Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cika, though she isn't chubby but ta fi Nihad warce iska me karfi idan aka yi xae iya tafiya da ita... Lol, tsayinsu daya haka ma shape din large eyes dinsu, sae dai kana kallonsu kasan Nihad tafi Nihal wayewa nesa ba kusa ba, ganin Nihad isn't taking anything Nihal tace "But kince kema xa kiyi shopping kin fasa ne?" Nihad ta yatsina fuska tace "I won't shop here" Nihal bata kuma ce mata komai ba, har ta gama daukan duk abinda xata bukata a makaranta, sannan ta dau ma Umma turarurrukan da tace, wani tsadadden turare da ta san Nihad na so ta daukar mata, Nihad ta amsa tace "Thank you" Daga haka ta saka shi cikin cart din, Nihal ta dau wayarta tayi dialing number da Khalil ya sa mata with the intention of asking him a question, can kuma dae kawai ta katse ta fasa kiran nasa sbda Nihad dake ta kallonta, wasu turarurrukan biyu ta deba ta sa a cart sannan tace "Shikenan na gama" Nihad ta tura cart din suka nufi counter. Suna tsaye counter din Nihad tace "Na manta xan dau Sanitary Napkin" Daga haka ta juya zuwa in da zata dauka, khalil ya shigo cikin mall din with facemask, yana hango Nihal a counter ya nufi wajen yana kallonta yace "Naga kiran ki..." Nihal tace "Oh bansan ya shiga ba" Yace "Ohk, sun gama in dau kayan?" Xata yi magana kawai wata yarinya kamar balarabiya ta nufosu tana kallon Khalil closely tace "KJay?" Juyawa yayi da sauri, Ta wara ido kafin ta ce komai yace "Ohh Nadiya, daga ina haka?" Ta kyalkyale da dariya tace "How wonderful i recognized u upon the nose mask KJay..." Ya kalli Nihal da sauri yace "erm, yi hakuri don Allah minti daya..." kawai yace "Mu yi magana a waje Nadiya" yana fadin haka ya bar wajen da sauri, Sai a sannan Nadiyar ta kalli Nihal dake ta kallonta daga sama har kasa, Nadiya ta daga mata hannu tace "Hi" Nihal tayi murmushi ta daga mata hannu ita ma, juyawa tayi ta bi bayan khalil da har ya fita mall din, Nihal ta bi ta da kallo, har gadon baya ta saki dogon baΖ™in gashin kanta, daga ganinta kasan half cast ce, sae ga Nihad ta ajiye Sanitary Napkin din a kan counter, tana kallon Nihal sai kuma ta kalli inda take ta kallo amma tuni Nadiya ta fita daga mall din, Nihad tace "What are u staring at?" Nihal ta dauke kanta da sauri tace "Nothing" ma'aikatan wajen ne suka kwasar masu kayan xuwa mota bayan an biya kudin kayan, Khalil na jingine jikin mota ya rungume hannunsa, ganin sun fito ya xaga ya bude booth din motar, wanda ya tayasu fito da kayan ya shigar cikin booth, Nihal ta bude handbag dinta ta dau dari biyar ta basa, yayi mata godiya sannan ya wuce, tuni Nihad ta shige bayan mota, Nihal ta xauna gaban motar, ya tada motar suka bar shopping mall din. Tunani iri iri ke yawo a xuciyar Nihal, she can't even think straight, Nihad kuma ta kasa kunne taji Nihal tayi ma Khalil maganar wayarta amma shiru, har ta shirya rashin mutuncin da xa tayi mata suna shiga gida don dab suke da isa gidan kawai ta ga Nihal ta kallesa tace "Ina son xan maka magana don Allah" Bai kalleta ba idonsa na kan titi yace "Toh ina jin ki Hajiya" Ina a polite state tace "Jakar Nihad yana wajenka ko?" Yayi Ι—an yi shiru kamar baxai ce komai ba, Nihal dai kallonsa kawai take, sai kuma yace "Eh yana wajena" Tace "Toh xaka bani don Allah idan mun isa gida" Yace "Toh ba damuwa, in sha Allah" Nihad ta galla masa wani tsinannen harara ta kauda kai, da yace baxai bada ba ya gani mana, suna isa gida yayi parking Nihad ta bude motar ta sauka ta tsaya nan parking space babu yabo babu fallasa