Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Aryan yazo nan a
jawabinsa sai gaba dayan yan
majalisar suka dada dimaucewa
suka firgita ainun.
Wazirin sarki ARYAN ya dubeshi a
rude yace,
Ya shugabana lallai muna cikin
tsananin masifa domin babu wata
runduna ta mayaka da zata iya yin
wannnan barna face wannan
bakuwar runduna wacce aka ce a
halin yanzu ta kama kasashe dari
biyu da arba'in da uku a wannan
nahiya.
Sai da sama da kasashe tamanin
suka hada kai da dakarun taron
dangi domin su kawar da wannnan
BAKAR RUNDUNA amma suka kasa.
Ance wannan bakuwar runduna ta
wadansu irin mutane ce masu kirar
mutanen farko.
Ya shugabana bamu da wani zabi
wanda yafi mu hada namu inamu
kowa da kowa muyi hijira mubar
kasar nan gaba daya.
Lallai a gaggauta yin shela a
birnida kauye a bayar da wannnan
izini
Koda waziri yazo dai-dai nan a
zancensa sai sarki Aryan ya daka
masa tsawa, bama shi waziri ba
hatta sauran yan majalisar dake
wajen sai da suka firgita
Sarki ARYAN ya dubi waziri cikin
tsananin fushi yace, wacce irin
maganar banza kake yi ne haka? "
Shin ka manta ne cewa wadanan
abokan gaba ance sun iso har
kauyen Garul Aswar, wane isasshen
lokaci ne damu wanda har zamu
iya gama shiri mu yi hijira basu zo
sun riskemu ba?"
Ko kuma kana so ne sai muna kan
hanya suyi mana kofar rago su
ritsamu suyi mana kissan kiyashi?"
Dukkan namijin kwarai baya gudu
ya bar mahaifarsa domin itace abar
tutiyarsa.
Anan aka haifi iyayenmu da
kakanninmu wadanda suka bayar
da jininsu don kare iyalansu da
dukiyoyinsu har aka samemu ashe
kuwa ya zama wajibi muma mu
bayar da jininmu don kare
bayanmu koda kuwa dayanmu ba
zai tsira da rayuwarsa ba.
Bisa binciken da nayi a yanzu duk
kasashen dake bayanmu duk an
kamasu, wadanda make gabanmu
haka
Mu kadai ne muka rage, wannan
alama ce mai nuna cewa su kansu
wadanan rundunar bakaken dakaru
sun san cewa muna da karfi.
Ya zama dole mu tsaya mu jajirce
muyi iya kokarinmu ya zamana
cewa kafin akar biri, biri yayi barna.
Ka tuna cewa koda mun ce zamu yi
hijira a yanzu abu ne mawuyaci mu
tsira tunda duk kasar da zamuje a
gabanmu ko a bayanmu tuni
wadanan bakin dakaru sun kamata.
Ta ina zamu bi mu wuce har mu iya
barin nahiyar gaba daya?
Gwara mu tsaya mu bar abin tarihi
wanda ba za'a taba mantawa dashi
ba.
Abinda nake so da ku shine maza
aje a bayar da shelar cewa kowa
yayi shirin yaki ban daukewa duk
wanda ke da kashin lafiya ba face
kananan yara da tsofaffi.
Wanda duk yayi kokarin guduwa ni
da kaina zanbi sawunsa na zare
masa ruhin numfashinsa.
Koda gama fadin Hakan sai sarki
ARYAN ya mike tsaye ya fice daga
cikin dakin taron.
Humairu da Hashlar na biye dashi a
baya.
Ai kuwa suma yan majalisar sai
suka mike tsaye gaba dayansu cikin
sauri suka bisu a baya duu.
Nan take aka bayar da shelar shirin
yaki
Nan fa dakaru suka yi ta tuttudowa
daga cikin birane da kauyuka suna
taruwa a kofar birnin akayi ta fito
da makaman yaki gamida tarkuna
iri iri har dama irin wadanda anfi
shekara da shekaru ba'a sake yin
amfani dasu ba.
Kafin cikar kwana daya da yini daya
kofar birnin LURHAJ ta cika da
dakarun yaki sama da mutum
miliyan Ashirin da biyar ga sunan
tsubi tsubi, sahu sahu
Wasu akan dawakai, wasu akan
rakuma da Alfadarai wasu kuma a
kasa.
Yan baka dabam, masu takobi da
garkuwa dabam, sai kuma yan
masu da yan majajjawa.
Kai komai yawan runduna da
kwarjininta idan taga wannan ta
mutanen birnin LURHAJ sai
hankalinta ya tashi domin ta san
cewa kawar da wannnan din ba
karamin aiki bane.
