Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mu tafi nace" Amsan ledan yayi tana gaba ya bi bayanta har main parlor, tana ganin ya tsaya bakin kofa tace "Aa shigo kanka tsaye" Still yaki shiga, Inna tace "Wai ba ni nace ka shigo ba, ni fa na haifi me gidan" Mumy dake kallonsu tace "Ka karaso" Shiga parlon yayi da sallama, Inna ta kulle kofa tana nuna ma Mumy ledan tace "Wllh Maryam ashe siya min yayi da albashin sa, kin dai ga bare ne fa amma yasan kyautata ma tsohuwa" Mumy tace "Toh Allah ya saka da Alkhairi, maa sha Allah" Inna tace "Allah sai naji ya fiye min Hamid da su Farooq sau dubu" Mumy dai bata ce komai ba, Inna ta rike ha6a tace "Allah yayi maka albarka ka ji" Yace "Ameen Nagode" Bude kofar parlon aka yi Nihad ta shigo, still tayi bakin kofar tana kallon Khalil da mamaki, sai kuma ta kalli Inna da Mumy tace "Me wannan kuma yake yi har cikin parlor?" Mumy tace "Uwarki yake yi" Nihad ta hade rai tace "Mumy parlon mu fa, privacy dinmu, this is uncalled for gaskiya, ko su Aminu da suka yi shekara da shekaru a gidan nan xa a bari su shigo nan balle wannan driver din..." Mikewa Mumy tayi tana ganin haka tayi hanyar stairs da sauri, Mumy bata fasa bin ta ba, Inna tayi kasa da murya tana kallon Khalil tace "Wallahi duk hakuri muke da ita, duk ta fi karfin kowa in gaya maka, shi yasa kwanaki da ta je ta kai karar ka gu na wai in sa a kore ka nace waa? Me ka min xan maka sanadin aikin ka, wllh naki biye mata shine ta kullace ni har yau, dama dai bansan mugun halinta bane shine xan biye mata amma ai kaga ban biye mata ba gashi har yanxu kana aikinka cikin rufin asiri har da siyo min apple, ni duk inda harkar rashin gaskiya take ba ni a ciki, Nihad kam bata da gaskiya wllh" Khalil dai kansa na kasa, Inna tace "In ji suna baka abinci isasshe dai?" Yana murmushi yace "Ehh ana bamu" Inna tace "Toh shkkn, can gidan Habubakar din ma ka iya dinga xuwa kullum, ai yanxu kam ka zama ɗan gida" Murmushi yayi yace "Nagode Hajiya" Tace "Yauwa je ka" Juyawa yayi ya fita daga parlon. Da daddare Nihad na kitchen tana pancake da xata ci kafin ta kwanta Sudais ya shigo kitchen din, cup din hannunsa ya ajiye a sink yana kallonta yace "Lahh Aunty Nihal ma tace mana tayi pancake ta ci yau a makaranta" Nihad na juya pancake dinta ba tare da ta kallesa ba tace "Did u spoke with her today?" Yace "Yess, Uncle driver ne ya kira mana ita, muna ta magana da ita for long" Juyawa Nihad tayi ta ajiye spatula din hannunta tace "Who is uncle driver?" Yace "Wannan da yake kai mu school" Ta bude baki, sai kuma tace "Yaushe ya kira maku ita?" Sudais yace "After magrib prayer" Sake baki Nihad tayi tana kallonsa, jin kaurin pancake dinta ta kashe gas din da sauri ta fita daga kitchen din, sama ta tafi bangaren Umma, har bedroom ta shiga ta sameta tace "Umma kinsan da wa Nihal ke waya yanxu?" Umma tace "Wa?" Nihad tace "Wai