Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Ji tsiya, Driver kuma?" Nihad ta kasa cewa komai tayi tagumi, Husnah tace "Tabb shine kika yi shiru, to me kike jira da har yanxu baki tambayesa ba?" Nihad tace "Toh me xan ce masa? Bayan ban ga sanda ya dauka ba, Har wayata fa na cikin jakar, idan ba sata yake son yi ba ai xai ba Aminu ya ajiye min" Husnah tace "Ehh lallai wannan mutumin ya rika, shi ke ta ja min busy kenan? Wato dai har ya bude jakar" Nihad ta xaro ido tace "Na shiga uku, gashi kin xuba abubuwa kika ce cikin jakar" Husnah ta mata wani kallo tace "Ke dalla to meye, koma me ya gani cikin jakar ba shi ya ga duhu ba, kuma ma bansan uban me kike jira da har yanxu baki tambayesa jakarki ba, ko tsoronsa kika fara ji? ai ba ma tambayarsa xa ki yi ba wai ko ya ga jaka ko bai gani ba, kawai ce masa xa ki yi ya baki jakar ki da ya dauka kar kiyi masa rashin mutunci, kuma kada ya sake ta6a maki kayanki ko da kuwa a titi kika yar don baki aikesa ba" Nihad dai ta rasa abun cewa tunani iri iri ke yawo a ranta, Husnah ta kyabe baki tace "Ni dai ki adana min prophylactics din nan foreign ne ba na kasar nan bane kuma tsada ke garesu, Codeine din kuma shi ma nasan ba kya sha, kar ki je ki xubar ki adana mana gaskiya" Tashi Nihad tayi ta bar mata wajen ta koma seat din baya abun duniya ya isheta, yanxu mutumin nan duk ya ga abinda Husnah ta saka mata a jaka? To amma ya ma yi mugun rainata gaskiya, waye shi da har xai bincika mata jakarta?? A daddafe Nihad ta yi lectures daya tace xata tafi gida, Husnah tace "Ke don Allah ki saki ranki, ko Abba ne ya ga jakar nan ya dauka ya bincika ai sai haka, me xai dameki akan wani shegen driver dinku ya bude jakar ki? Ae rashin mutunci mafi muni xaki masa idan kin koma gida anjima, ni abinda ya fi damu na ma wayarki ne wllh, don matsiyacin sai ya iya dauka yace xai je ya siyar bai san wayar nan sai ta siye duk yan kauyensu ba, yanxu kawai ki xo mu je police station, cikin lokaci kalilan xa ayi tracking" Nihad ta zaro ido tace "In tona ma kaina asiri kenan, kin zata na gaya ma kowa cewar na yarda jaka da waya a ciki? To har Nihal bata sani ba" Husnah tace "In kince ayi cikin sirri babu tonon asiri ai sai ayi hakan, duk fa mutanena ne, amma wllh so nake a walakanta sa idan aka ga wayar a wajensa, a nakada masa shegen duka" Nihad tace "Husnah bari in je gida ko xan ji saukin abinda ke damuna, i can't endure anymore" Husnah ta ta6e baki tace "Wllh kina da sa ma kai damuwa, duk ki bada space din da lamarin driver xai dinga damunki haka, to wai shi wannan driver din daga ina ya xo yake abu isa isa da gadara haka?" Mikewa Nihad tayi tace "Duk yanda ake ciki xan kiraki da wayar Nihal ai tana da number ki" Daga haka ta fice daga hall din, tun da ta fara school din bata ta6a trekking da kafafuwanta har bakin titi ba sai yau, haka nan ta tsayar da adaidaita shi ma xata iya kirga iya sau nawa ta hau sa a rayuwarta, suna isa gida ta sauka ta bude jakarta ta basa kudi sannan ta shiga gidan, Aminu ne kawai bakin gate, ta Ι—an bi compound din da kallo sai kuma tayi kasa da murya tace "Aminu baka tambayar min driver din can ko ya ga jakata ba kuma?" Aminu yace "Anya, don ina da yakini da ya gani xai nuna min, ai shi mutum ne me gaskiya da amana" Ta wani galla masa harara tace "Dallah Malam rufe min baki, duka duka kwananku nawa tare xaka san yana da gaskiya da amana, ashe kai dolo ne ma ban sani ba? To bari ka ji wayata ce ta kusan miliyan daya da rabi a jakar nan" Driver ya gwalo ido yace "Subhanallahi, subhanallahi...." Nihad ta saci kallon wanda ke tahowa ganin