Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

min haka ba, Aganani ka tuna fa da irin abubuwan da na yi maka a baya." "Ai abin da ya wuce ya wuce, kuma idan ka lura a
wancan zamanin kaine rike da igiya ni kuma amatsayin bawanka sai abinda kake so zan yi, ka tuna fa da irin hadarin dana tsunduma kaina a ciki, sanin kanka ne daidai da rana daya idan sirrina ya tonu cewa ina taimaka maka to ni kuma sai addu'a domin kuwa nagama yawo, ko dai ban rasa rayuwata ba, to ya zama dole na karashe sauran shekaruna a gidan maza."
Aganani yayi shiru yana duban Alhaji Banasare.
"Ina fatan yanzu dai ka gane abin da nake nufi, yau da ace mutum abin yarda ne to da bazan kama ka ba, nasan cewa hodar iblis din da kake tsammanin tana gurin Rayyanu idan na rike ta na ce na kwace
ba bu yarda za ka yi, tunda dai ba za ka kai karata ba gurin hukuma."
Aganani yayi murmushi sannan yace "Mun dade da kai na kuma san halinka da kuma wasu daga sharrikanka, sanin haka ne yasa zuciyata take gargadina akan cewa zaka iya neman fansa akaina."
Aganani ya yi shiru na dan lokaci yana duban Banasare, in ka dauke sauti hucin Aganani duk
fadin gidan shiru yake kamar makabarta. "Zaka fuskanci shari'a nan da yan kwanaki."
Aganani ya ci gaba da cewa.
"Sai dai kuma ba dole ne ka kai lokacin a raye ba..."
Bai sake cewa da shi komai ba daga wannan kalami na karshe da yayi sai kawai ya dubi yansandan uku dake tsaye suna gumi kamar masu hadiyar kunama sannan yace da su.
"Ku ba shi abinci, kun san an ce bakonka Annabinka."
Sannan ya kyalkyale da dariya. Amsa kuwwar dariyarsa ta ratsa ko'ina cikin gidan. Sannan ya juya
ya fice daga dakin bai ko sake juyawa ya kalli Banasare ba.
.
Yansandan uku suka yi shiru na dan lokaci suna duban Alhaji Banasare, sannan dan gajeren cikinsu
ya fita waje. Ba a dade ba sai gashi dauke da kwanon abinci, ko da yake idan aka yi la'akari da girman kwanon bai kamata a kira shi da kwano ba sai dai ko gwangwanin madara. Dan mitsitsin
kwano ne abincin dake ciki bai fi cokali biyar ba.
Suka ajje kwanon a gaban Alhaji Banasare, sa'annan suka ja da baya suna kallonsa zuru-zuru kamar kurame.
Zuciyarsa na tafarfasa kamar za ta fashe don bacin rai, yanzu kam ya tabbata Aganani niyyar kashe shi
yake. "Mene ne to abin yi?" Ya tambayi kansa.
"Gudu shi ne abin yi yanzu" ya ce cikin zuciyarsa.
Wannan ita ce damarsa ta karshe, idan kuwa har ya
sake ya gama cin abincin bai gudu ba, to daure shi za su sake yi, shi da gudu kuma sai ko a kiyama idan ana yi. Ya dubi kwanon abincin da ke gabansa, sannan ya
janyo shi kusa da shi ya bude, wani abu ne ciki, taliya-taliya, shinkafa-shinkafa. Shi kansa bai san ko mene ne ba. Ya dauki abincin ya kai bakin sa, zuciyarsa cike da tunanin hanyar da zai bi ya kubutar da kansa. Abincin ya yi tauri da yawa in ya
tauna sai ya ji kamar danko, sannan kamshin abincin ya fi kama da warin man gelo fiye da abincin.
Abincin kawai dai yake ci ba don yana so ba, sai don yana son yansandan su sakankance da cewa abincin yake ci. Mintina biyu suka shude, sannan ne ga farin cikinsa sai yan sandan suka fice daga
dakin. Daya daga cikinsu ya jingina da kofar dakin,
bayansa na fuskantar cikin dakin yayin da biyun suka janyo kujeru suka zauna suna fuskantar juna.
Ba a dade ba da afkuwar hakan sai kowannensu ya kunna sigarinsa, sannan suka cigabada hirar
wasan kwallon kafar da za a yi tsakanin kungiyar yansanda da kuma ta gandirebobi.
