Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi, amma lallai yarinyar nan shaidaniya ce a siffar mutum..." shi dai khalil bai ce komai ba, mai gadi yace "Ga can abinci da aka kawo mana, na debar maka naka na ajiye" Khalil yace "Aa na koshi, yanxu wanka nake so xan yi" Mai gadi yace "To mu je in raka ka bangarenku" A tare suka nufi boys quarters din bayan mai gadi ya dauko wata er jakar kayan Khalil da ya bari a dakinsa tun xuwansa da safe, suna shiga parlon banda warin kartin maza babu abinda yake, ko ina soo dirty and unkept, ga saminu yayi bake bake kan 3 seater yana kallo ga plate din abinci da ya ajiye saman kujeran, Isiya na one sitter yana shan rake da yake tarawa nan kasa gefensa, Shafi'u kuma na 2 seater ga tasa plate din abincin ya gama ci ya bari saman kujera, Mai gadi ya nufi Saminu yayi kasa da murya yace "Saminu ko xaka ɗan sam masa waje ya dinga kwana a dakinka, ka gansa bashi da matsala wllh..." Ko rufe baki Mai gadi bai yi ba Saminu yayi saurin cewa "Aa nima dakin yayi min kadan" Mai gadi ya kalli Isiya dake jin abinda ya ke cewa, kafin mai gadin yace masa komai yace "Toh wai ba falo kace xai dinga kwana ba" Shafi'u yace "Shi dai na gani, Duka dakunan kaga ai babu waje, wa ke son takura" Khalil ya amshi jakarsa dake hannun mai gadi, mai gadi yace "Ko xa mu je can dakin nawa ka dinga kwana" Khalil yace "Aa kar ka damu, kayi komawar ka bakin gate" Yana fadin haka ya nufi space da aka tanadar domin dinning area a parlon, Kofar da ya gani ya bude ya ga kitchen ne, ya dinga kallon yanda suka mayar da kitchen din kamar na mahaukata duk da ba girki suke ba, tsintsiyar da ya gani wanda bai ga alamar ana amfani da shi ba ya dauka, ya hau share dinning area din, mai gadi ya juya ya fita daga parlon da sauri jin kamar ana horn. Cikin yan mintuna khalil ya gama gyara area din har da mopping, yana gamawa sai ga mai gadi ya kawo masa wani yakunannen zanin gado, amsa yayi ya shimfida a saman tiles din wajen, sannan ya bude window, ya shiga bandakin dake parlon, still yayi yana bin bathroom din da kallo, ko public toilet is far far better and neater than this, fita yayi ya koma gun mai gadi don ya amshi omo. Abba yayi shiru yana sauraron Mumy, Mumy ta ci gaba tace "Kawai ita Hajiya duk wani abu na cin mutunci da cin fuska shine dai dai a wajenta, ai wannan ba rayuwa me kyau bane, har take cewa ka sallamesa, da yayi me? Ruwa fa ta dauka gun me kayan marmari ta watsa masa a jiki, kawai dai ka haifi yaro baka haifi halinsa ba, haka ta sa Habibu a gaba daga baya ta gaji ta saukar da kanta, mai aikin gidan nan ba dadin Nihad take ji ba, Nihal kuma ba haka take ba, na rasa wannan baƙin hali irin na Nihad ni kam, ni dai ba haka taga nake mu'amala da jama'a ba balle tace, kai kanka ba haka mu'amalar ka da jama'a yake ba, to halin wa ta yo haka, idan ba shiga hakki ba wllh kar ka fara ce ma bawan Allahn nan komai, a kan me xata ce sai ya bata makullin motata ta tafi gantalinta da yamma sbda rashin kunya ma bata yi shakkar cewar motar tawa bace, kuma naga ai ba ita ta basa makullin ba ni na basa, to a kan me xai bata..." Abba dai yayi shiru bai ce komai ba, ganin ta gama fadin abinda xata fada yace "But that doesn't warrant u to slap her publicly Maryam, why not ki bari idan kuka dawo gida ki hukunta ta?" Mumy tace "Wato na goyi bayanta kenan Yallabai, ai yanda tayi rashin kirkinta a bainar jama'a gwara nima na hukuntata a cikin jama'ar dai dai kenan, ni fa i am not in support of walakanta d'an Adam Yallabai, kuma babu wani da ya fi wani a wajen Allah sai wanda yafi tsoronsa, idan ma xaka share xancen nan ka je ka huta to gwara ka share" Abba bai kuma cewa komai ba, Mumy tace "Can i excuse my self?" Yace "Alright" ta mike tayi masa sai da safe sannan ta fita, Umma ta fito daga bedroom din Abba don duk ta ji yanda suka yi da Mumy, tana ta6e baki tace "Yau ni naga neman suna kiri kiri gun talakawa, ita a neman sunan ma ta rasa inda xata dinga yi sai wajen talaka? Ai kamata yayi ta dinga kutsa kanta cikin manyan mutane ana yi da ita, ta nan ne neman suna xai mata rana, amma ke kice duk abinda talaka yayi dai dai ne, a dole sai kin burge?" Abba ya