Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a kai ba "Hodar
Iblis!" ta tambayi kanta
.
Ta sake daukar daya wasikar ta fara karantawa, ga
mamakinta sai taga a ashe amsar waccan wasikar ce da ta
gama karantawa yanzu.
Na ga sakonka Alhaji, na kuma dawo gida lafiya
zan zo jibi, tare da bayanin yarinyar da za mu sa ta yi
aikin, tuni har na sa babban yarona binciken wacce ya ga
kanta ya waye da bariki...
"Kamar ni ke nan!" Surayya ta yi dariya, sannan ta aje
wasikar ta fice daga dakin.
Ba'a fi mintuna biyar da faruwar hakan ba sai ga Surayya
ta shiga dakin saukar bakin dauke da jakun-kunanta guda
biyu ta sami mutumin da ta sa aikin zaune yana karanta
mujalla, tana zuwa sai ta mika masa dan mukullin, "Na
gode.." Ta ce da shi,
"...ni zan tafi sai kuma wani lokacin."
Ya bude baki yana kallon ta cikin mamaki. "Hajiya me ya
sa zaki tafi tun yanzu, ko dan..." Irin kallon da ta yi masa
shi ya sa shi ya yi shiru.
"Sai an jima" Tace da shi. Kafin ya sake buda baki ta fice
daga otal din, tana fitowa ta sami mota ta ɗaga mata
hannu ta tsaya "Falmanda otal" ta ce da direban motar
.
Falmanda otal ita ma katuwar otal ce a nan garin
banasariyya, tana ɗaya daga cikin kayatattun otal dake
garin Ko babu komai a kalla dai tana da manya-manyan
dakunan kwana, wanda mutum biyar za su kwanta ba
tare da wani ya shaƙi numfashin wani ba. Fulawowi da
yan kyawawan dukus-dukus din bishiyoyin dake
Falmanda otal su ma abin kallo ne, in ka dauke inda
motoci ke bi, da
kuma inda aka yi shuke-shuke ko ina tayil ne a otal din.
Lokacin da ta iso otal din, sai ta fara tunanin ko
mafarki ta ke yi?
.
A zaune a farfajiyar otal din akan kujera, bakin
tabarau a idonsa sigari a bakinsa, mujallar kwallon kafa a
hannunsa, daya daga cikin samarin nan ne, wanda suka
jefar da ita a bakin kogi, abu daya ta tabbata shi ne ba zai
taba gane ta ba, saboda daman ganin dare ya yi ma ta,
bai kuma taba ganin ta ba, sai ranar da Rayyanu yasa su
dake ta.
Farin ciki ya lullube ta, hakika sa'a a bangarenta take. Ta
kasa gaba ta kasa baya, zuciyarta cike da tunanin abin da
ya kamata ta yi, tuni ta fara tunanin cewa wannan ita ce
damar da take jira ta rama abin da Rayyanu ya yi mata.
Duk da yake dai da farko ba ta yi niyyar farawa takan
Rayyanu ba, abin da ta yi niyya shi ne ta fara ta kan
Haidar, wanda shi ne musababbin faruwar komai. Sai
kuma ga shi hannun agogo ya dawo baya. "Tabbas
wannan dama ce a gare ni mai girma." Ta ce cikin
zuciyarta.