.
Dogon ya dubi gajeren dake saye a bakin kofar sannan ya ce da shi yana murmushi.
"Malam dogo lamba nawa za ka buga." Dan gajeren ya busa hayakin sigarinsa sama sannan ya ce,
"Rabon da na yi kwallon kafa tun ina firamare a da dai lokacin ina yaro lamba tara nake dokawa, ban sani ba yanzu babu mamaki tun da na kara girma ko ina iya doka casa'in."
Yansandan suka fashe da dariya, har da sowa, sun shagala da dariyar da suke. Babu wanda ya lura da
lokacin da kwanon ya yi sama yaketa iska sannan ya daki keyar dangajeren dansandan dake jingine
a jikin kofar. Ba su gane hakan ba sai bayan da suka gama dariya sai suka lura ashe shi wanda ya
bada dariyar ba dariya yake ba. Maimakon hakan ma sai ya kwalla ihu mai tsanani yansandan biyu
sun gama rudewa babu wanda ya yi tunanin cewa Alhaji Banasare ne ya yi jifan ba Banasare ya harbo daga cikin daki da gudu kamar kibiya, taiɓarsa ba ta hana shi gudu ba, saboda gudun da yake gudun tsira yake.
.
A daidai lokacin da yansandan suka mike tsaye domin shigowa dakin, shi kuma Banasare ya kawo kofa, abinka da kato, ya banke yansandan biyu, kan dogon dansandan ya daki karfen kofar dakin dake fuskantar wanda yake ciki. Dansandan ya
saki bindigarsa ta yi gefe guda kafarsa ta shura sau daya sannan shi ma ya sume.
Dansandan na uku ya fi kowa rashin sa'a, domin bangazar da Banasare ya yi masa bai same shi a daidai ba, sai ya same shi a wuya, tun kafin ya taba
kasa ya sume.
Banasare bai jira komai ba, sai kawai ya nufi babbar kofar fita daga cikin gidan tuhumar, tun
kafin ya karasa ya jiyo hayaniyar yansandan abakin kofar, hakan shi ya sa shi tsayawa cak kamar an soke shi da kibiya.
Daga bangaren hannunsa na hagun wata doguwar bishiya ce ta turare. Lokaci guda dabarar tsira ta zo
masa, abin kawai da yake tsoro shi ne, Yan sandan na iya hango shi yayin da ya kai iya tsayin
katangar. Alh. Banasare ya dubi zungureriyar katangar mai
dauke da tsago-tsagon din kibiyoyi masu tsinin gaske a kanta, sannan gabansa ya fadi da ya tuna
da cewa ko ya hau bishiyar ba zai iya dirge kan
katangar ba. Ya sake duban bishiyar a karo na biyu nisan dake tsakanin katangar da bishiya bai wuce taku daya ba.
"Da dai su kashe ni a banza gara duk abin da zai faru ya faru, koda kuwa zan karye ne idan na dire a bayan katangar."
Wannan tunanin dake cikin zuciyarsa shi ya kara karfafa masa gwiwar hawa bishiyar, domin samun dammar tsallaka zungureriyar katangar. Lokacin da ya hau bishiyar, numfashinsa sama-sama ne, saboda haki da kuma gajiya. Taibarsa ta yi yawa, rabonsa da shiga halin wahala irin wannan
ya fi shekara ashirin. Bugu da kari kuma, ga girma ya fara kama shi, ya dai daure ya cigaba da hawa bishiyar kirjinsa na bugawa, wani lokaci yakan zame ya dawo baya saboda nauyinsa da kuma
santsin bishiyar turaren wacce jikinta babu kaushi sosai.
Abin da ya hango a bayan katangar shi ya kara bugun zuciyarsa sannan farin ciki ya lullube shi. Ya dubi bayan katangar, iya ganinsa ga mamakinsa sai ya ga babu komai sai ruwan kogin kwara Fetal kamar madubi yana sheki. Cikin rawar jiki sai ya yunkura yakara sama har dai ya kai ga wani dan siririn reshe na bishiyar sannan ya taka shi jikinsa
na rawa. Reshen ya bada wani sauti kuk! Kuku!! Saboda nauyinsa.
