Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

girman kawai na fada a zuciaya Karfe goma daman kowa ke tafia dakinsa ya
kwanta.tare muka miqe da ya abdullah saboda
kullun haka muke yi sai mubar yaya da anty su
gane.
Wuf!naji ya cafkoni yana fadin wa na kama?
Yauwa Allah yaya.ya abdullahi ya fada yana ta
murna
nace wlh dazun... Yace e mana dazun kika ruga
ko?
Zanyi magana anty ta qaraso.don Allah faruk
kayi hakuri ka kyaleta
don tana yarki ko? Toh kin yarda zakiyi mani
azumin rantsuwar dana yi,,?
Tayi saurin cewa eh
ya karkada kai cikn dariyar nan tasa wadda na
fassara ta da dariyar qeta..yace sorry wani baya
yiwa wani kaffara,,
nace wlh anty dazun ya bani
eh dazun na baki amman dana baki sai kika
Zubar, toh ba haka naso ba,ko zan kyale ki sai kin
daina kyamar sa,in ba haka ba na dinga
Zuba miki shi kenan har...na bude baki zanyi magana
kenan naji TUF a fuska,ya tofa mani tare da sakina
nayi saurin tofar da shi tare da rugawa kitchn
don in wanke fuska ta....kin gani ko? Toh wlh sai
nayi maganin ta
inaji anty ta bishi tana bashi hakuri,amma ya
qiya wai na raina mashi wayo ne
kawai ta kyale ni yayi maganina,,shi kuwa
abdullah sai murna yake yana fadin..maganin
mai kyankyami kenan..ko a haka zakiyi aikin
asibitn?ai qara yaya ya hora ki tun a gida
barta kawai naji yace
Na hau gado raina a bace,sai naga anty ta shigo
tare da miqo mani waya,yi sauri ki yi magana
muktar ne.ina amsa tayi waje,na kanga a
kunnena ina fadin hello.muryata ta dishe sabda
bacin ran ya faruk
shima ya amsa hello my dear ya dai?
Lafia lau,na fada ya kake?
Da sauqi
na danyi murmushi,me ke damunka?
Ke!!!
Sai naji wani abu yarr,kwatan kwacin wanda naji
dazun,saboda yanayin yadda ya fada maganar
duk na rikece meena sonki na neman haukata ni
na lumshe idanu a hankali naji wani dadi na ratsa
zuciata nace ,karka damu,i'm urs 4ever insha
Allah
nagode my love.kin kwanta ne?
Nace yanzu haka ma akwance nake
yargayu ya fada tare da yin dariya
miye na gayu a ciki,don na kwanta yanzu?
Hankalinki a kwance yake shiyasa ni ko kin ganni
nan fita ma zanyi
fita?
Na bukata
eh wlh,wani frnd dina zan kai wa saqo sai...
Cikin daren nan haka?goma fa ta wuce kodai
wurin yarinyar ka zaka?
Walh bani da ita,ke kadai ce meena believe me
kai yaya kada ka shafa mani mai a baki ko
dai...?
Kin san Allah?
Kada ka rantse naji ance yar wajen baba auta
kuma kake so
shirun dana ji yayi ya tabbatar mani da lallai ya
shiga rudani,saboda wata qila baiyi tunanin nasan
maganar ba
hello r u on d line?
Yes meena me kike son na fada maki ne yanzu
nace gaskia
o.k ki jirani gobe wajen karfe daya zuwa 2 na
rana
kai da wasa nake maka,ni wlh ban damu
ba,saboda nasan ni kake so,tun yaushe nasan
maganar kake tunani?ko changin fuska na taba yi
maka?
Duk da haka tunda kince na fada maki gaskiya ke
dai ki jirani goben.
Nifa nace...kinyi fushi ne?..a'a amm..ai ni ina son
zuwa ko don naga gimbiyata idan ba fushi kikayi
ba da gaske,,to zan ga hakan ta special cook of
delicious, o.k?