Sarki ARYAN ne ya zamo jagoran
wadanan mayaka, Humairu da
Hashlar na taimaka masa, kuma
sune akan gaba rundunar mayakan
sun zuba ido kawai suga ta inda
abokan gabar zasu bullo.
Dama an tura dakarun leken asiri
gabas da yamma, kudu da arewa
Izuwa dazuzzuka sunyi kwanton
bauna akan bishiyoyi masu tsawo
wadanda da zarar sun hango
abokan gaba zasu ruga suzo su
sanar.
Idan mutum yaga su sarki ARYAN a
cikin sulken yaki a wannan Lokaci
dole ne yasan cewa maza sun fito
da shirin ayi ta ta kare domin hatta
Humairu da Hashlar sun rufe
dukkanin jikinsu da kayan karfe
hatta kawunansu kuwa sun sanya
hulunan karfe idanunsu kadai ake
gani.
A ranar kwana da yini daya ne
kuwa wani dan leken asiri da aka
tura yammacin dajin ya falfalo da
gudun tsiya Izuwa kofar birnin
LURHAJ inda su sarki ARYAN suka
yada sansani.
Da isowarsa gaban sarki sai ya zube
kasa yana haki ya kwashi gaisuwa
sannnan ya dago kai ya dubi sarki
ARYAN yace ya shugabana na
hango wadannan dakarun sumame
yanzun nan sun durfafo wannan
gari namu bisa giwaye.
Narantse da darajar iyayena ko a
labari ban taba ganin mutane masu
irin girmansu da kwarjininsu ba.
Sarki ARYAN yace, nawa ne
adadinsu? "
Dan leken asirin yace, gaba
dayansu basu fi su dubu daya ba
yanzu haka sun ketare
kwazazzabon Bamhar suna daf da
isowa kwarin kusara.
Koda jin haka sai sarki ARYAN yai
murmushi yace, "kadan ne daga
cikinsu kuma an turo su ne neman
su Humairu domin tabbas labari ya
riski Sarkinsu bisa dakarunsa guda
uku dasu Humairu suka kashe,
Koda sarki Aryan yazo nan a
jawabinsa sai kuma ya dubi
Humairu da Hashlar yace, ni da ku
da kuma dakaru dubu kozo muje
mu tari wadanan abokan gaba tun
gabanin su iso nan kofar birnin,
Ina son mu kashe su duka amma
mu bar daya jal daga cikinsu
wanda zai koma ya kai labari.
Koda jin wannnan batu sai Hashlar
ya dubi sarki ARYAN cikin alamun
tsoro yace, ya shugabana anya
kuwa zamu iya da mutum dubu na
rundunar wadanan abokan gaba? "
Ka tuna fa cewa da kyar muma
muka kashe mutum uku kacal.
Maimakon sarki ya baiwa Hashlar
amsar tambayarsa sai ya dubi
Sarkin yakinsa wanda ake kira
BARDE HABWAN yace, wanda duk
ya karaya ya koma da baya ba sai
ya biyomu ba.
Koda gama fadin Hakan sai sarki
ARYAN ya zaburi dokinsa da gudu
ya nufi cikin daji.
Cikin sauri habwan, humairu da
Hashlar suka rufa masa baya
sannnan sauran dakaru dari tara da
casa'in da tara suka bisu duu.....
Kai kace yakin ne ya barke a
sannnan,
* * *
Sarkin yaki garbuza da dakuru
dubu na tafe bisa giwayensu suna
bin sawun kafafun su Humairu da
Hashlar sai suka iso wannan wuri
wanda ake kiran kwarin kusara.
Shi dai kwarin kusara wata yar
sirriyar hanya ce wacce manyan
dogoyen duwatsu suka sa ta a
hanya.
Tun kafin su garbuza su iso wannan
wuri na kwarin kusara ashe su sarki
ARYAN sun iso sun yi kwanton
bauna akan saman duwatsun.
Rabin dakarun da suka biyo sarki
ARYAN duk yan baka ne kuma ya
gaya musu cewa da zarar ya basu
umurnin harbi su tabbatar da cewa
sun harbi wuyan dakarun da
fuskokinsu kada su kuskura su ce
zasu harbesu a gangar jikinsu.
Sarki ARYAN ya bayar da wannnan
umurni bisa la'akari da labarin dasu
Humairu suka bashi bisa gurmuzun
da suka yi da wadannan
samudawan.
Sai da su Sarkin yaki garbuza suka
iso tsakiyar wannan kwarin sai
sarki ARYAN ya bayar da umurnin a
bude musu harbi
Nan take kuwa yan baka suka fara
sakin harbi kafin dakarun garbuza
su daga garkuwoyinsu su fara kare
harbin tuni an kashe musu sama da
mutum dari biyu.