Banasare ya takarkare sannan ya tsunduma cikin ruwan kundum!!!
.
Karar sautin fadawa ruwan, shi ya janyo hankalin yansandan da ke waje, suka rugo cikin gidan da
gudu sannan ne fa suka sami yansandan nan uku summamu.
A daidai lokacin da yansandan nan suke kokarin farfado da yan uwansu dake sume, shi kuma
Banasare ya je gida.
Mutane da dama sun yi mamakin ganinsa sannan lokaci guda suka tabbatar da cewa guduwa ya yi. Wurjan-wujan ya shigo unguwar, rigarsa a feffece,
bakinkirin, ko takalmi babu a haka ya shigo unguwar, mutane suka yi ta darewa suna bashi hanya.
A can cikin dakin Banasare tuni ya sauya kayan da
suke jikinsa bai ko damu da ya sake wanka ba. Sannan ya bude wata boyayyiyar loka da ke
karkashin gadonsa, ya yi ajiyar zuciya lokacin da ya
ga abin da yake fatan samu, har yanzu tana nan kwance inda ya ajjeta rabon da ya yi harbi da ita
yau shekara goma sha takwas kenan. Mintina biyu da yin hakan sai gashi cikin marsandi ya fice da gudu daga cikin gidansa, masu gadin gidan suka yi cirko-cirko cikin mamaki suna kallonsa kamar zakarun da ruwa ya doka.
Aganani mu-sha-gara ya goge gumin dake tsatstsafowa daga goshinsa. Dole ne ya isa gidan azabtarwar cikin kankanin lokaci, domin tabbatar da cewa an kame Banasare, hakika indai Har Banasare ya gu...
Tunaninsa ya katse a daidai lokacin da ya bude kofar babbar dakin shakatawarsa, a zaue a kan daya daga cikin manyan kujerun da suka saba zama don tattaunawa, Alhaji Banasare ne zaune kafarsa daya a kan daya sannan bindigarsa na
hararar kirjin Aganani mu-sha-gara, "Barka da zuwa" Banasare ya ce da shi.
Jikin Aganani ya dauki rawa, lokacin da ya dubi bindigar, sautin muryar Banasaren da ya doki
dodon kunnensa kamar sautin muryar fatalwa ne a cikin dokar daji.
.
************ ********** **********
.
Surayya ta yi ajiyar zuciya lokacin da ta bude kofar dakin falon sannan ta shiga. Sai bayan da ta rufe kofar dakin bayanta ne sannan
hankalinta ya kwanta. Abin da ya faru a ranar ya yi matukar sa ta kaduwa, yanzu kam ta san tana cikin
hadari, hadarin ma kuma bakarami ba.
"Mene ne dalilin da ya sa dansandan yake son kaita ofishin yansada?" Ta tambayi kanta.
Ta sake ajiyar zuciya a karo na biyu a daidai lokacin
da ta zauna a kan daya daga cikin kujerun dake falon, karfe biyar da rabi agogon dake dakin yabuga.
Gidan shiru kamar makabarta, ba ka jin komai sai
sautin ganyayyaki shuke-shuken da iska ke bugawa abayan gidan, sai kuma sautin tafiyar
ruwan kogin kwara. Surayya ta muskuta a kan kujerar sannan tasake dulmiya cikin kogin tunani. "In har tana son ta cimma burinta to dole ne ta boye kanta a wannan sihirtaccen gidan, domin kuwa fitarta da rana na iya kawo barazana ga rayuwarta.
.
"Malama muna son yi miki wasu yan tambayoyi" Maganar dansandan ce ta sake dawowa garai- garai a cikin zuciyarta. Har yanzu ba ta samu amsar tambayar dake
zuciyarta ba. A yan kwanakin da suka wuce ta tabbata yansanda basa zargin ta da komai, saboda
hoton ma da ta dauka a tsorace ta dauka ta gudu,
kuma a lokacin da ta dau hoton babu ko maigadi daya a duk fadin farfajiayar gidan a lokacin gaba
dayansu suna tare da Aganani Musha-gara. To idan haka ne kuwa menene dalilin neman da
yansandan suke mata? Ta sake tambayar kanta.
