Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta dubi
Humairu tace, " ta yaya akayi kasan
wadanan abubuwa? "
Humairu yayi murmushi yace, "Ni fa
tsohon mafarauci ne wanda ya
gudanar da rayuwarsa gaba daya a
cikin daji. "
Yana gama fadin Hakan sai
lushairat ta juya ta sake goya
jaririnta a baya wanda tuni ya dade
da yin barci, sannnan ta lalabo
duwatsu guda biyu ta karyi wani
ice, ta hada kyastu ta kunna wuta a
jikin icen ya zame mata fitila, ta
kunna kai Izuwa cikin dajin.
Amma kafin ta tafi sai da ta dauki
Addar Humairu.
Tun Humairu na hango lushairat
har sai da ta kule a cikin dajin ya
daina hangota.
Tafiyar lushairat keda wuya sai ya
fada cikin kogin tunani, inda ya
rinka tuna duk abubuwan da suka
faru a baya tsakaninnsa da
abokansa wadanda dakarun sarki
labarusa suka kashe, da duk irin
gwagwarmayar da suka yi shi da
Hashlar da kuma yadda yayi
rabuwar karshe da mahaifiyarsa da
masoyiyarsa laila.
Humairu ya tuno da yadda suka
iske kauyensu bayan an kashe
kowa an kone gidajensu.
Koda yazo dai-dai nan a tunaninsa
sai ya kamu da tsananin bakin ciki
ya fashe da matsanancin kuka.
Yana cikin wannan hali ne yaji
motsi daga can wani sako, alamar
an durfafo inda yake.
Cikin firgici ya lalubi inda takobinsa
take yaji bai jita ba,ya yunkura da
nufin ya mike tsaye ya nemi
maboya, amma sai ya kasa saboda
a wannnan lokaci kafar tasa ta kara
yin tsami da kumburi fiye da farko,
gashi dafin kibiyar data sokeshi
yana yi masa tsananin zogi da
radadi.
Bisa dole Humairu ya saduda ya
zuba ido kawai Izuwa inda yake
juyo wannan motsi.
Sannnu a hankali motsin ya rinka
karuwa, kuma wani irin takun
sawu ne mai karfi yake tunkaroshi.
Kwatsam!m Ba zato ba tsammani
sai ga wata narkekiyar kura mai
tsananin muni da girman gaske ta
bayana a gaban Humairu.
Ita dai wannnan kura tafi shekara
Ashirin a cikin wannan daji, kuma
mafarauta sun dade suna kokarin
kamata kosu kasheta amma abun
ya gagara.
An sha yin gangami a fito farautar
wannan kura amma sai a kwana
bakwai ana nemanta ba'a ganta ba.
Duk bayan kwana talatin sai
wannnan kura ta fito ta yiwa
fatake ko mafarauta mummunar
barna, ta kashe mutane da yawa.
Har ma an canfa wannan kura da
cewar iska ce ba dabba ba,
musamman da akayi la'akari da
siffarta.
Dama Humairu ya dade yana jin
labarin wannan kura,don haka a
yanzu da yayi arba da ita sai ya
firgita ainun ya tabbatar da cewar
ajalinsa yazo.
Kurar ta tsaya cak! A nesa kadan
suka fara kallon kallo ita da
Humairu tana nazarinsa.
Koda ta lura da raunin dake kafarsa
domin idanunta suna ganin komai
sarai a dajin kamar ba dare bane.
Koda kurar ta gane cewa Humairu
ba zai iya tsinana komai ba sai ta
yanke shawarar kawai ta daka
tsalle sama ta turmusheshi tayi
masa kwab daya.
Ai kuwa sai ta daka wawan tsalle a
sama zata dira akansa.
Humairu ya kwarara uban ihu irin
na wanda yaga mutuwa muraran!
Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai
kawai yaji jini yayi tartsuwa akan
fuskarsa, yana dago kai yaga an
raba gangar jikin kurar gida biyu ta
fado kasa matacciya.
Yana kallon kasa yaga takobinsa na
digar da jini, kuma ba wani bane ke
rike da takobin tasa ba face
gimbiya lushairat wacce ke goye da
jaririnta. A daya hannun nata kuwa
ganye ne da saiwar bishiyar da ta
tafi nema.
Bai san sa'adda ya wangame ba
yana
Kallon lushairat idanunsa a kafe
kamar gunki.
******* DUGUNZUMA!!!
LITTAFI NA 4
PART 4
ADVENTURE STORY
NASEER SHEHU TEARLOW
*******
Ai kuwa sai ta daka wawan tsalle a
sama zata dira akansa.
Humairu ya kwarara uban ihu irin
na wanda yaga mutuwa muraran!
Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai
kawai yaji jini yayi tartsuwa
akan fuskarsa, yana dago kai yaga
an raba gangar jikin kurar gida
biyu ta fado kasa matacciya.
Yana kallon kasa yaga takobinsa na
digar da jini, kuma ba wani
bane ke rike da takobin tasa ba
face gimbiya lushairat wacce ke
goye da jaririnta. A daya hannun
nata kuwa ganye ne da saiwar
bishiyar da ta tafi nema.
Bai san sa'adda ya wangame ba
yana
Kallon lushairat idanunsa a kafe
kamar gunki.
Har sai da tazo ta tsugunna a
gabansa ta fara kwance tsumman
da aka daure raunin nasa dashi
sannnan ya dawo cikin haiyacinsa
yana mai yin doguwar ajiyar
zuciya.
Lokacin da lushairat ta gama
kwance tsumman taga irin zurfin
raunin nasa sai hankalinta ya
dugunzuma ainun,
Shi kansa jarumi Humairu sai da ya
firgita da ganin raunin yaji kamar
yace ta sare kafar gaba daya ya
huta.
Kawai sai lushairat ta sake yagar
gefen rigarta ta cusa a cikin bakin
Humairu ta dubeshi tace, ihun da
zaka yi yanzu sai yafi wanda duk
kayi a baya.
Tana gama fadin Hakan sai ta mike
tsaye taje ta saro wata danyar
jijiyar bishiya doguwa tazo ta kama
hannayen Humairu ta dauresu
tamau a jikin bishiyar, sannnan ta
kama daya lafiyayyeyar kafar tasa
itama ta daureta tamau.
Daga nan sai ta dake wannan
ganyen bishiya data samo, dama
busasshe ne, ya zama gari.
Wannan saiwar bishiyar kuwa sai
ta zubata a cikin wani dan karamin
kasko data dora akan wuta ta shiga
dafawa.
Koda tazo ta sake zama a gaban
Humairu ta debo wannan dakakken
ganyen zata cusa a cikin ramin
raunin sai ta dubi Humairu, shi
kuwa sai yayi mata murmushi.
Koda ta cusa maganin a cikin
raunin a karo na farko sai Humairu
yayi wani irin zallo, ya rintse
idanunsa ba tare da yayi ihu ba.
Al'amarin da yai matukar bata
mamaki kenan, amma daya bude
idanunsa sai ga hawayen wuya ya
zubo masa.
Haka dai taci gaba da cusa garin
maganin yana ta mutsu-mutsu
yana hawaye har ta gama sa masa
magani.
Tana gamawa sai ta dubeshi tayi
masa jinjina, tace Mazaje da yawa
wadanda suka sami irin wannnan
rauni idan akazo ana sa musu
wannnan magani mutuwa suke yi
kosu suma, amma kai, yanzu gashi
ka jure, tabbas ka cika GWARZON
JARUMI mai juriya abin kwatance.
Ina mai tabbatar maka da cewa
nan da cikar sa'a guda kumburin
kafar taka zai sace gaba daya,
kuma zaka iya taka kafarka muci
gaba da tafiya. "
Koda jin wannnan batu sai farin ciki
ya lullube Humairu ya dubi
lushairat yayi mata godiya bisa yi
masa wannnan magani da tayi.
Koda jin wannnan godiya sai
lushairat tayi murmushi tace, "Ai
bai kamata kayi mini godiya ba tun
da har yanzu banyi maka rabin
abinda kayi mini ba nida jaririna.
Ko anan na rasa rayuwata nida
dana ka gama cika alkawarin da ka
daukarwa mijina.
Lallai kana bina bashi don ka
sallama rayuwarka don ceton tamu
rayuwar nida dana.
Ina mai tabbatar maka da cewa
RINTSI DA TSANANI daka shiga a
can gidan sarautarmu ka shigo har
ka sami damar fita a raye babu
wani jarumi da zai iya ta iba
Marigayi ba."
Koda tazo nan a zancenta sai
idanunta suka ciko da kwallah,
hawaye ya subuto mata, nan take
tausayinta ya kama Humairu, ya
dubeta cikin alamun tausayawa
yace, "ya shugabata hakika
rayuwarki abar tausayi ce,tunda kin
taso a cikin Daula, jin dadi da mulki,
amma yanxu gashi kece a cikin daji
kina rayuwa irin ta dabbobi
wadanda basu da gidan kwana da
abinci sai sun nema dare da rana.
Lushairat ta gyada kai tace, "Ai ni
da kai duk ababan tausayi ne tunda
kaima an tarwatsa kauyenku da
Danginku.
An rabaka da abokanka, kuma
aminanka wadanda tun yarinta ku
ka taso tare kuma kuka shaku da
juna ainun kamar hanta da jini.
