Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da bayaninki ba, amma
ga wata, me ye KAUNA?"
"kauna" wannan itace mai neman tarwasa zuciya
lokaci guda."
" ya akayi kika san duk wadannan?" ya rubuto
"saboda na jiye wa jikina."
"idan nace karya kike banyi laifi ba?"
"baka yi ba, idan na ji hujja!"
"Very good. Zan kira ki yanzu don rubutu ba ya
yi.
Gabana ya fadi, bana son jin muryansa, firgitani
zai yi,ya hargisa tunani na..................... Raki ta
fara yi a hankali.
"My husband ' nayi dariya, na dauka cikin yar jin
kunya na fadi "HELLO" A hankali.
"kina ji na?" ya fadi a hankali,nayi murmushi
nace 'uhm'
Zan baki bayani ta reference to me and you.
Meena shi so abu ne mai wuya, idan kin manta
bari na fada miki sbd tsananin son da nakeyi
miki,ya sanya na zubda hawaye a gabanki,so ya
haddasa mini kiyayyar dan uwana,sonki yasa na
yiwa iyayena karya. Tsananin son da nake yi miki
yasa 'yan uwa suke tausayina.
Kauna kuwa itace tasa na lashi takobin dana
kawo ki gidana. Kauna ta sanya na zuba miki ido
kike yadda kika ga dama kauna ta sanya na
danne wa zuciyata sha'awarki har saikin yarda
don karin kanki.
Meena lkcn da nake sonki banji kunyar kowa
ba,haka na tunkareki da maganar,aka gargadeni
amma na take maganar iyayena.
Har yanzu baki sona,kawai kina dan tausayina ne
sbd i believe cewar da kina sona wlhy. Meena da
kin faranta mini rai kmr yadda na faranta miki.
Anyway wannan kenan. Idan kin gamsu ina iya
cewa mu kwana lfy.
Nayi shiru kwalla kawai ke zubo mini a kumatu,
kina jina meena? Da kyar na iya furta, uhm.
Sai da safen kenan? Ya fada a hnkl.
Nayi krfn hali, Allah ya kaimu. Daga ji ba haka
yaso ba. Na kshe wayar da sauri tare da runtse
idanuna tamau.
Na jawo wa kaina daman hausawa na ce,baki
yasan abinda zai fada,amma bai sanme za a
mayar masa ba.
Tun daga wannan rana ban kara buga masa
waya ba,ko text. Shima haka koda muka hadu
washe gari,bai nuna mini wani abu ba,kmr bamu
taba wata magana ba. Ni ma kuwa na share.
Haka zama yacigaba kullum ba dadi,ni a ganina
shi namiji ya daure,sai ni mace na kasa? Na
dauko alwashin in zamu kare zamanmu haka
bazan taba zuwa inkai kaina ba,kmr yadda yake
tunani.
Tunanina ya tsaya wuri daya,shima sonda yake
mini akwai rauni a ciki,sbd inba haka ba,yadda ya
lura na kamu da sonsa,sai yazo muci gaba da
rayuwarmu,amma ya basar sai ni?
A dalilin yawan tunani da rashin cin abinci ya
haddasa mini ciwon ulcer.
Ranar da mukayi kwana uku da gana jarabawa
ana sauran sati daya bikin ya abdullah,ina
kwance daki cikin matsanancin ciwon zuciya,ji
nakeyi kmr ta tsage don tsananin azaba.
Na mike da kyar na nufi kitchen. Don Allah grace
bani ruwa masu sanyi kwarai idan ma akwai
wanda ya fara kankara bani shi. Ki zubo mini
madara a cup kmr cokali hudu.
Lafiya dai ko aunty?
Na danyi murmushi tare da cije lebe, wlhy kirjina
ke zafi kmr ya bude.
Aunty ba zaki je asibiti a dubaki da wuri ba?
Ke dai bani abinda na umarceki dashi da sauri.
Da kaina na hada da ruwan sanyi na dama,kafa
kai na yi ina sha harna shanye. Ina ajiye kofin
wanda ya shiga cikina yana dawowa,gaba daya
na amayar dashi nan da nan suka rude.
Na mike zuwa daki,amma ina! Sai nayi kasa
ragwab! Ihu suka saki lkc guda tareda dora
hannuwa bisa kai.
Ban kara sanin abinda ke faruwa ba, na bude ido
na a hnkl na ganni kwance bisa gado na. Ya
abdullah da ya faruk tsaye bisa kaina.
