Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baka ga dama ba sai ka shanya bakin ka ci gaba da baccin..." Jin motsi a parlor ta juya ta ga su Husnah bakin kofar duk sun shigo, alama tayi masu da su karaso, Khalil dake ta lura da ita ya karasa bakin kofar dakin bata ankara ba kawai gani tayi yayi banging kofar dakin almost on her face sannan ya sa makulli ya kulle, buda baki tayi da shock tana kallon kofar su Husnah suka karaso da sauri, tana zaro ido tace "Kun ga abinda yayi min yanxun nan" Naf ta kwankwasa kofar da karfi tace "Ashe dai kai karamin ɗan iska ne mahaukaci tunda har ka kulle kofar, da ka jira mu karaso kaga ikon Allah mana, wallahi da sai mun ji uban da ya tsaya maka yau kafin mu bar nan, kuma wallahi kaji kunya tunda har mata suka tsorata ka ka kulle kofa da sauri" Nan duk suka hau gaggayan bakaken maganganu marasu dadi a bakin kofar dakin, ita dai Nihad mamakin abinda yayi mata ya sa ta kasa cewa komai sai kallon kofar take, suka kare masa zagi na cin mutunci tass sannan Husnah na huci tace "Mu je, ai akwai wani lokacin, ni ban san shegen matsoraci bane ba ma ai...." Duk Khalil na jin su, and he was calming himself and controlling his mood at the same time, duk da it's too much and too heavy for him, lokaci daya launin idonsa ya canza, daga karshe ya daina juyo muryarsu gaba daya, Mikewa yayi walking slowly ya tafi bakin window ya tsaya yana kallon waje ko kiftawa baya yi, tunda ya xo gidan sai ranan ya ji da gaske he truly hate the sight of Nihad, at first he was trying his best not to hate her sbda bai iya tsanar mutum, shi yasa yake kokarin ganin bai tsane mutum ba no matter what, but he now realized he hate everything about her, da ya san xai zo gidan nan har ya hadu da ita da ya hakura da zuwan nasa no matter what and he is going to loose nothing, juyawa yayi ya tafi jakarsa ya bincika har kasa ya fiddo wani abu me kamar diary da pen dinsa, ya bude plane page yayi rubutu da bai wuce layi uku ba ya ajiye pen din yana kallon takardan, rufewa yayi ya mayar karkashin jakar ya kulle sannan ya mike ya koma gun window din ya tsaya, he is so hurt, it's been long he felt this way, but they can't just come and insult him then go scot free, wayarsa dake vibrate saman gado ya karasa kamar bai son tafiyar ya daga pillown ya dau wayar, Nihal ce ke kiransa, ya ajiye wayar ya zauna gefen gado har ya katse, sake kira tayi hakan yasa ya dauka ya daga ya kai kunne cikin low voice yace "Barka da yamma Hajiya" Nihal ta gaishesa tace "Friend dita fatima tace min ka amsar min sakon nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi" Gently yace "Ameen, ya karatu?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Allah ya bada sa'a" Tace "Ameen nagode" Yace "Ki turo number Tailor din naki" Tace "Toh xan tura maka, nagode" Yace "Yauwa sai anjima" Daga haka ya katse wayar ya ajiye gefensa. Da daddare Nihad ta shiga bangaren Umma da sleeping dress dinta, zama tayi a bedroom dinta har ta fito daga bandaki tace "Ya aka yi Nihad?" Nihad tace "Umma dama wancan drivern xaki taya ni yi ma magana gobe da safe xai kai ni can gidan Aunty Kamila da kayana idan ya so daga can sai Naf ta zo da mota ta kwasar min kayan mu tafi hostel" Umma tace "Toh ke me yasa baxa kiyi masa maganar ba, tsoronsa kike ko me?" Nihad ta wani zaro ido tace "Cabdi, inji tsoron wa? Ko Abbana bana tsoronsa sai wani mere Drivern gidanmu, kawai bana son ko wani magana ya sake hadani da shi har abada a gidan nan, don naga ba shi da manner sannan ya gama rainani, tunda Mumy ta mareni a gabansa shkkn ya daina respecting dina yana ganin dai dai muke, duk Mumy ce ta janyo min komai, to wannan yasa na yi vow har motar ma baxan dinga shiga