Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da take tayi karfin halin tashi tana layi ta koma cikin gidan, kitchen ta shiga tana kallon wukar da ya bata ta wurgar daxu, karasawa tayi ta dau wukar hawaye me xafi na sauka idonta, jingina tayi da cabinet tana kuka a hankali, to ai in tayi hakan wuta kawai xata, jefar da wukar tayi daga karshe ta fito parlon tana bin ko ina da kallo hawaye na bin idonta, karamar wayarsa ta gani saman kujera ta karasa da sauri saman kujeran ta dau wayar ta shige dakin da ta kwana, xaunawa tayi gefen gado hawaye wasu na bin wani a idonta tayi dialing number Nihal, tana sa wa sunan Nihal ya fito baro baro, ta kai kunne, yana fara ring ba a wani dau lkci ba Nihal ta daga, kasa cewa komai Nihad tayi tana kuka a hankali ta runtse idonta, jin shiru ba ace komai ba cikin sanyin murya Nihal tace "Hello" Nihad ta fashe da matsanancin kuka tace "Na shiga uku Nihal, kinga abinda su Abba suka min ko, dama ashe har Abba baya so na, dama haka aka tsaneni a gidan nan ban sani ba? wayyo Nihal wllh da Allah baxai jefani wuta ba yau da na kashe kaina kowa ma ya huta, zuciyata kamar xata fashe nake ji yanxu, i can't take this any longer, me yasa su Abba xa su min haka, sun san ma meye aure kuwa?" Kuka take kamar ranta xai fita, Nihal dai tayi shiru bata ce komai ba, Nihad na shessheka tace "Pls ki turo min number Husnah yanxu ta nan, nasan kina da shi send it now plss i need it...." Tana gama fadin haka ta katse wayar ta fada kan gado tana rera sabon kuka, ko minti daya ba ayi ba Nihad taji shigowar message a wayar, ta mike xaune da sauri taga number Husnah ne Nihal ta turo mata, da sauri ta hau kiran number, yana fara ring Husnah ta daga tace "Hello" Nihad ta rushe mata da kuka tace "Husnah tawa ta kare, Abba na ya tsaneni baya so na, Husnah kila ma ba su suka haifeni ba wallahi" Da sauri Husnah ta rage volume din Mp da suka cika a daki tace "Calm down Nihad, kar ki je ki sa ma kanki wani ciwon mu shiga uku, wllh tsoron xuwa gidan nan naku nake saboda yayanki, babu ta inda kuma xan san halin da kike ciki tunda bani da number kowa a gidan, Nihal da nake da number ta tana school da na kirata tace min haka" Nihad tayi karfin halin cewa "Husnah kin san wa Abbana ya aura min?" Husnah ta gyara xama tana gwale ido tace "Aa waye?" Nihad ta kwanta gefen gado hawaye me xafi na sauka idonta tace "Husnah of all people wai drivern gidanmu Abba ya aura min" Husnah dake xaune sai da ta mike tsaye tace "Whattt???" Bude kofar dakin aka yi Nihad ta mike xaune da sauri lkci daya ta hade rai, yana mata wani kallo ya karasa cikin dakin fuska daure yace "Kar ki sake ta6a min waya a gidan nan" Wani matsiyacin kallo tayi masa ta wurgar da wayar tana ta6e baki tace "Wannan gwangwanin kake kira waya?" Kallonta kawai khalil yake babu ko kiftawa trying his possible best to calm himself, Nihad ta ja tsaki ta tashi ta koma can karshen gado ta xauna fuska daure tace "Wai waya, kai baka ma ji kunyan kiran wannan waya ba" Gyada kai yayi ya juya ya durkusa ya dau wayar da batur dinsa da yayi gefe daya ya mayar sannan ya mike ya nufi kofa ya fice daga dakin, wani sabon kukan ta saki tace "Wayyo Allah na." Wajen karfe sha biyu da rabi Nihad da har ta gaji da kukan da take ta ji ana kwankwasa gate din gidan, kamar tana expecting hakan ta mike da sauri tana share idonta ta fice daga dakin, dai dai fitowarsa shi ma daga dakin da yake, ta wani hade rai, ko kallonta bai yi ba ya nufi kofa ya fita, wani mugun tsanarsa