Da sauri ya karaso,sannu meena! Na banka mishi
wata uwar harara,yayi saurin sunkuyar da kai.
Ya abdullah ya matso,sannu! Nayi murmushin
krfn hali da dan guntun kwalla a idona, nace
yauwa.
Ya kike ji yanzu?
Da sauki. Na fada a hnkl,bani ruwa insha dan
Allah. Ya miko min robar. Babu mai sanyi?
Ke dai sha wannan sbd yanzu ance ki daina shan
ruwa masu sanyi kwarai, da abu mai zafi ko
maiko da mai yaji.
Ko sauraronsa ban tsaya yiba, na amshi ruwan
nasha, waya ja mini? Na tmbyi kaina.
Ya abdulla ya zauna bakin gadon, meena! Ya kira
sunana a hnkl, na kalleshi ba tareda na amsa
ba,kanki farau karatu? Kawai kin dauki damuwa
da tunani kin dorawa kanki, har ya janyo miki
ciwo?likita yace, kina fama da yawan
tunani,wanda ya haddsa miki matsanancin
damuwa,baki cin abinci yadda ya kamata.
Kwalla suka zubo mini, ya faruk ya matso. Don
Allah meena kiyi hkr.....
Kallon dana banka mishi ne yasa maganar ta
makale bai karasata ba.
Ya abdullah ya kalleni ya kalleshi,yana son
fahimtar wani abu kmr zai yi magana,sai ya
mike, Bari na dan fita waje ina zuwa.
Har yakai bakin kofa na kwala masa kira, ya
waigo, don Allah hada mini ruwan wanka a toilet.
Kafin yayi magana ya faruk ya mike, je ka kawai
bari na hada mata.
Yana fita ya kalleni,tuni kaina ke kallon bango
tunda naji ya fadi haka.
Meena! Meena!! Meena!!!! Dake fa nike kika
kyaleni,kinji? Baki yi mini magana? Allah ya baki
hakuri,fushi kike yi da ni meena? To kiyi hakuri
na tuba don Allah a gafarceni."
Abinka ga SO hana ganin laifi nan da nan
zuciyata ta karaya,tausayinsa ya kamani. Na
fashe da kuka,ya rungumeni a jikinsa ya
lallashi,"sorry laifinane,banza kara ba,please."
wallahi meeena ina sonki,banson abinda ke bata
miki rai.yanzu ki fada mini me ye damuwarki har
ulcer ta kama mini ke?
Na fizgi jikina,"yaushe rabonka da na ganka?ya u
sati nawa kenan baka zama agida?sai cikin dare
kake dawowa,ya ay bazan damu ba?
Yayi murmushi,"wannan yasa kika damu har
ulcer ta kamaki?"
kin manta hidimar Abdallah kai na take meena?
zirga-zirga tayi mini yawa shiya sa,ke kuma naga
ba ki damu dani ba shi yasa.
"shiya sa kake waya da yan matan ka idan ina
falo ko?" ya kyalkyalce da dariya "au ashe ana
kishina? Yi hakuri daga yau na bari.muje nayi
maki wanka...
Na kudundune fuskata ina fadin" Allah ya
sauwake mini".
"haka kika ce?" na daga kai. "lallai akwai ranar
maida magana."
ya kwaso iyayen magunguna ya nuna mani."
wadannan duk ki tsare shansu,dr yace insha
Allahu tunda bata kamaki sosai ba zaki rabu da
ita during short period of time.
A bar damuwa da yawan tunani, aringa cin abinci
kada yan biki su zo a ganki a rame,kinsa kuwa
duk wanda ya yi mini magana wallahi cewa zanzi
ciki gareki."
Na kwalo ido,ya fice yana dariya "kiyi wankan
zance lifechamp a gyara dakunaan baki,saboda
yan daurin aure.
Ikon Allah,cikin kwana 2 na murmure har na dan
fara maida jikina,saboda magungunan yawancin
su duk na cin abinci ne.
Ina zaune falo su ya abdallah suka shigo da
buhunan kaji da saura kayan dafe - dafe kala-
kala.
"malama ki tashi yau fa zakuyi aikin nan."
" na sani. Akaiwa su merry su fara gyarawa kafin
nazo." hafsa nake jira ta ce sun kusa shigowa
abuja. Hohoho ina ruwan garaje,don dokin zuwan
nasu ne aka make falo?"