tare da shi ba, wannan ma kawai dole ne ya sa don babu yanda xa ayi kayana ya dau adaidaita sahu" Umma tace "Balle ma shiga adaidaita Sahu ba girmanki bane, ita kuma Maryam in taga disgaki gaban ma'aikatan gidan shine dai dai sai ta ci gaba, shi yasa a rayuwa kar ki kuskura ki raga ma talaka ina maki wannan hudubar, don da ya ga fuska shikenan raini sai wanda ya manta, barin yan kauyen nan shi yasa ko kallon arziki kar ki yarda ya hadaku ma" Nihad tace "Ai ni dama bana masu kallon arxiki Umma" Umma tace "Ya dai fi miki, ajin ki daban da nasu, shkkn ki je ki kwanta goben xan masa magana idan Allah ya kai mu" Nihad tace "Nagode Umma" Zata fita dakin Umma tace "Kuna dai waya da Aliyun ko?" Nihad ta juyo tace "Ehh muna yi, yanxu ma da shi muka gama magana na fito" Umma tace "To madallah, yaushe xai kara zuwa?" Nihad tace "Umma kinsan akwai wani business din Abbansu a can kasar waje shi ne manager so he is not always in Nigeria, though sauran business din Abban nasu na nan kasar ma duk shi ke running dinsu, haka ne ma yasa bayan watanni kadan yake shigowa Nigeria, amma yace min in a month time xai shigo in sha Allah" Umma tayi shiru, Nihad tace "His father owns a big company shi da wani White Man, so Aliyu is managing it for him in there" Umma ta ɗan yi murmushi tace "Ba shakka, Allah ya sanya Alkhairi, kice koman baban nasa a hannunsa yake" Nihad tace "Ehh, he is his dad favorite also" Umma tayi murmushi tace "Kamar ke kenan ko" dariya kawai Nihad tayi ta nufi kofa Umma ta bi ta da kallo har ta fita daga dakin sai kuma ta sauke ajiyar xuciya. Washegari Umma ta samu Khalil bayan ya dawo daga kai su Amina makaranta, da ladabi ya gaisheta fuskarta kamar bata ta6a dariya ba tace "Kai nan da karfe tara xaka kai Nihad gidan yayarta" Khalil da kansa ke kasa yace "Toh Hajiya" Juyawa tayi ta bar sa wajen a tsaye, ya daga kai ya bi ta da kallo. Kamar yanda Umma tace karfe tara saura Nihad ta fara fitowa daga akwatunan ta nan balcony ta ajiyesu ta tafi bakin gate tana kallon Khalil dake zaune, Ta ɗan tabe baki tace "Ga akwatunan da xa a sa a booth a can balcony" Ko kallon direction din da take tsaye bai yi ba, sai ma kara hade rai da yayi, tace "Malam magana fa nake maka fa" Still khalil yaki kallon inda take balle ta sa ran yace wani abu, Aminu ya mike da sauri ya tafi balcony din Nihad ta bi sa da kallo, sai kuma ta kalli khalil cike da takaici amma ta kasa ce masa komai, har Aminu ya gama kwaso kayan ya ajiye a garage, ya taho gun khalil yace "Ɗan bude booth din a xuba su" Mikewa Khalil yayi ya tafi gun motar bayan ya bude booth ta makullin ya shiga driver seat, Nihad ta bi sa da wani shegen kallo, tana mamakin irin wannan feeling din da yake, sai kuma ta ji haushin kanta da bata sa Aminu ya kwaso akwatunan ba tayi ma wannan banzan magana ya kyaleta, bayan ya tada motar ta tuna bata ma Mumy sallama ba, komawa cikin gidan tayi ta tafi bangaren Mumy, khalil ya fi minti sha biyar a kofar gida yana jiranta cikin mota, tana sane tayi xamanta cikin gida don yayi ta jiranta a mota, sai da taga ta 6ata minti ashirin sannan ta mike ta fita tana rike da handbag dinta, back seat ta zauna ta kulle motar tana kallonsa, ya ɗan kwantar da driver seat ya rufe idonsa kamar mai bacci, da har xata masa magana ta tuna sabon vow din da ta dauka na cewar ba maganar da xai sake hadata da shi, yau ne last. Har bayan minti biyar bata ga ya bude ido ba balle ya tada motar su bar wajen, ta wani hade rai tana kallonsa, wasa wasa har sai da aka yi minti goma suna nan a haka, tana ta control din kanta kar tayi masa magana, Aminu dai sai lekosu yake yana dariya kasa kasa, wato sai ya rama shanyasa da tayi cikin mota, tana ta xaune motar ta cika tayi