Mintuna biyu suka shude tana tsaye, daga karshe ta yanke
shawarar abin da ya kamata ta yi, sannan sai ta nufi cikin
otal din, ta yi wa kujerar da saurayin ke zaune kallo daya
sannan ta dauke kanta. Ta na tafiya kamar dawisu, ta nufi
inda sauran jama'a ke zaune suna shakatawarsu, tun
kafin ta karasa
gurin da samari da yammata ke juyawa, zuwa ga kallon
ta, zuciyar samarin cike da yabo na kyaun cikar halittar
Surayya, zuciyar magidantan wajen su kuma cike da
takaicin ganin yarinya kyakkyawa ta
shiga yawon bariki. Ba ta ko lura da abin da suke ba, sai ta
wuce kai tsaye gurin mai saukar baki na otal din, yana
zaune a wani dan karamin daki, wanda aka kirkire shi a
tsakiyar wani dakin, ta hanyar yin amfani da
bangon gilashi, mai saukar bakin ya karbe ta, tare da
faffadan murmushi, manya-manyan farare hakoransa
suka bayyana a fili kamar jerin luwadu. Saurayin bai yi
aune ba yana karatun mujallarsa sai ya ji kamshin turare
ya bugi hancinsa, ya dago kai lokaci guda da sauran
mutanen dake otal din,
kamar dai sauran shi ma ya yaba da kyawun
Surayya, fiye da kowa kuma dake gurin, tsigar
jikinsa ta yi yar!!! Shi kansa sai da abin ya razana shi, ya
kuma ba shi mamaki, domin karo na farko tun lokacin da
ya fara yawon duniya sai yau ne ya hadu da macen da ya
ji kaunarta ta mamaye masa zuciya. A da can wani
zamani da ya wuce bai san menene so ba, sau da yawa ya
kan yi dariya ga wadanda ya ji suna cewa, wai ina son
wane, ko ina son wance Hakika yau ya gane kuskurensa.
Kallo daya ya yi wa Surayya, ya tabbatar masa da cewa
yar bariki ce, irin suturar da tasa, da kuma yadda
take tafiya, kanta a dage fuskarta a hade, shi ya
tabbatar masa da hakan.
Tunanin farko da ya fara fadowa zuciyarsa shi ne "Shin
Surayya za ta dace da aikinsu kuwa?" Shin zai iya yarda da
ita kuwa? Ya sake tambayar kansa, bai
sami amsar tambayar sa ba, sai ga Surayya ta sake fitowa
daga cikin dakunan otal din. A wannan karon ba shi ba,
hatta mai saukar baki, sai da ya nuna alamar rikicewa da
irin kyawun Surayya. Tana sanye da bakar riga ta siliki
wacce ta kama jikinta tsam-tsam, zanen rigar shi ma irin
silikin rigar ne,
kusan iya gwiwa ta daura shi, kanta babu
dankwali, sai gashin kanta ke kyalli kamar madubi,
kafarta sanye cikin takalmi baki mai gashin robar,
sarkokin da Grace matar malam Jackson ta bata su
suka kara fito da kwalliyarta, fuskarta a boye a bayan
bakin tabarau, babu alamar murmushi a
fuskarta, ta tsaya kerere tana duban mutanen da ke
farfajiyar otal din daida, a daidai lokacin ne saurayin ya yi
karfin hali ya daga mata hannu, ta dube shi a yatsine
sannan ta dauke kai, daga karshe sai ya ninke mujallar da
yake karantawa, sannan ya nufo inda take tsaye. "Dake fa
nake yan mata."
"Jin ka nake dan samari." Ta ce da shi
"Ya kamata mu sami guri mu zauna, ko kuwa me ki ka
gani yan mata?" Ya tambaya.
"Haka ne fa dan samari." A karo na farko, sai tausasan
lebbanta suka fadada izuwa murmushi, saurayin ya yi
kokarin ganin kwayar idonta ta cikin bakin tabaran,
amma maimakon haka, sai ya yi nasarar hango hoton
mummunar fuskarsa, ta cikin tabaranta.
Sun yi kimanin mintuna arba'in suna hirarsu, irin ta yan
bariki, hirar da duk mai mutunci ba zai so ya ji irin ta ba,
duk da yake kuwa Surayya na yin ta ne kawai don ganin
ta ribta shi ya yarda da ita, duk abin da ake Surayya na da
masaniyar cewa, zaman da saurayin nan yake zama ne na
zaben yarinyar da za ta fitar da hodar Iblis din uban
gidansa Rayyanu. Surayya ta yi mutukar sakin jikinta
wanda daga karshe saurayin ya fara tunanin ko ita ma
wai
ta fara kaunarsa ne.
.
"Mene ne aikinka?" ta tambaye shi.
