Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Rayyannu ya ajje wayar talfon din. Ta fada kan
gado ta fara kuka, "Allah ka karbi raina
na huta da wannan kunan rai" Abin da ba ta sani
ba shi ne guntun daddagin begen Haidar shi ne har
yanzu ke addabar zuciyarta.
.
******* ****** ******
.
"Sai na nuna wa wannan yarinyar matsayina." Rayyanu
yace cikin zuciyarsa, a dai-dai lokacin da
ya yi kwafa, sannan ya fara danna lombobin talfon
a hankali, bayan yan dakiku, aka dauka
Bayan yan dakiku, aka dauki wayar acan daya
bangaren "Wa kenan?" Aka tambaya a can daya
bangaren,
"Haji Rayyanu ne"
"Oho daman kai ne, yallabai yaushe ka dawo daga
(Colombia) din ne?" "Saurara da kyau" Rayyanu ya katse
masa tambayoyinsa na kwakwa "Jiya na dawo." Ya ba shi
amsar tambayarsa ta farko, sannan ya ce "Ina son ganin
ka kai da abokin nan naka wanda kuka yi min aiki
kwanakin baya."
"Lafiya Oga ka ke son ganinmu?" Aka tambaya a can daya
bangaran.
"Lafiya kalau." Rayyanu ya ce "Ina son zan nuna
wa wata marar kunya matsayinta ne."
"Wacece wannan yallabai?" aka tambaya,
"yarinyar nan mana dana ke ciyarwa nake
shayarwa, na saiwa gida da motocin hawa, na kuma daga
rayuwarta daga ajin karshe zuwa ajin farko na rayuwa,
amma don rashin godiya, wai ni za ta ci wa mutunci, ka
san daman.."
"Yallabai mu iso yanzu ne?" Aka katse shi cikin
doki. "A'a" Rayyanu ya ce, "Ba na son gaggawa, so nake
na bar ta ta sakankance kamar na manta da ita, sai
kuma mu dirar mata misalin (2:00) na dare."
"An gama" Aka ce cikin ɗoki, daga can daya
bangaren.
Haji Rayyanu na iya jin sowar wanda yake yi wa
talfon din, ya yi sauri ya ajje kan talfon din, don gudun
kar dodon kunnensa ya yi dameji, muryar mai dariya
acan daya bangaren ita ta tuna masa da kukan dodo
.
******* ******* ********
.
Mahaukacin dukan kofar da ake yi shi ya farkar da
Surayya Monika daga cikin nannauyan barcin da take yi.
Da farko ta dauka mai gadinta ne Mu'azu,amma da ta
tuna da cewa ko wani abu muhimmi ne ya faru, mu'azu
ba ya buga mata kofa haka, sai dai ya danna kararrawa,
sanin haka shi ya sa Surayya
ta tashi a firgice. Cikin rudanin rashin sanin abin dake
faruwa. "Monika!" Taji wata kakkausar murya ta yi kiran
sunanta, sunan da aka fi sanin ta da shi a bariki. Ba ta
amsa kiran ba, ko da yake kafin ma ta amsa tuni an yi
mata zagi ya kai cikin kwando.
"Ki bude tun da ba gidan abanki ba ne" Aka ce da ita. "Na
ji Rayyanu ba gidan ubana ba ne. Ga ni nan kuma zan
bude tun da babu gadona a gidan"
Surayya ta amsa, a daidai lokacin ne ta matsa daga
bangaren arewa na falon in da tagar dakin take, sannan a
hankali ta janyo tagar ta leka, abin da ta gani ya sa ta
daukewar numfashi, ya kuma kafar da yawun bakinta. A
tsaye a bakin kofar dakin
Rayyanu ne tare da wasu samari majiya karfi guda
biyu, basu da kyan gani, dayan yana sanye da
doguwar riga fara jallabiya har kasa, kafarsa sanye cikin
takalmin roba, kansa babu hula, sai
nannadadden gashin da a ƙalla ya kai wata biyar bai ga
ruwa ba, hannunsa a cikin aljihun
jallabiyarsa, daya kuma hannun rike da bulalar
kebir. Saurayi na biyun shi ya fi ba ta tsoro,
fuskarsa irin wacce ka saba gani ce a duk lokacin daka
leka zagayen birirrika a gidan ajje naman daji (Zoo)
fuskar mai dauke da sharbeben bulle, da gashin baki irin
na kafiran da can, su suka sa hantar cikin Surayya kadawa
a take a nan taji gumi
ya rufe ta, ta san cewa yau za ta ga rashin mutunci.
