Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Allah yaya baka ckn tsarin mazan da nake so in aura ta fannin kyau, kudi, ko wani abu wanda ya shafi wannan bangaren, sai dai kawai kullum nakan yi maka addu'ar Allah saka maka da alkhairi bisa ga rikon da kayi mana ni da dan uwana, ta hnyr ba mu ilimi da tarbiyya mai kyau kasan a rayuwa... Babu tsammani muka jiyo sallamar ya mukhtar. Kafin hafsa ta rufe bakinta wurin amsawa ya kunno kai a dakin, ganin yadda mukayi tsaitsaye fuskarsa ta nuna alamar tsarguwa. Hannu kawai suka ba wa juna ya juya ya bar dakin. Da yake ba kwana yaya mukhtar ya yi ba a ranar ya koma, amma kafin ya tafi sai da ya kara jamin kunne da na bi a hankali sosai, to ka wai na bishi dashi, ya faruk kuwa bamu qara ganinsa ba sai dare, misalin karfe takwas muna kwance daki na ji Baba na kwallan kira, da hanzari na fito a rude, kila wani abun ya kulla, abin da kawai zuciyata ke bani kenan har na iso tsakar gida inda ya ke zaune bisa tabarma yana cin tuwon dawa miyar lalo. Baba na gani na fada tare da tsugunna wa gabansa, ina ta zaro ido kansa sunkuye yana lomar tuwon ya ce Faruk ke kiran ki a waje, ki amso sako.na danyi shiru lkcn ne ya dago muka hada ido, ko baki ji abinda na fadi bane? Naji Baba na fada a sanyaye, tare da mikewa nayi waje, da man akwai yar karamar hijabi a wuyana.
Ko da ta isa gurinsa, ya tsareta da. Idanunsa kamar zaiyi kuka, ya ce ki taimaka ki ceci rayuwata, wallahi ina matukar kaunarki, ta amsa masa da cewa gaskiya yaya kayi hakuri, ba zan iya zama da kai amatsayin mata ba, ina, ba zai yiwu ba, ya sunkuyar da idanunsa yana hawaye, can kana ya mike ya goge hawayensa ya ce, na gode kanwata, Allah Ya baku zaman lpy da shi wanda ki ka ce kike so...
Kawai ya fice hawaye na cigaba da zubo masa.
Nan ta ji tausayinsa ya kamata, da ta koma tunowa da Yaya Mukhtar inta, sai tayi murmushi ta shige ciki.
Akwana atashi ba wuya, ana ta shirye shiryen bukin Mukhtar da Meenah..
Sai murna suke, amarya da ango, shi ko farukh bai kara ko lekowa gidan ba sai ana saura kwana 1 da daurin aure, ya zo mata da kudi masu yawa cikin enbelop, ya ce gudumuwarsa, sannan da kayan daki ma duka shi yayi....
Ranar daurin aure yazo, aka daura aure.....
Amarya sai lokacin ta danji hankalanta ya dan kwanta, manya da iyaye duk suka ja mata kunnuwa da zaman hakuri gidan miji, ta hakura da dukkan abunda ya shige mAta ta fawwalawa ubangiji mai kowa mai komai, sannan kowa dai ya fadi bakinsa, kamin a dauki amarya akai gidan miji....
Ahaka aka tafi da amarya da a lullube har aka kaita aka baro dakinta, tana lullube.a hakan tana jin kirjin ta na bugawa, ko maiye dalili ta kasa tantancewa, da ta tuno yanzu yayaMukhtar ne Angonnata sai ta dan ji sauki, amman bugun kirjin yaki tsayawa..
Can ta ji anshigo, ta kara nokewa cikin lullubinta ta na jin kunya, ko da ya zo kusa da ita kanshin tularensa ta shaka ta lumshe ido, tana fadi cikin ranta, yau kuma irin tularen Yaya yasa...
Kawai taji ya bude lullubin a hankali, ya sa hannu ya daga habrta, ta lumshe ido, sai cewa yayi, Ina farin cikin zamanki amatsayin mata a gari, ina son.....