tana jiran jakarta. Nihal ta sauka ya bude mata booth ya saukar da kayan kasa, xagawa tayi xuwa gun Nihad tace "Ki tafi ciki, ai xan amsar maki" Nihad tace "Nooo, Baxan tafi ba, ina nan ina jira" Khalil dake jin abinda tace, ya dai kwashi kayan Nihal gaba daya ya kai mata can bakin kofar shiga main building din gidan ya ajiye, Nihal na tsaye har ya dawo yana kallonta yace "Anjima da daddare xan baki jakar idan na shiga can bangaren kenan" Nihad tace "Ban gane anjima da daddare ba, kai ko kunyan sata baka ji ba a ranka, to tun wuri ka shiga yanxun nan ka fito min da jakata kar in tara maka mutanen gidan nan, wallahi rashin mutunci xan maka don ma kaji in gaya maka" Khalil ya kalleta yace "Toh" Daga haka ya tafi wajen mai gadi yayi xamansa, a fusace Nihad ta kalli Nihal tace "Kina dai gani ko, wllh sai na nuna masa wacece ni yau kar ya fito min da jakata" Nihal tace "Ba sai da nace ki shiga ciki xan taho maki da shi ba, toh ai gashi nan kin ji" Nihad tace "Na ji me? Ai jakata baxata kara minti biyar a hannunsa ba, bari ya gani" Tana fadin haka ta juya fuuu ta wuce cikin gida, ita damuwarta kar ya ba Nihal jakar ta bude taga kayan Husnah dake ciki, Nihal ta nufe Khalil dake kusa da mai gadi ta mika masa ledan hannunta tace "Gashi nan na daukar maka kai ma, amma don Allah kayi hakuri ka bamu jakar yanxu" Yana kallon ledan yace "Nagode sosai Hajiya, Allah ya saka da alkhairi.... Bari in dauko maki jakar" Daga haka ya mike ya nufi chalet, ta bi sa da kallo sannan ta bi bayansa, da ya lura tana biye da shi, sai yayi slowing pace dinsa, tana isa kusa da shi tace "Ina son xan maka tambaya" suna ci gaba da tafiya ba tare da ya kalleta ba yace "Ohk ina sauraronki?" Tace "Tell me... who are you?" Ya Ι—an yi jim sai kuma yayi saurin cewa "Ban gane abinda kike nufi ba" Tace "Nasan ka gane" Yace "Da gaske ban gane ba" suna isa Chalet din kafin tace komai, yayi maza yace "Ina xuwa in dauko jajad yanxu" daga haka ya shiga ciki ta bi sa da kallo, ba a dau lkci ba ya dawo rike da jakar Nihad, a bude zip din jakar yake, ya mika ma Nihal ta amsa, babu abinda idonta ya fara cin karo da sai kwalban Codeine da prophylactics da ke saman jakar, lkci daya ta rude apart from being shock, bata san sanda ta rungume jakar ta juya da sauri xata bar wajen ba, yace "Ga wayarta" Nihal ta juyo da kyar amma ta kasa barin su hada ido, ta dai amshi wayar da yake mika mata ta juya ta bar wajen tana tafiya da sauri, tana shiga gida direct dakin Nihad ta wuce, Nihad xata fito daga dakin kenan suka kusa cin karo, Nihad ta koma baya, Nihal ta shiga dakin ta jefa mata jakar a kasa tana girgiza kai sadly tace "Nihad meye wannan a cikin jakar ki??" Nihad ta kalli jakar lkci daya gabanta ya fadi, Nihal ta karasa cikin dakin ta xauna gefen gado ta dafe kanta, Nihad dai sai kallon jakarta take tana tunanin abinda xata ma khalil taji sanyi a ranta, ko daxu da ta bude jakar bata ga abubuwan nan a saman jakar ba, wato shi ya daura su saman jakar ya bar zip a bude don Nihal ta gani, Bayan kusan minti daya Nihad ta kalli Nihal, hawaye ta gani idonta, Nihad tace "Look Nihal wllh wllh ba kayana bane na Husnah ne, haba don't u trust me?? kema kinsan i can neva posses such stuffs, i swear to God na Husnah ne, shi kuma munafuki algungumin da ya daura a saman jakar ya jira ya ga abinda xai faru da shi a gidan nan" Tana fadin haka ta durkusa ta hau tattara abubuwan dake cikin jakar ta kulle, Nihal dai bata ce komai ba ta mike a sanyaye ta ajiye mata wayarta a gefen gado sannan ta fice daga dakin.