da tafi ta ko yaushe take ji a ranta, even with joke baxata ta6a kiran wannan mutumin wai mijinta ba, mijinta ta ina? Shi har ya isa ya xama mijinta? This is even weird to imagine, bakin kofar parlon ta tafi ta tsaya fuska daure, yana bude gate din Umma ta shigo, har kasa ya durkusa yace "Barka da xuwa Hajiya, ina yini" Wani kallo Umma tayi masa sae kuma ta kyabe baki ta wuce ta bar sa durkushe a wajen, Nihad na ganin Umma ta taho da gudu ta Rungumeta ta sakar mata kuka da karfi tace "Umma na shiga uku, me yasa Abba xae min haka, me yasa Abba xae lalata min rayuwa, Umma ashe duk ba sona ake a gidanmu ba ban sani ba" Umma ta rungumeta cike da damuwa tace "Yi shiru mu shiga ciki Nihad, yi shiru" A haka Umma ta ja xuwa parlor, khalil da ya bi su da ido ya tafi kan dakalin da ya xauna daxu ya xauna, Umma na rungume da Nihad bayan ta zauna kan kujera tace "Wai ba nace kiyi shiru ba ko in tashe in tafi ne?" Nihad ta girgiza kai tana shessheka a hankali tana goge idonta, Umma tace "Ke yanxu kin yarda an aurar da ke kenan?" Nihad ta daga kai tana kallon Umma da kumburarran idonta, ba idonta ba har fuskarta ya koma ja, Umma tace "Ohh kin yarda kenan an daura maki aure da Driver?" Nihad ta girgiza kai disgustingly tace "Allah ya kiyaye wllh" Umma tace "Toh Alhamdulillah, yanda ko wace budurwa take rayuwarta haka xaki ci gaba babu batun auren kowa a kanki, kar ki kuskura ki amince wai kina da wani wai shi miji, a nan din ma bai wuce ɗan aiken ki ba kuma drivern ki, ki sa a ranki kema budurwa ce da xata iya shiga duk inda take so ta fito, ki ci gaba da rayuwarki yanda kika saba, sannan kar ki kuskura ki raga masa balle ya ga fuskar kawo maki raini, ba kowa bane shi facce drivern gidanku kuma har a yanxu dreban ne, kuma ɗan aike" Nihad tace "Toh Umma yanxu a gida daya xa mu xauna da shi kenan? Wallahi i just can't imagine that, ta yaya xa ace muna gida daya da shi?" Umma tace "Ka ji ki, Toh ina ruwanki da shi? Meye hadin ki da shi? Rayuwarki kawai xaki dinga yi kamar kina gidan ubanki, kar ki yarda ko kallon kirki ya hada ku da shi, har yau shi din ma'aikacin gidanku ne don haka a karkashin ki yake" A hankali Nihad tace "Toh, amma Umma shikenan baxan ci gaba da karatuna ba kenan" Umma tace "A saboda me? Ai kwantar da hankalin ki, yanxu daga nan gidan Alhaji Abubakar xan nufa tunda dai sun aurar da ke sai su bari kuma ki ci gaba da karatun ki" Nihad ta sauke ajiyar xuciya tace "Nagode Umma" Umma tace "Kar ki yarda ki kara xubar da hawayenki a banza a hofi, ke da ma kika samu freedom din kanki yanxu, da kin tashi fita kawai fitar ki xa ki yi kanki tsaye babu neman izinin ko wani shege, sanda kika ga dama kuma xa ki dawo babu me tuhumarki" Nihad da ta ji hankalinta ya kwanta sosai tace "Haka ne Ummana" Umma tace "Toh ko ke fa, sannan duk kawayenki xa su iya xuwa nan su dinga kwana kuna yini tare, kuyi duk wani sabgarku a nan babu me cewa don me" Nihad tace "Gaskiya ne Umma, amma ni damuwata kawai ganinsa da xan dinga yi a gidan, baxai yiwu ya koma can gidan ba kawai gaba daya ni kadai in zauna a nan, wllh i hate the sight of him, na tsani ganinsa, na tsanesa" Umma tace "Aa ke kuma, ai xai ci gaba da aikinsa na tuki, kinga duk safiya xai dinga xuwa can gidan kilan kuma sai ya dawo da Abbanku daga office sannan ace xai dawo nan gidan" Nihad ta yatsina fuska, Umma tace "Ke ma abinda idan kika fita kilan sai daren xa ki dinga dawowa gida" Nihad tace "Dama mana, yanxu kawai xance su Husnah da Naf su kwaso kayansu