Kawai ta bude ido, ta ce Yaya Farukh me kake yi a dakina??????
da Hada Hausa Book stories
GIDA BO KOSHI BA
¤¤10¤¤
Ai kuwa, ta rude shi kuwa sai murmushi ya ke, ta soma tunanin rabonta da sa Yaya mukhtar a idonta tun ranar da ya ya gargadeta da karta yarda Yaya farukh ya rudeta da kalamansa, nan ta tuna ko shirye shiryen bukinma awaya suke magar, kullun ya ke cikata da kalamansa na soyayya, can sai ta ce, ko dai bakinsu daya da yayafarukh..... tunanin me kike haka? Maganar sa ce ta dawo da ita hayyacinta!
Ya ce ni Farrukh ni ne mijinki ba mukhtar ba! Nan da nan ta soma matsanancin kuka, tana fadin ba na sonka, ba na sonka, kuma ba zan taba sonka ba, ka cuceni ka ci amanata, kuma ba zan taba yafe maka ba, kuma dole ka sallameni ya......
Ba ta karasa ba ya rufe mata baki da tafin hannunsa, kawai ta galla mai uban cizo, nan ta rapka mishi kyawawan mari ba adadi..tana kara kai masa duka a kirji tana kuka, sai da ya bari tayi mai isarta sannan ya rungumeta yana kokarin lallashinta, kawai ta tureshi sai da ya bugu sosai kamar ba mace ta turashi ba, ya durkusa yana kuka kaman wani mace, yana bata hakuri, meena kiyi hakuri, ki min kowace wulakanci, amman ki daina ambaton saki,,,,, nan ta yi shiru tace ka fitarmun daga daki ban son ganinka...
Kaman wani soko yace tom ya fice, a haka kowanne ya kwana da takaici.(Daren farko)
Akwana a tashi gurin Allah ba wuya, yau watanninsu shida da aure, wulakancin yau daban na gobe daban, shi ke mata komai, kai wani sa'in har sashi girki ta ke shiko yana biye mata saboda so da kauna, a hakan ta soma makaranta, en wajen aikinsa ma duk sun san yadda ya ke ji da ita, ita kuwa ko a jikinta.
Abu daya ya daure mata kai har yau bata kara jin motsin yaya mukhtar ba tun wancan lokacin. Wata rana tana dawowa daga makaranta, ta samu go slow. Dai dai cikin go slow din wata mota ke kusa da taa ta, wani ta hango kaman yaya mukhtar yana washe baki da wata kusa da shi, zance suke akan zai aureta, abin ya daure mata kai, nan yake cemata kema kin san ke zan aura, er uwarcan tawa ma ba wani sonta nake ba tun lokacin balle ma da yanzu na huta tayi aure tuni!!! Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un abunda kawai take ambato ke nan, can ta kwala masa kira Mukhtar!!! Ya juyo, ko da ya ganta, be wani damu ba, sai suka cigaba da tafiyarsu.... Ita kuwa da kyar ta kai gida, kanta na mugun sarawa ta ji zazzabi ya lullubeta, kawai ta kasa daurewa ta kira layin hafsa ta zayyane mata komai... Nan hafsa ta soma kwantar mata da hankali, ta ce ai daman halinsa kenan amma,
Ki dai kwantar da hnklnki,ki kuma kama
mijinki,wlh meena kowa sai cewa yakeyi,kun
dace da juna, kuma kinyi sa'ar miji. Dangi kmr su
cinyeku da mgn.
Ngd hafsa. Na fada a sanyaye na kashe wayar.
Na rasa me zanyi,kuka ko me? Hnklna idan yayi
dubu tashe yake,kafin kace me? Zazzabi ya
dawo,jiki ya fara rawar sanyi ga matsanancin
ciwon kai.
Kudundune nake cikin bargo,jikina kuwa kmr
mazari rawa kawai yakeyi.
Haba shi yasa ya mk baya zuwa saina
roka,shima a gurguje zan gnsh,duk dadin bkn da
yake yi mini wato yaudara ce,lallai maganar yaya
ta fito, da ya ce cikakken dan duniya ne.
Yana da wacce yake so zai aura a legos,ni
haukan banza nakeyi kenan? Kullum hnklna yana
kansa,na damu kaina akan ya shiga wnai
hali,kokarina kullum ya faruk ya hkr ya sallameni,
kai jama'a ashe ya manta da ni yana can ya
rungumi budurwarsa ta gsky.
Wai ko ya aureni daman ya making mind dinsa
sai ya aureta,kenan ni dole na zame masa ba
don yana sona ba.ita ce yake wa son gsky.
