Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta dauke tunanin daga
zuciyarta, sannan ta sanya tunanin wani abu
daban a gurbin wannan tunanin da ta tsana.
Amma duk a banza ba ta iya tsawon minti daya
sai tunanin ya darsu a zuciyarta. Abin kuma
takaici duk lokacin da tunanin ya darsu a
zuciyarta sai ta ji kamar ruwan batir ko
narkakkiyar dalma aka diga mata a tsakiyar
zuciyarta.
Surayya monika ta yunkura a hankali, a daidai
lokacin da agogon bangon dakin ya ke nuni da
sha biyu da rabi. Ta zauna a kan gadon bayanta
jingine da bangon dakin.
Baka jin motsin komai, sai kukan namun ruwa,
tsuntsaye da kuma gugin da ke gudana a cikin
kogon kwara.
"Mene ne amfanin rayuwarta." Ta tambayi kanta.
Ta bar gidan mahaifanta saboda kwadayin abin
duniya, wanda ba shi da tabbas, gashi kuma daga
karshe, ba tasami ribar komai ba sai bakin ciki
kala-kala, masu tafasa zuciya da ramar da
gangar jiki
"kaicona." Ta ce cikin zuciyarta. A da can wani
lokaci da ya wuce, ta dauka babu abin da ya fi
rayuwar bariki dadi domin a tunaninta matar da
ke zaman aure kamar ta rako yan uwanta mata
duniya ne, sai yanzu ne ta gane kuskurenta
yanzu kam ta san darajar kowacce diya mace shi
ne gidan mijinta. "Yanzu da a gidan mijina na ke
haka zata faru a kaina?" Ta tambayi kanta.
Sannan tunanin kawarta Sa'adiyya ya fado mata
a rai. Ita kanta abin yabata mamaki da ta ga
tunane-tunanen gidan suna ta giftawa cikin
zuciyarta. Kamar hoton majigi. "Shin ko
Sa'adiyya yanzu ta yi aure." Ta tambayi kanta
me yiyuwa yanzu ma ta sami da ko yaya.
Surayya ta ci gaba da duban bangon dakinta
tunane-tunane mara sa ma'ana suka yi ta
ninkaya cikin zuciyarta, Tunanin Rayyanu ya fado
mata, ya fi komai ciwo cikin zuciyarta, domin
kuwa ita ta yi sanadiyyar mutuwarsa, sai yanzu
ne take nadamar duk abubuwan da ta aikata, da
ta sani duk ba ta aikata hakan ba, abin da ya
kamata ta yi lokacin data warke daga raunin da
ta samu a kafa shi ne ta koma gidansu, ta yi
rayuwa irin ta mutane amma kaddara ta riga fata,
ba ta yi hakan ba gashi kuma yanzu abin ya
zame mata masifa.
Tunanin Haidar shi ya fi damun zuciyarta
ayammacin ranar, ba za ta iya daina tunanin ba a
dacan ta dauka ta tsane shi ba kuma za ta sake
kaunarsa ba, to amma yanzu ta fara fargabar har
yanzu son sa na nan cikin zuciyarta, sai dai kuma
can cikin zuciyar tata tunanin ramuwar gayya
shima na nan yana dada tafarfasa mata rai.
"Ba zan auri karuwa ba." Ta tuna irin kalaman da
Haidar ya sha yin amfani da su akanta, hawaye
ya kwararo kan kumatunta, hakika har yanzu tana
kaunarsa. "Ya ya zan yi da raina." Ta ce cikin
zuciyarta.
Bata san abin da ya sa ta yanke shawarar ba, ita
dai kawai taji wata zuciya na cewa da ita, "Ki
sulale ki koma garinku gurin iyayenki shi ya fi
miki, domin idan ki ka bari azzaluman nan suka
kama ki, to ke taki ta kare, ke kadai ba za ki iya
yi musu komai ba." Lokaci guda ta amince da
shawarar amma kafin nan fa. "Sai na sake ganin
kyakkyawar surarsa gobe" Kafin nan bar garin
nan" Ta ce cikin zuciyarta. Ba wani take nufi ba
daya wuce Haidar.
