Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suna jiran ma su zama
cikinsu. Kasan dakin tayal ne wanda aka
lilliba masa bargon sitira da lallausan kilishi, bangon
dakin launin sararin samaniya ne, daga bangaren kudu
kuma wani katon gilashi ne wanda ke kunshe da
kyakkyawan hoton wani gida irin ginin mutanen Sin.
Sannan daga saman gilashin wani kyakkyawan agogo ne
shan kwallon dafa, agogon ya mallake shi ne ranar da aka
yi bikin
shekarunsa talatin da haihuwa, sannan a tsakiyar fale-
falen agogon an rubuta cikin siraran haruffa
AGANANI MU-SHA-GARA
Karfe goma da rabi na safe agogon ya nuna. Aganani mu-
sha-gara ya lalubi gaban aljihun rigarsa, ya dauko abin
kunna taba, sannan ya kunnawa karan sigarinsa wuta, ya
fesa hayaƙi sama, ya kuma murza gashin bakinsa sannan
yaci
gaba da cewa.
"Abu daya da zai fi ba mu wahala shi ne inda zamu same
ta." Ya dan yi shiru sannan ya ce da su. "ina fatan akwai
wanda ya san gidan Rayyanu acikinku?"
Yansandan suka gyada kai kamar kurame, "Ina tunanin
wani abu." Ya ce da su yana zazzare idanu. "Ina son
mutum uku daga cikinku, su kaiwa gidan
Rayyanu ziyara a daren yau, saboda ina tsammanin
Surayya yarinyar sa ce.
.
"Ranka ya dade, kana tsammanin za ta zauna a can ne?"
Wani dogo daga cikin yansandan ya tambaya. "I to, tana
iya zama a can, abin da ba ku sani ba shine, ba ta san
muna neman ta ba, matsalar kawai a
nan daya ce shi ne ba mu san kamanninta ba, amma in
dai mun samu hotonta to tazo mana gidan sauki saboda
na tabbata za ta fita yawo tunda ba ta zaton komai." Ya
dan yi shiru sannan yace, "Ku je gidan ku bincika ina
tsammanin ko ba ku same ta ba a can za
ku sami hotonta ku bincika sosai, sauran kuma ba sai na
fada muku ba, na san kowa a cikinku gwanine wajen iya
nazarin hoto kallo daya.. Kun dai gane, ku warwatsu ko
ina, ina tsammanin ganinta nan da kwana biyu." Aganani
ya yi shiru sannan yayi murmushi.
Jikin yansandan ya dauki rawa gaba daya, saboda sun san
abin da murmushin ke nufi.
"Idan mun kama ta" Aganani ya ce, "Ita ma za ta bi
hanyar da Rayyanu ya bi" Sannan ya dada da cewa, "Ba za
ta kai labari ba, ita kadai ta rage a hanyarmu,
dole ne kuma mu kawar da ita.
.
********** ********** **********
.
Tun safiyar ranar ake ta lullumi, sau da yawa sai ka ga
gajimare ya lillibe rana kamar za ayi ruwa, idan kuma an
jima can sai ka nemi gajimaren ka rasa. Haka aka yi ta yi a
ranar. Mutane sun ji dadin
yanayin tun da a kalla dai ko ba ayi ruwa ba gajimaren ya
ceto mutane daga zafin dake addabarsu, ta hanyar
lullube hasken rana sannan ya saki iska mai dadi.
.
Misalin karfe goma da rabi na dare, sai gajimaren ya sake
mamaye sararin samaniya, a wannan karon harda
rugugin aradu da kuma walkiya mai hasken
gaske.
Sassanyar iska mai ratsa kashi da bargo ta ci gaba da
busawa sannan lokaci guda ba zato ba tsammani sai aka
tsuge da ruwa kamar da bakin kwarya, nan da nan
mutane suka shiga tsereren
kaiwa gida wasu har karo suke da yan uwansu garin
gudu, saboda ruwan ya zo musu ne babu gargaɗi.