fam amma taki cewa komai kuma bata sauka ba har sai da aka yi minti ashirin da biyar sannan ya bude ido ya gyara zamansa ya kunna motar suka bar wajen, da yake ya ta6a kai Nihal gidan yayarsu kamar yanda ta ce masa, saboda shi ma baya son wata magana ta hadasa da Nihad direct gidan ya nufa ba tare da ya damu can din ne ko ba can ba, the ride was so silent, ko wannensu fuska a tamke, lkci lkci take satan kallonsa sai kuma ta kyabe baki ko ta ja tsaki can kasa kasa, har yayi parking dai dai gate din gidan kamila ya kashe motar, Nihad ta bude ta sauka ta tafi ta kira mai gadin gidan tace "Don Allah ka zo ka sauke min kayana a mota" Ya fito daga gate din ya bude booth don khalil ya riga ya bude, nan ya ciro mata akwatunan ya kai su bakin gate, kafin ya ciro na karshen tana kallonsa tace "Don Allah ka je kace ma wancan drivern nace ba sai ya wani zo yana kai ni makaranta ba don bana bukatarsa kwata kwata" Mai gadin ya tafi yana kallon Khalil bayan sun gaisa yace "Wai Hajiya tace ba sai ka zo kai ta makaranta ba" Khalil yace "Ok" Juyawa yayi ya tafi ya cire akwatin karshe ya kulle booth din, khalil ya ja motar yayi zoom off, Nihad ta bi sa da harara tace "Uwa motar ubansa, wllh ni ce sanadin aikinka a gidan nan mu dai je zuwa, sai kayi da ka sanin sanina a rayuwarka" Shi da mai gadin kallonta yake yana kokarin kai akwatunan cikin gidan, ko karamin bata dauka ba haka ta bar masa su dukka ta wuce ciki, Kamila dake parlor tace "Mutanen Maryam Abatcha American University" Murmushi Nihad tayi tace "Aunty ina kwana?" kamila tace "Lafiya lau, amma fa ki kira warce xata xo ta dau kayan naki xuwa hostel don karfe sha biyu xan fita nima" Nihad tace "Ehh tace min karfe sha daya xata zo" Kamila tace "Toh ya dai fi, daxu ma Mumy ta kirani wai in sa maki ido nace toh" Nihad tayi dariya tace "Aunty kamila mumy sai tayi ta treating dina kamar wata er yarinya" Kamila tace "Gaskiya kam, ga ki ke ba yarinya ba, makarantar ki ma ba ta yara ba" Dariya kawai Nihad take, Kamila tace "Atoh dai" Karfe sha daya Naf da Husnah suka iso kofar gidan Kamila na tsaye compound duk suka saka akwatunan a motar Naf, Bayan sun gama tace "Toh Allah ya tsare" Nihad tace "Ameen Aunty" su Naf suka mata sallama, tana kallonsu har suka bar compound din ta juya tayi komawarta ciki, murna a cikin Nihad ba a cewa komai, a haka ta koma rayuwarta a hostel babu me sa ta babu me hanata, duk sanda Mumy ta kirata sai ta shige bandaki ta kulle su yi waya don kar ma taji hayaniyar su Naf da Husnah, night party kuwa sai wanda suka mance ne baxa su ba, duk yanda suka so rinjayar Nihad ta dinga shan kwayoyin da suke sha bata ta6a sha ko da wasa ba, sau daya Husnah ta shammace ta ta xuba mata a lemo shi ma sai da ta kwana ta yini tana baccin wahala, hakan ya sa suka rabu da ita da batun drugs, sai kuma suka fara jan ra'ayinta zuwa kwanan hotels da suke da boyfriend dinsu, nan ma dai ta ki, ko min daren da suka yi a waje ita dai sai ta dawo hostel, duk sanda suka yi waya da Umma sai ta ja mata kunne kan cewar kar fa ta dinga bin duk wani wuri da xata iya haduwa da Abbanta ko Farooq, ita kanta Nihad is so careful about that, a haka har suka fara exams, duk cikinsu Nihad ce ke maida hankalin karatu, sauran ko bude takarda, duk sanda Mumy ta bukaci Nihad ta zo gida sai tayi karyan karatun exams yayi mata yawa, bayan an gama exams din ma don kar Mumy tace Nihad ta zo gida Umma ta sa kamila ta kirata tace xa su garin mijinta, haka nan aka kare hutu Nihad na hostel abun ta suna baza life, su ne har Kaduna da hutun, sau biyu ta je gidan Kamila shi ma ɗon Aliyu ya shigo kasar ne xa su hadu sai taje gidan kamila shi ma ta ce masa mijinta ne yayi tafiya take taya ta zama......