mike ya fita daga parlon, compound ya fito, dai dai nan khalil ya fito daga dakin mai gadi ya amshi omo, ganin Abba ya nufesa ya gaida shi da ladabi, Abba ya amsa yana kallonsa yace "Ibrahim, a dinga hakuri da yaran nan don Allah, sannan duk sanda Nihad ta sameka da batun amsan makullin mota kana da number ta ka kirani, idan wanda xaka bata ne sai ince ka bata, don ba wai bata iya driving ba, tana driving to where ever she wants to, just sbda security purpose ne bana barin suyi driving din da kansu, so kar kayi zaton bata iya driving din bane, and u gat respect them all kamar yanda xaka yi respecting dina ka ji" Khalil da kansa ke kasa a hankali yace "Toh in sha Allah Alhaji" Abba yace "Sun baka daki a can boys quarters din ko? Don nasan akwai empty room da Habibu ya bari" Khalil yace "Ehh an bani" Abba na kallon omon hannunsa yace "Wanki xaka yi da omo?" Yace "Eh xan wanke bandaki ne" Abba yace "Ohk good, wannan ai yayi kadan, no problem xa a kawo maka daga cikin gida yanxu" Yace "To nagode Alhaji" daga haka Abba ya juya ya koma cikin gida, khalil ya koma can boys quarters din. Abba na komawa part dinsa ya kalli Umma yace "Ki ba ko Sudais ne blanket with some detergents ya kai boys quarters" Umma tace "A kai ma wa a can?" Abba yace "Driver" Umma tace "Aa da dai kaje gun uwar dakinsa ta bada a kai masa, ni kam bani da old blanket, kaji Alhaji da wani xance, shine yace ka basa blanket din?" mikewa Abba yayi ya fita, ya tafi bangaren Mumy, tana daki ya sameta yace "Maryam blanket xaki ba Sudais with some detergents ya kai ma driver din can" Mumy tace "Sudais ai yayi bacci yallabai" Abba yace "To bani" Wani blanket dinta ta dauko, sannan ta dau pack din omo da sabulu with toothpaste ta hada ta ba Abba, Abba ya amsa ya fita dakin, a stairs ya hadu da Nihal xata dakinsu, tace "Abba where are u going with the blanket" Yace "Boys quarters xa a kai ma drivern can" Nihal tace "Ohk, bari in kai Abba" Abba yace "Good" Amsa tayi daga hannunsa don dama da Hijab a jikinta ta juya ta koma downstairs ta nufi kofar fita main parlor, boys quarters din ta nufa, tayi Knocking duk da kofar a bude take, isiya ne ya karaso ganinta ya gaisheta da ladabi xai amshi blanket din yace "Wanki ne Hajiya?" Tace "Aa, ina sabon driver yake?" Jin haka Khalil dake bandaki xai fara wankewa ya fito ya nufi kofar, kallonta ya dinga yi don da farko ya xata Nihad ce, amma sai yaga ba itan bace don wannan fuskarta bai rabo da murmushi, ya amshi abinda take mika masa, yace "Nagode sosai" Juyawa tayi ta sauka chalet din, ya koma cikin parlon yana kallonsu Isiya yace "Ku yi kokari ku bar barin kofar nan a bude sbda sauro" Da ido duk suka bi sa, lkci daya suka kya6e baki, ya ajiye blanket din ganin omo, sabulun wanki da na wanka sannan ga Toothpaste ya kwashe su gaba daya ya wuce bandakin, ya bata fiye da minti talatin yana wankin bandakin don sae da omon yayi rabi, lkci daya bandakin ya dawo hayyacinsa, wanka yyi ya fito, ya kulle bandakin da makulli sannan ya cire makullin ya koma dinning area, ya shimfida babban bargon wanda laushinsa ba a cewa komai, ya bude window dake wajen sannan ya kwanta ya rufe ido, bayan minti sha biyar yaji ana magana, ya bude ido ya ga Saminu tsaye a kansa, shiru yayi yana kallonsa, Saminu yace "Makullin bandaki da ka kulle xaka bada" Khalil yace "Ohk, dama kuna amfani da bandakin kenan?" Saminu yace "Yo me xai hana" Khalil yace "Ohk, shine ku ka bar shi yanda na samesa?" Bai jira Saminu yace komai ba, yace "Amma dai kamar babu bandaki a dakunan naku iya wannan kadai ne ko?" Saminu yace "Akwai mana, amma wannan din muke shiga gaba daya ai" Khalil ya ciro makullin da ya ajiye a aljihun gaban rigarsa ya mayar aljihun wando sannan ya gyara kwanciyarsa ya rufe ido, xuwa yanxu daga Isiya har Shafi'u na tsaye parlon suna kallonsa gaba daya, Saminu yace "Toh wai kai gayen nan me kake nufi tukunna ma dai" Mikewa Khalil yayi ya tsaya sai ga Saminu ɗan tsut a gabansa, Khalil na kallonsa da kyau ya tsaya dab da shi yace "Baxan bada ba nake nufi" Shafi'u ya koma ya xauna haka ma Isiya suna kikkifta ido, sui sui Saminu ya bar dinning area din shi ma yana gwaggwale ido.




