya
saba katuwar dabbar da ya farauto
a daji. Daga wanda ya kamo katon
zaki sai wanda ya kamo katuwar
damisa kura da sauran manyan
dabbobin daji masu matukar hadari
da ban tsoro.
Nan take jaruman bakwai suka
zube dabbobin a gaban sarki
ARYAN
A matsayin sun bashi su kyauta
alokacin da maroka suka rinka yi
musu kirari suna kodasu a
matsayin manyan jarumai da babu
kamarsu akasar.
lokacin da sarki ARYAN yaji kirarin
da ake yiwa su Humairu yayi yawa
Sai ya daga hannu sama kowa yai
shiru, fadar tayi tsit! kawai sai ya
mike tsaye ya dubi jama'a yace,
"Ni ban yarda da jarumtakarka
wadanan samarin guda bakwai ba.
Kuma ko sau daya basu taba
birgeni ba saboda sun kamo
wadanan mugayen dabbobin daji.
"Yaku jama'ata zaku gasgata
zancena bayan na jarraba karfin
dantsena da iya yakina akansu ni
kadai.
Saboda haka yanzu ni kadai zan
yakesu su bakwan.
Na rantse da darajar karagata
dayansu ba zai iya yi mini rauni ba,
idan kuwa yayi mini, na yarda zan
sauka daga kan karagata na bashi
ya hau.
Koda jin wannnan batu sai mutane
suka firgita kuma suka cika da
tsananin mamaki har wadansu ma
suka fara tunanin ko sarki yasamu
tabin kwakwalwa ne.
Abinda ya janyo haka kuwa shine
kowa a birninsa yasan irin
jarumtakar wadanan mafarauta
guda bakwai domin duk shekara
idan akayi gasar jarumtaka sune
suke lashewa.
Shi kuwa sarki ARYAN bai taba
shiga wannan gasa ba tunda shine
mai shiryata.
Abu na biyu a tsawon shekara
goma sha uku da sarki ARYAN ya
hau kan karagar mulki bai taba fita
yaki ba da kansa.
Duk sa'adda yaki ya taso sai dai
sarkin yakinsa ya wakilceshi.
To wai shin mutumin da bai taba
fita yaki ba, kuma ba'a taba ganin
jarumtakarsa ba shine yanxu zai
tari manyan gwarzaye bakwai? "
To wai shin menene takamarsa?"
Tambayoyin da jama'a suka kasa
amsawa kenan.
Sarki ARYAN ya sauko daga kan
karagar mulkinsa ya cire
alkyabbarsa sannnan sai ya juya ya
dubi matarsa gimbiya lushirat cikin
murmushi.
Itama sai ta maida masa da
martanin murmushin fuskarta cike
da annuri babu wata fargaba.
Al'amarin da ya kara baiwa kowa
mamaki kenan domin anyi zaton za
a ga hankalinta ya dugunzuma.
Sarki ARYAN ya zare takobinsa ya
fuskanci zaratan jaruman bakwai
wato su Humairu yace,
"ku nake jira kuma bayan mun
gama wannan yaki da makami na
yiwa kowannenku rauni daya
bayan daya zamu gwada karfin
dantse dimin naga iyakar
jarumtakar taku.
Sa'adda su Humairu sukaji wannan
batu sai suka kama dariya suna
yiwa sarki ARYAN wani irin kallo
cikin rauni domin sun san cewa ko
ba a gwada ba ai linzami yafi karfin
bakin kaza.
Koda Sarki ARYAN yaga haka sai ya
rugo Izuwa kansu ya fara kaiwa
humairu wawan sara a wuya
Cikin bakin zafin nama Humairu ya
sunkuya takobin ta sari iska ya zaro
tasa takobin suka ci gaba da
artabu.
Suma su Hashlar sai suka zare nasu
takubbansu suka rufarwa sarki
ARYAN.
Wohoho! Wanda ya iya ya huta,
tabbas jarumtaka da sadaukantaka
baiwa ce, wanda duk Allah ya bashi
sai dai a kyaleshi kawai domin yafi
gaban wargi.
Lokacin da aka fara wannan
gurmuzu tsakanin sarki ARYAN da
su Humairu sai hankalin kowa a
fada ya dugunzuma domin su
bakwan sun kasa koda lakutar jikin
sarki ARYAN kuma ya zame musu
alakakai duk da cewa suna kawo
musa hari ko ina.