Kwalla suka zubo mini,ina zan kai hakkin ya
faruk? Mutumin da yasan ciwon kaina,yake
kaunata kmr ransa,shi yasan cina,shana,sutu
ra,lafiyata da kuma ilmina, bai taba gajiya da ko
daya ba kullum kara nuna min kauna yake ina
gwasale shi.
Yau kadai ta isheni ishara,da gayya nace, Fura
zan sha. Amma ya tafi ya nemo mini, don na
bata masa rai naci indomie kada furar ta samu
shiga,bai nuna damuwa ba,dukda wannan bai yi
fushi ba,dai da ya tmbyni me nake marmari.
Na ci kuka kmr raina zai fita,ciwo kuwa ya karu
musamman ciwon kai,sbd uban kukan da nake
faman ruzga.
Ina nan kwance har aka kira sallar azahar,krfe
1:30 naji karar shigowar motarsa,lkcn nakai
makura a galabaita.
Ji kake jim jim ana ajiye kaya lkcn daya shigo. A
tunaninsa bacci nakeyi,ina jin ya zauna bkn gado
yayi shiru.
Nishin da nake yi ya jawo hnklnsa,da hnzr ya
hawo gadon tare da yaye bargon, Innalillahi wa
inna ilaihi raji'un. Meena jikin ne haka? Cak! Ya
daukeni bisa kirjinsa kmr wata 'yar
yarinya,turarensa ya kara rikitan kwalwa.
Gudu gudu haka ya fito dani ya saka mota,kmr
wanda ke shirin tseren motoci ya figeta a guje
mukayi asbiti.
Yan aikin gidan kowa yayi cirko-cirko, kamar
mahaukaci ya daukieni da gudu yana fadin,
Doctor! doctor! doctor!" fitowar likitan yasa shi
yin shiru, "please duba mini ita, jikinta yayi zafi
da yawa,ta galabaita doctor taimaka""kwantar da
hankalinka yallabai,komai zai zama normal muje
wancan dakin". muna shiga ya kwantar da ni bisa
gado, na dan kalleshi a galabaice na maida idona
na rufe ciki da matsanancin tausayisa.Babu bata
lokacin likita ya fara aikinsa,ya sanya mini karin
ruwa da allurai,daga nan bacci yayi awon gaba
da ni.Ban farka ba,sai wajen biyar na
marecce,zaune yake bisa kujera daga gaban
godan ya tallabe fuskarsa da hannuwa yana kallo
na.Ganin na bude ido ya sauke hannun tare da
matsowa,"yaya dai meena? jikin da sauki ko
akwai matsala?" "da sauki,jikin ne dai kawai ba
karfi""Dole ne wannansai a hankali zai koma
normal.Ga furarki na dauko miki,ko ice-cream din
zaki fara sha?
"zan sha furar"Na fada a hankali.ya tallaboni ya
jingina mini filo,sai da ya bani ruwa da roba na
kuskure baki na,sannan na sha furar wadda shi
ne ke bani ita a baki.Na kura masa ido ina kallon
sa ciki da tausayi, idona yayi narai-narai alamar
kwalla.yayi murmushi,"ya ya dai ?tsikar jikina ta
tashi,na ji wani abu yana ratsa jikina kamar an
tsikaran allura."Me ne ne? ya kara fada a hankali,
nayi saurin sunkuyar da kai ina murmushi."surpr
ise!!"ya fada a hankali.Na dauke kaina alamar na
koshi, ice -cream din fa,na miko? Na dago kai
alamar "Eh".Duka robar na shanye yaji dadi
haka,sannan ya maidani na kwanta,"Bari naje
gida na dawo kinji? Nace to.A hankali. Ya yi
dariya tare da girgiza kai, ya fita yana dan
waiwayena,ko mamakin kallon da nake yi mishi
yake yi?Na tambaye kaina.kawai na sami kaina
da jin wani irin nishadi da annashuwa na nemi
ciow na rasa,kawai matslata rashin karfin jiki.Na
lallaba na sauko na shiga toilet na yo alwala,ina
sallame sallar la'asar naji motsin bude kofar.