07087865788✍🏻


💖💖 *NIHAAD* 💖💖




By _Khaleesat Haiydar_✍🏻






~~~~~~


Washegari Monday har karfe tara Nihad na ta kwance a dakinta, karfe tara da rabi aka bude kofar dakin, ta juya ganin Umma ce ta shigo ta mike xaune a hankali, Umma tace "Baxa ki makarantar bane Nihad, naga yau Monday" Nihad tace "Lectures din karfe goma ne, Nihal ta tafi islamiyya?" Umma tace "Tun yaushe, ke dai kam na san ba xa ki ba" Nihad bata ce komai ba, Umma ta juya ta fita, sauka tayi daga saman gadon ta shiga bandaki, nan ma sai da ta bata kusan minti arba'in sannan ta fito, shiryawa tayi cikin tsadadden bakar Abaya, wurin shirin ma ta 6ata kusan minti talatin, banda kamshi babu abinda ke tashi a ko ina na jikinta, sosai Abayar ta amshi farin fatarta kai kace balarabiya ce, ta dau karamin handbag ta sa flat shoe sannan ta fito daga dakin bata kulle ba don Hafsah xata shiga tayi mata gyaran dakin sannan ta wanke mata bandaki, tana tafiya kamar bata son tafiyar ta tafi part din Mumy ta bude kofar parlon, xaune ta ganta parlon tana waya, ta cire takalminta nan bakin kofa ta karasa ciki a hankali, ta xauna saman kujera fuskar nan nata babu yabo babu fallasa, har Mumy ta gama wayar sannan ta gaisheta, Mumy ta amsa mata ita ma a dakile without looking at her, mikewa tayi tace "Xan tafi makaranta" Mumy tace "Allah ya tsare" fita tayi daga parlon ta wuce part din Umma, Umma tace "Ashe dai za ki, toh Breakfast din fa?" Tace "Xan yi a makaranta" Umma tace "Toh Allah ya tsare" Kamar xata yi kuka tace "Umma ni gaskiya baxan iya shiga mota daya da wannan yaron ba" Umma tace "Toh yanxu ya xa ayi, idan na tafi na amsar maki makullin kin san anjima xa a dauko yara a makaranta" A hankali Nihad tace "Toh pls Umma zaki bani makullin motar ya Farooq" Umma ta rike ha6a tace "Farooq, to bari dai in dauko maki" cike da farin ciki Nihad tace "Yauwa Umma, karfe hudu xan dawo in sha Allah baxan wuce haka ba" Mikewa Umma tayi ta fita daga parlonta ta wuce dakin First son dinta, makullin dake jikin kofar ta murda sannan ta bude ta shiga ciki ta dauko makullin motarsa ta fito, farin ciki sosai Nihad tayi ta mashi makullin tana murmushi tace "Umma nagode" Umma tace "Toh ki tafi a hankali dai, kar ki kwarzane masa mota mu shiga uku" Nihad tace "A hankali xan tafi Umma" Daga haka tayi ma Umma sallama ta fita daga parlon cike da murna, ta fitowa compound taga mai gadi xaune tare da Khalil, lokaci daya ta wani murtuke fuska, ta nufi mai gadi tana juya makullin hannunta tace "Hey Bude min gate xan fita" Tashi yayi da sauri ya tafi xai bude gate din, ta nufi motar yayanta, ta gefen ido khalil ya bi ta da kallo, har ta shiga motar, bayan ta gama warming tayi zoom off out of the compound duk don ta tada k'uran interlock, Mai gadi ya daga mata hannu yace "Allah ya tsare Hajiya" ko kallonsa bata yi ba balle ta tanka, ta ja motar tayi gaba, kulle gate din yayi ya dawo yana kallon khalil yace "Hajiya ce xata bata motar Farooq da yake baya gari, kuma ina tabbatar maka uwarta bata sani ba, dama Umman ke daure mata tayi ta abinda ta ga dama a gidan nan ai, kai kam huta roro" Khalil yayi murmushi yace "Yanxu ina xata haka?" Mai gadi ya xauna yace "Wai Makaranta mana, kasan jami'arta shegen tsada ke garai" Khalil yace "Ita er uwarta fa?" Mai gadi yace "Baiwar Allah, ba daxu ka ajiyeta