"Ina cikin hadari" Ta ce da kanta. Sannan gabanta ya fadi, jikinta ya dauki bari, lokacin da ta tuna da irin rashin imanin da Aganani ya nunawa Rayyanu, ba zata taba mantawa da rashin imanin da kuma azabar
da ya gana masa ba kafin ya kashe shi.
Ta yi zumbur!! Ta tashi daga kan kujerar da take zaune sannan ta fara safa da marwa cikin tsakar
dakin, kanta a sunkuye tana kallon dardumar tsakar dakin, amma a zahiri ba dardumar tsakar dakin take kallo ba, hoton abin da ya faru da Rayyanu take gani garai-garai kamar a lokacin abin yake faruwa.
Ta tuna inda kartin nan suke tumurmusa Rayyanu,
"Ina hodar iblis din!!" Kakkausar muryar Aganani ce inda yake tambayar Rayyanu bayan sun gama
lugwigiwta shi kamar lemon yara.
Ta tuna lokacin da bakin Rayyanu ya bude kamar zai yi magana amma hakan ba ta samu yiyuwa ba,
har yanzu surayya tana da burin ta san abin da Rayyanu ke son fada, ta tuna irin yadda bakinsa ya motse sannan ya dan bude lokacin da yake son yace.."
Wani zazzafan gumi ya zubo mata a fuska ta sa hannu ta goge fuskarta a daidai lokacin da gumin
yake kokarin shigar mata ido.
Zuciyarta ba ta yarda ta amince da abin dake darsuwa cikinta ba, to amma wasu dalilai ma su tsauri su suke son tilasta mata amincewa da abin.
Tun sa'r da ta dau hoton zuciyarta ke raya mata cewa sunanta Rayyanu ke son fada wa AGANANI Mu-sha-gara"
"Ina hodar iblis din" ta sake tuna tambayar Aganani mu-sha-gara in da yake tambayar Rayyanu.
Hoton Rayyanu inda yake kokarin yin
magana ya sake bayyana garai-garai a zuciyarta.
Tabbas sunanta yake son fada, abin da ta kasa tabbatarwa ada shi ne shin sunanta yake son fada
ko ba sunanta ba. Yanzu kam ta san cewa sunanta yake so ya fada ko shakka ba ta yi a kan Hakan, domin in ba hakan ba menene dalilin son yi mata tambayoyi da yansandan suke?" Ta tambayi kanta.
Abin da kuma ya dada dagula mata lissafi shine ta yadda aka yi har yansandan suka gane ta, ita dai ta
san ba su isa su gane ta ba daga fadin suna kawai. Ta kuma san Rayyanu ba zai iya bayyana musu
kamanninta ba a lokacin, musamman ma idan akayi la'akari da irin halin da yake ciki.
Ta ci gaba da safa da marwa cikin dakin, "Babu ta yadda za'a yi yansandan su gane ta in har ba hoton
ta suka samu ba." "To a ina suka sami hotonta" Ta tambayi kanta.
Ga mamakinta sai ta ji amsar tambayar ta darsu
zuciyarta. "A dakin Rayyanu suka sami hoton."
Surayya ta ce da kanta. Ta tuna da tangamemen hoton data baiwa Rayyanu tun zamanin duniya
tana yi da su, wani sassanyan gumi ya fara kwarara a gadon bayanta. Yansandan ba wawaye ba ne"
Tace cikin zuciyarta. "Ko da Rayyanu bai fada musu da hoton ba, suna iya binciken gidansa tun da dai
ya fada musu sunanta. Tsoro da fargaba suka kama ta, sannan ga mamakinta sai ta ji wani
zazzafan hawaye ya kwararo kan kumatunta. "Shin yanzu da a gida nake gidan gaban iyayena
haka za ta faru kuwa a kaina?"
Ta tambayi kanta.
.
Sannan ne fa ta juya ta nufi wani dakin dake fuskantar wanda take ciki, dakin Grace ne matar
jackson. Hasken ranar dake ratsowa ta cikin
gilashin dakin ya isheta ganin duk abinda take bukatar gani. Ta matsa jikin bango akwatin hodar
iblis din Rayyanu ce. Surayya ta bude akwatin
sannan ta dubi hodar Iblis din dake ciki.
"Ba zan bar kowa ya dora hannunsa akanki ba" Ta
ce da hodar Iblis din kamar mutum ce ita.