.
An ya kuwa Rayyanu ne da kansa zai sa ayi mata Haka ba
taji tsoron bude kofar ba saboda tsabar tsoro da karaya
da ta yi kofar ta bude a hankali da farko, sannan daga
karshe ta taho da karfi ta hadu
da bangon dakin hakan shi ya sa wani bangaren
simunti daga jikin shafen dakin fadowa akan
sawun Surayya.
Surayya ta dubi Rayyanu, sannan shi ma ya dube ta,
tana sanye da duguwar riga ta barci, marar wadataccen
hannu. Kanta babu dankwali.
"marar mutunci nazo na ga iyakar rashin kunyarki"
"Ni ba marar kunya ba ce." Ta ce da shi.
Abin kamar hadin baki shimma Rayyanu yana daga
hannu sai ya talle ta da mari tas!!
"Ni ka mara Rayyanu?" ta ce da shi cikin shesshekar kuka,
"Sai ka gane kuskuren ka."
"Kuskurena?" Rayyanu ya ce yana dariya sannan
ya harari daya saurayin mai jallabiya.
Bai jira komai ba sai ya daga bulalar dake
hannunsa ya fara shararawa Surayya. Ta kwalla
kara mai tsanani a daidai lokacin da ruwan bulalar ya yi
ta zuba a gadon bayanta har sai da ta kasa
kuka abin kawai dake fitowa daga bakinta shi ne "Wayyo
Allah Haidar ka zo ka kwace ni dan kai fa ake yi min
wannan wulakancin! Wayyo Haidar ka
zo ka kwace ni kar ka bari na yi fushi da kai.." Tun tana
fadar haka har ta kasa. Bayan da Haji Rayyanu ya ga ta
kasa kuka sai ya
tsaida saurayin sannan ya kama hannun Surayya da
niyyar ya tashe ta, sai ta fadi kasa.
"Ku dauko min ita" Ya ce da samarin.
Mummunan ya kama kafafunta, shi kuma
mamuguncin ya kama hannunta suka yi mata cali- cali
suka nufi waje da ita. Haji Rayyanu ya bude but
din motarsa ya ce su jefa ta ciki suka jefa ta ciki,
sannan suka rufe. Mintuna biyu da yin haka sai can
mummunan nan ya nisa ya ce da Rayyanu "Ina jin
fa yarinyar nan ta mutu"
"Ni ma abin da na ke zato ke nan" Rayyanu ya ce. "Amma
abin da za mu yi shi ne mu kai ta can cikin
ciyayin nan na bakin kogi mu yarda ita da safe a tsince ta,
ni kuma daga nan zan sallame ku zan koma kwalambiya a
yau din nan. Daman babu wanda ya san na dawo, ko da
yansanda ko wasu
sun tsince ta babu wanda zai dora alhakin kisan kanta a
kaina tunda bana nan, kuma ku ma ku yi shiru da
bakinku."
.
"An gama Oga." Suka amsa baki daya. Bayan yan mintuna
suka isa bakin kogi karfe daya da rabi na dare babu kowa
a bakin kogin, suna zuwa suka bude bayan mota suka
sake yi mata cali-cali sannan suka zabi inda ya fi ko'ina
surkukiyar ciyayi suka jefa ta, ta faɗa amma ba ta motsa
ba, Rayyanu ya dube ta, sannan ya taka idon sawunta da
kafa
bata motsaba. Sannan suka shiga mota suka ware. Ba su
fi mintuna biyar da barin wajen ba aka tsinke da ruwan
sama kamar da bakin kwarya.