driver din ne ta daure fuska ta juya ta nufi cikin gida da sauri, xaunawa Khalil yayi gefen Aminu ganin yanda yake zaro ido kamar mara gaskiya yace "Me ya faru kake buda ido haka" Aminu yace "Ba nace maka ta yarda jakarta ba daxu har tana tambayata ko na gani, to wllh wai har da wayarta na miliyan biyu da rabi a cikin jakar" Khalil ya ciro karamar wayarsa yace "To ta huta..." Aminu yace "Atoh dai, Ta kuwa huta wllh, don yau tana sa uban a gaba ya siya mata sabo wallahi sai ya siya, sai dai uwarta ta hana amma tsaf in dai ita ce xai siya mata, kai kaji waya har miliyan uku, ni yanxu na samu irin kudin nan ai kauye xan koma in tada gini malam, inci me kyau in sha me kyau, sannan in kara mata biyu...." Khalil na kallonsa yace "Haba?" Aminu yace "Wllh tllh, albashin namu fa Hajiya ke amsowa a wajensa ta bamu, Ni dai ban san ko nawa yake bata ba amma dubu 50 50 take bamu, kuma da farkon xuwana akwai wani lkcn da ya ta6a bani da kansa wllh dubu 70 ya bani, to kilan dai har da kyautatawa ce irin tasa ban dae sani ba" Khalil dae bai ce masa komai ba. Nihad na shiga cikin parlor ta tafi dakinta direct, xaunawa tayi gefen gado ta rafka tagumi abun duniya ya isheta, tun da shegen mutumin nan ya xo gidan nan bata da kwanciyar hankali, bude kofar dakin aka yi Nihal ta shigo da sallama, Nihad ta daga kai tana kallonta, Nihal ta karaso ta xauna gefenta tace "Amma ba ki jira ku gama lectures din yau ba kika taho ko" Nihad ta yatsine fuska tace "I am tired, kawai shine na dawo" Nihal tace "Toh ki kwanta ki huta, xuwa yamma sai ki rakani shopping din, kinsan gobe sunday xan tafi fa" Nihad tace "Wa xai kai ki shopping din??" Nihal tace "Khalil" Nihad ta juya ido tace "Waye haka?" Nihal tace "Driver..." Nihad ta bude baki ta rike ha6a tace "Wai khalil? Shi uban wa ya basa wannan suna yana driver? Ni fa na xata kinyi wani saurayi ne Khalil ban sani ba, shi driver din ne yace maki sunansa khalil?" Nihal dai kallonta kawai take, Nihad ta gyada kai tace "Tabdi, ana iskanci a duniya, shi yasan ma'anar Khalil din ma kuwa?? Yau naga mutumi da karfin hali, ke kuma wawuya shine kika yarda sunansa Khalil, to wllh karya yake ba abinda ya hadasa da wannan sunan" Nihal tace "To ko ma dai meye sunan Abbanmu garesa, ko so kike in kira sunan Abba gatsau?" Nihad tace "Toh meye don kin kira tunda ba sunan Abban kika kira ba? Meye don kin ce masa Ibrahim ba shine sunan nasa ba? Wato dai ke kika makala masa khalil din kenan?" Nihal tace "Aa, yace haka ake kiransa dama, ni bani na sa masa ba" Nihad ta bude baki tace "Ji shegen karya, to karya yake munafuki, uban wa ke ce masa haka? Amma fa mutumin nan yayi mugun raina maki wayo ma dai, a kauye wa yasan wani khalil, dama Halilu yace shine xan yarda, to wai tsaya ma tukun, fira ku ke har yake gaya maki sunansa khalil??" Mikewa Nihal tayi tace "Woo na gaji da question and answer din nan, Ko ma meye sunansa ba abu bane da za mu tsaya muna bata lkci akai, ni dai anjima ki shirya mu je Sahad store din" Nihad tace "Allah ya kiyaye in dai can xaki wllh baxan je ba, ga wajaje irinsu wellcare kice min Sahad, ai kowa da kowa ke xuwa Sahad" Nihal ta juya ta kalleta, sai kuma ta girgiza kai kawai ta fita daga dakin. Nihad ta rike ha6a tace "Ji maye wai khalil, shi a lallai ya xo gidan masu kudi bari ya maida sunansa irin na yan gayu wai khalil, aa Khalo ba khalil ba" Ta ja tsaki ta mike ta shige bandaki. Ta a fitowa ta koma gefen gado da take xaune ta xauna, tunani ta shiga yi a ranta, to ko dai taje can chalet din da kanta ta duba jakarta ne? Ta kalli agogo lkci daya ta mike ta fito