"amma zakuje gidan amaren ko?"q ya bukata.
Nace " komin dare kuwa"
karfe sha daya da rabi suka iso.moya hudu cike
da mutanen kano da garhi. Tsalle,ihu,murna har
sai da muryata ta dushe, aiki ya hana mu kebe
da hafsa,sai wajen hudu da rabi na figeta mukayi
lambu."
"hafsa kinyi kiba wallhi"
tayi dariya"ke kuma kin rame"
"bari ke dai,labari ke cike da cikin nan nawa.ina
alhassan?"
Yana kano,yace na gaisheki,sai jibi zasu iso ana
gobe daurin aure...
Kwana nawa zai yi? Na bukata.
Daya yace,sbd zai tafi germany sarowa abbansu
motoci ranar litinin.
A ni hafsa,kina sonsa?
Ta kyalkyace da dry,sosai ma.
Na tabe baki,kowa abinsa zam-zam banda ni
hafsa.
Kamar yay?
Hafsa auren dole nayi,bana soyayya ba,daga
baya Allah ya dora mini jarabar sonsa,lkcn da shi
kuma bata ni yake ba.
Kin cika zargi wlhy,bakin fada mini ya baki hkr
ba?
Eh! Amma nothing change ya kamata ace daga
wannan mun zama normal ma'aurata hafsa.
Ta dafa kafadata, kada kiyi kuka.
Ga shawara daya, kawo kunnenki! Na zare ido,
Allah?
Kina wasa,ke dai sha kuruminki kafin nabar gidan
nan,komai zai daidaita.
Allah yasa hafsa ya faruk shu'umin mutum ne.
Duk shu'umancinsa zai zo hannu,ke dai dole ki
cire kunya idan kina son success.ba matsala
hafsa,i will try my best.
Karfe bakwai da rabi an hallara falo ana ta
kwakwazo gidan gwanin dadi, wai waccan
kilbabbar yarinyar wacece? Na tmby hafsa.
Tayi tsaki, diyar kanen b.kano ce.
Wane ciki?
B.rilwanu.
Wacce tayi kara2 london?
Ita ce fa! 'Yar ji! Haka naji dangi na fada
mata,kin san ita kadai ce 'yarsa.
Shine aka shagwabata haka?
Hafsa tayi murmushi, kadan kika gani,rannan
y.mktr na zuwaa,zamansa ke da wuya ta haye
masa cinya tana shagwaba,sai ya siyo mata ice
cream.
Waccan katuwar? Na fada tare da mamaki. Tayi
dry, zancen kike so.
Sallamar yaya ta maida hnln kowa gareshi. Inna
tace harka dawo? Yace eh, an gama shirya maku
ko ina.
Yauwa bacci daman nakeji tashi mu tafi ko kuna
nan? Ta tmby su gwaggo maryama da sauran
yara.
Gsky inna kuje boys qtrs din nan,ni a nan zan
kwana nida su hafsa.
Ke maryama don me? Inji g.hadiza.
Sbd katifun bazasu ishemu ba,ni kuwa bazan iya
kwana mu 2 ba.
Sannu giwa wadandan kattin katifun yaushe za a
matse?
Maryam tace, dama kyaleta kukayi hadiza kuzo
mu tafi.
Tace to.
Duk suka fice aka barni daga ni sai hafsa da
gwaggo duk ba,u lura da 'yarji dake kwance cikin
kujera ba.
Meena zoki bani tea. Ya faruk ya fada. Jin haka
hafsa da gwaggo suka koma dakina.
Ina cikin hada masa ta taso cikin shagwaba,ga
wata 'yar iskar riga dake jikinta mai hannu
daya,siket din ya matseta,kiri kiri an wulakanta
babban leshi mai tsada.
Ya faruk nima zan sha tea din. Me zan gani?
Tsaye take bayansa ta sagalo hannuwanta a
wuyansa.
Nayi kallon da hararar amma a banza ba tasan
inayi ba,sai shine naga jikinsa yayi sanyi, ka ji
zan sha. Ta fada tare da dora kanta bisa nashi
na runtse ido na bude sunyi jawur.
Bari to! Tsaya...... Ya fara 'yan kame kame da
kyar ya iya furta, Zakiyya zauna a hada miki ko
bakiga nima sai an bani ba?
A'a kai nake so ka......
Chafka daya na yiwa wuyanta na hada da
bango,nan da nan idanuwanta suka fito,a rude ya
tako, Meena!....