Mintina bakwai da faruwar hakan sai titinan Banasariya
suka zama babu kowa kamar an share. A can ma daya
daga cikin fitattun titunan da aka fi sani a birnin
Banasariya, kowa ya shiga gida babu kowa a waje in ka
dauke yan kalilan din motocin da ba su da gata wadanda
ke tsaye a cikin ruwan yana dukansu.
Abin da ido zai iya gani kenan. Sai dai kuma bayan
motocin dake tsaye cikin ruwan akwai wasu kuma daban.
Mutanen uku suka fito daga cikin duhun jikakken
daren, bakinkirin da su kamar aljanu kowannensu
sanye yake da doguwar rigar ruwa ta leda tafi da
hularki, sannan kuma sawayensu sanye cikin
takalmin roba baki, kowannensu rike yake da
cocilan, a gaban aljihun kowacce rigar ledar da suke
sanye da ita kuma an rubuta cikin kananan
harufa (Banasariyya Police).
Dogon cikin su ne ya buda tangamemiyar kofar
gidan. Yayin da sauran biyun suka bi shi a baya,
dayan dan tsattana ne mai fuskar matsorata, dayan
kuma dan gajere ne, mai katon kai kamar murhu,
kowanne rike da cocilarsa a hannun dama suna
dallara haskenta izuwa cikin gidan.
Suka ratsa ta cikin kyawawan furanni da shuke-
shuken dake farfajiyar gidan, cikin sanda kamar
aljannu, ruwan saman kuma na ta zanar su amma
hakan ba ta dame su ba, kokarinsu kawai shi ne sukai ga
kofar dakin.
Lokacin da suka kusa da kofar dakin sai dogon
dake yi musu ja gaba ya daga hannunsa sama,
sauran biyun suka tsaya cak, lokaci guda kmar a
gurin fareti.
Suka yi shiru na dan lokaci, ba su ji motsin komai ba, sai
ruwan saman dake tafkar saman kwanukan
gidan, sannan kuma babu alamar haske a cikin
dakunan gidan. Dogon ya yi mamakin abin da ya
sa haka.
"Ina tsammanin babu kowa a ciki."
Dogon ya ce da sauran cikin rada. "Kar dai mu yi saurin
shiga," Dan tattsaman ya ce.
"Ina ganin mai yiyuwa tana ciki tana barci, abin da
nake ganin ya fi shi ne, mu sai mu zagaya ta baya
ko za mu ga budaddiyar taga sai mu shiga ta baya
mu dan duba"
"Haka ne," dogon ya ce da su. "Ni bari na jira ku anan,
idan kun shiga sai na biyo
ku a baya"
Dogon dansandan ya jingina da bangon dakin
ruwan saman yana dukansa, amma shi a lokacin
zuciyarsa ta tafi ga tunanin abinda ke iya faruwa a
cikin dakin. Idan akwai abin da ya ki jini bai wuce tashin
hankali ba, irin wadannan mutane irin su Rayyanu
abin tsoro ne, domin su na da matukar hadarin
gaske. Tun ranar da Aganani ya zabe su a matsayin
wadanda za su zo gidan gabansa yake faduwa,
sakamakon wani mummunan tunani da ya darsu a
zuciyarsa.
Tsayiwar da yake a halin yanzu cikin ruwan saman,
tunanin ne a zuciyarsa.
"Yanzu idan suka sami irin mutanen su Rayyanu ya
zasu yi. Yan safarar miyagun kwayoyi suna da
hadarin gaske saboda mafi yawancin su suna da
bindigogi ba su kuma da cikakken hankali.
Jikinsa ya dauki rawa,duk da ruwan saman da ake
shekawa kamar da bakin kwarya hakan bai hana
shi gumi ba. Ya lalibi bindigarsa dake kwibinsa na
hagu, ga mamakinsa sai ya ji bindigar ba ta kara
masa kwarin gwiwar komai ba, kuma bugu da kari ko
harba bindigar bai taba yi ba, rabonsa da harba
bindiga tun a gurin koyon aikin dansanda. Sannan
mafi wayancin aikin da ake sa shi ba su kai wannan
hadari ba, jikinsa ya sake daukar rawa a karo na
biyu.