Saurayin ya yi dariya, duk da yake kuwa dariyar na iya
firgita kananan yara, "Aikina yan mata ki ke son ki sani?"
Surayya ta gyada kanta.
"Aikina shi ne CI A SAUKAKE."
Surayya ta yi dariya "Ashe dai hanyar mu guda dan
samari, ni ma abin da ya fito da ni kenan yawon duniya,
yau shekarata biyu kenan, amma har yanzu ba bayani,
ban sami abin bukata ba,
"Mene ne abin bukatarki yan mata?"
"Kudin gaggawa." ta ce da shi cikin murmushin
yaudara. Saurayin ya yi jim, zuciyarsa ta kasa yanke
shawara kwakkwara, shin zai iya amince mata kuwa?
Sannan ya dubeta cikin zargi ya ce, "Da za ki iya
wani aiki da kin sami abin bukatarki kudin
gaggawa amma da hadari fa. Idan kuma na fada miki
aikin babu zancen janyewa dole ne sai kin yi ko kuma..."
Surayya ta yi murmushi, ta ce "Na fahimta ba sai ka fada
ba, na gane ka san fa ba yau na fara bariki ba."
"Da kyau yanmata, ashe kina ganewa."
Sannan ne ya saki jiki ya fara labarta mata, abin da za ta
yi.
.
********** ******** *********
.
A dakin Surayya wanda ke Almanda Otal aka
shirya taron, tuni samarin sun hallara, Rayyanu
kawai ake jira, wanda kuma shi ne zai zo da hodar Iblis
din, samarin biyu suna zaune a cikin biyu daga cikin
kujerun dake dakin, dukkansu suna shan taba,
kowannensu ya boye mummunar fuskarsa a bakin
tabarau. Ko kadan yanzu Surayya ba tajin tsoronsu,
ramuwar gayyar da ke zuciyarta su suka kashe
duk wani tsoro, zuciyarta a bushe take kamar
dutsen da ke tsakiyar sahara. "Yau ne zan fara
ganin cikar burina" ta ce cikin zuciyarta.
Kwana biyu kenan tun haduwarsu da saurayin nan,
"Sakaran banza." Ta ce a cikin zuciyarta, ta yi mamakin
ganin yadda ya fada cikin tarkon da ta kulla masa haka da
gaggawa, kamar wasa sai saurayin nan ya zayyane mata
bukatarsa a fili, "Ina tsoron fa kar a kama ni" Surayya
kenan ke fadi lokacin da take kokarin kara rifta shi a rami
gaɓa dubu.
"Babu mai kama ki..." Ya ce da ita, "...in dai kin yi yadda
na sanar da ke, to babu abin da zai faru. Kedai kawai ki yi
kokarin ganin kin yaudari mai binciken kome ya nema a
gunki kar ki ki yarda ki hana shi, abin da nake son ki gane
shi ne yadda kike da kyawun halittar nan ba dukkan ɗa
namiji ne zai ganki ya kyale ba, to balle kuma lalataccen
mutum irinsa." Saura kadan dariya ta kubucewa Surayya
"Yau ga lalatacce yana cewa kuma wani wai lalatacce.
"Duk ranar da za a yi tafiyar sai ya sami yarinyar da zai
tafi da ita, kin gane ko?" Ya ci gaba da cewa, "Su kansu
matuka jirgin ruwan sun san da haka, kin ga kuwa kina
cusa kanki zai yarda da ke, idan kuwa ya amince miki to
babu bincike a kanki domin tare za ku shige jirgin, ke bari
ma na fada miki, ba za ku
shiga jirgin ba sai bayan an gama duk bincike- binciken
da za'a yi, kuma shi mutumin da nake baki labari shi ne
babban jami'in tsaro mai bincike na gabar kogin garin
nan, kuma duk lokacin da babban jirgi ya zo, da shi yake
tafiya, saboda idan za'a sauke kayan ma sai ya sake
bincike na musamman, ina fatan kin gane manufata? Ya
tambaya, Surayya ta gyada kai,
"Saboda haka jibi za mu zo da komai da komai nan otal
din, zamu zo tare da babban Ubangidanmu, shine kuma
zai zo da hodar Iblis din, saura kuma dame? Za mu same
ki a can kasar masar din idan kun sauka, mu zamu bi ta
jirgin sama, kina isa zamu hadu da ke a can." Duk
wannan tunanin ta na yin sa ne lokacin da
take tsaye a bakin tagar dakin tana leke, awa biyu kenan
suna jiran Rayyanu, har yanzu bai zo ba.