Kada ka tabani wlhy zan kasheta idan kayi gign
tabani.
Meena ki taimaka kada kiyi kisan kai...
Kabace min da gani.
To sakarta zan wuce,amma saki wuyan don
Allah.
Ka tafi daki ya faruk. A guje ya wuce na tafi,don
Allah saki 'yar mutane.
Yana shigewa na saketa,nana da nan ta hau yin
tari,ko alama ban tausaya mata ba,na fara bata
lafiyayyun mari guda uku.
Zatayi kara na toshe bakin, 'ke yar iska ce? Ba
'yarji kike ba,ko 'yar gani ne sunanki.wlhy kiyi
nesa da mijina don ubanki.
Shine zakiyi mini karuwanci a gida? Burum naji
ya fito ko kallonsa banyi ba.
Nacigaba da cewa,wlhy ko kallonsa kika karayi
saina cire miki makogaro duk a huta da karuwa
irinki,banza.
Kwalla kawai ke zuba a idonta,fskrta kuwa tuni
ta kumbura sbd mari.
Ke meena? Haka kike da mugun kishi? Na balla
mishi uwar harara, saura 'yar iskan karuwanka
dake maka waya ina jin na fara samun daya.
Na figeta na wurga waje, aje ayi bacci. Na jawo
kofa garam!
Ya ruko hannuna na fizge,ya kara na fizge sai
kawai ya sureni ya yi dakinsa dani.
"ina zaki gwaggo ta ganki cikin wannan tashin
hankali,ki je mini?" ya dorani bisa gado,"ki kwanta
ni zan kwana bisa kujera mu ga abin da goben
zatayi"
"kin dai ballon ruwa doon wannan wani sabon
tashin hankali ne" na ja bargo kawai na kyaleshi
ina fadin "wa ya ja?"
Hada Hausa Book stories
GIDA BAI KOSHI BA
¤¤16¤¤
Babu irin tambayar da ba ayi wa zakiyya ta fadi
me ya same ta a fuska ba,amma amsar daya
ce"ba komai" har aka gaji aka kyaleta. Dagani sai
ya faruq muka san gaskiyar magana.
Koda yan daurin aure suka zo ma sunyi
tambayar,amma sai ta ce "ba komai."
sam tabar shigowa gidan daga boys quaters sai
harabar gidan,cewarta ta fi son zama can. Kowa
yana mamakin wannan sudden change.
Muna tsaye akitchen ni da hafsa muna harhada
take aways na party da za ayi yau.
Tace"shegiyar diyar nan kila ya faruq ta yiwa
iskancita ya bubbugeta,hakan nake zargi."
Na kyalkyace da dariya" nice nan na yi
maganinta"
ta zaro ido"WHAT" na bata labarin yadda abun ya
faru,
"kin burge ni mutumiyar,kinga kinyi mini maganin
yar banza da yanzu ta addabemu.
"tausayi ta bani na so jiya na kara ja mata
kunne,zazzabin da ta yi ya ceceta. Yanzu ga shi
ta maida mini hannun agogo baya."
"wannan ba matsala bane,daman ke ce mai fushi
don na lura har yanzu hankalinki ba kwance yake
ba, yana son ba ki hakuri kin ki ba shi fuska. A
yadda na fahimta sam ba ya son bacin ran ki.
"kyaleshi,sai na gara shi nima"
ta kyalkyace da dariya " ku gara juna dai,ina
kallace-kallacen fina-finan syy da karance-
karancen ban taba ganin irin taku ba.
Ko wani girman kan tsiya ,wallahi kamar kada na
tafi kawai na tsaya don ganin irin rayuwar da
zaku yi"
murmushi kawai na yi.
Karfe 4 duk an gama shiryawa,motata
hafsa,gwaggo maryam da inna zan dauka kowa
ya tafi sai mu kadai. Na dauko jakata ina lalubem
makulli ya ce dauke ni inda kika aje. Inna ce ta
leko" tsohuwa muna waje ki yi sauri"
"to inna, kuje ina zuwa,makulli zan dauka."
daga can kofar gidan na jiyo karar motar, na leka
ta taga a harzance,uche na hango ya fice da
ita.sugwaggo a ciki.
Aguje na fito amma ina! A falo nayi kicibus da
shi,ya ci uban gayu shi ma blue material ya
saka,ya hadu iyakar haduwa.
"ina zaki haka da gudu?"
na tsaya ina shessheka, "wallahi Uche...........