"Yanzu idan Surayya na tare da wasu cikin dakinfa?" ya
tambayi kansa.
Saura kadan ya shide gurin don tsoro lokacin da
yaji an kwankwasa kofar da yake tsaye kusa da ita.
"Babu kowa ciki, kana iya shigowa" wata murya ta
ce da shi.
Dogon dansandan ya yi ajiyar zuciya lokacin da ya gane
muryar dan gajeren nan ce.
Mintuna biyu da faruwar hakan sai gasu a tsakiyar
dakin shakatawar. Ba su kunna lantarkin dakin ba,
maimakon hakan sai suka yi amfani da cocilarsu
domin nazarin dakin binciken gaggawa ya
tabbatar musu ba bu komai na karuwa a dakin sun
bincika lungu-lungu na dakin amma ba su ci
nasarar ganin koda kundin hotuna daya ba.
Adaidai lokacin ne tocilar dantsamiririn dan sandan
ta hasko tangamemen hoton Surayya dake jikin
bangon dakin yansandan uku suka yi ajiyar zuciya
daga daya ba bukatar sake dogon bincike, kowa ya san ko
hoton wacece hoton Surayya monika ne,
hoton yarinyar da suke nema ruwa a jallo.
***
Alhaji Banasare ya juyo a firgice sannan kuma cikin
mamaki, kafin ya bude baki yansandan sun buga
masa agogon maza (Ankwa) Sannan suka tura shi waje
suka je cikin motarsu suka yi gaba da shi, shi
kansa bai san inda za su kai shi ba.
Yan sa'o'i kadan da faruwar hakan, motar asibiti
tazo tana jiniya ta dauke gawar Rayyanu daga
dakin Alhaji Banasare.
Wasu daga cikin mutanen unguwar ba su yi mamakin
kama Alhaji Banasare ba, saboda tuni
daman tsurku da gulma sun cika gari cewa dan
safarar kwayoyi ne, yayin da yan karawa miya
gishiri suke cewa wai dan yankan kai ne, haka dai
aka yi ta surutai, kadan daga cikin mutanen
unguwar ne suka tausaya masa, wanda mafi yawancinsu
masu ci ne a gindinsa.
Bayan da suka yi tafiyar yan mintina sai Alhaji
Banasare ya ji motar ta tsaya, yansandan biyar suka
cakumo shi suka yiwo waje da shi yayin da sauran
suke tsaye a baya suna muzurai da dogayen
bindigogi a hannunsu.
"Ban san laifin da na yi muku ba"
Alhaji Banasare ne yake cewa da yansandan.
Sannan ga mamakinsa sai ya ga ashe bakin ruwa
aka zo da shi.
Wani dankareren jirgin, ruwa ya yi wa idon Alhaji
Banasare sallama launin fari da shudi ne. Sannan a jikin
jirgin an rubuta (Banasariyya Police)
Yansandan suka tusa keyarsa zuwa cikin jirgin ta
hanyar yin amfani da matattakalar da ta gangara
har bakin gabar kogin......
.
"Yana da kyau na san laifin da na yi.." kafin yakarasa wani
katon dansanda mai mukamiki kamar marikin lema ya yi
taku biyu gaba ya wanke shi da
mari tas!!
Jini ya fara zuba daga bakin Alhaji Banasare. "Ba ka ma
san abin da ka yi ba?" Dansandan ya buga masa tsawa.
"Maraba gasasshe" ya ce sannan ya fashe da dariya. Shi
ne babban yaron Aganani Mu-sha-gara, ɗan gajere ne
mai katon kai kamar murhu.
.
********** ********* ***********
.
Ma'aikacin ya buda baki kamar zai yi magana amma
kalmar da yake son fada ba ta sami fitowa ba.
Surayya ta dube shi a daidai lokacin da ta Mike tsaye.
"Na gode" Ta ce da shi, tana murmushi.
"Sai yaushe kenan?" ta tambaye shi tana lumshe idanu.
"In da son samu ne na samu adireshinki ko kuwa
me ki ka gani?" Ya tambaye ta.
"Sunana Aliyu, ke kuma ga shi ban san naki sunan ba"
"Kada ka damu," ta ce da shi, "Sunana Sa'adiyya shi
kenan? Bari na baka adireshin nawa" ya yi shiru ya miko
mata biro da takarda ta zana masa adireshin iska, shi
kuma dadi ya rufe shi azatonsa gaskiya ne.
"Zan tafi Aliyu na gode, ina zuba idon ganinka" Suna bude
kofar dakin sai ta ji hayaniyar jama'a ta sake cika mata
kunne suka nufi kofar fita daga dakin karbar hotunan,
Aliyu a gefen ta suna hira kamar da gaske.
.
Dogon dansandan ya rufe jaridar da yake karantawa,
sannan ya yi mika. Shi daman tuni yayi zaton haka, ya san
wahalar banza kawai za su sha,
idan banda yana jin tsoron Aganani da ba abinda zai sa
shi wannan aikin wahala. Ya dubi agogonsa, yayi kimanin
sa'o'i biyar kenan
yana gurin yana jiran gawon shanu.
"Yaushe za'a ce ka yi ta duban yarinya guda cikin
dubunnen jama'a" ya ce cikin zuciyarsa. Daga inda
yake yana iya hangen mutane suna shiga suna fita daga
dakin karbar hotunan. Ya yi mamakin abin da
mutane suke yi da hoto har suke wahalar da kansu haka,
shi dai indai ta shi ne da ba a dauki hoto ba,
domin shi hoto in ba wanda ya shafi aikinsa ba bai damu
da shi ba ko kadan domin shi a gurinsa barnar kudi ne. Ya
sake duba agogonsa, sannan ya mike tsaye.
"Abin kwai da ya fi shi ne, na yi tafiyata gida na huta in ya
so da yamma na sake fitowa domin na
san wahala ce kawai, tun daga shi.."
Numfashinsa ya dauke, lokacin da ya ga yarinyar ta nufi
bakin titi, yar bakar jaka a rataye da ita. Duk a cikin
yansandan Banasariya babu wanda yafi shi tsoro da
lalaci, sai dai kuma idan akwai abin da ya fi kwarancewa
akai shi ne gane SIFFAR YAN ADAM.
"Ko shakka babu wannan ita ce Surayya.
Irin yadda ya ji gabansa ya fadi shi ya kara tabbatar masa
da hakan. Ya yi sauri ya nufi inda take.
"Hajiya Ji mana" Ya ce da ita.
Da farko ba ta yi zaton da ita ake ba, amma jin ya dada
kiran sai Surayya ta juyo, gabanta ya fadi
lokacin da suka yi ido hudu da dansandan, ita kanta ba ta
san dalilin faduwar gaban ba. "Hajiya muna bukatar dan
wani jawabi daga
gurinki" kafin tayi magana, sai ta ga ya tsaida mota
"Police Station" Ya ce da dan-taski din, muryarsa na rawa.
.
********** ********** *********
.
Alhaji Banasare, ya dulmiya cikin kogin tunanin abin da
ke faruwa kamar a mafarki.
A duk lokacin da ya hada uku da uku sai ya ga biyar,
amma a halin yanzu ya fara ganin shida.
Babban abin da ya fi daure masa kai shine, dalilin dayasa
ake son dora laifin kisan Rayyyanu akansa. A iya saninsa,
babu wani ma'aikacin hukumar da ya san sirrinsa da
kuma sana'arsa ta fasakwaurin miyagun kwayoyi. Sai dai
kawai jita-jita da ake yi agari. "Jita-jita kuma irin wannan
wani abu ne da ya zama ruwan dare gama duniya, domin
duk
sa'ad da jama'a suka fahimci kana samun makudan kudi,
kuma ba tare da sun san wata takamaimiyar
sana'ar ka ba to dole ne ka ji irin wannan jita-jita.
"Aganani Mu-sha-gara ne kawai ya san sirrina"
Banasare ya ce cikin zuciyarsa. Gidan ya yi shiru ba ka jin
komai sai sautin zubar ruwa a kwanukan
gidan tuhumar. Alhaji Banasare ya muskuta a cikin
kurkukun
dakin da aka kulle shi ciki, hannunsa da kafafunsa a daure
tamau da agogon maza (Ankwa).
Ko shakka babu yanzu yasan wanda ya kulla masa
wannan sharrin.
"AGANANI?" Ya tambayi kansa. Uku da uku da sun fara ba
shi shida, Aganani Mu-sha-gara ne, abin da ya karawa
lamarin launi MA shine, gawar Rayyanu da aka kawo
dakinsa.
Yau da a ce kama shi kawai aka yi ba tare da an kawo
gawar wani dakinsa ba to da sai ya yi tsammanin
ko kawai zargi ne ya tsananta a kansa aka kama shi. To
amma gawar Rayyanu ita takara tsoratar dashi, yanzu
kam ya san kamun da aka yi masa na yan wasu mutane
kalilan ne dake son cimma wani burinsu.
Ya zargi kansa saboda saurin amincewa Aganani mu-sha-
gara da ya yi. Naira miliyan arba'in ba abar amincewa
kowa ce ba. Yanzu kam ya gane duk abinda Aganani ke
shirin aikatawa. Jikinsa ya dauki rawa saboda wani tunani
da ya Fado zuciyarsa.
Ko shakka ba ya yi yanzu ya san hodar Iblis din na
hannun Aganani, "Wannan shi ne dalilin kashe Rayyanu"
Ya ce cikin zuciyarsa. Jikinsa ya sake daukar bari lokacin
da ya tuna da shi kadai kenan ya san da
maganar hodar Iblis din. Saboda haka shi ma yanzu
rayuwarsa na cikin hadari gumi ya rufe shi
sharkaf.
Ya motsa hannayensa da kafafunsa dake daure tamau.
Idan ya motsa su sai ya ji kamar kara daure shi suke.
"Ina hanyar tsira?" ya tambayi kansa. A wani zamani da
ya huce, Alhaji Banasare ya yi sanadiyyar
Mutuwar mutane da dama, in dai za ka kawo cikas ga
sana'arsa to sunanka matacce. Amma duk da
abin da ya yi a da, ya fi kowa tsoron mutuwa. Idan akwai
abin da ya fi tsoro da fargaba bai wuce mutuwa ba,
wannan shi ne abin da yasa ko
makabarta ba ya son zuwa. Idan an yi rasuwa a
makwabtansa, sai dai ya aika likkafani da turare a
matsayin sana mai kudi ya sake jijjiga ankwar dake
hannunsa, sai ya ji ta sake daure shi tamau kamar
hannayensa za su yanke su fadi.
Ya rufe idonsa jikinsa na bari lokacin da ya tuna da irin
tukwanen da ake jerawa a saman kabarin matacce.
Mutuwa!! Hakika yana tsoron mutuwa, duk da yake kuwa
shi ma a zamaninsa ya yi sanadiyyar asarar
rayukan jama'a da dama.
.
************ ******* **********
.
"A wane dalili!" Surayya ta ce da dansandan cikin tsawa a
daidai lokacin da dan taksi din ya ja ya
tsaya a gabansu tuni har yara sun fara taruwa agurin.
"Kin ga ba...ba wani dogon surutu na nema da ke ba
kawai dai na ce muna son magana da ke ne..."
"Ba za ni ba!!" Ta ce da shi cikin karaji, "Me ka dauke ni ne
yar iska ko me, na ce ni ba za ni ba! Ba
na ra'ayinka!! Bana kaunarka!! Dole ne sai ka takura min
na bi ka? To na bika ina..."
"Malama dakata, ban gane abin da kike nufi ba."
"Ai daman ba za ka gane ba, tun da abin naka babu
gaskiya." Kafin kiftawa da bismilla ta tara masa mutane,
nan da nan gumi ya fara ketowa daga goshin dansandan.
Wasu daga cikin mutanen suna
kokarin su tambayi abin da ke faruwa amma fargaba ta
hana su, saboda ganin rigimar da dansanda ne ba su sani
ba ko wani laifi ta yi yake son kamata.
Dan taksi din da dansandan ya tsayar ya ga za'a bata
masa lokaci, sai ya sauke gilashin tagar gaba
ya leko da kansa yace,
"Yallabai ko na yi gaba ne?"
"Jira...jira ni minti biyu" dansandan ya ce yana in'ina,
sannan ya juyo ga Surayya wacce tuni
mutane yan tsurku har sun fara tambayar ta abin da ke
faruwa."
"Wai kawai don ya nemi ya cusa kansa a gurina nace ba
na ra'ayinsa, shi kenan wai na yi laifi."
Surayya ce take fadawa jama'ar dake tambayarta. Nan da
nan gurin ya dau hayaniya saboda jin abin
da Surayya ta fada.
"Yallabai gaskiya ba haka ake yi ba." Wasu daga cikin
tsagerun samarin da suka taru a gurin ne
suke cewa. Mutane da dama a gurin ba su yi ko da
shakkar abin da Surayya ta fada ba, saboda al'adar
mutane a yanzu sun dauki dansanda a matsayin wanda
ya fi kowa iya sharri.
"Malama da ke nake fa, gara tun wuri ki zo mu tafi ki
amsa tambayoyinki, cikin arziki tun kafin na
dauki mataki matsananci akanki."
Duk maganar da dansandan nan yake ta karfin hali ce,
saboda shi a gurinsa ba don kunyar idon jama'a
ba da tuni ya bar ta ta tafi, ba don komai ba kuwa sai don
abu guda.
Tuni ya fara addu'ar Allah ya sa kar wani dansanda dan
uwansa ya zo wucewa ta gurin. Saboda idan
suka kai ta ofishin yansanda ya ce da su ya kama ta da
me?" Muddin ya fadi dalilin daya sa ya kama
Surayya to hakan na nufin ya tona sirrin Aganani,
domin kamun da za ayi mata na Aganani Mu-sha-gara ne
ba kamun hukumar yansanda ba bakuma
sa son kowa ya sani. Jikin dansandan ya dauki
rawa da ya tuna da aika-aikar dake shirin faruwa shin
yanzu idan hakan ta faru yaya zai yi da Aganani? Ya
tambayi kansa cikin fargaba, Aganani na iya kashe shi.
"Ba za ni ba, sai dai ka kashe ni!!" Surayya ta ce da
dansandan cikin karaji. Wasu samari guda biyu
karti, madoka kato kuma bakake, suka diro a gurin kamar
an jefo su daga sama, daga su sai
yankakken gajeren wando iya gwiwa babu riga,
kowannensu rike da galan din fetur, daya daga
cikinsu rike yake da galan din fetur guda biyu.
Dayan kuma galan din fetur ne daya kawai rike a
hannunsa na dama, hannunsa na hagun kuma rike da
tsinkakken takalminsa silifa launin rawaya.
Tun kafin a karasa sanar da su abin dake faruwa suka ce,
"Karya ne!!!" gaba dayansu. "Ba ka isa ka kafi da ita ba,
rashin mutuncin naku ya tashi daga kan yan cuwa-cuwa
kuma ya koma kan mata?"
Sannan dayan ya dubi dayan ya ce, "Kai baba!! Wannan
bawon ba shi bane ya yi mana rashin
mutunci kwanaki ba, ka gane shi ai? Shi ne wanda rannan
ya rike ƊANBA'U ya ce sai ya kai shi.
"Ah! Ah!! Ah!!!" Dayan ya ce cikin karaji "Na gane shi ai
baba, Wallahi ba za ka tafi da ita ba, sai dai ka
tafi da mu. Mu daman mun saba karo da ku." Saurayin
daya ya shiga tsakanin dansandan da
Surayya. Damar da dansandan ke jira kenan domin
tuni daman ya gaji da cacar bakin shi ma so yake Surayya
ta bar gurin kar abin da yake tsoro ya faru.
Dansandan ya yi wuf ya rike gefen gajeren wandon
saurayin da ya shiga tsakaninsu da Surayya. "Rike ni da
kyau, ni na isheka...!!" Saurayin ya ce da shi yana ciccije
baki.
Dayan saurayin ya yi sauri ya tsaida babur sannan ya ce
da Surayya:
"Hau ki tafi yan mata ki bar mu da karamin ARNE."
.
Surayya ta dan yi jim amma jin mutanen dake gurin sun kara mata karfin gwiwa sai ta hau dan kabu-
kabun ya sa giya sannan ya falla da gudu da Surayya wacce ke bayan babur din wasu daga
cikin mutanen dake gurin da kuma yara suka dauki sowa da tafi gabadaya. Sannan kallo ya dawo kan dansandan da samarin wanda tuni sun fara kokawar kwacewa daga hannun dansandan, wannan ba wani sabon al'amari ba ne ga yan cuwa-cuwa.
.
*********** ********** *********
.
Tun zuciyarsa na bugawa gami da mummnan tunanin abin da yake zaton zai faru gare shi, har dai
daga karshe tsoron da fargabar suka gushe sannan bakin ciki da fushi da kuma tunanin ramuwar gayya suka maye gurbin.
Alhaji Banasare ya fara haure-haure, sannan zazzafan hawayen bakin cikin halin da yake ciki ya fara kwaranya akan kumatunsa. Abin da ya fi bashi haushi fiye da komai shi ne cin amanarsa da Aganani ya yi, ya dubi shekarun da suka wuce tun
Aganani mu-sha-gara yana karamin dansanda suke harka tare, amma abin mamaki sai gashi yau ya ci amanarsa... Tunaninsa ya katse lokacin da kofar dakin ta bude
sannan yansandan uku suka shigo suna muzurai,
kowannensu dauke da zungureriyar bindiga harbi ka ruga. Ba su yi masa magana ba, sai suka cakumi
babbar rigarsa, wani kuma ya dauki kafafunsa
suka fito da shi daga cikin dakin mai kamar akurki. Suna zuwa sai suka jefar da shi tim!! A tsakar dakin
mai kamar akurki. Suna zuwa sai suka ja da baya suna kallonsa, kamar yadda kuraye ke kallon naman da suke shirin fadawa.
Mintunansu uku da rabi a gurin tsaye, kamar an dasasu. Kofar dakin ta bude sannan Aganani mu- shagara ya shigo dakin, sankonsa na kyalli kamar an haska madubi da fitila, sannan kansa na barazanar taba saman dakin. Shigowarsa ke da
wuya sai duk yansandan dake gabansa suka zama yangajeruna duk da yake kuwa suna da tsayi. Irin
yanayin da ya bayar yayi kama da yanayin da zaka gani yayin da rakumi ya tsaya a gaban shanu.
Shirun dake dakin da kuma kasancewar Aganani mu-sha-gara su suka sauya yanayin dakin lokaci
guda, kamar yadda kalanzir ke sauya ruwa.
Yansandan suka kame kamar ruwa ya cinye su fuskokinsu suna duban kasa, sannan zuciyoyinsu na harbawa kamar yadda manunin dakika ke harbawa.
"Ku kunce shi." Aganani ya ce da yansandan. Kafin kiftawa da Bismillah sun kunce Alhaji
Banasare. Mutanen biyu wadanda yan kwanakin da suka wuce abokaine suka dubi junansu alamun tsana karara suke a fuskokinsu.
"Ka ba ni mamaki Aganani" Alhaji Banasare ya ce muryarsa na rawa.
"Ba abin mamaki bane idan aka yi la'akari da irin kudin dake cikin harkar." 45,000,000 Miliyan arba'in ba karamin kudi bane da har za'a iya amincewa wani akanta, ina tsammanin ba dukkan zuciya ba ce za ta iya hakurewa miliyan arba'in. Kasa kanka amatsayina za ka gane cewa idan kai ne ni da abinda za ka yi kenan. Ka dade kana jan zaranka yadda kake so, saboda haka ni ma lokaci ya zo daya kamata na ja nawa zaren. Aganani mu-sha-gara ya yi shiru, sannan ya ci gaba da cewa.
"Ban ji dadin abin da ya faru ba tsakaninmu da kai Banasare, saboda ka kyautatamin a baya duk da
yake dai nasan bautar da nayi ma tafi karfin abin da kake bani, wannan shine dalilin da yasa nayi
amfani da wannan dama don ganin nima na gina kaina, Aganani ya yi murmushin mugunta sannan ya ce.
"Zan yi maka taimakon karshe Banasare, taimakon
da zan yi maka kuwa shi ne na kashe ka domin ina ganin mutuwarka tafi zamanka, kuma hakan shine
zai hutar da kai kuma ya hutar da ni.
.
*********** ********* ************
.
Karar wayar talfon din ta cika dakin sannan koriyar danjar dake jikin kan talfon din ta yi haske.
Aganani ya nufi talfon din da sauri koriyar danjar na nuni da cewa yaronsa ne ke bugo wayar karfe
bakwai da rabi na dare, agogon dake jikin bangon dakin ya nuna, Aganani ya yi mamakin abin dake
tattare da waya domin yaransa basu saba bugo masa waya ba a irin wannan lokaci.
"Yaf!" Aganani mu-sha-gara yace cikin kan talfon din.
"Banasare ya gudu!!" wata murya taceda shi daga can daya bangaren irin yadda sautin muryar me
maganar ke fitowa ta cikin talfon din, shi ya sa Aganani tunani cewa kadan ya rage mai maganar
ya fashe da kuka saboda fargaba. Fuskarsa ta koma toka-toka, sannan idanunsa suka yi jajur kamar gauta fuskarsa ta yamutse kamar an taka dan tunfafiya,
"Me kuke nufi da ya gudu!!!" Aganani ya yi haushi cikin talfon din.
"Wal..wallahi...yallabaimuma saida muka sami kanmu sumammu sannan...
"Ya isa haka sakaran banza!!"
"kuna nufin kace sumar da ku ya yi?"
"Haka aka yi yallabai lokacin da ka bar mu ji..jiransa kafin ya gama cin abinci shine...
"Yi min shiru shashasha! Saurara da kyau, ina son ku zagaye duk wata kofa da kuke tunanin za ta iya
bashi hanyar gudu, nasan ba zai iya guduwa ba, yana nan ku yi kokarin samun sa kafin nazo."
"Abin da ka ce shi za'a yi yal..yallabai" mai maganar
ya ce cikin in'ina. Aganani ya yi shiru na dan lokaci sannan yace: idan har kuka sake ya gudu baku kama shi ba to ina baku shawarar da kowannenku ya sai wa kansa likkafani kafin na karaso." ya ajje kan talfon
din kararaf! Yana huci kamar kumurcin maciji..
.
********** ********* *********
.
Alhaji Banasare bai gasgata abin da kunnensa suke jiye masa ba.
Ya yi saroro yana sauraran Aganani Kamar wanda yake tsammanin ya tabu.
Kamar ya san abinda ke zuciyarsa sai Aganani mu-sha-gara ya ce:
"Ko kusa kar ka yi tunanin ba kaina daya ba, da hankalina abin da nace haka ne babu ko shakka aciki, daidai kaji ba wai kunenka ne yake karya ba." Sannan ya ci gaba da cewa.
"Bari na maimaita abin da nace babu mamaki lokacin ko gayan tuwo ya toshe ma kunne abin da nace shine, mutuwarka tafi rayuwarka, itace kuma zata hutar da ni ta hutar da kai."
Kakkausar sautin muryar Aganani ya daki dodon kunnen Banasare, sannan lokaci guda jikinsa ya
dauki bari, abinda ya gani a idon Aganani mu-sha-gara, shi ya tabbatar masa da cewa Aganani na iya aikata abinda ya ce.
"Bai kamata ka yi

Please Login or Register in order to submit comment