.
******* ****** ********
.
Sautin kukan da Surayya ta kwalla ya daki dodon kunnen
mu'azu maigadi, wanda ke kwance akan
dogon bencin dake kofar gidan. Jikinsa na ta
makyarkyatar zazzabi, tun safe yake fama da
zazzabin, tuni jikinsa ya dauki zafi kamar kwanon tuya.
Kukan da ya ji Surayya ta kwalla shi ya sa shi ya manta da
zazzabin dake addabarsa, a lokaci guda kuma ya tashi
zaune zumbur, jikinsa na rawa kamar mazari, sannan ne
kuma ya sake jin Karar mari, Surayya ta yi wani irin kuka
mai ban tausayi, kukan kamar sukar kibiya ce a kunnen
Mu'azu,
"Yarinyar da ta dade tana yi min mutunci, yarinyar arziki
wadda ta tsamo ni daga cikin matsananciyar
wahalar rashin aiki, ta kuma ke ninka min abinda ya
kamata ta biya ni da shi, dole ne na ceci rayuwarta daga
hannun marar mutuncin nan."
Mu'azu maigadi ya sake cewa cikin zuciyarsa,
sannan ya ciji yatsa cikin takaici da ya san cewa Rayyanu
dukan ta zai yi to da bai bar shi ya shiga
gidan ba duk da cewa kuwa yana fama da zazzabi, domin
yaji lokacin da su Rayyanu suka zo amma ya
kasa tashi ya bude musu kofa saboda juwa da
ciwon kai dake daukarsa, ya ji kuma irin cin
mutuncin da zagin da Rayyanu ya yi masa, duk da haka
bai tashi ba, amma kukan Surayya ya isa ya tashe shi ko
da kuwa a kabari ne. Ya ce cikin zuciyarsa duk da yake
kuwa bai yarda da hakan ba.
Mu'azu mai gadi ya zare takobinsa tsirara sannan
ya nufi kofar dakin da sanda, ta hanyar boye jikinsa a
cikin duhuwar fulawowin dake farfajiyar gidan, tun kafin
yayi rabin kofar dakin sai ya ji kamar an dabaibaye masa
kafa, ya tsaya cak kirjinsa na dukan uku-uku, tsoro ya
kama shi hakika ba wani abu ne ya hana shi tafiya ba, sai
mummunan
tunanin daya fado zuciyarsa kamar daga sama "Rayyanu
na iya halaka ka fa!" Zuciyarsa ta ce dashi. Zuciyarsa na da
hujjar fadin hakan, domin kuwa a watan da ya wuce ne
Mu'azu maigadi ya ga wani abu da ya ba shi tsoro da
mamaki, duk da
yake kuwa bai fadawa kowa ba, har ita kanta uwar
dakinsa Surayya bai bar ta ta sani ba.
.