Babu abinda yafi baiwa mutane
mamaki face tsananin zafin naman
sarki ARYAN da yadda ya kuntata
jaruman bakwai kuma ya zamana
cewa yana iya sara da sukansu ta
kowanne bangare, gabas da
yamma, kudu da arewa da kuma
sama da kasa harma wata irin
alkafira yake yi a kasansu ko a
samansu yana tarwatsasu da karfin
saransa.
Sai da aka shafe rabin sa'a cur! Ana
wannan gurmuzu an rasa mutum
daya daga cikin jaruman bakwai
wanda ya sami nasarar taba jikin
sarki ARYAN.
Nan fa fadar ta rude da shewa aka
rinka yiwa sarki tafi ana mamakin
irin wannnan jarumtaka tashi.
Koda ganin haka sai sarki ARYAN ya
sauya salon fada ya zama kamar
tsuntsu mai fuka-fukai ya zamana
cewa a samansu Humairu yake
shawagi yana kai musu sara, kafin
kafarsa ta raba kasa sai a shafe
dakikoki masu yawa, ai kuwa bai
dade da fara yin hakan ba ya
dimautasu.
A Lokaci guda ya sami nasarar
yankar kowa daga cikinsu.
Wani a hannu, wani a kafa, wani a
kirji, wani a gadon baya.
Duk su bakwan babu wanda bai yi
masa rauni ba, kawai sai yayi
alkafira a sama ya dira a can gefe
daya nesa dasu ya mayarda
takobinsa cikin kufe yana
murmushi.
Koda ganin haka sai gaba dayan
jama'ar dake fadar suka rude da
tafi aka hau yiwa sarki ARYAN
jinjina cikin tsananin al'ajabi domin
babu wanda ya san cewa yana da
irin wannan jarumtaka.
Su kuwa su Humairu sai suka cika
da tsananin bakin ciki domin a
tarihin jarumtakarsu tun daga
kurciyarsu kawo Izuwa girmansu
ba'a taba samun wani jarumi da ya
taresu ba har ya sami nasarar
akansu sai shi sarki ARYAN din
Dukkaninsu sai suka kama tsuma
cikin tsananin fusata musamman
Kaimur wanda yake ji da
tsagwaron karfin dantse yana
ganin cewa idan ya matse sarki
ARYAN sai ya kakkarya masa
kasusuwan jiki ko kuma idan ya
bangajeshi da kirjinsa.
Bayan sarki ARYAN ya maida
takobinsa cikin kufenta sai ya cireta
gaba daya daga cikin jikinsa.
Sannnan ya cire rigar jikinsa, sai ga
damtsensa da kwanjinsa sun
baiyana a fili karara, duk jijiyoyin
jikinsa sun tashi sun kumbura sunyi
burdin burdin.
Babu wanda ya taba ganin sarki
ARYAN a cikin wannan kama don
haka sai aka cika da mamaki su
kansu su Humairu sai da suka ji
wani abu a jikinsu, domin Kaimur
ne kadai mai irin siffar jikin sarki
ARYAN.
Nan take sarki ARYAN ya dubi su
Humairu yayi murmushi yace,
"Nasan ku mafarauta ne
kowannenku yana tafe da magani
a jikinsa.
Maza ku yiwa raunikan jikinku
magani, sannnan mu gwada 'yar
kashi domin nafison mu kara a
Lokacin da kowannenku yake da
isasshen kuzari.
Kuyi sauri ku tsayar da jinin jikinku
dake zuba don kada ku rasa
kuzarin.
Ba tare da gardamar komai ba
kuwa kowannensu ya buda jakar
guzurinsa ya dauko magani yasa a
rauninsa.
Sai bayan 'yan dakiku sa'adda
kowannensu ya sami nutsuwa
sannnan sarki ARYAN ya dubesu
yace,
"To ku shirya ga namiji nan bisa
kanku.
Kamar hadin baki sai sarki ARYAN
da Kaimur suka rugo da kan juna a
Lokaci guda, ai kuwa suna haduwa
suka bangaji juna da kirji, tamkar
dutse da dutse ne suka hadu
kirazan nasu suka ba da wani irin
sauti duum! Kuma ko gezau
dayansu baiyi ba, sai kallon juna
suke kawai irin kallon nan KAR TA
KAR.