Nayi dariya nace ba matsala,daga haka muka
bankwana na kashe wayar
Nasan yanzu anty ta kwanta don haka na bar
wayar ta kwana wurina
wayar ya muktar ta kore mani haushin ya
faruk,barci nake kasariqa kamar a mafarki na
dinga jin wakoki,..kidi yaqi qarewa ashe waya ce
ke ringin ina ruwan ba saban ba.da kyar na tashi
na kalli agogo karfe 3 da kwata na dare
na dauko wayar sai naga an rubuta DARLING
nayi kuri da ido,nasan wannan sunan sai yaya,toh
ko anty yau dakinta ta kwana ne shiyasa yake
nemanta awaya? Toh ni na dauka? Tunda ban
san abinda zan fada mata ba
na kura mata ido tana ta ringin har ta katse,sai
ya qara bugowa,kai yaya akwai naci
gaskiya tsoro nake ji bana iya fita da sai na
daure na kai mata.ko ko in dauka sai in fada
mashi cewa tana hannuna? Alabarshi idan shi
yana iyawa sai yaje dakin anty ya kirawota,to me
ma zata yi masa cikin dare?
Kai yaya akwai fitina,eightn missed calls,an
rubuta nayi saurin dauka
hello yaya ba anty bace,meena ce wayar
hannuna ta kwana
na sani dama na tadaki ne don in gargade ki
cewa,kiyi ma kanki kiyamulaili ki daina kyamata
idan har kina son zaman lafia.ko kina tuna yanda
mama ke mani ne? Kema zaki dauko?.to ki tuna
ita mahaifiyata ce,dole nayi hakurin,amma ke
babu dalili
Ko danaji yayi shiru sai nai qasa da murya daman
gata, ta mai bacci na ce..to yaya,amma kuma
dazu ai ban fa yi kyamarka ba,
waya fada miki haka a ke rashin kyama? Gabana ya fadi
na rude a lokcn, Sai nace
kayi hakuri dare yayi lokaci ya wuce,
idanunki ne suka yi maki gizo saboda ko minti
biyar bamu yi ba
kamar zanyi kuka na fara roqonsa,don Allah yaya
kayi hakuri kaga fa banyi kyamarka ba,na
biyun ma don ka tofa mini,wlh da cewa kayi in
tsotse bazan zubar ba
toh ai kinji na fison ki saba ki daina kyamata.
haba yaya,
haba meena,
ya kwaikwayi maganata,.kin san gabanni rasuwar
abba akwai ranar da yace mani na riqqe ku
amana.kada mu kyamaci junan mu
bana kyamar ka yaya
qarya ne,idan kuma kina gardama toh ki bari idan
na qara tofa maki, ba zaki yamutse fuskar ki ba,wannan ne zai sa
in yarda kuma in kyale ki,
Allah idan ban yamutse fuska ba, zaka kyale ni kwarai kuwa
yauwa yaya na gode,gobe ma na yarda ka tofa ni
kuma wlh ba zan canja fuska ba, shi kenan?
Allah ya kaimu ya fada
nace amin nagode
kike wani saurin godiya kin manta da minti
gomanki
na zaro ido yaya ban fa zubar da wannan ba
amman kin gaza cika mintuna
na shiga (3) uku!
yayi dariyar qetar nan tasa yace tara ma shigar
ta zakiyi,saboda sai da nace miki ba zaki iya ba
,ke kafaffa kikace kin ji kin gani
tunani na a kasa zaka zuba ina zaune, ban san a hannu zaka bani ba,.na fada kamar mai
shirin yin kuka
dariya kawai yayi,yace kina bani mamaki duk kin
wani rude akan abinda bai taka kara ya karya
ba,ni kuwa duk abinda kika sani ya fito daga
jikinki meena ba na kyamarsa, zan ma iya sha muddin bai sabawa addininmu ba (Addinin musulunci.
to ai yaya.........
ke dai kika sani,yanzu ke nake jira ki bani lokaci
sai nayi shawara!
kaga har an kira salla,
ni kike fadawa sai kinyi shawara?
Dole ne saboda in samu lkcn dazan iya daure wa
har na cika lokc na,ayi mani wannan alfarmar
don girman Allah yaya
zuwa yaushe?
Zan sanar da kai idan lokc yayi,pls a taimaka.na
qara fada kamar zanyi kuka
o.k, ba matsala,je kiyi sallah,ya kashe,na kalli
wayar nace kaya da yari
kome anty zata ce idan ta duba taga wannan
waya da mukayi kusan awarmu 2?
