Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ku bi yaron cikin fararen kaya kada ku sake ya
bace muku duk inda za shi ku bishi a baya tabbas
na san zai kai ku ga Surayya.
"To kuma yaya za mu yi da Alhaji Banasare ko ka
manta da cewa shi muke nema yanzu." Wani dogon dansanda ne ke magana. Dangajeren
dansandan nan ya yi shiru yana tunani, sannan sai
ya zaro selular da ke aljihunsa, ya fara daddanna
lambobin. Da ya san cewa a lokacin Alhaji Banasare
na barazana ga rayuwar Aganani da bai buga
wayar ba.
.
"Ka zabi inda ka ke ganin ya dace na harbeka ba
na son bata lokaci."
Idanun Aganani mu-sha-gara suka fito tulu-tulu
kama idanun kwado. Da kyar ya ke shadar
numfashi, idanunsa a kan hancin bindigar da ke
hannun Banasare. "Haba Banasare, ka tuna abin da na yi maka fa, duk
fa da taimakona ka sami arzikin da ka ke takama
da shi."
"Kada ka bata bakinka mu-sha-gara." Alhaji
Banasare ya ce. "Ai ban manta da abin da ka yi min
ba. Shi ne ma ya sa na ke san karya kafafunka da alburushin dindigata, sannan na fasa kokon
kanka, na yi ido biyu da kwakwalwar da ke shirya
maka tunanin cin amanar aboki.!
Banasare ya daga bindigar ya yi saitin kirjin
Aganani mu-sha-gara ya ce.
"Sai wataran abokina, mu kuma sai mun..." A daidai lokacin ne salular da ke aljihun Aganani ta dau ki kara..........
.
Mutanen biyu suka dubi junansu na dan lokaci,
Aganani mu-sha-gara na jiran ya ji sallamar
harsashi a kokon kansa, shi kuma Banasare na
sauraron karar salular sai dai kuma har yanzu
idanunsa akan Aganani su ke baya ko kibtawa.
Hannun Aganani ya kai ga aljihunsa da niyyar ya dauko salular da ke kara. Ganin cewa Banasare na
kallon sa kuma bai ce da shi kala ba, sai hakan ya
dada masa kwarin giwa. A hankali sai ya zaro
salular daga cikin aljihunsa sannan cikin gaggawa
sai ya daga salular zuwa bakinsa, tun kafin salular
ta kai ga saitin inda zai yi magana ya lura da kamanin Banasare fuskarsa ta yamutse sannan
wani dangajeren murmushi ya bayyana akan
lebban bakinsa.
Idanun Aganani mu-sha-gara suka fito kulu-kulu,
ya san abin da murmushin ke nufi, ya kuma so ya yi
magiya amma abin da ya biyo baya shi ya tabbatar masa da cewa ya makara.
Karar bindigar ya gauraye ko'ina cikin gidan, gami
da farin hayakin da ya tashi sama yana ninkaya a
sararin samaniyar dakin. Alhaji Banasare ya so
alburushin bindigar ya sami Aganani a tsakiyar
kokon kansa, amma sabanin hakan sai alburushin ya wuce kai tsaye ya daki tafin hannun Aganani
wanda ke rike da salular.
Aganani ya kwalla kara a tsorace sannan radadi da
karfin harbin suka jefa shi baya kansa ya dako
wani dankaramin teburi da ke tsakar dakin kafin
kiftawa da Bismillah jini ya hada ko ina a jikin hannun da aka harba.
Ya dubi Banasare a tsorace yana murkususu a
tsakar dakin.
"Don Allah ka yi min rai, wallahi zan baka duk abin
da ka ke so."
"Ba na son komai daga gareka." Banasare ya ce lokacin da ya sake daga bindigar da niyyar sake
harbawa.
"Abin kawai da nake bukata a gurinka shi ne
ranka, shi nake san rabaka da shi, amma ni bayan
wannan bana bukatar komai a gurinka"
Banasare ya yi wani dan gajeren murmushin da ya fito da jerin jerarrun hakoransa, ya tabe baki
sannan ya saita fankadeden kirjin Aganani, ya ja
kunamar bindigar. Tun kafin dan yatsan Banasare
ya kai ga kunamar bindigar Aganani mushagara ya
rufe jajayen idanunsa sannan ya ja dogon
numfashi na karshe yana jiran alburushin ya ratsa kirjinsa. Ya yi mamaki lokacin da yan dakiku suka
shude bai ji komai ba. To amma ya so ya ji karar
bindigar ta bada wani dan makararren sautin da ya
yi kama da irin sautin da za ka ji idan ka karya
dansiririn itace busasshe.
