Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Alhaji Banasare
ne, "Dauki Rayyanu" wata zuciyar ta ce da shi. Ya
dauki kan talfon din, sannan ya tambaya "Wace
ce?"
.
"Saurara da kyau." Aka ce da shi "Ni ce Surayya
Monika, da kuma za ka dauki Shawarata da sai na ce da
kai kayi sauri ka hada tsummokaranka ka
bar garin nan tun da sauran kwananka,
Ubangidanka ya turo yansanda za su kama ka kasan kuwa
in suka kama ka to kashinka ya bushe."
.
"Me kike nufi?" Rayyanu ya tambaya. "Kin ga
Surayya Wallahi idan ba so ki ke..." Rayyanu ya yi shiru.
Idan har ba kunnensa ne ke fada masa karya
ba ya ji kukan jiniyar yansanda. A can daya
bangaren talfon din Surayya ta kyalkyale da dariya,
sannan ta ce "SUN ISO. Habawa! Dan samari, duk
sharrinka kalilan ne akan na mace, sakayyar kisan
da ka yi wa Mu'azu ce ka fara gani tun a duniya."
.
"Idan sun kama ni ba!" Rayyanu ya ce a fusace,
"Idan kuma na ƙwace kashinki ya bushe! Yarinya
wannan dai kin yi nasara, amma ki tuna fa ba
kullum take juma'a ba,
.
"Mu zuba mu gani dan samari." Surayya ta ce, ko
Surayya dake can daya bangaren tana sauraro ta ji
kwakkwaran dukan kofar dakin da yansanda
suka fara yi ta yi sauri ta aje kan talfon din.
.
********** ********** **********
.
Rayyanu ya leka tagar dakin, a daidai lokacin da
aka ci gaba da dukan kofar da kafa daga inda yake
tsaye yana hangen yan doka guda uku suna jiransa a
gindin hawan benen, a kofar otal din
kuma M.K. Aganani Mu-sha-gara na zaune yana
zazzare idanuwa, salula a hannunsa yana ta faman
babatu kamar zai amayar da hanjin cikinsa, jajayen
idanunsa, hade da kakkauran gashin bakinsa, su
suka sa yawun bakin Rayyanu ya kafe, "Hanya mafi sauki
na gudu, domin idan na yi musu bayani ma a
banza" Rayyanu ya ce a cikin zuciyarsa, yanzu kam
ya tabbatar kashinsa ya bushe idan suka kama shi,
ya tabbatar yansandan Alhaji Banasare ne suke
yiwa aiki don haka duk wani bayani ma a banza,
hanya mafi sauki ya gudu. Aka ci gaba da dukan kofar da
kafa, tuni har kofar
ta fara alamun yin saranda, Rayyanu ya leka tagar
dakin, har yanzu yansanda na nan, don haka sai
kawai ya ja da baya ya fara tunanin abin yi kofar
dakin ta bada kara, sai ta fara budewa kadan-
kadan, ko da Rayyanu ya lura sai ya ga ashe yansandan su
biyu ne aka turo masa, don haka sai
kawai ya nufi karkashin tangamemen gadon dake
dakin ya shige ciki, idonsa akan saitin kofar dakin,
bai fi dakika goma da shigewa ba, kofar dakin ta
balle da wata irin kara marar dadin ji, kofar ta fadi
kan kafet din tsakar dakin, yansanda biyu suka bayyana a
dakin, suna dube-dube, ba su ga komai
ba, Rayyanu yana ganin kafafunsu, don haka sai ya
matso gaba-gaba yana jan ciki a daidai lokacin ne
yansandan biyu suka matso gaba-gaban gadon
suna dube-dube, Rayyanu ya ziro hannayensa biyu
ya kama kafar yansandan dai-dai ya fizga da karfi,
yansanda suka zube babu shiri daya daga cikin
yansandan ya yi ƘARAR RAZANA
Rayyanu ya yi sama gaba daya ya ɗago da gadon,
ya rufe yansandan, sannan ya nufi kasan benen da
gudu, bai dade ba ya zo matattakalar da za ta kai
shi kasan benen na karshe don haka sai ya fara
tafiya a hankali, ko da ya karaso sai ya leko a nan
ne ya ga yansanda biyu, su kuma suna hawowa bene, ya
yi wuri-wuri ko zai ga gurin buya babu, ya
kama kofar wani daki zai shige sai ya ji a rufe, ya
juya kuma zai koma baya da gudu sai ya jiyo
wadancan yansandan da ya rufe da gado su kuma
suna biyo shi don haka sai kawai ya yi kan
wadancan na gabansa da gudu, kafin su farga ya banke su
ya wuce idonsa ya rufe ba ya ko tunanin
akwai saura a waje bai tsaya ba yana gudu sai ya ji
wani abu mai kama da kafar doki ya daki kafarsa
ya kwalla kara a lokaci guda kuma ya fadi, ya dago
kai suka yi ido hudu da wanda ya yi dukan.
Aganani Mu-sha-gara ne.
.
*********** ********** ***********
.
Surayya ta aje kan talfon din sannan ta yi
murmushi, sannan ta ce cikin zuciyarta "Kadan ma
ka gani azzalumi" Tana zaune akan kujerar da
Grace ta saba zama ne.
Lokacin da Surayya ta yi nasarar kwace hodar iblis din
nan daga hannun su Rayyanu sai taga babu
wani waje da zata ji dadin buya sai gidan su Malam
Jackson, da matarsa Grace, tun da ga shi yanzu
tana da kudi, me zai sa ta dami kanta, abin kawai
da za ta yi shi ne ta sayo kayan abincin da zai ishe
ta, ta yi zamanta a nan gidan tunda ba kowane ya san da
gidan ba.
Zaman da take a yanzu a cikin babban falon
Jackson take, da kuma talfon dinsa take amfani
gurin aikata abin da taso. Koda ta aje talfon din sai
ta ga ya kamata ta tafi bakin gabar kogin domin ta
sha iska, don haka sai ta koma dakin barcin da Grace ta
saba amfani da shi kafin ta tafi. Inda kuma
a nan ne Surayya ta ke kwanciya a yanzu, a nan ne
ta zabo yar karamar singileti fara, sannan ta daura
zanen atamfa kore mai adon furanni, launin gwal,
bayan ta gama shiri tsaf, sai ta nufi bakin kogi. Tana
zuwa sai ta shige cikin jirgin ruwan da ta dauka, haya
lokacin da za ta gudo, ta yi zamanta a ciki tana
tunanin kuma abin da zai biyo ba ya, abin da take
jira ta ji shi ne shin yan sanda sun kama Rayyanu,
ko kuwa ba su kama shi ba, idan ba su kama shi
ba, ita za ta shiga nemansa har sai ta danka shi a
hannunsu, idan kuwa sun kama shi, to burinta ya cika
kenan, "Saura da me kuma?" ta tambayi kanta
"Saura HAIDAR" zuciyarta ta ba ta amsa.
UMMUL ABA'ISI, kenan wanda shi ne salsalar duk abinda
yafaru. Tabbas saura shi. "ta ce cikin sassanyar murya,
"Sai shi ma ya gane kuskurensa" Ga mamakin Surayya, sai
ta ji tana tausayinsa. "Shin har yanzu daman son Haidar
na cikin
zuciyarta? Ta tambayi kanta?"
Sassanyar iskar bakin kogin ta ci gaba da kada
gashin kan Surayya, masu santsi da sheki, daya
daga cikin mayen karfen da ke jan hankalin duk
namijin da suka yi ido hudu da ita kenan "HAIDAR!
haba zuciya kar ki zalunce ni mana, bana son
Haidar na tsane shi" ta ce a hankali. Ita kanta ba ta
yarda da kalamin da ta furta ba, hakika ta san har
yanzu akwai soyayyar Haidar a tare da ita "Amma
dole ne na nuna masa kuskurensa. "Yadda ya
wulakanta ni sai na rama.. Tunaninta ya gushe, adaidai
lokacin da ta ji dirin karar injin jirgin ruwa.