su dawo nan mu zauna" Umma tace "Shikenan kuwa" Nihad ta sauke ajiyar xuciyar relieve, Umma tace "Kin ci abinci kuwa?" Girgiza kai Nihad tayi, Umma tace "Me yasa? To tashi ki tafi kitchen ko indomie ne ki dafa" Nihad tace "Toh" Mikewa tayi cike da energy ta wuce kitchen, sosai ta samu nutsuwa bayan abubuwan da Umma ta gaya mata, ta dafa indomie sannan ta fito, Umma tace "Bari in xo in tafi don in samu Alhaji Abubakar a gida" Nihad tace "Umma bani da waya wllh" Umma tace "Akwai nokia din yayanku bari ko Amina xan ba ta kawo maki anjima" Nihad tayi Murmushi tace "To Umma Nagode" sai da ta gama cin indomie sannan Umma tace ta taso ta rakata, Nihad ta mike suka fito compound da Umma, har sannan khalil na xaune inda yake, Ya mike yana kallon Umma yace "Sai anjima Hajiya" Umma ta wani kallesa, sai kuma ta kyabe baki ta ci gaba da tafiyarta Nihad ta hade rai tana biye da ita a gefenta, Komawa yayi ya zauna ya bi su da kallo, suna isa gate Umma tace "Toh sai kin ji ni, idan Amina ta kawo maki wayar sai ki kirani don xan sa a siyo maki sim ayi register sai ta taho maki da shi" Nihad tace "Toh Umma" Umma tace "Maza tafi kiyi sallah ga azahar yayi, sai ki kwanta ki huta" daga haka tayi mata sallama ta wuce, Nihad ta kulle gate din, fuska daure ta nufi cikin gidan. Har bayan magrib Nihad na ta jiran Amina ta kawo mata waya amma shiru, gashi babu yanda xata yi ta kira Umma duk da tana da numberta a kai, wannan ne yasa ta kara shiga wani damuwa, karfe takwas da rabi ta mike a hankali ta fito daga dakinta, dai dai nan Khalil ma ya fito... sosai gabanta ya fadi ta ɗan koma baya, sai kuma ta daure fuska, ko kallonta bai yi ba ya shiga parlor, ta bi sa da kallo taga kamar fita zai yi, tuni turarensa ya gauraye duk parlon, ko burgeta kamshin nan nasa baya yi, ta kasa kunne taji ko fita gate xai yi, ai ko taji ya bude gate, da sauri ta shige dakinsa ta kulle kofar, banda kamshi babu abinda dakin ma yake, ta tafi gefen gado ta dau karamar wayarsa da ta gani ta hau dialing din number Umma sharp sharp, yana fara ringing Umma ta daga hade da sallama, Nihad ta marairaice tace "Umma ni ce" Umma tace "Aa Nihad, Number waye haka duk zero zalla" Nihad tace "Wayar yaron nan ne Umma, ya fita yanxu shine na dauka da sauri na kiraki kafin ya dawo" Umma tace "Kin ji shiru ko, wllh ba a samu anyi rijistan layin yau ba sai gobe wai, don haka gobe da kaina xanje ayi, ita kuma Amina tana dawowa islamiyya xan bata ta kawo maki kin ji" Nihad tace "Toh shkkn Umma, Allah ya kai mu goben" Umma tace "Toh Ameen, sai da safe daughter" Daga haka ta katse wayar, Nihad na duba call logs don ta kira Husnah tunda daxu ta saka numberta a wayar amma bata gani ba alamar ya goge number, instead sai number Nihal ta gani wanda ko awa daya ba ayi ba da suka yi wayan da ita, ta dinga kallon number babu kiftawa, bude kofar dakin aka yi, Nihad ta zaro ido hade da kurma ihu a tsorace ta saki wayar hannunta jikinta na rawa, tsaye yayi bakin kofa yana kallonta da wani Strict expression, lkci daya ta wani sha kunu ita ma, can dai ta tafi can jikin bango har sannan gabanta na faduwa amma bata nuna hakan a fuskarta ba, ya karaso cikin dakin ta hadiye wani abu da ya tokareta a makogwaro da kyar xuciyarta sai bugawa yake tana kara shigewa jikin bango, yana dukawa zai dau wayar ta yi hanyar kofa a mugun guje, da hannu daya yayi hanzarin fixgota ta fasa ihu tana kokarin kwace kanta tace "Wallahi xan cijeka idan baka sakeni ba, ni me xanyi da gwangwanin wayarka"