Haka dai Humairu da lushairat suka
ci gaba da hira har Izuwa tsawon
sa'a guda basu sani ba.
Kamar da wasa Humairu yaga gaba
dayan kumburin kafarsa ya
sace,kuma ta daina zogi da radadi.
Cikin mamaki ya yunkura ya matsa
kafar, nan ma sai yaga ya iya takata
har ma ya mike tsaye daram! Ba
tare da ya dafa komai ba.
Al'amarin da ya jefashi cikin
dumbin farin ciki kenan mara
misaltuwa.
Bai san sa'adda ya kama yin tsalle
da Rawa ba.
Ita kuma lushairat sai ta bishi da
kallo tana ta faman yi masa dariya.
Suna cikin wannan hali ne suka jiyo
sukuwar dawakai daga can nesa,
cikin hanzari suka kashe wutar da
lushairat ta dafa magani kuma suka
kwashe komai nasu daga wajen
suka baje kasa sannnan suka ruga
Izuwa cikin duhuwar bishiyoyi suka
buya.
Suna nan a boye sai suka hango
wadansu mahaya Kimanin su
arba'in sun durfafo inda suke a
sukwane bisa giwaye.
Duk sa'adda sawun giwayen ya
bugi kasa sai kaji dajin gaba daya
ya kama girgiza kamar sama zata
dawo kasa.
Ba wasu bane akan wadanan
giwaye face wadansu zakwakuran
dakarun sarki labarusa mafiya
kwarjini da karfi.
Sai da wannnan zuga ta iso dai-dai
inda su Humairu ke boye sannnan
suka ja tunga suka tsaya suka kama
waige waige da kalle-kalle suna
muruzai kamar zasu ci babu.
Ga fitilun wutar ice nan a hannunsu
suna haska gabas da yamma, kudu
da arewa ko zasu ga wani abu,
kuma sun kasa kunnuwansu ko
zasu ji wani motsi komai
kankatarsa.
Sai da suka shafe dakika dari da
Ashirin a haka sannnan daya daga
cikinsu ya sauka kasa daga kan
giwarsa ya sunkuya ya damki kasar
wajen ya shinshinata.
Kawai sai ya dubi sauran 'yan uwan
nasa yace, tabbas bil'adama yazo
nan bada jimawaba, mu bincika
cikin duhuwoyin can babu mamaki
wadanda muka zo nema sunji
motsin zuwanmu sun ruga sun
buya."
Koda lushairat ta jiyo wannan batu
sai hantar cikinta ta kada, ta kamu
da tsananin tsoro jikinta gaba daya
ya kama tsuma.
A wannan Lokaci suna kwance a
cikin ciyawa sunyi rub-da-ciki ita da
Humairu, kuma suna daf da juna.
Koda Humairu yaga jikin lushairat
ya kama karkarwa har hakoran
bakinta sun fara gugar juna, a
koyaushe za'a iya jiyo motsinsu, sai
yai wuf! Ya janyota Izuwa kan
kirjinsa ya rungumeta kuma ya
toshe bakinta da hannunsa guda.
A hakan suka mike tsaye a hankali
suka kara gaba suna tafiyar sanda,
hannunsa guda na rike da
sharbebiyar wukarsa.
Kafin wadanan dakarun su iso cikin
wannan duhuwar bishiyoyin tuni
sunyi nisa har sun bar cikin
duhuwoyin.
Sai dai suna isa karshen bishiyoyin
suka yi kicibis da wani Ruwa mai
dauke da tabo, kuma babu wata
hanya daza su iya bi su ratse
wannan tabo.
Saura kiris! Ma santsi ya kwashesu
su fada cikin tabon, suka yi tirjiya
suka kurawa tabon idanu cikin
alamun tsananin tsoro, kuma a
Lokacin ne suka jiyo takun sawun
dakarun a can cikin duhuwoyin da
suka baro.
Humairu ya dubi lushairat cikin
karamar murya yace, Ranki ya dade
ba muda wani zabi face mu fada
cikin tabon nan mu nutse a cikinsa
mu buya kafin mutanen nan su iso
nan.
Cikin fishi da tsoro lushairat ta
dubeshi tace, "Baka da hankali ne?
"ai duk abinda ya fado cikin
wannan tabo ba zai yi rai ba.
Ni ban damu da rayuwata
ba,amma na damu da rayuwar
jaririna.... "
Kafin lushairat ta gama rufe bakinta
tuni Humairu ya shammaceta ya
doki wuyanta da hannunsa, kawai
sai ta Sulale zata fadi kasa, yai sauri
ya rukota, kuma ya ciro jaririnta
daga Bayanta ya rungumeshi a
kirjinsa ya daka tsalle suka fada
cikin ruwan tabon suka lume a
cikinsa gaba daya.