Da yake garkuwar tasu garbuza ta
karfe ce sai ya zamana cewa da
kibiya ta dira a jikinta kaga ta kare.
Koda sarki Aryan yaga harbin
bashida sauran amfani sai ya zare
takobinsa ya kwarara uban ihu
yana mai bayar da umurnin a
afkawa su garbuza.
Nan take kuwa Humairu da Hashlar
da sauran dakaru suka zare
takubbansu suka daka tsalle Izuwa
kasan duwatsu suka dira akan su
garbuza.
Nan take wurin ya yamutse aka
ruguntsume da azababben yaki.
DUGUNZUMA..2!!!
LITTAFI NA BIYU
PART 2
NASEER SHEHU TEARLOW
******
Koda sarki Aryan ya ga harbin
bashida sauran amfani sai ya zare
takobinsa ya kwarara uban ihu
yana mai bayar da umurnin a
afkawa su garbuza.
Nan take kuwa Humairu, Hashlar da
sauran dakaru suka zare
takubbansu suka daka tsalle Izuwa
kasan duwatsun suka dira akan su
garbuza.
Nan take wurin ya yamutse aka
ruguntsume da azababben yaki.
Duk inda sarki Aryan, humairu da
Hashlar suka durfafa sai dai kaga
maza na zubewa kasa ratata
tamkar sarki ya hana dawa
tsayuwa.
Haka kuma duk inda garbuza da
sauran dakarunsa suka kutsa cikin
dakarun su sarki Aryan sai dai kaga
suma suna yin gagarumar barna.
Al'amarin da ya matukar girgiza
kowanne bangare kenan domin
asarar rayuka ta shafesu su duka.
Sai da aka shafe kusan sa'a ana
wannan artabu ya zamana cewa
babu abinda kunne keji face ihun
mazaje da haniniyar dawakai da
giwaye,
Jini kuwa ya rinka fallatsi da
famtsama sassan jikin bil'adama ya
kama shawagi a sama yana
zubowa kasa.
Ana ckin wannan hali ne Sarkin yaki
garbuza ya farga cewa idan aka ci
gaba da yakin a haka za'a iya yin
ragas.
Koda fahimtar hakan sai garbuza ya
kurma uban ihu yana mai baiwa
dakarunsa inkiya akan su dan ja da
baya nan take kuwa dakarun suka
bi wannan umurni suna ja da baya
kadan sai su Aryan suka ja da
bayan aka tsaya akayi cirko cirko
ana kallon juna.
A sannnan ne aka fahimci cewar
dakarun su garbuza basu wuce
saura su dari uku ba, su kuwa
dakarun su sarki ARYAN basu wuce
saura su dari shida ba, alhalin dama
can sau biyu suka ninka su garbuza.
Kaga kenan dai babu bangaren da
zai iya daga hannu yace ya sami
nasara.
Koda ganin haka sai Sarkin yaki
garbuza ya nuna sarki ARYAN da
takobinsa yace,
Ya kai wannan takadarin jarumi
kayi sani cewa idan muka ci gaba
da wannnan yaki a haka jama'ata
da jama'arka duk karewa zasu yi.
Shawarar da zan bamu itace ni da
kai mu kara wanda duk ya kashe a
tsakaninmu ya zama shugaba sai
yayi duk yadda yaso da sauran
dakarun dake tsaye anan.
Idan kuma baka son mu yi wannan
fada nida kai ka bani ragowar
jarumai biyu wadanda suka kashe
mana wadansu dakaru namu guda
uku acan wani kauye da ke can
baya na tafi dasu Izuwa ga
sarkinmu.
Sa'adda garbuza yazo dai-dai nan a
zancensa sai sarki Aryan yai shiru
yana nazari da tunani.
Daga can sai ya dubi garbuza yace,
bazan baka wadanan jarumai biyu
ba, don haka na yarda mu kara yaki
ni da kai.
Koda ka sami nasara akaina ina mai
baka sako ga sarkinka ka gaya
masa cewa nayi alkawari kafin a
gama wannan yaki shima sai jini ya
zuba daga jikinsa.
Koda jin haka sai garbuza ya bushe
da dariyar mugunta sannnan ya
murtuke fuska yace, inda ka san ko
wanene sarkina da baka fadi haka
ba.
Ina tabbatar maka da cewa a halin
yanzu duk duniya babu sadauki ko
kuma gwarzon mayaki kamar
sarkina.