.
"Yau Rayyanu zai yi kaduwar da bai taba yi ba a
rayuwarsa..." ta ce cikin zuciyarta.
Tunaninta ya katse a daidai lokacin da hancin wata
zungureriyar mota ya danno kai cikin otal din, kofar
motar ta bude Rayyanu ya fito dauke da bakar jaka, mai
dishi-dishin fari, bata tatsaya bata lokaci ba, sai ta juyo ta
ce da samarin da suke zaune "Ina zuwa." Sai kawai ta
shige bandakin dake fuskantar dakin, babu wanda ke da
masaniyar abin da ta shiga yi, dukkan samarin kuma
babu wanda ya san da zuwan Rayyanu, kofar dakin ta
bude a hankali, Rayyanu ya shigo dakin kamar fatalwa, ba
su san ya shigo dakin ba sai da ya yi gyaran murya
sannan ne suka yi firgit.
"Sannu da Zuwa" Suka ce da shi, bai amsa ba, yana tsaye
ne a tsakiyar dakin idonsa akan kofar bandakin, yana
dube-dube, kamar kullum
hannunsa na hagun a cikin aljihun kwat dinsa,
hannunsa kuma na dama rike da kyakkyawar
akwatin nan, babu yadda za'a yi idan ba an gaya maka ba
ka yi imani da cewa miliyan arba'in ne a ciki, kamar
sauran shi ma Rayyanu idonsa a boye a cikin bakin
tabaron, sai dai nasa daga samansa an rubuta "Colombo"
Zungureren karan sigari a bakinsa hayaki na fita ta hanci,
gwani ne wajen iya shan taba, bai ko damu da zaro
hannunsa daga aljihun ba, don rike sigarin, har yanzu
yana duba cikin zargi da rashin yarda, duk da yake
samarin na da taurin zuciya, sai da zuciyarsu ta yi laushi
tubus, tsoro kuma ya kama su, domin sun san idan ran
Rayyanu ya baci, yafi kumurcin maciji hadari.
Rayyanu ya yi taku biyu gaba sannan ya juyo bayansa na
fuskantar bandakin, ya fuskanci
samarin a lokaci guda kuma ya zuke sigarin dake bakinsa
ya fitar da hayakin ta hanci daya, sannan ya saki sigarin ta
fado, ya sa kafa ya take ta,
"Ina yarinyar take?" Ya tambayi samarin cikin
kakkausar murya. Kafin su amsa, sai muryar Surayya ta
ratsa sararin dakin, yadda sassanyar iska ke ratsa jiki,
"Gani nan!" Rayyanu ya juya firgigit, sannan ya yi
mutuwar tsaye, Surayya na tsaye a bakin dakin, hancin
yar karamar bindigar da Grace ta ba ta na barazanar
sakin harsashi zuwa cikin Rayyanu, gaba daya samarin
sun yi mutuwar tsaye babu mai motsi.
Da ka gansu sai ka dauka gumaka ne, bakin tabaran dake
idon Rayyanu ya fado kasa kar, sukayi ido hudu da
Surayya, babu alamar tausayi ko imani a fuskarta, wani
abu ya taho ya tokare makogwaron Rayyanu saboda
kaduwa da tsoro, da kyar yake numfashi, tunda yake bai
taba ganin fatalwa ba sai yau, sai dai kuma fatalwarsa ta fi
ta kowa haɗari. "Fatalwa da bindiga! Dana san za ta yi
fatalwa da ban kashe ta ba.
.
"Kada ka yi tsammanin fatalwa ka ke gani" Muryarta ta
sake ratsa shirun dake dakin, kada kuma ka yi tsammanin
ba zan harbe ka ba, daidai nake da na harbe ku ku duka,
ka san an ce rama cuta ga macuci ibada ce, ina son jakar
da ke hannunka. Rabin minti na baka ka yanke shawara
da ranka da Naira miliyan arba'in wanne ka fi so? Sannan
ta kalle shi ta yi dariya, "Kowa ya kwana lafiya shi ya so
Rayyanu, amma kai ba ka so zaman lafiya ba, arzikin da
kake tunanin za ka yi ba za ka yi shi ba, sai kuma na ga
karshen ka."
Dakin ya yi tsit ba ka jin komai sai bugun zuciyar su
Rayyanu, "Ki yi hakuri"
"Hakuri?" ta kyalkyale da dariya " Ashe taurin
kanku na banza ne dan samari, ka tuna lokacin da kake
duka na, ko hakuri ban baka ba fa, amma kai gashi har ka
karaya!" Ta ba da baya kunamar bindigar ta yi kara kur,
sannan ta ce da samarin da suke zaune, kamar gumaka,
"Ku ce da shi ya aje akwatin a kasa, idan kuma ba haka
ba, to ta kanku zan fara sai kun fara mutuwa kafin shi"
Jikin samarin ya dauki rawa, dogon cikinsu ya ce da
Rayyanu "Aje mata Rayyanu in har kana son mu tsira da
ranmu"
"Me kake nufi kenan?" Rayyanu ya tambaye shi.
"Abin da nake nufi shi ne idan baka aje ba za mu hadu
mu karya wuyanka muba ta jakar, domin mu rayuwar
mu tafi kudi, ina amfanin badi babu rai"
"Ka fadi gaskiya abokina" daya saurayin ya ce.
Surayya na jin su ba ta ce komai ba, har yanzu
bindigar na saitin kirjin Rayyanu.
Rayyanu ya dubi samarin, sai ya ga idan har bai
bada jakar ba, to ba abin da zai hana su kashe shi su ba ta
jakar.
"Yanzu muna ji muna gani naira miliyan arba'in zatabi
ruwa?"
"To mene ne?" daya saurayin ya ce "Gara rayuwar mu da
duk arzikin duniyar nan,
"Lokacin ka ya cika Rayyanu" muryar Surayya ce mai
dauke da tsananin barazana ta sake ratsa dakin. Rayyanu
ya saki jakar ta fado a kasa tim, sannan ya juya ya kalli
samarin a fusace, ya ce "Banzaye matsorata, yanzu kuna
nufin ku ce min mun yi sallama da kudin kenan.
Miliyan Arba'in! Miliyar Arba'in!! Miliyan Arba'in!!
Sannan ya kwalla kara yafadi a tsakar dakin, miliyan
arba'in.
"TA LEƘO TA KOMA" Muna ji muna gani"
Surayya ta matso da sauri kusa da inda ya fadi ta daki
kansa da gindin bindigar dake hannunta nan take ya
sume, samarin suka motsa da niyyar su rufo mata, kafin
su tashi tuni ta ja da baya ta sake rufe su da hancin
bindigar, "Kada ku zolayi kanku, domin kuwa daidai nake
da na hallaka ku gaba daya, ku shiga bandaki ku rufe
kanku!" ta buga
musu tsawa gaba dayansu, kowannen su
hannayensa a sama suka shige bandakin. Surayya ta yi
sauri ta kulle su a ciki ta zare kubar mintuna kadan da
faruwar haka, sai ga ta a cikin jirgin ruwa, ta nufi gidan
Malam Jackson, gudun hijira kenan koda jirgin ya harba a
cikin ruwa sai Surayya ta yi
murmushi.
"BAZAN AURI KARUWA BA"
Ta Tuna kalaman Haidar.
.
********* ********* **********
.
"Karya kake munafukin banza, kai ma wato yanzu ka koyi
munafurci ko?
Tunda muke da kai Rayyanu na taba zaluntarka? Tab! Ai
wannan zancen banza ne ka ce min wai mace ta kwace
maka abin da zai kai darajar miliyan arba'in, mace fa ka
ce, kai Rayyanu hankalinka kuwa daya kake fada min
wannan zancen banzan?"
ALHAJI D. BANASARE ya yi shiru yana kallon
Rayyanu cikin takaici fuskar Rayyanu kamar
madubin da aka kwarawa ruwa sai kyalli takeyi. Ta jike
sharkaf da gumi. "Alhaji Wallahi ba laifina ba ne, na fada
ma ritsa mu ta yi da bindiga, ta doke ni akai, ta kulle
kuma
yarana a bandaki, ka san kuma idan har ban bata ba
kashe ni za ta yi. Yanzu Alhaji duk iya zaman da muka yi
da kai na tsawon shekaru muna wannan sana'a ba ka
yarda da ni ba? Ka tuna fa irin hadarin da na sha jefa
kaina wajen ganin hodar iblis dinka ta samu shiga."
Rayyanu ya yi shiru na dan lokaci, sannan ya ce "Na yi
mamakin ganin cewa kafi damuwa da kudi fiye da ni, duk
da yake kuwa duk son kudin ka baka samunsu sai da
taimakona, ai kamata ya yi tunda ka yi wa kudi mugun
sabo, to ka fitar da hodar iblis din da kanka, kuma kai
kanka ka san baka da wanda ya fi ni. Kai na daina rokonka
da ka yi hakuri, idan baka yarda da abin
da na fada ba, to kasa hukuma ta kama ni, a
matsayin wanda ya sace maka hodar iblis"
Rayyanu ya yi dariya ganin fuskar Alhaji D. Banasare ta
koma toka-toka.
"Ya isa haka." Alhaji Banasare ya ce da shi, "Da na dauka
da gaske maganarka haka take, duk fadan da nake yi ina
yin sane domin kada ka sake yarda a yaudareka nan gaba,
amma maganar da ka yi yanzun nan ita ta tabbatar min
karya kake, wato kai dabararka ita ce idan ka rike hodar
iblis din bani da ikon yin komai, saboda kana ganin a
matsayina na mai aikata babban laifi ba zan tunkari
HUKUMA BA.
"Ka yi kuskure Rayyanu, wannan kuma ya nuna
min kai karamin dan fasa-kwaurin miyagun
kwayoyi ne, tunda baka san alakar dake
tsakaninmu da jami'an tsaro ba" Alhaji Banasare yace.
"Amma kada ka manta na yi alkawari duk inda hodar Iblis
dina take sai ta dawo, za'a dauki lokaci babu mamaki
mako guda, wata daya, ko ma shekara amma na san za ta
dawo.
"Sau da yawa Rayyan, mutane irinka masu hadama sun
sha cuta ta, ta hanya dabam-dan suna ganin kamar za su
tsira, to hakika sun ga kuskurensu daga karshe. Duk
wanda ya cuce ni dole ne na rama, babu wanda ya taba
cuta ta, ya kai labari, yau shekara arba'in da tara 49
kenan ina safarar miyagu kwayoyi. Kasancewa tun kafin a
haifeka kenan, ban taba samun wanda ya kawo mun
karyar rainun hankali kamarka ba" Alhaji Banasare ya yi
shiru yana kallon Rayyanu, ko ido baya kiftawa, sannan
ya ci gaba da cewa "Yau da ace yarinyar nan da ta ritsa ku
da bindiga ba bahaushiya bace zan iya kusan yarda,
amma bahaushiya fa, zai yi wuya na yarda, na San al'adar
matan turawa ce rike
bindiga tare da sauran matan wasu kabilun Nigeria,
amma matan mu sun cika tsoro, bindigar ma ba sa son
gani fa, amma sai ga shi kana kokarin shayar da ni karyar
wai yarinyar yar bahaushe ce ta ritsa ku, ku uku da
bindiga ta kwace muku abin da zai kai darajar naira
milyan arba'in, haba Rayyanu, yanzu kana nufin kace min
famfamfam kenan da milyan arba'in, yau shekara goma
sha daya kenan ina shirin samun wannan hodar iblis ɗin
baka san irin wahalar dana sha ba, wajen samunta, tun
da na
ke ban taba samun mai yawanta ba, sai ga shi cikin sa'a
guda ka salwantar min da ita? Lallai a gaishe ka ɗan
samari. Kana nufin ka ce min
"TA LEƘO TA KOMA" kenan?
Zai yi wuya dan samari. Dole ne sai hodar iblis dina ta
dawo, duk tsiyarka" Sannan YA daga Dan yatsansa yana
nuna goshin Rayyanu yace, "Ba kuma za ka kai labari ba,
kamar sauran na
can, kuma zan shawarce ka, abin nufi shi ne ka sayi
likkafani dan samari babu mamaki kwanakinka aduniya
ba su fi haka ba.." ya daga yan yatsu biyar a fuskar
Rayyanu, "Tashi fice munafuki!" ya buga masa tsawa mai
kama da aradu.
.
*********** ********* ************
.
In ka dauke Alhaji Banasare dake sanye da farare kaya
riga da wando na shadda duk dakin kowa sanye yake da
bakaken kaya, su goma sha biyu ne banda Alhaji
Banasare. Kujerun dakin kowacce na dauke da mai bakin
kaya da gashin baki guda daya, dakin kamar majalisar
dinkin duniya, ba don masu damara sun yi yawa ba.
Za ka yi mamaki idan aka ce ma wannan taron anyi shine
akan yadda za'a nemo hodar iblis din da Rayyanu ya
salwantar. Abin mamakin da ya fi kowanne kuma shi ne
yau ga masu hanawa ayi za kuma su yi, babban jagorar
tawagar shi ne mataikakin kwamishinan yansanda
M.K. AGANANI MU-SHA-GARA wanda ke
zaune kusa da Alhaji Banasare, yana zazzare idanu,
dankareran mutum ne, mai kwarjinin gaske yanada fadin
kirji, kansa mai kama da kankana na dauke da kananan
idanu irin na maciji, gashin bakinsa wanda sai ya turar da
shi gefe guda yake samun damar shan iska, shi zaka fara
gani idan ka hango shi daga nesa, sau da yawa mutane su
kan tuna da zamanin su Lamarudu, aduk lokacin da suka
dubi gashin bakin M.K Aganani Mu-sha-gara, dogo ne na
innanaha, idan ya fara mikewa tsaye
sai ka fara tunanin kamar ba zai kare ba, akwai jita-jita
dake cewa shi ne ma'aikacin dansanda da ya fi kowa tsayi
da ban tsoro. Idonsa kamar gauta yana da faffadan hanci,
mai kama da usir, abin mamaki kyeyarsa ce kadai ke da
gashi, amma idan ka dawo sauran bangaren kansa kamar
kwai yana kyalli kamar bakin kuturun tawada.
.
M.K. Aganani Musha-gara ya dade yana cin amanar
gwamnati da kuma kungiyar yansanda, amma a boye, ba
kuma sanin kwamishinan yan sanda na Banasariyya. In ka
dauke shi kansa tare da mutane goma sha daya da ke
goya masu baya, wadanda su ma yake lasa musu zuma, a
duk lokacin da aka dace, babu wanda ya san aika-aikar da
yake aikatawa. Babu wanda ya san takamaiman yarensa.
Wasu sun ce gara ne. Wasu sun ce Bakatafe ne. Allah ne
dai masani. Yau shekaru ashirin da tara yana taimakawa
Alhaji Banasare wajen safarar miyagun kwayoyinsa, ko da
yake ko ba'a fada ba, kasan cewa ba karamar zuma ake
lasa masa ba Albashin da Alhaji Banasare yake biyan sa,
ya rubanya wanda yake samu a
gurin aikinsa sau shida da wani abu. Karatun
yaransa zuwa kasar waje da kuma kayan abinci irin na
alatu dake kwarara a gidansa duk wata Alhaji Banasare ne
ke daukan nauyin.