Surayya monika ta zauna akan tattausan kilishin tsakar dakin ta mike kafafunta sannan ta bude
jakarta ta dauko hotunan data wanko ta zuba su
akwatin sannan taci gaba da kallonsu kamarba
tataba ganinsu ba.
Zaman da tayi dirshan akan kilishin dakin tana
duban akwatin, ta san abin da ya kamata tayi. "Ki dauki akwatin da hotunan ki kaiwa kwamishinan
yansanda ki yi masa bayani, kin ga shikenan kin
fitar da kanki, ko dai hukunci zai hau kan ki to da
sauki tunda dai kin tsira da rayuwarki."
Zuciyarta ce ke ba ta shawarar haka, amma
maimakon hakan sai Surayya ta mike tsaye ta nufi tagar dakin dake fuskantar katon lambun gidan,
iskar bakin kogin dake kadawa ita ta sa furanni da
fulawowin shuke-shuken gidan su ma suka fara
rawa kamar kida ake musu. Surayya ta dubi
fulawowin zuciyarta cike da tunani, "ba zan auri karuwa ba" Ta tuna inda Haidar ya mare ta "Ni ka mara Haidar sai ka gwammace baka mare ni ba."
Ha! Ha!! Ha!!! Dariyar Haidar ce inda yake cewa
"Haba yarinya ba ki isa komai baTunanin abubuwan da suka faru a baya su suka kara rura wutar bakin ciki da kuma mummunar aniyar ramuwar gayyar dake zuciyar Surayya. Ta dubi furannin shuke-shuken sannan ta ce da
kanta: "Sai na rama Haidar sai na rama sai ka yi bakin ciki, sannan kuma ka yi kuka da hawayenka kamar yadda na yi."
Abin kenan da ke zuciyar Surayya, wacce ita aganinta ramuwar gayyar ita ce kawai hanyar da zata huce haushinta.
"Sai na rama koda kuwa shi ne zai zama abu na karshe da zan yi aduniyar nan" ta sake
maimaitawa kanta.
.
************ ************ *********
.
HAIDAR ya muskuta akan gadon da yake kwance, sannan ya juya kan bangarensa na dama.
Sa'o'insa biyu kenan amma barcin ya gagare shi, ya dade yana haure-haure a kan gadon amma hakan
bai sa barcin ya dauke shi ba.
A duk lokacin da ya rufe idonsa sai ya ga Surayya inda ta durkusa a gabansa tana rokonsa don Allah
ya so ta ya kuma kaunace ta koda na minti daya ne.
Wasu lokuta kuma sai ya ga inda yake sharara mata mari da kuma inda yake hankaɗa ta Cikin ruwa.
Yau kusan wata biyu kenan da faruwar lamarin, amma tun ranar da abin ya faru sai ya ji duk
al'amuran duniya sun rikice masa. Shi kansa abinda ya yi wa Surayya yana ba shi mamaki, Surayya kyakkyawa ce ajin farko, ba kuma dukkan ɗiya mace ba ce take da irin kirar Surayya, to amma
menene dalilin wulakantata da ya yi. Shi kansa bashi da amsar wannan tambayar.
Ranar da abin ya faru bai yi barci ba, haka kawai abin kamar wasa, sai ya ji duk tunaninta ya rufe masa zuciya. Babu abin ma da ya fi ba shi mamaki
irin yadda ya ji duk tausayinta ya kama shi.
"Haba Haidar bai kamata ba kai ma da bakinka kake cewa da ni karuwa, da ka san irin kaunar danake ma da ba ka kira ni da hakan ba, ka tuna fa
kaunar ka ce ta sa na sayar da yancina da martaba ta ta ɗiya mace da kuma ajina na durkusa a
gabanka nake rokonka da ka so ni, haba Haidar ka tausayawa zuciyata kar ciwon sonka ya zama ajalina..."
.
A duk lokacin da ya tuna da lokacin da Surayya ke fada masa wannan kalamin sai ya ji ya tsani kansa, abin kamar wasa, sai ga shi yau ko abinci ba ya iya ci sosai saboda tsabar tunaninta, abin bakin ciki kuma tun ranar da abin ya faru baikara ganinta ba, ballantana ya ba ta hakuri...
"Hakurin me zai ba ta..." Ya tambayi kansa, a daidai lokacin da ya yunkura ya tashi ya zauna, sannan ya kunna wutar lantarki dakin ya gauraye da haske.