Koda yake ita anty ma ai suna wayar ta
tara.uhmm na miqe don bada farali
Na dan yi tsam da rai!! Ina tunanin irin girkin da
ya kamata nayi wa ya muktar,wanda zai qayatar
da shi
dariya na danyi ,ya kamata har yangidan yau nayi
suprisn dinsu,ba ya muktar kadai ba
agogog da manne bangon dakina na tsurawa ido
ina nazarin lkc.karfe 8 saura wasu yan mintina
yau lahadi na tabbatar da cewa ko za'ayi saurin
tashi toh zuwa sha daya ne saboda mafi aksari
ranar wkends ba'a fiye tashi da wuri ba.don haka
babu maganar kalaci sai dai abincin rana
abba kuwa ruwan tea aka hada masa da yanciye
ciyensa na yara
na miqe da saurin lkc da na tuno nauoin abinci
da aka koya mana skul
maganar sa na tuno inda yake cewa rayuwata ina
son dankalin turawa shine best food dina..nayi da
riya dana tuno ra'ayin su daya da ya faruk shima
yana son dankali don baya gundurarsa
ina zuwa kitchn na tarar abba na shan tea grace
kuma na fere masa dankali zata soya ita kuma
mary na tsaye tana ta zuba
toh uwar surutu kin fara ko?
Oh anty gud mrng.duk suka ce lkc daya.abba ya
juyo cike da murnar ganin yace morng anty nace
mrng abba ya dai..ya dan yamutsa fuska yace
not ba
na dan kalleshi cike da mamaki yadda yaron ke
actn kamar ubansa.lallai dgaskiyr hausawa da
suke cewa gado girman da..shima haka zaka ga
yaya yana magana wani lkcn yana yamutsa fuska
anty yau bakya bacci ne?merry ta fada tana
kallona
nace a'a muktar zai zo nan
yes grace ta fada tana murna don sun san yau
akwai kyautar kudi
na kalli merry qaro dankalin nan da dan yawa
grace ta fere sannan ki dora mani zobo bisa
wuta
*(tabdi gaskiya ban iya rubuta maku abincin da
tayi don suna da yawa sun kai page 4 har da wani
wai biscuit din manshanu)*
a hankali cikn natsuwa da kayatarwa muka jera
komai bisa dinning table.lkcn karfe shabiyu da
rabi
na jiyo motsin anty a daki alamar ta tashi.sannan
na jiyo qarar shower alamar ana wanka a
toilet.hakan ya tabbatar mani da yaya ne
zan tafi daki don yin wanka kenan ya abdullah ya
shigo
wai me ake dahuwa ne agidan ya gwauraye da
qamshi haka.tun a compound nake jin wannan
buagaggen qamshin yana ratsa zuciata
dariya kawai nayi nace mrng...tare shigewa ta
cki ina jin uwar labari merry nayi masa bayani
eh lallai kema yarinya kince somthn
Sanyenake cikin hadaddun wasu riga da skirt yan
kanti,irin na indiyawa jajaye masu gajeren
hannu,rigar kuma qarama amma ta rufe cibina
sai kuma shi skirt din dake da fadi
na gyara gashina ya zubo gefe ta hanyar tsifar
da nayi kadan,daga gaba.yanayin kwalliyar da ke
jikn rigar ya sa na sanya sarqa yar qarama mai
fadi wadda ta kwanta bisa wuyana sosai
wasu dogayen takalma na saka mas tsini kalar
jinin kare wadanda anty ta sawo mani last yr da
taje umra
na juya na qara juyawa,lallai zan ba ya muktar
mamaki....wai sai an gama ja mana aji za'a fito
a bamu abincn ko kuwa? Muryar anty naji daha
falo
da sauri na fice ina dariya,shaf na manta da
mayafin kayan ban rufa ba saboda sauri
iye iye lallai yau meena akwai abinda ke faranta
ran nan naki inji anty ta fada
ya abdullah ya ballo mani harara wai don ana
cewa tana kama da karishma kapoor shine yau
har da yin shigarta mts,yayi tsaki kilbibu
na zauna bisa kujerar dake kallonsu na kalli
gefena, ya faruk ne zaune ya quran ido,nayi
saurin gaidashi,don nasan kila shima dalilin
tsareni da idon da yayi kenan
maimakon ya amsa sai naga ya kalli anty yace
serve me pls am hungry, na dan danna mata wani harara, maimakon ya ce in zuba masa sai cewa yayi wani "serve me pls" mtsew!!!