07087865788✍🏻


πŸ’–πŸ’– *NIHAAD*πŸ’–πŸ’–




By _Khaleesat Haiydar_✍🏻



13.....



Zaunawa Nihad tayi ta dau wayarta ta bude, nan ta ga miss calls da ya wuce misali, ta shiga call logs ta ga kiran Aliyu guda daya wanda yayi mata tun da safe, bata san sanda ta sauke wani ajiyar xuciya ba, so he did call her, wani Murmushi tayi, tayi dialing number sae da ya kusa katsewa ya daga, tayi kasa da murya tayi masa sallama ya amsa, jin yayi shiru a hankali tace "Can you hear me?" Yace "Yea ina ji" tace "You called da safe, bani da lafiya shi yasa ban samu dagawa ba" Yace "Baki da lafiya? Me ya sameki?" Ta langwabar da murya tace "Na tashi da xaxxabi ne" Yace "Subhanallah, how are u feeling now?" Tace "Da sauki shi yasa har na samu na kiraka" Yace "Since when were u sick?" Tace "2 days ago" Ya dan yi shiru, sai kuma yace "I am sorry, Allah Ubangiji ya baki lafiya" Ta lumshe ido tace "Ameen" Yace "Hope kina iya cin abinci?" Tace "Ehh daxu na samu na ci" Yace "Get well soon dear" Ta dan yi shiru sai kuma tace "Kayi hakuri da abinda ya faru few days back" Yace "Nihad" Tace "Na'am" yace "Daga ina akayi employing driver din nan?" Tace "Wllh ban sani ba i just saw him over night a gidan" Yace "Ya sunansa?" Ta gyara xama tace "Halilu" Yace "Good, yana gidan har yanxu ko?" Tace "Yana nan wllh, rashin mutunci kuwa sae abinda yayi gaba, i have just decided in dinga hawa adaidaita from henceforth idan xan je makaranta" yace "You don't worry, i will bring an end to everything" tayi wani Murmushi tace "Trust u dear" Yace "A gidan yake permanently ko yana xuwa ya tafi ne?" Tace "Aa a nan yake permanently ba inda yake xuwa" Yace "Ohk, gobe xan shigo kano in sha Allah" tace "Toh Allah ya kai mu" Yace "Ameen, i will call u back later" Tana Murmushi tace "Alright dear" daga haka ya katse wayar ta lumshe ido ta bude cike da farin ciki, at last they will bring an end to this forsaken driver, tasan tun da har ya shiga trap din Aliyu kuma ya shiga uku. Nihal na ta xaune parlor a dining area har kusan karfe tara na dare, she her self don't even know what exactly she is sitting down there for, har Umma sai da tayi mata magana ta tafi ta kwanta ita da xata yi tafiya gobe, amma bata bar wajen ba, Farooq ya shigo parlon ganin ita kadai yace "Me kike yi a nan?" Ta kirkiri murmushi tace "Ba komai kawai ina duba waya ne" Yace "Ohk, xo ki amshi sako ki ba Aminu" Tace "Toh" Mikewa tayi ta bi bayansa har xuwa bedroom dinsa ya dauko wani takalminsa ya mika mata yace "ki kai masa" Ta amsa tace "Toh" Yace "Gobe da yaushe xa ki tafi?" Tace "Da safe in sha Allah" Yace "Ohk" Juyawa tayi ta bar wajen, tana fitowa compound ta tafi bakin gate inda Aminu yake, Bata ga Aminu a wajen ba sai khalil, yana ganinta yace "Barka da yamma Hajiya" Ta gyada kai kawai tace "Ina Aminu?" Yace "Ya Ι—an fita xai dawo yanxu" Tace "Ohk, ba nisa yayi ba?" Yace "Ehh ban san ko yyi nisa ba" Ta koma gefe ta tsaya tace "Ok i will wait" shi dai Khalil bai ce komai ba, but from all indication he was uncomfortable with her by his side, bayan kusan minti daya tayi breaking silent din tace "Daxu na maka tambaya baka ce min komai ba" ya ki kallonta yace "Ohh, yi hakuri Hajiya wani tambaya kenan?" Tace "Kawai cewa