Ya halarci yaki guda casa'in da
shida a rayuwarsa amma ko digon
jini bai taba diga ba daga jikinsa.
Ba'a taba kaishi kasa ba, kuma duk
abinda ya sa a gabansa sai sami
nasara.
Koda jin haka sai sarki Aryan yayi
guntun murmushi yace, "ai shi
tsautsayi bashida rana, kuma ba
kullum ake kwana akan gado ba.
Lallai wannan karon sai na rugaza
tasirin jarumtakar Sarkinka.
Koda jin wannnan batu sai garbuza
ya fusata ainun ya ruga Izuwa kan
sarki Aryan yana mai daga katuwar
takobinsa sama yana kururuwa.
Shima sarki Aryan sai ya rugo
gareshi yana ihu, ai kuwa suna
haduwa suka kacame da
azababben yaki.
Nan fa ragowar dakarun garbuza
dasu jarumi Humairu suka ga abin
al'ajabi irin wanda basu taba gani
ba, domin ana fara wannan
gurmuzu sarki Aryan ya zamewa
garbuza alakakai ya kuntatashi.
Tsananin zafin naman sarki ARYAN
ya wuce tunanin kowa dake wajen.
Gashi dai kiri kiri garbuza yafi sarki
ARYAN girma da tsagwaron karfin
dantse, amma kuma da yake sarki
ARYAN ya fishi zafin nama da
gocewa da iya sarrafa takobi sai
gashi ya kuntatashi.
Bugu da kari sarki ARYAN bai tsaya
kai sara da suka kadai ba sai da ya
hada da kai naushi da bugu hannu
da kafa kuma ya rinka yin alkafira
yana shawagi a saman garbuza kai
kace ya kasance tsuntsu mai fuka-
fuki.
A haka ne ya sami nasarar yankar
garbuza a fuska yayi masa wani
katon bille akan kumatunsa kuma
ya jera masa duka goma sha daya a
kirji da kafafunsa biyu a sama.
Tun garbuza yana yin baya baya
yana taga taga har sai da ya fadi
kasa, takobin hannunsa fadi can
gefe daya ya baje a kasa
magashiyan kafin garbuza ya
yunkura ya mike tsaye tuni sarki
ARYAN ya sake afkawa ragowar
dakarun garbuza, cikin kankanin
lokaci ya kashe su gaba dayansu su
dari ukun.
Wani irin mugun kisa ya rinka yi
musu yana shaftare musu
makogwaro da kaifin takobinsa a
Lokacin da suma ya rinka shawagi
a kansu.
Dukkaninsu suka rikito kasa daga
kan giwayensu suka zube kasa
matattu.
Koda garbuza ya ga abinda ya faru
ga sauran dakarunsa sai ya yunkura
cikin zafin nama ya ruga inda
takobinsa ta fadi domin ya dauka
amma sai sarki ARYAN ya dako
tsalle daga inda yake ya doki
bayansa ya kifa da rub da ciki.
Kafin ya dago ya juya Aryan ya
daka tsalle ya dira a gabansa ya
dora kaifin takobinsa akan
wuyansa.
Garbuza ya waigo ya dubi sarki
Aryan cikin tsananin fusata jikinsa
na tsuma yace, me kake jira dani,ka
kashe mana?
A wannan Lokaci Humairu, Hashlar
da sauran dakaru sun bude baki
kawai suna kallon ikon Allah sun
kasa koda motsi saboda tsananin
mamaki bisa ganin wannan
gagarumar jarumtaka da sarki
ARYAN yayi.
Sarki Aryan ya dubi Sarkin yaki
garbuza ya yi murmushi irin na
manyan jarumai wadanda suka
yarda da kansu yace, bazan kashe
ka ba, domin inason ya zamana
cewa kai kadai ne ka koma wajen
Sarkinku a raye domin ka isar da
sakon da na baka gareshi.
Tabbas idan yaga wannan rauni
danayi maka a fuskarka kuma yaji
cewa na kashe sauran dakarunka
zai yarda cewa kafin a gama
wannan yaki shima sai jini ya zuba
a jikinsa.
Lallai sai na rugaza tarihin
jarumtakarsa a duniya.
Koda sarki Aryan yazo nan a
zancensa sai garbuza ya mike tsaye
cikin takaici ya ruga Izuwa inda
giwarsa take ya daka tsalle sama
ya haye kanta sannnan ya juya da
baya ya nausa Izuwa cikin daji da
gudu.
Tafiyar Sarkin yaki garbuza keda
wuya sai su Humairu suka rugo da
gudu Izuwa inda sarki ARYAN yake
suna masa jinjina.
Maimakon suga sarki ARYAN yana
murna sai suka ga idanunsa sun
ciko da kwalla har hawaye ya zubo
masa.