driver, yanxu su Sudais suke ce min ai ya kira masu ita, ranan da xa mu je shopping ne fa ya amshi numberta, toh a ranan da xa mu kai ta school ma ya kirata ya fi a kirga, sai ga yanxu su sudais suka xo suna gaya min ai driver ya kira masu ita" Da wani expression Umma tace "Driver? Wani drivern ni Sumayya?" Nihad tace "Driver dae da kika sani" Umma tace "Ko dai Nihal ta fara hauka ne?" Nihad ta kyabe baki ta zauna gefen gado, Umma ta dau wayarta ta hau kiran Nihal, yana fara ring Nihal ta daga, Umma tace "Nihal kiran me ku ke yi ke da drivern gidan nan?" Nihal tace "Driver kuma?" Umma tace "Ban sani ba" Nihal tace "Wallahi ba komai Umma kawai wani lkcn yana ba su Sudais ne mu yi magana da su" Umma ta kunduma mata zagi tace "Kanin uwarki ko na ubanki? Banda xubar da aji meye na wani waya da drivern gidanku? Sa'anninki na waya da mutanen arxiki ke kina waya da driver, ke wace irin yarinya ce? to wllh xan ci kaza kazanki idan baki kama kanki kin goge number tasa ba, kaji min gantalalliya dai" Nihal dai tayi shiru, Umma tace "Na dai gaya maki tun wuri ki goge number nan ko in ci maku ke da shi" Umma na kai wa nan ta katse wayar, sosai ranta ya baci, ita kam wace irin yarinya ce Allah ya bata, duk abun kaskantar da kai ta iya shi, banda haka meye ya kai ta dinga waya da driver, Nihad tace "Wllh Nihal is so annoying, how comfortable is she making call with that wretched man" Umma tace "Ki kyale mahaukaciya mana" Nihad ta mike ta tabe baki ta fita daga dakin, Zaga dakin Umma ta dinga yi. Nihad na gama pancake din ta shiga bangaren Abbanta, bayan ta gaishesa tayi shiru saboda Mumy dake zaune a parlon, Abba ya kalli Mumy, murmushi kawai tayi ta mike ta bar masu parlon, Abba na kallonta yace "Ya aka yi daughter?" A hankali tace "Abba na tambayi wata kawata gyaran screen din wai 150k ne" Abba yace "Har 150k?" Ta marairaice tace "Eh Abba" Shiru yayi, can yace "Ohk gobe zan tura maki, amma baxa ki wajen gyaran ke kadai ba, ko ku je da farooq?" Da sauri tace "Aa Abba ba kace driver ba?" Abba yace "Ohk, no problem sae ku je tare, kin gyara account din naki ne?" Tace "Aa sae next week, I'm busy with lectures throughout this week" Abba yace "Ohk xan sa kudin a account din Farooq sae ya baki" Ta hadiye abu da kyar sai kuma tace "Abba driver din bashi da account?" Abba yace "No I don't know" Tace "Abba idan yana da shi kawai ka sa mashi tunda tare xa mu, ba sae ka tura ma ya Farooq ba" Yace "Ohk, Allah ya kai mu goben" tace "Ameen" mikewa tayi bayan ta ma Abba sae da safe ta fita tana Murmushi, tana da kusan 70k a account dinta, ga kuma dala dari biyu da Aliyu ya bata, now with additional 150k from her father, latest iphone is sure gobe. Washegari Nihad na ta kallo ta window har Khalil ya tafi ajiye su Amina a makaranta, Hijab ta saka har kasa ta sauko, gun Aminu ta nufa yace "Barka da Safiya Hajiya" Tace "Aminu