Hakika Kaimur yayi tsananin
mamaki domin duk wani abu mai
rai idan ya hada kirji dashi a
saninsa sai wannan abu yaje kasa
tunda ko bishiya ko dutse
ragargazarsu yakeyi.
Koyaushe yana alfahari da karfin
kirjinsa.
A fusace Kaimur ya sungumi sarki
ARYAN ya dagashi sama ya
damfarashi da kasa, sai kawai ya ga
sarki ARYAN ya dire da kafafunsa
shima sai ya sunkuceshi ya dagashi
sama Maimakon ya damfarashi da
kasa sai ya makashi a jikin bango.
Take Kaimur ya fado kasa ya baje
yana murkususu ya kasa mikewa
tsaye.
Nan fa fadar ta sake kaurewa da
shewa gami da jinjina.
Koda su Humairu suka ga abinda ya
faru ga dan uwansu Kaimur sai
suka fusata suka rugo gaba
dayansu Izuwa kan sarki ARYAN
sukayi masa rubdugu sunayi masa
luguden duka ya zamana cewa sun
lullubeshi har ya tsugunna kasa.
A wannan Lokaci ne gimbiya
lushirat ta firgice bata san sa'adda
ta kwalawa sarki ARYAN kira ba
cikin ihu da razana.
Ai kuwa yana jin kiranta sai ya taso
da dukkan karfinsa ya tarwatsasu
ya hau su da naushi da bugu da
hannu da kafa,sai gashi yana watsi
dasu kamar yara na gara tamola.
Kafin a jima duk su shidan ya hada
musu jini da majina duk sun zube
kasa a galabaice an rasa wanda zai
mike tsaye daga cikinsu.
Koda ganin wannan gagarumar
jarumtaka da sarki ARYAN yayi sai
gimbiya lushirat ta mike tsaye
zumbur daga kan kijerarta ta rugo
gareshi cikin tsananin farin ciki ta
rungumeshi.
Jama'a kuwa suka sake rudewa da
shewa aka hau buga tambura ana
busa algaita, mawaka na yiwa sarki
ARYAN kirari.
Lokacin da Humairu yazo dai-dai
nan a tunaninsa sai ya dago kai ya
dubi sarki ARYAN cikin matukar
damuwa yace,
"Ya shugabana kaima ka sani cewa
ni din da dan uwana Hashlar bamu
isa mu tareka da yaki ba domin
ruwa ba sa'an kwando bane, don
haka dole ne mubi umurninka.
Amma fa ka sani cewa wannan
hanya da kake shirin bi ba mai
bullewa bace idan kuka bita kana ji
kana gani za'a shigo har cikin
birninka a cika da yaki.
Koda jin wannnan batu sai idanun
Sarki ARYAN suka ciko da kwallah
har hawaye ya zubo sannnan ya
dafa kafadar Humairu yace , "na
gani a cikin madubin Bokana cewar
zakayi tsawon rai a duniya abinda
nake so da kai shine, idan har
matata ta haihu to duk abinda ta
haifa na bar amanarsa a hannunka.
Itama matar tawa na bar amanarta
a hannunka.
Ka tsare lafiyarta da rayuwarta
komai rintsi da tsanani.
Shin ka dauki wannan alkawari?"
Cikin firgici Humairu ya dubi sarki
ARYAN yace, ya shugabana saboda
me Zaka dora mini wannan nauyin
alhalin kasan cewa ba zan iya ba.
Ka sani cewa a halin yanzu fa
mahaifiyata da masoyiyata laila
suna can a hannun wadanan
samudawa na kasa tserar da
rayuwarsu da lafiyarsu.
Yaya kuma yanzu zaka sake dora
mini wani nauyi?"
Nifa ban taba yin imani da tsafi ba
saboda mahaifina bashida addini
face farauta.
Saboda haka ni ban yarda cewa zan
iya kubuta ba daga shairin
wadanan samudawa ba.
Gaskiya ba zan iya karbar wannan
amana ba tunda nasan cewa
kokarin da zakayi a wannan yaki ko
rabinsa ba zanyi ba.
Koda jin haka sai sarki ARYAN ya
dakawa Humairu tsawa yace, dole
ne ka daukar mini wannan
alkawari saboda kana daga cikin
kalilan mutanen dasu rayu bayan
wannan yaki.
Kai ne kadai xaka iya sake kafa
tubalin wannan birni namu mai
albarka.
Fatana shine dan da matata zata
haifa ya shugabanci sabon wannan
birni.