Merry da Grace ne gaba su Emmanuel na binsu a
baya,rike da ledoji.Grace ta ajiye ta
hannunta,wadda ke dauke da kula katama da
babba, sai mercy ta rabe tata lemu ne da ayaba,
apple da kuma inibi a ciki.Su Emmanuel kuwa
lemuke ne da kayan tea a cikin tasu. "Sannu
Aunty" Nayi murmushi,tare da mikewa ina linke
hijabin,yauwa merry,ya gida?Ba ta amsa ba,su
Emmanual suka fara,"SannuAunty,Allah ya baki
lafiya". Nace,Amin". "Oga ne ya kawo mu yace,ki
yi hakuri zai je ya dawo yanzu,bazai dade ba"
Nace "ba matsala" "Ga abince nan yace mu baki
kice,kafin ya dawo"."Me ne ne? Na bukata ina da
yatsina fuska,don ba kamai nake son ci
ba."Farfesun koda ne soyayyen dankali,akwai
kuma yamballs a ciki"
Na fadada murmushina,"Amma kun kyauta,kamar
kunsan abin da nake son ci kenan".Grace ta
cabe,Oga ne yace ayi miki,wai shi ne best food
din k""Zuban na ci bada yawa ba" Na yi hakan
don kada zuciyata ta samu nasarar nazarin wani
abu.Naji dadi abincin nan sosa,saura kadan na
karasa cinyewa suka turo kofa,Alhaji Habibu ne
da Aunty Asiya, sai Alhaji Garba da Aunty Hadiza
matarsa,shi Oga ne karshen shigowa.Very
good,taci abincin ko merry?"Ta rusunar da kai
"yes Oga.ya zauna bakin gado, sannu meena,ya
kike ji yanzu?.Duk kunya ta kamani yadda ya
wani shige mini,na kasa magana, Alhaji Habibi ya
ce,Malam ka fa takurata......"Me ye takura anan
Habibu? Alhaji Garba ne ya katse,duk suka matso
bakin gado suna fadin,sunnu Amin".A hankali
nake fadin yauwa"Aunty Hadiza ta kara
matsowa, "Wata nawa ne Aminatu? "Sam ban
fahimci tambayarta ba,nayi tunanin ko maganar
hutun makaranta ne takeyi,nace sati uku aka
bamu" Duka suka kyalkyale da dariya.ya faruk ya
dafa kafadata,"wai cikin suke magana,wata
nawa.......""Wallahi bani da ciki"suka kara yin
dariyar.Nan da nan na kule,wannan wane irin
wulakanci ne,me suke nufi da ina da ciki,ko na
zama yar'iska a nufinsu?Rainin hankalin yayi
yawa,a gabansu Merry za'a ci mini fuska?"Na
fada musu ba ciki gare ki ba,amma sun ki
yarda"ya kalli Aunty Hadiza,"kun yarda yanzu ko?
Ni idan nayi karya ita ba zata yi ba ko?.Ai duk
bakin ku daya".Alhaji Garba ya fada.Na
sunkunyar da kai na saki ajiyar zuciya a
hankali,sai yanzu na fahimcesu.Basu bar asibitin
ba sai bayan isha'i,nayi ta mamakin irin rudewar
da yayi akan ciwon nan,har da tattaro su
Aunty.Da zasu tafi ko wane ya ajiye mini rafar
kudi. Alhaji Habibu ya ce,"mun dai zo wannan da
tsiya tunda tashi na kamaka aka yi mana,da
bamu zo ba mun shiga uku".suka kyalkyace da
dariya.yaushe zaka dawo ta arziki tunda wannan
ta tsiya ce?Gobe zamu koma gida yau din ma
don likita ya dage shi yasa na hakura,amma gobe
tara a gida zata yi mun".