......."
"ni ne na ba shi makullin, saboda ina son tafiya
da matata."
yau ina na kalla na yi sallah? Na tambayi kaina
ina murmushi,dadi kamar ya halakani,amma na
dan basar na ce" haba ya za a yi kaje party
babba da kai,wannan ai sai mu yara."
"dalilin da yasa kuka sanya mishi family & friends
shi zai kai ni,me ya hana ku sanya kids party?"
gaba nayi ina dariya, haka ya biyoni muka taho
ina shirin tsayawa dayan gefen na ji an jefoni da
makulli, "waye direbanki?"
banyi magana ba na duka na dauka. 180 na dinga
gudu tuni na wuce su hafsa. Duk ya rude "please
meena rage gudun" na dinga yi masa dariya.
Muna isa yayi ajiyar zuciya"wash! Wannan shi ne
wuya makarantar kare...
Gurin ya kawatu,amrya da ango sunyi kyau sosai.
Kiri-kiri ya faruq ya hana ni sakat,ina kallon ya
muktar sai safa da marwa ake yi amma ba fuskar
magan.
Da yayan kakai suka gaisa,ni kuwa ko kallo,na
lura wannan abun da nayi ba karamin dadi yayi
wa ya faruq ba.
Karfe 7 aka gama partyn,muka koma gida a
gajiya.
Washe gari karfe 11:30 aka daura aure. Ranan
iyaye maza suka bar Abuja,mata kuwa washe
gari misalin karfe 2.
Allah ya taimaka su merry sun gyara ko ina,
saboda ban baro gidan amarya ba sai bayan
magariba.
Ko ina sun kintsa har da tukuicin turaren kamshi
nayi ta sanya masu albarka.
Karfe 9 na fito wanka,kai tsaye gaban madubi
dagani da tawul, kamar ance in kalli
bayana,kawai naga mutun tsaye daga shi sai
jallabiya fara.
Ya kura min ido kamar wanda bai sanni ba, ni
kuwa kunya kamar na bude drower na shige. Na
daure na cije na kalleshi, "wani abu kake so ne
yaya?"
ya tako zuwa kusa da ni, nan da nan gabana ya
ci gaba da harbawa da sauri da sauri, ya tallabo
kuguna na fada jikinsa ta baya, a hankali ya ce"
YES I NEED SOMETHING"....
Yadda maganar ta ratsa cikin kunnuwana yasa
tsikar jikna tashi yarrrrrrrrr.
" nazo tayaki kwana meena! Ni na kawo kaina
saboda na lura baza ki taba gane damuwata
akanki ba?"
wannan shi ake kira babu zato babu
tsammani............
"i love u meena, and i'm in need of u! Don Allah
ki ceci rayuwata, yau ki sadani da farin cikin da
na dade ina mafarkin samu shekara da shekaru."
na shiga uku! Na fada a hankali, ashe ya jini.
" bari kira wa kanki banuwa, jst love me @ this
nyt, son da nake gani a idonki, please ki nunan
shi zahiri meena, don Allah meena save...........
na runtse ido da karfi..kayi hlr yay kunya
nakeji..ya janyo ni da karfi saura kadan tawul din
ya balle na hanzarta rikeshi da hannuna...ya
sunkuyo da fuskarsa suka hadu da tawa ahankali
ya furta zan cire maki kunyan meena jst agree wt
me........na dora kaina a kirjinsa nidai kunya
nakeji ya kara rungumeni sosai haba ma blvd
kodai bakya sona......ya dago fuska kina
sona????.....ina sonka amman..ya sakeni daura
zaninki dauro alwala muyi sallah....
babu abunda jikina keyi sai kerma..kallo daya
zaka mani kasan cewa a rude nake....haka
mukayi rakaa biyu tare da dafa kaina yayi wata
addua sanna ya mike jallabiyya naga ya cire
daga shi sai gajeran wando..com on swty azo
aimin tausa innallihai na fada a hankali..ko
sainazo na dauke kine????na mike kawai ba tare
da nayi wata maganba gabana kawai ke fadi na
dadde ina tunanin wannan rana yau gashi Allah
ya kawu ta naji kamarta koma..wai nice yau zan
kwana da ya faruq kwana irinta maurata...
kuka na fara a hankali na isa bakin gado,
"malama ki cire mini wannan hijabin kafin ki
karaso."
kai jama'a shi ko ajikin sa, sai ma wata
annashuwa da yake yi, kuka na ya karu, ya sauko
yana fadin" ke kwantar da hankalinki, wasa nake
yi, yi shiru zolaya ce kawai zuwa nayi muyi
kwana babu abinda zan miki."