Dukkan burina yanzu ya rataya a
wuyanka.
Da wannnan furuci nake yi muku
sallama sai ku fara shirin fita yaki. DUGUNZUMA!!!
LITTAFI NA DAYA
PART 6
LITTAFIN YAKI
*******
Koda jin haka sai sarki ARYAN ya
dakawa Humairu tsawa yace, dole
ne ka daukar mini wannan
alkawari saboda kana daga cikin
kalilan mutanen da zasu rayu
bayan wannan yaki.
Kai ne kadai xaka iya sake kafa
tubalin wannan birni namu mai
albarka.
Fatana shine dan da matata zata
haifa ya shugabanci sabon wannan
birni namu mai albarka.
Dukkan burina yanzu ya rataya a
wuyanka.
Da wannnan furuci nake yi muku
sallama sai ku fara shirin fita yaki.
Lallai gobe da asuba zamu fita mu
tari wadanan abokan gaba kafin su
iso nan su riskemu.
Koda gama fadin Haka sai sarki
ARYAN ya juyo ya fice daga cikin
dakin ya bar Humairu da Hashlar a
tsaye cikin tsananin tashin hankali
da damuwa gamida da matukar
mamaki bisa yadda al'amuran suka
kasance.
Duk su biyun sai suka zauna suka
sake yin tagumi suka yi shiru suna
tunani har Izuwa lokaci mai tsawo.
Daga can sai Hashlar ya dubi
Humairu a Lokacin da idanunsa
suka ciko da kwallah yace,
"ya kai abokina ka tuna cewa mun
rasa abokanmu su ILsam, mun rasa
iyayenmu mata da kuma
masoyanmu wadanda muke da
burin aurensu.
Kauyenmu wato asalin mahaifarmu
an baje shi an kona shi. Bamu da
sauran wani farin ciki a doron kasa.
Yanzu gashi mun zo nan domin mu
kubatar da rayuwar miliyoyin
jama'a amma sarki yaki bamu
hadin kai yace, mu shirya muyi
yakin da mun san cewa babu
nasara acikinsa.
Ya kai abokina na sani cewa muna
da burin mu kwato iyayenmu mata
da masoyanmu daga hannu
wadanan samudawan amma fa
burina na matacce wanda ko a farki
ba zai cika ba.
Zamu iya guduwa mu bar wannan
nahiya gaba daya domin mu tsira
da rayuwarmu amma menene
amfanin mu gudu mu bar
iyayenmu da masoyanmu acikin
bala'i, kunci da bakin ciki mara
tukewa.
Mu maza ne kuma kowanne namiji
an san shi da jajircewa akan
gaskiyarsa da tsare mutuncinsa
dana iyalansa da kuma na kasarsa
wanda duk bashida kishin
wadanan abubuwa uku bai cika
mutum ba.
Tabbas sarki ARYAN yayi gaskiya
domin da dai mu mutu ragwaye
gwara mu mutu mazaje, wata ran
za'a yi labarinmu anan gaba har
mu zamo abin misali ga mutanen
baya.
Abinda nake so da kai shine ba
gudu ba ja da baya.
Kawai mu tsaya ayi wannan yakin
damu. Sa'adda Hashlar yazo nan a
zancensa sai hawaye ya zubowa
Humairu ya rungumeshi duk su
biyun suka fashe da kuka suna
masu kankame juna kamar bazasu
daina ba.
Lokacin da sarki ya koma cikin
gidan sarauta sai ya nufi turakar
gimbiya lushirat fuskarsa cike da
annuri tamkar babu wani abu dake
damunsa a cikin zuciyarsa.
Da shigarsa cikin turakar sai ya
hango gimbiya lushirat zaune akan
luntsumemen gadonta ta juya
baya.
Cikin sanda ya karasa daf da ita
yasa hannayensa biyu akan
idanunta domin ya rufe mata
idanu.
Kawai sai yaji ruwan hawaye akan
hannunsa, a firgice ya juyo da
fuskarsa ai kuwa sai ya ganta a jike
sharkaf da hawaye, Al'amarin da ya
matukar girgiza hankalinsa kenan
ya dubeta cikin tsananin mamaki
da kaduwa yace, ya ke abar begena
wane ya bata miki rai har ya saki
kuka haka? "
Ki fada mini ko waye yanxu nan
uwarsa ta haifi wani.