Ranar Asabar da safe ne abin ya faru, ba zai manta da
ranar ba, kamar kullum, sai ga Rayyanu cikin mota, yana
zuwa sai Mu'azu ya bude masa kofa, bayan ya
wuce ciki ya yi fakin da motar a kusa da inda
rumfar Mu'azu take, sai ya bude kofar kujerar baya ta
motar ya dauko wata bakar jaka daga ciki, ya nufi but din
motar, abin tsautsayi sai jakar ta kwace
daga hannun Rayyanu, ta fado kasa, kallon farko da
Mu'azu ya yi wa kayan da suke zube a kar bai shaida
komai ba sai wata yar karamar bindiga mai barazana ga
wanda ke kallon ta, kallo na biyu kuma da Mu'azu ya yi
sai idonsa ya hango masa wasu yan kananan ledodi
kunshe da wani gari-gari fari tas a ciki, ya yi kokarin ya
fahimci ko mene
a cikin ledodin amma bai ci nasara ba, sai dai kuma a can
cikin zuciyarsa ya fara tunanin anya kuwa wannan ba ita
ce abin da ya sha jin labari a bakin mutane ba, "HODAR
IBLIS!" Rayyanu ya tsince kayan ya maida su cikin akwati
sannan ya jefa ta a bayan motar ya kulle, ya juya suka yi
ido hudu da mu'azu maigadi, A kullum Mu'azu ya tuna da
irin kallon da Rayyanu ya yi masa, sai ya ji hantar cikinsa
ta kada, kallo ne mai dauke da tsabagen gargadi da
barazana. Mu'azu ya yi ajiyar zuciya saboda mummunan
tunanin da zuciyarsa ta tuno masa, jikinsa ya yi matukar
mutuwa, tuni har ya fara tunanin da wahala kuma ya
sake gaba da gaba da Rayyanu, bai karasa tunanin ba
saiya ji tim! Kamar an daki buhu, sannan ya ji sharaf,
alamar faduwa, gumi ya keto masa, kamar ana zuba
masa ruwa, a daidai lokacin ne ya ji su Rayyanu sun nufo
wajen da yake
boye, nan da nan ya tashi a guje ya koma kan
bancin da yake ya sake kwantawa, idonsa rabi a rufe rabi
a bude, "Wasu masu kama da birirrika sunyi wa uwar
gidansa Surayya cali-cali, suna zuwa suka jefa ta a bayan
mota, sannan suka shife cikin motar suka tashe ta.
Rayyanu ya fito daga cikin
filawoyin shi ma ya shiga motar, suka yi ribas suka fice
daga gidan da gudu. Mu'azu mai gadi ya tashi aguje ya
nufi kofar gidan a daidai lokacin ne ya hangi danjar
motar su Rayyanu, ta nufi bakin kogi, mintuna biyu da
faruwar hakan sai ga Mu'azu akan
kekensa takobinsa a kafadarsa ya nufi bakin kogin
kekensa na waka kurki-kurki.
.
******* ***** ******
.
Sai an yi kamar za a dauke ruwan, sai a sake
kecewa kamar da bakin kwarya, hatta kifayen dake cikin
kogin kwara a wannan lokacin sunsan ana tafka ruwan
sama duk da yake kuwa su daman a cikin ruwan suke, to
ballantana kuma Surayya wacce ke kwance a tsakiyar
sarkakiyar
ciyayin bakin kogin.
Samarin da ke tuka motar suka kalli junansu
sannan suka yi dariya. A daidai lokacin ne babban ladanin
masallacin Banasariyya ya kwalla kiran sallar farko.
.
********** ********* *********
.
Rugugin jirgin saman shi ya dawo da masu tarar yan uwa
da abokan arziki hankalinsu, sai bayan da rugugin jirgin
saman ya lafa ne, sannan suka fahimci cewa ashe jirgin
sama ya sauka. Zungureran jirgi ne fari, mai dauke da
zanen shudi-shudi a jikinsa, a jelarsa an rubuta "KLM"
jirgin Turai ne daya kuma daga cikin fasinjojin da jirgin
ya kawo Rayyanu ne, sanye da riga da wando, kwat
bakake idonsa a boye a cikin bakin tabarau, a saman
tabaran daga sama an rubuta kamar haka (Colombo)
hannunsa na hagun sanye cikin aljihun
kwat dinsa, hannunsa na dama kuma rike da
hannun jakar da ya ratayo a bayansa baka, mai dishi-
dishin fari, babu alamar farin ciki ko bakin ciki a fuskarsa,
abin kawai da za a iya kwatanta
fuskarsa da shi a wannan lokaci shi ne bangon
siniman.
Ya biyo jerin gwanon mutanen suka nufi kasa ta
hanyar matattakar jirgin saman. Bayan sun karaso kasa
sai ya wuce kai tsaye ya nufi inda ake tarar baki, yana
fitowa farfajiyar filin jigin saman sai ya fara waige-waige,
lokaci guda kuma ya duba agogonsa, karfe uku da rabi na
rana ya iso gida Najeriya, rabonsa da Najeriya yau wata
guda kenan da kwana uku. Wata zungureriyar mota ta ja
ta tsaya a gabansa,
Rolloyis dinsa ce. Samarin biyu masu kama da
birirrika suka fito kowannensu sanye da doguwar
jallabiya, kamar da gaske idan ka kalle su daga kafarsu
zuwa kirjinsu sai ka dauka mutanen kirki ne, amma
lokacin da ku ka yi ido hudu sai ka tabbatar da
kuskurenka ka kuma gwammace yin ido hudu da damisa
akansu.