Kawai sai anty ta ce, ina nasan ta kan wannan abncn faruk? Meena a
taimaka a zuba mana
na yunkura kenan, ya abdullahi yace ko sai
munjira muktar....
Kan uban can..yaya ya surmiya wani uban zagi
duk muka kalle shi hankali tashe
ni zaki mayar dan iska? Ya banko mani wannan
maganar?ke yanzu har kinyi girma kina ganin kin
cika mace zaki kawo mani raini?
Idona yayi narai narai zanyi kuka,ya buga
tsaki,shine kika bazo gashi da wannan uwar
kwalliyar don saurayi ko?kaga yar iska
hankalina ya tashi na rushe da wani irin kuka
ke tashi ki canzo kaya tare da sako hijab ko
kuma nayi ta kwallo....
Da gudu nabar wajen ban ma tsaya ida sauraren
abinda zai fada ba
Na fada bisa gado ranar farko da na taba yin
kukan maraici
hankalin kowa ya tashi a gidan,na fi minti talatin
sannan naji motsin an shigo dakin,,ko ban dago
kaina ba ina kyautata zaton anty ce,sai na qara rushewa da
kuka
a hankali ta dago ni ba
tare da tace komai ba,na qara runtse idona tare
da kwararo wasu kwallan
daga ji kasan itama ckn bacin ran take,a hankali
ganin ba nida niyyar daina kukan ta ringa shafa
mani baya alamar lallashi...kwallanta suka zubo
mani,hakan ya tabbatar mani da zargi na wato
itama kukan take yi
haba kamar zuga ni take yi na qara sakin wani
kukan ,dagoni tayi, da sauri na bude ido na wa zan
gani?ya faruk ne riqe dani yana zubda kwalla
nayi zumbur na miqe zan bar dakin,ya damkoni
zan kwalla qara ya toshe mani baki
haba meena?toh yi hakuri bazan qara ba
ya danyi shiru..kina bani mamaki,kin sanni da
fada to tunda baki so ba sai ki kiyaye ba
ina son nayi magana ya toshe mani baki
kiyi hakuri kinji bazan qara ba.amman ina roqonki
da ki rage wannan rashin kunyar,meye amfanin
barin gashin a waje don saurayi ya gani..ke
bakya son yayi dokin ki idan kinje gidansa?idan
kuma kina nuna tsiraicinki tun a waje ina kike ga
saura?
Yayi ta bani baki yana lallashina..har na hakura
tare da nuna masa hakan da ido
yace toh da sharadin bazaki qara nuna damuwa
ba.don Allah kada hakan ya dami zuciarki meena
na daga kaina alamar na yarda
yayi ajiyar zucia tare da sauke hannunsa a hankli
na tura a dauko muktar yanzun nan yayi mani
waya sun iso airport
uhm kawai nace
kada ki sauya kayanki,amma make sure kin dora
hijab saman kayan koda qarami ne pls
nace toh kawai
ina sakawa nayi hanyar waje ya riqo ni,nayi
saurin juyowa wannan abun fa ya fara damuna
wai me ke damun yaya ne?
In topa miki miyau a puska? Ya nuna bakinsa
nayi saurin tsuke fuska sai naga shima ya daure
tasa
bana son wannan abun ka kyale ni
kafin ya qara Magma nayi falo abuna
Na fito fuskata wayam kamar bani na gama rigar
kuka ba,shima naga ya biyo ni yana dariya
eh lallai mun yarda da mgnrka da kace kai kadai
zaka iya shawo kanta.anty ta fada cike da murna
ya abdullahi kuwa dariya ya hau yi
ina cikn zuba abincn ya muktar yayi sallama,wani
kallo naga yaya yayi min,ban san ko name ye ba
abncna ya yiwa kowa dadi,wani santi da ya faruk
yayi sai da kowa yayi dariya..saboda ko loma
shidda baiyi ba ya fara bada tarihin karas(carrot)
yana cewa kun san shi ainahin karas aslnsa fari
ne da kore,toh sai malamn kimiyya sukayi masa
aure ya koma jah
duk aka bushe da dariya,ana fadin kwarai kuwa
haka ne
zuwa can kuma yace gaskia zanzo na rage shan
drinks,wannan haduwa haka har yafi na company.