Al'amarin da ya matukar firgitasu
kenan, hankalinsu ya dugunzuma
ainun,
Cikin sanyin jiki Humairu ya risina a
gaban sarki ARYAN yace ya
shugabana ina dalilin zubar
wannan hawaye naka?
Kamata yayi ka kasance mai
fаrinсiki bisa wannan nasara da
muka samu ta kashe dakaru
Kimanin dubu na wadanan abokan
gaba.
Sa'adda sarki Aryan yaji wannan
batu sai yayi ajiyar zuciya yana mai
share hawayensa sannnan ya dubi
Humairu yace, ya kai jarumi mai
sa'a da nisan kwana, kayi sani cewa
wannan nasara da muka samu ba
nasara bace.
Gagarumin bala'i ne ga
mutanenmu domin tamkar mun
tsokano tsuliyar dodone a Lokacin
da yake kwance yana barci.
Wannan hawaye daka ga ina
zubarwa kuwa bana komai bane
face na hango halin da kasarmu
zata koma.
Tabbas sai an rushe dukkanin
gidajenmu, an kone komai.
Sai an kashe dukkanin mazajenmu
Babu sauran masu tsira face
kananan yara da mata
Ya kai Humairu ka kasance mai rike
alkawarin dake tsakaninmu
Lallai ka kare rayuwar matata har
Izuwa Lokacin da zata haihu lfy
Kuma ka reni abinda zata haifa
acan wata nahiyar dabam
Komai daren da dadewa ina sa ran
cewa dan da matata zata haifa zai
dawo birnin LURHAJ ya karbi
karagar mulkinsa.
Yanzu ku tashi muyi sauri mu koma
can kofar gari domin mu cigaba da
shirin tarar abokan gaba domin da
zarar garbuza ya kai sakona zasu
taho gaba dayansu ayi wannan
gagarumin yaki.
Sa'adda sarki Aryan yazo nan a
zancensa sai jarumi Humairu yace,
Ya shugabana ina mai neman
alfarma guda daya.
Inason yanzu nida Hashlar ka
kyalemu mu bi sawun wannan
badakare da ya tafi kaiwa sarkinsu
sakonka domin muga inda
sansaninsu yake mu ceto rayuwar
iyayenmu mata da masoyanmu
wadanda muke son mu aura anan
gaba. Lallai zan kasance mai cika
alkawarin dake tsakanina dakai,
wato zan dawo domin na tserar da
rayuwar matarka.
Koda sarki Aryan yaji wannan batu
sai ya dubi Humairu cikin alamun
tausayawa yace,
Ya kai wannan jarumi kayi sani
cewa ko ka kadan bana yin
kokwanto bisa duk abinda kace
zakayi.
Na yarda cewa zaku iya
Zuwa ku karbo iyayenku da 'yan
uwanku, amma fa ku sani cewa
koda kun karbosu abune mawuyaci
ku dawo tare dasu har nan a raye
domin na tabbatar da cewa sai
abokan gaba sun kure muku gudu
sun riskeku.
Idan ma basu riskeku ba akan
hanya ba, ko kun iso birninmu ai
dai baza a fasa yin wannnan yaki
ba kuma kuna ji kuna gani zaku
rabu dasu.
Ku daina tunanin akwai sauran
rayuwa ga jama'armu a wannan
nahiya har da kuke sa ran zaku auri
masoyanku kuci gaba da zama.
Ina tabbatar maku da cewa
wadanan abokan gabarmu sai sun
mamaye ko ina a wannan nahiya
tamu sai ya zamana cewa an
manta da irin zuri'armu sai tasu.
Wanda duk yai saura a cikinmu ya
gudu Izuwa wata nahiyar dabam
shine kadai zai iya bayar da
labarinmu.
Bazan hanaku zuwa aiwatar da
abinda ke ranku ba,don nasan kai
mutum ne mai sa'a amma ina mai
dada rokonka da kada ka karya
alkawarin dake tsakaninmu.
Laila kafin na fadi na mutu a
wannan yaki inason naga Lokacin
da zaka dauke matata ka fitar da
ita daga wannan nahiyar gaba
daya.
Idan har ka cika alkawari ka dawo
zan sanar da kai hanyar da zaka bi
ka sulale daga cikin birninmu koda
kuwa ana tsaka da wannnan yaki.
Koda jin haka sai jarumi Humairu
yace, tabbas zaka sameni mai cika
alkawari. DUGUNZUMA!!!