One more free page.

07087865788✍🏻



💖💖 *NIHAAD* 💖💖




By _Khaleesat Haiydar_✍🏻






End of free pages...


Har aka kare hutun wata biyu Nihad bata nufi hanyar gidan Kamila ba balle nasu gidan, kamar yanda Mumy ke kiranta kullum haka ma Abbanta, a ko da yaushe cikin demanding kudi take daga wajensa kuma ko sau daya bai ta6a hanata ba, da tayi magana xai tura mata fiye da yanda ta tambaya, Umma ma kusan kullum sai ta kirata, duk kuma wannan abun Abba da Mumy na xaton Nihad na Kebbi tare da Kamila, Umma ce kadai ta san Nihad na kano sai kamilar, gaba daya Kamila ta daina xuwa gida a zuwan tana can kebbi, idan da wani abu sai dai Umma ta shirya ita taje gidanta, A kullum Mumy bin Nihad take da addu'a, ta rasa dalilin da hankalinta ya ki kwanciya tun barin Nihad gidan, bata da rest of mind kwata kwata, gashi babu abinda xata iya yi game da hakan, ko me xata ce ma Abba baxai ta6a fahimtar ta ba sai dai ma ya juya xancen, a ko da yaushe ta kira Nihad sai ta mata nasiha a kan ta dai kula kuma banda rawan kai da yin kawaye, sai Nihad tace "Mumy ni da ba kowa na sani ba a garin sannan babu inda muke zuwa, kawai karatu nake ta yi against next semester" A haka dai kullum take gaya ma Mumy. Ranan wata juma'ah Nihad da kawayenta duk suka shirya xa su je duba wata kawar Zully da tayi rashin lafiya, Naf ke driving din, Husnah tace "Amma fa ku kirata ko an sallameta asibiti kar mu je mu yi wahalar banza" Zully tace "Ai ko dai" wayarta ta dauka ta kira kawartata Yusra ta sa handsfree, tana dagawa Zully tace "Ya kuna asibitin har yanzu?" Yusrah tace "Wani asibiti da aka sallame mu tun jiya, ni kin gan ni a Bristol ina shan Ac, Saurayina Alhaji Muktar ne ya biya kudin kwana hudu sai gashi tafiyar gaggawa ya kamasa yau da safe kuma yace min xai kwana uku a Abuja, sai jibi kudin xai kare shine nace gwara in yi zamana a nan" Zully ta kyalkyale da dariya tace "Me ya fi ranki, to bari mu taho can din kawai" Yusrah tace "Ai ko ku zo, ga abinci ga enough drinks, sannan ga Ac 24/7" Zully tace "To sai mun iso" Tana katse wayar, Naf ta dau hanyar Bristol, Husnah tace "Mu ma muje mu sha Ac kawai" Dariya duk suka yi, Nihad tace "Amma yaushe xa mu fito, kunsan ni bana son xuwa irin wajajen nan in broad daylight" Husnah tace "Mu da xa mu shiga daki mu yi xaman mu meye na wani damuwa" Nihad bata ce komai ba ta ci gaba da danna wayarta, suna isa makeken hotel din Naf ta samu wajen parking, Dai dai nan wayar Nihad ya fara ringing, ganin Abba ne ta ɗan wara ido, Husnah ta kalleta tace "Waye?" Nihad ta nuna mata screen din wayar, Husnah tace "Ohk, bari kawai mu sauka mu tafi ciki, sai ki tsaya motar ku yi waya, idan kun gama ki fito ki kulle sannan ki kirani mu gaya maki room number" Nihad tace "Ohk" Duk suka sauka daga motar, Naf ta mika mata makulli suka wuce ciki, tuni wayar Nihad ya katse sai ga Abba ya kara kiranta, dagawa tayi hade da sallama tace "Abba ina yini?" Yace "Lafiya lau dear, how are you?" Tace "Alhamdulillah Abba ya aiki?" Abba yace "Mun gode Allah, yaushe xa ku yi resuming ne?" Nihad tace "In two weeks time Abba" Abba yace "Ohk, yaushe kamilar tace maki xa ku dawo?" Nihad tace "Ana saura 2 days mu koma school, tare da mijin xa mu dawo gaba daya" Abba yace "Ohk that's good, take care dear" Nihad tace "Alright Abba, bye" Katse wayar Abba yayi, ta bude motar ta sauka sannan ta kulle, tana rike da jakarta bayan ta kulle motar ta nufi entrance din hotel din tana kokarin dialing number