gaskia kam ya muktar ya fada yana dariya
ana gamawa ya kalli anty,kwashe mani sauran
cake din nan da bisciut ki sami inda kika zuba
mini,saboda na tafi dashi office
abba yai karaf yace daddy nima ina so
yace to bar masa kwara 2
biyu na bukata?
Ko kallona baiyi ba yace idan kin raina kiyi masa
wani,nima kinga sai in qara don wannan din ba
isata zaiyi ba
ya dan juyo kaina,bama zan qara sawo masa
biscuit ba daga yau!
aifa an bani, anty ta fada tana dariya.shifa faruk
bai iya cin kwan makauniya ba,idan abu yayi
masa dadi shi kenan.ko yanzu na tabbatar da
taki ce ta sameki,kamar yanda zan huta
ya kalleta cikin yar dariyar nan tasa yace hutunki
kam yazo jamila, yayi daki abinsa.........
a Hada Hausa Book stories
GIDA BAI KOSHI BA
¤¤5¤¤
Nidai nayi wa ya muktar signal da mu koma waje
don zamufi sakewa
muna fitowa ya abullah ma ya fito ya shiga
motarsa yabar gidan,,nasan iyakarsa zone broosh
gidn su salma
muna zama ya kalleni,,u relly suprsd me,believe
me ban taba cin abinci da na ji dadinsa ba irin
naki meena..ina son cake din nan da biscuit,yaya
ya rigani wlh kunya ce ta hanani cewa ya bar
mani.nayi niyyar sai mun gama nace ki kwaso
mani in tafi da shi,toh ya riga ni dole na hakura
laifinka ne ai ba sai ka fadi mani ba alabarshi
su....
Naso kamanta hakan, amman na kasa, saboda
ganin abba ma da kyal ya bashi kwara 2 toh ina
gani?..kin san kuma halinsa ba wuya ya cabo wa
mutun maganar da zata qona masa rai
kwarai kuwa halinsa ne,..ba matsala nxt tym idan
ka dawo zanyi maka da yawa..shikenan
kafin in fara magna,ina son yi maki wasu yan
tambayoyi.ina aka ajiye maganar contrler
nayi dan jim nace uhmm tundai daga lkcn da aka
ce ya dakata bai qara dawowa ba har yau
kema kina kewarsa?
Wace irin tambaya ce wannan yaya?
Da ina son cntrlr da har yanzu bamu kai haka
ba..GIDA BAI KOSHI BA BA AN BAWA NA DAWA
BA
yaji dadi kwarai,
Ina kallon wani naija film. ina
kuma shan tea,hankalina kaf yana ga film din nan
dokar da mahaifin yarnyr ya kafa masa ita da
sauraynta wanda ya taho tun daga canada
sam ya hansu kusanci juna,sai dai nesa nesa
nayi kasaqe lkcn da ya fara balbala fada lkcn
daya kamasu suna kissin, nayi rewindn har sau 2
yaci gaba da fadan cewa,bazan yarda da wannan
sakarcin ba,tunda ba aure kuka yi ba
hankali na ya tashi,na shiga rudani,lallai yaya ni
ya mayar er iska, miyau dinsa da ya zuba min a hannu, ai shima fasararsa daya da wannan, tun har ya watsa mun a fuska, nufin sa in sha kenan!!!
na shiga 3 wani irin birkitacen yanayi na tashin
hankli,ko ya fara shaye shaye ne? Tambayar
dana dinga nanatawa a zuciata kenan,idan ba
mashayi ba wanda ya rasa hanklnsa da
natsuwarsa yaushe hakan zata faru a tsakaninmu
innalillahi wainna ilaihi rajiun, agaskia
abubuwansa gareni sun canza matuka.na fada a
hankali tare da dafe kaina kamar ina fama da
ciwonsa
kwalla suka zub mani,dole in samu ya abdullah
don fada mashi wannan gaggarumar matsala
Aikinsa kenan idan yana mani fada yace na
maidashi daniska,ashe ni ya mayar ban sani
ba..amma bari in samu abdulla zan fara
tuntubarsa da maganar tare da kwatanta masa ni
abin da nake zargi muji me zaice
ke lafia kika qura wa wuri daya ido kina zubda
kwalla?