LITTAFI NA BIYU
PART 3
LITTAFIN YAKI
NASEER SHEHU TEARLOW
********
Lallai kafin na fadi na mutu a
wannan yaki inason naga Lokacin
da zaka dauke matata ka fitar da
ita daga wannan nahiyar gaba
daya.
Idan har ka cika alkawari ka dawo
zan sanar da kai hanyar da zaka bi
ka sulale daga cikin birninmu koda
kuwa ana tsaka da wannnan yaki.
Koda jin haka sai jarumi Humairu
yace, tabbas zaka sameni mai cika
alkawari.
Nan take Humairu da Hashlar suka
yiwa sarki ARYAN sallama sannnan
suka juya da baya suka falfala da
azababben gudu Izuwa cikin daji.
Kaji manyan mazaje wadanda babu
ruwansu da hawa doki domin sun
saba da gudun kafa wanda ya kai
tafiyar Zango dari.
Sai da Humairu da Hashlar suka
kule a cikin daji sannnan su sarki
ARYAN suka kada dawakansu suka
zaburesu da gudu suka koma birnin
LURHAJ.
Tun daga nesa dakarun yaki dake
tsaitsaye a sahu sahu a bakin kofar
gari suka ga dawowar su sarki
ARYAN sai suka rude da shewa suna
yi musu jinjina don sun tabbatar da
cewa sun sami nasara a wannan
fita da suka yi.
Abinda ya daurewa kowa kai shine,
ganin fuskar sarki ARYAN a
murtuke babu wani sassauci.
Cikin sauri aka budewa su sarki
ARYAN kofa suka kunna kai.
Da isarsu kofar fada sai ga wata
kuyanga ta fito daga cikin gidan
sarautar a guje fuskarta cike da
annuri.
Kuyanga ta zube kasa a gaban sarki
Aryan tana haki tace,ya shugabana
sarauniya ta haihu lafiya.
Koda jin wannnan batu sai sarki
Aryan ya kamu da tsananin farin
ciki, nan take ya duro daga kan
dokinsa ya ruga Izuwa turakar
matarsa lushirat.
Yana shiga ya isketa kwance akan
gado ga kyakkyawan jaririnta a daf
da ita lullube cikin mayafi yana
barcinsa abinsa.
Sarki ARYAN ya matso daf da
lushirat fuskarsa cike da annuri ya
sumbaci goshinta yana mai yi mata
barka da haihuwa lafiya sannnan
yace,
Wane suna ya kamata a sawa
wannan jaririn? "
Koda jin wannnan tambaya sai
hawaye ya zubowa lushirat tace,
banida zabi bisa sunan da za'a
sawa wannan yaro tunda abune
mawuyaci ka rayu Izuwa ranar da
za'a yi bikin radin sunansa.
Koda jin wannnan batu sai jikin
sarki Aryan yai sanyi ya dauki
jaririn ya rungumeshi a kirjinsa,
kawai sai idanunsa sun ciko da da
har hawaye ya fara sartu bisa
kumatunsa sannnan ya dubi
lushirat cikin alamun tsananin
tausayawa yace, tabbas ba zan ga
ranar da za'a yi radin sunan
wannan yaro ba abinda nake so
dake shine, ki sawa wannan yaron
sunana domin naji a jikina kuma
bincikena ya tabbatar da cewa
shine zai gajeni har ma sai ya fini
jarumtaka kuma shine zai karbi
karagar mulkin kasar nan a hannun
wadanan abokan gaba namu.
Koda sarki Aryan yazo nan a
zancensa sai lushirat ta fashe da
matsanancin kuka ta mike tsaye ta
rungume sarki tace,
Ya kai mijina kayi sani cewa ba zan
iya rabuwa da kai ba a yanzu.
Lallai kazo mu yi sauri mu bar
wannan nahiya gaba daya tun
kafin wadanan abokan gaba su iso
garin nan.
Sa'adda sarki Aryan yaji wannan
batu sai ya janye jikinsa daga cikin
nata ya dubeta cikin fushi yace,
Ya ya kike tsammanin cewa zan iya
guduwa na bar jama'ata a cikin
masifa?
Ta yaya kike tsammanin cewa zan
iya barin karagar mulkina wacce na
gada a wajen ubana saboda tsoron
mutuwa?
Idan nayi haka na karya tarihin
iyayana da kakannina, domin a duk
cikin zuri'armu ba a taba samun
sarkin da ya mika wuya ba ga
abokan gaba sai dai ayi yaki a
kaishi kasa.
Na rantse da darajar iyayena ba zan
mutu rago ba sai dai na mutu
jarumi.
Ni ki kyaleni na tsaya na kare
mutuncina da jama'ata amma ke
da jaririnki lallai zaku bar wannan
nahiya gaba daya domin kuje ku ci
gaba da sabuwar rayuwa a wata
nahiya dabam.