Kamar yarda aka saba yau ma sai ga shi an taru a babban
falon Alhaji D. Banasare, ana tattaunawa.
.
"Kana nufin ka ce min yaron ne ya yi sama da fadin
KOKEN din ne?" Aganani ya tambaya cikin muryar da za
ka iya kira ta jami'in tsaro mai aiki tukuru. "Kwarai kuwa"
Banasare ya ce "Ka ji fa zancen nan wai mace bahaushiya
ta ritsa maza karti guda uku ta kwace abu a hannunsu, zai
yi wuya Aganani.
Abin da nake so da kai shi ne ku tattausa min Yaron nan
sai ya yi Aman gaskiya. Ba sai na bata lokaci ba wajen
fada ma abin da ya dace ku yi, amma ina so daga karshe
ku zo min da labarin inda ya boye hodar iblis din......
.
Aganani ya daga kai ya dube shi, sannan ya ce.
"An gama"
A zahiri Aganani Mu-sha-gara samsam bai ji ko
rabin abin da Alhaji Banasare ke fadi ba, abin da
kawai ya ji sosai shi ne wani yaro ya salwantar
masa da koken din naira milyan arba'in.
.
"To da na bar aikin dansanda kenan, wannan damar ba za
ta wuce ni ba!" Ya ce cikin zuciyarsa. "A yi niyya!!!
Ya buga wa yansanda tsawa. Suka mike duka lokaci
guda suna rawar jiki kamar sun ga mala'ikan
mutuwa. Aganani ya mike daga kan kujera gaba
daya yan sandan sai suka zama kamar mota agaban jirgi,
tsakanin kansa da silin din rufin ɗakin bai kai kamun tafin
hannu ba. Sannan ya dubi Alhaji
Banasare ya buda baki zai ce bai sani ba, su nema
da kansu, sai talfon din ya dau kara, Banasare ya yi
sauri ya dauka yansandan na kallon sa.
.
"Wa ke magana?" Ya tambaya. "Saurara da kyau!" Aka ce
da shi, "Da ni ne kai to
da sai na nemi Rayyanu a sariyana Otal idan kuma
ba ka gaggauta ba, ka yi sallama da hodar iblis
dinka kenan."
.
"Wace ce ke magana? Mene ne sunanki?" Alhaji
Banasare ya tambaya bakinsa na rawa "Sunana kake son
ka ji? Ban sani ba." Aka ce da shi, a lokaci
guda kuma wayar telfon din ta katse.
.
********** ********* **********
.
Surayya ta yi murmushi, sannan ta aje kan talfon
din, ta duba agogonta, karfe shida da rabi na
yamma agogon ya nuna "Bari na basu mintuna biyar." ta
ce cikin zuciyarta, "na san kafin nan sun
kusan isa Otal din. Ba'a dade ba sai ta sake daukar
talfon din, ta sake buga daya daga cikin jerin
lambobin da ta samu a gurin wani ma'aikacin
"NITEL"
A can daya bangaren Rayyanu ya dubi agogon dake
manne a jikin bangon dakinsa dake Sariyana
Otal karfe shida da mintuna talatin da shida. Ya kai
kimanin sa'o'i uku kenan yana zaune, yana ta
zulumin saɓanin da ya shiga tsakaninsa da
Ubangidansa Alhaji Banasare. Zuciyarsa kuma cike
da tunanin abin da Surayya ta jefa shi a ciki, "Haka
Surayya ta yi min?" Ya ce cikin raɗa "Sai na nuna
mata iyakarta, daga yau ta sake yi wa wani. Duk
ran da na kama ta sai na karya wuyanta." Ya ce
cikin fushi, "Sai dai kuma ina zan fara nemanta
yanzu, a ina take? Ya tambayi kansa kamar amsar
tambayarsa, sai talfon dinsa ta dau kara, da farko da ba
zai dauka ba domin ya dauka

Please Login or Register in order to submit comment