Koda jin wannnan batu sai gimbiya
lushirat tasa hannunta ta share
hawayenta sannnan ta dubi sarki
ARYAN cikin nutsuwa tace,
ya kai mijina kayi sani cewa duk
abinda ya faru tsakaninka da Boka
KURHAS IBINI LAMRAS jiya naji
kuma na gani don haka kadaina
tunanin zaka boye mini wannan
Al'amari.
Hatta duk abinda ka tattauna dasu
Humairu acan dakin baki na gani
kuma naji.
Tabbas bamuda sauran farin cikin
rayuwa domin burinmu ya rushe,
shawarar da zan bamu kawai itace
mu kashe kanmu yanzu a cikin
wannan daki mu huta da takaicin
da zai zo ya samemu anan gaba
domin tabbas za'a kasheka, ni
kuma za'a dauke ni a tafi dani,
Ta yaya kake sai zan iya rayuwa a
doron kasa alhalin na san cewa
babu kai.
Ka sani cewa a duniya babu abinda
nake so sama da kai kuma banida
kowa sai kai.
Ka tuna da alkawarinmu na cewar
babu abinda zai rabamu face
mutuwa kuma mutuwar ma sai dai
ta daukemu a lokaci guda.
Lokacin da gimbiya lushirat tazo
nan a zancenta sai hawaye ya
zubowa sarki ARYAN ya rike
kafadunta yace,
Yake matata ke kuwa yaya akayi
kika san abinda ya faru tsakanina
da boka kurhas alhalin sanda na
kadaita dashi a cikin turakata kuma
sai da na kulle kofofi da tagogi
kuma yaya akayi kika san abinda
ya faru tsakanina dasu Humairu a
dazu acan gani?"
Lushirat tayi ajiyar zuciya tace, da
farko dai a jiya sa'adda kuka shigo
cikin turakarka kai da Boka KURHAS
tuni ni ina cikin turakar baku sani
ba saboda haka ina ganin
shigowarku sai na fada karkashin
gado na buya har Izuwa da kuka
gama maganganunku kuka fita.
Na dade ina kuka da bakin ciki a
karkashin gadon sannnan na fito.
Ina fitowa kuma sai nayi arba da
madubin tsafin boka kurhas, ina
ganin madubin na gane cewa lallai
mantashi yayi saboda rudewa da
fargabar abinda zai zo.
Kawai sai na dauki madubin na tafi
dashi turakata na boyeshi ba tare
da kowa ya gani ba.
A dazu ne na dauko madubin na
shafeshi da hannun hagu kamar
yadda naga boka kurhas yayi da
nufin naga abinda zaku tattauna
kai da su Humairu saboda tun a
fada nayi zargin cewa ba komai
zaku tattauna ba face irin maganar
da kukayi kai da Boka KURHAS.
Ai kuwa nan take naji duk
maganganun da kuka yi, Al'amarin
da ya kara jefani cikin matsanancin
bakin ciki kenan na kama kuka
shine ka shigo yanzu ka iskeni ina
kuka.
Koda gama wannan jawabi sai
lushirat ta dago matashin kai ta
dauko wannan madubin tsafi ta
mikawa sarki ARYAN.
Yana karbar madubin sai ya
dokashi da kasa ya tarwatse,
sannnan ya dubi lushirat a Lokacin
da hawaye yaci gaba da zubo masa
yace,
"hakika tsafi bashida rana a gareni
tunda ya kasa kawar da abinda zai
kawo rabuwata dake kuma ya kasa
hana tarwatsewar farin cikin
rayuwarmu.
Yake matata inaso ki sani cewa ina
ji a jikina cewar lallai zaki haifi
abinda ke cikinki kuma a bayan
bama nan abinda kika haifa komai
dadewa sai yayi mulki a wannan
birni na LURHAJ.
Kinga kenan mutuwarmu a yanzu
dai-dai take da rushewar tarihin
birninmu har abada.
Idan kuwa kika haihu zamu bar
baya.
Sa'adda sarki ARYAN yazo nan a
zancensa sai lushirat ta dubeshi
cikin matukar damuwa yayin da
hawaye keta sartu bisa kyawawan
kumatunta tace,
Menene tabbacinka cewar Humairu
zai iya tserar da rayuwar abinda
zan haifa domin naji ka bashi
amanarsa da tawa?"