ina son tambayarka ne don Allah" Aminu yace "Toh Allah ya sa na sani Hajiya" Tace "Yaron nan Driver yana da account number ne?" Aminu yace "Anyaa, gaskiya ban ta6a jin yace xai cire kudi ba" Ta ta6e baki tace "Okay" Juyawa tayi ta koma ciki, tun jiya take avoiding ya farooq wannan ne ma yasa ta ki zama a parlor, ta koma dakinta tana jin dawowar Khalil ta sauko kasa da sauri, hade rai tayi ganin Ya Farooq a parlor ta gaishesa tayi ficewarta ba tare da ta jira ya amsa ba, Direct wajen khalil ta nufa babu yabo babu fallasa tace "Ehm ya ma ake kiranka? Abbana yace ka bada account number" Khalil ya kalli Aminu kamar dai yana jiran Aminu ya bata amsa, a fusace tace "Malam ai ba Aminu xaka kalla ba, da kai nake ni xaka kalla" Ya kalleta yace "Ohk, bani da account" Ta masa wani kallo tace "I thought as much" sai kuma ta ja tsaki ta juya ta koma ciki, Aminu yayi kasa da murya yace "Alhaji fa ya tambayi account din naka kasan ko ihisani xai maka" Khalil ya girgiza kai yace "To ai bani da account din ne" Aminu yace "Kashh" Nihad ta daidaici lkcn fitan Abbanta ta fito parlor da sauri yana ganinta yace "Yauwa kin amso account din" Tace "Abba bashi da shi, kawai ka sa a na kawata Husnah ita ta ma san wajen gyaran don nata ma ya ta6a lalacewa kamar nawa, don haka ita xata raka mu" Yace "Okay, forward the account to me via Sms" Tace "Toh Abba nagode, Allah ya kara budi" Yace "Ameen" Daga haka ya fita parlon Mumy tayi masa Allah ya tsare, Umma na tsaye bakin kofar kitchen tana kallonsu, Bayan fitan Abba Nihad ta juya da sauri xata bar wajen Mumy tace "Zo nan me xa a gyara?" Tace "Mumy laptop dina ne yake bani matsala shine xai tura min kudin gyara" Mumy tace "Toh amma lallai sai an sa kudi account din Husnah? Me yasa baxa ki je ki gyara account dinki ba, kuma nace maki bana son alakar ku da yarinyar nan kin ki ji, wai sai na fara nakada maki duka a gidan nan xaki nutsu Nihad?" Nihad ta marairaice tace "Mumy Coursemate dita ce fa, dole muna haduwa a class ko ban kulata ba ita tana kulani kuma ita kadai tasan inda ake gyara laptop din nan tunda nata ma ya ta6a lalacewa" Farooq yace "Dauko laptop din naki da ya lalace ki kawo min" Juyawa tayi ta kallesa, Umma ta karaso parlon tace "A saboda ka fara gyaran laptop??" Mumy tace "Ta dai je ta dauko masa laptop din da ya lalace" Umma tace "Toh naga ai ba shi ya bada kudin gyaran ba da xai hau tuhumarta" sum sum Nihad ta wuce sama, cikin lkci kankani ta shirya ta dau jakar laptop dinta ta fito, Umma kadae taje tayi ma sallama Umma tace "Toh Allah ya tsare daughter" Aminu ya kalli Khalil bayan ta fita yace "Kai fa yanxu huta roro, adaidaita take hawa xuwa duk inda xa ta." Nihad bata dawo gida ranan ba sai da sabon Iphone dinta dal a kwali, babu wanda ta sanar ma ta canza waya banda Nihal da Umma, Umma na jujjuya wayar tace "Gaskiya ne er daddy, yanxu duk kawayen naki su ma