main parlor Umma tace "Aa har kin dawo er baba" Nihad ta gaisheta sannan ta fita balcony har sannan taga yana xaune tare da Aminu a bakin gate, komawa ciki tayi ta shiga kitchen sannan ta bude kofar kitchen din da xai sada ka da back yard din gidan wanda ta nan ma xaka iya xagawa har xuwa Chalet, ganin yanda Hafsah ke kallonta ta sha kunu tace "Ya dai da kallo haka ke kuma?" Hafsah ta kauda kanta, Nihad ta fita da sauri ta xaga ta baya sai Chalet, bata ga takalmin kowa a bakin kofar ba alamar su Isiyan ma duk basa nan kenan, a hankali ta bude kofar tana leka parlon sannan ta shiga, da sauri sauri ta fara dudduba parlon, har xuwa dining area bata ga alamar jakarta ba, har bandakin dake parlon sai da ta bude, wanda sai da ta kusa amai, ta kullo da sauri tana yatsina fuska ta yi hanyar dakunan chalet din, duk dakuna biyun dake a bude sai da shiga tana tottoshe hancinta tsabar tsami da doyi, na ta bincika kaf Ghana must go da ta gani a dakunan amma bata ga jakarta ba, dakin da khalil ke ciki ta murda ta ji a kulle, to ko dai nan dakin aka ajiye jakar nata shine har da kullewa da makulli, tunanin inda xata fara nemo spare key ta shiga yi, can ta zare key din dake jikin kofar su Isiya ta juya ta fita da sauri ta xaga ta koma kitchen, sai da ta wanke hannunta da morning fresh ta hada har key din tana yatsina fuska sannan ta shigo parlor, har wani tashi taji xuciyarta ke yi sbda warin da ta dinga inhaling, kazami irin wannan har shi xai takura mata a gidan nan ya dinga shiga gonarta, dubi wajen da suke kwana wanda ita ko pig take rearing baxata bari yayi rayuwa a irin wannan kazantaccen wajen ba, tana wannan tunanin ta faki idon Umma dake waya ta shige bangaren Abbanta, direct dakinsa ta wuce bayan ta shiga parlor, nan ta hau bude duk wani drawer da ke dakin, a bedside drawer ne ta ga bunches of spare keys na gidan, tayi murmushi ta kalli na hannunta sannan ta hau duba irinsa, kaf irinsu guda uku dake wajen duk sai da ta dauka incase of necessity sannan ta mayar da drawer din ta kulle ta mike ta fice daga dakin, kitchen ta sake bi ta xaga xuwa Chalet din, da sauri ta shiga ciki ta nufi hanyar rooms din, dakin dake kulle tayi facing, ta hau gwada makullen hannunta da sauri da sauri, lkci daya ta bude dakin, wani farin ciki ne ya lullubeta, ta shige ciki ta kulle tana bin ko ina da kallo gabanta na faduwa? Banda kamshi babu abinda ke tashi a dakin, rigarsa da ta gani saman gado ya sa ta gane shine a dakin, rike ha6a tayi.... to gidan uban wa ya samo wannan turaren da ya xuba a dakin haka, bata daina bin dakin da kallo ba ta karasa middle of the room, the room look so different kamar ba a chalet din ba, babu tarkace da kaya kamar irin na su isiya sannan everywhere looks so neat and tidy, ta kyabe baki without bothering ta hau yin abinda ya kai ta dakin, Duvet ta gani kamar an rufe abu da shi ta tafi da sauri ta daga sai ga jakarta a ajiye saman gadon, xaro ido tayi wani farin ciki ya lullubeta, ta bude jakar tana bincikawa da sauri, banda abubuwan da Husnah ta xuba mata a jakan sai nata tarkacen bata ga alamar wayarta a ciki ba, nan kuma ta marairaice tana bin dakin da kallo, a ina to ya ajiye mata wayar?? Sake jakar tayi ta nufi tasa jakar kayan dake dakin, sai bin jakan take da kallo kafin ta durkusa ta xuge zip din, ko karasa bude zip din bata yi ba tayi ido hudu da wayarta, babu bata lkci ta dauka, dai dai nan kuma aka bude kofar dakin, tsabar rudewa da tsorata da tayi bata san sanda ta mike ta saki wayar jikinta na rawa tace "Wayyoo... Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"