Sarki Aryan yai ajiyar numfashi
sannnan yace, "Boka kurhas ya
tabbatar mini da cewa Humairu tun
yana mutum ne mai sa'a da nasibi
duk abinda ya sa a gabansa sai yai
nasara.
Bisa wannan daliline yanzu na dora
dukkan burina a kansa.
Koda jin wannnan batu sai gimbiya
lushirat ta rungume sarki ARYAN ta
sake fashewa da matsanancin kuka
shi kuma ya shiga rarrashinta. * * *
A can sansanin su sarki labarusa
kuwa Lokacin da aka kai laila cikin
tantin sarki aka daureta sai sarki
labarusa ya shiga cikin tantin da
nufin ya afka mata domin tun
sa'adda ya kyalla ido yai arba da ita
ya aiyana Hakan a zuciyarsa.
Yana shiga cikin tantin sai ya iske
matarsa zuraiha zaune daf da laila
tana bata madarar shanu a koko
tana sha.
Cikin fushi sarki labarusa ya dubi
zuraiha yace, saboda me zaki
shayar da wannnan fursunar
alhalin ta kasance mai wargi da
raini a garemu? "
Ba tare da alamar tsoro ko
damuwa ba zuraiha ta juyo ta dubi
sarki larbusa tace, bisa alkawarin
dake tsakanina da kai har a gama
wannan yaki baza ka afkawa wata
'ya mace ba haka ne ko ba haka
bane? "
Cikin alamun kunya sarki larbusa ya
kau da kai sannnan yace, ai ban
kawota nan domin wani abu ba sai
domin inason nasa ayi mata azaba
mai radadi saboda ta kuranta
masoyinta a kaina, kuma ina son na
yiwa masoyin nata kisan gilla a
gaban idanunta.
Zuraiha tayi murmushi tace, shin
babu inda zaka sa ayi mata azabar
ne sai anan cikin tantinka?"
Kada ka manta cewa a cikin
alkawarinmu akwai batun cewa
bazaka azabtar da mata ba, kuma
ba za'a yi musu fyade ba.
Ba kai ba ko a cikin yaranka duk
wanda ya karya wannan doka sai
ya fuskanci hukunci domin doka ce
wacce muka gada tun iyaye da
kakanni a duk sa'adda muka fita
yaki.
Ka tuna cewa baka da wani buri
wanda yafi ka mamaye wannan
nahiya gaba dayanta ya zamana
cewa dukkan kasashen nahiya suna
karkashin mulkinka.
A wannan nahiya kasashe dari biyu
da arba'in da uku ne,
A halin yanzu mun ci kasashe dari
da tamanin da shida da yaki kuma
a ko ina ka kafa jama'armu sunci
gaba da mulki.
Yanzu saura kasashe hamsin da
bakwai kacal burinka ya gama cika.
Kasar da muka durfafa a yanzu
wacce ake kira birnin LURHAJ itace
mafi girma da yawan mayaka daga
cikin kasashen da suka rage mana.
Ka taka a hankali kuma ka kiyaye
alkawarin dake tsakaninmu domin
idan ka saba daya daga cikinsu nida
sauran matan jama'armu zamu iya
yimuku bore mu bata muku
dukkan shirinku.
Yanzu zan dauki wannan fursuna
na tafi da ita tantina bazan baka ita
ba har sai ranar da ka kamo
masoyinta in yaso ku fafata yaki kai
da shi a gabana a gabanta domin
muga iyakar jarumtakarsa tunda ta
kodashi ta kurantashi akanka.
Na sani cewa kayi yake-yake a
rayuwarka sama da guda casa'in
kuma babu wani da namiji wanda
'ya macce ta haifa wanda ya taba
kaika kasa. Ina alfahari da wannnan
daukaka taka ya kai mijina saboda
haka xan zuba ido naga yadda zata
kaya tsakaninka da saurayin
wannan yarinya.
..
Koda gama fadin Hakan sai zuraiha
ta kwance laila daga jikin dirka
sannnan ta ingiza keyarta gaba a
cikin wulakanci suka fice daga cikin
tantin suka bar sarki larbusa a
tsaye sororo kamar yaro mara
wayo zuciyarsa a kufule yana
mamakin yadda wannan mata tasa
ta dade tana yi masa kama karya a
cikin harkokinsa kuma gashi ta
zame masa alakakai sai juyashi
take kamar waina a kasko alhalin
duk duniya babu wanda ya isa ya
daga masa dan yatsa face ita.