Ma same ku gidan gobe".Alhaji Garba ya
fada.muka yi sallama suka tafi,har sun kai kofa
Aunty Asiya ta dawo,kayan nan da na baki ki dai
na shansu haka nan,kinji?"ko kallonta banyi ba,ta
juya ta fice da sauri.ba tasan cewa,ko tabasu
ban yi ba,tunda ta bani,ko drower ban taba
budewa ba balle na taba su.Karef takwas ya
maida su Grace, ina nan kwance na saka wancan
na kwance wannan,har ya dawo daga kaisu.Daga
shigowar sa har zamansa akan idona,wai ashe
haka yake da kyau?Dazun suna magana da su
Alhaji Habibu baka taba cewa,abokinne kamar
yayyensa ne.ya kalleni,sai naga yayi murmushi
ya dauke kai.Ban so hakan da yayi ba,har dan
kara gyra kwanciya nake yi yadda zan ganshi
sosai."wai me ne ne meena? ya fada yana 'yar
dariya,kumatunsa ya lotso point din ya
bayyana,kunya ta kamani,na snkunyar da kai ina
murmushi.Kokina bukarta wani abu n, kin kasa
fada?"ya kara tambayata yana ci gaba da yar
dariyansa wadda na fi komai so a tare da
shi,idan ya yi ta tana kara wa funkrsa kyau fiye
da in yayi murmushi."Uhm-uhm" Na fada a
hankali.to kallon na mene tun dazu na lura da
ke,ko mosti nayi idon ki na kai na"Kamr na bude
kasa na shige don kunya,Allah ba komai"Na fada
ina yan kame-kame.Haka ake so aji,ba wani
abun".ya miki,ni kuma na gyar kwanciyata,ma'a
na na matsa inda zai kwanta yau kawai na tsinci
kaina da son jinsa kusa da ni.Idona kansa ya
gama shirin kwanciya,abin haushi,sai na ga ya
dauki filo ya kwanta bisa kafet.Na bishi da kallo
na takaicr,ya dago ido muka hada ido,na yi saurin
dauke kaina,Good night'ya fada yana murmushi.
Hada Hausa Book stories
GIDA BAI KOSHI BA
¤¤11¤¤
Ban san lokacin da na harareshi ba.sai naga ya
bushe da a,ya maida kansa a filo tare da rufe
idanu,yana fadin tuba nake,mu kwana lafiya"Don
karfin hali,ni ma sai na maida idanuna na rufe
wanda nasan yaudarar kaina kawai nayi,babu
wani alamun bacci a tare da ni.Ba'a fi minti
talatin da kwanciyasa ba,na ji yana fitar da
nufashi a hankali,alamar ya samu bacci.Zaune na
tashi na tsura masa ido.lallai Abba yayi gado,shi
ma haka yake barcinsa,ya kududune wuri daya
kamar karamin yaro,kana hango murmushi a
fuskarshi,idona ya kai ga hannunsa,yatsun
hannunsa zara-zara ga dogayen akaifa an
yankesu dai dai,sunyi kyau abinka ga fari.Wannan
tsafta ta yaya daman likita ne.Kafarsa na birgeni
da gani zata yi taushi,ko ita kadai ta isa ka gane
yana hutawa a rayuwarsa.Nayi murmushi,"miskili
ya faruk.
jan class kiri-kiri yau ya kasa bacci kusa da
ni,saboda ya lira ina son haka shi ne za'a ja mini
aji shiga miskili"Yau kadai zan hakura,gobe
dole......motsawar da yayi yasa na kwanta da
sauri,abin haushi ashe ba tashi zaiyi ba,juyawa
yayi.Ban sa ya bani baya ba,na kalli
kansa,sumarsa liya-liya kwance bisa wuya ta sha
gyara,yana da girma,amma ba kato ba ne,gashi
moderate {tsakiya).maganar maryam faruk ta
fado mini a rai,"Ina sonki da babana"Haka ta ke
kiransa, saboda sunan babanta ne,ko ni a
gabanta sai dai nace yaya kawai,ba dai ya faruk
ba."Meena kinyi sa'ar miji wallahi sweety(haka ta
ke kiran mijinta) yake fada mini a office dinsu
babu wanda bai san yana son ki ba.Ashe tun kina
yarinya yake sonki,har zolayarsa General Director
ke yi,yana ce masa,angon Amina,baban Amina
sannan kuma yayanta.lokacin da kika fara sanar
da ni baki son sa,ban yi bacci ba,kawai ina
tausaya masa.sweety kuwa kamar zaiyi kuka don
bakin ciki,wallahi sai an sha wahala,ga
kyau,kudi,takama,kasaita,sanna jan aji,kin san irin
wadannan mazan tsada suke yi yanzu.Ina
anfanin shegen surutu ga namiji kamar aku?tun
ana fadin gaskiya har a kai ga karya?Amma na
miji na basarwa yana takama shi ne mini mai
class,ki gode wa Allah,wallahi kada ki butulce
masa meena.....ke bana son ji.Wannan kalma ita
yasa ta yi shiru ban mantawa fushi tayi lokacin
koda muka fito lecture tafiyata tayi.Dai-dai
lokacin da ya kwants rigingine,kansa na kallon
silin,wani bugun zuciya ya zo mini da sauri.Anya
ba son ya faruk ke damuna ba,abun fa ya fara
wuce misali.Murmushi nayi,don na gan
amsar,lallai sonka nake yi ya faruk,har cikin
raina.kwalla suka zubo mini,tausayinshi ya
kamani,Na yi kamar na koma bisa kafet din don
tsannanin begensa.Ban taba jin abin da nake ji
ba,ko daman ba son ya mukhtar nake ba da
farko?wannan yanayin sam daban yake da wanda
naji baya a kansa.
Shin ko maganar mutane zata tabbata ne da
suke ce,ina son sa?yaushe nake sonsa?ya aka yi
suka gane ni na kasa fahimta?ya taba fada mini
cewa,Meena kina sona,kawai tsabar kishina da
son zuciya......."Lallai na kusa yarda da
maganarsa,saboda akwai lokacin bana
mantawa,muna zaune a filo Aunty zata wuce ya
kamo hannunta yana fadin,come my love...."Na
banka masa harara,wadda na dade da tuhumar
kaina ko me yasa?Amma ban gano amsa ba,anyi
hak ba sau daya ba,ba sau biyu ba.Duk da
masifarsa a duk lokacin da haka ta faru sai dai
naga ya yi dariya ko murmushi.Na dafe kai
na,lallai akwai matsala,in haka ne ya faruk ya
ganoni yanzu shi yasa ya basar,to me ye
ma'anar dariya ko murmushi da yake yi?
Maganarsa ta fado mini,Ni faruk zan baki
mamaki, in don ni ne,sai kin nema da kanki"To fa
yanzu meye abin yi ni Aminatu? Na ja wani
guntun tsaki,haba lokacin dazai kawo kansa me
nawa ya gani?ni fa mace ce.Da kyar bacci ya
dauke ni,waien hudu saura.Don haka ban jima ba
naji yana tashina na tashi nayi sallah.Abu biyu ya
fado mini a rai,lokacin da na gama sallah.shin in
gaidashi ko in kyale?Ba tare da ba yanke ani
hukunci ba,na durkusa a hankali na furta, ina
kwana?"Murmushi yayi tare da tsareni da ido,ni
kaina sai da naji wani banbarakwai,na sunkuyar
da kai cikin jin kunya.Sai da ya mila,sannan yace
"ya karfin jikin?""Alhamdulillahi!"Na ba shi amsa
a gajarce.Da kansa ya hada mini tea na sh da
cake shi kumasauran frur jiya naga ya kara wa
ruwa ya shanye.ko me yasa ya ki bani da kansa?
tambayar da ta dade a raina,har muka
gama.Shiru babu wanda ya ce wa kowa kala,wai
me ye haka ya ke neman canza mini ? ko yan
tambayoyyin da yake mini ya kiya.Me ya hanaki
bacci jiya? kamar daga sama naji tambaya,nan
da nan na dimauce,sai kama-kame.da ke fa
nake,na ce me ya hanak bacci jya,ko kona tunani
bani ba ne?.
Nan da nan na kara diriricewa,kai wannan
mutumin shu'umi ne,kafin na bashi amsa likita ya
turo kofar.ya kallemu yana \yar dariya,ya nufoni
da file rungume.please Doctor taimaka mini ka
dubata,ta wahala da yawa"duk mukayi
dariya,wato yana kwaikwayon yaya jiya da ya
dauko ni a rude.Duk dokin sallama ne yasa ba
zaka yi wanka ba?A'a idan mun je gida ma yi,ko
meena?Na yi saurin dauke kaina.Ni kaina na fara
jin haushin kaina,ni wannan mayen kallon da
nake yi masa har ya kai ga ganewa.Takwas da
rabi ya sallame mu,da yake abonki ne da shi aka
tayami tatara kayan.Na kama yaye zanen gadon
da bargo,yaya yace,madam ba namu bane
wannan,ajiye" abu har kamshi suke da
shi.Tsohowar asibitinsa da na sani, sam ba ta kai
haduwar haka ba,lallai ci gaba da dadi a rayuwa,
Bas barni na dauki ko cokali ba, motar ma yaya
ya bude mini na shiga muka tafi,abin mamaki ko
kallona bai yi ba,ya maida hankalinsa a titi ni ke
satar kallon sa kamar munafuka.
Na fito ina 'yar miki ya kalleni cikin murmushi,"ki
je ki yi wanka".Na langabe kai,"kayan fa?" ya
guntse dariyarsa,"zamu shigo da su yanzu".Na
feso wanka na bata fiye da awa daya ina
tsafatce ko ina,shafar kanta yau ta
dabance,jikina ya dinga wani irin kamshi,saboda
hadin da na yi masa na body fantasies apple,
resberry,da kuma vanilla.Wani sabon leshi na
dauko sky blue dinkin riga da skirt ya yi matukar
karbata leshin,duka sawata daya,tun cikin
wadanda ya yi mini ne lokacin da na gama
makaranta.Das! ya zauna jikina don ma na yi dan
wuya ba kamar da ba,farin gazar kawai na shafa
masa,turai 'yar'adu'wa shi ne daurin kallabina na
yau ya fi na kullum,saboda gashina na fiddo
kwance bisa goshina,ya lankwafa ta cikin
daurin.Na yi murmushin mugunta,duk
miskilancinka na tabbata......miyau ya sarkeni
lokacin da ya shigo babu zato.Bai taba yi mini
kyau irin yau ba.kananan kaya ne jikinsa,bakin
jeans mai tambarin butterfly a baya,sai T shirt
round neck,sky blue,rubutun jikin rigar ya dau
hankalina,an rubuta,Tm waiting.Na kalli kwayar
idonsa,shin ko haka ya ke nufi a zuciyarsa,gayya
ce ta sanya.....Kin tsareni da ido,ke ba ki amsa
sallamata ba,baki kuma bani izinin shigowa
ba,kin barni tsaye kamar dogari".kunya ta
kamani,kwakkawaran motsi wannan dizgi ya fara
isata,idan yaga haka me zai hana ya basar,amma
don tsabar raini....."Daman chocolate da biscuit
dinki zan baki,ga su nan a kwalaye,ko wane
hurhudu ne,naga sabbin shigowa ne shi yasa,idan
sun miki dadi sa ki yi magana a karo miki"Wai
ina ya yi wanka? Na tambayi kaina,dariyasa ta
katseni, wannan wace irin tambaya ce
Meena?"kinyi tambaya kin kuma basar da ni.A
dakina nayi ko ba kya so?"Don taikaici sai na bar
dakin wannan shi ne nade tabarmar kunya da
hauka.Na shiga kitchen na tabbata ko shirmen
merry ya mantar da ni,sai dai na makaro,ko zama
banyi ba,na ji sallamar su Alhaji Habibu da Aunty
Asiya.Raina ya baci,bawai zuwansu ya bani
haushi,a'a zama na kasa da shi na tabbatar
idanuna ba zasu daina kallonasa ba,na dafe
kaina,"Ni Meena tawa ta magana" Ina haka ya
shigo,"Meena Asiya na magana".Na runtse idona,
Ina zuwa" Na ba shi amsa a gajarce.Tunanina ya
fita na saki ajiyar zuciya da karfi,Grace ta
matso,Aunty head ache?(ciwon kai)"
Na girgiza kai kawai tare da mikiewam bude idon
da zanyi naga mutum tsaye nan da nan jikina ya
kama rawa,Na rabashi zanwuce yayi saurin rada
mini,control your self.Da sauri na fice gabana sai
ya fadi,wannan na sani tuna ina yarinya,kullum
maimakon raguwa sai karuwa ma kaomai ke
yi,ga rawar jiki,wanan kuma kwana biyun nan ya
sameni.yawan kallonsa kuwa na barshi a
cewar,asiri yayi mini Zauna suke bisa lumtsa-
lumtsan na falon baki,ya wani rungumota ko
kunyata ba sa ji."salamu alaikum"Aunty ta yi
karaf,"wa'alaikumus salam"shi kuma na
amshe,"Amarsu ta ango mai dadin tuwo".Na yi
murmushi ciki da zolaya kamar yaron goye.Na
zauna kujerar da ke kusa da tasu,"ya karfin jiki?"