07087865788 ✍🏻


πŸ’–πŸ’– *NIHAAD*πŸ’–πŸ’–




By _Khaleesat Haiydar_πŸ“–βœπŸ»





12.....


Tsaye Khalil yayi bakin kofa yana kallonta with a weird facial expression, bata sake yarda sun hada ido ba banda faduwa babu abinda gabanta yake, sai kuma ta hade rai xata durkusa ta dau wayarta da ya fada saman jakar, yayi hanzarin shiga cikin dakin ya sa kafa yayi changing position din jakar yana kallonta, tana ganin haka ta bi jakar cike da tsiwa tace "Wai kai yaushe na fara wasa da kai a gidan nan ne da xaka dinga raina ni haka? ina ruwanka da kayana ko a saman titi na jefar da xaka ta6a min, how dare you?" Tana fadin haka ta ja tsaki ta kara dukawa zata dau wayar, ya dauke jakar a wajen, buda baki tayi tana kallonsa da mamaki, sai kuma ta nufesa da nufin cakumosa yanda ta saba amma ganin kallon da yake mata sai kawai ta tsaya tana harararsa, cike da rashin kunya tace "Wallahi idan baka mika min wayata a dakin nan ba xan maka sharrin da har abada baxa ka mance ba, ka bani wayata nace..." cikin kakkausar murya yace "Idan kin fasa..." Ta kankance ido tana kallonsa da mamaki jin abinda yace, ji take kamar ta kifa masa mari, da a waje ne wllh ba abinda xai hanata marin sa, Yana mata wani kallo ya ajiye jakar a gabanta yace "Idan kin isa ki ta6a" A fusace tace "Toh wai kai idan kana sata sai ka rasa wayar warce xaka sata sai tawa a gidan nan? A kaina satarka xai kare? Idan na ta6a uban me ka isa ka min? Wllh sai na ma sharrin da baxaka ta6a mantawa da ni ba" Duk wannan babatun da take bata yarda ta ta6a jakar ba, banda faduwa kuma babu abinda gabanta yake barin da ta ga irin kallon da yake mata, jakarta dake gefen gado ya nufa ya dauka ya dawo inda take ya jefa mata a gabanta yace "Dauki ki fita... Abubuwanki dake ciki xa su fi wayar muhimmanci gare ki" Kamar xata yi kuka tace "Ni wllh ka bani wayata kar in hadaka da Abbana da yayana" Da Husky voice yace "Dauka jakar ki nace ki fita" Bata ce masa komai ba ta tafi ta dau jakarta tana jin kamar ta fashe da kuka, ta nufi kofar tana tafiya a hankali, ta gefen ido ta saci kallonsa sae kuma ta dawo da gudu ta fixgo jakarsa ta nufi kofa a guje kamar an aikota, tana shiga parlorn plate din da su Isiya suka ci abinci suka bari a wajen ta take sai da ta tafi tsuuu kamar xata tashi sama sae ga ta a kasa timm, jakarsa kuma yayi can hanyar kofar fita, nata kuma yayi wajen Tv, gwalo ido tayi tana numfashin wahala da kyar tace "Wayyoo Abbana, wayyo bayana ya karye" tsaye yayi bakin corridor din dakunan ya rungume hannunsa ya jingina da pillar din wajen yana kallonta irin dai dai kenan, ta fashe da matsanancin kuka tana jujjuya kanta tace "Wayyo Allah na a zo a taimakeni bayana ya karye, baxan iya tashi ba" karasowa cikin parlon yayi zai tafi ya dau jakarsa, tana ganin haka ta yunkura ta tashi ta nufi kofar da gudu ta figi jakar tasa, a dari da sittin ta fice ko bin ta kan nata jakar bata yi ba a parlon, bai san sanda ya bi ta ba, tuni har ta dau hanyar kitchen yace "Keeeee dau wayarki ki ajiye min jakata" haba da ya kara tuna valuable dinsa dake jakar kawai ya bi ta, tana isa kofar kitchen ta murda ta ji sa a kulle, ta gwalo ido tace "Na shiga uku, Hafsahhhh uban wa yace ki kulle" tana ganin ya nufota kawai ta ajiye jakar a kasa tana kallonsa xuciyarta na bugawa, yana isa gabanta ya duka ya dau jakarsa sannan ya bar wajen. Nihad bata san sanda ta fashe da kuka ta sulale wajen ba tana cewa "Wallahi sai na maka rashin mutunci a gidan nan, kawai mutum kamar maye ya