Wannan ya samo asali ne
sakamakon wani babban sirri dake
tsakaninnsu don haka zuraiha ta
zame masa kadangaren bakin tulu.
Har dare yayi gari ya waye sarki
larbusa bai rintsa ba sakamakon
tunani da damuwa bisa rashin
ganin dawowar su Sarkin yaki
garbuza.
Nan take jikinsa ya bashi cewa lallai
ba lafiya ba.
Don haka sai ya fara tunani a ransa
cewa anya kuwa maganar da laila
ta fada masa ba gaskiya bace?"
Koda yaji ya fara wannan tunani sai
ya mike tsaye zumbur ya fito daga
cikin tantinsa ya Dakawa gaba
dayan dakarunsa tsawa yace,
"kowa ya kintsa a juya da baya
domin a koma wannan kauye na
Garul Aswar, wato kauyensu
Humairu.
Gama fadin Hakan keda wuya sai
aka jiyo sautin sawayen giwaye
sun durfafo sansanin.
Nan fa kowa ya zuba idanu akan
hanya sai aka ga su Sarkin yaki
garbuza sun dawo a sukwane
fuskokinsu a murtuke babu annuri
kamar wadanda aka aiko musu da
sako mutuwa.
Garbuza na rike da wani buhu
dauke da wani abu a ciki, da isowar
garbuza gaban sarki larbusa sai ya
tsaida giwarsa ta tsaya cak,ta daga
kafafunta na gaba sama alamar
tana gaisuwa ga sarki larbusa
sannnan ta ajiye kafafunta kasa.
Sarkin yaki garbuza ya sauko daga
kan giwar rike da wannnan buhu
kawai sai ya zazzage abinda ke
cikin buhun agaban sarki.
Ba komai bane face kawunan
wadanan samudawan uku na sarki
larbusa wadanda ya turasu su
kashe mutanen da aka jiyo rurin
ihunsu bayan angama da kauyen
Garul Aswar.
Koda sarki larbusa ya ga kawunan
wadanan dakaru nasa sai ya fusata
ainun ya kwarara uban ihu mai
tsananin firgitarwa, gaba dayan
dabbobi da tsuntsaye dake dajin sai
da suka razana suka kama guje
guje daga cikin ramuka suna
neman sabuwar maboya, wasu
kuma suna sauya sheka.
Nan take sarki larbusa ya dubi
giwar Sarkin yaki garbuza ya gabza
mata naushi a ciki take giwar tayi
ruri ta fadi kasa ta baya rikica, ko
motsi ba ta kara yi ba ta zama
gawa.
Larbusa ya kara kwarara uban ihu
wanda yasa dukkan dakarunsa da
bayin da aka kamo suka dimauce
suka rinka dunkule jikinsu saboda
razana, kasa ma ta kama girgiza
Sarkin yaki ne kadai bai fita
haiyacinsa ba.
A wannan Lokaci idanun sarki
larbusa sun kada sunyi jawur
tamkar garwashin wuta kuma
ilahirin kofofin gashin jikinsa sun
bude suna fitar da tiririn zufa.
Tunda Sarkin yaki garbuza yake
tare da sarki larbusa bai taba ganin
fushinsa ba irin na wannnan lokaci.
Cikin tsananin fushi da kakkausar
murya Sarki larbusa ya dubi Sarkin
yaki garbuza yace, yaya akayi aka
kashe mini wadanan dakaru
nawa?"
Sarkin yaki garbuza ya risina a cikin
alamun tsoro da biyayya yace, "ya
shugabana Lokacin da muka isa
wannan kauye sai muka iske
sababbin gawarwaki na samari
guda biyar sannnan kuma muka ga
gawar wadanan dakaru naka.
Abinda na fahimta shine,
wadannan samaru sun cika
jaruman gaske kuma sune suka yi
ragas da dakarunmu uku.
Sarki larbusa ya dubi garbuza yace,
wane irin kisa kuka iske dakaruna
sun yiwa samarin biyar? "
Garbuza yace, sassarasu suka yi
gunduwa-gunduwa.
Koda jin haka sai sarki larbusa ya
jinjina kai yace,
Samarin basu biyar bane akwai
ragowar su, ragowar tasu ne suka
kashe dakaruna kuma sun gudu
sun bar kauyen.