Duk da tambayar tata tazo mani kwatsam a
bazata.kma hnklna ya tashi,krijina ya buga sai
dai hakan bai hanani tattaro natsuwata ba da ke
neman tarwatsewa
na fada mata cewa ina tausayawa yaron da
yarinyar dake ckn film din ne
toh Allah ya sauwake maki ta fada tare wucewa
ckn dakinta
ya abdulla ya shigo ckn uniform din NYSC. Zai
tafi aiki
albishirinki
nace goro.ckn doki da murna
sati mai zuwa laraba result dinku zai fito
na daka tsalle ina murna
daga daki anty ta fito tana tambayr lafia? Ke
kada kaset din nan fa ya haukat....
Anty bashi bane ba yanzu ya abdullah yake min
albishr da nxt wk result dinmu zai fito
oh congrats.ta koma cki abinta
shi kuma yaya yayi breakfast ya tafi..anty ta
leqo nafa manta faruk yace kiyi masa faten
dankali shi zaici da rana da drinks mai dadi
nace toh tare da miqewa na nufi kitchn
mislain karfe 2 ya dawo lunch
ina daki naji anty na kwalan kira na fito da
sauri,ta dago mani kwalin,.. sabuwar waya aka
sawo maki
amma nagode,na fada ina mai qarasawa inda
take,ckn yar dariyar murna,na duba da kyau duk
da ban bude kwalin ba wayar tana da kyau ta
burgeni
bude mu gani inji anty
na kuwa bude,wai Allah dadi ya cika ni, daman
ina son wayata ta zama unique,kuma kalarta pink
sabda shine my best color
Shuuu i752 ne sunanta,yar madaidaiciya
na kalleshi cke da murna nace nagode yaya,Allah
ya qara bude
sai da yayi murmush sannan yace amin.motarki
ma na nan tafe nan da kwana shidda in Allah ya
yarda
dadi ya qara firgita ni nace godia nake yaya
na sanya maki layn mtn,zain da glo sabda triple
sim ce.kudi kuma ba yawa 5000k idan kika cinye
da wuri toh ki nemi tsohuwar ta siya maki ya
nuna anty da yatsa
mukayi dariya gaba daya tare da qara godia na
wuce ciki
ya muktar na fara kira da wayar aiko munsha
firar mu har sai da aka kira la'asar sannan
a falo ina ta yan latse latse na don gano sirrin
wayar,babu inda bana shiga
anty da ya abdulla sai tsiya suke mani wai ba
sabun ba..iyakata da su murmushi kawai
ban da dade kwanciya daki ba,naji qara alamun
text mssg ya shigo
lamba na gani ba suna
toh waye? Ga abinda ak rubuto
"though a moments glimpse fresh ur image
clips,ur zeal lyk ur beauty shines,ut success
immense exuberant concern n scaring qualits
undiminshed by yearing
gud nyt n hav a speedy rcvry,its me faruk, save
my number
na karanta, na qara karntwa,amma na kasa
fahimtar inda wannan saqo nasa ya nufa
i was con fused akan me yake nufi
Na kasa yanke huknc akan mssg
ina haka wani ya qara shigowa,nayi saurin bude
wa ko na sami amsar farko.abin haushi sai naga
yace bako godiya ko?