Ta yi mamakin jin hakan, domin duk iya zamanta
da su Jackson bata taba ganin babban jirgi ya wuce
ba, amma da taji karar injin wannan jirgin ta san
kato ne. Ba'a dade ba sai ga jirgin ya bayyana a fili, ga
mamakinta sai taga a hankali yake tafiya, tana
kuma iya hango yansanda hudu akan saman jirgin
kowannensu rataye da bindiga na biyar din neba
tagane ba, wanda shi ta lura kamar a kwance yake,
hannayensa a daure a bayansa. Duk ta sami ganin
hakan ne sakamakon hasken fitilar cikin jirgin ruwan da
ta haskake ko'ina cikinsa, amma babu
alamar fitilar waje. Zuciyar Surayya ta fara bugawa
tsakanin hakarkarinta, "Kamar Rayyanu" ta ce a
hankali, lallai kuwa shi ne. Ta gane hakan ne ta
hanyar wani dansanda da ya tashi Rayyanu zaune,
ya kwara masa ruwa akai. "Ina za su kai shi" ta tambayi
kanta, a daidai lokacin ne to jirgin ya matso
kusa da inda take yana tafiya a hankali, nan da nan
Surayya ta yi sauri ta fice daga jirgin ta buya a
tsakanin sarkakiyar bishiyoyi da ciyayin da suke
bakin kogin. Daga inda take boye tana iya hangen
fentin jirgin ruwan fari sol, an yi masa layi da fenti launi
kore, a tsakiyar koren kuma an rubuta da
bakin fenti "Banasariyya Police" Ba'a dade ba, jirgin
ya wuce inda take boye bayan ya dan gota ta
kadan sai ta yi sauri ta koma cikin gidan da gudu,
tana zuwa ta buda wata loka, ta yi sa'a ta sami abin
da take nema kyamarar Malam Jackson ce. Ta sha
ganinsa yana buda lokar yana daukowa, ga shi
cikin sa'a bai tafi da ita ba, ta buda kyamarar babu
sauran dodon daukar hoton a ciki, amma akwai
sabo wanda ko amfani ba'ayi da shi ba, a kusa da
kyamarar a ajje. Ba a dade ba da yin hakan sai ga
Surayya cikin jirgin ruwanta ta dafawa su Rayyanu baya
abin duka ya faru ne cikin abinda bai Gaza minti goma
ba.
.
Tafkeken gida ne mai dauke da dakunan gana
azaba, irin na yan sandan ciki, har guda shida,
kowanne daki yana dauke da masu azabtar da
mutum guda shida, babban dakin shi aka kai
Rayyanu, tuni har an tube shi daga shi sai gajeren
wando. A ka'ida yansandan ciki su suka saba irin wannan
tuhumar duk wani mai laifin da yaki fadin
gaskiya. A yau kuma sabanin sauran lokuta M.K
Aganani mu-sha-gara ne ke azabtar da Rayyanu.
Wasu karti guda biyu masu kama da ƙwaɗi, suka
kama kafafun Rayyanu suka jefa shi sama, suka
kauce ya fado sannan suka haushi da duka tun yana kara
har ya kasa sannan Aganani ya daga
musu hannu suka tsaya sannan ya matso kusa da
Rayyanu ya daki bakinsa da kwabdeden
takalminsa. Bakinsa ya fashe jini ya fara zuba,
"Ina koken din ta ke?!" Aganani ya daka masa tsawa.
"Ban dauka ba." Rayyanu ya ce, "Wallahi Surayya ce."
"Karya ka ke fadi gaskiya idan ba haka ba kuma
yau za ka gwammace dama ba a haife ka ba."
Rayyanu ya yi shiru saboda azaba, kirjinsa kamar
zai fashe Aganani ya dakawa kartin tsawa, nan da
nan daya katon ya yi tsalle ya fado akan kirjin Rayyanu,
ya yi wata irin kara mai ban tausayi da
razanarwa, hatta Surayya wacce ke make a kofar
dakin tana daukar hoton abin dake faruwa sai da
ta tsorata da irin azabar da ake ganawa Rayyanu,
ita kanta ta san cikin hadari take yar kafar dake
jikin dankareriyar kofan dakin azabtarwar ita ta baiwa
Surayya damar daukar hoton duk abin da ke
faruwa.
Rayyanu ya some, kafin ya farko an kawo wani
katon diro cike da ruwa, Aganani ya cakumi
wuyansa ya daga shi sama da hannu daya kamar
yartsana, sannan ya dilmiya kansa cikin ruwan sai daya
daga cikin kartin ya taka cikinsa da kafa,
ruwan da ya sha ya fara bulbulowa ta baki da
hanci, kamar fashewar mitar ruwa, Aganani mu-
sha-gara ya daga hannu suka tsaya, sannan ya
matso kusa da shi ya ce, "Yaro! Kar ka yi wasa da
rayuwarka akan naira miliyan arba'in, ko ka fada min
inda ka boye koken din ko kuma na yankaka
da ranka." ya ce da shi cikin tsawa.
Bakin Rayyanu ya bude, amma ya kasa magana,
abin kawai da ya yi nasarar fitarwa shi ne,
"Surayya." "Wace ce Surayya?" Bakin Rayyanu ya sake
nuna alamar "Monika."
Aganani ya yi fushi, domin shi a zatonsa Rayyanu
bai sani ba ya ce don haka ya sake dakawa kartin
tsawa "A sake dabara!" ya ce da su. Daga saman
dakin, kamar tsafi, igiyoyi biyu suka taho a daure a
bakin kowacce igiya kugiya ce. Aka yi sama da Rayyanu
kamar kara, suka raba
kafafunsa biyu, suka daure shi kowacce kafa a
daure a jikin kugiya daya. Sannan suka fara lila shi
tun Rayyanu na numfashi har ya kasa, su kuwa ba
su daina ba, suka ci gaba da tsalala masa bulalar
wayar lantarki, duk bayansa ya fashe, yana ta zubar da
jini, Aganani mu-sha-gara ya daga hannu
suka tsaya, sannan ya matsa gaba, kusa da ina kan
Rayyanu ke lilo kafafunsa a sama "Wace ce
Surayya?"
Bakin Rayyanu ya ce "Monika."
Bakin ciki ya sake kama Aganani har yanzu shi ya dauka
Rayyanu ban sani ba yake cewa, cikin fushi
ya zaro wuka mai kaifi daga aljihunsa ya yanyanke
igiyoyin da Rayyanu ke lilo akai, ya fado kasa da
wuya, sannan kafarsa ta dama ta dan motsa bai ko
kara motsawa ba, Aganani ya daga shi tsaye sai ya
ji ya yi nauyi, yana sakinsa sai ya fadi sharkaf. Surayya ta
dauki hoton gurin, sannan ta zurare ta
tabbata Rayyanu ya mutu.
.
Aganani ya ja da baya sannan ya zaro farin kyalle
daga aljihun rigarsa na gaba ya goge fuskarsa, da
kuma sankonsa wanda ke kyalli, "Ya mutu." ya ce
da kartin, da kuma sauran yansandan da ke dakin. "Abin
da ya rage yanzu shi ne mu nemi yarinyar da
ya ke ta fadi Surayya, na tabbata koken din tana
wajenta, amma idan har muna son mu sami dukiyar
mu cikin ruwan sanyi dole ne mu san yadda za'ayi
mu kawar da mutum guda."
yansanda suka kalle shi idanuwan su cike da tambayar
abin da yake nufi,
"Abin nufi a nan shi ne..." ya ci gaba da cewa,
"...kun san yanzu babu wanda ya san da hodar
Iblis din daga mu sai Alhaji Banasare, sai kuma
yarinyar nan Surayya, wacce yanzu na tabbata ta
dauki hodar iblis din, saboda haka idan muka kawar da
Alhaji Banasare ya rage daga mu sai
Surayya kenan, muna kama ta an gama. Kudi ya zo
kenan kuma kowannen ku dama dazu na fada
muku abin da zai samu naira miliyan daya da rabi,
kunga duk sai mu yi ritaya, ko me kuka gani yara?"