Aganani mu-sha-gara ya bude idanunsa a hankali jikinsa na bari hannunsa na zogi da radadi, kamar
wanda aka sokawa Allura, idanun nasa da kyar
suke dauko masa sauran surar Banasare wanda ke
tsaye a kansa, dishi-dishi ya ke iya ganinsa, amma
hakan bai hana shi gane cewa bindigarba ta
hannun Banasare ba. Cikin rudewa da rashin fahimtar abinda ke faruwa, sai ya yi ta yan maza ya
kara bude idanunsa sosai. Ga farin cikinsa, sai ya ga
bindigarba ta hannun Alhaji Banasare mai makon
bindigar wata sullubebiyar wuka ce tana kyalli
kamar madubi a cikin rana. Jikin Aganani ya dauki
bari ya tabatar yanzu kwanansa ya zo karshe a duniya, domin ya san irin mahaukacin kaifin da
wukar ke da shi mafi yawan lokuta da ita ya ke
yanka kayan marmari idan ya zo gidan shakatawa,
ya yi mamakin yadda aka yi Banasare ya dauki
wukar.
"Tun da bindigar ta ki na harbeka da ita, bari to na yi amfani da wukarka kaima yau sai ka ji irin abinda
ake ji idan an yanki abu da wuka.!
Banasare ya fara matsowa kusa da inda Aganani
ke kwance, ya yi mamakin abin da ya hana
bindigar tashi, to amma daya tuna da tsawon
lokacin da ya dauka bai yi amfani da ita ba, sai mamakin ya kauracewa zuciyarsa, abin kawai da
ke ransa shi ne ya yi maza ya soke Aganani, tun
kafin wani ya shigo gidan.
Irin yadda idanun Banasare ke jujjuyawa kamar
idon yartsana, lokacin da ya matso shi da wukar,
shi ya fi tsorata Aganani mu-sha-gara, ya tabbatar babu abin da zai hana Banasare kashe shi.
"Na tuba ka yi min rai." Aganani ya roka muryarsa
na rawa.
Banasare bai amsa ba, sai ya ci gaba da matsawa,
yana muzurai. Aganani ya fara jan gindi yana ja da
baya har sai da bayansa ya hadu da bangon sannan ya dago kai bakinsa na rawa ya ce.
"Don Allah ka yi min rai kada ka kashe ni."
"Kisa kam ya zama dole sai dai ko kace na yi a
hankali kar na so ki wannan katon cikin naka da
wuka, na san babu komai a ciki sai giya."
Harbin da aka yi wo Aganani, shi ya fi damuwa, ya san in badan harbin ba, yana iya doke Banasare
bugu daya kamar yadda zai buge kuda daga
bayan hannunsa, amma ya san hakan bai yiyuwa,
irin yadda hannun ke zogi ya san da wahala ya iya
doke koda dan kankanin yaro ne.
Mu-sha-gara ya sha jin labarin Aljannu tun yana karami, sau da yawa ya kan misalta kamanninsu a
zuciyarsa duk da yake kuwa bai taba ganinsu ba,
to amma lokacin da ya dubi idanun Banasare
wadanda ke, jujjuyawa, sai ya fara tunanin an ya
kuwa, wannan mahaukacin da ke kansa baya daya
daga cikin ire-iren Aljannu?
.
************ ********** ************
.
Haidar ya juya firgigit, lokacin da ya ji sassanyar
muryar ta yi kiran sunansa. A tsaye a kansa sanye da doguwar riga shudiya..........SANYE DA SHUDIYAR RIGA MAHAIFIYAR SA CE
"Tunanin me kake yi ne haka?" ta tambaye shi.
"Babu komai momi." Ya ce da ita. Mahaifiyar tasa ta yi shiru tana dubansa na tsawon dakiku, sannan sai ta dago hannunta a hankali ta rike kugunta, ta ce da shi.