sa min ido a gidan ubana duk ya bi ya takura ni" Sai kuma ta mike ta xaga ta shiga cikin gidan, Umma dake parlor ta kalleta daga sama har kasa tace "Lafiya?" Nihad tace "Ina Hafsah?" Sai ga Hafsah ta fito daga bangaren Mumy, Nihad ta nufeta tana huci tace "Ke mahaukaciyar wace gari ce da xaki rufe min kofa bayan kinsan na fita?" Hafsah tace "Ayya kiyi hakuri wllh ban san baki shigo ba, na xata kin bi ta gaba kin shigo" Nihad ta mata tsawa tace "Aa ta hancinki na bi na shigo" Tsaki ta ja ta juya ta bar wajen kamar xata tashi sama. Umma dai ta bi ta da ido, direct dakin Nihal ta tafi, Nihal har ta gama shiryawa tana kallon Nihad tace "Ohk baxa ki rakani din ba" Nihad tace "Nihal idan na fara yi ma wancan driver din rashin mutunci ke ce ta farko da ke fara jin haushi, wllh duk abinda na masa kar ki ga laifi na, don haka tun wuri ki je ki samesa ki amso min wayata da jakata dake wajensa" Nihal dake kallonta with confusion tace "Me ya kai jakarki da waya wajensa kuma?" Nihad tace "How will i even know?? I mistakenly dropped my bag at the gate jiya, ko sani ma ban yi ba...." Nihal ta katseta tace "How will u mistakenly drop a whole bag not even purse Nihad?" Nihad ta hade rai tace "And that is none of ur concern, kawai abinda nace maki shine ki amsar min kayana a wajensa kar in fara rashin mutunci na, don wllh idan bai yi hankali ba sai na gaura masa mari kuma ba abinda xai faru" Dariya ta ba Nihal, sai dai bata yi ba, tace "Ke yanxu wa yace maki shi ya dau maki jaka?" Nihad tayi saurin cewa "Aminu ne ya gaya min, kuma don't forget wayana na ciki" Nihal tace "Amma ai ba yaki bane, xa ki iya samunsa politely ki tambayesa jakar, na tabbata xai baki" Nihad ta yi wani dariyar rainin hankali tace "Koh? To sannu, shi drivern xan je in sama politely sbda ina tsoronsa ko? To abinda baki sani ba, Aminu ce min yayi satar jakar yayi niyyarsa yayi shiru, bai kuma san Aminun ya gansa ba, to idan yana sata sai ya fara ta kan kayana a gidan nan? Kaii amma mutumin nan ya kara bani tsoro wllh" Nihal ta dau karamin handbag dinta tace "Yamma na yi, xan tafi shopping" Nihad ta hade rai tace "Ohk baxan raka ki ba kenan?" Nihal tace "Oh na xata kince ai baxa ki ba" Nihad ta harareta tace "Yaushe nace maki haka?" Nihal tace "Toh dauko hijab dinki mu tafi" Nihad bata ce komai ba ta juya ta fita, Nihal ta bi bayanta, babban dalilin da yasa Nihad xata shopping din nan kawai don Nihal ta amsar mata jakarta da wayanta gun khalil, Nihal na fitowa parlor Umma tace "Har kin shirya auta?" Nihal tace "Eh na shirya" Umma tace "To kar dai ki manta turarena" Nihal tace "Toh baxan manta ba" Umma tace "To ya kika tsaya, ga yamma na yi" Nihal tace "Ina jiran Nihad" Umma ta kalleta tace "Nihad? ita tace maki xata?" Nihal tace "Eh" Umma tace "Ke da xaki yi maza kije kiyi abinda xai kai ki ki dawo, meye kuma sai kun yi zuga kamar yan matan amare Nihal" Nihal tace "Aa nafi son mu je tare" Umma tayi shiru bata kuma cewa komai ba, Nihad ta fito sanye da Hijab ita ma, Tana kallon Nihal tace "Mu je" Nihal ta kalli Umma tace "Sai mun dawo" Umma tace "Allah ya tsare" Nihad tace "Umma xa a taho maki da wani abu ne?" Umma tace "Aa babu komai, Allahj ya tsare" Fita suka yi daga parlon, Nihad ta hade rai ganin khalil da Aminu, Nihal ta nufesu tana kallon khalil tace "Idan baka yin komai xa mu iya tafiya yanxu?" Ya mike yace "Ohk" Motar ya nufa, Nihad ta bi sa da wani shegen kallon tsana, duk Aminu na lura da ita, Nihal ta bude front seat xata