Ya tambaya yana zazzare idanu. "Haka ne yallabai!" Suka
amsa gaba dayansu, dakyau yarana, saboda haka yanzu
ga abin da ya
kamata mu yi wajen kawar da Alhaji Banasare."
Sannan ya fara fada musu shirinsa na makirci.
Bayan ya gama sai ya sami mutum hudu, ya ce "ku
za ku kai shi." sannan ya nuna dayan ya ce, "kai kuma
gobe karfe bakwai na safe zan jira ka a
ofishin kwamishina, bakwai daidai ka bugo waya,
ka sanar da shi cewa akwai rikici a gidan Alhaji
Banasare, ka gane ko, ni kuma zan yi sauran."
"Yes Sir" dansandan ya amsa, gaba dayansu suka
watse.
.
*********** ********** ***************** ******** *********
Misalin karfe hudu da rabi na asuba, Alhaji Banasare ya
fito zuwa danƙareren masallacin Allah ga nakan da ya
gina, a kofar gidan shakatawarsa, wanda kuma wai shi ne
babban limamin duk da
yake kuwa shi kansa bai san ka'idodin zama liman din ba.
Ba'a dade ba ya tada sallah guntun talakawan unguwa
wadanda kwadayin abin duniya ya tsone wa ido suka bi
shi.
Yansandan hudu dake jiransa ya fita tun awowi biyu da
suka shude suka shige gidan dauke da gawar Rayyanu
suna yi mata cali-cali suka shige
cikin gidan da ita ba'a dade ba suka fito. Karfe bakwai na
safe daidai M.K Aganani ya shiga shimfideden ofishin
kwamishinan yansanda na Banasariyya, kamar jiransa
dama talfon din yake ya
shigo ya daukara, yana shigowa sai ya kame, ya yi
gaisuwa irin ta yansanda sannan ya dau kan talfon din, ya
fara magana, kwamishin yansanda SULAIMAN S. BABA
yana kallon sa. Dan gajere ne kakkaura, shima yana da
dan tarin gashin baki, amma ba can ba,
ba don Ƙoshi ya yi masa yawa ba, da kuma tsufa da ya
fara kama shi, da sai ka kira shi kyakkyawa, yau
shekarunsa talatin da takwas kenan yana aikin dansanda,
ita ce kuma ta zo daidai da shekarar sa ta goma sha daya
akan kujerar kwamishinan yansanda na Banasariyya.
Aganani mu-sha-gara, ya aje talfon din, "Menene?"
Suleman ya tambaya,
"Ni ma ban gane ba" Aganani ya ce "Peter ne ya bugo
waya daga unguwar su Alhaji Banasare, wai ya ji hayaniya
a gidan kamar ana fada, sun je gidan
kuma an ki a bude, to ka san yadda Alhaji Banasare yake
a garin nan don haka suka ji Tsoron haurawa."
"Kwarai kuwa sun yi daida da suka sanar da mu."
Kwamishinan ya ce "Amma ka ce masa su sake "Try" idan
ba'a bude ba to su karya gidan su shiga ni na sa su."
"An gama Sir." "Ka kuma tura musu karin yara ko abin zai
fi karfinsu," Kwamishina ya ce.
"Yes Sir" Aganani ya amsa.
.
Alhaji Banasare ya shigo tangamemen falon dake da
doguwar tasbaha tana jan kasa kamar da gaske, yana
zuwa sai ya wuce bangaren falon na bangaren kudu yana
zuwa sai ya bude kofar da
niyyar ya dauko wasu kudade da ya aje su tun shekaran
jiya, kofar lokar ta bude gawar Rayyanu ce ta biyo kofar
ta fado kan kafar Alhaji Bansare,
wanda ya daka tsalle guri guda, sannan ne ya gane
Rayyanu shi kansa duk da taurin kansa sai da abin ya
girgiza shi, "Rayyanu!" ya kira sunansa, sannan
ya durkusa ya dafa kirjinsa. A daidai lokacin ne babbar
kofar falon ta bude yan sanda suka cika falon, su bakwai
ne kowanne dauke da bindiga harbi ka ruga, "ku kama
shi." Wani jami'i Peter yace, yana zazzare idanuwa ba
wasa.