"Karya ka ke Haidar, tabbas akwai abin da ke damunka, na lura yan kwanakin nan ko abinci ba ka san ci sosai, ko baka jin dadi ne?"
Haidar ya daga kansa ahankali ya dubeta, sannan ya girgiza kansa.
"To in lafiyarka kalau, mene ne dalilin zama jugum din kana tunane-tunane?"
Haidar ya dago fuskarsa ahankali suka sake hada idanu da mahaifiyarsa. Kusan dakiku biyar da wasu yan digunguna suna duban juna. Haidar ne ya fara kawar da fuskarsa.
"Haidar abin da nake so da kai idan wani abu ne ke damunka sai ka sanar da ni, bai kamata ba kabar abin kai kadai ya yi ta ci maka rai." Mahaifiyarsa ce ta ci gaba da fadin hakan. A daidai lokacin da Haidar ke mammatsa yan yatsun hannayensa, fuskarsa na duban kasa, babu alamar walwala a fuskarsa.
"Momi walla..." ya yi shiru yana dubanta, maganar ta makale a bakinsa, bai sami damar karasa kalaminsa ba saboda in har zai sanar da ita gaskiyar lamarin to dole ne ta ji batun Surayya, wadda a tunaninsa ba zata taba amincewa da ita ba.
"Wallahi me?, ci gaba mana, me kake son fada." Ta ce da shi cikin tattausar murya.
Jin sauyawar muryarta ya yi mutukar bashi mamaki. Ya dago kai suka hada ido. "Fadi mana, Haidar me kake bobboyewa ne, ba maganar Surayya ka ke son yi ba ai daman na san dole ne sai wata ran ka dawo kana sonta, na cin ta ma kawai ya isa ya jefa ka cikin wannan jarabar, dubi yadda ka lalace kamar tsunken sakacen hakori, yanzu duk yan matan garin nan ka rasa wacce ka ke so sai wannan lalatacciyar yarinyar, haba É—annan ka yiwa kanka fada mana, har yanzu ace ba ka san abin da zai zame maka sharri ko alkhairi ba, ban hana ka ka so wacce ta ke ranka ba, amma yana da kyau mutum ya duba irin daya kamata ya tanada dan shukawa."
Jikin Haidar na rawa kamar mazari ya yi mamakin yadda aka yi har Hajiya Binta ta fahimci abin da ke ransa. To amma daga karshe sai bai yi mamaki ba daya tuna irin haukan son da yake yi wa Surayya a yan kwanakin nan wasu lokuta, har sunanta ya kan kira a fili saboda kauna, shin to ko anan mahaifiyarsa ta fahimci hakan ya tambayi kansa.
"Ki yi hakuri momi wall... Wallahi ni duk na rasa yadda zan yi da so..."
"Karasa mana, wato ka rasa yadda za ka yi da santa ko, kana nufin kenan ba zaka rabu da ita ba kenan? Shikenan tunda ka ki kaje ka yi abin da ka so. Kafin kalamin nata na karshe ya gama dukan dodon kunnensa, tuni ta bar gurin ta bar shi a sunkuye.
"Momi.." Maganar tasa ta makale a bakinsa, fadin ta bashi da amfani, domin wacce ya ke son fadawa ta shiga daki ta bugo kofar a bayanta, ya yi shiru yana sauraron amsa kuwar sautin bugo kofar, kwakwalwarsa ta kasa tunani babu abin da ya ke ji sai kalaminta.
"Shi ke nan tunda ka... Ki... Ka... Je... Ka... Yi.. Abin da... Ka... So!!!
.
************ *********** **********
.
Bakar motar fijo (505) ta shigo lungun a hankali kamar ana tura ta da hannu. Su uku ne a ciki direban motar sanye yake da bakar riga suwaita, farin wando da hula hana salla. Na biyun dan gajere ne mai katon kai, sanye ya ke da doguwar riga da wandanta shudaye hula zannabukar, ta samar wa kanta matsugunni a tsakiyar kansa, kamar ya kifawa murhu. Na ukun su dogo ne dan tsololo kamar lawurjen wando, sanye yake da dogayen kaya kamar dayan, dan'uwansa sai dai shi nasa farare ne.