Yanzu kam ya tabbata ya kamu da ciwon sonta batare da ya san hakan ba, shin daman haka so yake,
ba ya zuwa sai a lokacin da ba'a bukatarsa.
"Yanzu ina zan ga Surayya ko na dan ji dadi." Ya tambayi kansa, sannan ya tashi tsaye a kan gadon ya kifa kansa jikin bangon dakin yana tunani.
.
"Kai ne wanda nake so Haidar ba zan kuma taba iya daina son ka ba." Maganar Surayya ce ta sake
dawowa zuciyarsa begen ganinta ya sake lillibe masa zuciya, ya tuna irin yadda take caba kwalliya
ta zo har gurinsa domin su yi hira amma ya wulakanta ta, sai ga shi kuma yanzu shi yake son ganinta. Dandanon gishirin da ya ji abakinsa shi ya tabbatar masa da cewa HAWAYE ne ke kwarara daga idanunsa.
.
***
"A shirye nake da na kashe ka, kamar yadda kai ma ka yi niyya da farko." Alhaji Banasare ne ke fadin hakan. Aganani mu-sha-gara ya dubi hancin
bindigar dake barazana ga rayuwarsa.
Da za ka ajje bindigar da sai hirar ta mu ta fi dadi, amma hakan da ka yi tana iya tashi fa..." AGANANI ne yake cewa da BANASARE. "Babu abin da ya shafe ni, ko bindigar ma ba ta
tashi ba, ni zan tashe ta da kaina, amma da farko ina son ka dauko min jakar hodar iblis din da ka kwace daga hannun Rayyanu domin tawa ce ba taka ba. Idan ka yi hakan, shi ne zai sa na yi maka kyakkyawan harbi daya akai, ka ga sai ka yi mutuwar gaggawa ba tare da ka wahala ba.
Abin da Aganani ya gani a idonsa shi ya tabbatar masa da cewa yana iya aikata abin da ya yi niyya...
"Ba ta gurina jakar." Aganani ya ce muryarsa na rawa.
"Karya kake Aganani, gara tun wuri ka kawo min kayana Idan kuma ba haka ba, to zan yi maka kisan da za ka dade ba ka mutu ba, da farko sai na harbe kafaffunka sannan kuma na fasa kokon
kanka da alburushin bindigata" Sannan ya dada dacewa, "Mutuwar irin ku ita ta fi sauki, sannan kuma
rahamace ga al'umma na san cewa ni ma mai laifi ne kamar ka, amma ina ganin ka fi ni hadari ga al'umma. Banasare ya yi shiru, sannan ya saita
hancin bindigar kan kirjin Aganani ya ce "Zabi daya, mutuwar sauki ko ta wahala, ka dawo min da
kayana sai na kashe ka farat daya, idan kuma ka ki to sai na karairaya kafafunka kafin ka tafi barzahu.
.
********** ************ ***********
.
Duk lokacin da ya sanya abincin a bakinsa, sai ya ji kamar ya dawo da shi, ya dauke hannunsa tsam
daga abincin sannan ya fice daga dakin ya nufi gindin dan gajeren famfon da ke tsakar gidan ya
wanke hannunsa, sannan ya wuce kai tsaye ya zauna akan kujerar da ke daf da wata bishiyar dorawar turawa.
"Surayya" Wannan suna ya zame masa tamkar ruwan dalma ne cikin zuciyarsa, a duk lokacin da
sunan ya darsu a ransa, sai ya ji zuciyarsa ta dauki
radadin bege, idan aiki ya ke, to aikin ya kare kenanHajiya Tabawa ita ce mai otal din, ta matsa kusa da
yan sandan, suka yi kuskus. Na yan mintuna tana
muzurai, da kyar ta ke numfashi, yansandan hudu
daga cikinsu suka shige cikin otal din, sauran biyun
kuma suka tsaya a bakin kofar suna muzurai.
Usman ya dan yi gaba da niyyar su bar wajen, Haidar ya yi sauri ya rike rigarsa ta baya ya janyo
shi baya, sannan cikin murya kasa-kasa.