Husnah, sunanta ta ji an kira, ta juya da sauri, wani tsohon saurayin Husnah ne, ya nufota da sauri yace "Hi Nihad" Ta ɗan yi murmushi tace "How are you Kabir" Yace "Alhamdulillah, ya kwana biyu?" Tace "Cool" Yayi er dariya yace "Kina da appointment yau a nan kenan?" Ta ɗan kallesa sai kuma tace "Tare da kawayena nake, suna ciki" Yace "Ohk maa sha Allah, ya school" tace "Fine" A tare suka jera xuwa cikin reception din hotel din yana jan ta da hira, zaune yake a haraban hotel din karkashin inuwa tare da wani da baxai wuce sa'ansa ba yana sauraron duk abinda yake ce masa, da ido ya bi ta da Kabir, at first he quickly imagined ba ita bace kamace kawai, but yanayin tafiyarta da kuma jakar hannunta wanda duk ya sani ya sa shi ajiye goran ruwan dake hannunsa ya bi ta da kallo babu ko kiftawa, Buga table din abokinsa yayi da mamaki yace "Heyy!!" Da sauri ya dauke idonsa daga kallonta ya kalli abokin nasa, abokin yace "Why are u staring at her that way, burge ka tayi ko me? Kaga yarinya da saurayinta sun zo holewarsu kayi ta kallonta?" Still bai ce komai ba sai kallon abokin nasa yake babu ko kiftawa, Abokin yace "Khalil" Sauke idonsa yayi daga kallonsa sai kuma ya sauke ajiyar xuciya yace "Yea mamaki abun ya bani shi yasa na bi su da kallo" Dariya Sultan yayi yace "Haba kai ma ai kasan wannan ba sabon abu bane, yan matan yanxu kam ai sun xama abinda suka zama sai addu'a, basa ma jin kunyan iskanci yanxu, ko wani hotels ka bi su ne, baka lura bane ko 10 mins ba ayi ba set of 3 girls suka wuce mu a nan, su ma kuma duk gun samarin suka zo na sani" Shi dai khalil bai ce komai ba, he was really shock, yarinyar da aka ce tana Kebbi ce ya gani a Bristol, Sultan yace "Kai dai tunda kana da Nadeeyah and upon her parents wealth she is decent sai ka gode ma Allah" Murmushi kawai khalil yayi, Sultan yace "Kuma kuna magana da ita all this while?" Khalil yace "Muna yi" Sultan yace "Tasan kana kano?" Girgiza masa kai kawai khalil yayi, Sultan yace "Ya batun turawa gidansu?" Khalil yace "Yana nan" Sultan yace "Toh Allah ya nuna mana, but ya kamata kayi nazarin duk abinda nace maka Khalil, pls do so Frnd" Khalil ya sauke ajiyar xuciya yace "In sha Allah, and i appreciate u Sultan" Sultan yace "Nima nagode da ka bani lokacinka har ka saurareni" Murmushi kawai khalil yayi, Sultan ya mike yace "Toh ka koma can inda ka samar ma kanka aiki kar a fara nemanka ko" Khalil yace "Ina jiran wani ne still" Sultan yace "Wa kenan?" Khalil yayi kasa da murya yace "Another caring frnd like you" Sultan ya sauke ajiyar xuciya yace "All this shall come to pass in sha Allah Khalil" khalil ya ɗan yi murmushi ya mike tsaye ya mika masa hannu sannan yace "I truly appreciate ur care Sultan, nagode kwarai" Sultan yace "Mention not abokina" Har mota Khalil ya rakasa sannan ya dawo ya zauna inda yake zaune har sannan yana cike da mamaki, har karfe shidda na yamma yana xaune wajen bai ga fitowar Nihad ba balle shi mutumin da ta shiga ciki da, kiran Aminu ne ya shigo wayarsa ya ciro ya daga ya kai kunne, Aminu yace "Toh na ji ka shiru daga cewa xaka bakin titi ka dawo" Khalil yace "Ina nan dawowa yanxu" Aminu yace "Toh ga manyan mangwaro ma Hajiya Inna ta zo ta bada a ajiye maka" Khalil yayi murmushi yace "Toh nagode, sai na dawo" daga haka ya katse wayar. Har aka yi magrib Khalil bai ga fitowar Nihad ba, babu warce ta fado masa a rai sai Mahaifiyarta, ya ji tausayinta sosai, mata me kirki da mutunta ɗan Adam, and