Dukkanin ukun yan sanda ne amma da wahala ka gane hakan, domin yansandan biyu masu dogayen kaya, sun fi kama da malaman makaranta fiye da yansanda, sai dai wasu lokuta dan tsurkun din gashin bakin da suka tattara shi ya ke barazanar fallasa ko su su wane ne. Motar ta bi tsayin layin ahankali tana tafiya, har izuwa lokacin da ta karasa kofar gidansu Haidar ba tasauya yana yin tafiyarta ba, yansandan uku suka dubi kofar gidan sannan lokaci guda suka dauke idanunsu cikin gaggawa, kai kace wani abin kunya ko fargaba suka hanga a kofar gidan. Motar ba ta daina tafiya ba har sai da je karshe layin sannan ta lankwasa ta nufi titin da yayi bangaren hagu, tana shan kwanar sai ta tsaya a kofar wani masallaci dake daf da kan kwanar layin. karfe biyu saura kwata agogon dake jikin motar ya nuna. Mutane ukun suka dubi juna babu wanda yace da kowa uffan kamar kurame sannan guda biyun masu dogayen kaya suka fito suka nufi masallacin daya daga cikinsu ya dauki gwangwani ya zagaya dankaramin bandakin da ke bayan masallacin yayin da shi kuma dayan ya tsugunna a gaban wani gwangwanin da almajirai suka cika da ruwa ya fara alwala.
Shi kuma direban da ke jan motar ya yi zamansa ciki, yana zukar sigari yana fitar wa ta hanci kamar salansa, mintuna uku suka shude a dai-dai lokacin Haidar ya fito daga cikin gida dauke da littattafan Ilmin addinin Islama guda uku, ko da yake dan sandan bai fahimci ko littattafan menene ba.
.
Fom! Fom!! Fom!!!
Sautin hon din motar da direban
motar ya danna ya ratsa cikin masallacin, nan da nan yansandan biyu wadanda ke sanye da dogayen kaya suka fito daga masallacin daya a bayan daya, suna muzurai, kowannensu rike da carbi suna ja, duk da yake kuwa, bakinsu da zuciyarsu basu fadin komai, sai tunanin hanyar da za su yi su bi Haidar inda za shi ba tare da ya gane
suna binsa ba. Dan gajeren ne ya bishi a baya yana jan carbi, idan
kaga yadda ya ke tafiya sai ka rantse da Allah, shima kamar sauran magidanta ne wadanda ke kokarin isa gidajensu bayan an idar da sallah. Kusan mintuna biyar kenan da bin Haidar sai ga dan gajeren dansandan ya dawo.
"Ashe makaranta za shi." ya ce da su.
"Wacce makarantar kuma" Dan tsololin ya tambaya. "Ba ka ga litattafan addini ne a hannunsa ba, ai zauren wannan gidan ya shiga shi ne na wuce sai da na je karshen layin na juyo, ina tsammanin kuma shi da ya fito sai wajen biyar da rabi ko shida,
zuwa bakwai." Ya dan yi shiru yana dubansu na dan lokaci, sannan ya ce da su.
"Ku tafi ku barni anan, domin idan muka ci gaba da zama mu da ku anan to mutane na iya fara zargin
wani abu, ka da ku dawo sai sha biyun dare ni ina nan ina zagawa.
Bayan sun tafi ya nemi guri a kofar masallacin yana jan carbi, kamar sauran mutanen da ke kofar
masallacin bambancin kawai shi ne shi ba salati ko sunan Allah yake kira ba abin da zuciyarsa ke cewa
shi ne.
"Ka gama ka fito ka same ni ina nan, mu nan wuni nan kwana wai kwarkwata ta ga kan mai kora."
.
********** *********** *************
.
"Meka ke so to na baka? Fadi duk abin da ka ke so Aganani mu-sha-gara ne ya ci gaba da magana.
Abin da na ke son ka bani, guda daya ne, shi ne katuro min wannan katon cikin naka na soke shi da
wuka."