.
*********** *********** ***********
.
Surayya monika ta yi murmushi, fararen hakoranta suka
bayyana afili, lokacin da ta tunkari ma'aikacin wanda ke
fitowa daga cikin dakin na'urorin wanke
hotuna hannunsa na dama rike da jakar zuba hotunan.
"Barka da aiki." Ta ce da shi a daidai lokacin da mutanen
dake cikin dakin suka juyo kusan lokaci
guda suka dube ta sannan kuma lokaci guda suka maida
hankalinsu gurin karbar hotunan kowa na kokarin shiga
gaban dan uwansa don mika
rasitinsa. Duk da yake na'urar sanyaya dakin na ta
kwararar da sansanyar iska hakan bai hana Jama'ar
sharbar gumi ba wanda mafi yawansu maza ne,
mata uku ne kawai in ka hada har da Surayya cikin
lissafinka.
"Sannunki da zuwa." Ma'aikacin ya ce da ita, gami da dan
murmushi.
Suka yi ido hudu da Surayya, zuciyarsa ta buga sannan ya
ji tsigar jikinsa ta yi yar!! Jikinsa ya dauki rawa, Surayya
Monika ta dan kara matsawa gaba ta sake haske shi da
murmushin Allah kashe ni don dadi.
"Ki...na bukatar wani abu...ne...."
Ma'aikacin ya tambaya muryarsa na rawa. Rabonsa da
ganin kyakkyawar yarinya kamar wannan dake gabansa
har ya manta, mata da yawa kuma kyawawa su kan zo
gurin domin wankin
hotunansu amma mafi yawan su ba kyawawa bane,
akwai wasu lokutan da kyawawan suke ziyartar gurin sai
dai kuma, ba su fiye shigowa cikin dakin karbar hotunan
ba, sai dai su zauna cikin
mota a waje, su kuma direbobinsu su zo su karbar musu.
To amma duk cikin matan da ya gani a baya ba zai iya
tuna wadda ta kama ko da kafar Surayya
wajen kyau ba. Sannan kuma akwai wani abu dake tare
da ita wannan yarinya dake tsaye agabansa wanda ke jan
hankalinsa da kuma duk wata nutsuwarsa kamar yadda
mayen karfe ke jan karfe. Surayya ta kanne idonta na
dama sannan ta ce
cikin muryar da za ka iya kira sarewa.
"Kwarai kuwa ina bukatar taimako dan samari"
Ma'aikacin ya yi murmushi sannan ya ji farin ciki ya
lillibe shi don jin cewa an kira shi dan samari. Wasu
mutane guda biyu dogo da dan tsattsama wadanda ke
tsaye daga baya-baya suna jiran su
sami yar kafar da za su mika rasitinsu don karbar
hotunansu, suka dubi junansu, sannan kuma
lokaci guda suka dubi Surayya cikin mamaki domin jin
cewa ta kira ma'aikacin wai dan samari. Mutanen biyu
suka yi murmushi, tsakaninsu da su
Surayya bai fi taki uku ba, amma duk da haka sun ji abin
da take fadi Dogon mutumin ya kalli dan tattsaman
sannan ya matsa kusa da shi ya yi kasa-kasa da muryarsa
sannan ya ce.
"Ka ji abin da take cewa da shi kuwa? Wai dan samari."
Suka tuntsure da dariya sannan suka tafa, dan
tsamirmirin ya ce da dogon.
"ya kusa sa'an ubanta fa dubeshi ka gani zai kusan
shekara arba'in da biyu, kawai don dai yana jin dadi ne
don haka bai motse ba, amma ka ji don daurewa karya
gindi wai dan samari! Tab!! Agaishe da samari." Suka sake
fashewa da dariya, hakan ne ma ya sa har wasu daga
cikin mutanen dake turmutsitsin karbar hotunansu suka
juyo domin ganin abin da samarin biyu ke yi wa dariya.