. Duk da haka ban yarda ba, sai daya ce "ke ma
kin san da haka raina tun jiya zan kamaki ko?"
na yi murmushi tare da cire hijabin ya koma yana
dariya"matsoraciya"
mun kwanta shiru!! Zuwa can na ji ya dan miko
hannu, nayi saurin matsawa jikinsa, nasan hakan
yake bukata, amma sai me??????????????
Dai dai ina! Na makaro da wayau da dabara ya
faruq ya maidani cikkakiyar mace.
NI KUKA, SHI KUKA NI DAI NASAN KO KUKAN
ME NAKE YI,TO SHI FA?????????????????
Karfe 6:30 na bude ido, babu kowa dakin na
fashe d kuka,ashe dama cika baki ya faruk
yakeyi mini yana sona. Mutumin dana ringa
gamawa da girman Allah,amma kmr kara zugashi
nakeyi?
Da kyar nakai kaina toilet duk wani sirrin gyaran
jiki Allah ya taimakeni maryam ta karantar dani.
Daga zaune nayi sallah. Ina cikin lazimi ya
shigo,na yi saurin kifa kaina a cinya,tare da sakin
kuka a hnkl.
Motsin shigarsa toilet naji ina daga kai naga an
yaye bedsheet din an shimfida sabo.
Ina nan zaune harya gama wankewa ya fito,ya
shanya. Banji shigowarsa ba,sai dai naji mutum
ya daukeni cak! Babu inda ya direni sai dakinsa
tsakiyar gado.
Ya fice,ba a fi minti 2 ba ya dawo da tea da
soyayyen kwai. Kuka kawai nakeyi, baice mini
komai ba,sai dai ya kamani na kwanta jikinsa a
hnkl ya bani tea din da kwan nayi kat! Sannan ya
dauko wasu magunguna ya bani nasha. Ya
maidoni na kwanta. Shima ya kwanta kusa dani
ya maido kaina a kirjinsa.
Aminatu!!! Na ji wani yar!!! Bai taba kirana da
wannan sunan ba, Allah yayi miki albarka....
Wannan kalma tun jiya nake jinta bakinsa...
Na rasa kalmar da zanyi amfani da ita wajen
gode miki,hakika kin shayar dani zuma mai
dadi,wanda nasha mafarkin samu, Allah bai bani
ba sai yau. Kin cika 'yar halas meena,i'm really
proud of you. Na dade da wani ciwo a raina yau
kece kika wanken,Allah ya biyaki da aljanna.
Lkcn dana auri jamila yarinyar nan bata cika
mace ba, da nayi mata magana sai cewa
tayi,fyade akayi mata lkcn tana secondary skul
cewarta 'yan fashi. Daga karshe na gane karya
tai min.
Na dagi kaina ina dubansa cike da tausayi,lallai
ya faruk ya cika mai hkr.
Meena kiyi hkr da halina,muyi zama jindadi,pls i
love you meena,with all my hrt.
Kai ni dai ban san yadda wadannan maganfanu
suka tsaya ba,bacci yayi awon gaba dani.
Ina bude ido najini garau babu sauran ciwon
jiki,na kalleshi yana ta sharar bacci, hannuna rike
da nashi.
Bawan Allah duk sai naji tausayinsa ya
kamani,kwalla suka zubo mini,yayi saurin bude
ido,zo, menene, Matson ya akayi?
Naki yarda mu hada ido sbd kunya. Ya tashi
zaune, bana son wannan kunyar fa. Ya fada cikin
shagwaba,har da turbune fuska irin yadda yara
kanana keyi.
Ban san lkcn da dariya ta kubuce mini ba. Ya
sauka bisa gadon ya bude wadrop dinsa ya fara
fiddo wasu irin manyan jikkuna guda tara sai 'yar
karamarsu ta cikon gomar.
Nayi galala ina kallonsa ya kamo hannuna,
Lefenki ne zaki gani?
Hada Hausa Book stories
GIDA BAI KOSHI BA.
Karshe...
¤¤17¤¤
Lefe kuma? Sai a lkcn na tuna she fa baiyi mini
lefe ba.
Lkcn da nake ganin kayan nan banso zuciyata ta
tuna mini da na ya mktr ba,sbd saina hangosu
kmr gwanjo.