a islamiyya ba, hutun makaranta ta dawo, amma kaga kullum sai taje islamiyya abunta..." Khalil yace "Wacce makarantar take ita?" Mai gadi yace "Ba nace maka a Zaria take, Ahmadu Bello" Khalil bai kuma cewa komai ba. Nihad na driving tayi dialing number Husnah, Yana fara ringing Husnah ta daga, Nihad tace "Kin shiga school ne?" Husnah tace "Me yasa kika kashe wayarki jiya bayan munyi dake kina tahowa?" Nihad ta sauke ajiyar xuciya tace "It's a long story, but ya na ji muryarki haka, are you okay?" Husnah tace "Partially" Nihad tace "Where are u at now?" Husnah tace "Ni'ima guest palace" Nihad tace "Really? To bari in taho nan kawai, nima I'm not even in the mood of attending lectures today" Husnah tace "Sai kin xo" Katse wayar Nihad tayi ta dau hanyar Ni'ima guest palace din. Nihad na isa tayi parking ta kirata, nan Husnah ta sanar mata room number dinta, Nihad ta sauka motar ta shiga ciki, Knocking tayi kofar dakin, Naf ta bude, Nihad ta d'an buda ido ganin Husnah a kwance ta lulluba, ta kalli Naf tace "Is she okay?" Naf tace "Shigo in kulle kofa" Nihad ta shiga ta karasa gun Husnah, ta xauna gefen gadon tana kai hannu jikinta tace "Ya dai Husnah?" Husnah ta mike xaune tana ta6e baki tace "Ashe Yaks d'an iska ne duk bamu sani ba" Nihad ta ɗan bude ido tace "Me ya faru?" Husnah tace "Kawai yaje ya sha kwayoyinsa jiya in gaya maki yayi assaulting dina" Nihad ta xaro ido tace "Really?" Husnah tace "Wllh ke dai in gaya maki, ban da abunsa ai i wouldn't have denied him" Nihad tace "Where was Nafee then?" Husnah tace "Ita suna tare da saurayinta, kin san shi ma ya zo" Da mamaki Nihad tace "Yaks??" Husnah tace "Ai kuwa baki ga yanda ya dinga tambayarki ba, nace kina hanya duk ya damu baki iso ba, ke gwara ma da baki xo ba din, kilan rashin xuwanki ya sa haka ya faru," Nihad tayi shiru, can tace "Tabdi, kuma a Tahir guest palace din?" Husnah tace "Wane Tahir, ai ba a can muka yi birthday din ba, ke kinga haduwar birthday din nan kuwa Nihad?? Gaskiya na jima ban ga birthday da yayi haduwar na Maska ba, it was light" Nihad tace "Ni xancen yaks ne ya tsaya min a rai, Shi yasa fa kike ganin bana kula clique dinsu, bana harka da maza marasu aji" Husnah tayi dariya tace "Ni kawai way of approach dinsa ne ya kona min rai, amma what's there? norms ne ai, someone that i have been crushing on from day one" Nihad tace "To karfe nawa ku ka bar wajen?" Husnah tace "Kai dare yayi fa sosai, ke ni fa wllh gwara ma da Allah ya hanaki xuwa nace maki, don da ban san ya xan yi da ke ba a wajen ga uban daren da muka yi, cabb to wa ma xai saurareki, gaskiya birthday din nan yayi armashi, ai da naga daren yayi sosai shine na fasa komawa hostel kawai muka kama daki a nan ni da Surayya, ita Naf fa sai yau da safe ta xo nan ta same mu" Nihad ta kyabe baki ta ajiye handbag dinta tace "I am jet hungry banyi breakfast ba, me suke siyarwa a nan?" Husnah tace "Ke bamu dade da waya da Ayman ba xai taho mana da abinci yanxu, bari in kirasa ince plate uku xai kawo, shi ma jiya ya dawo daga Egypt" Daga haka Husnah ta kirasa ta sanar masa ya dado wani plate din, bayan ta ajiye wayar tana kallon Nihad tace "Amma jiyan me ya hanaki xuwa don Allah?" Nihad ta sauke wani ajiyar xuciya irin na takaici tace "Husnah in gaya maki wani sabon driver Abba ya dauka, kin san