Sai bayan da duk ta gama shawarwarin sannan
ta tuna hodar iblis din, wacce kuma ta tabbata
saboda ita ake barazana ga lafiyarta. Sam-sam,
ta manta da zancenta, tunanin rayuwar da ta
gabata shi ya rufe tunanin hodar Iblis din, to
amma yanzu ta tuna da ita. Surayya ta yi shiru
tana tunanin abin da ya kamata ta yi da hodar
iblis din.Karfe daya saura kwata dabarar abin da za ta yi da hodar iblis din ta fado zuciyarta, hakan kuma da zata yi shi zai kawo karshen duk rigimar.
To daidai lokacin da wannan ke faruwa ne, yansandan hudu suka shiga da Haidar tangamemen falon Aganani Mu-sha-gara. Ba karamar razana ya yi ba lokacin da Haidar ya
fahimci Dakin a cike yake da masu bakaken kaya.
.
*********** *********** ***********
.
Abin da ya fi damun Haidar lokacin da ka durkusar da shi a gaban Aganani, shine jajayen idanunsa da
kuma murɗaɗɗen gashin bakinsa, bai taba zaton daidai da dakika daya akwai alamar imani akan
fuskar da yake duba ba.
"Ko kadan bani da tausayi Dan samari." Aganani Mu-sha-gara ya ce kamar wanda ke karanta zuciyar Haidar, idan har kana so mu rabu da kai lafiya to ka tabbatar ka yi abin da muka umarce ka, yin hakan shi zai tserar da rayuwarka da kuma ta
wasu mutum biyu da muke sa raida zuwansu kowanne lokaci daga yanzu.
"Su wanene." Haidar ya tambaya muryarsa na rawa.
"Za ka gansu nan ba da dadewa ba, ko da yake ba wani dadewa za su yi ba, amma domin kana ganin su zamu wuce da su kai tsaye zuwa gidan tuhumar mu, suda ka sake ganinsu, kuma sai ka cika mana umarninmu, idan kuwa ka gaza, to zan yayyanka
su a gabanka!!" Aganani ya ce da shi cikin daga murya. "Me ka...ka ke so na yi?" Haidar ya tambaya, yawun
bakinsa ya gama kafewa karaf, hantar cikinsa ta hade da hanjin sa don fargaba, kwakwalwarsa duk
ta rikice, bai gane duk abin da Aganani ke nufi ba.
.
Sai bayan karfe biyu da rabi daidai ne Haidar yafara fahimtar inda aka sa gaba, kofar falon ta bude sannan yan sanda uku suka shigo su da mutane biyu mace da namiji. Magidanta, ne sannan cikin
rudani da tashin hankali marar misaltuwa Haidar ya fahimci ko su wanene, bai taba gaskata hakan ba
sai da mahaifiyarsa ta kira sunansa. Mahaifinsa na tsaye fuskarsa a hade bai ce komai ba. "Ina fatan ka gane su." Aganani ya ce yana dariyar
mugunta.
Ba su bar Haidar ya amsa ba, cikin bin tsari da umarnin Aganani Mu-sha-gara, sai suka angiza
keyar mahaifan nasa suka sake fita da su.
"Kada ka damu, gidan tuhuma za mu ajiye su, babu kuma abin da zan sa ayi musu in har ka bi umarninmu. Saboda haka abin da nake so da kai
shine belin mahaifanka na hannunka.
Haidar ya yi shiru yana sauraron jawabin Aganani, akan Surayya.
"Yallabai Wallahi rabona da ita ya fi wata uku." "Kada ka yaudari kanka dan samari, mun san masoyiyar ka ce, kuma duk inda ta ke ka fi mu sani,
abin da nake so da kai, shine za mu sake ka gobe da safe, ka tafi duk inda take ka nemo mana ita, abin kawai da muke so shine, ka yaudareta ka kawo ta gidanku, mutanen mu suna nan suna jira. Bayan mun sake ka gobe da safe, za mu baka, sa'o'i biyu kafin mu tura yaranmu su yi jiran zuwanku.
"Yallabai ban san inda zan fara nemanta da na ce..."