Tambaya ce wannan ko raini?ko da yake kada
nayi saurin daukar abun da zafi,it seems kamar
ban gane turancin nasa ba ,ya danyi mani
tsauri...sai kawai nai masa reply kamar haka
"sorry, and long silnce doesnt mean u r 4gtn,d
prob is d inablty 2 figure out d best wrds 2
qualify u..i'm really glad tnk u n nyc nyt too
na tura masa,,ban bata lkc ba nayi servn number
sa
bacci mai dadi ya fara yin gaba dani
a hankli wayata ta fara rera waqar yori yori alamr
kra ne ya shgo
haka akeyi na tmbyi kaina,toh lallai ko akwai
matsala.saboda ban hada baccina da komai
ba,dole ne na ringa kashe wayata na dauka da
sauri nace hello
kin fara bacci ne?
Uhm kawai nace
meena na kasa yin nawa,,yadda ya fadi
mgnar,sai tausayn sa ya kamani,nace me yasa?
dagajin yadda yake maganaar kasn yana ckin
bacin rai
meena ayau nayi kukan maraici
hankali na ya tashi,sai naji alamar yana zubar da
kwalla
na tabbata da abba nada rai babu wanda zanyi
wa kuka
matsala ta dami zuciata na rasa wanda zan fada
wa na sami sauqi meena,,ya fada a hankali.ina
tunanin rayuwata tazo qarshe
wai me ya faru? Na fada hankali na tashe...kina
iya fitowa falo?.yaushe? Na bukata..yace yanzu
gaskiya bazan iya ba tsoro nake ji
ba gani ba,me zai kamaki meena?.ya fada kamr
mai shirin rushewa da kuka
bazan iya ba
toh ni inzo dakin ki?
Na zaro ido ckn mamaki,tamkar yana a
gabana,,a'a wlh..na kalli agogo karfe daya da rabi
fa...ya qara qasa da murya toh shine me don
nazo dakinki yanzu munyi magana?
Kai yaya,bafa zan yarda ba, kayi hakurin gobe...
Mutuwa zanyi matuqar na kwana da wannan
maganar a zuciata
nadan yi shiru cike da alajabi sanna na ce kana
iya fadi mani yanzu
bani da enuf crdt a wayata
kashe na bugo
mtseew yaja wani dogon tsaki,tare da kashe
wayar..nayi ta bugawa amma yaqi dauka
daga qarshe ma naji ya kashe wayar baki daya
Na kalli wayar raina bace,shin ni kadai yaya ke
yiwa wannan abun ko kuwa?ya zama dole na
sami ya abdullah muyi wannan zancen da shi
ko yana la'akari da canjin da ya faruk yayi kuwa
suddenly?
I'm his ynger sis,d same mum n dad,y is he
treatnd me lyk a new gal frnd?
Gaskya na gaji,ya abdullah zan sanar,kuma naji
cewa shin haka yake yi masa shima,ko kuwa ni
ya raina
idan har ya tabbatar mani da cewa,lallai ni kadai
yake yiwa haka to zan tattara kayana ba tare da
kowa ya sani ba,na gudu zuwa garhi,saboda
gaba ban san me zai kasance ba
da wannan tunane tunanen in koma can in saki
can,bacci yayi awon gaba dani
Karfe 4 na yamma ya abdullah ya dawo kamar
kullum daman zaune nake ina jiran
dawowarsa,anan harabar gidan bisa rest chair
ya karaso yana fadin,ni kike jira? Toh gani miye
labari?
Haushi ya kamani,nace na lura baka dauki
maganata serious ba,da safe lkcn danayi maka
waya kaqi barina ko maganar na qarasa,amma
ka kashe wayar
yayi murmushi,me kike son nace maki?kin san
cewa ina wurin aiki,sannan kin kasa zuwa strait
2 d point,kina ta yan kame kame,ni kuma ga ni
bana iya fahimtar ki,ta hakan yasa na kashe don
nasan zamu hadu yanzu,kamar yadda na baki
lokcn
wai me ya hadaki da yayan? Saboda ni kaina na
kasa gane abinda ke damunsa yan kwanakin nan
shekaran jiya dakina ya kwana, wai baya jin
dadin jikinsa,sannan gidan ya damesa, baya
sonsa
naje wurin anty jamila ina tambayarta ko sunyi
wata yar hatsaniya ne tace a'a ,kuma ta yadda
da ya kwana
toh jiya kuma da magrib ya sameni yana ta
kuka,wai yayi rashin abba,sannan lallai yau ya
tabbata maraya,ke ni ma har ya sani kukan
mun jima muna kuka,daga karshe ya shaida mani
cewa,ya samu matar da yake so ya aura,amma
baban kano da baban garhi sunce matar bata yi
masu ba,shi kuma yace ita yake so.to kinji
matsalar dake damunsa a tunani
wacece yarinyar?na tambayeshi
wlh bai sanar dani ko wacece ba
na kwashe yadda muka yi dashi jiya da daddare
na fada masa,
toh ai kinji meena ya fada tare da tsuke
fuska,duk duniyar nan yaya baya da wadanda ya
fi kusa dasu daga ni sai ke,kin san ko da can bai
yarda anty ta shigo maganar sa ba,wanda ta
shafi yanuwansa da danginsa ba
gaskiya laifinkine,saboda ai atleast sai ki fito
falon kamar yadda ya bukata,shi yana ganin mu
kadai zai fada mawa ya samu sauki
Da bai son mu bashi shawara da bai tuntube mu
ba da maganar..maganar miyau kuma ai kema
kin san wasa ne ya ke,ya dauke ki da wata
manufa yaji me?