"Alhamdulillah" "Ba ki dai amai ko?" Na daure
fuska, "Wai ke Aunty wa ya fada miki ciki
gareni.......?""kyaleta Meena,ciki ma gareki sai
me?Kafin ki fara yi ita ta rigaki".Ya salam! jikina
ya bada wani dam!!!! kunya ta lullubeni,su kuwa
abin takaici dariya naga suna yi."Gaskiya bazan
dauki managar ban...."Grace ce ta shigo da
katon tire,Merr na binta a baya..suna ajiyewa na
shiga serving dinsu,ina satar kallonsa,mamaki
kawai nake bashi.kowa ya yi kat!!Ni kaina nan na
ci nawa,Aunty ta kalleni,"mu shiga ciki,mu yi
gulma zaki ce malama"ya faruk ya fada yana
dariya.Ni kuwa har da tuntube nake yi don
sauri.Mun dade muna hira,wani abin har kunya
Aunty ke bani idan ta fada,muna cikin cin abincin
dare Alhaji Garba ya zo banda Aunty Hadiza.A
nan ne nake jin wani sirri a ban
taba jinsa ba,"kasan Allah bazan maidata ba,idan
kuka dameni kuma zan cika dayan sakin ya koma
uku.Yanzu haka iyayenta sunyi fushi da
ita,maganar mutane ma ta isheta, karuwanci abu
ne mai kyau? kawai na kawo wa kaina cuta?
yanzu haka zuwana test biyu, Allah ya tsirar da
ni,sai na kai kaina? yarinyar na sha kamata gidan
dan iskan nan Alhaji Naziru donta maidani
sakarai ce mini ta yi kawunta ne,kuma harka
banza jiya bistoriya kawarta ke shaida mini ta
tafi saudiyya,itada su nananduwa da dubulle shi
yasa na kai Abba kano hutu,ko zai dawo Abuja
sai nan da wata uku."karuwanci?
Innalillahi wa'ina
ilaihi raji'u,lallai biri ya yi kama da mutum,nasan
wannan mutumin,shi ne wanda na taba rakata
gidan Aunty Hauwa sada muka biya, wai zata
gaida kawunta, ta barni a mota fie da awa daya
da rabi.sannan ta fito ko jikina ya bani Aunty
bata da gaskiya,saboda hakan da na karanta a
fuskanta,sai kame kame ta keyi. yana tsaye bisa
bene sai faman daga mata hanun yake yi,ta
maida masa tare da yi mini yake,wanda a lokacin
na yi tunanin dariya ce.Kash! Aunty ba ta kyuata
wa kanta ba wallahi.Bawan Allah ya faruk duk
sai da na kara jin tausayinsa.Har mota muka
rakasu,muna dawowa na shige daki,na tsak
wanka,ranar farko da na saka rigar barci fara yar
guntuwa duka iyakarta gwiwa,kamshi ko ta
ina,yau zan ba shi mamaki na haye gado ina jiran
shigowarsa ciki da fargaba.
Karfe goma tayi shiru,sha biyu kai har wajen
daya da rabi banji ya shigo ba,Nan da nan raina
ya baci,na lallabo a hankali na bude kofa.wayam
folan ba kowa,na kara sadadawa na leka na baki
shima ban ganshi ba.Na yi turus! Akwai
matsala,wato dakinsa ya tafi,me yake nufi?Na bi
shi can?Na girgiza kai, Never"Ciki da takaici na
koma na kwanta,duk wannan gayun nayi sa a
banza kenan?lallai ya faruk ya cika dan
wulakanci.karfe shidda na bude idona na
hanzarta gabatar da sallah,na fito kitchen cikin
wata matsiyaciyar sadda kalar kwaiduwar
kwai.Na fere dankali na dafashi batare da na
datsashi ba,na ajiye gefe don ya huce,sannan na
dafa nama na nikashi, daman na soya kayan
miya na hade da naman na kara ba su tsoro tare
da zuba spices da maggi.Na dauko dankalin nan
na dinga debe saman sannann na kwakware
tsakiyarsa in debo kayan miyan nan da suka ji
nama da kayan hadi in ciki ramin,na maida
murfin na rufe,har na gama sannan na kada kwai
na dinga tsoma dankali ina soyawa a mai.
Sadiq Halima mai kaunar ku akoda yaushe...
-Hada Hada Hausa Book stories
GIDA BAI KOSHI BA
¤¤12¤¤
Na gama kenan Grace ta shigo na ce,yauwa
muna da gyararriyar gyada? tace,"Eh Aunty an
cire jan kwafasar ta koma fara?" tace,kwarai"
yauwa debo mini kofi hudu" ta washe baki,Aunty
kunun gyada zaki y mana? "uhm!"Na fada a
gajarece.Tana kawowa na wanke ta tas tare da
fiddo ragowar bawo ta koma fara kal.Nasa a
blender

Please Login or Register in order to submit comment