Aganani ya katse shi, tsawar da ya bugawa Haidar saida ta sa hanjin cikinsa ya murda. "Ban damu da inda za ka nemo ta ba, duk inda za
ka shiga ka shiga ka nemota bana son zancen banza, kwana uku kacal nabaka, daga nan babu kari" Sannan ya dada da cewa "Idan har baka
samota ba, to sai ka taho da likkafanin iyayenka a matsayin GUDUNMAWA" Amsa kuwwar ta ratsa tangamemen falon.
.
************* ******** ************
.
Karfe shida saura yan mintuna Haidar ya isa unguwar. Babu mutane sosai a kan tituna kasancewar safiya ce, ya yi kuma sai bai hadu da
koda mutum guda da ya sani ba ballantana a dame shi da yan kananan tambayoyi. Cikin sauri ya shige cikin gida, wanda a bude ya kwana. Bakin ciki ya lillibe zuciyarsa lokacin da ya lura cewa duk dakunan barcinsu a bubbude su ke. Shi kansa bai san abin da ya dawo da shi gidan ba.
Abin da ya kamata ya yi shi ne daga gidan Aganani ya wuce kai tsaye neman Surayya. To amma
tambayar da ta ci gaba da sintiri cikin zuciyarsa shine, ina zai fara tafiya neman Surayya babu mamaki
rashin sanin amsar wannan tambaya shi ya dawo da shi gida.
Haidar ya ci gaba da safa da marwa zuciyarsa na tafarfasa hakika ya shiga masifa, domin abin da zai
nemo a bashi belin iyayensa, kamar neman kahon jaki ne, domin ba zai taba samu ba, gashi kuma Aganani ya ce da shi kwana uku kawai yabashi, abin da kuma ya fi damunsa, shi ne babu wanda zai
kai kukansa gurinsa, domin Aganani ya ce da shi idan har ya sake ya fadawa wani abin da ake ciki
ya yi sallama kenan da iyayensa.
.
Wani dan makararren motsi shi ya tsaida Haidar cak, sannan ya tsai da tunaninsa, ya juya a hankali
yana kallon kofar shigowa gidan. A hankali cikin fargaba ko yansanda ne suka biyo shi, sai ya nufi kofar da farko da ya dauka iska ce ke turo kofar gidan. A tsorace ya leka kofar gidan domin ganin kowanene.
Bai taba zato ba ko a mafarki, bai kuma taba tunanin ko tsammanin ganinta ba. Da farko bai
ganeta ba, har saida ta dan yi murmushi. Ba shakka wannan bashi ne karo na farko daya taba ganin
murmushin ba, ko shakka kuwa ba ya yi ya san mutum daya ne me irin wannan murmushin ita ce
SURAYYA MONIKA.
Tana tsaye tana kallonsa. Sanye take da doguwar riga JA mai shara-shara, sai dai bata fito da surar jikinta ba, kanta lillibe yake da farin Gyale Yaran biyu suka dubi juna na dan lokaci, kamar yadda suka saba awani lokaci da can da yawuce, sai dai wannan kallon babu wanda ya tsani
wani a tsakaninsu, kowa na bege da farin cikin ganin abin sonsa.
Surayya ta bude baki za ta yi magana amma maganar ba ta sami fitowa ba. A ganinta Haidar ya kara kyau fiye da lokacin da ta fara ganinsa,
kirjinta ya ci gaba da bugawa, ba ta taba tsammanin har yanzu tana son sa haka ba.
"Su...Surayya." Haidar ne ya fara kiran sunanta. A yadda ta ji muryar Haidar sai ta ji kamar sarewa ake hura mata a kunnen.
"Haidar." Ita ma ta kira sunansa, sannan cikin kunya sai ta sauke fuskarta ta daina kallonsa,
Haidar ya matso kusa da ita sannan ya ce,
"Surayya na dade ina begen ganin ki."
Ta daga kai cikin mamaki, bata taba zaton Haidar zai taba kaunarta ba, amma abin mamaki sai gashi yanzu yana cewa wai yana kaunar ganinta. Ta dube shi sannan ta ce.
"Ganina fa ka ce Haidar." "Abin da na ke nufi kenan." Ya amsa sannan ya dauke kansa gefe guda.
"Surayya na san ba za ki sake kaunata ba na san kin tsaneni, saboda wulakancin da na yi miki,
amma wallahi Surayya tun bayan rabuwarmu na tsinci kaina cikin..."