ai ya bude ma Habibu Shago" Husnah ta gwalo ido tace "Don Allah, kina nufin yanxu babu Habibu? Allah sarki, kai amma xaki yi kewan Habibu, sau da yawa fa da shi kike hada baki, gashi duk inda kika ce ya kai ki kai tsaye yake kai ki, har ma ya jira ki" Nihad ta marairaice tace "Ke dai bari, ai ni aka yi ma da Habibu ya bar driving, sau nawa yake kai ni Tahir ko Bristol or prince hotel, kuma ya jirani komin dadewar da xa mu yi, sau nawa xa mu fita in amshi mota a hannunsa shi ya tafi harkar gabansa nima inyi tafiyata, sai na gama xan kirasa mu hadu a busstop mu koma gida, Yawanci ba shi nake aika ya siyo min duk abinda nake bukata ba, ai har kuka sai da nayi da naji Abba ya bude masa shago, Habibu ai mutum ne" Husnah tace "Amma fa ya ci kudinki ba karya" Nihad tace "I wish Allah xai ta6a xuciyar Abba ya dawo mana da Habibu kawai" Husnah tace "Toh shi sabon da aka dauka fa?" Nihad ta gyara xama tace "Ai shi xan baki labari yanxu, wato wani tatattcen d'an iska, mara kunya Abba ya dauko mana as driver Husnah, kinsan jiya a kansa sai da Mumy ta mareni har sau biyu a titi cikin jama'a? Husnah as i am talking to u now i am boiling inside, tun shekaranjiya nake cikin ɓacin rai da bakin cikin mutumin nan, daga fara aiki shekaranjiya har ya raina ni baya girmama ni, ina masa magana sai yayi min banxa ko kuma ya kalle wanda ke kusa da shi irin dai kamar ba da shi nake ba da na kusa da shi nake, ko kuma ya kara min sheggun kunnuwansa gaba, irin dai na raini da tantiranci, Husnah yayi mugun raina ni wllh, yanxu maganar da nake maki motar ya Farooq Umma ta bani makulli na fito da shi, baxan juri xama a mota ni da shi yana driving dina ba...." Tuni har hawaye ya cika idonta, Husnah dake ta sauraronta da mugun mamaki ta gyara xama tace "What?? Shi ordinary driver din yake duk wannan abinda kika lissafo min kuma kika kyalesa? Ta yaya kika basa wannan fuskar ya rainaki daga fara aikinsa Nihad? Waye shi haka, kuma a ina Abba ya samo sa?? Wai ma garin yaya kika yi creating room for this bullshit" Nihad na shessheka tace "Baxa ki gane ba, wllh irin yan iskan nan ne yaron, cikin ruwan sanyi yake raininsa da rashin mutunci, idan kin gansa ma xa kiyi xaton baya magana nan ko katon ɗan iska ne, yanda fa kika san motarsa haka yake jin kansa daga fara aiki" Husnah ta rike ha6a tace "Tabdi... to kuwa xa mu yi maganinsa, but what did Abba say about it? Ko baki kai kararsa ba har yanxu?" Nihad tace "Babu wani action da Abba ya dauka tunda Mumy ta zuzzuga sa, har Umma ma ta saka baki amma Abba yaki daukan kwakkwaran action, the painful part of it is that Mumy supporting dinsa take kamar ta ta6a saninsa, kinsan yanda take abubuwanta dai, to wllh a kansa ta gaggaura min mari jiya a tsakiyar Hotoro dalilin da yasa na fasa xuwa Tahir palace kenan, to wannan ne har xan dinga basa kudi yana kai ni duk inda nake so ba tare da yayi casting dina ba wataran? Ina ai baxai yiwu ba, bana harka da fitsararrun yara ni...." Husnah tace "Calm down besty, shi karamin kwaro ne wllh, kuma xa mu yi maganinsa, Clique dinmu kadai mun ishesa" Naf dake ta sauraronsu ta kyabe baki tace "Lallai wnn ɗan iska ne number 1, daga wani kauyen aka samo maku shi halan? Shi a yan kauyen ma shege ne fa" Nihad tace "How will i even know, wlh d'an rainin wayo ne na karshe, gashi baya wani