Idanuwan Aganani suka yi kuru-kuru, kamar idanun kwado, bai taba ganin tashin hankali irin wannan ba, lallai gaskiya ne da ake cewa
tsammanin zaka mutu ya fi mutuwa ciwo. Aganani ya zargi kansa da wauta rashin ajiye tsayayyen mai
gadi a gidan shakatawar tasa, a tunaninsa babu wani mahaluki da zai iya kasadar kai masa farmaki,
sai yanzu ne ya gane kuskurensa. Karar razanar da ya kwalla gami dakarar harbin bindiga suka cakude sannan suka bada wani irin
sautin marar dadin ji kunnen wanda hankalinsa ke kwance.
Abu uku ne suka faru kusan lokaci guda na farko,
Banasare ne ya yunkura ya soki Aganani a baya, na biyu Aganani mushagara ya kwalla karar
razana, duk da yake kuwa sukan da aka yi masa ba wani tasiri sosai yayi ba a sakamakon abu na uku da ya faru.
.
Doguwa ce siririya wankan tarwada, kanta babu dankwali, sanye ta ke da doguwar riga tsukakkiyar launinja, wacce ta fito da duk wasu surori da ke jikinta, dogon hannunta ya dace da dara-daran fararen idanunta, sunanta SISILIYA, ko da yake wasu
daga cikin yaran Aganani sukan kirata da wani lakabi wai
(Promise Lady) babu mamaki hakan
yana da dagantaka da kyawawan lebban bakinta jajaye wadanda ke dauke da alkawarin tattausan
murmushin da ke tafiya da imanin wadanda suka damu da murmushin matan banza.
Banasare ya fada gefe guda, hannunsa na dama a
dafe da kugunsa, ya ci gaba da murkususu.
Aganani mu-sha-gara ya yunkura da kyar ya jingina bayansa da bango yana duban Sisiliya,
wacce ke tsaye a kansa tana yi masa kallon yaya aka yi ka bari haka ta faru."
"Ya mutu ne?" Aganani ya tambayeta muryarsa na rawa, a daidai lokacin da ya kalli Banasare wanda
ke kwance, gefe guda. "Ina ruwanka da mutuwarsa darling? Ko kana
nadamar mutuwar makiyinka ne?"
Aganani ya girgiza kai, yana ciccije baki saboda azabar da hannunsa ke yi.
"ki yi wani abu mana, yaya za ki tsaya a nan kina kallo... kallon?" Aganani ya buga mata tsawa. Cikin gaggawa
Sisiliya ta nufi inda kan talfon yake ta danna lambobin sannan ta fara magana a hankali.
"Barka dai." Shiru "Sisiliya ce ke magana. Adaidai
lokacin da take maganar ne Allah ya yi wa A.D. Banasare cikawa. Har izuwa dakikarsa ta karshe a duniya A.D. Banasare bai daina tunanin hodar Iblis din sa ba, tun sa'ar da ya ji alburushin bindigar ya
ratsa kugunsa, ya tabbatar mutuwa zai yi, to amma yanzu ba mutuwar ya ke fargaba ba, abin kawai da
yake kona masa rai shi ne zai mutu ba tare da ya rama cin amanar da Aganani ya yi masa ba abu na karshe da ya tuna a yayin mutuwarsa shi ne
babban yaronsa Rayyanu, Rayyanu! Shi ne sanadi, a haka su Banasare YABAR DUNIYA.
.
********** ********* ***********
.
Aganani Mu-sha-gara na zaune, hannun da aka
harbe shi daure da katon bandeji, ya juyo a hankali ya dubi Sisiliya wacce ke kusa da shi, ita ma sanye
da kayan yansanda, kamar sauran mutum goman da ke zazzaune suna fiskantarsa.
Dakin ya yi shiru a daidai lokacin da dogon dansandan ya ci gaba da yin bayanin abubuwan da suka faru, tun daga lokacin da suka tafi farautar Banasare bakin ruwa har zuwa lokacin da suka hada Haidar da mutum uku su yi gadinsa lokacin
da ya zo inda daya dangajeren dansandan nan yace da mutum biyu din su tafi su barshi sai Aganani
ya daga masa hannu Dansandan ya yi shiru yana sauraron abin da zai biyo baya, zuciyarsa cike da fargaba ko ba su yi daidai ba"Da kyau." Aganani ya ce cikin wata bakuwar murya wacce bai saba yi musu magana da ita ba. "Kun yi kokari. Ya ci gaba da cewa "Sai dai kokarin ku ya zama na banza, kama tuna fa har yanzu ba mu cimma burin mu ba, ina Surayya bamu san inda take ba."