Ya yi shiru yana dubanta bai iya karasa maganar ba.
Surayya ta matsa a hankali sannan ta dafa kafadarsa ta ce da shi.
"Ban tsane ka ba Haidar, kai ne ka tsaneni, nasan kuma da wahala ka kaunace ni abinda kawai daman ya kawo ni shine, na yi maka kallon
karshe domin yau zan bar garin nan.
Tun sa'ar da ya yi ido hudu da Surayya ya gama shagaltar da shi sam-sam ya manta da halin da
yake ciki jin cewa yau zata bar garin shi ya dawo masa da mummunan tunanin abubuwan da suka faru a daren jiya. Nan da nan kamanninsa suka juya, gumi ya lillubeshi, kamar ruwa.
"Menene kuma na ga duk..."
Haidar ya yi sauri ya rufe bakinta.
Surayya ta yi shiru tana sauraron sautin in jin mota. Ta kofar gidan motar ke wucewa, Haidar
ya yi sauri ya janyo hannunta ya ce "Shigo daga ciki." Abin da ta ji a muryarsa, shi ya hana ta musu ko tambaya, Haidar ya leka kofar gidan ahankali. Bakar motar fijo (505) ce ke tafiya kamar ana turata, ta mike can karshen layin sannan ta
karkata ta bi barin hannun hagu. Haidar ya tabbata ba tafiya suka yi ba za su dawo.
"Su wanene?" Surayya ta tambaya a razane.
Haidar ya dube ta babu damar boye mata dole ne ya sanar da ita
"Yansanda ne Surayya."
Ta dube shi ta ce "Wa suke nema?"
Haidar ya girgiza kai ya ce da ita "Zo mu shiga ciki."
"Ina su Momi ba sa nan ne?" Haidar ya girgiza kai cikin takaici, "Ba sa nan Surayya." Ta dubeshi alamun tambaya karara su ke a fuskarta. "Ina
suka tafi, Haidar?"
"Inda babu wanda ya isa ya dawo da su sai ke."
"Me ka ke nufi?" Ta tambaye shi arude.
"Wannan yansandan ke suke nema, idonki idonsu, kama ki za su yi." Sannan ya dada da cewa
muryarsa na rawa.
"Surayya wallahi muna cikin masifa, labarin na da tsayi abin kawai da nake son ki sani shi ne, ke ake so na nemo, idan an kama ki a saki iyayena,
idan kuma ban nemo ki ba, to ni da iyayena munyi sallama kenan.
"YANKA SU... ZA A YI!"
.
************** ********* **********
.
Sai da suka share kusan mintuna hudu, babu wanda ya sake cewa komai, sannan a hankali sai
Surayya ta dago kanta ta dube shi ido da ido sannan ta ce da shi, cikin kakkausar murya, irin yadda ta fadi maganar saida ta sa hantar cikinsa
ta kada.
"Me ya sa ka tunanin zan kai kaina ga yansanda domi belin mahaifanka?" Ba ta ko damu da ta dauke fuskarta gefe guda ba yayin fadin
maganar.
Haidar ya dube ta cikin kaduwa, bakinsa na rawa, yace
"Surayya ba wai ina so ki kai kanki gare su ba ne domin a saki iyayena, abin da nake so shi ne mu
shawarta a tsakaninmu domin mu gano ko akwai hanyar fita."
"Babu wata hanyar fita Haidar, hanyar fita daya ce in dai har abin da ka fadi abin dogara ne, na kai kaina ga azzaluman shi ne mafita." Ta dan yi shiru tana dubansa, sannan ta ce da shi.
"Tambaya daya ce, mai wuyar amsawa Haidar shine zan iya kai kaina domin fansar mahaifanka?
Ka tuna fa Haidar babu wani abu tsakaninmu sai tsana, da kiyayya."
"Ba zan auri karuwa ba." Abin da ka ke cewa kenan, amma abin mamaki sai gashi kana kaunar ganin karuwa da ka ke ki da tsana ta kai kanta
ga yansanda domin ganin an saki mahaifanka.