Suka bude masa kofa, shi kuma Rayyanu ya shiga bayan
motar ya kame, sannan su ma suka shiga "Ina muka nufa
yallabai?" Dayan ya tambaya.
"SARIYANA OTAL" ya ce dasu "An gama kuma za'ayi."
Suka amsa gaba daya.
.
******* ******* *******
.
"Ah!! Lallai Surayya kafa ta yi sauki, har da sauri
haka." Surayya ta yi murmushi sannan ta kalli
GRACE, doguwar mata ce siririya hancinta kamar biro
saboda tsawo, tana da idanu dara-dara launin sararin
samaniya, baturiya ce yar kasar Ingila, yawon bude ido
ne ya kawo ta Najeriya ita da mijinta JACKSON.
"Sannu Surayya" Jackson ya ce da ita daga baya. Ta juya
ta kalle shi sannan ta yi murmushi, "Nagode Jackson" Ta
ce da shi, sannan ta sake kura masa ido, tana al'ajabin
irin taimakon da ya yi mata, yau kimanin watanta daya
kenan da kwana uku a gidan lambun Jackson, katon gida
ne, wanda ke
dauke da tafka-tafkan kyawawan dakunan kwana guda
uku, gidan an gina shi ne acan tsallaken gaɓar kogin
kwara, misalin kilomita ashirin da uku kenan daga
unguwar Banasariyya. Babu ko gida daya a gurin in ka
dauke gidan Jackson, wanda shima ya gina shi ne a nan
domin ya kadaice kansa
daga hayaniyar jama'a. Jackson ya gina wannan gida ne
tun kusan shekaru shida kenan da suka shude, ba don
komai ba kuwa sai don ya sami damar nazarinsa cikin
nutsuwa, ba tare da hayaniyar jama'a ta dame shi ba
Malam Jackson, Edita ne na wata mujallar ingila, duk
kuma wata
uku sai ya zo Najeriya, domin yin nazarce-nazarcensa, a
ka'ida kuma baya wuce sati daya a duk zuwan da zai yi,
Malam Jackson dogo ne shi ma kamar matarsa, sai dai
kuma ya fi matarsa tsawo da kadan, yana da tarin suma,
wacce ta zubo masa har kafada, hancinsa ya lankwaso
kamar kugiya, yana
da siraran lebban baki, jajaye kamar yankan reza.
Awannan safiyar malam Jackson yana sanye ne da bakar
riga mai gajeren hannu, a kirjinta an rubuta "Sun
Flowers." Yana sanye da farin wando da hula hana Sallah
fara, agogo "Sorinta" a hannunsa. A irin
wannan shigar ne kuma Jackson ya tsinci Surayya kwance
male-male a kan gadonsa a kuma cikin dakinsa, wanda
idan ya je kamun kifi yake hutawa aciki. Koda Surayya ta
kalle shi sai hoton ranar da suka hadu da Malam Jackson
da kuma irin taimakon da
ya yi mata suka fara bayyana garai-garai a
zuciyarta, har yanzu kuma hankalinta a tashe yake
saboda rashin sanin halin da Mu'azu mai gadi ke ciki, ta yi
mamakin rashin ganin dawowarsa. "Lallai wani abu ya
faru" ta ce cikin zuciyarta, hakika lokaci ya yi da ya
kamata ta fara ramuwar gayya kwanaki talatin da ukun
da suka shude ta yi su ne cikin tunanin yadda za ta rama
abin da su Haidar da Rayyanu suka yi mata, amma da
farko dai shi ne ta
bar wannan gidan lambun, tun da ta sami sauki, wani abu
kuma da ta fahimta shi ne Rayyanu ya
dauka ta mutu, idan kuwa haka ne to ba zata taba bari ya
gan ta ba, har sai lokacin da ta samu cikar burinta
"Sai na rama wulakancin da Haidar ya yi
min" ta ce cikin zuciyarta. "Rayyanu kuma ya shiga
masifa tunda ya yi kokarin kashe ni. Zan kuma nuna
musu ni yar halak ce."