nayi, xan iya sanin ko kai waye?" Yayi shiru na few seconds, sai kuma yace "Ohk amma ina son ya kasance tsakanina da ke, don ba kowa nake ba labarina ba" Nihal tace "In sha Allah nayi alkawarin rike maka sirrin ka" Murmushi yayi ya gyara xama yace "Kinyi alkawari har yar uwarki baxa ki gaya ma" Nihal tace "Nayi alkawari" Yayi kasa da murya yace "Kamar yanda na sanar maki a baya, ni sunana Ibrahim, amma a kan kirani da Khalil, ni haifaffen garin getso ne...." Ta katse sa tace "Garinsu Malam Habibu?" Yace "Ehh, garinmu daya, har kuma yanxu iyayena na garin duk da baabata yar Nijar ce, don ta kan daukeni da kannena mu je Nijar a shekarun baya" Nihal dai tayi shiru bata ce komai ba tana ta kallonsa, ya sosa kansa yace "Nayi karatun primary, daga bisanni na daura da na sakandari inda na dakata a aji na uku ban ci gaba ba har yau, Baabata ta saka ni gareji a wancan lkcn, amma Allah bai yi xan maida hankali in koyi gyaran motar ba, kawai na koma aikin plumbing tare da wani d'an kanin babana a garin, sai dai ban dau lkci ina aikin plumber ba kasancewar na iya karatu da rubutu dai dai gwargwado ya sa wani a garin namu me suna Alhaji Mu'azu ya ajiyeni shagon chemist dinsa ina jire masa shagon, na kuma fi shekara takwas ina xama a shagon har daga bisanni Allah yayi masa rasuwa, da farko na samu wani aikin wanki da guga a gidan wani commissioner nan cikin garin kano, wani yaron me chemist din yayi min hanyar aiki a gidan, to yarinyar gidan ta kan xauna tare da ni mu yi hira, idan xata yi fita ba me nisa ba ni take sa in rakata, duk wani aike nata ni ke xuwa, kuma duk abinda aka girka a gidan da kanta take debo min ta kawo min, tana da kirki ainun, kuma baxan ta6a mance alkhairinta gareni ba, ita ta karfafa min gwiwa muke turanci tare, wanda banyi dai dai ba ta gyara min, bata kiran sunana kai tsaye sae dai ta ce min Kay... Wannan kusancin namu ya sa mahaifiyarta warce 'yar daya daga kasashen larabawa ce ta tilasta mai gidan sai da ya sallameni, a nata tunanin soyayya muke da yarinyarta, wanda kuma ba haka bane, sunan yarinyar Nadeeyah... da ita muka hadu a Supermarket daxu..." Nihal dae kallonsa take ko kiftawa babu, ya shafa kansa yace "Yauwa abinda na mance ban gaya maki ba shine ina da iyali da yaro daya wanda Allah yayi ma rasuwa ko wata biyu ba ayi ba yanxu, kuma shekarunsa biyar a duniya ya rasu" Nihal ta buda ido sosai tana kallonsa with shock, ya sauke kansa daga kallonta, he was looking sad, a hankali tace "Hasbunallah, Allah ya gafarta masa" Yace "Ameen, sunan matata Jiddah, wannan dalilin ya sa Nadeeyah kan kirani da Kay... Wani lkcn kuma ta kirani da KJay, har garinmu na kai ta wajen matata Jiddah" Nihal dai bata ce komai ba, Khalil yace "Bayan kusan sati uku da sallamata da aka yi daga gidansu Nadeeyah, shine Habibu yayi min hanyar wannan aikin a nan gidan, kin ji takaitaccen tarihi na...." Ta daga kai ta kallesa, kallonta yyi jin bata ce komai ba, a hankali tace "Allah ya taimake mu baki daya" Yace "Ameen" Aminu ne ya shigo compound din rike da leda, yana ganinta da farko sae da gabansa ya fadi don a xatonsa Nihad ce, sae ya ga ba ita bace, Aminu ya washe baki yace "Barka da dare Hajjaju" yana fadin hakan ya shige dakinsa da ledan hannunsa, Khalil