Shin in tambayeka Haidar, idan aka yi haka, son kan bai yi yawa ba? Kiyayyarba tayi yawa ba?
Tsanar ba ta yi yawa ba? Haba Haidar ka san ai ba za ta sabu ba bindiga a ruwa." Ba abin da tafada ne ya sa shi kaduwa ba. Irin yanayin ko in
kula din da ke fuskarta shi ya fi sashi firgita fiye da kalamanta, Haidar ya dube ta cikin kunan rai,
bai kamata ta fada masa haka ba. Ya ce cikin zuciyarsa, amma da ya tuna irin wulakancin da ya yi mata a baya sai ya ga bata da laifi.
"Surayya duk wannan maganganu ba su taso ba, shawararki na ke nema, na san na yi miki laifi na wulakanta ki wani lokaci da can da ya wuce,
amma duk da haka ina son ki fahimci ab..."
Surayya ta katse shi. "Ko kusa kada ka yi zaton zan bada kai na domin ceton rayuwar wadanda
ba su san darajata baBabu irin zagin da ba ku yi min ba kai da mahaifiyarka, ta muzanta ni muzantawar da bazan taba mantawa da ita ba, ka tuna fa ni ma ina da iyaye kamarka ba daga sama aka jeho ni ba, so da kaunar da na ke yi maka gami da wulakacin da ka yi min su suka yi sanadiyyar duk wata masifa da muke ciki. To amma Daman ance in zaka gina ramin mugunta to gina shi gajere,
domin ba ka sani ba ko kai za ka tsunduma.
Haidar me ka fahimta yanzu kaga daga karshe duk masifar da na shiga saboda kai ta zo karshe, domin masifar da ka ke ciki kai da
wacce take kin nawa tafi wacce na shiga."
Ta yi shiru tana dubansa, hannunta rike da kugunta. Tunanin abubuwan da suka faru abaya
tun karshen haduwar su suka ci gaba da kai kawo tsakanin zuciyarta da kwakwalwarta.
Haidar bai tabbatar da irin kaunar da yake yi mata ba sai bayan da ya fahimci cewa ashe duk irin masifar kaunar da Surayya take yi masa
ayanzu ta bi iska. A haka ya tsaya gabanta sororo yana kallon ta zuciyarsa na kuna, ga
mahaifansa da shi kansa cikin halaka, sannan kuma ga wacce ya ke kauna a yanzu fiye da komai ta nuna masa kiyayya a zahiri, abin ya
bashi mamaki domin lokacin da ya ganta ya dauka begensa da ke cikin zuciyarta ne ya sata dawowa gareshi, hakika yasan yanzu ya yi
kuskure.
Suka hada ido da ido babu mai ko kiftawa.
Tunanin da yake na tafarfasa masu zuciya dole ne ya zabi daya ko dai ya rabu da mahaifansa
cikin halaka, ya zabi abar kaunarsa Surayya ya lallabetta, ko kuma tunaninsa ya katse na dan
lokaci. Abin kawai da zai yi shi ne ya fita waje ya kirawo yansandan da kansa, ya hada su da
Surayya domin duk wata kauna bayan ta uwa da uba suke bi. Kafin ya gama karasa tunanin ne
sassanyar murya mai kashe zuciyarsa da katse
tunaninsa da kuma karya duk wani kwarin gwiwarsa ta sake kwararowa zuwa cikin kunnensa.
"Haidar ban taba ganin abin da nake kauna da so kamar ka ba, na san ka sani har zuwa yanzu ina kaunarka, amma sai dai bakin alkalami ya
bushe domin ni kam na hakura da soyayya, saidai ciwon sonka ya kashe ni, amma hakuri kam na hakura." Sannan ta dada da cewa.
"Daman zuwa na yi domin na yi maka kallon karshe a matsayinka na wanda na fi kauna, sannan kuma wanda na fi wahala a kansa. Allah
ya hada fuskokinmu da alheri."