Kiran sunanta da Jackson ya yi shi ya dawo da
Surayya hankalinta, sannan ta fahimci ashe tunani ta ke.
"Tunanin me ki ke yi Surayya?" Jackson ya
tambaye ta. "Ba komai" ta ce, tana murmushin yake
amma zuciyarta a cike take da tsanar
HAIDAR DA RAYYANU
.
"Surayya" Jackson ya ci gaba da cewa cikin
harshen turanci "Ki yi hakuri, ki rabu da su, kin ga yanzu
ke kadai babu yadda za ki yi da su,
musamman shi Rayyanu din. Abin da nake ganin ya fi shi
ne, idan kin tashi tafiya sai ki koma gida kai tsaye, ki je ku
shirya da iyayenki.
.
****** ******* ********
.
Misalin karfe tara na safe ne Surayya ta fito dauke da
bakar jaka rataye a kafadarta, tufafin sawa ne irin na
turawa Grace ta ba ta, da kuma yan kunne da abin hannu
na mata masu tsada, tana tafe Jackson a gefenta na hagu,
Grace kuma a gefenta na dama, rike da hannunta, tana ta
faman kuka hakika ta shaku da Surayya, matukar
shakuwa, bakin kogin suka nufa, suna zuwa sai Surayya ta
yi
ido hudu da wani dan karamin jirgin ruwa irin na
turawa. "Sai ki tafi a cikinsa." Jackson ya ce da ita,
"Idan kin je tashar jiragen ruwa na Banasariyya, sai ki
tambayi Ahmad, idan an nuna miki shi sai ki bashi
mukullin jirgin ki ce masa ni na turo ki da shi kice masa
sai bayan wata uku zan dawo." Bai jira tace komai ba, sai
ya zaro damin kudin ingila daga aljihunsa ya mika mata
"Ki canza wannan zuwa
kudin nan Najeriya za su ba ki a kalla naira dubu dari
shida da hamsin. Allah ya taimake ki ya ce da ita." Sannan
ya ja da ba ya domin ya basu damar ganawar karshe ita
da matarsa Grace.
.
"To Surayya." Grace ta ce cikin harshen turanci "Sai wata
rana." Sannan ita ma ta buda jakarta ta zaro wani abu, ga
mamakin Surayya sai taga wata yar karamar bindiga ce
irin wacce matan turawa ke rikewa, "Za ta yi miki amfani"
Grace ta ce da ita duk da yake Surayya ba ta ko taba rike
bindiga ba balle tayi amfani da ita hakan bai hana ta
karba ba,
Jackson ya buda baki zai yi magana sai ya yi shiru bai ce
komai ba Sannan ita ma Grace sai ta ja da baya ta koma
kusa da mijinta ta tsaya tana kallon Surayya idonta cike
da kwalla.
Surayya ta shiga jirgin sannan ta danna gurin da ake
tashin jirgin kamar yadda Jackson ya koya mata, sannan
ta juyo ta miko hannayenta a lokaci guda, "Na gode
muku" ta ce da su, "Ba zan taba mantawa da ku ba."
Sannan ta harba cikin ruwan da gudu, ba ta ko kara
waigowa ba, har sai da ta ƙule. Grace na tsaye a bakin
kogin tana kuka
Jackson ya dafa kafadarta sannan suka juya suka nufi
gida, da niyyar su ma su bar Kasar.
Misalin karfe goma da rabi su ma jirginsu ya daga sai
Ingila, Grace ta leko ta tagar jirgin sannan ta ce "Surayya
sai wata rana."