yace "Karfe nawa xa kiyi tafiyar gobe?" Tace "Da safe in sha Allah" Yace "Ohk, ke kadai ce ai ko?" Ta Ι—an yi shiru sai kuma tace "Aa yawanci tare da Nihad muke tafiya, idan sun ajiyeni sai su juya" Yace "Ohk" ajiye takalmin hannunta tayi tace "Idan Aminu ya fito ka basa inji ya Farooq" Yace "To" Tace "Sai da safe" Yace "Allah ya tashe mu lfya" Juyawa tayi ta nufi cikin gidan ya bi ta da ido letting out a Sigh. Washegari da safe Khalil ya fito ta dalilin aika Aminu da Abba yayi ya kirasa, A balcony ya tadda Abba ya gaishesa da ladabi Abba yace "Xaka ajiye Nihal a Zaria, tare xa su tafi da yar uwarta sai ku dawo tare" Khalil ya sunkuyar da kai yace "Na gane... Amma sai dai na tashi yau bana jin dadi ranka shi dade" Abba yace "Me ke damunka?" Khalil yace "Ina jin ko malaria" Abba yace "Ya salam, Allah ya sauwake, baka da net ne?" Khalil ya girgiza kai yace "Aa bani da" Abba yace "Toh anjima xan baka kudi kaje ka siya" Khalil yace "Toh nagode Abba" Abba yace "Madallah, Amma ko kai da Saminu ne ku je asibiti a duba ka yanxu" Khalil yace "Toh in sha Allah" Abba yace "Kafin ku tafi ka sanar da ni" Yace "Toh nagode" Abba yace "Ba damuwa tunda farooq na nan sai yaje ya ajiyeta, kaje kawai" Khalil ya sakema Abba godiya sannan ya bar wajen, da Nihal kadai ce xai kai ta, but kasancewa tare da Nihad ne shi yasa ya gwammace yace bashi da lafiya, dalilin da yasa ma ya tambayu Nihal jiya kenan ta sanar masa tare da Nihad ne, tun jiyan kuma yayi deciding he won't be going shi yasa ya tashi da wannan plan din, he just can't withstand driving that far with Nihad in the car... Abba na shiga parlor ya ga Nihal har ta fito da jakunkunan kayanta, yace "Nihal ki jira in yi magana da Farooq ya kai ki, driver yace baya jin dadi" Shiru Nihal tayi tana kallon Abba, sai kuma ta nemi kujera ta xauna, Abba kuma ya tafi dakin Farooq, sai ga Nihad ta fito rike da handbag dinta tana kallon Nihal tace "Ke wai wannan yaron ne xai kai mu har Zaria? Ni gaskiya i can't withstand seating that long in the car with him, in har da shi ne gwara in fasa kawai, kar ma yaje da gangan ya kasheni a hanya idan muna dawowa" ko kallonta Nihal bata yi ba balle ta tanka ta, sai ga Abba ya fito yana kallonsu yace "Ku fita da kayan Farooq xai kai ku yanxu" Nihad ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Better" Trolly din Nihal daya ta dauka ta fita waje, tana ta tsaye a bakin motar har Nihal ta fito tare da Amina dake rike da wani Trolly din, Bayan farooq ya fito duk suka shiga motar, Mumy na tsaye balcony bayan tayi ma Nihal addu'ar Allah ya kai ta lafiya Allah ya tsare, Ummu ma na balcony din a tsaye, a duk sanda Nihal xata koma makaranta sai ta ji kamar xata yi xaxxabi, duk cikin yaranta babu wanda take ji har ranta kamar Nihal, a haka har farooq ya gama warming motar ya fita, Aminu ya daga masu hannu yana cewa "Allah ya bada sa'ar karatu, ku kuma Allah ya maido ku gida lafiya" Nihad da ke xaune back seat ita da Nihal ko kallonsa bata yi ba, Farooq da Nihal kadai suka amsa da Ameen.... Bayan sun dau hanya wayar Nihal dake jakarta ya fara ring, Nihad ta juya tana kallonta, bude jakar tayi ta fiddo wayar tana kallon screen din ta ga Khalil, Nihad ta kikkifta ido don ta kara