irin wannan ke hannunsu kenan?" Nihad ta washe fararen hakoranta tace "Ehh wllh Umma, shi yasa nima na dage sai da na canza, ai abun kunya ce ace ni kadai ce ban canxa waya ba a cikinsu" Umma tace "Ai ko kina da gaskiya abun ki" Nihad tace "Umma kinsan me?" Umma tace "Aa sai kin fada" Nihad tace "Umma xa mu fara exams nan da kamar sati uku kuma wllh ina son in koma hostel don in dinga karatu sosai, nasan Mumy da Ya farooq xa su xuga Abba kuma baxai bari in koma ba, pls ko xaki taya ni convincing Abbana?" Umma tace "Gaskiya ya kamata ki koma hostel din don ki maida hankali kiyi karatu sosai, amma kinsan me xai faru?" Nihad tace "Aa" Umma tace "Zan ce ma Abbanku Mijin Kamila xai yi tafiya kasar waje kuma xai yi kusan wata biyu a can, tace ki je ki dinga tayata kwana idan ya so daga can sai ki dinga xuwa makaranta, ita ma Kamilan xan sa ta kira Abban naku" Nihad ta wara ido cike da farin ciki tace "Yauwa Ummana, wannan shawarar taki tayi wllh" Umma tace "Kinga kawai daga nan sai kiyi komawarki hostel har sanda xa ku gama jarabawan, babu wanda xai san baki gidan Kamila" Nihad tace "Ai kuwa Umma, don Allah gobe da safe kiyi ma Abba maganar da wuri, on Thursday ma nake son in koma ni dai" Umma tace "Toh shikenan, Allah ya kai mu goben, ai gobe Wednesday" Nihad ta fita dakin cike da farin ciki, shi yasa take son Umma, haba she will be free for a while, babu me takurata. Da safe babu wani bata lkci Umma tayi convincing Abba, yace "Toh Allah ya kai mu alhamis din" Umma tayi murmushi tace "Ameen Yallabai, sai kayi ma Maryam magana da kanka ko?" Yace "Aa kema xa ki iya yi mata ai, menene a ciki" Umma tace "Aa gwara dai kai kayi mata, kace mata Kamila ce ta roki alfarman Nihad ta koma wajenta na kwana biyu mijinta xai yi tafiya" Abba yace "Ohk, amma suna da driver ne a can da xai dinga dropping dinta school?" Umma tace "Anya, da yake kasan shi yake ajiye kamilan duk inda xata je" Abba yace "Toh duk safiya sai Ibrahim ya dinga xuwa can yana daukarta ya ajiye ta makaranta, when ever her lectures is terminating sai ta gaya masa yaje ya dauketa ya maida ta gida" Umma tace "Hakan ma yayi kam" kafin Abba ya fita aiki ya shiga bangaren Mumy, nan ya sanar mata abinda Umma tace masa, Mumy tayi shiru alamar ta ma rasa abinda xata ce, Abba yace "Sai ki gaya ma Nihad din ta fara shiri" Mumy ta sauke boyayyen ajiyar xuciya tace "Alhaji idan Nihad taje gidan Kamila babu me kwaba mata, kasan ta da rawan kai fa, tana nan gida ma ya aka karke balle bata gida" Abba yace "So what are u insinuating?" Mumy ta girgiza masa kai kawai, Abba yace "Kar taje ta taya er uwartata xama kenan?" Mumy tace "Ko daya ba haka nake nufi ba" Abba yace "Toh Maa sha Allah, gobe alhamis ta shirya ta koma can gidan" Daga haka ya fice daga parlon, har ran Mumy bata son xuwan Nihad gidan Kamila amma to ya xata yi? Hakan ya sa ta tunani iri iri.