*Da kun kai hannunku xa ku danna wajen fowarding littafin nan xuwa groups ku dubi girman Allah, ku dubi darajan annabi S.A.W, da kuma son da ku ke ma iyayenku ku tuna da cewar nace don girman Allah ayi hakuri kar a min sharing to groups with over thousand members, plss i am begging sincerely ba da fada ba ko gadara, ayi hakuri a min wannan alfarman, masu siya kawai don su tura groups su yi hakuri domin Allah kar su yi haka, And if u should come across this book roaming in any group kayi kokari kayi subscribing before reading saboda ba free book bane, ur conscience shouldn't allow u to read my dear, ko yaya ne try and give something, ina kuma alfahari da duk wa enda suka yi patronizing dina, ina kuma maku fatan alkhairi...*


Nihad is just....

500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

And u show ur evidence via 07087865788



Hadeta Khalil yayi da bango fuskarsa a daure yana kallonta cikin kakkausar murya yace "Zan maki gargadi na karshe, kar ki sake ta6a min wayata a gidan nan, kar kuma ki sake shigo min nan, ina me baki wannan shawarar" Nihad dai gabanta sai faduwa yake ganin how huge he is a gabanta, ita bata ta6a sanin ma haka yake da tsayi ba, gashi ya murtuke fuska uwa ba drivern gidansu ba, amma duk hakan bai sa ta fasa daure masa nata fuskar ba ita ma, sai dai bata ce komai ba, komawa baya yayi yana kallonta, irin kallon kyama sannan ya nuna mata kofa calmly yace "Fita" Ba musu ta nufi kofa, tana isa dai dai kofar ta juyo ta kallesa tana wani yatsine fuska har da harararsa tace "Sai ka gaya min nawa ka siya shegen wayar taka in baka kudin wanda ya fi shi yanxun nan, ban ta6a ganin wanda ke takama da rakani kashi ba sai kai" Still yayi yana kallonta babu ko kiftawa, tana gama fadin abinda xata fada ta bar wajen da sauri tayi hanyar dakinta ta shige ciki ta kulle kofar tana sauke ajiyar xuciya, jingina tayi da kofar wani bakin ciki da takaici ya turnuketa wai yau ita da drivern gidansu ne kadai a gida daya har yana gaya mata maganar banza, ta ji xuciyarta na tafarfasa, she is still yet to believe this, ta kasa yarda wai da gaske wannan mutumin Abba ya sa su gida daya su dinga xama, how will that even be, fadawa tayi saman gado ta fashe da kuka tace "Wayyo Abba me yasa xaka min haka" Ita da dai drivern nan ai gwara ko almajiri ne Abba ya nemo mata su xauna gida daya, ta ci kukanta me isarta bacci ya dauketa a haka. Washegari har kusan karfe goma bata fito ba ga wani mugun yunwa da take ji, tashi tayi da kyar daga karshe ta shiga bandaki tayi wanka ta fito, daya daga akwatunanta dake dakin ta bude ta fiddo wata doguwar rigarta ta saka, xaunawa gefen gado tayi feeling so sad and dejected, daga karshe ta mike ta nufi kofa tana tafiya a hankali ta bude kofar ta fito parlor, babu kowa parlon sai take away din abinci da ta gani a tsakar parlon, ta saci kallon ko ina na parlon sannan ta karasa inda abincin yake tana ta6e baki ta bude take away din tana kallon abincin ciki, jollof rice ne sai sheki yake da katon kaza, ko rabi kuma bai ci ba, kazar ma bai wani ci ba ya bari, ta bude ledan dake wajen taga drinks ne sai chocolates me yawa, vibration din waya taji saman kujera ta kalla da sauri amma bata ga wayar ba, wanda hakan yasa ta gane wayar na karkashen throw pillow dake saman kujeran, har xata kai hannu ta daga pillow din ta ji an kulle kofar kitchen, sosai gabanta ya fadi ta juyo da sauri suka yi ido hudu da shi ya fito daga kitchen din rike da cup din shayi, sai a sannan ya ji vibration din wayarsa ya karaso da sauri, wanda tun kan ma ya karaso Nihad tayi hanyar dakinta tana harararsa, ya ajiye cup din hannunsa ya bi ta da kallo har ta shige dakin, xaunawa yayi saman