Tuni na mika amanarku ga jarumi
Humairu na kauyen Garul Aswar.
Jarumin da bincike ya tabbatar da
cewar sai ya rayu a wannan
gagarumin yaki da za'a fafata.
Laila kibi wannan jarumi Humairu
bisa duk irin umurnin da zai baki
domin na aminta dashi dari bisa
dari.
Koda sarki Aryan yazo nan a
jawabinsa sai lushirat ta sake
fashewa da kuka tana mai cewa,
Yanzu shikenan wannan da dana
haifa zai taso kenan a matsayin
maraya kuma a cikin rayuwar wuya
da rashin sanin makoma mai kyau.
Cikin hanzari sarki ARYAN ya rufe
bakin lushairat da tafin hannunsa
yace, kada ki kara fadin Haka.
Na gaya miki cewa wannan da, da
kika haifa lallai komai daren
dadewa sai ya gajeni saboda haka
koda zaku sha wahala to fa
wahalar mai wucewa ce, zaku sha
dadi a gaba.
Yake matata inason ki daukar mini
alkawari guda daya.
Alkawarin kuwa shine inason ki
raini dana kamar yadda iyayena
suka reneni wato ki koya masa
dakewar zuciya irin tawa ya
zamana cewa bai san tsoro ba
sannnan kuma kisa a horar dashi
koyon fada da yaki da yaki tun
daga kurciyarsa har Izuwa
girmansa.
Duk irin wahalar da zai sha akan
wannnan horo kada ki ji tausayinsa
kiyi masa sassauci domin ba gata
za kiyi masa ba.
Wannan shine iyakar wasiyyar da
zan bar miki kuma ina ganin cewa
wannnan shine kalamina na karshe
a gareki domin daga yanxu bana
jin zamu sake ganin juna.
Zanje mu ci gaba da shirye shiryen
yaki domin a ko yaushe abokan
gaba zasu iya isowa nan.
Koda gama fadin Hakan sai sarki
Aryan ya mikawa lushairat jaririn ta
karba sannnan ya juya ya nufi kofar
fita daga cikin turakar kai tsaye ba
tare da Ya waigo ba.
Koda ya kai bakin kofar yasa
kafarsa guda daya a waje sai
lushairat ta kwala masa kira ya
tsaya cak.
Lushairat ta ajiye jaririn nata akan
gado sannnan ta ruga da gudu ta
rungume Aryan tana mai fashewa
da sabon kuka tana mai cewa, ya
kai mijina kayi sani cewa rabuwa
da kai ba karamar masifa bace a
gareni domin ka sani cewa a halin
yanxu banida kowa a duniya face
kai da wannnan jaririn nawa.
Idan babu kai waye zai ci gaba da
bani kulawar dakeke bani?"
Koda jin tambaya sai hawaye ya
zubowa sarki Aryan yai shiru bai ce
komai ba kawai sai ya janye jikinsa
daga cikin na lushairat ya fice da
sauri.
Sau daya ya sake waigowa ya dubi
jaririn ya kau da kai ya tafi ita kuwa
lushairat sai ta ci gaba da kwala
masa kira tana ci gaba da kuka har
sai da ya bace mata da gani.
Wannan shine abinda ya faru a
birnin LURHAJ bayan sarki Aryan da
tsirarun dakarunsa sun koma gida,
kuma sun sami nasara akan su
Sarkin yaki garbuza.
******
Acan sansanin su sarki larbusa
kuwa, Lokacin da sarki larbusa ya
ga su Sarkin yaki garbuza sun dade
basu dawo ba sai ransa ya baci,
cikin tsananin fushi ya dubi wani
bardensa wanda ake kira DAUJIN
yace dashi, maza ya kamo giwarsa
ya kawo masa domin ya hau kuma
shi ka dai zai bi sawun su garbuza
domin yaga abinda yasa suka dade
basu dawo ba.
Nan take daujin ya cika umurni yaje
ya janyo giwar sarki ya kawota
gabansa yasa ta durkusa kasa bisa
guiwoyinta hudu har sarki larbusa
ya yunkura zai hau kan giwar
kenan sai aka hango Sarkin yaki
garbuza shi kadai bisa giwa ya
tunkaro sansanin a guje fuskarsa a
yamutse babu annuri kuma ga
katon bille na yankan takobi akan
kumatunsa.
Koda aka hango garbuza a cikin
wannan hali sai kowa ya cika da
tsananin mamaki.
Shi kuwa sarki larbusa sai yaji
zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar
zata kone saboda tsananin fushi.