shiga Nihad tayi saurin cewa "Me xa ki yi a gaba ke kuma?" Nihal tace "I prefer seating here" Nihad ta ja tsaki ta bude back seat ta xauna, Tuni mai gadi ya bude gate din suka fita compound din, Khalil yace "Wani supermarket din xa mu Hajiya?" Nihal tace "Ko wanda ya fi kusa" Nihad tace "Kai Malam mu tafi Sufi Mart" Khalil dai driving dinsa kawai yake, next thing kawai Nihad taga ya dau hanyar wani store din daban, ta kankance ido tace "Wai kai kurma ne baka ji inda nace ka kai mu bane?" Driving dinsa kawai yake kamar bai san da shi take ba, Nihal ta juya ta kalleta tace "But ai duk daya ne Nihad" Nihad ta galla mata harara tace "To da ke nake ke kuma?" Nihal ta dauke kai bata ce mata komai ba, A Danja Khalil ya sauke glass din motar ya amshi facemask hannun wani yaro sannan ya basa kudi ya kulle glass din, Nihad ta kyabe baki, sai kuma ta ja tsaki ba dai wanda yace mata komai a motar. Parking Khalil yayi a inda aka tanadar don parking a harabar Supermarket din, ya kashe motar yana kallon Nihal, tace "Baxa mu dade ba in sha Allah" Nihad tace "Toh da kike cewa haka wa xai dauko kayan idan mun gama siyayyan? Ai sauka shi ma xae yi daga motar ya kwaso kaya ba wai zama xae yi a driver seat ba" Nihal ta kalleta tace "But the staff in there will do that, it's not necessary" Nihad tace "Wallahi u have a very big problem, what is then the use of him? Why then did he have to drive us here if he can't come out and help? Sannu good Samaritan" Nihal ta kalli khalil tace "Sae mun fito" Yace "Toh a fito lafiya" Ta bude motar xata sauka yace "Amma bari in sa maki number ta idan kin gama sae ki kirani in dau maki kayan" Tace "Akwai masu daukan kayan a ciki kar ka damu" yace "Toh idan da wani abun sae ki kirani" Tace "Toh" wayarta ta mika masa yayi dialing number din sa sannan ya mika mata, amsa tayi ta kira number, karamar wayar dake aljihunsa ya fara ring, tace "Nagode" daga haka ta bude motar ta sauka, Nihad dake ta kallon ikon Allah ta ja tsaki me tsayi sannan ta sauka, ko barin wajen motar basu yi ba tace "Me ye na wani exchanging digit da driver idan ba kaskantar da kai ba Nihal? Me yasa ke kin fiye over sabi a rayuwarki? Ni ban san me yasa ke da Mumy ku ke yin haka ba wllh" Nihal taki tanka mata, Nihad tace "Though wannan ba damuwata bace, my problem is ban ji kin masa maganar jakata da wayana ba?" Nihal tace "Xan yi" Suna shiga mall din, Nihal ta fara daukan abubuwan da ta xo siya tana xubawa a cart Nihad na tura mata cart din, duk inda suka gifta sae an kallesu don babu wanda bazai ce su ba yan biyu bane, they look so cute, beautiful and adorable, kawai dai Nihad ta fi Nihal haske da tsayin hanci with more cute lips, ita kuma Nihal ta fi Nihad

9 Comments On NIHAAD
avatar
lawal-1

1 year ago

Reply

The book is not complete thank you

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to lawal-1

tuntubi wannan nambar 07087865788 don siyan complete na littafin

avatar
aishat-5

1 year ago

Reply

Gaskiya naji dadi book dinnan

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to aishat-5

Wow munji dadi da hakan

avatar
maryama-4

1 year ago

Reply

Is very fantastic Allah ya Kara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to maryama-4

Ameen

avatar
maryama-4

1 year ago

Reply

Allah ya Kara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to maryama-4

Ameen

avatar
maryam-3-9-1

6 months ago

Reply

This book is so interesting

Please Login or Register in order to submit comment