kujera yana kallon throw pillow din kamar me son gano ko ta ta6a ko bata ta6a ba, da sauri ya dau wayar kafin ya katse ya daga ganin Abba ne, gaishesa yayi da ladabi Abba ya amsa yace "Anjima da yamma ka daukota ku zo gida ina son magana da ku" Khalil yace "Toh in sha Allah" Abba yace "Ai motar na can gidan ko?" Khalil yace "Ehh yana nan" Abba yace "Ina sauraronku xuwa nan da bayan la'asar" Khalil yace "In sha Allah" Daga haka Abba ya katse wayar, ajiye wayarsa yayi ya jinginar da kansa da kujera, this spoilt his mood the more, Allah ya sani he can't endure staying under the same roof with this Brat, he wish this never happened, he detest the sight of her, da yasan this is how things will end babu abinda xai kawosa gidansu, da baxai fara ba, yanxu ta yanda ma xai ce ta shirya su je gida shine babban aiki a wajensa, ko magana baya son yana hadasa da ita, mikewa yayi ya dau wayarsa ya zura a aljihu ya fice daga parlon xuwa compound don ya fi zama comfortable xama a nan, abinda Nihad bata sani ba shine shi ya ma fita shiga damuwa kawai dakewa yake yi, kuma bata ki jininsa ba yanda shi ya ki jininta. Ganin yunwa na neman mata illa ta kara fitowa parlor, this time around hanyar kitchen ta nufa tana bin ko ina da kallo, ga kayan abinci amma babu kayan miya, gashi ita ba gwanar cin indomie ba ce, babu yanda ta iya haka ta dafa indomien ta fito ta wuce dakinta, tana ajiye indomien ta fashe da kuka sosai cike da tausayin rayuwarta, why did this happen to her, waye yayi mata haka yayi ruining happiness dinta all of a sudden, tasan duk rashin jin ta ko da singlet bata xama comfortable zama a inda ba gidansu bane, ko su Husnah da take bi she is very cautious of her self and her body, kuka take yi sosai wishing duk wannan abun bai faru da ita ba, indomien da bata ci ba kenan daga karshe, kawai ta tashi tayi alwala tayi sallahn azahar ta kwanta gefen gado hawaye na sauka idonta. Ana la'asar Khalil ya shigo parlor ya zauna yayi dialing number Abba, Abba na dagawa ya gaishesa sannan yayi kasa da murya yace "Abba tace ita baxata ba" Abba yace "Ohk, ba ta waya" Khalil yace "Toh" Mikewa yayi ya nufi hanyar dakin da take ciki, yanda kasan yana kallonta jikin kofar haka ya hade rai yana kallon kofar, sai kuma yayi Knocking kofar, Nihad da ke kwance har sannan ta mike zaune tana kallon kofar, sai da ya sake Kwankwasawa ta mike xaune ta wani hade rai, sai kuma ta tashi ta tafi gun kofar ta bude cike da tsiwa tana harararsa tace "Lafiya kake kwankwasa min kofa Malam? Ko da bashi ne?" Mika mata wayar hannunsa yayi ba tare da ya kalli fuskarta ba, ta kalli wayar da kamar baxata amsa ba sai kuma tayi tunanin kila Umma ce, fixge wayar tayi daga hannunsa tana kallon Number sai taga number Abbanta ne, sosai gabanta ya fadi, tayi karfin halin kai wayar kunne, cikin sanyin murya tayi sallama, Zaro ido tayi tana sauraron abinda Abba ke ce mata with strictness, can ta kalli Khalil da ya koma can gefe ya jingina da bango ya rungume hannunsa, Abba bai bar ma Nihad space din cewa komai ba ya katse wayarsa daga karshe, ta fashe da wani matsanancin kuka tana kallo Khalil tace "Allah ya isa, ban yafe maka ba wllh, yaushe kace min mu je can gida nace Aa?? Wallahi ni baxan ta6a yafe maka ba" Sai kuma ta durkushe wajen tana kuka sosai ta kalli wayarsa dake hannunta tayi wurgi da shi ta mike ta shige cikin daki ta fada kan gado tana rera kuka, ya dau wayar tasa ya bar wajen. Bayan Nihad ta ci kukanta ta koshi ta mike ta dau hijab din da tayi sallah ta saka sannan ta fito daga dakin, compound ta fito ta gansa xaune driver seat ya bar motar a bude alamar dai ita yake jira, fuskarta a murtuke ta bude back seat ta shiga ta xauna, ya sauka