Bani son irin wannan shirmen tunanin hauka kike
zaki ringa zargin dan...
Nifa ban zargeshi ba
idan baki zargeshi ba mi ya kawo wannan
maganar mts ya buga tsaki..lallai ke yarinya
ce,ni wlh nayi tunanin kina da hankali, ashe da
sauranki
ya miqe tsaye ni zanje nayi wanka
shiru nayi ba tare da nace komai ba
ina nan zaune har yayan ya dawo,nayi saurin
miqewa na taroshi,tun kafin ya fito daga mota na
bude masa kofa tare da fadin sannu da zuwa
ko kallo na baiyi ba,bare na sa ran amsawa
na miqa hannuna da sauri kawo jakar na shigar
maka da ita
nagode kawai ya fada,tare yin gaba abinsa
don Allah yaya kayi hakuri,wlh... Wani kallo ya
jegeni da shi,maganar ta tsaya don kanta,amma
duk da haka ina biye da shi a baya
a bakn kofa mukayi kicibis da anty wai zata je
gidan yayarta ta qara ganota sabda an sallmota
daga asibt
toh kawai yace muka yi ciki
maimakon ya zauna falo yadda ya saba sai
kawai ya wuce dakinsa,na kuwa bishi saboda
hnklina ya gama tashi da ramar da naga yayi
tsakanin jiya da yau kawai
Gashi kuma sai ya koma mani kamar abban mu
sak.ko kallona baiyi ba,yayi kwanciyar sa bisa
gado,,na tsugunna bakin qofa na jingina da bango
don Allah yaya kai hakr
ki tashi ki bar min daki tun kafin ranki ya baci,ko
don kinga cewa ina tariraiyarki kwana 2 shine
yasa kike neman ki kawo mani raini
ya dan tsirtar da miyau,wlh kinyi kadan.shawara
ce na nema kika gwasaleni,toh insha Allah bazan
kara kwatanta hakan ba,saboda bake kadai ce
yaruwata ba,ko abdullahi na tsaya kansa alhmdla
ya isan sharen hawaye,don haka ki fice man
daga daki
zafin maganar sa ya sanya na rushe kuka tare
da cifa kaina a cinya
baiyiwa kizo har dakina kina yi man kukan babu
gaira,ban zage ki ba,ban kuma dukeki ba,sabda
haka kukanki zai iya janyo miki hakan ya
faru,gara ma ki rufawa kanki asiri kawai ki fice
man daga daki
don Allah kayi hakuri ni abinda yasa naki fitowa
tsor..
Nace zanzo dakinki ba kika hana? Ko cinye ki
zanyi,kuma kina maganar falo ke kadai nace ki
fito falon ki zauna
kawai ku mata don dai Allah yayo ku da karamar
kwakwalwa mts yaja tsaki ki tashi meena ki fitar
mani daga daki
na qara fashewa da kuka don Allah..
Ke!!!.
Ya daka mani tsawa,ki daina hadani da abinda
yafi qarfina,,ina son kadaicewa in samu hutu
kawai ki fita
raina ya gama baci,wannan

Please Login or Register in order to submit comment