Barka da sallah fams, Allah Ubangiji ya maimaita mana


07087865788✍🏻


💖💖 *NIHAAD*💖💖




By _Khaleesat Haiydar_✍🏻




Har daki Umma ta tadda Nihad tace "Toh Abbanki ya amince sai ki fara hada kayanki" Cike da farin ciki Nihad ta mike ta rungumeta tace "Nagode sosai Umma" Umma tace "Sai dai fa Abbanki yace driver xai dinga xuwa duk safiya yana daukarki ya kai ki makarantar sannan idan kun gama lectures ya maida ki gida" Nihad ta zaro ido tace "Toh Umma ya xan yi?" Umma tace "To na dai amsa ma Abbanki, amma ke yanxu sai ki samu Drivern kice masa ba sai ya je ba, xaki dinga tafiya da motar Kamila, should Incase Abbanki xai masa magana...." Nihad tace "Toh shkkn Umma" Umma tace "Xaki makarantar yau?" Nihad tace "Ehh ina da lectures karfe sha biyu" Umma tace "Da sauran lokaci ai, sai ki fara harhada kayanki against tomorrow..." Daga haka Umma ta juya ta fita dakin, Murna a wajen Nihad ba a cewa komai, she is going to have enough freedom yanxu, wanka ta shiga bandaki tayi sannan ta fito ta shirya, bayan ta shirya ta fita xuwa bangaren Mumy, Mumy na gyaran bedroom dinta Nihad ta jingina da kofar dakin da damuwa tace "Mumy kin ji abinda Abba yace?" Mumy ta kalleta tace "Na me kenan?" Nihad ta marairaice tace "Mumy ni ba son zaman gidan Aunty Kamila nake ba, it's so boring there, ni kuma ban san ya xan yi ba" Mumy tace "Then u speak for ur self Nihad, ni me kike son ince a nan?" Nihad tace "I don't Know what to tell Abba" Mumy tace "Ki nemi abinda xaki ce masa ai baxai maki tilas sai kin ji ba" A hankali Nihad tace "Toh" Daga haka ta fita daga dakin ta koma dakinta, hada kayanta ta shiga yi a akwatunan ta cike da farin ciki, bayan ta gama ta sauka downstairs tayi breakfast, sae wajen karfe sha daya da rabi ta fita gidan zuwa makaranta ranta fari sol, yau ma dai adaidaita Sahu ta tafi ta hau bata bi ta kan Khalil ba, su Husnah da Naf har sun fi ta murna da ta sanar masu xata dawo hostel ta kuma gaya masu irin plan din da Umma tayi ma Abbanta, Husnah tayi shewa tace "Kai amma Allah ya shi ma wannan Umman albarka, Allah tana sonki sosai, ta san kan komai..." Nihad tace "Ke dai bari, ba don ita ba i will keep on being miserable in that house ga Yaya Farooq ga Mumy, the house is already a living hell for me, yanxu gobe xan taho da kayana hostel, har na gama hadawa kafin in fito" Husnah tace "Kuma albishirin ki, kin san saurayina ya kama mana tsadadden hostel a off K, xuwa next week xa mu koma wllh..." Nihad tace "Haba dai" Husnah tace "Wallahi, dama ina ta son xan gaya maki sai in manta, yanxu kinga Da ni, ke, Naf, Zully, da Ummi xa mu xauna dakin, ita Ummi part time xata dinga xama kinsan tafi zama wajen saurayinta sai in baya gari ne take xuwa hostel" Nihad tace "But bamu yi yawa ba Husnah? Kinsan fa bana wani son takura a rayuwata" Naf dake danna wayarta tace "Kin ji ki, 2 bedroom ne fa sannan har da parlor with two toilet, ai baki kai ni rashin son takura ba" Nihad tace "Ohk that's enough...." Kamar shekaranjiya da jiya yau ma dai haka suka shiririce a Cafeteria babu wanda ya shiga lectures cikinsu, daga karshe ma suka fita xuwa cin pizza a cikin gari, suna wajen cin pizza Nihad tace "Lah gashi har xan dawo hostel ba ku je gidan mu kun ga wawan yaron can ba" Husnah tace "Ai ko yau ya kamata kawai mu je" Nihad tace "Toh ae ke wannan gashin dake kanki ne matsalar