Kamar tana gurin.
.
*********** ********** *********
.
In ka dauke bambacin sa'o'i da ake samu duk abin da ya
faru ne kusan lokaci guda, sa'o'i biyar da wani abu, bayan
tashin su Grace zuwa Ingila Rayyanu ya sauka a gida
Najeriya. Sannan sa'o'in
Surayya hudu da yan mintuna da zuwa SARIYANA OTAL
sai ga zungureriyar motar su Rayyanu shi da yan
ta'addansa sun isa. Suna zuwa suka yi fakin da motar
sannan suka nufi wajen saukar baki, ba'a dade ba, aka ba
su daki mai lamba (10) hawa na biyu. Surayya na zaune
akan kujera tana leken
tagar dakinta, mai lamba (7) hawa na goma, sai
taga zungureriyar motar ta malalo cikin harabar
otal din kamar ba za ta kare ba saboda tsayi. Abin ya yi
matukar ba ta mamaki, ya kuma kada hantar cikinta,
"Rayyanu!!!" ta ce cikin ajiyar zuciya. Sannan ta yi shiru
tana tunani "Ya kamata na fara wani abu..." ta ce,
"...tunda ga Allah ya kawo min shi har nan." Lokaci guda
kuma sai dabara ta Faɗo mata. Ta tashi daga kujerar,
sannan ta matsa kusa da ɗan karamin teburin dake tsakar
dakin, mai shan kuri, tana zuwa ta ɗau kan talfon din
sannan ta buga lambobin da take so.
"Sariyana otel." Akace da ita a can daya bangaren
"Ina son ganin ka da gaggawa don Allah." ta ce da shi,
...ni ce bakuwar da ta zo sa'o'i hudu da suka wuce, daki
mai lamba (7) hawa na goma." "Ga ni nan zuwa ranki ya
dade."
Tuni Surayya daman ta san zai zo, musamman ma da ta
tuna da irin kallon nuna sha'awar da ya yi mata lokacin
da ta zo otel din,
daɗin daɗawar kuma daga zuwanta har ta fara yi wa
masu hidimar otel din watsi da kudi, shi kansa naira dari
uku ta bashi.
.
Aka kwankwasa kofar, "Shigo" Surayya ta ce a
sanyaye, kofar ta bude sannan ya shigo, shi ne mai karbar
baki, kuma shi ne mai baiwa duk wanda yazo otel din dan
mukullin ɗaki, dogo ne fari kakkaura, yana da cin zanzana
a fuska, yana da kananan idanu kamar na maciji, fatar
bakinsa ta dafe ta yi baki, hakan shi ya sa Surayya ta tuna
da tarihin ƘABUSU.
A wannan ranar yana sanye da
shudayen kaya riga da wando, kafafunsa kuma
sanye cikin tsohon takalminsa wanda ke kokarin yin
dariya kowane lokaci daga yanzu. "Gani na zo ranki ya
dade." Ba ta bar damar ta wuce ba sai ta ce cikin iko "Don
Allah wani aiki za ka yi min, dan karamin aiki ne, sai
dai kuma ladansa na da yawa."
"Wanne irin aiki ne Hajiya?" Ya tambaya cikin
mamaki. Ba ta bashi amsar ba sai ta ci gaba da cewa
"Aikin zai iya kawo maka ladan Naira dubu biyar."
Mutumin ya yi ajiyar zuciya hade da hucin da ke
barazanar yage labulan dakin, idonsa ya zazzaro sannan
ya hadiyi yawu kut! Kamar ansa giyar mota
"Fada min na ji Hajiya zan yi miki ko wanne iri ne."
Tuni ya fara tunanin abin da zai yi da kudin.
"Za ka iya tunawa da bakin da suka zo yanzu
yanzun nan?" "Na tuna su Hajiya."
"Nawa ne lambar dakin da ka ba su?"
"Lamba (10) hawa na biyu." "Kana da wani dan mukullin
ne bayan wanda ka ba su?"
Ta tambaye shi.