Ya yi shiru na dan lokaci sannan ya ce "Ya kamata mu kawo karshen abin nan tun yana da zaki, kada mu sake ya sauya dandano zuwa daci, saboda abu guda. Amma abin haushi, sai gashi wai wata yarkaramar yarinya ta hana cikar burinmu, ku tuna fa sanadiyyar abubuwan nan kadan ya rage ni ma na bakunci lahira, in banda na yi sa'a Sisiliya ta fado gida kamar daga sama da yanzu nima kun sani a lissafin wadanda suka bakunci lahira. Aganani ya yi dariyar mugunta sannan ya dubi yansandan. Babu wanda ya gwada ko da murmushi ballantana dariya, kowa ya san abin da dariyar ke nufi, masifa ce ba wani abu ba. Suka yi tsit suna sauraron su ji sakamakon da dariyar ta haifar, zai yi wahala ka ji ko da motsi a cikin dakin, in ka daukes autin da ganyayyakin bishiyun ke bayarwa, a yayin da iska ta busa su.
Aganani Mu-sha-gara ya yunkura a hankali, ya mike tsaye, ba kowanne mutum ne zai iya juriyar Aganani ba, duk da irin radadin da hannunsa ke yi, gami da zafin da bayansa ke yi inda aka soke shi da wuka, haka bai hana shi mikewa tsaye ba, abin sam-sam bai dame shi ba, kamar ba a jikinsa raunin yake ba, kai ka ce harbin da aka yi masa a tafin hannu harbin danko ne ba harbin danko ne ba harbin bindiga ba. Ya duba agogon da ke manne a jikin bangon dakin, karfe goma sha biyu saura kwata.
Ya daga hannun da bashi da raunin sannan ya nuna uku daga cikin yansandan wadannan mutane su ne suka fi aiwatar da mafi yawancin munanan sana'ar Mu-sha-gara, su ne aka tura su binciko gidan Rayyanu, domin nemo hoton Surayya Monika.
"Ina son ku je ku sami Suraj." Ya ce da su, Suraj shi ne sunan dansandan nan da aka bari yana gadin Haidar a kofar masallaci.
"Bai kamata mu jira har sai wannan yaron ya kai mu ga kama ta ba, abin da na ke so ku yi idan kun je shi ne, ku kamo shi ku zo min da shi nan, na san yadda zan yi masa" Sannan ya dada da cewa "Ina bukatar ganinku da shi nan da karfe daya na dare, idan kuka wuce haka to kada kus ake na sake ganin munanan fuskokinku daga can ma kawai ku yi gaba ku shiga duniya, domin masifar da za ku gani idan kuka dawo baku zo min da shi ba, tafi wacce za ku tarar idan kun shiga duniya ku bace min.
Ya buga musu tsawa, yansandan uku suka fice daga dakin gudu-gudu sauri-sauri har wani yana cin dunduniyar dan uwansa.
Aganani ya dubi sauran yansandan ya ce, "Nan da kwana uku za mu gama da wannan Dil din daga nan sai kowa ya kama gabansa.
.
********** ************ **********
.
Motar ta ci birki a kofar masallacin kuu!!!. Yansandan uku suka yi tsalle suka dirdiro daga cikin motar. Tun kafin su gama taka kasa dangajeren dansandan mai sanye da doguwar riga ya mike tsaye, Zurat! Kamar wanda aka soka da tsinin mashi.
"Lafiya?" Ya tambaya duk da yake kuwa ya tabbata babu lafiya din.
"(Boos) ya ce mu tafi da shi yanzun nan yana son ganinmu da shi cikin gaggawa"
Dogon dansandan ne ke magana
"Kan me ya ke son ya gana da shi?"
Gajeren ya tambaya.
"Allah masani, amma idan ka damu da ka san dalilin sai ka tambayi (Boss) idan mun koma" Dogon ya amsa. Dan gajeren ya yi shiru sannan ya ce da su, "To yanzu a wacce mu ke."
Kai ka san a wacce mu ke" Dogon ya amsa, "Ai kafi mu sanin makama, domin kuwa kai ke gadinsa ko ka bari ya kubuce maka."