Koda isowar garbuza daf da sarki
sai ya ja tunga ya sauko da sauri
daga daga kan giwar ya zube kasa
a gabansa ya kwashi gaisuwa yana
mai sunkuya da kansa kasa.
Larbusa ya dakawa Sarkin yaki
garbuza tsawa yace, ina sauran
dakarun da na hadaka dasu kuma
waye yayi maka rauni haka akan
fuska?"
Ba tare da garbuza ya dago kai ba
ya dubi larbusa sai yace, ya
shugabana kayi sani cewa kamar
yadda ka umurcemu mun koma
Izuwa wancan kauye amma bamu
riski kowa ba a can amma mun ga
sawayen mutum biyu."
Nan take muka ci gaba da bin
sawayen har sai da ya kaimu Izuwa
wani kwaroro mai tsawo wanda
dogoyen duwatsu guda biyu suka
sashi a tsakiya.
A dai-dai wannnan lokaci ne aka
shammacemu kawai sai harbin
kibiyoyi muka ji, kafin mu kare
kanmu da garkuwoyi an kashe
mana mutane da yawa kuma a
sannnan ne abokan gaba suka fito
daga maboyarsu suka zare
makamai suka afka mana aka
ruguntsume da azababben yaki.
Daga cikin abokan gabar har da
Sarkin birnin LURHAJ wanda ake
kira Aryan.
Ya shugabana ina tabbatar maka
da cewa tunda nake fita yaki a
rayuwata ban taba karo da
sadaukin jarumi mai naci da zafin
nama ba tamkar sarki Aryan.
Kai kadai ne zaka iya dashi, cikin
abinda bai wuce sa'a daya ba ya
kashe gaba dayan dakarun da ka
hadani dasu ya zamana cewa saura
ni kadai,
Nan fa muka shiga gurmuzu nida
sarki Aryan, sama da tsawon rabin
sa'a muna fafatawa amma na kasa
koda lakutar jikinsa.
A sannnan ne ya sami nasarar
yankata a fuska kuma yai tsalle
sama kamar tsuntsu ya rinka jera
mini naushi a kirji da kafarsa har sai
da ya kaini kasa.
Na baje cikin matukar galabaita sai
gani nayi ya dira a gabana ya sa
min kaifin takobinsa a wuyana.
A fusace na daka masa tsawa nace
me yake jira dani, kawai ya
kasheni.
Koda jin haka sai sarki ARYAN yayi
murmushi yace, abinda yasa ba zai
kasheni ba shine yana son nazo na
gayamaka cewa kafin a gama
wannan yaki kaima sai ka zubarda
jini...
Kafin garbuza ya gama rufe bakinsa
tuni sarki larbusa ya zaro wata
gajeriyar wuka a kugunsa cikin
bakin zafin nama ya sokawa
garbuza a goshinsa.
Take wukar ta lume ta fito ta
keyarsa jini ya kama kwararowa
kasa kai kace idaniyar ruwa ce ta
balle kawai sai garbuza ya bingire
kasa matacce.
Al'amarin da yai matukar razana
gaba dayan dakarun sarki larbusa
kenan da sauran bayin da aka
kamo dake daure cikin sarkoki.
Sarki larbusa ya tofawa gawar
Sarkin yaki garbuza yawu sannnan
yace,
"Girmanka da sadaukantakarka duk
sun zama na banza tunda har
kanaji kana gani aka kashe mana
mutane kuma mutum daya jal ya
zame muku alakakai "
Koda gama fadin Hakan sai sarki
larbusa ya takarkare ya kwarara
uban ihu mai tsananin firgitarwa
wanda zai iya tarwatsa dakaru
komai yawansu a filin yaki.
Nan take sarki larbusa ya bayar da
umurnin ayi shirin yaki a durfafi
birnin LURHAJ.
Mutum dari kacal ya bari a sansanin
domin su bayar da tsaro ga
matarsa da kuma bayin da aka
kamo.
Nan take sarki larbusa ya jagoranci
dakarun yaki suka bar sansanin
suka durfafi hanyar da zata kaisu
birnin LURHAJ.
Idan mutum ya dubi wannnan
runduna tasu sarki larbusa dole ne
ya firgita komai dakewar zuciyarsa
saboda kwarjininsu da kuma irin
tarin kayan yakin da suke dauke
dasu.
Tabbas in da sarki larbusa ya san
abinda zai biyo baya da bai bar
kowa a wannan sansanin ba.
********
ASHE duk abinda ya faru yanzu a
sansanin su sarki larbusa jarumi
Humairu da Hashlar na labe a cikin
duhuwar

Please Login or Register in order to submit comment