daga motar ya tafi ya bude gate..... Har suka kusa gida Nihad bata daina hawayen da take ba a motar, Horn khalil yayi mai gadi ya leko ganinsa ya daga masa hannu yana washe hakora ya bude gate din, Khalil na parking ya kashe motar ya sauka ya tafi gun Aminu, tuni Nihad ta shige cikin gida, Aminu yayi kasa da murya yana zazzare ido yace "Wani labari muke ji haka mutumina??" Khalil yace "Na me fa?" Kafin Aminu yace komai, Khalil yace "Bari in shiga in fito yanxu" Aminu yace "Toh ina nan ina jiranka" Juyawa khalil yayi ya nufi entrance din gidan, Khalil na tsaye balcony yayi dialing number Abba ya sanar masa sun iso, Abba ya masa izinin shigowa har parlonsa, babu kowa main parlor, Khalil yayi sallama bangaren Abba, Abba ya amsa sannan ya shiga ciki, kansa a kasa ya zauna nan saman Carpet ya kara gaida Abba, Abba ya amsa ganin Nihad bata shigo ba yace "Tana ina?" Khalil yace "Ta riga ni shigowa" Nihad kuwa tana shiga gidan dama direct bangaren Umma ta tafi, Abba ya mike ya fita, a side din Umma ya ga Amina yace "Ina Nihad?" Amina tace "Tana dakin Umma" Yace "Ki shiga ki kira min ita" Amina ta juya ta koma ciki, Abba ya koma parlonsa, bayan wasu yan mintuna sai ga Nihad ta shigo parlon Abbanta kanta a kasa, sallama tayi da muryarta da har ya fara dashewa saboda kuka, bata yarda ta daga kai ba balle ta kalli Abbanta, ta nemi waje daga opposite din inda khalil ya zauna ta zauna, Cikin rawar murya tace "Abba ina yini" Abba bai amsa ba, bai kuma kalleta ba, dai dai nan Umma ta shigo parlon da sallama, kallonta kawai Abba yake, Khalil ya gaisheta ta amsa ta zauna fuskarta dauke da damuwa tana kallon Abba, Abba dai ya kalli Khalil yace "Nagode da wannan alfarma da ka min na auren yarinyar nan Ibrahim, Allah Ubangiji ya baka aljanna" Khalil yayi kasa da kai a hankali yace "Ameen" Abba yace "Ina kuma fatan Allah Ubangiji ya baka hakuri da juriyar zama da ita.... In dai da akwai wani abu kar kayi kasa a gwiwan kirana ka sanar min koma menene shi" Nihad ta fashe da matsanancin kuka tana kallon Abba tace "Abba wallahi bana sonsa kuma baxan ta6a sonsa ba, na tsanesa na tsanesa, ni baxan ta6a xama da shi a gida daya ba, wallahi i hate him...." Mikewa Abba yayi lokaci daya ya sauke mata mari me lafiya a fuskarta, ihu ta fasa ta dafe kuncinta, Umma ta bude baki tana kallon Abba, sai kuma tace "Haba Alhaji, Haba Alhaji...." Dakatar da ita Abba yayi a fusace yace "Bana son jin komai daga gareki, ki tashi ma ki fita" Umma ta ja bakinta tayi shiru, cike da bacin rai Abba na kallon Nihad yace "U think i brought u here to ask for ur opinion? Is that what u think?" Abba ya girgiza kai cike da takaici yace "You are nothing but a disappointment to me Nihad, i regret having u as a child...." Kuka kawai Nihad take tana jin kamar a mafarki wai ita Abba ya mara kuma yake gaya mata wannan maganganun, wanda ko fada bai ta6a mata ba tunda aka haifeta, Strictly Abba ya

9 Comments On NIHAAD
avatar
lawal-1

1 year ago

Reply

The book is not complete thank you

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to lawal-1

tuntubi wannan nambar 07087865788 don siyan complete na littafin

avatar
aishat-5

1 year ago

Reply

Gaskiya naji dadi book dinnan

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to aishat-5

Wow munji dadi da hakan

avatar
maryama-4

1 year ago

Reply

Is very fantastic Allah ya Kara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to maryama-4

Ameen

avatar
maryama-4

1 year ago

Reply

Allah ya Kara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to maryama-4

Ameen

avatar
maryam-3-9-1

6 months ago

Reply

This book is so interesting

Please Login or Register in order to submit comment