"Ina zaka tafi kuma, me ya yi ruwanka da su,
aikinsu suke hirar mu muke, ba wani abu muka yi
musu ba, yanzu idan muka bar gurin haka cikin
gaggawa suna iya zaton ko wani abu ne." Usman ya yi murmushi.
"Ka san ni fa matsoracin yansanda ne ban cika son
wani abu ya hada mu da su ba."
"Kana bani labari." Usman ya ce ba tare da ya yi
kasa-kasa da muryarsa ba. Sannan su biyun suka ci
gaba da hirarsu da suka katse. "Oh, kana ji ko Usman, uhm-uhm, me nake cewa ne ma da?"
"Inda ka ke cewa wai ina da labarin yarinyar ka
Surayya."
"Yauwa, to kana ji ko, wallahi wannan yarinyar nan
ta kauna ceni, kauna kuma ba kankanuwa ba, kauna babba na ke nufi ta hakika, wallahi Usman a
lokacin..., ka ga dai ba zan boye maka komai ba,
sanin kanka ne duk garin nan babu wanda bai san
Surayya yar bariki ce ba, amma saboda kauna ta da
take, cewa ta yi in har zan aureta ta yi min
alkawarin ta daina yawan bariki har abada, kuma na tabbatar da hakan, domin a bakin kogin Usman
yarinyar ta durkusa gwiwoyinta a kasa tana
rokona wai na kaunace ta, amma kasan abin da na
yi mata?" Usman ya girgiza kansa cikin mamaki.
"Angizata na yi cikin ruwa, a lokacin Usman babu
wacce na tsana a duniya kamar ta, na tsane ta ne, sabanin yanzu Usman." Haidar ya yi shiru yana
duban Usman, hannayensa cikin aljihun dogon
wandonsa.
"Ina fatan ka fahimci yarinyar da na ke magana
kai."
"Haba Haidar." Usman ya ce "Wanene garin nan bai san Surayya monika ba?"
"Usman." Haidar ya kira sunansa, Saurayin yana
dan girgiza kai, alamun takaici karara su ke a
fuskarsa.
"Na tsinci kaina cikin wani kangi Usman kangin da
ban san ranar fita cikinsa ba, har sai na yi ido hudu da Surayya, ina son ka sani Usman kangin da na
shiga ba wani abu ba ne face tsabar sonta da ya yi
dirar angulu cikin zuciyata ba tare da ya shawarce
ta ba, daya shawarci zuciyata Usman da ban bari
kaunar Surayya ta lullube zuciyata ba, ka dube ni
Usman ka ga duk yadda na lalace saboda begenta, amma har yau ban yi ido biyu da ita ba, rabona da
ita tun lokacin da na hankada ta cikin kogi wannan
kusan wata biyu kenan." Haidar ya yi shiru yana
kokarin mai da kwallar da ke barazanar fitowa
daga idanunsa.
"Abin da ya fito da ni bakin kogin nan kenan usman, na zauna ko zan ganta na dan ji sanyi a
zuciyata, sai gashi na yi rashin sa'a. Ko mai kama da
ita ban gani ba. Usman ina zaton za ka taimaka min
duk inda ka ji duriyarta ka sanar da ni, domin ya
zama dole na ganta cikin kwana biyu in kuwa ba
haka ba, ai ban san yadda zan yi da sonta da ke cikin raina ba.
"Zan taimaka maka, in Allah ya yarda." Usman ya ce
cikin tausayawa Haidar.
Dan gajeren dansandan da ke daf da su Haidar ya
yi ajiyar zuciya lokacin da ya ji karshen hirar ta su.
Ko shakka ba ya yi yanzu kam ya san Surayya da suke nema ita wannan surayin ke magana, Dan
gajeren dansandan ya yi murmushi sannan ya ce
gara da Allah ya sa na saurari hirar da su ke bari su
dogo su fito na basu labari.
.
Yansandan biyar suka yi shiru suna sauraron
dangajeren dansandan mai kai kamar murhu yana ta bayani.
"Idan har akwai mutumin da zai yi mana
sanadiyyar kama yar banzar yarinyar nan da ke
wahalar da mu to wannan saurayin ne, domin irin
yadda na ji yana surutun begenta, dole ne ya yi
duk abinda zai yi don ganin sun hadu, dansandan ya daga hannunsa ya nuna mutum uku, ya ce ina
son

Please Login or Register in order to submit comment