kuma ya Farooq na gari wallahi" Husnah tace "A jakarki ba kina yawo da Hijab din sallah ba" Nihad tace "Eh" Husnah tace "To ara min kawai in sa don baxan iya wani komawa hostel ba" Nihad tace "Ohk" Zully tace "Kawai ku tashi mu tafi yanxu tunda biyu ya wuce" Naf tace "Amma yana gidan idan mun je yanxu?" Nihad tace "Nace maku 24/7 babu inda yake xuwa, da ma talla ya kasa a bakin gate din da ya dinga ciniki" duk suka kwashe da dariya, tashi suka yi gaba daya suka nufi motar Naf Husnah ta shige gaba, Nihad da Zully suka zauna baya, gaba dayansu tsadadden abaya suka saka, Nihad ce kadai ta sa atamfa da gyale. Karfe uku da yan mintuna Naf tayi parking dai dai gate din gidansu Nihad tace "Ashe dai xan iya gane gidan" Husnah tace "Ka ji ta bayan na gama baki direction kenan" Nihad ta sauka daga motar praying and hoping that khalil na bakin gate, sauran yan matan ma duk suka sauka daga motar, ta shiga gaba suna biye da ita har suka shiga gate din gidan, Aminu ya mike yana masu barka da xuwa, Nihad na kallonsa daga sama har kasa tace "Ina Drivern?" Aminu yace "Ai ko minti biyar bai yi da barin nan ba, yaje can ciki ya watsa ruwa yace min" Nihad tace shit a xuciyarta, why today of all days xai bar bakin gate din, kallon su Husnah tayi sai kuma da turanci tace masu su shiga ciki kawai kafin su fito xai dawo bakin gate din, a haka duk suka bi ta har xuwa main parlor din gidan, Aminu ya bi su da kallo, direct parlon Umma ta tafi da su, Umma ta fito daga dakinta jin sallama tana kallonsu tace "Sannunku da xuwa" Duk suka gaisheta suka xauna saman kujera, Nihad tace "Umma frnds dina ne da nake yawan baki labarinsu, Zully da Naf, Husnah kuma tana xuwa gidan nan ai kin ganeta ko?" Umma tace "Kwarai kuwa na gane Husnah, sauran ne dai sai yau na san su, Allah sarki, sannunku da zuwa yan mata, ya karatu?" Duk suka amsa da Alhamdulillah, Umma tace "Madallah, kun kwaso rana kuwa" Daga haka tace "Ina zuwa" fita tayi daga parlon, Naf tayi kasa da murya tana kallon Nihad tace "Is she ur step mom that u are talking about" Nihad tace "Yeah she is" Naf tace "Waow she is really nyc wllh, very nyc woman" Nihad tayi Murmushi tace "Sure she is" Ba a dau lkci ba sai ga Hafsah da tray din lemo da ruwa ta ajiye masu bayan ta gaishe su ta fita, sai gata ta dawo da warmer din abinci da plates da spoon, ta ajiye ta fita, duk suka sauko suka yi serving kansu, Nihad ma ta dau plate ta debi abincin. Aminu na ganin shigarsu Nihad gida dama ya tafi da sauri ya kai ma Khalil tsegumin Nihad ta xo da kawayenta su biyar suna ta tambayarsa da harshen turanci, ko minti daya bai kara a chalet din ba ya koma bakin gate da sauri ya zauna, sai bayan la'asar su Naf suka shirya xa su bar gidan bayan sun ci sun yi nak, har da coslow Umma ta hada masu, Umma tace "Toh kin kai su sun gaida Maryam kuwa Nihad?" Nihad tace "Tana nan ko?" Umma tace "Aa tana ciki, su je su gaisheta" Ta fita da kawayen nata xuwa ɓangaren Mumy, duk basu xauna ba suka gaida Mumy da bata wani sake masu fuska ba, kai kana ganinsu kaga yara marasu tarbiya marasu kamun kai, Nails Naf tayi fixing a farcenta, Zully kuwa kana iya hango tatoo dake bayan wuyanta duk da mayafin abaya dake jikinta, Husnah kuma boobs dinta da bayanta ba a cewa komai kuma farko da Mumy ta santa lkcn farawansu makaranta ba haka take ba, yar siririya ce ita