Akwatuna biyar kayan sawa ne super wax ce
karama a ciki,qura kuwa tafi ashirin a ciki,leshi
kuwa karami shine na dubu hamsin. Galiloli da
materials kai kace a textile insustry kake. Ba
anan take ba,saida muka bude jikunna biyu na
gaba,rigunan bacci inner wears da gyaluluwa
kusan kowanne kaya akwai gyalensu.
Ashe abu na gaba sauran biyun takalmomi ne
kawai da jikkunansu bila adadin. Na kyalkyace da
dry,sai naga ya shaka. Au na manta. Wani katon
akwati naga ya jawo muna budewa saiga english
wears da wanduna hadaddu,ga kuma fakistan
nan da riga da siket irin na indiyawa,suma kala
kala.
Ban san lkcn dana fada jikinsa ina murna ba.
Yayi murmushi, saura karamar jakar bude da
kanki,ita jiya na amsota banki,yanzu haka idan
kin gani kin kuma dauki wadanda zakiyi amfani
dasu,to bankin zan maidata alabarshi idan kina
bukatar wata saiki ringa zuwa can kina canzawa.
Na hanzarta budewa don ganin wadanne irin
kaya ne haka da ajiyarsu sai ban..... Gaba daya
numfashina ya nemi daukewa. Jakr nan shake
take da gwalagwalai da diamond sarka da
'yankunne,'yan hannu,,zobbe kai harda sarkar
kafa. Na dauko wanis etin diamond wanda yafi
kowane girma,babu shakka na ganeta.
Itace na gani a wani shagin balarabe lkcn da
mukaje umrah cikin wani azumi ina aji biyar.
Na dauki sarkar ina dubawa yadda take walkiya
ta birgeni sosai, a tunanina fashion ce. Aunty
jamila na kusa dani ya faruk kuma na bayanmu
bansan me yake dubawa ba. Aunty kinga sarkar
nan ta birgeni woh! Gsky ta hadu bari na sayeta.
Ke set ce fa,kinga sauran agogo da 'yan hannu.
Ta katseni tareda dauko 'yar battar. Don Allah
malam nawa? Nas tmby balaraben da turanci ya
fada man kudin aunty tace yayi mana combine
da kudin naija. Da gudu muka bar shagon don
firgita lkcn daya fada mana,miliyan tara da rabi
kenan.
Sayayyar da bamu karasa yiba kenan. Gida yaya
ya samemu sai tsiya yake yiwa aunty wai munji
kunya. Tana dry tace, eh munji kunyar....
Kin tunata ko? Ya katsen tunanina. Na snkyar
dakai...
Tun a lkcn na sai miki ita,wannan agogon fa kin
tuno shi?
Tun a lkcn nasai miki ita,wannan agogon fa kin
tunoshi?
Na kalleshi na gwal ne,wanda shi kuma cikon
dubu goma ya hana na sayoshi duk a saudiyyar.
Ya kara dauko mini wasu set na gwal guda 5 'yan
dubai design'design,wadan nan fa?
Na zaro ido, sune da mukaje dubai yace na
tayashi zabe anbashi sautu ne,matar abokinsa.
Har aunty na tambayarsa wace ce? Ban mantuwa
ya gwasaleta yace,ina ruwanki dako wacece
tunda bake na sanya zaben ba?
Batayi fushi ba,amma tabar wurin. Nace, yaya
kmr wa take? Sai cewa yayi,kmt take. A lkcn na
dade ina mamakin ya abokinsa zai auri karamar
yarinya kamata?
Kin ganesu ko?
Na fada jikinsa ina dariyar kunya,wato ni ya
maida matar aboki?
Na gode yaya, na gode......
Ya rufen baki da hannunsa, nine zan gode miki
meena,Allah ya barmu tare.
Nace amin.
Yaushe zaki ban 'yan hudu?
Da sauri na boye fuskata jikinsa ina dariya,ya dan
doki bayana, SHY GIRL. Yana dariya shima.
Munyi shiru babu mai cewa uffan,ya janyoni
jikinsa na fada da karfi. Kai yaya wai mene ne
haka? Na fada cikin shagwaba.
Ya lumshe ido,kunya zan cire miki,tunanina ta
fita,ashe da saurana....
Nayi saurin rufe fuskata a jikinsa, a ni meena da
fa tsorona akeyi,don Allah baki mamakin ganinki
kwance o jikina ba?