"Eh ina da shi, daman kowane daki makuli biyu ne da shi
saboda ɓata, daya muna bada shi ga mai dakin daya
kuma mu rike." Ya yi shiru lokacin da ya ga Surayya ta
mike ta dauko wata jaka dake kan gadon, sannan ta bude
ta, a cike take da masu launin siminti, wazobiya, jikinsa ya
fara rawa, "Ina son ka ba ni daya dan makullin na
dakinsu, gobe zan dawo maka da su, ina son kuma idan
bakin
sun fita, ka yi min waya domin na sani." Sannan ta yi
masa murmushi. "Idan har ka yi abin da na saka ka ci
Naira dubu biyar, yanzun nan kuma zan baka."
"Ina zuwa." ya ce da ita, ya fice daga dakin da sauri ba a
jima ba ya dawo yana zuwa ya mika mata dan makullin
har da durkusawa." Ta karbi dan mukullin, sannan ta jefa
masa, damin
wazobiya "Naira dubu biyar ne, ina kuma jiran
sako da zarar sun fita."
"An gama Hajiya." har ya juya zai fita sai ya juyo yace da
ita "Sai dai kuma Hajiya ya kamata na san dalilin ki na son
shiga dakin."
"Rakumi na ne ya bata shi ne nake son na duba shi, ko ya
shiga ɗakin." Ba ta kara kallon sa ba sai ta nufi tagar dakin
wajen kujerarta ta zauna.
Maganar da ta yi ita ta gargade shi, kada ya sake wata
tambayar.
Mintuna uku da yin haka sai Surayya ta ji talfon din ta ya
dau kara, ta dauka ta kai hannunta.
"Sun fice" Aka ce da ita.
Ta yi sauri ta aje kan talfon din, ta nufi kofar ɗakin da
sauri, dan mukullin da ya ba ta a hannunta, tana zuwa sai
ta hau abin rage hanya, ya yi kasan benen
da ita, zuwa hawa na biyu, mintuna uku sai ga ta a kofar
dakin. Ta zura dan mukullin ta bude dakin, tana shiga ta ji
kamshin turare ya bugi hancinta. Tangamemen daki ne
mai dauke da wangamemen gado mai kama da filin
wasan kwallo, dakin ya yi mutukar tsaruwa, ta yi
mamakin ganin cewa daga
zuwan Rayyanu har ya barbaza kayansa ko'ina cikin
dakin, ta fara dube-dube, ita kanta ba ta san abin da take
dubawa ba, ta birkita nan ta duba can, ba ta ga komai ba,
sai bayan da ta gama ne sannan ta yi ido hudu da wata
jakar wasika wacce ke aje akan teburin da ke can bangon
dakin. A gefen jakar wasikar kuwa wata wasika ce ajje ko
linke ta ba a yi ba. A kan farar takarda aka rubuta ta, ga
dukkan alamu ba a dade da gama rubuta ta ba,
domin har da biro a kan ta, tana zuwa sai ta fara daukar
wasikar da nufin karantawa, a sannan ne to sai ta ga
adireshin dake bayan wasikar na wata unguwa ce a can
cikin kasar kwalambiya, ta zaro wasikar ta fara
karantawa, duka wasikar layi takwas ce an kuma rubuta
ta da koren biro.
"Rayyyanu ina son ka dawo da gaggawa domin
abin nan ya samu, zata kai ta Naira miliyan arba'in, mai
kyau ce don haka sai ka sami yarinyar da za ta fitar mana
da ita, ka san yanzu yadda abin yake idan ba mace ba
babu wanda ya isa ya fita da abin daga Najeriya. Sai ka
zo."
A.D banasare Gumi ya lullube Surayya lokaci guda,
kirjinta ya fara bugawa, damar da take jira ta samu
domin ta tabbata abin da ake magana ba wani abu ba ne
face... Ta yi tsaye tana tunani, idan banda maigadi Mu'azu
ya dan sanar da ita labarin Rayyanu ba to
da ba za ta taba gane me ake magana

Please Login or Register in order to submit comment