ma, amma lkci daya ta dawo uwar mata, Duk gaba daya sun tsargu da kallon da Mumy ke masu, Nihad tace "Za su wuce ne Mumy shine suka shigo su gaisheki" Mumy tace "Toh maa sha Allah, Allah yayi albarka" suka amsa da Ameen suka fita daga parlon, Mumy ta kira Nihad ta dawo, Mumy na kallonta tace "Kar ki kuskura ki wuce bakin gate din gidan nan" A hankali Nihad tace "Toh" Daga haka ta juya ta fita tana turo baki. Downstairs ta tarda su, Zully tace "Ur mother is too serious oo" Nihad ta kyabe baki ta fita suka bi bayanta, Naf tace "The real African Mothers they are talking about" Duk suka kwashe da dariya, tsaye Nihad tayi balcony ganin har sannan Khalil bai fito ba banda Aminu kawai da take hangowa a bakin gate, Naf tace "Toh ina ɗan iskan drivern ne?" Nihad tayi shiru, sai kuma tace "Ina xuwa, ku jira ni" Gun Aminu ta tafi tana kallonsa tace "Kai Aminu har yanxu bai fito bane, zai ɗan rage ma kawayena biyu hanya ne" Aminu yace "Ni ma kin ga shi nake ta jira a nan Hajiya" Juyawa tayi ta koma balcony tace "Idan na tafi chalet da few minutes ku biyo ni can din" Tana fadin haka ta dau hanyar chalet din, bata ga takalmin kowa a bakin kofa ba, dama isiya da Saminu gantalallu ne wani lkcn idan suka gama duk abinda suke da safe sai su fita, su da dawowa kuma sai biyar xuwa shidda, a hankali ta bude kofar parlon duk da haka sai da yayi kara, ta shiga da takalminta tana yamutse fuska tana bin ko ina da kallo, ba laifi yau parlon bai yi kaca kaca ba, kuma babu wari, cikin sanda ta nufi corridor din dakuna, ta kai hannu handle din kofar dakin da Khalil yake ta murda a hankali ta tura kofar dakin, mikewa zaune yayi da sauri daga kwancen da yake saman gado, lkci daya ya hade rai kamar yanda ita ma ta hade rai, Tana masa wani kallo tace "Samun waje, kana bakin aikin ne xaka shanya baki da yamman nan kana bacci?" Khalil ya dau pillow ya daura kan wayarsa dake gefensa sannan ya saukar da kafarsa daga saman gadon, kallon fararen ƙafafuwan nasa take wa enda kamar bai ta6a taka kasa ba har ya mike tsaye calmly yace "Don ina aiki gidanku ba shi ne ya baki daman ki fado min daki kanki tsaye kamar ba musulma ba Hajiya" Wani dariyar rainin hankali tayi tace "Toh ai naga ba da dakin ka zo gidan ba, ko da shi ka zo?? kuma ashe kasan aiki kake gidanmu amma kake min rashin kunya iri iri saboda kai fitsararre ne, banda rainin hankali ma yanxu lokacin shigowa daki a kwanta ne? Shi kansa mai gidan naga yana wajen aiki yanxu haka, to idan ka ga dama ka fito Mumy tana kiranka, sako ne dama aka bani in isar maka kuma na isar, idan kuma

9 Comments On NIHAAD
avatar
lawal-1

1 year ago

Reply

The book is not complete thank you

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to lawal-1

tuntubi wannan nambar 07087865788 don siyan complete na littafin

avatar
aishat-5

1 year ago

Reply

Gaskiya naji dadi book dinnan

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to aishat-5

Wow munji dadi da hakan

avatar
maryama-4

1 year ago

Reply

Is very fantastic Allah ya Kara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to maryama-4

Ameen

avatar
maryama-4

1 year ago

Reply

Allah ya Kara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to maryama-4

Ameen

avatar
maryam-3-9-1

6 months ago

Reply

This book is so interesting

Please Login or Register in order to submit comment