magana nake gaya maku, yanda kuka san kurma, cikin ruwan sanyi yake rashin mutunci da raini, ga wani ji da kai, to kana aiki karkashin mutane kana driving ina wani ji da kai??" Kwankwasa kofar aka yi, Husnah tace "Ayman is here..." Naf ta nufi kofar ta bude, wani matashi ya shigo dakin rike da takeaway uku with many drinks da bottle water, Ya ajiye ledan yana kallon Nihad yace "Manyan mata, ashe dai kina kasar nan Nihad?" Nihad tace "To an zuga Abbana ya ki kai ni UK karatu ba dole a gan ni a kasar ba" Dariya yayi yace "Gaskiya ne, to ya kwana da yawa, kinsan ku manya ne ba kowa ku ke replying ma chat ba both WhatsApp and IG" Nihad tace "Not at all" Husnah ta mike ta dauko takeaway daya ta ajiye ma Nihad, Ayman na kallon Husnah yace "I think bari in kama wani dakin kawai" Husnah tace "Ohk then" Daga haka ya fita daga dakin, Naf ta ja tsaki tace "Sai shegen girman kai, wato jira yake in fara masa magana ko" Husnah tace "Ke dai kowa sai kice yana da girman kai bayan kema kina fama da naki, duk fa Salman ne ya hura maki kunne ki daina kula kowa sai ki dinga fakewa da ana maki girman kai" Naf tace "Ni fita ma xan xo in yi yanxu, amma xan dawo later" Husnah tace "Ina xa ki? Baxa ki ci abincin ba?" Tace "Idan na dawo xan ci" Husnah tace "Kar fa ki ki dawowa Naf, saboda ke naki gayyato Zully nan fa" Naf tace "Ke wllh xan dawo, wani Alhaji ne ke ta damuna da kira ya shigo kano, to yayi min alkawarin waya dama, shine xan je" Husnah tace "Ahh, to maza ki je, Allah ya sa mu ga latest iphone" Naf ta dau figigin gyalenta tace "Toh Allah ya sa bari in je, Nihad idan na dawo xa mu tsara yanda xa ayi da ɗan kauyen can shi kuma" Nihad tace "Toh sai kin dawo" Daga haka Naf ta fita daga dakin, Husnah tace "Tabdi, yau ni naga karfin hali wai barawo da sallama, wannan idan yayi wata daya a gidan ai sai dai kuma ya koma rayuwa cikin main building ya bar boys quarters kawai" Nihad tace "Sai yanzu rashin barina in xauna a hostel da Mumy tayi ke kara damuna sosai, kinsan da na hakura amma tun da aka kawo wannan drivern damuwan ya dawo sabo" Husnah tace "To ko xaki kara gwada yi ma Abba magana?" Nihad tace "Babu yanda Umma bata yi da shi ba, amma da yake Mumy da ya farooq sun hure masa kunne ya ki amincewa, sae dae kawai yayi ta bani hakuri wai there is time for everything" Husnah tace "Gaskiya in har ba sallaman driver din nan aka yi ba xaki takura sosai, gashi Abba baxai baki mota ba ko" Nihad tace "Ba fa ruwan Abba, Mumy ce matsalar gidan nan sae yaya Farooq, amma ae Umma tayi kokarin ganin

9 Comments On NIHAAD
avatar
lawal-1

1 year ago

Reply

The book is not complete thank you

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to lawal-1

tuntubi wannan nambar 07087865788 don siyan complete na littafin

avatar
aishat-5

1 year ago

Reply

Gaskiya naji dadi book dinnan

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to aishat-5

Wow munji dadi da hakan

avatar
maryama-4

1 year ago

Reply

Is very fantastic Allah ya Kara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to maryama-4

Ameen

avatar
maryama-4

1 year ago

Reply

Allah ya Kara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to maryama-4

Ameen

avatar
maryam-3-9-1

6 months ago

Reply

This book is so interesting

Please Login or Register in order to submit comment