Nayi murmushi, inayi ma sosai ma.
Lallai ni kuwa na dade ina tunanin ranar dazan
rungumeki na danyi kissing din karamin bakin
nan.
Keda abun ya dameni kwarai,sai dabara ta fado
mini tunda kina kyamar tsartar da miyau da
nakeyi,kawai nace zan dura miki shi baki.
Ya tallabo fuskata na runtse ido sbd kunya,ina
tsoron hada ido dashi ba tun yau ba,akwai wani
abu dake cikin idanuwansa wadanda ke haifar
mini da kasala ga faduwar gaba.
Da frko nayi tunanin tsoro ne ke haddasan
hakan.amma daga baya na gane matsananciyar
kauna ce.
To wai idan haka ne tun yaushe kenan na kamu
da son ya faruk? Kar dai ace tun ina karama
sonsa ke damuna,kai ba lkcn bane....to yaushe
ne....?
Ranar dana fara zuba miki yawu a hannu, sai na ji kamar kissing dinki na yi a bedroom(en uwa a kiyayi irin paruwar hakan sabida Shaidan la'ananne)
dinki,wlhy meena saura kadan shaidan yaci
galabata a kaina shiyasa kikaga na fice dakin da
sauri.
A tunanina hakan zai samar min sauki,amma
abinda bansani ba nayi babban kuskure,na rantse
da Allah meena,gaba daya hnklna ya gama tashi
da kaunarki.
Washe gari na tafi garhi idan baki manta ba
harna siyo miki waya. To a kaduna nayi cinikinta.
Wlhy kmr mahaukaci na dinga yiwa su baba kuka
da hawayena,abin takaici sukaki amincewa
wanda a lkcn zuwana ne na takwas da maganar.
Wai Allah jikan abba yace kada a sake a sanar
daku dangantakarmu.
Ranar da nayo miki waya nace ki fito falo,ina son
magana dake cikin dare,wlhy meena lkcn kallonki
kawai nake sonyi,bana son zuwa dakinki
sbd gudun rudun shaidan. Kika kife mini ciki
ranar har kuka nayi,ga bakin ciki ana neman
haramta mini ke,ga na jamila don tun lkcn bama
kwana daki daya tuni na koreta ta koma nata, da
yake munafuka ce ko a jkinta.
Duk wani hali da kika shiga gidan nan a
kaina,wlhy ina sane kawai i'm just pretending.
Allah yaga zuciyata nayi hakan ne don kawai na
jarrabaki sosai,kidan wahala donki gane
muhimmancin sona.
ya yi dariya,wallahi kinji na rantse? tun a tapiyarda mukayi na fahimci son da kike yi mini,kawai
akwai wani abu da kika dora wa zuciyan a
kaina,wanda a lokacin babu wanda ya isa ya
kankare miki shi.Abdullahi ne mutumin farko da
ya fara sanar da ni hakan,bayan na fahimce ki.
wata rana da daddare na je dakinsa muna hira
akan aure da nake son karawa ban di fada masa
yarinar ba.Bana mantawa ya kalleni yana
dariya,kasan wani abu yaya? Na girgiza kai,Akwai
wani abu da na fahimta tsakanika da meena.....A
lokacin ba ki ji yadda gabana ya fadi ba,tunanina
ko ya gane ina son ki ?Amma sa na ji ya
ce,wasa-wasa yarinyar nan kishinka ta ke
yi,saboda rashin wayo lokutta da dama ina lura
da ita,ba ta son kana shishige wa Aunty
jamila,nan da nan sai ta daure fuska ko ta bar
wurin,musanman idan ka tsakaniku ba,wata rana
sai anyi karamin yaki gidan nan,tana iya furta
maka so gaban Aunty jamila,ita ma ta rama abin
da ta ke yi maka.kai kowa ina lura da ita ko
magana ka cika yi wa Aunty sai ta
harareta,wanda baka san tana yi ba.Kinji fa?tun
daga ranar na saki da al'amarin Abdullahi,becau
se i realized yaron he is very sharp and
intelligent.sai dai na basar kawai tare da ce
mishi bana son zargi.firar daga nan ta kaste
ranar,maganarsa kuwa na yi wajen wata tana
damuna.Baban kano kuwa ban sami matsalarsa
ba,cewa kawai ya yi,naje duk yadda muka yi da
su baban inyi biyayya.kallonki

Please Login or Register in order to submit comment