Kafin ya farga ta fice daga gidan. A haka ta barshi tsaye babu wata kwakkwarar shawara azuciyarsa. Ya taho a hankali cikin kaduwa
sannan ya leka kofar gidan, tana tafiya a hankali ya hango ta, sannan bangaren kudu take bi,
sabanin yansandan da suka yi arewa, Haidar ya tabbata yansandan da ke can kan kwanar ba za
su taba tsammanin ita ce ba, domin ba za su yi mata sanin da za su iya gane ta ba, ba tare da sun ga fuskar ta ba. Me yiyuwa ma su za ci
bakuwace ta zo gidan da ta ga babu kowa shine ta kama gabanta. Yana kallonta tana tafiya, babu ga tsuntsu babu ga tarko, shi bai mika ta
ga yansanda ba ballantana a sakar masa mahaifansa, sannan shi kuma bai sami cimma nasarar samun soyayyarta ba. Wani zazzafan
hawaye ya zubo masa, a kan kumatunsa bai damu da ya share hawayen ba sai ya ci gaba da
kallon ta, har ta bace, bacewar da ya ke tsammanin ta bace wa rayuwarsa kenan har abada, ya juya ahankali, bai damu da tunanin ko yansandan suna kallonsa ko ba sa kallonsa
ba, abin kawai da ke ransa shi ne ya ya zai yi yaceci mahaifansa. Tabbas ya san bai iya bada rayuwar Surayya don ganin an saki mahaifan nasa, ga shi dai abin kawai da zai yi shi ne ya
leka kofar gida ya ce da su ga ta can amma hakan ya gagara, ya bari ta sullube masa. A dacan yana tunanin hanyar da zai yi ya same ta,
amma lokacin da ya sameta din sai ya ga ba zai iya abin da aka umarce shi da ya yi ba, ya yi shiru yana tunani.
TA LEKO TA KOMA kenan
babu Surayya, sannan kuma ya san rashinta na nufin ya yi sallama da iyayensa kenan. Ya nufi dakin mahaifiyarsa cikin kunan rai sannan ne to ya ji wani abu mai radadi ya
tokare masa kirji ciwon da yake ji ba shi musaltuwa can cikin zuciyarsa, nan ya kifa kansa akan gadon da ke dakin, sannan ya ji wani abu mai tsananin duhu ya mamaye idanunsa,
sannan kuma ya daina tunanin komai da komai.
.
A haka yansanda suka same shi, kwance rai ahannun Allah daya daga cikin yansandan ne yaji tausayi sannan ya ce akai shi asibiti ko da
kuwa yin hakan na nufin Aganani zai kona su da ransu ne.
.
************ *********** ***********
.
Karfe takwas daidai ta shiga taski din, kafin tashiga saida ta tabbata babu kowa ciki daga ita sai direba, gabanta na faduwa, domin tunanin a
kowanne lokaci ana iya damkarta ta baya, amma babu abin da ya faru. Direban ya dubi akwatin mai dishi-dishin fari da ja, dake kan cinyarta, sannan ya dauke kai, lokaci guda kuma ya yi mamakin abin da ke cikin akwatin, babu wanda zai dubi akwatin ya yi tunanin akwai
hodar Iblis din naira miliyan arba'in a ciki, babu kuma wanda zai taba yarda da cewa tuni akwatin ta yi sanadiyyar mutuwar mutane uku.
Surayya ba ta ji dadin abin da ta yi masa ba, amma duk da haka tana son ya ji irin abin da taji lokacin da ya wulakanta ta tana begensa
.
Ta gama tunanin kawo karshen abin dan haka tace da dan taksi din.
"Sauri na ke yi kada ka dauki kowa, fadi duk abinda kake so na biya ka, bai bata lokaci ba, sai ya ribanya mata abin da za ta biya, sannan ya sawa motar giya ya figeta a guje.
.
Minti biyar suka zo ofishin. Sun yi jayayya ta tsawon lokacin kafin su daidaita da yansandan daga karshe Wani Sajan ya shiga ofishin kwaminshinan ya ce da shi.
"Yallabai wata yarinya ce ta takura dole sai ta ganka, mun yi mata barazana ma amma duk a banza, ba tako girgiza ba ballantana tsoro, tace wai a fada ma wani abu ne da ya shafi miyagun kwayoyi a hannunta kuma har da wata kyakkyawar akwati."
SULAIMAN S. BABA kwamishinan yansanda ya daga kansa sannan yace da shi. "Ku cajeta, sannan ku taho min da ita, amma ka tabbatar kai ka dauko akwatin ba ita ba."