Jeka tantin matata kace da ita tazo
wannan fursuna yanzu
Nan take Sarkin yaki yaje ya cika
umurni sai ga zuraiha tareda laila
ta tasota a gaba.
Da zuwansu sai sarki larbusa ya
zare wata karamar wuka mai karfin
tsiya a jikinsa ya yanki damtsen
hannun laila wajen ya dare jini yai
feshi.
Laila ta kwalla ihu sakamakon
tsananin zafi da taji.
Sannnan sarki larbusa ya dora
tsinin wukar akan makogwaron
laila yace, "mutum nawa ne basa
nan daga cikin mutanen kauyenku
a sa'adda muka far masu?"
Jikin laila na karkarwa tace, mutum
bakwai ne"
Koda jin haka sai sarki larbusa ya
bushe dariyar mugunta yai jifa da
laila tamkar an jefar da tsumma ya
dubi Sarkin yaki garbuza a fusace
yace, maza ka sake diban dakaru
dubu uku ku bazama neman
wadanan ragowar jaruman biyu a
duk inda suke.
Lallai ku kawo mini su a macce ko a
raye kafin sarki larbusa ya gama
rufe bakinsa tuni Sarkin yaki
garbuza ya ruga Izuwa inda
giwarsa take yana mai yafito
dakarunsa da hannu.
Nan da nan dakaru dubu suka dane
nasu giwayen suka rufa masa baya
suna masu tsala gudu ba sassauci.
ME ZAI FARU IDAN SU SARKIN YAKI
GARBUZA SUKA HADU DASU
HUMAIRU? "
SHIN BURIN SARKI LARBUSA ZAI CIKA
NA MALLAKAR NAHIYAR GABA
DAYAN SANNNAN YA KARA GABA?
TA YAYA SU HUMAIRU ZASU IYA
KUBUTARDA 'YAN UWANSU MATA DA
KANANAN YARA DAKE TSARE A
HANNUN SU SARKI LARBUSA?
Mu hadu a Dugunzuma littafi na
biyu don jin cigaban wannan
kasaitacen labari.
DUGUNZUMA!-2
LITTAFI NA BIYU
PART 1
LITTAFIN YAKI
#NASEER SHEHU TEARLOW #
******
Lokacin da gari ya waye a birnin
LURHAJ sai sarki ARYAN ya shirya
taro na musamman kuma na
gaggawa shida yan majalisarsa.
Bayan kowa ya hallara a cikin taron
sai ga wani sabon Al'amari wanda
ya daurewa 'yan majalisar kai suka
cika da tsananin mamaki.
Ba wani abu bane face ganin
shigowar sarki Aryan tare dasu
jarumi Humairu su biyu dukkaninsu
a cikin shigar yaki.
Cikin firgici 'yan majalisar suka
mike tsaye gaba dayansu suna
masu matukar al'ajabi amma
dayansu baice uffan ba har sarki ya
zauna akan kujerarsa da ya saba
zama.
Humairu da Hashlar suka tsaya a
bayan kujerar da sarki ya zauna.
Sarki Aryan ya dubi yan majalisarsa
gaba daya yai gyaran murya
sannnan yace,
"ya ku yan majalisata na sani cewa
kun yi matukar mamaki bisa
ganina a cikin shigar yaki da nayi
da wadannan mafarauta.
Koda sarki Aryan yazo nan a
zancensa sai yai shiru, kawai sai ya
dubi Hashlar.
Nan take Hashlar ya warware
yankakken hannunsa mai dungulmi
kowa ya gani, Al'amarin da ya
firgita yan majalisar kenan
hankalinsu ya dugunzuma ainun
fiye da farko sarki yace, "ya ku yan
majalisata kuyi sani cewa masu iya
magana sunce gani ya kori ji.
Dukkaninku kun san cewa
wadanan mafarauta na bayana da
suka zo daga kauyen Garul Aswar
sun kasance gawurtattun jarumai
masu dakawa maza gumba a
hannu kuma su bakwai ne.
Dare da rana basa rabuwa amma a
yanzu wani babban bala'i yazo
mana wanda ya kashe sauran
abokansu mutum biyar shine
sanadin rashin hannu daya ga
Hashlar kamar yadda ya nuna
muku kuka gani.
A yanzu haka an baje kauyensu na
Garul Aswar an kashe dukkanin
manyan mazajensu, an sace
matayensu da kananan yaransu.
Koda sarki

Please Login or Register in order to submit comment