Suna lumewa ya zaro wani karan
bishiya mai huda saman tabon don
zukar iskar numfashi.
Faruwar hakan keda wuya sai ga
wadanan dakI'll aru na sarki
labarusa sun rugo da gudu Izuwa
wajen suna haska fitilun itatuwa
dake hannayensu.
Koda suka yi kicibis da wannnan
kogin tabo sai suka yi tirjiya suka
tsaya cak! Suka yi nazarin wajen
gaba daya basu ga alamar sawun
komai ba.
Wani daga cikinsu sai ya dubi
shugabansu yace, "Anya kuwa
wadanan muke nema basa cikin
wannan tabo?"
Koda jin wannnan tambaya sai
shugaban nasu ya daka masa
harara gamida tsawa yace, baka da
hankali ne?"
Ai duk wani abu mai rai idan a cikin
wannan kogi ya mutu kenan, kuzo
mu garzaya Izuwa wancan
bangaren, a can nake zargin sun
buya.
Nan take su duka suka ruga suka
bar wajen.
Sai bayan yan dakiku kadan da
tafiyarsu sannnan Humairu ya dago
Izuwa saman kogin tabon tare da
lushairat wacce har a sannnan bata
farfado ba daga dogon suman da
tayi.
Shi kuwa jaririn nata in ban da tabo
da ya wanke masa fuska da sai
kace dariya ma yake yi saboda
wutsil wutsil kawai yake yi da
hannayensa da kafafunsa yana ta
gyada kai.
Cikin hanzari Humairu ya jinjin a
kirjinsa sannnan ya goya lushairat a
bayansa ya daureta tamau.
Koda ya juya da nufin ya ruga daya
bangaren wanda bashi dakarun
suka bi ba sai yayi arba da daya
daga cikinsu a tsaye rike da
sharbebiyar takobi a hannunsa
yana tsuma.
Ba wani bane face wannan
badakaren wanda yace yana zargin
cewa wadanda suke nema suna
nan a cikin wannan tabon.
Ashe dama shi kadai ne ya jiyo
motsi a cikin duhuwar bishiyoyin,
da yake shine akan gaba.
Koda Humairu yayi arba da
wannnan badakare ya dubi
bayansa da gefensa ya tabbatar da
cewar shi kadai ne ya tsaya, sauran
yan uwan nasa sun yi gaba, sai
kawai ya falfala da gudu Izuwa
kansa.
Ai kuwa shima badakaren sai ya
rugo Izuwa gareshi yana mai daga
takobinsa sama cikin mugun nufi.
Yayin da ya rage baifi saura taku
hudu ba su hadu sai kowannensu
ya daka tsalle sama suka kaiwa
juna mugun hari.
Shi dai badakaren wawan sara ya
kaiwa humairu a wuya da nufin ya
tsinke masa kai, cikin bakin zafin
nama Humairu ya sunkuya, amma
duk da haka sai da kaifin takobin
ya yanke masa wani bangare daga
cikin gashin kansa.
Shi kuwa Humairu tuni ya sokawa
badakaren takobi a kasan wuyansa
gefen kirjinsa.
Takobin ta nutse a cikin kirjin
badakaren ya kwarara uban ihu ya
durkushe kasa.
Ihun nasa ne ya cika dajin gaba
daya da amsa kuwwa, har sauran
yan uwansa dakaru suka jiyo ihun
nasa daga inda suke, suka juyo da
sauri a guje kuma a fusace.
Suna isowa bakin gabar wannan
kogin tabo sai suka iske gawar dan
uwansu durkushe a kasa bisa
guiwoyinsa.
Koda suka ga sawayen Humairu sai
suka sake bin sawunsa a guje har
suka fara hango Humairu daga
nesa goye da lushairat yana ta
falfala masifaffen gudu.
Nan fa suka kasa tsere dashi, duk
da cewar su akan giwaye suke sai
suka kasa cimmasa, domin karfin
gudunsa ya shallake hankalinsu da
tunaninsu.
Kai inda ace mutum na nan a cikin
wannan daji yana ganin irin
azababben gudun da Humairu keyi
zai yi zaton iska ce take kara masa
karfin gudun.
Kafin a jima da fara yin wannnan
tsere tuni na gaba yai gaba, na
baya sai labari, domin tun dakarun
na hango Humairu sai da ya bace
musu bat! Ya kule a cikin dajin.
Amma saboda naci basu daina
binsa ba har tsawon sa'a uku.
A sannnan ne giwayensu suka gaji
likis! Suka zube kasa tare dasu.
******
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment