Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wane irin mutum ne
da baya jin hakuri?na miqe tare da wurga masa
wayar da ya sawo mani
Allah ya qara baka hakuri,kuma ga wayar kanan
nagode.amma aba wata ni bani bukata
Zumbur ya miqe,ni kuma na kwasa da gudu
dakina,ina shiga na rufe kofar da danmukulli,Allah
ya taimakeni na yiwa kaina kiyamullaili,sa
boda
ina zare mukullin naji ya turo kofar ba tare da
yayi magana ba
na tabbatar da ban kulle ba,yau kashina ya
bushe,kuka na saki da karfi,hankali duk ya tashi
wannan wace irin rayuwa ce? Mutum kullun ckn
neman fitina
qarar danmukulli naji alamar za'a bude dakin
wani tsalle nayi sai hani tsaye tsakar dakin ina
zare eyes
a hankali ya bude kofar ya shigo,sai kyarma nan
da nan jikina ya dauki rawa,shi kansa ya lura da
tsananin tsoro da tashin hnklin dana shiga
don sai ya maida kofar a hankali ta rufe tare da
tahowa inda nake tsaye.yanayn fuskarsa ya qara
razana ni,nayi saurin zamewa qasa na tsugunna
tare da makalkale jikina kamar wacce ya yiwa
sabon kamu
nayi kasaqe!! Ina jiran naji ya shaqoni ko kuma
yasa qafa yayi kwallo dani,shiru har wajen minti
5 na dago kai inga ko fita yayi,saboda ko
motsinsa bana ji,tsugunne yake gabana ya tsare
ni da fararen idanunsa nayi saurin maida kaina
a hankali ya fara magana,rashin kunya ko
meena?ni faruk yau kikawi tsageranci don ki
nuna mani cewa u r matured enuf,kema kin zama
cikakkiyar mace
toh bari kiji wlh,wannan ya zama na 1 kuma na
karshe,kin san halina,,toh lallai kiyi notcn wannan
ban magana 2,sannan am alwys streat 4wrd
Kada mu fara haka dake saboda wahala zaki
sha,ladabi da biyayya na sanki da su,to ku riqe
kada ki bari su kubuce maki,
maganar waya kuma ban fahimce abinda kike
nufi ba..ina son ki sake maimaitawa
nidai kayi hakuri,na fada ahankali
bance kinyi man laifi ba,ina sin kiban amsar
tambayata
ai....ai
ai me?kike wani korar tumaki kawai malama baki
da hujja,ya jefoni da wayar idan baki so,kina iya
yarwa,saboda bata gabana,sannan idan kika qara
gigin irin wannan,Allah sai kin sha mamaki
kaima yaya na kasa gane gaskiyar damuwar ka a
kaina
shiyasa kika jefan da waya
na zaro ido wlh....kada ki rantse azumi zai hau
kanki saboda jifata kikayi don ki nuna
Allah ya baka hakuri bazan qara ba na katseshi
ya dalle mani baki da yatsansa baba.sai son
laifi,amma tsoro na biye bayansa,da son bada
hakuri,kin bani hakuri yafi goma
na murza labbana cikin jin zafin dallar da yayi
mani
ke bani son lambo ya fada
haba yaya da zafi fa
daman zafin nake son kiji..sabodanima kin
wahalar dani
kalamar tazo mani banbarakwai, nace na wahalar
da kai kamar yaya
maimakon ya bani amsa sai naga ya miqe tare
da komawa bisa stool din madubi na,ya zauna
tare da canza zancen da cewa
Meena aure zanyi amman su baba sunce yarinyar
bata yi masu ba,miye shawara
hakuri nabashi amsa a gajarce nima na koma
bakin gadona na zauna
bazan iya hakuri da ita ba gaskiyar magana
in kuwa haka ne wannan maganar tafi
karfina..tunda bazan baka shawara ba kaki
biyayya
kada ki kware mani baya don ke kadai zaki iya
taimako na a wannan auren
wacece yarinyar na tambaye shi,maimakon ya
bani amsa sai ya ci gaba da cewa
alkawari daya nake son kiyi mani,ni kuma na yi
maki alkawalin bazan qara baki miyau ba
kisha.sannan zan kaiki germany ki zabi motar da
kike so saboda zamani wlh duk tsadarta kin
yarda? shan miyau a kuma na ganni ina tuka qatuwar
motar kaina sanna ta zama mallakina ba tare da
tunanin komai ba yaya yace zaki iya?kin fa san
girman alkawari nace insha Allahu yaya zan iya
koma menene very good ya fada tare da yin wani
murmushi ina son gobe ian Allah ya kaimu na
hada da uche ya kaiki garhi kin san hausawa
hausawa na cewa gida bai koshi ba ba a bawa
dawa ba don haka maganar muktar ki soke ta
kice su baba NI KIKE SO KI AURA......
da Hausa Book stories
GIDA BAI KOSHI BA
¤¤6¤¤
iyakar abinda naji kenan ***********salati na
dinga ji ta ko ina,na bue idona a hankali biji biji
nake ganin kowa sai dai da alama ina ganin
duhun mutane wadanda bana iya cewa ko su
wanene a hankali suka dan washe amman ba
garau ba asibiti nake kwance bisa gao bakina da
hanci na cikin abun qarin iska wato oxygn ga
kuma qarin ruwa ana yi mani dr naji an kwada masa kira,tare da bude kofar
tare da bude kofar aka fita da gudu ban gane ko
wacce murya bace wannan haka ina jin muyoyi
da yawa ana cewa sannu amina tambayar danaji
wata muryar namiji yayi ita ta tuno mani da
maqasudidn zuwa nan na wurin wai meye ainahin
faruwar.....bai qarasa ba naji muryar mace na
baa amsa..na iso kenan naga faruk ya fito da ita
rumgume duk ta sandare,don wlh munyi tunanin
ta rasu...jin an anbaci sunan yaya nasyasa naji
numfashi na ya fara sama,na da nan naji ana ta
salati wasu kuma dama kuka suke yi pls gt
out,naji an fada lkcn da aka shigo daga nan ban
qara sanin inda nakeshiga
wannan karon koda na bude idanuna garau na
gansu,babu wata alama da ke nuna bacci ko
gajia a atare da da su.....an cire mani oxygn din
dana gani din dana gani daga farko ,amma har
yanzu akwai qarin ruwa a tare dani...lallai
hanklina ya dawo jikina..kwana nawa nawa atare
dani?bani da mai amsa mani tambayar nan ole
na hakura...na rushe da kuka lkcn dana tuna da
maganar yaya wannan waane irin balai ne? wai
ni...shigowar wani lkita ne yasa ya tsaida mani
tunani na amman har kkcn idanuna basu bar
zubar da hawaye ba...ya kalleni ya qara kallona
ya girguza kai ckn nuna alamar damuwa,sannan
ya jawo wani dan qaramin tebur ya zauna gaban
gadon daidai inda fuskata take ..muka hada ido
hada ido yai mani murmushi tare da fadin wipe
ur tears...banyi gardama ba na aikata hakan sai
dai ko hannuna ban baro daga wurin ba wasu
suka biyo baya .......amina kalleni da kyau
,sannan ki saurare ni tare da bani cikakkiyar
amsar tambayoyin da zanyi maki da fatan kin
fahimce ni.....na daga kai alamar eh..kin shirya
mutuwa kibar abdullahi?..tambayar tazo mani a
hargitse na rasa me zance masa saboda tashin
hankali dana
Ina nufin abinda na tambayeki,sbd a gsky kina
kan hanya. Wace irin damuwa kika shiga haka da
har zuciyarki ke neman bugawayau fa kwananki
takwas ana,alluran da muka yi miki banyi tunanin
dakin tashi zaki iya fada wa wani dogon tunani
ba,kamar yadda na fahimta. Ya dan lumfasa,kiyi
hakuri mu shawo kan matsalar ko,idan kika yi
wasa zaki iya barazanar rasa rayuwarki. Ya fara
lallashina a hankali tareda bani shawarwari ta
hanyar tsorata ni sosai. Ya lura cewa na nutsu
sosai,hankalina ya dawo jikina sannan ya fara
jero mini tambayoyi.
Mene ne matsalar data jefaki wannan tashin
hankali? Zan fara magna kenan ya daga mini
hannu,ban da kuka. Na goge idanuna,shigowar
nurse yasa naki magana, tana fita ana kiran
sallah,ya kalleni,bari na hada miki abinci kafin na
dawo.
Tea mai kauri ya bani da soyayyen dankali da
kwai,yace in cinye kafin ya dawo. Yasa hannu ya
cire mini karin ruwa,tas! Natada komai. Ina
gamawa nurse na shigowa,ta taimaka mini na
shiga toilet nayi wanka tare da alwala,don rama
sallolin da ake bina.lokacin daya dawo,maimakon
ya cigaba dayi mini tambayoyin sai naga ya
canza zancen ta hanyar kunna mana wata tashar
hoto mai dauke da wake wakensu masu kyau. A
hankali a hankali harna fara sakewa cikin kwana
daya,a kwana na 2 ne na fara damuwa naga ya
abdullah. Dadi ya kama dr,yace shi ya hanasu zo
sbd jikina amma inyi hakuri gobe za a sallameni
kuma shi zai mayar dani har gida. Nace to.
Washe gari ta kama juma'a,karfe 12 muka isa
gida cikin motarsa,babu abinda gabana keyi sai
faduwa. Duk iyakacin kokarin da naso inyi
alokacin ganin hawaye basu zubo mini ba na
kasa. Zubowa kawai sukeyi ba kakkautawa.
Gaisuwa kawai akayi dashi yace zai koma yayi
gargadin cewa a guji abinda zai kara tada mini
hankali. Hankalina ya tashi ganin baban
garhi,gwaggo maryam,baban kano,da kuma baba
auta.
Sannu kawai ake ce mani,ya abdullah kuwa ko
motsi ya kasa sbd ni kawai yake kallo duk ya
rame. Nida aunty muke zaune bisa kujera
doguwa,gwaggo maryam na gefenmu bisa
karama,ya abdulla na daga kasa da gwaggon,sai
su baba dake bisa dogayen dake kallon tamu.
Duk da yawan sannun da nake samu daga su bai
hana zubowar hawayena ba, maimakon su ragu
karuwa ma kawai suke.
Banyi mamakin rashin ganin yaya ba,sbd ranar
aikice. Baban kano ya gyara zama sannan ya
fara magana, bazai yiyu ace mutum lafiyarsa lau
har ya kamu da bugun zuciya ba,ke hajiya jamila
iyakar abinsa kika sani kena? Tace eh baba,kaifa
abdullah? Ya kalleni,a harabar gida na barta na
fita,ko dawowa banyi ba yaya yayi mini
waya,suna asibiti. Ganin halin da take ciki ne
yasa nayi muku waya. Kukana ya karu baban
garhi yace tsohuwa meya sameki ne?(da yake
haka yake kirana). Cikin tausaya wa gwaggo tace
goge hawayen kinji meke damunki? Na nisa
zuciata tayi min zafi raina ya kara baci hankalina
ya tashi matuka, ya faruk ne yace zai hadani da
uche.........na rushe da kuka,aka dauki salati. Ya
hadaki dashi kamar yay? Inji baban kano
wai muje garhi wurinku,nace, shi.....shi....
wai
shi.....kukan ya kuma karuwa
cikin kidima gwaggo tace wai shi me? Wai shi
nakeso zan aura.......
Ya abdullah na gani da aunty jamila a kwance
sun some.
Wuri ya rude da tashin hankali.da kyar aka samu
suka farfado,bayan sun sha watsa ruwa.
Gwaggo kuka mu kuka su bab kuwa kowane
idanunshi ya kada yayi jah!!!
Wannan yaro,wannan yaro naiyi mana adalci
ba,sannan ya tabbata kafaffe,marar jin magana
abibda baba auta keta nanatawa kenan.
Tun farko saida yaya hadiza tace hakan na iya
faruwa,amma kowa yai burus da
maganarta,maganar hausawa ta tabbata 'duk
abinda babba ya hango,yaro koya hau dala....kun
dai san karashen ehee'.
Dakata maryam inji baban garhi,ya
katseta,tsohuwa! Ya kira sunana,na daga kai na
kalleshi,jeki hado kayanki duka. Ya kalli gwaggo
dake shirin magana yace zata koma gidana na
garhi da zama. Ya abdullah ya rushe da wani irn
rikitaccen kuka mai ban tausayi.
Sole kayi hakuri barinta nan hadari ne tunda
harya bijiro da wannan rigimar,baban kano ya
fada. Cikin zubar kwalla aunty ta kallesu tace
akwai aure tsakanin su kenan?
Kwarai kuwa. Inji baban garhi.
Kirjina yayi wani irin dam! Ras!! Ras!!! Sbd
faduwa,kaina ya sara kwarai da gaske. Na dafe
kaina, wayyo baba na shiga uku,yau mun bani...
Ke dakata bari jawo mana banuwa. Inji gwaggo
maryam. Na kra rike kaina gam,don ji nake kamar
har wuyana don azaba, baba waye bare cikinmu?
Na fada cikin tsoro da fargaba. Babu bare
cikinku,jininku daya. Da sauri ya abdullah yace ya
dangantakar take baba,kuma menene dalilin
hakan? Ya gyara zama,sannan ya fara magana a
hankali wanda kwai ya fashemawa a ciki.
Alhaji bara'u rano shine mahaifinsa. Mahaifiyarsa
kuwa itace babba gidanmu,wato yaya saude (ina
rabi'ah kinyi gsky). Allah ya jikan rai ta rasu
wurin haihuwarsa,son ko ganinsa batayi ba.
Duk gidanmu babu wanda jinisu yafi haduwa
sukafi shakuwa sosai irin mahaifinku da ita,ko
kamarsu tafi fitowa zar zar.
Ta dade da aure bata sami haihuwa ba. Lokacin
da mahifinku na karatu kano gidanta yake sauka.
Kamar da kuke ganin kunayi da faruk,mahaifiya
rsa ya dauko,ke kuma abbanki, to kinga kuwa
babu wani banbanci.
Shekarar da abbanki ya yi aure shekarar ne ta
sami ciki,tun a lokaci tabar wasiccin don Allah
kome ta haifa insha Allahu kada ranta ko babu
ranta bishir ne zai reni yaron. Duk dangi sun san
da haka,sbd ko ina ta zauna maganar kenan.
Akwai lkcn da alhaji ya kawota gida don a
kwatanta mata sbd yana ganin sambatun nata
sunyi yawa,kodon ta dade bata sami ciki ba?
Inna tayi mata nasiha irinta mata,amma daga
karshe ta kafe cewar ita kadai tasan abinda take
gani,da kuma irin mafarkan da takeyi,tunda Allah
yasata sami cikin.
Sannan tanaso a ba bishir abinda ta haifa ne
riko,sbd ba a son irin matar da alhajin zai auro
ba.sai bayn rasuwarta abubuwan sukayi ta dawo
mana. Inna ta fara renon faruk,yanayin shekara
da wata 5 abbanku yazo ya tafi dashi. To kunji
dangartakarku,baban kano shine mahaifinsa,wato
alhaji bara'u.
Duk muka dago kai muka dubeshi kamr hadin
baki.
Baba shi yayan yasan haka? Inji ya abdullah.
Kwarai kuwa,abinda ya bata mana rai shine bishir
yayi garhadi kada a sake a nuna muku cewa
bashine ya haifi faruk ba,mu kyaleku a haka.
Tun bara yaje mana da maganar yana sonki
muka kwabeshi tare da tsoratarshi na zan amshe
ki daga wurinsa,matuqar bai janye maganar
ba,kamar ya hakr sai kuma kamar wata 4 da
suka wuce..yaje da auta na hadashi yayi masa
tatas.wlh bamu taba tunanin cewa zai qara tada
zancen ba,wato shine ya debota tun daga
tushe,yayi maki wannan karam-da-rutsi,
ba dole
zuciar yrnya ta nemi bugawa ba
toh da ayi aika aika ai qara na rabata da gdn dan
banza
miqewa anty tayi ta shige daki nima na miqe na
nufi nawa dakn don hada komatsaina
ina fitowa nace ya abdulahhi don Allah dauko
mani dayar jakar,ko tsinke ban bari ba nawa,,sai
gado da madubi
karfe 4 saura muka bar garin abj baban kano ke
tuqa motar.baban garhi na zaune kusa da
shi..nida baba auta muke zaune a baya..tunani
kawai nake abuna
haba shiyasa da ina mkrnta butsu butsu naga
yazo wai yazo ziyarar bazata,toh wai tun yaushe
ma ya fara sona?
Amman yayi wauta saboda sam shi ba irin mijin
da nake so ba kenan tsarin rywta
sam bana sonsa,na frko yana da mata,nafi son
saurayi...kai jama'a kenan mahaifinsau daya da
ya muktar,ya rasa wanda zaiyi kasayya da shi sai
dan uwansa,sabda tsabar son zucia
ga saurin hasala,ni kuma zucia toh ina kaga aure
haka?..wlh na auri yaya ai naci baya don ya tsofe
mani
duk da yafi ya muktar kyau wlh shina ke so,don
kyau ba hali muni,na fi son mai sanyayyar zucia
da sauqin kai
wayyo abba idan ya dawo skul bai ganni ba koya
zaiyi
Allah sarki anty tayi fushi dani ko ya za'ai naci
amanar ta?kai amma yaya bai mana adalci ba
ko ina wayata? Wato ya muktar yasan
dangantarkar sa da shi?
Haka naita tunane har muka iso zaria suka tsaya
sallah
misaln qarfe tara muka isa garhi..baban kano ko
ckn daren ya tafi bai kwana ba
inna dije ta rasa ina zata saka kanta don dadi ta
qara mani dakin hafsa wadda take sa'ata ,itama
bana ta gama skul
Kwana yau 4 har na fara sakewa.saboda yadda
baba ke dawainiyya da ni,komai na gdn ya canzo
duk don naji dadi..ganin haka yasa na ware na
saki jikina,kullum sai mun zagaya gdn yanuwa
nida hafsa.daga qarshe mu zame gdn inna
fira,,abinda ya bana mamaki yadda har yau
baban bai qara yi mani mgnr yaya ba ko a
tambayeni wani abu
ranar fana cika sati 2 ina zaune ina karanta
littafn rabo ne
kwatsam naji muryar yaya abdullahi.da gudu na
miqe na saki wata uwar qara murnar
ganinsa..inna tayo waje da gudu tana fadin
lafia?,,ina riqe dashi muna ta daiya,ta fito tace
haba nidai nasan ba banza ba..muka zauna falo
na zauna kusa dashi haba sai kuka..inna tace
daga murna sai kuka?
Ai tafia ma zanyi tunda kuka take
nayi saurn goge hawayena nace nayi shiru
ke zaman qauyn ma ya amshe ki..kinga yadda
kikai far.inna tace amma fa akwai rama..hafsa
na shrin magana yaya faruk yai sallam..inna tace
abdullahi akwai shakiyyi shine baza kace tare
kuke ba
au bai fada ma inna?na tsaya muna gaisawa da
su amadu mai rake?mun same ku lafia?ya fada
tare da kallo na,nna dauke kaina gefe
shiko ramar baiyi ba wato hnkln sa kwance yake
sai mu..mgnr sa ta dawo ni..inna ya baqi?..ta
dalla masa harara baqin daka koro
ya zaro ido ni wlh inna baba ya taho mani da ita
lo....kai rufe mani baki kafaffen wofi duk wa ya
janyo? Tayi shigewar ta daki
yayai dariya kawai..na miqe nima nai shigewata
daki..yaya abdullh ya biyoni naji dadn hakan
saboda dama akwai tambyr da zanyi masa
ko zama baiyi ba nace ina anty da abba?
Ya dan tabe baki,yace bari meena bayan tahowar
ki rigima ta kaure.kinga yadda anty ke qasqanci?
Wai damn ita aka maida sakarai saboda haka sai
dai yaya ya zaba ko ita ko ke,shi kuma da ransa
ya baci yace ya zabe ki idan ta ga dama ta
zauna idan bata ga dama kuma tasan inda dare
yai mata..toh yanzu tana gdnsu nayi nayi
muje,ya rantsae yace ,idn har ba zat dawo ba,wlh
tayi ta zama shi bazai jeba..kuma anso abba
zaiyi..yanzu mgnr ki yazo yi baba tare da basu
hakuri
Hnkl na ya tashi,tausayn anty ya kamani,na kalli
ya abdlh nacekasan Allah bana son yaya,kuma
ban taba jin ina sonsa ba ko kadan a zuciata,don
haka ka...
Meena yaya yana sonki,ban gane hakan ba sai
bayan kin bar gdnsa,ke in baki lbr....yaudara ce
da son zucia kada ka saurare shi,muci amana
wlh kaji tsoron...
Shi muka gani a bkn kfa ba zato,ba
tsammani,.gulmata kuke yi ko?
Na tsuke fuska na dauketa gefe,ya abdlh yace
a'a shawara nake bata
o.k kaje inna na magana
yana fita naga ya shigo,sai kawai na miqe zan
fita,ya fizgoni na fada jkns,kada kice zaki ringa yi
mani gadara komai a hnkli ake binsa,don haka ki
koma ki zauna.mgna kawai zanyi dake
na zame jkn na zauna bisa kujera,shima ya janyo
dan qaramn tebir ya zauna..........
a Hada Hausa Book stories
GIDA BAI KOSHI BA
¤¤7¤¤
Meena ki tausaya mani don girman Allah.kada ki
zalunci danuwnki,bana tunanin zan iya daina
sonki daidai da sec 1
kayi hkr ni kuwa bana jin zan iya snk daidai da
sec 1..wlh u r nt my typ idan na aure ka naci
baya,ko alama ban taba jin kana brgni ba
ya kalleni ckn bacin rai ni kike fadawa haka
meena
ckn haln ko in kula nace iyakr gsky ta na fada
mak...kin fi son bare da danuwnk
waye bare?na bukta
ya dallo mani idanu.baki hada komai ba dashi illa
kara,,ni kuwa...
Yaya bana sonka kayi hkr mubar maganr nan
ni meena?.ya fada ckn tashn hnkl..don Allah kiyi
mani adalci..kefa kika dauki alkwali,,,na rashn
sani ba?
Abnda yasa kika a ina lallabaki,bana son nazo
nayi wani abu kice na cuceki..amman zan baki
assgnmnt nan da sati 1 don Allah ki fara sona,ni
kuma nai makialkwln zan jiyar dake dadn da baki
taba ji ba dunia
kayi wa kanka kiyamullai yaya kaje ku sasanta
da matarka nikam nafi karfn ka wlh sai yaya
muktar saurayi sabon jini
wani tsaki ya buga tare da wrgo mani wayata da
charga yace zan baki mamaki wlh wato ke
lallashi baya maki....ya juya zai fita ya juyo yace
wlh sai na aure ki saboda ina sonki
GIDA BAI QOSHI BA BA BAWA NA DAWA BA
Ta fiddo ta fara latse latse kenan,wayata ta fara
rngn,ya muktar ne naji dadin hakan
hello na fada yayi ajiyr zucia me ya samu
wayarki 2days.
Nayi murmush,kwana 2 a kashe take,kasan ina
garhi ita kuma na barota abj,sai da su ya...
Wai da gaske ne?ya katseni,nace me fa?
Magnr dake tsaknin ki da yaya faruk
gaky ne amma yanzu komai ya daidaita
na fada masa abnd baba ya kidanya,yayi ajiyar
hrt,kin san Allah meena daman na zargi haka tun
farko,ina gudn kada na fada maki wani abu ya
faru
uhm kawai nace,yayi tsaki irin na ban
haushi,daman ina lura da shi tun kina skul a sati
sai yayi zuwa biyar.ga wani munafukn kallo da
yake maki
haba yaya cool down komai ya wuce na fada ckn
yaryanga da shagwaba
uhm ke kike ganin haka,ni nasan waye faruk.tun
baki da wayau,ki fa tuna idan naje abj idan mun
kebe muna hira irin sintirin da yake yi duk ya
kasa zaune ya kasa tsaye,haka kuma idan ina
gidan nan komai kikai laifi ne,sai ya hauki da
fada har ta shafeni
Ko kin manta ranar da muna zaune falo duka
gidan ana hira da daddare,kamar wasa ya janyoki
jikinsa ya hada bakinsa da naki wai kisha
miyau,sbd ya lura tunda ya zauna kike wani
yatsuna dan ya tsirtar dashi?
Duk mai hankali ya zai dauki hakan? Wane yaya
kika ga yana yiwa kanwarsa irin wannan horon,in
har da gske ciki 1 suka firo? Ko wannan kawai
bai zama alamar tambaya babba ba meena? Ina
tunaninki da hankalinki suka tafi a wancan
lakacin? A lkcn nafi dora wa jamila laifi,sbd itace
katuwar jaka,dakikiya mara tunani,p. Abinda yasa
kika ga na fita daga falon,haushi naji sbd lkcn
daya sakeki wani mayen kallo ya biki
dashi,wannan mu maza kawai mukasan
ma'anarsa.....
Kabar tashin tashina,tunda baba.....
Ke kike ganin haka,faruk baida mutunci amma
barshi,idan yasan wata aibai san wata ba,zan zo
ranar juma'ar nan muyi magana da baba,don na
turo magabatana,kin amince? Na danyi
murmushi,na amince yaya,ka zo kawai. Ngd
meena,zan kiraki anjima,ok? Nace yes my dear.
Tare da kashe wayar na dan kalli mutuniyar ta
wutsiyar ido kamar ta daura hannu sama ta
kurma ihi. Hafsa ta matso,wai meye naji kina ce
mishi yabar tashin tashina? Na danyi
murmushi,magulmata suka fada mishi rikicina da
yaya,duk ya rude shine yake tada mini wasu
abubuwan da suka faru abuja,sai nace ya daina,
yanzu dai ya rokeni alfarma yana son na bashi
izini yazo wurin baba suyi magana...
Me kika ce mishi? Ta katseni ciki nuna farin ciki
dajin dadi. Na danyi dariya, yazo kawai nace,koya
kika gani? Kafin tayi magana,fatima tabar dakin.
Muka kyalkyace da dariya,har da tafa hannuwa.
Amma kin birgeni mutuniyar,saidai zan baki
shawara daya amma ba yanzu ba, ki bari mu
koma gida tukunna. Nace ba mtsala 'yar uwa.
Wayata tayi 'yar kara alamar sako ya shigo. Ina
dubawa naga an rubuta 'message from ya faruk'
kinga kuma wani sako daga ya faruk,kai Allah ya
raba mai rai da naci. Kin cika daukar abu da
zafi,ki karanata mana, menene a ciki idan bai
miki ba sai ki goge. Inba ke ba waza a kula yace
naci? Ki dubi yadda suka bar garin nan,yanzu
haka basu isa kaiwa ba,don ya damu.... Kai ya
isa,kada a isheni,bari na karanta ko daman can
ba cewa nayi bazan duba ba.
Rayuwata!!!
Ya muka barki? Meena ina fama da azaba a
zuciyata kece rayuwata,rasaki na iya sanya wa
na rasa kaina,ki dubi abubuwan da suka
faru,meye laifina a ciki,kodon nace ke nake so?
Ki tausaya wa dan uwanki,kada ki jefani cikin
mawuyacin hali don Allah. Alkawarina yana
kanki,kamar yadda zan cika naki a duk lokacin da
kika shirya karba.
Mukhtar dan uwana ne,ba naki ba. Na fiki sanin
halinsa,sha'awarki kawai yake,baya sonki,ni ne
masoyinki mai kaunarki.............
Nayi saurin gogeshi duka,ba treda na karsa
karantawa ba don takaici. Daga na gidan inna
muka wuce sai dare muka koma gida. Muna cin
tuwo ya mukhtar ya kira,mun jima kafin muyi
sallama, kamar hadin baki,ina wanke hannuna ya
faruk ya kira,nayi saurin zuwa na kashe wayar
baki daya sbd nasan nacinsa.
Muna zaune daki muna kallon wata drama da
akeyi ta 'yan korea, mai suna heaven fates,nace
yauwa hafsa wace shawara ce za a..... Ban mnta
ba,son Allah bari a karasa wnn episode din,naga
yadda za a kare. Kinsan Allah ki raba kanki da
kallon dramas. Sbd me? Ta bukata hankalinta
nakan tv. Ban sani ba na fada cikin jin haushi.
Dai dai lkcn aka gama ta juyo,kin cika saurin
fushi da yawa,wannan wasan yanda kyau don
baki fara daga farko bane,shiyasa kike ganin
rashin kyansa. Ke dai kika sani na fada ina
murumushi. Kinsan shawarr da zan baki? Sai kin
fada nace da ita ina kallonta. Akan mgnrki ce
dsu ya faruk,kin san ita gsky 1 ce amina,kuma
rayuwar duniya da kike ganinta wlhy abu ce mai
hadari. Duk macen duniya budurwa
kamarki,kullum addu'arta ba zata wuce Allah ya
bata miji na gari wanda yasan mu2ncinta,iyaye
nta da kuma 'yan uwanta ba. Maza da kike
ganinsu kyal kyal na rariya ne,wanda kike hangen
mtnci da soyayya gareshi zaki zo daga karshe ki
gane ba hakan bane. Bance miki duka ba a wasu
daga ciki kamar yadda muma matan muke.
A yanzu zaman nan da ake amina baki da kamar
ya faruk,sbd shi ya rikeki,ya kuma raineki,har
ki....ke kada kiyi sabo malama,akwai mai rainon
wani banda Allah?na katseta cikin bacin rai,don
fara gano inda ta nufa.
Tayi murmushi, bana nufin haka,sbd da taimakon
Allah,kuma shi yabashi ikob komai. Da fatan kin
fahmceni? Tacigaba da cewa a mkrnt idan ana
lbrn aure da yawa nakanji kawayena na fadin
sunfi son aure mai mata,sbd yawanci sunfi sanin
darajar mace. Ranar nan jinki kawai nakeyi wai
ba kya son mai mata,sai saurayi,idan kishi ne
yaja ki fadin haka to kinyi kuskure kina iya auren
saurayin,lkcn da kika gane dadin zama ke kadan
yayo maki wata ya zakiyi?
Ga mgnr tsufa,kiji tsoron Allah meena,duka yaya
idan yayi gudun hohoho yayi shkra talatin da
takwas zuwa da tara. Amma a fuska saiki rantse
da Allah shkransa talatin daid ai. Haka naji su
inna nayin wannan zancen rannan ita da baba.
Yana da kyan jiki dana fuska,banga makusarsa
ba,sbd wlhy yanzu idan ya jera da ya mukhtar sai
ace shi ne kane ba wa ba. Kuma ko zabe
akeyi,kin san sai an zabi.......
Look! Hafsa ya isheni haka nan,bana son ji....ki
rage wannan....i dnt want 2 hear d hell of
nonsense. Na kara daka mata tsawa. No wonder
naga an tuza miki kudi dazai tafi,ashe na
campaign ne... Baki fahimceni ba meena....
Bazan kuma taba fahimtarki ba,gargadin dazan
miki na karshe shine,ki iya bakinki,kada takai
muyi wulakanci........
Da wa? Allah ya baki hkr,me yayi zafi haka
meena? Nace bana so dai na fada miki,wlhy ki
daina. Insha Allahu anyi na farko ai. Ta fada tana
rike da haba,kmr wata tsohuwa. Ta bani dariya
amma na kame don kada ta dauki maganata
wasa.
Baku da gsky,sbd kuminiyarku tayi yawa,wace
wainar ake toyawa adakin da kuka ki fitowa, har
karfe sha daya ta gabato,ko yau bama cin abinci
ne a gidan?
Hafsa ta mike,kai inna,yau fa ke ce da girki.....
Au daman da gaske kuke mgnr jiya? To bazan
girka ba,idan baku yi k.......inna babu ruwana,
hafsa ce da wannan 'yan kakale kakalem.
Na sani tsohuwa,kullum idan girkinki yazo,sai dai
muji kamshi,amma ita sai.....
Sallamar ya suleiman ta hanta karasawa. Ya
akayi ne inna kike ta faman bambami,ana jinki da
an shigo soro?
Sallamr yaya muktar ta hana inna magana ko
amsa bamu tsaya yi ba mykayi daki
wane nake gani haka kamar muntari,baba ya fada
yana dariya
inna tace ai kaifa yanzu ka ganshi ko ai tun dazu
ya zo
ya durkusa har qasa suka gaisa ganin yadda
yake ta yan sunne sunnen kai ne yasa inna tashi
ta shige daki
kallo daya baba yayi masa ya gane lallai akwai
wani abu,shi a tunaninsa ya dauka ko mgnr fati
ce yar wajen baba auta
ya akayi ne muntari?
Ya qara saddar da kai qasa yace,damn uhm uhm
y dan sosa qeya
kai bana son skrci ni din zaka yi wa boye boye?
nace menene
kamar zai nutse qasa dn kny haka nan ya daure
ya fara mgn.dmn munyi mgn da amina ne,shine
tace nazo wurinka,,yayi shiru baba yayi dan
tsaki.kai ni ban fahimci bayaninka ba
tace ne nazo na nemi izni idan ka amnc mgbtana
suzo ayi mgnr aurenmu
dawa? Baba ya tambya,,yace da ita aminar kake
so? Ya qara tmbr sa
eh baba
tun yaushe
gsky zamu yi shkr 3
naso zuwa nan amman ya faruk ya hanani
ashe yana da wata manufa sai yanzu na gane
tsohuwa!! Ba zato naji baba ya kwalan kira
ina zuwa na durkusa nace gani baba,gabana sai
faduwa yake
mene alakar ki da muntari?
Na shiga rudani sai kame kame..kin yi
shiru?..nace sona yake yi
kefa?tambyr razo mani a bazata nace nima
kina sonsa?nayi shiru.yace kiyi mgn sbd ina son
fita hkkn ki ne.kada a tauye maki kina sonsa
kuwa?
Nace eh baba ina sonsa
yayi murmsh

Please Login or Register in order to submit comment