tabbatar da sunan da ta gani a jiki, bata san sanda ta bude baki ba don mamaki, Nihal ta daga kiran ta kai kunne, Dubara Nihad tayi ta matsa dab da ita ko xata ji abinda xai ce, daga daya bangaren Khalil yace "Kin tashi lafiya Hajiya?" Nihal tace "Alhmdlh, ina kwana?" Yace "Lafiya, ban samu damar kai ki ba, kuma kin tafi ba mu yi sallama ba, Allah Ubangiji ya tsare hanya, ya kai ku lafiya, ya baki sa'ar abinda aka je nema" Ta sauke idonta kasa tace "Ameen nagode" Yace "Sai anjima" Tace "Nagode" Katse wayar yayi, Nihad ta matsa tana kallonta da kyau tace "Nihal ba driver din nan bane ya kira ki?" Nihal ta ki cewa komai, Nihad ta saki baki tana kallonta, Farooq dake jin su yace "Wani Driver?" Da sauri Nihad tace "Ji fa yaya, driver din gida fa, meye hadinta da shi har ma zai kirata yanxu??" Farooq dai sai kallon Nihal yake ta madubi, Nihal ta hade rai tace "You have problem Nihad, komai ke sai kin san yanda kika yi kika canxa masa ma'ana, what's wrong with me having the drivers number, naga har number Saminu ina da shi me yasa be xama laifi ba? Ke lkcn da Habibu yake nan baki da numbersa? Waye yafi communicate da Habibu a gidan banda ke?" Nihad tace "Noo, ae Habibu daban wannan daban, kuma Habibu sai ta kama muke magana da shi a waya...." A fusace Nihal tace "Toh wannan din ma kamawa yayi muka yi maganar a waya" Farooq yace "Toh wai ke Nihad ina ruwanki??" Kallonsa Nihad tayi, lkci daya ta hade rai bata ce komai ba, yace "Ke ce ai kika dau girman kai kika daura ma kanki but there is nothing wrong to have people that are under you phone number" All through the journey Nihad bata sake cewa komai ba amma fuskarta a daure yake. Satan kallon Nihal take taga tana bacci, a hankali ta dauke wayarta dake kafarta ta bude don ita bata sa password, ta shiga call logs tayi blocking number Khalil sannan tayi deleting ta mayar mata da wayar ta ajiye. Har Nihad suka kai Nihal Zaria bata ce ma kowa komai a motar ba, Farooq ya kalleta yace "Sauka ki kama mata kaya ku shiga hostel" Ta Ι—an daure fuska ta bude motar ta sauka, nan ta taya Nihal suka kwashe kayanta xuwa hostel din, bayan Nihad ta ajiye jakar karshe ta juya xata wuce Nihal tace "Are u still angry? Toh kiyi hakuri" Nihad ta kalleta tace "Baxan yi ba, ba dai driver ya fi ni ba" Nihal tayi Murmushi tace "Ya xa ayi driver ya fi ki, kema kinsan babu wanda ya fi ki a wajena, kiyi hakuri i didn't mean to make u angry" Nihad ta harareta tace "Kamar da gaske" Rungumeta Nihal tayi tace "Wllh kema kinsan da gaske nake blood" Nihad tace "Toh shkkn na hkura" Nihal tace "Toh nagode" a tare suka koma gun mota inda Farooq ke jiran Nihad, Nihad ta bude jakarta jin wayarta na vibrate, ganin Aliyu ke kiranta ta daga, bayan sun gaisa yace "Xan shigo kano in the evening, ki turo min address din gidanku" Nihad ta wara ido tace "Are u coming to our house" Yace "Ki turo ina jira" daga haka ya katse wayar, Farin ciki ne ya lullubeta, bai ta6a cewa xai je gidansu ba sai yau, a baya babu yanda bata yi da shi a kan ya xo gidan nasu ba amma sai ya ki, har ta kagu ta gansu a gida ta tambayi Umma abubuwan da xata dafa masa, nazari ta shiga yi... or is he coming because of that useless driver?? Ohh God that will be very great.