"Yana da kyau a ce mun dan kebe guri guda, kinga
hayaniyar mutane ta yi yawa a nan." Ma'aikacin ya ce da
Surayya yana dan murmushin da yake tsammanin shi ne
murmushin da ya fi kowanne daukar hankalin mace a
gurinsa, ko da yake a can bangaren Surayya ita
murmushin nasa ya zo mata ne a matsayin irin kamannin
da zaka gani a fuskar wanda aka sokawa allura. "Yana da
kyau ace mun kebe din" ta ce da shi tana rangwada a
gabansa kamar dawisu. Tuni ta gane cewa ta saye
zuciyarsa, farin ciki ya lullube ta saboda ganin ta karya
zuciyarsa ta yin amfani da
kyakkyawar surarta, ta san kuma a shirye yake da ya mika
soyayyarsa a gareta, hakan kuma yana da matukar
muhimmanci a gareta.
Ma'aikacin ya nufi wata yar siririyar kofar daki dake
fuskantar katon dakin karbar hoton daga bangaren kudu
sannan ya zaro dan mukulli daga aljihunsa ya bude
sannan ya shiga Surayya na biye
da shi a baya. Surayya ta dubi dakin lokacin da
ma'aikacin ya maida kofar ya rufe sannan ya dawo ya
janyo daya
daga cikin kujeru biyu dake dakin ya zauna ita ma
Surayya ta janyo dayar ta zauna.
Dan kankanin daki ne mai kamara akurki in ka dauke
kujeru biyu da teburin dake dakin da kuma wasu tarin
takardu dake kusurwar dakin yamma maso kudu, babu
komai a cikin dakin sai fankar
dake juyawa a saman dakin wanda tuni ta sa Surayya
fargaba, kar ta fado musu aka, saboda atunanin Surayya
fuka-fukan fankar na iya cin karo da bangon dakin yayin
da take juyawa, saboda kankantar dakin.
"Sai dai ki yi hakuri Hajiya kin ga dan dakin namu kamar
roko shi muka yi."
"Babu komai." Surayya ta ce da shi tana murmushi
sannan ta ci gaba da cewa "Daman wasu yan hotuna ne
nake son samunsu da gaggawa yau din nan bana son su
kai gobe saboda tafiya zan yi da
su idan an jima." Ta dubi agogonta sannan ta yatsine
fuska, lokaci guda kuma ta sake haske ma'aikacin da
tattausan murmushinta.
"Taimakon kenan da nake son ka yi min ka ga (film) din
ko dodon ma ba'a fito da shi ba, a fada min ko nawa ne
zan biya."
Ma'aikacin ya yi murmushi cikin mamaki sannan yace,
"Ranki ya dade wannan ai ba wani abu, daman ai muna
irin wannan aikin na gaggawa kudin kawai ake riɓanyawa,
amma Hajiya tun da ke ce zan iya yi miki a madaidaicin
farashin na da."
"Na gode." surayya ta ce da shi.
Sannan ta dube shi har yanzu tattausan murmushin bai
bar fuskarta ba.
"Ai har yanzu ba ka bari na karasa fada ma taimakon da
nake son ka yi min ba." "Kamar me fa?"
Ma'aikacin ya tambaya cikin mamaki.
"Za ka iya kuwa?" Surayya ta tambaye shi, a daidai lokacin
da ta bude jakarta ta dauko dodon hoton wanda ke
nannaɗe a cikin wani dan karfe, sannan ta rufe jakar.
"Fadi mana ranki ya dade." Ya ce da ita "Ai babu
taimakon da ba zan iya yi miki ba ai darajarki agurina ta fi
komai.." ya dan yi shiru, cikin dan jin kunyar abin da ya
fada. Shi kansa bai san lokacin
da kalmar ta kwace masa ba.
Surayya ta dube shi sannan tace da shi, "Ni ma ai
fahimtar haka ne ya sa nake neman taimakon agurinka,
naji dadi kuma jin cewa ashe wai har ina
da wata daraja ta daban a gurinka."