Surayya ta zauna akan kujerar ta sunkuyar da kai, akwatin na kan teburin kwamishinan kusan yansanda uku kuma tsaye suna jiran umarni. Kwamishinan ya daga musu hannu sannan suka fice daga dakin.
"Bayanin yana da tsayi." Ta ce da shi, "Amma kafin na fara ina son ka bude akwatin domin ganin abun da ke ciki." Lokacin da ta bude akwatin ta yi mamaki, domin babu wani kwakwaran canji da ya bayyana a fuskarsa. "Fadi jawabin ki." Ya ce da ita bayan ya gama gani.
Kusan sa'a daya da mintuna ashirin tana bashi labari, tun daga soyayyarsu da Haidar har zuwa inda su Aganani suka kama iyayen Haidar a matsayin garkuwa, sannan ta dada da cewa. "Wai sai ya kai ni za su saki iyayen nasa."
.
Bayan sa'a daya da rabi su Aganani Mu-sha-gara sun zo hannu, babu zato babu tsammani aka shammace su babu damar yin wani abu, babban falonsa yansandan suka ritsa su da bindiga. A lokacin da aka ritsa su din har da yansandan nan guda uku da suka kai Haidar asibiti, suna mai da jawabi ne to aka ritsa su. Lokacin da Aganani Mu-sha-gara ya ga an ritsasu babu mafita kusan bindigogi ashirin da doriya suna yi musu barazana sai ya dora hannu sama, sauran yaran su goma sha daya gami da yarinyarsa Sisiliya suka yi koyi da Aganani suka daga hannayensu.
Aganani ya dubi sauran yaransa ya yi murmushi sannan yace.
"Wannan shi ne karshen mafarkinmu na zama miloniyoyi, da mun samu da mun ji dadi, sai dai kuma bakin alkalami ya bushe domin kuwa babu mu babu mallakar ko da kwandala a duniya TA LEKO TA KOMA." ya ce da su, sannan ya dada da cewa "kada ku zarge ni ku zargi kanku da kuka amince da ni."
.
************ *********** ***********
.
Kwanaki kusan goma sha biyar kenan da faruwar al'amarin wanda duk ya yi da kyau zai ga da kyau, Aganani ya zama tarihi shi da yaransa gaba daya.
An yi wa Surayya afuwa, a matsayinta na wacce ta kawo karshen abin, sannan kwamishina ya ce da ita. "Ki tabbata kin koma gurin iyayenki kada ki sake na kara ganinki a garin nan, in ba da aure ba. Na baki kwana ashirin ki shirya ki tafi.
.
************* ************* ********
.
Karfe goma da rabi na safiyar ranar Surayya ta isa gidan. Haidar na kofar gida zaune ya yi tagumi, ya yi mamakin abin da Surayya ta yi, sai dai kuma har yanzu ya rasa yadda zai yi ya shawo kanta duk iya kwanaki shida da ya yi a asibiti da ita aka yi zaman. Ana cikin jinyar tasa ne kanwarsa ta dawo daga makaranta don haka sai jinyar tasa ta zama ta mutum uku. Tun ranar da aka sallame shi bai kara ganin Surayya ba sai yau.
"Sannu Haidar yaya jikin naka." Ta ce da shi lokacin da ta karaso kusa da shi. Ya yi murmushi, cikin farin ciki sannan ya ce, "Da sauki Surayya."
Ta kawar da fuskarta don kunya sannan ta ce da shi,
"Haidar daman zuwa na yi na yi sallama da kai ni tafiya zan yi, sai kuma fatan Allah ya hada fuskokinmu da Alheri."
Ya dube ta a firgice, sai lokacin ne ya lura da jakar da ke hannunta. Ya bude baki zai yi magana, sai ta daga masa hannu. Ta matso kusa da inda yake zaune sannan ta dafa kafadarsa, daga inda yake yana iya jin hucin numfashinta a fuskarsa.
"Haidar na san duk abin da ke cikin zuciyarka a game da ni, yanzu kam na yarda kana kaunata." Sannan ta dada da cewa "Sai dai kuma wani

Please Login or Register in order to submit comment