such a nyc woman didn't deserve Nihad as a child... Wayarsa ya dauka yayi dialing number Nihal ya kai kunne, tana dagawa tayi masa sallama, ya amsa yace "Ya kike?" Tace "Alhmdlh, ina yini?" Yace "Lafiya lau, ya lectures?" Tace "Ya shirin jarabawa dai" Yace "Ohh haka ne, ya shirin jarabawa?" Tace "Alhmdlh" yace "Tare xa ku dawo da er uwarki kenan?" Nihal tace "Noo, ai ita tana kebbi" Yace "Ko?" Tace "Eh" Yace "Ita da wa suka tafi kebbi?" Nihal tace "Wannan yayar tawa da ka kai ni gidanta kwanaki" yace "Ohk, yaushe xa su dawo?" Tace "Jiya da na tambayi Umma tace min nan da sati biyu" Khalil ya ma rasa abinda xai ce, jin shiru tace "Hello" Yace "Eh ina jin ki, to shkkn, dama tambayarki xan yi ya jarabawa" Tace "Toh Nagode" Yace "Sai anjima" Daga haka ya katse wayar, kallon cikin hotel din yayi, yana ta xaune har kusan Isha'i ganin Nihad ba fitowa xata yi ba ya mike ya tafi can inda yayi parking motar gidansu Nihad ya shiga ya bar hotel din, direct gidan Kamila ya nufa, bayan sun gaisa da mai gadin yace "Matar gidan na nan?" Mai gadin yace "Ehh tana ciki" Khalil yayi shiru, sai kuma yace "Ohk an aiko ni wajenta ne" Mai gadin yace "Toh bari ayi mata magana" Yana shiga gate khalil ya juya ya shiga motar ya bar layin. Direct gida khalil ya nufa erasing everything off his mind kamar ba ayi ba, after all it's none of his business and will neva be any of his business. Bayan sati biyun da Umma tace ma Abba su Nihad xa su dawo kano, sai ga Nihad tare da kamila a gidan da yamma, babu irin rokon da Umma bata yi ma Kamila akan su xo gida tare da kyar dai daga karshe ta yarda suka taho gidan da Nihad, akwatin kayanta daya kawai ta dawo gida da, tun da suka shigo gate Khalil ke kallon Nihad, ita kuwa shaff ta mance da wani batunsa a gidan sai yanxu da ta gansa, tana ganinsa kuwa mood dinta ya canxa, shkkn kuma ta dawo miserable house din nan da driver din nan a ciki, noo gaskiya ita dai baxata iya ba, xata roki Umma ta yi come up with another plan da xai sa ta sake barin gidan, Kamila ce kawai ta amsa gaisuwan mai gadi da khalil da ke gaisheta, Nihad kuwa tafiya take cike da isa ta nufi entrance din parlor, tayi wani kyau ta kara haske, kana ganinta kasan bata da damuwar komai, ba komai ya haddasa mata kara haske ba sai cream me shegen tsada irin nasu Husnah da take shafawa yanxu, ga sabulu ga shower gel, Khalil ya bi ta da kallo, suna shiga parlor Aminu yayi kasa da murya yace "Kaga yanda tayi wani haske tayi kyau uwa warce ta tafi duniyanci?" Khalil bai ce komai ba, but he really felt sorry for Abba and Mumy, ya jima bai hadu da mutane masu kirki da karamci irin tasu ba, a watanninsa kusan shidda a gidan Abba ya ja sa

9 Comments On NIHAAD
avatar
lawal-1

1 year ago

Reply

The book is not complete thank you

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to lawal-1

tuntubi wannan nambar 07087865788 don siyan complete na littafin

avatar
aishat-5

1 year ago

Reply

Gaskiya naji dadi book dinnan

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to aishat-5

Wow munji dadi da hakan

avatar
maryama-4

1 year ago

Reply

Is very fantastic Allah ya Kara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to maryama-4

Ameen

avatar
maryama-4

1 year ago

Reply

Allah ya Kara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to maryama-4

Ameen

avatar
maryam-3-9-1

6 months ago

Reply

This book is so interesting

Please Login or Register in order to submit comment