"Yana cikin gida" Dangajeren dansanadan ya ce da su. "Tun kusan sha daya ya shiga har yanzu kuma bai fito ba, ina tsammanin kuma shi da fitowa sai gobe. Abinda ke damuna shi ne zuwa zamu yi kai tsaye mu yi sallama idan ya fito mu tafi da shi ko kuwa ya ya za mu yi da shi, na san dai idan muka yi haka dole ne iyayensa su san yansanda ne suka kama shi, me yiyuwa kuma su yi zaton ko laifi ya yi, kaga dole ne su je neman belinsa gobe da safe, wanda hakan na iya gurbata shirin mu gaba daya, tunda kamun da aka yi masa ba shi da alaka da hukumar yansanda.
"Ka fadi gaskiya fa." Dogon dansandan ya ce, "Sai dai kuma, duk hakan ba za ta fitar da mu ba, daman (Boss) ya ce in har bamu je masa da shi ba, to ya ce yana shawartarmu da mu shiga duniya, baya bukatar ganin munanan fuskokinmu"
yansandan hudu suka yi shiru suna shawarwari "Wani lokaci na kan yi mamakin (Boss) idan ya ce abu kamar mahaukaci" Dogon ne ke magana. Dangajeren ya yi shiru bai ce da shi komai ba, kusan dakiku uku, sannan ya daga kansa ya ce "Gaskiya na fara gajiya da abubuwan nan domin hadarin da ke cikinsu ya fi alherin da ke cikin harkar yawa" Ya dago kai ya dubi yansandan uku sannan ya ce "Shin kuna zaton idan (boss) ya cimma burinsa zai sakemu kuwa?"
yansadan uku su ka yi shiru, sannan wani dan tsattsama daga cikinsu mai fuskar matsorata ya ce "Idan har muka tsira da lafiyarmu daga wannan harka to mun yi sa'a tabbas, saboda haka zancen abin da za mu samu ma bai taso ba, ni daman tuni na fitar da rai"
"To mu koma kan abin da ke damun mu, yanzu yaya za mu yi mu kama yaron nan."
.
Kamar amsa tambayarsu, sai ga Haidar ya fito
daga cikin gida, daga shi sai gajeren wando da
riga (T-shirt) a kirjinta an rubuta (Beautiful lady).
Tun kafin ya karaso inda suke, yansandan suka
dubi juna, sannan kafin su gama yanke shawara,
Haidar ya shiga cikin wani dan matsakaicin kanti
wanda ake sai da kayan masarufi, yansandan
hudu suka koma cikin mota, sannan direban ya ja
suka nufi kofar kusa da kofar kantin sannan suka
tsaya. Biyu daga cikinsu suka fito.
Haidar ya fito daga kantin dauke da gwangwanin
man kashe kananan kwari (Mobil) ya yi turus ya
tsaya, lokacin da yaga yansandan shi suka nufo.
"Dan samari, muna bukatar yin wata yarkaramar
tafiya da kai."
Haidar ya dubesu jikinsa na rawa, babu abin da
ya ke tsoro irin dan sanda. "Laifin me na yi?" Ya
tambaya.
"Idan mun je ka ji." Suka ce da shi.
Bai yi gardama ba sai ya bisu, suna binsa a baya,
suna zuwa sai suka tura shi cikin motar su hudu
a baya daya direban kuma gaba, karfe daya saura
mintuna ashirin yansandan suka kai shi gaban
Aganani Mu-sha-gara.
Tun da Haidar ya ke, bai taba ganin mummunan
mutum da tsoratarwa irin Aganani ba.
***
Ta bude idanunta a hankali tana duban surar
dakin. Tun sa'o'i uku da suka wuce take kwance
amma ko da wasa barci ya ki ya zo mata. Ta san
abin da ya hana ta barci, amma ba ta son ta
tabbatarwa da kanta hakan. Misalin karfe hudu
da rabi na yammacin ranar, tunanin ke ta kai
kawo a tsakanin zuciya da kwakwalwarta, ta
tsani tunanin domin wanda take tunanin dominsa
ta tsane shi tun wasu lokuta da suka wuce, wasu
lokuta takan daure

Please Login or Register in order to submit comment