07087865788✍🏻


πŸ’–πŸ’– *NIHAAD*πŸ’–πŸ’–




By _Khaleesat Haiydar_✍🏻





14.....



Karfe biyu saura Nihad suka iso gida tare da farooq, yana kashe motar ta bude ta sauka, kallon direction din Mai gadi dake kulle gate tayi bata ga khalil ba, ta juya ta wuce cikin gida, direct part din Umma ta tafi, Umma dake parlonta tace "Oyoyo, har kun dawo?" Nihad tace "Ehh Umma, yau dai in gaya maki bata yi kuka ba da xa ku tafi" Umma tace "Toh ai gwara haka, kukan ba shi da amfani" Nihad ta xauna gefen Umma tace "Umma guess what?" Umma tace "Aa... ni kinsan i am not a good guesser, gaya min abinda ya faru daughter" Nihad na Murmushi tace "Umma Aliyu xai xo gidan nan yau" Shiru Umma tayi tana kallonta babu ko kiftawa, can tace "Wani Aliyu?" Nihad ta wara ido tace "Aliyu dai Umma" Umma tace "Amma ba kince min ya daina daga kiranki ba?" Nihad tace "Ehh wllh, kawai sai na ga kiransa jiya Umma, he called me him self" Umma ta girgiza kai tace "Nihad.... Nihad, bakya ji Nihad, baki jin magana wllh, na gaya maki ki

9 Comments On NIHAAD
avatar
lawal-1

1 year ago

Reply

The book is not complete thank you

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to lawal-1

tuntubi wannan nambar 07087865788 don siyan complete na littafin

avatar
aishat-5

1 year ago

Reply

Gaskiya naji dadi book dinnan

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to aishat-5

Wow munji dadi da hakan

avatar
maryama-4

1 year ago

Reply

Is very fantastic Allah ya Kara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to maryama-4

Ameen

avatar
maryama-4

1 year ago

Reply

Allah ya Kara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to maryama-4

Ameen

avatar
maryam-3-9-1

6 months ago

Reply

This book is so interesting

Please Login or Register in order to submit comment