Ta dan girgiza kanta sannan ta dan matsa gaba ta dora
kyawawan hannayenta a kan teburin ta ce da
shi, "Ba na son kowa ya ga hoton sai kai kadai, saboda
hoton sirri ne a gareni kai ma kuma ganin irin mutuncin
da na ga kana da shi ne ya sa zan amince da kai na baka,
na san ba za ka so ka tona
sirrina ba." Ta yi murmushi.
"Haba Hajiya aikin fi karfin ko..komai a gaurina." yace
muryarsa na rawa duk lokacin da ta furta dadadan
kalamanta sai ya ji kaunarta ta kara shige masa zuciya irin
kalaman kwantar da hankalin da take yi masa magana da
su yanzu su suka sa jikinsa rawa numfashinsa kuma
sama-sama.
"Wannan ba damuwa." ya ce da ita lokacin da ya mike
tsaye. Surayya ta mika masa dodon hoton, ya karba.
"Dan jira ni ina zuwa." ya fita da sauri ya maida kofar ya
rufe.
Ba'a dade ba sai ga shi ya dawo dauke da kwalaban lemo
guda uku a hannunsa da kuma kofin roba guda daya ya
ajiye a kan teburin dake gaban Surayya.
"Sai ki dan jira ni." Ya ce da ita, "Nan da yan mintina zan
zo miki da hotunan." Sannan har zai fita sai yadawo, ya
leka karkashin teburin ya janyo lokar
teburin, daga cikinta ne ya zaro wani littafi na Kasar Turai
wanda ke dauke da hotunan kyawawan guraren
shakatawa da kuma tallace-tallacen finafinan daukar hoto
da kyamarori ya ajje a kan
teburin a gaban Surayya.
"Ga abokin hira nan" Ya ce da ita.
"Na gode, har da wannan wahala haka? Ni da ka bar ni
ma haka ai babu damuwa.
"Ah! Haba Hajiya ai kin wuce wannan." Ya ce da ita a
daidai lokacin da ya nufi kofar dakin sannan ya sake
juyowa suka hada ido da Surayya. Magidancin mutumin
da kuma matashiyar yarinyar suka dubi junansu na dan
lokaci. Sannan ya juya ya
fice daga dakin zuciyarsa cike da tsabar kaunarta.
Mintuna ashirin da daya daidai sai ga shi ya dawo cikin
dakin da Surayya ke jiransa hannunsa rike da jakar
hotunan.
"Har an yi me?!" Surayya ta tambaya cikin mamaki. "Har
an gama." Ya ce da ita yana murmushi.
Surayya ta ajje littafin dake hannunta, sannan ta karbi
jakar hotunan ta zazzage su. Kala uku ne hotunan ko
wane kati bibbiyu.
Hotunan sun yi kyau matuka, fiye da yadda Surayya take
tsammani. Hoton farkon ya nuna Aganani tsaye a kan
Rayyanu lokacin da katon nan ya yi tsalle ya fado akan
kirjin Rayyanu.
Hoto na biyu kuma ya nuna inda Aganani ne ya ɗaga
Rayyanu sama ya dulmiya kansa cikin dirom ruwa. Sai
kuma hoto na karshe, Aganani Mu-sha-gara ne
rike da kwalar rigar Rayyanu lokacin da yake kokarin
daga shi amma kuma rai ya yi halinsa.
.
Surayya ta yi ajiyar zuciya sannan ta maida hotunan cikin
jakarsu, ta kuma bude tata jakar ta jefa jakar
hoton ciki ta rufe. Ma'aikacin na tsaye a kanta fuskarsa
sharkaf da gumi alamun tambaya karara suke kuma
abayyane a fuskarsa.
.
************* ************ ************
.
Yansandan goma sha daya suka yi shiru suna saurarena.
Aganani ya ci gaba da cewa, "Idan son samu ne yana da
kyau a ce mun kama yarinyar nan cikin kwana biyu."
Ya dan yi shiru yana dubansa sannan ya yi nazarin
tafkeken falon da suke ciki. Kujeru sama da ashirin sun yi
layi a cikin dakin shakatawar

Please Login or Register in order to submit comment